Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maka bansaniba! bansaniba!! Tunda ban sansuba,
Amma kuma bakajiba shine yaukuma kasake zuwako?
Toh" yakake San nayi maka saboda Allah iye?

Shikam Abdul-jabbar tunda wannan saurayin yafara magana yayi mutuwar tsaye, tareda zubamasa idanu tamkar yaga wata sabuwar halitta wace babil Adamuba domin kuwa bai fahinci abunda saurayin yake fadaba,

Y Y K ya katseshi dacewa toh" Malam ya isahaka nan munji mun kuma gode Karka dokemu, domin naga kiris yarage kado kemu saboda munzo gidanku Neman "Humaira KO?

To kasa ido kagani daga yau daga Rana irin ta yau bazamu kuma zuwa Neman "Humaira gidan kuba insha Allahu, ballan Tana kasamu damar fadamana maganar DA taimaka dadi kaji KO?.

Saurayin zai kumayin magana sai Y Y k Yace Jinan Malam don Allah kayi tafiyar NA nace munji kodole ne saika kasake maimai tawa iye?
Saurayi yatafi yana gunguni tareda cewa kada Allah yasa kujimana, kawai kunwani damun mutane dawata "Humaira Humaira sai kace wata yar gwal, ba "Humaira ba kodai Harawace kune kukasanta bamuba.

Abdul-jabbar yadawo DA dubanshi kanY Y K Wanda shima idonsa nakan Abdul-jabbar din,

D"akyar ya iyabude bakinsa Yace Nawa wai meke faruwa ne?
Saboda Ban fahimci abunda wannan guy din yakefadaba,

Y Y K Yace mushiga daga cikin mota zanfada maka abunda kefaruwa.
Baiyi musuba yabude mota daker ya'iyadaga kafafunsa yashiga saboda nauyin DA sukai masa,

Y Y K Yasanar dashi duk abunda yafaru harzuwan dayake tayi ancewa batanan, yaci gaba dacewa ninasan Tana nan tadai kifito wane kawai zuwan kashe danyi shine akace Wanda akacemun wai ai "Humaira suntashi,
NA" girgiza kwarai da gaske domin kuwa bantaba tunani cewa gidan dasuke ciki nahaya neba, sai a wannan Rana nayi iya bincikena don nagane inda suka koma amma Allah baisana ganeba,

Nayi tunanin nasanar dakai abunda kefaruwa.
To kuma sai natuna in harna nafada maka abunda kenan to kana iya shiga wani hali, domin kuwa nasan halinka sarai dasaka abu Cikin rai, don haka sai kawai nace Bari in barshi harka dawo sai musan abunyi.

T"urkashi babbar magana wai dansanda yaga gawar soja, tashin hankali Wanda ba'asamashi Rana,
To shine yafaru da Abdul-jabbar domin
kuwa jiyayi kansa yana sarawa gawani daci dayaji bakinsa yayi,
Y Y k yadafa kafadarsa yace Nawa I hope kafahimci abunda nafada kuwa?
Ya kallesa DA idanuwansa dasuka kada sukai jajir kamar anwatsa masa barkono,

Y"ace lallai nayi zurfi Cikin SON abunda narasa, saudayawa RAI yakan kwadaitu dawani BURI wanda yake ganin shine hanya daya TAK da rayuwa zata gudana Cikin kwanciyar hankali da NUTSUWA, amma sai Kaga Cikin Dan kankanin taki Mutum yarasa wannan abun to yaya kenan ZAIYI?

Y Y K Yace sai yayi hakuri yabarma Allah komai domin kuwa shike maganin kowani irin matsala a rayuwa,
Ya girgiza Kai Yace gaskiya ne yanzu shikenan narasa "Humaira maisanyina kenan? Yace a ah wayafa damaka cewa karasa ta?
Insha Allahu indai "Humaira rabon kace to zamusan inda suka koma, aishi bawa bayataba cire tsammani Daga Rahamar ubangiji,
Saboda haka nan abunda nakeso dakai yanzu shine ka kwantar DA hankalinka kacire komai a zuciyarka,

Don Allah kada kajama kanka wata cuta, dubi dai yanzu yanda kakoma sai kace Wanda ya shekara yana jinya, please kamai da komai ba komai ba kuma zamuci gabada binciken in da suka kuma dayardan Allah za muganta kajiko?
B"atare daya kalli Y Y K Yace muje kawai,
Yace ok yanzu LUFHAT PHARMACY mukanufa don kasayi maganin KO? Yace a ah gida zaka kaini,

Yace bangane gida zankai kaba to shi maganin kumafa? Yace nafasa siya, Cikin matsananci mamaki Yace a ah nifa banganeba kanabufi baza kasha maganin ba kenan? Yace eh haka Na kenufi,

Cikin bacin rai Y Y K Yace wai mai yasa kake yin hakane? Kana nufin zaka zauna daciwo ajikin ka? shin wai anfadamaka SO" haukane?
Ko kuma Kai kadai ne mutumin dayafara soyayya a duniya dazaka wani rikicewa mutane,
Toh" Bari kaji ingaya maka kafin Kai dubunka sunyi dabasu samu abunda suke soba sukai hakuri toh" ballantana Kai,

Tsaya nan ka kashe kanka abanza awofi "Tana can kilama tamanta dawani Abdul-jabbar, tasamu wani Kai kana nan kana tunanin banza DA wofi don hak!

Yadoka masa wani uban lhun daya sashi Yai shuru, yace Yusuf kakaini gida inzaka kaini idan kuma baza kakainiba to sai nafita maka daga mota,

Y Y K yaja tsaki mtsww tareda cewa a ah tsaya don Allah Malam kar kafasa mun dodon kunne , yaja motar suka tafi yana Dada cewa oho dai Kai kasani niba abunda ya dameni,

Y Y K baigama yin parking ba Abdul-jabbar, yabude Marfin motar yafita yamaida marfin dakarfi yarufe jikake gaffff!!!

Y Y K yabi bayansa DA kallo daker yakedaga kafafunsa Yana tafita yana hada hanya, yatabe baki tareda cewa Allah Yai maka sauki yaja motar shi Yai gaba.
Ta kofar baya yashiga daki batareda kowa yasan shigarsaba, yazube kangado jabar tamkar anzubar dakayan wanki, yadafe kansa sakamakon sarawar dayaji Yai masa,

Hakanan kuma yaji kirjinsa yana harbawa DA Sauri DA Sauri, yasa hannu da Sauri yadafe kirjin tareda cewa washhhhh. Saikuma yaga dakin yana juya masa A"hankali yarufe idosa daga nan kuma baisake sanin inda yakeba.

To adai-dai wannan lokacin ne kuma Humaira tadauki ruwa abokiti daniyar tayi wanka, shigarta bayike dawuya sai kaji kwachauuuu!!
Bokitin yakucche ruwan yazube,

gaba daya jikinta yadauki Rawa yayinda gabanta kedakan uku-uku ,
umma dake tsaye bakin fanfo tace Lafia meke faruwa?


๐Ÿ’žLUFHAT CE๐Ÿ’
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’NU
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’žN
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žSA
๐Ÿ’DA ๐Ÿ’ž
Page16-19๐Ÿ’
๐Ÿ’ž
๐Ÿ’DA
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žSA
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’žN
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’NU

NA

๐Ÿ’ MEENAT๐Ÿ’ž ๐Ÿ’žUMAR๐Ÿ’ FARUQ๐Ÿ’ž


Dedicated to my Family Allah yakara mana k'aunar juna Amin,

----------------------------------------
ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION


PEN: THE STRONGEST WEAPON
----------------------------------------



only exquisite and whizkid writers are opportune to be writers





โœ๐Ÿพ





T"ana tsaye jikinta sai rawa yake yayin da kirjita yaci gaba da bugawa,

umma ta leka bayin tana cewa lafia? Cikin rawar murya tace ruuh wanh !! yaah zu beeeee!!!
Umma ta tsura Mata ido saka makon ganin datai jikinta sairawa yakeyi, tace wai Humaira saunawa zanfada miki inzaki shiga bayi kidinga yin Add'du'a?

Da sauri tace umma wallahi inayi ko yanzuma nayi basan ya'akaiba kawai naji bokitin ya kubuche mun,
Tace toh" Allah yakwauta ni miko mun bokitin nazubo miki wani ruwan, ta dauko Tamika Mata har A"lokacin jikinta rawa yake, ta rintse ido tareda dafa kirjinta aranta take fadin innalillahi'wa'inna'ilaihir'raju'un,

Umma tace gashi tabode ido da Sauri tace toh" tareda karban ruwan, tana wanka tana maimaita Kalmar innalillahi acikin ranta,.

Umma tace toh"Abba "Humaira munga mota Allah yasa Albarka ya kuma kade tsautsayi da hasara, Yace to Amin kuma gobe insha zantafi Zaria yau yakamata natafi toh"amma naga yamma tayi, sannan kuma Malam Yace saidai nabari DA sassafe natafi, idan kuma nadawo mutafi yola akan maganar saukar daza'ayi domin kuwa Malam Yace dawuri zamu koma Chan yola din.
Tace yanzu duk agobe kakaje Zaria kuma kadawo katafi yola? Yace insha Allahu duk a gobe za'ayi ai Zaria kusane saidai ko yola, KO shima aiba'amota zamu tafiba jirgi zamushiga in Allah ya yarda, tace to Allah ya yardan mana ya kuma kaimu goben lafia to Amin, ya mike tsaye tareda cewa Bari na fita waje gurin Malam tace toh"

D"a Sauri tashiga dakin fitowarta daga kwanka kenan, don haka da Sauri DA Sauri tagama shiryawa tana kokarin saka hijab. Umma tace waishin wannan saurin duk nazuwa Ina ne? Ta kalle ta tareda cewa umma banace miki zanje gidan su HANAH da HALEEH bah,

Tace yanzu da yamman nan zakije gida jansu? Cikin sha'gwaba tace umma to aida gidan su Hanah dana Haleeh banisa, tace to Ai shikenan saikiyi sauriki dawo tunda kinsan bason fitar yamma nikeyiba, to umma Ai bazan dadeba yanzu zakiga nadawo natafi toh" kidawo lafia ki gaishe da Hajiya Hafsatu da Mariya toh" zasuji ungo kudi mota, umma inadashi, to karadai tace toh" nagode tafice tareda cewa sai nadawo adawo lafia Allah yasa,

A ah budurwar kauye sai Ina kuma? tace Allah Malam indai baka daina ce mun budurwar kauye ba to zance nafasa auran, Yace au toh"kice kinfasa kigani yarinya idan ban hau buzunaba, saikinzo kina cewa don Allah Malam ka aureni yafadi Cikin zolaya yana dariya, tace wah nicezan rokeka saika aureni? yace eh Saikin Rokeni, tace a haka zanrokeka Kai duk furfura sai kace narasa maisona?

Yace sosai ma kuwa yoh ke aibaki saniba ingaya miki irinmu masu furfura yan matan yanzu sukeso, saikiji suna cewa aini yan tsofaffun nan sun iya rukon aure Dan haka irinsu yansamu Na aura
Ta kyakyale da dariya tace Kayyah!

Amma duk budurwar data auri tsoho kamar ka gaskiya taci baya,
T"abdijam nikam ina budurwa kamarta bazan auri tsoho ba, tab wane Mutum aini nan dakagan ni saurayi gal aleda Zan aura ba tsohoba irinka Kai duk furfura,

Abba Yai gyarar murya da Sauri Humaira ta waiga Aikuwa sukai four eyes dashi , da gudu taruga hanyar kofar gida domin kuwa bata luradashi agurin ba Sam,

ya kwala Mata Kira Adda! Adda!! Adda!!!, tace na'am zonan, tazo tanarufe fuska da hijab saboda kunya Abba yaji a firarsu da Malam,
Malam yace yar,nemakai,

Abba Yace inazakije yanzu da yamma nan Cikin inda-inda tace um- umh dama- dama Malam yai dariya Yace zataje fadamusu kadawo, dariya Abba yayi shima Yace toh" shine za'aje yanzu DA yamma, why note dabaza abari har gobe ba? cikin shagwaba tace Abba please let me go I come back soon, Yace OK amma fakidawo dawuri, tace to tareda cewa Malam Dan tsoho bye saina dawo Yace Allah ya kiyaye tafice da sauri,

Malam Yai murmushi yace shakiyiya yau bazatayi karatun yamma ba kenan, Abba yace a ah waidama tanayin Karatu shine tafita unguwa da yamman nan?

Yace eh ta nayi, toh" barina kirata tadawo yamike da Sauri, Malam ya dakatar dashi tareda cewa a ah kyale ta kawai aibata wasa da karatu, Bari ka gani bayan sallah isha'i zakaga tazo tauka kasan yanzu hadda takeyi tana kokari sosai, saidai yau kam baza'agane kantaba tunda kadawo to sai tafadama wayannan kawayan Nata, wadan da kullun suna tare sai kace Aluf da Lam sannan hankalinta zai kanta,

Abba yakoma ya zauna Yai murmushi domin kuwa yaji dadin Abinda Malam yafada, tabbas yasani tanada kokari karatu tunbata Kai hakaba Yace to shikenan Malam tunda kace a kyaleta, sukaci gabada tattaunawa akan al'amuran duniya me cike da abun mamaki da al'ajabi.


A"kofar gidan su Hanah mai'adai-daita yasauketa bayan tabiyasa kudi, saita shiga cikin gidan tareda sallama Hajiya Hafsatu maihaifiyar Hanah ta amsa Mata dacewa maraba da Humaira tace yauwa sannu Hajiya inayini? Lafia qalau yasu "ummaki da "gwaggo Da "Malam? duk suna lafia sunce a gaisheki to madallah ina amsawa, yayanki" dai yana makaranta koh"? tace eh yana can toh Allah yabada sa'a
tace Amin,

Hajiya "Hanah tana nan kuwa? Tace ta nan Cikin hausama kisameta yanzuta tashi nan wurin, tace to tareda hayewa sama.

A hankali ta lallaba tarufe Mata ido, tafara laluben KO wane amma bata ganeba Can sai tajawo hijab dinta takai hancinta D"a Sauri tace Humeeh tasakar Mata ido suka fada kangado suna kyalkyala dariya Humaira tace yah akai kika ganeni? Tace kamshinki kawai naji naganeki,

Tazaro ido alamar mamaki hada wani kamshi nakeyi daban Wanda yasa'ake saurin ganeni dashi? Cikin zolaya Hanah tace. "eh mana" (kasan cewar sarar dasuke fadakenan in sukai magana) kinsan special dinki yariga ya bataki da kamshinsa me shiga rai takai karshan maganar dayin dariya,

Harara ta watsa mata tare da cewa banso iskanci zakifara KO? Cikin dariya kasa- kasa tace sorry me wasafa nake miki, Amma kinsan Allah bazancan wasa ba kamshinki yasa naganeki, tacigaba da cewa toh ya'akayine? Naganki da yamman nan kuma nasandai bamuda buki yau ko? Domin dai jiya munje munyi karatu balle ince ko school zamutafi, don haka yanzu Ina muka dosa kuma?

Tayi dariya tace gidan Doctor muka dosa Hanah tace kin Rama kenan KO? tace "eh mana" toh" ya kikaji? tace very cool don haka indai gidan "D" nane am ready to go oya tashi mutafi,

Humaira tace Toh" zakin mazallako wai da daga ciki rokon uban kwabo, inke kinshirya toh"mu bamu shiryaba yar gidan doctor, tace aini nayi zaton kunshirya ne danaji kince can muka dosa, toh" yar iska bamu shiryaba toh" wallahi gara kuyi kushirya inba hakaba kuma intafi nikadai , a haba dai kina iya Kai kanki kenan? Me zaihana tace eh nasanza ki'iya, yanzu kinsan me ne ne?

Tace sai kinfada, saka hijab mutafi gidan su Haleeh nazo muku D"a albishir maidadi, tace DA gaske? tace Allah kuwa toh" tashi mutafi tasaka hijab suka fice,

Haleeh tace yana ganku yanzu badai karatu zamuje bako? Hanah tace a ah kinga wacce tace inzo muzo gurinki waitazo mana da albishir mai dadi, tace ah Haba dai? Allah kuwa toh" feso mana muji man ta special tafada Tana Mata dariya Humaira tace nagane abun'naku iskanci ne to nafasa fadin albishir din,

Haleeh tace tuba mukeyi Addan "Abba A"utan "Umma beben "yah Himu ta Hanah DA Haleeh Dan fadamana kinji? Suka kyalkyale da D"ariya tareda cewa "eh mana" tace albishirinku? sukace goro fari kalkal,

Tace "Abba yadawo dazu wani irin ihu su kayi tareda rungumeta suna dariya, tace kadaku karyanifa kuyi ma umma ahasara, Hanah tace wayyo dadi jibi zamuyi Candy "Abba ya dawo yau kice zamu balle bishasha KO mai kikace? Haleeh tace kwarai kuwa da gaske tace kunsan abunda Abba Yace?

Sukace saikin fada, cewa yayi idan jarabawar mutayi kyau to America zaikaini nayi karatu Na me kyau acan. Suka kuma saika ihu sukace wow ammafa zakifasa taro gaskiya Humeeh kin hadu wallahi , Abba ya birgeki sosai tace nikuma tawani bangaran abunbai birgeniba,

Hanah tazaro ido alamar mamaki tace ke koh" saboda menene? tace saboda zanyi miss dinku dayawa fa kuma zamu koma yola dazama, dasauri suka hada baki sukace yoh meh?

tace yola , Cikin sanyin jiki sukace gaskiya zamuyi miss juna sosai amma kuma dasauki tunda akwai Waya mun dinga communicaty ,Halee tace saukinta kenan ma, tasake cewa kunsan Allah ni mamaki nake wai zamuyi candy Sainaga kamar munyi kanana ,Hanah tace me wallahi bamuyi kananaba gawasu nan basuko kaimuba sunayin candy,

Humeeh tace ah basai mugama karatunmu da sauri ba Haleeh tace eh kumafa hakane, sukaci gaba da tattaunawa akan yanda candy zaya kasance,

Humeeh tace kubari natafi gida Cikin zolaya tace Haleeh su O oh fatace muyi Sauri mukaita gidan doctor inba hakaba kuma she take herself to him"

Haleeh tace au hakane? Hanah tace eh dole naje gidan "D" dina kunsan inaji dashi sukace "eh mana" ta "D D" tareda tafawa tace ni kadaice bawata sukai dariya tareda mikewa suka raka Humeeh ta hau adai-daita sahu, sannan kowa tanufi gida tunda tsakanisu banisa.


๐Ÿ’ž๐Ÿ’LUFHAT CE๐Ÿ’ž๐Ÿ’
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’"NU
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’žN
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žSA
๐Ÿ’"DA ๐Ÿ’ž
page20-24๐Ÿ’
๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž"DA
๐Ÿ’๐Ÿ’SA
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’N
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž"NU


NA

๐Ÿ’žMEENAT๐Ÿ’ ๐Ÿ’UMAR๐Ÿ’ž FARUQ๐Ÿ’ž


This page belong to charming boy Muhammad Bangee's yola, Hey boy where are you? I have bee looking for you since kasan meh ?nayi miss shirmenka sosaifa ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œmissssSsss boyyyyyyy onceeeee againnnnn.



-----------------------------------------
ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION


PEN: THE STRONGEST WEAPON
-----------------------------------------



only exquisite and whizkid writers are opportune to be writers





โœ๐Ÿพ





Da misalin 6:00 pm na yamma suna zaune kallo suke suna kuma Dan taba fira kadan kadan, sai Baba Lami tace Hajiya wai shin maigidana yadawo kuwa? tace aibakidade tafita sai naji motsin shigarsa daki kodana leka haryayi bacci, nace to kila hada maganin bacci suka bashi to koshifa? aiyasamu yadan huta tunda kila achan basu samun lokacin bacci,


Baba Lami tace yoh inazasu samu lokacin bacci wanna aiki nasu kullum suna tsaye kamar hakori, Ai yanzu zasusamu damar hutawa da kyau tunda
aisungama KO?


Tace yoh inafa sukagama sundai samu Hutu nadan wani lokacin lallai kam aisuna kokari sosai Mama ta tabe baki tace aiyaga zaya'iyane shiyasa yadau karma kansa wannan Aiki yaro sai shegiyar kafiya, kodayake ai barewa bata gudu danta Yai Rarrafe ko? Baba Lami tace wannan magana haka take, toh" Ai shikenan Allah yakyau tai murmushi tace Hajiya kenan kedai kamar bakison wannan aiki na megidana, to kuma Ai naga aikin nasu yanada kyau sosai,
tace to Allah yabashi sa'a akan dukan abunda yasa gaba tace toh Ameen Addu'ar dayaka Mata kiringayi masa kenan A"matsayinki Na UWA, tace hmmm baba Lami kenan toh" ai kullum inayimasa toh" Allah ya amsa tace Ameen, hakanan suka cigaba dafira har'akakira sallah magrib suka tashi don suyi sallah.

Da misalin 10:30 pm 5nadare Suna Cikin kallo T.V atashar MBC 2 baba Lami hartafara hamma alamar tafara jin bacci, tace Hajiya maigidana baizo yadauki abincinsa bafa kodai saina Kai masane? gashi hartafara gyangyadi, Tace toh" nima bansan abinda yahana sa zuwa yaci abincinba, baba Lami tace kila duk gajiyarce tahanasa zuwa toh barina tashi nakai masa can dakin nasai,


Assalamu'alaikum maigidana? shuru maigidana shuru babu asma tace a ah maigidana yau wani irin bacci ne haka, shin wai kamayi sallah kuwa? ta kuma kiransa haryanzu shuru bai amsaba tace a ah wannan bacci Na lafia ne kuwa?

Saita ajiye abincin takoma Cikin gida tana cewa Hajiya wanga bacci DA maigidana yakeyi yau nalafiya ne kuwa? Ina ta tadashi bai tashi ba wanda dakakira sa saudaya yatashi amma yau nakirashi yafi akirga bai tashi ba,

Mama tace a toh" kirabu dashi mana idan yagaji DA baccin yatashi, tace a ah Hajiya wannan bacci bana akyalesa bane domin ni nagama kamar baya motsi fa,

Da sauri tace baya motsifa kikace? tace Allah Kuwa zomuje kigansa Cikin hanzari tamike jikinta haryana Rawa tanufi dakinsa,

Tace Kai! Kai!! kai!! harsau uku tunda dama bakiran sunan sa takeyiba, wani irin bacci kakeyi haka ne yau? ta bubbugasa akafa amma ko motsawa baiyiba tadafe kirji tare da cewa nashiga uku baya motsi kodai ya Mutu ne? I tama baba Lami duk tarikice tace a ah Hajiya bai mutu ba KO kikira abokinsa "yusufa yazo akaisa asibiti, amma kafin nan barina debo ruwa azuba masa KO suma yayi? dasauri taje tadauko ruwa mesanyi acikin fridge suka yayyafa masa,


Amma har alokacin kodan yatsansa bai motsaba, tace Hajiya kira "yusufa yazo akaisa asibiti da Sauri tace toh takoma Cikin gida tadauko wayarta jikinta sai rawa yakeyi, Da kyar tasamu Y Y K yana zaune yana kallon labarai saiyaji wayarsa tana ringing kodaya daga saiyaga Ashe Mamace,

Da Sauri yarage volume T.V ya amsa wayar Cikin ladabi haryana dukawa tamkar yana'agabanta,


Yai sallama tare da cewa sannu mama inayini? Da Sauri tace lafia qalau don Allah Kai maza kazo Dan"uwanka bayada lafia, Zumbur yamike tare Da cewa ya salam! mama gani nan zuwa yanzun nan,

Koda ya isa gidan yatarar dasu tsaye chirko -chirko baba Lami sai kuka takeyi, I takam mama karfihali kawai takeyi yayin da sai salati take tafamayi, aranta kuwa saifadi take Allah dai yasa bamutuwa yayiba,


Yana ganinsa yace lnnalillahi'wa'inna'ilaihir raju'u Allahumma'ajirni'fimusibati'wa'aKlifni'khairan minah,


Mama maiyasa meshi ne? tace toh wallahi bamusa niba, baikuma tsayawa dogon bincike ba kawai yasun gumesa yafece sukabi bayan sa yasashi mota yace mama kishiga mutafi tace a ah baiyajeba kutafi tare Da baba Lami kawai, yace shiga muje baba Lami tace toh bari nadauko hijab, da Sauri yashiga mota yatayar sukanufi asibiti,


Koda suka isa asibiti Da Sauri akateresu, suka nufi emergency room dashi,
Doctor I S G ne akansa yanata kokarin ceto Rayuwarsa, ankwashi awoyi kafin doctor yasamu yafar fado KO shima saida taimakon oxygen numfashin sa ketafiya dai dai
Doctor yazaro hand kacif daga Aljihun labcot dinsa yashare gumin daya tsatsufo agoshinsa,
Yaduba agogon hannun sa yaga karfe uku da rabi nadare ya girgiza Kai tare da kallon inda "Abdul-jabbar yake kwance lallai yadafe rabonda yaci karoda matsala irin ta "Abdul-jabbar.

Baba Lami tuntana kuka haryayi shuru bacci nemaya dauketa, shikam Y Y K bai'iya runtsawaba saboda baiga fitowar doctor ba,domin kuwa baisan awani hali amininsa yakeba.
Da Sauri doctor yafito yanufi office din,Cikin sauri Y Y K yabi bayan sa zuwa office, yace doctor wai meyasami Dan uwana ne? yace gaskiya Y Y K bazan boyema kaba datake yasan Y Y K din, Abokinka yakamu da ciwon zuciya ,
Zumbur ya mike tare da cewa ciwon zuciya kacefa? yace kwarai da gaske domin kuwa hartafara kumbura,

Sannan DA alama
abokin nan naka yabada taurin kai saboda yazo nan nafada masa abunda kedamusa harda magunguna masu kyau narubuta masa yasiya yasha before ciwon Yai worst Amma baiyiba, I don't know why?

Shikam Y Y K mutuwar tsaye yayi ahankali ya zauna meye abunyi yanzu?
Yace abinyi kenan mubari yadawo hayyacisa tukun Kaga sai'asan yaza'yi,


Yace some times "Abdul-jabbar yanada kafiya wallahi saida nacemasa muje asai maganin Amma yace shi Sam a ah,

Please doctor don girman Allah katai makenu yanda Allah ya taimake ka,wallahi shikadai ne agurin maihaifiyarsa, karkabari yarasa rayuwarsa don Allah kaji?


Doctor yace Y Y k ka kwantar da hankalisa insha Allahu zaisamu lafia,
Kasan cewa darayuwa D"amutuwa duk suna hannun Allah idan yazo saiya tashi idan kuma baiso hakaba toh" fabawanda ya'isa yatadashi kanaji ko?


Y Y k ya kada Kai alamar gamsuwa,
D"domin shikam duk ya rikice yaja Dogon numfashi yace toh" shikenan ubangiji yabasa lafia, yace to Ameen addu'ar daza aimasake nan.

Baba Lami baba Lami Y Y K yakira sunannta tai figigit tafara tare dacewa sannu yusufa ni har bacci yafada daukata,

Toh" ya jikin maigidan Nawa dasuki daiko? Eh dasuki saidai doctor yamasa alluran bacci, insha Allahu zai farko normal tace toh Allah ya bashi lafia, yace Ameen mutafi nakaiki gida kiyi sallah tunda naga asuba takusa,
tace asubafa kace nadabo ? Yace eh baba Lamin tunda Hudu darabi yanzu aikiga kuwa asuba takusa KO?

Tada gaKai Cikin tsananin mamaki yanzu har sukai asuba,

Sun iske mama tsuru tsuru domin kuwa tunda sukatafi bata rintsaba, tana tarokon Allah yabasa lafia,

Yai Mata bayayin komai saidai yabiye Mata abinda kedamusa gudun karta daga hankalita, tace to shikenan Allah yabar zumunci, katafi gida Kaga iyalinka shikuma ubangijit yabasa lafia Yace Ameen idan nayi sallah zuwa karfe shida sainakoma tace tace toh nagode kwarai DA gaske, bakomai mama aidani dashi duk dayane, toh ka gaishe dasu Jamila Yace zasuji yafice daga gidan,

WASHE GARI
D"amisalin 8:15 Am nasafe , Alh mahamud ne yafito Cikin shirinsa natafi ya Zaria,
Sungama magana da Malam kenan yana kokarin bude mota saiga Humaira dagudu tafito Cikin gida Cikin shirinta tsaf,

Malam ya kalleta yace su budurwar kauye sai'ina kuma DA sassafan nan haka? Tace Malam kadainafa nibanaso ,Yai dariya Yace a ah nikam bazan dainaba,

T"ace to shikenan Cikin sha'gwaba tace Abba nima zanije Zaria naga "yah Himu nadade bangasaba,

Malam Yai murmushi yace aukema Zaria kikeson kije,?
Tace eh kaima zakajene? Yace a ah kedai kisamu atafida ke,tace aidani Abba zaune KO? Cikin wasa Yace a ah ni bazanje dakeba,

Tafara bugakafa Cikin sha'gwaba tace don Allah Abba katafi Dani nayi miss "yah Himu sosai, yamakale kafada alamar a ah tace please Abba kaji?

Yace toh zagaya kishiga mota tace yauwa Abba Na thanks ta kalli Malam tayi dariya sannan tace Kaga Abba Na zaya tafidani kaiko baza'a tafida kaiba, yai dariya Yace basai nace afasa tafiyar dakeba tace Ai Abba Na bazaifasa tafiya Dani ba KO?

Yai murmushi batare Da Yace komai ba sukai sallama da Malam yaimusu fatan Allah yakiyaye hanya a dawo lafia kuma agaida masa da Abokinsan, Abba Yace zaiji insha Allahu yaja mota suka tafi.

๐Ÿ’ž๐Ÿ’LUFHAT Luv yours all FANS

Please Login or Register in order to submit comment