Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa Magajin family baya haihuba, Cikin lokaci kankani aka baza Neman A'isha tareda abinda ke Cikin ta, saida kome kama Da ita basu gani ba balle ita kanta toh" ballanta Na su saran ganin abinda ke Cikin ta,

Tun "ana saran ganin A'isha har "aka fidda rai, yayinda kwana ki suka tafi tareda satittika da watan'ni shekaru, sunja Sosai yayinda Hamman Soja yaci gabada gudarar Da "aikin sa, ganin shekaru sun tafi sunja amma har awannan lokaci, Hamman Soja da Aina'u shuru ba haihuwar, saboda haka nan sai su Baba gen suka yanke shawara cewa" Hamman Soja yasaki Aina'u sai ta "auri wani KO" ALLAH yasa tasamu rabonta, tunda shi bazai haihuwa duk dacewa basu debe tsammani ba daga RAHAMAR ungijiba "aikam Aina'u ta tuma kasa tace ita "abarta da mijinta zata zauna dashi "a haka, don haka sai "aka kyale ta, saidai Kuma hakan yabata daman yin abidan duk tagadama takeyi, sannan duk "abinda tace dashi Hamman Soja yake "aiki ,

itakam Hajiya idanu tasa musu yanzu tsakanin tada Hamman Soja sai gaisuwa, yayin kullum Addu'a takeyi ALLAH ya tsare A'isha aduk inda take tareda abinda ke jikinta, don tanaji ajikin ta cewa wannan cikin najikin Aisha Na halal ne yayinda shikuma
Hamman Soja take rokon ALLAH ya yaye masa "abinda keda mashi, domin tabbas kwai wani abun da'akai masa wanda yake damusa Amma KO" meyene "DA SANNU" Allah zaibaiya narai dashi,

Kwatsam Aina'u tace Hamman Soja ya ajiye aiki wai tunda yasamu kudi yafara business, aikam baiyi shawara dakowa ba ya ajiye aiki, yafa business, ranada Baba gen yaji yaimasa fada sosai Baba engr yace' ya kyale shi dama shi yace yanasan Soja toh Dan yanzu yace bayayi aiba dole,

Don haka sai yaci gabada da Business dinsa din sa, kwatsam, wata rana sai ya hadu dawata yarinya yar wani tsohon kwamishi Na ilimi Na nan Yola, sunanta Maryam yanu yansan ta DA aure itama haka, yafada mata baya haihuwa tace "eh zata aure sa haka saboda tana son shi,

"Aiko ba "adauki lokaci ba "akai bikin duk da rashin sanda Aina'u tanuna, wanda saida aka Kai ruwa Rana tukun na, watan Amarya Maryam biya da tarewa sai tafara rashin lafiya zazzabi sosai a lokacin tuni Hajiya tadaina aiki, don haka Hamman Soja ya dauki Maryam dakan shi yakata asibiti, bayan Doctor ya dubata tareda yan tambayoyi ya tabbatar musu da cewa Maryam tana dauke da Ciki Na wata daya da sari biyu,

Da sauri Hamman Soja yace Sam Maryam batada Ciki Doctor, ya kalleni shi yace haba yallabai kamar yabata daciki?... nifa nadu bata, Kuma kaganni Na Kai kusan shekaru goma sha biyar Ina aikin balle kace KO" ban iyaba ne

itakam Maryam hankalin ta yatashi, yayinda Hamman Soja ya kurawa Doctor idanu tabbas baza taba mantawa da wanannan fuskaba, yace eh haka ne "ainata bazuwa gurin ka shekarun baya dasuka wuce, kadubani' Ka kuma tabbatar Mani dacewa bazan Baba haihuwa ba, ka Kuma hadani da wasu Doctors suka dubani suma Kuma sunka tabbatar Mani dacewa bazan haihuwa, toh yanzu kuma ya'akai matata tasamu ciki?...,

Wani irin faduwa gaban Doctor yayi yayinda yaji zufana karyo masa "ahankali yace?...



๐Ÿ’Lufha ce๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page141-145

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)


----------------------------------------
*ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION*

*PEN:THE STRONGEST WEAPON*
----------------------------------------

_only exquisite and whizkid writers are opportune to be pen_


โœ๐Ÿพ


Lokacin danayi wani zazzabi tareda wani irin ciwon ciki mai tsanani, ga kuma jini yana tazuba mani saina shirya natafi asibiti saboda naga Likita,

don "atunani Na ciki nasamu yake rawa, don haka saidai kashhh Ashe ba haka bane, bayan likita yadubani don harda sikainin yace' najena yi bayan nakwo masa takardan sikaini din,

Sai yace Mani banida ciki "asalima mahaifata talalaci tayi guntu-guntu bazata iya daukar daba, saka makon sham magunguna barka tai dankeyi,

Yanzu haka masai yayi Mani aiki yacire domin batada amfani, "idan ba "acire ta ba toh" zantayin zubar jini ne, hankali Na yatashi sosai sai nace masa toh" zanje nayi shawara da mijina zandawo yace Mani toh", nikuma atunani Na bazan dawoba,

Sai abun mamaki tundaga wannan lokacin jini yake tazubo mani sosai, dole muka tafi nida gwaggo don "acire Mani mahaifa, tunda duk abinda yake faruwa ba wanda yasani dagani sai ita, Kuma "a lokacin Hamman Magaji yana can gurin aiki sa, don haka mukai tayin komai batareda yasani ba,

Bayan Doctor yacire mani mahaifa yace Mani shikenan banza taba haihuwa ba, muka dawo gida toh" tundaga ran muka fara shirya yadda zamuyi, tunda "a lokacin ansaka ranan auren Hamman Magaji da A'isha, bamu samu mafitaba saida "ana gobe sauri aure.

Sai muka shirya muka tafi Wani kauye, mukaje gurin wani mugun boka bayan mun fada masa, bukatar mu, yace karmu damu dai mubiya kudin aiki, basai anbarta da Lafiya sannan zata samu Cikin ta haihuba.

Toh shine ran da'aka kaita akuma dawo Da ita ba Lafiya, Wanda tadauki tsawon lokacin tana fama darashin Lafiya, bayan taji sauki ta tare saina fara tunanin yadda Zan hanata samun Cikin, nadauki alwashin cewa tunda bazan haihuba toh" itama bazan taba Bari tahaihuba,

Nayi ta tunani yadda zansamu mafita amma ban samu ba, watan "A'isha biyu da tareda sai nafahimci cewa tasamu ciki, saboda haka shine nai amfani da lokacin da Hamman Magaji yai hatsari, sai nacewa Hamman Magaji yakamata yaje yafara ganin Doctor saboda matsalan rashin haihuwar,

Wani abin mamaki shine baiyi mani musuba, sai yace mani toh" yauwa zayaje amma saita fara biyawa tagida tukun Na sannan yaje asibiti, yana fita, sai nikuma nashirya nadauki bindigar Hamman Magaji naje guri Doctor nace masa baya idan yazo tafada masa cewa bazaya taba haihuwa ba,

Toh Kuma bayan nayi nasara yakori A'isha, na kuma jegurin boka nace yayimata asirin da bazata dawo ba, sannan Kuma muka ce mashi muna San yaima Hamman Magaji asirin dazamu mallakesa,

Bayan yayi mani aiki sai yace toh" saidai muddun muka Bari Hamman Magaji, yai aure har yayi tarayya da matar har tasamu ciki, toh" daganan asirin zaya karye, mukace' ba matsala mu'a tunanin mu tunda baya haihuwa aiba zaya taba yin aure ba,

Kwatsam sai naji Hamman Magaji zaiyi aure, naso nahana amma hankan baiyu ba, tun bayan DA Maryam ta tare Saina fara tunanin, yadda Zan hanata samun ciki, Ashe bansani ba tuni tasamu ciki.

Wannan shine abinda na'aikata don Allah Baba engr kuyi hakuri, kace kar Hamman Magaji yasakeni' son shine yasa na'aikata haka saboda bana San wata ta haihu dashi yazo yana fifitata akaina, takarshe maganar tada sheshshekar kuka.

Hamman Soja ya harareta tareda cewa karya ki ke' munafuka bakya sona, asalima kedin makiyiya tace Kuma Saki "ainariga nayi shi, (kasan cewa lokackn dayai sakin batasani ba)saboda ni bazan Kara zama da azzaluma macuciya irin ki ba,

yayinda falon yakaure da surutu yan'iwa sai Allah wadai da halin irin ta sukeyi, dama dayansu sunajin haushin ta tunda kirikiri saita hana Hamman Magaji yai musu Alkhairi,
Baba general da Hajiya Binta kam Kala basuce ba,

Baba engr ne yace ya isa haka
Cikin bacin rai yafara fada sosai, yace nasan duk abinda Aina'u takeyi dasa hannun ki, Rakiya Kuma baki kyautawa kanki ba "ace yarki zakisa "amugun hanya da za'a cuci Dan dan'uwanki, tareda baiwar Allah "A'isha mai tayi muku haka dakuka rabata da mijinta, kunata kulla mugun aiki bawanda yasani toh" aigashi nan dayake batada Hakkiku "DA SANNU" Allah ya bayyana Ku,

Cikin bacin rai Baba general yace aidama duk abinda Mutum yake aikata wa aboye sharri ko hairan toh" fa DA SANN wata rana Allah zaya baiyya nashi mutane kowa yaganshi, ALLAH ya shirya Ku, sannan yatashi bar falon.

Baba engr yabi bayan shida kallo tabbas yasan ran dan'uwansa ya baci, ahankali itama Hajiya tabi bayan mijinta,

Sai falon yaitsit, shima Baba engr ransa yabaci sosai, sai yadubi gwaggo Rakiya data dukar dakai kasa, yace Rakiya ki dauki Aina'u kutafin gida domin Magaji yariga yasake ta Saki biyu,

zatayi magana yace banasan jinkomai, kawai kidauke ta kutafi duk shawarar damuka yanke zanfada maki, yace ku kuma kowa wacce ta tashi tatafi gida saboda haka sai ko" yatafi gida,

*************
Saida Aina'u ta kai wata viyar sannan takoma gidan Hamman Magaji, koshi saida Baba engr yanuna mashi bacin rai tukun, Amma dayace shi Sam bazaya baida "ita ba,

Kulawa sosai Hamman Soja yakeba Maryam, har Cikin ta ya'isa haihuwa ta haifi diya Mace, ranan suna taci suna Hajiya Saratu matar Baba engr, fadin shagalin da'akayi ranan suna ban baki ne saidai mai karatu yasani shagali 'akayi bana wasa ba,

A haka yaci gabada kulada Maryam da AMA haka suke kiran ta, tare Kuma da son A'isha Wanda yakasa boyeshi "agaban kowa nuna begenta yake, Wanda har hakan yafara damun Maryam, musamman dataga duk yabi falon su yaman'na photo A'isha saboda haka sai tafara nuna kishi,

Yayinda shi kuma tuni yaja mata burki dacewa tabari, baiyi matar dazata fi A'isha azuciyar shi ba, tasani cewa Aina'u hadasu akayi A'isha kuwa itace macen daya fara so", saboda haka "amatsayin tada ban'ne "a zuciyar shi,

Saboda haka idan har tana son farin Cikin sa toh" taso A'isha, batada yadda zatayi don haka dole tabi "abinda yace' amma kasan zuciyar ta tanajin haushi A'isha,

Amah nada shekara daya Maryam tasake haihuwar diya Mace, akasa mata A'isha Wanda Hajiya ce tace asa mata A'ishan ta, "aikam Hamman Magaji kamar yayi hauka don farinciki, yayinda yadauki so yadora akan Little esha wacce yake kirada Honey, itama shekarar tadaya Maryam tasake haihuwar diya Mace, sai "akasa mata Fatima wato sunan Hajiya kenan sai suna kiranta Zarah mama

Toh" Kuma tundaga kan Zarah mama Hajiya Maryam bata sake haihuwa ba, saboda haka sai suka cigaba da kulada yaransu, tareda yi musu tarbiyya mai kyau,

Aina'u kam da'ita da banza agidan Hamman Magaji duk daya, kilama har gara banza yafita daraja, domin kuwa kwata-kwata yafita harkarta baya shiga sha'anin ta,

bakin ciki ya isheta don haka sai ta iske shi daki tace itaka tagaji da'bakin cikin dayake mata saboda haka ya
bata takardan Saki,
ba musu ya rubuta Saki daya yabata,
yace gashi nan rabuwarki Dani shine Abu mafi sauki garayuwai ki.


shukaru sunja arziki ya bunkasa ga Hamman Magaji, yayinda kaunar A'isha ke karuwa "azuciyar shi saboda haka ya dukufa Addu'a Allah ya baiyyana A'isha tareda abinda tahaifa.

********"******
Kamar wasa,Abokan Hamman Magaji sukace yafito "takarar gwamna, aikam yafito, da lokacin zabe yayi Cikin sa'a yalashe zabe "inda yahaye kujerar gwamnan jahar Adamawa yola, yayinda yazama gwamna mai adalci wannan kenan.

A hankali ya sauke ajiyar zuciya tareda bude idanun shi ya zubawa Alh Mahamud, yace?....




๐Ÿ’Lufhat Ce ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page136-140

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)

edited by Zainuddeen zain

----------------------------------------
*ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION*

*PEN:THE STRONGEST WEAPON*
----------------------------------------

_only exquisite and whizkid writers are opportune to be pe writers_




โœ๐Ÿพ


"eh tabbas "anyi haka shekarun baya dasuka wuce nafada maka, saidai kasani' nima bada San raina na rubuta maka, cewa bazaka taba haihuwa ba, tilasta Mani "akayi, da sauri Hamman Soja yace ban fahimce kaba waye ya tilasta maka ka' rubuta Mani bazan taba haihuwa ba?... yafadi haka yayinda yakejin wani irin matsananci faduwar gaba,

Doctor yace shekurun baya dasuka wuce, "Ina zaune "a office din Na sai ga wata tashigo bako sallama, saidai kawai tanuna Mani bindiga, mamaki yakamani tareda tsoro Cikin karfin hali nace baiwar Allah Lafiya?...

tace Lafiya lau "aiki takeso nayi "mata "idan kuma bazanyi ba, toh" zata kasheni tafita batareda kowa yasani ba, Dan yanzu ma ba wanda yaga sanda tashigo,

"Idan Kuma kana ganin, bazan iya kashe' kaba toh" "aizan "iya kulla maka sharrin da Harka mutu bazaka manta dashiba,

Tabbas zata iya "aikata abinda tafada domin naga fuskarta" ba "imani, don haka Cikin faduwar gaba nace wani irin Aiki kenan fa?...

Sai tace Mani wani mutun" zayazo nadu bashi,' "idan nadu bashi nafada masa cewa bazaya taba haihuwa ba, sannan Kuma nayi masa" hayyar zuwa gurin wasu "Doctor's din "idan yaje "suma sufada masa cewa bazaya taba haihuwa ba,

Banida yadda zanyi don haka sai nace mata toh" sannan tafita tareda cewa sai nado, batafi minti talatin da fitaba sai gaka kashe go,

Don Allah Kayi' hakuri wallah koda nadubaka, lafiyar ka kalau ba abida yasame ka, saidai narasa abida yasa wannan matar tace nafada maka haka kagafarc.....Hamman Soja ne yakatse shi ta hanyar daga masa hannun,

gaba daya jikin sa rawayake yayinda yakejin kafafunshi kamar baza su'iya daukar saba, don haka sai yadafa table din Doctor tareda dukar da kashi kasa, domin kuwa wani irin nauyi yaji yai masa,Wanda tunda yake bai tabajin nauyi irin wannan ba,

Cikin tashin hankali yadaga Kai ya watsawa ma Doctor jajayan idanun sa, yace kana nufin "a wannan lokaci duk macen danayi tarayya da ita zata iya samun ciki?...., Doctor yace sosa kuwa tunda lafiyar ka kalau, saidai idan itace batada Lafiya,

Wani irin Kara Hamman Soja yayi tareda faduwa kasa Sumamme, ihu Maryam tayi Cikin matsananci tashin hankali, taduka tana jijjiga shi tana kiran sunan shi Amma baitashi ba, hannun ta Dora akai ta tace Na shiga uku shikenan Doctor ka kashe Mani mijina,

Doctor da shima jikinsa rawa yake da sauri, yazo ya taba Hamman Soja yaji bai mutuba sumadai yayi, yace kiyi hakuri ba mutuwa yayi ba sumace Ina zuwa ruwa ya dauko, yayyafa mashi, can saiya farfado da sauri ya mike tareda rike kwalar rigan Doctor, Cikin tashi hakali yace yasunan matar?...

Cikin matsananci tsoro yace bansan suna ta ba, Amma dai bazan taba matawa Da kaman'nin ta, Farace tanada kina ba sann... Hamman Soja ne yakatse shi da cewa nagode kasan cewar yagane wadda yake nufi, sannan yakama hannun Maryam wacce keta faman kuka suka fita da sauri daga office din.


Tun bayan fitar Hamman Soja DA Maryam, hankali Aina'u yatashi don haka saita kasa zaune takasa tsaye, sai faman safa DA marwa takeyi "atsakiyar falo, sai tunanin take tareda tambayar kanta "Ina Hamman Soja sukaje shida Maryam,
Kasan cewar tana bacci suka tafi,

tana Cikin wannan halin sai kawai taji sallama Maryam, dauri tajuya tana kallon su gabanta ne yafadi saka makon gani Hamman Soja, yanufe ta fuskashi ba'an'nuri don haka da sauri tajuya zata nufi daki,yayinda Hamman Soja yafinciko tada karfi ya yarda ita kasa timmm sai kace kayan wanki sannan yajata kiiiii yanufi dakinshi da ita,

wata irin katuwar bulala yadauko irin tasuce ta SOJOJi, aikam tuni idanun Aina'u suka fito waje saboda tsoro zatai magana kenan, saitaji saukar bulala dukan ta yake DA iyakacin karfi sa' "itako sai ihu takeyi tana fadin menayi maka?....Magaji, yana dukanta yana fadin "au tambaya ta kike abinda kikai Mani ko?....Hmmm "DA SANNU" idan jikinki yaci duka Zaki ba kanki amsar tambayar ki',

Maryam kam tana tsaye abakin kofar dakin sai kuka takeyi, takasa shiga kasan cewar itakam tana bala'in tsoron bulala, Amma dai sai faman bashi hakuri takeyi, cikin tsoro tace Ahmed kar kayi kisan Kai fa! yace Maryam "aiyau rai kadan zan ragewa yar iska, "idan Kuma nayi Na sarar rabata daran' nata toh" shikenan ta huna, nima nahuta domin idan muka cigaba da rayuwa tare toh" tabbas zan dauwama Cikin bakin Cikin abinda ta'aikata Mani yayinda, ita Kuma zata gwanmaci gara muguwar ta da bakin cikin dazan guma mata arayuwa, duk wannan maganar yanayin tane ya dukan Aina'u wadda tuni tagala baita, jikinta kuwa duk yafarfashe abu ga farar mace harjini nafita,

Itakam Maryam tuni takara tsorata ganin jini yafita ajikin Aina'u, hakan ne yasa take ganin da gaske Hamman Soja kisan Kai zayayi,

don haka da sauri taje takira layin gidan Baba engr ciki sa'a shida kansa' Baba engr yada wayar, aikam tana kuka tana fada masa abinda kefaruwa, Cikin tashin hankali yace toh" gashi nan zuwa shida Hajiya Saratu matar shi,

Cikin abinda baifi miti talatin ba suka iso gidan, dai-dai lokacin da Hamman Soja yace nasake ki Saki daya Aina'u Nasake ki Saki biyu nas.... DA sauri Baba engr yace Kul! kana karasa fada sainayi mummunan Saba maka, ashe bakada hankali Magaji?.....,

Da sauri yasaki bulalan yaje yafada jikin Baba engr yasaki wani irin kuka maiban tausayi, kuka yakeyi sai kace karamin yaro "ahankali Baba engr ya zauna dashi, yayinda yake Shafa masa baya yana cewa ya'isa haka.

Yace haba Magaji "idan rai yabaci "aibai kamata hankali ya gushe ba, kanasan kayi kisan kaine?.... sannan ya kalli Hajiya Saratu yace dake DA Maryam ku kama Aina'u kuje mukai ta asibiti, tace toh" dakyar suka iyafita da ita saboda nauyi tunda KO" motsi batayi,

Sanna ya dubi Hamman Soja yace Magaji meya faru ne haka?...Cikin kuka yace Baba Aina'u ta cuce rayuwa ta' ta ha'inceni taraba nida matata A'isha, don haka ni ba'abunda zance mata saidai Na bartada ALLAH "DA SANNU" kuma zata gane kurenta, Baba engr yace fada mun abinda tayi maka?....

Nan yafada mashi abinda Doctor yafada masu, rai Baba engr sosai yace tashi mutafi bamu Hamman Soja tashi suka fita,

A can asibiti Kuma da taimakon ALLAH dana likitoci Aina'u tafarar fado, yayinda Maryam taci gabada kula da ita harta jisauki Wanda bada San rain Hamman Soja haken tafaru ba, saidan tirsasawar da Baba engr yai mashi.

Gaba daya family an'hadu gidan Baba gen, Baba engr yadubi Aina'u yace Aina'u menene dalilin daya sakika ce sai Doctor ya rubuta wa Magaji cewa bazaya taba haihuwa?...
Cikin kukan nadama tace.?..




๐Ÿ’Lufhat ce๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page146-150

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)



----------------------------------------
*_ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN:THE STRONGEST WEAPON_*
----------------------------------------

~Don Allah kuyi hakuri narashin ganin posting Dina akan lokaci~


_*only exquisite and whizkid writers are opportune to be pe writers*_ .




โœ๐Ÿพ



Mahamud "Ina son ganin A'isha tareda "abinda tahaifa narokesu" gafara saboda, nasan nine silar shigan su duk wani kunci dasuka fuskanta arayuwa, saidai kashhh! ban San "inda zangansu" ba, don ALLAH katayani Addu'a Allah ya bayyana su "a duk "inda suke Afadin duniya nan, wlh Mahamud "Ina matukar bukatar su" kusada ni.

A" hankali yece Hamman Soja ka kwantar DA hankalin Ka, insha'Allahu " DA SANNU " ALLAH zaya baiyyanar dasu," kullum Addu'ar Dana keyi kenan Kuma inajin "Ajikina da yarda Allah sun kusa baiyana garemu.

Yace Hmmm! Mahamud na tabka babban kuskure "Arayuwata Wanda gashin nan har yanzu "Ina Da nasani yisa, Mahamud meyasa ban saurari A'isha ba lokacin da take fadin Hamman Soja ka saurareni ba?..., meyasa bankasan ce Cikin mutane masu _"BINCIKE"_?.... ba, farin Cikina guda "idan Na tuna cewa ban furta kalmar _SAKI"_ga A'isha ba,

Yace Hmmm! Mahamud kokasan cewa duk abinda yafaru dasa hannun Aina'u, Dasauri Abba Yace kamar ya?...nan yafada masa abinda yafaru, Cikin takaici
Abba yace "aikanta tayiwa,

"A hakali ya sauke Ajiyar zuciya tareda Mikewa yazo kusada Shi, kafadar shi yadafa yace Kayi hakuri Mahamud nine Silar rabaka Da yar'uwarka, Wanda ta dalilin haka ne yasa katafi kabarmu tsawon shekaru, baka dawoba sai yau daka zama babban Mutum,
Yafada yana murmushi,

Shima Murmushi yai yace Kai Hamman Soja, yace Allah you're a big Man nasan dai by now kanada iyali KO?...,
Yace eh inada Mata daya Asma'u" da yara biyu Baba na "Ibrahim da "Adda A'isha Yace masha'allah naji dadi da kasa A'isha Allah ya Albarkacesu"
Yace Ameen.

Toh yanzu kabani Labarin bayan rabuwa, murmushi yai yace "ai lokacin dana barnan Kaduna natafi, nan dai yabashi labari "abubuwa dasuka faru dashi,"agarin Kaduna da masu" dadi da marasa dadi,

Nan dai Hamman Magaji ya jajanta mashi marasa dadi, yayinda yai mashi farin Ciki ga masu dadi, yace toh" yanzu "Ina iyalin Ka suna can Kaduna nan ne?...,yace "a ah tareda su nazo saidai shi Baba Na "lbrahim yana can Abu Zaria yace ita Kuma A'isha tagama Secondary school din ta, yace madallah Ashe dai yaran Nawa Sungirma?.. Murmushi yai yace bafa wani babba bane saurin girma ne kawai _he just nineteen years go to twenty_ ita kuma A'isha _yanzu tashiga fiftieth years_ kasan yaran yanzu saikace "Ana zuba masu taki saboda saurin girma, Murmushi yai yace haka fa yanzu fa "Amah itama _fifteen years_ My "Esha Honey _fouteen_ itakuma "Zarah Mama _thiree teen_ kasan cewar basu dawani tseyarya tsakanin su" sosai, toh" kajiba toh" Allah dai yaraya manasu" yace toh Ameen , toh" yanzu "Ina su "A'isha da "Mamanta kace tare Ku kazo KO"?....,

"Eh "ai gidana yana nan "a Karewa GRA watan'mu daya kenan da tarewa agidan, da sauri Yace _one month_kana garin nan Amma bakaje family House ba haba Mahamud toh' kana "Ina?...., yace "aikamar yau muka tare toh" Kuma washe gari sai natafi America kasan cewar Ina gudanar da Business "acan toh" shine fa sai jiya nadawo, yace "OK

" Ashe muna tare kenan, kasan nimafa Business din nakeyi, shine fa su ALH NASIR JIMETA(abokinsa ne) sukasa nafito takarar gwamna, toh sai gashi kuma Cikin lkon ALLAH nazama Governor of Adamawa state, Abunfa
very Surpersi wai l'm a Governor Hmmm l can't believe saida nagan'ni a office din nan sannan fa nayarda.

yace Masha'allah A"iba "a Mamaki Da hukunci UBANGIJI kasan Mulki nashine kuma sai wanda yagadama yake ba, Addu'armu dai shine Allah yatayaka riko ya Kuma baka lkon" yimana Adalci, yace Ameen, yakai karshen maganar dayin dariya, shima dariyar yace toh" Ameen,

Sannan Ciki Zoyala yace' yanzu tashi mutafi family House, Ka karbi bulala gurin Baba general da Hajiya Kai harda Baba engr, shima sai yatsala maka nashi bulalan saboda tafiya dakayi kabar su', tsawon shekaru kaga daka can sai mutafi gidana kaga iyalina,

Dai-dai lokacin da suka fita office din Hannun su rike da juna suna dariya.

**********
Wani Kyakkyawan Dattijo nagani zaune "Akan lallausan kushin, yana karanta Jarinda idanusa man'ne Da _medicate glass_ Baba general kenan dottijon kirki managarci mai cikar kamala, Sallaman da'akayine yasa shi dagoda Kai,
tareda amsa sallama Cikin Matsananci Mamaki Yace Mahamud Kai ne?....Yace nine Baba.

Dai-dai lokacin da naga wata kyakkyawar Dattijiyar tana saukowa daga _steps_Hajiya Binta kenan, yayi danaji tana fadin "a ah wanake gani haka kamar Mahamud ?....,

"A dai-dai lokacin Da ta zauna, sukuma suka zauna "akasan kafet,
Tace general shin gizon da idanuna suka sabayi munne, kodai da gaske ne Mahamud Din'mu ne yau "agabana ?...
Murmushi Baba general yayi Yace Doctor tabbas Mahamud din'mu ne, sai kawai tafashe da kuka tace ashe zan sake ganinka Haba Mahamud me yasa kayi mana haka?...,
"Ahankali yamatso kusada ita cikin matsananci tausayita, yayinda yaji wani irin haushin kashi yaka mashi waima meyasa yatafi ya barsu?...,

Sai shima yafara kukan yana cewa kuyi hakuri Hajiya
nasan ban kyauta ba, amma insha'Allahu bazan sake ba kinji?...Baba General yace "a ah Doctor farinciki zakiyi kin gansa "araye Kuma Lafiya lau, Amma bawai kixauna kina Kuka ba, "Ahankali tasa hannu tashare hawaye shima yashare nashi,

Bayansu nutsu sai Kuma "a kafara gaisuwar yaushe gamo, toh" dagan nain kuma sai ya basu labari kamar yanda yaba Hamman Soja,
Baba general yace toh" _Alhamdullah_ ALLAH mungode maka, dama shi duk abida kaga yasamu BAWA toh" dama can rubutacce "Al'amarine daga ALLAH,

Ya UBANGIJINMU don tsarkin Mulkinka Ka "idan har A'isha tanareye itada abinda ta haifa toh" ka baiyyana mana da dasu" kamar yanda Ka baiyyana mana Mahamud
Dukkan su suka "amsa Da Ameen.

**********
Wani hadaddan folane mai dauke da kayan more rayuwa, wasu _3 beautiful flowers girls_nagani dukkan su suna sanye Cikin kayan _sports_, da "alama sun dawo daga motsa jikine. duk da cewa sunyi kama da juna domin idan kagansu zakace ko Hassana Da Husaina Da Gambo ne toh" biyu sunfi dakyar tsawon, babban Cikin su tana rike da Waya da " alama chatting takeyi, mai bimata Kuma ear piece ne makale akunnen ta tan,karamar Kuma tana t.v game, gaba daya hankalin su yatafi ga abida sukeyi, gaskiya yamma ta kyakkyawai ne sai kace yayan larabawa.

Can sai karamar ta "Ajiye remote din ta mike tana tsalle tareda fadi yeeeeehhh! "Dad is back, babban ta Dan harareta tace dalla yiwa mutane shuru me karya Dad ne zaya dawo ya zu?.... Ganin suna magana ne yasa

Please Login or Register in order to submit comment