Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga tace masa' sabangari zaya kaimu, yace toh' "adai-dai wani Dan matsakaicin gida aka saukemu bayan tafiya shi" kudi, sai muka shiga gidan yana dauke da dakuna uku,da kuma kicin da bayi tsakar gidan yana da fadi kadan, ga wasu manya-manyan tukwane Dana hango "acikin kicin din,

Daya daga cikin dakin muka shiga yana dauke da, gado biyu da Kuma tarkacen kaya tace bari Na kai miki ruwa kiyi wanka, Nace toh"

Bayan nayi wakan da ruwan zafi, tunda "a lokacin (hunturu ne) wato sanyi takawo Mani abinci, naci, sai take fada Mani sunan ta Hajiya Hafsatu amma Hajiya Magajiya ake kiranta', sannan gidan nan nata ne' "itada yarta, da mijinta yarasu aka raba gado aka bata sai tasiya, tana Kuma yin abinci takaiwa tasha, bayan tagama fada Mani sai tace toh" nahau gado Na kwanta nahuta "ita zata koma Tasha gurin sana'arta Nace sai tadawo ALLAH ya bada sa'a tace' Ameen tareda fita,

Haka naci gabada zama agidan Hajiya Magajiya, cikin kwanciyar hankali tana kula Dani sosai bata barina nayi "aikin wahala, saidai Dan motsa jiki kawai, ranan wata litini natashi Dana kuda Hajiya takira mai taxi yakaimu "asibiti,

Ciki "ikon Allah Na haifeka lafiya bayan "angama komai, "aka salla memu muka dawo gida, nikam ba "abida zancewa Hajiya saidai nace Allah yajikan ta', da rahama yasa Aljannar Fiddausi ce mako marta, domin tayi mani abubuwa dayawa arayuwa, bayan kwana biyu saita tambaye ni"wani suna nakeso asakama?,nafada mata akai maka huduba dashi, komai "ita ce tai mani kayan sawata DA naka da ragon suna duk itace' tayi da sati yaza gayo "akai suna,

Bayan suna saita cigaba da kula mu ni' dakai, da dafarko Da "Madona kake kama "amma daga baya saika rikida ka koma "Hamman Soja, kamar yanda"akace jarirai rikida suke" toh" haka yake,

domin kuwa rikida ka keyi naban mamaki, kullum kaman'nika sake fitowa yake Dana "Hamman Soja komai naka irin Na shine', hattada kunban kafarka irin nashi ne, hankali ya kwanta ganin yadda kayi Kama Da "Hamman Soja Wanda KO makaho yalalibeka yasan kaidin DAN SANE", "ahaka dai Na cigaba da goyonka harna yayeka,

lokacin da ka shekara hudu Hajiya tasaka "a makaranta islamiyya data boko "awanna lokacim Kuma tadade tanayi Mani maganar komawa gida, "amma saina ce' mata "a ah, bazani kowa ba wani lokaci idan tayi maganar komawa gida saina farayi kuka, dan'haka sai ta kyaleni tunda taga bana so",

************
Ranan Wata jumma'a daga makaranta aka kawo ka', baka da lafiya hankali mu yatashi sosai muka tafi "asibiti, bayan Likita yaduba ka' yace kana fama da ciwon zuciya, dan haka sai "aguji bata maka rai,nikam mamaki nayi tareda tambayar kaine cewa dama yara suna ciwon zuciya,?

"Ahaka dai mukai jinyarka' har kaji sauki, saidai Kuma tun bayan Da kaji saukin sai Na kula dawani bakon "al'amari daga gareka, shine sai ka zauna kayi shuru "abin Nada muna'
Duk da cewa dama Kai din bamai yawan magana bane,

"Amma Kuma wannan din yayi yawa sosai, ran saina tambaye ka mai kakeso sai kace Mani bakomai, can Kuma sai kace Mani Mama "ina BABA NA? gabana yafadi tareda jin wani irin tashin hankali, "amma Kuma sai ban bari kagane ba,

murmushi nayi Nace babanka bayanan, sai bakace komai toh" shikenan kuma
tundaga wannan lokacin sai ka cigaba da tambaya ta, "amsar daya ce nake baka shi BABAN Ka bayanan, ran sai kace yaushe baban ka zaya dawo? shuru Nai "Ina tunani "abida zanba ka? saboda karka cigaba da tambaya ta, sai Nace maka ba "Ai BABAN Ka yace bazaya dawowa ba,

toh" fa shikenan sai kadaina tambaya Na, duk da cewa bakasan BABAN ka ba Amma Ina ganin SON shi akwayar idanu ka,

Kanada shekara bakwa, ALLAH yaima Hajiya rasuwa, saka makon rashin lafiyar kwana biyu, nayi kuka sosai bayan tayi kwana arba'in, hankali Na yatashi lokacin da yan' uwanta "sukazo, Dan asiyar Da gidan, su" Kuma tafida "Maryam za'ai mata aure can garinsu sokoto,

Haka kuwa akai bayan ansiyar dagida, sai suka tafi da maryam, amma kafin su tafi saida Maryam takama mini gidan haya tabiya kudi, sannan Kuma tabani wasu kudin tace' narike,

A haka Na cigaba Da kula da Kai' gashi Allah yasa maka san karatu "aranka', Dan haka nasha wahala sosai gurin Neman kudin Da zakai karatu, ba abinda banyi ba nasiyar wa kosai, waina, wankau, aikatau, harda surfe da daka duk nayi, kai komai nasamu yinake, don kawai naga na'inganta rayuwar ka, nafara samun saukine lokacin da karfinka yakawo, sai kafar dako da Na baro, Wanda nasan duk baka manta da hakan ba,

Har lokacin DA ALLAH ya hadamu DA Alh ya'u Na Kaka, yatallafi rayuwan mu" wannan shine abinda yafaru arayuwa ta da Kuma Kai, takarashe maganar tareda share hawaye.

"Tabbas Abdul-jabbar bai manta wahalar dasu kasha ba shida Mama, Ahankali Abdul-jabbar yakejin wani irin tausayi Mama na ratsashi, tareda Sonta da Kaunar ta yana ratsa jini da bargon shi, yayinda yakejin wani iri. haushi babansa" musamman daya kasance mutun Mara BINCIKE, "acikin lamari sa domin inda yayi bincike tabbas da Mama bata shiga wani haliba, "ahankali ya dagoda kansa, ya kalli Mama fuskarsa shabe-shabe Da hawaye, hannun yasa yana share mata hawayen fuskarta tareda cewa, kiyi hakuri Mama na kidaina Kuka tabbas "anzalin ceki tareda yimaki mummunan fahimta, saidai kisani DA SANNU gaskiya zatayi halinta, kinji KO?
tace haka ne musamman ma "akan mahaifiyaka" Wanda "Naji LABARIN cewa yanzu shine Governor Adamaw! da sauri yace " a ah! a ah!! a ah!!! Mama basonjin koshi" wanene yanzu, tunda yace niba Dansa bane toh" shikenan, nima shi" ba babana bane' kece MAMA Na Kuma kece BABA na, dakarfi yake fadar maganar Wanda kanaji kasan baya cikin hayyacinsa, yace
saboda haka abinda nakeso shine kidaina kuka, saboda bana san ganin hawayenki kinji, sannan "ina Son duk Wanda ya kyautata maki a rayuwa, saidai kam Na tsani Wanda duk ya cuta maki, Mama ina Sonki! "Ina Sonki!! Ina Sonki!!! Mama Na!!!!!!!

A hankali jikinsa yasaki, saka makon alluran bacci da Doctor I s g yai masa, aikam cikin lokaci kankani nauyayyan bacci ya dauke sa, da sauri Y Y k yazo yadaga kasan daga kafar Mama, yayin da Doctor yai sauri jawo filo suka dorasa tareda gyaramasa kwanciyar,

Alh ya'u nakaka ya suke nauyayyan ajiyar zuciya, yace kiyi hakuri Hajiya A'isha kisani kowani bawa DA irin jarabawar da Allah keyi masa, Amma idan yayi Hakuri toh" "DA SANNU" zayaga kyakkyawa saka mako, yamaida dubansa ga Doctor yace Doctor Ina fata babu wani sauran matsala tareda Abdul-jabbar din KO?.... yace eh Alh bakomai darazan yasamu isassaa bacci toh insha Allahu sai tashi normal, saidai game DA ciwon zuciyansa sai andinga yin taka tsantsan da gudun bacin ransa, Alh yace toh " shikenan ALLAH yabashi lafiya gada suka "amsa DA Ameen, yace nadabo kamaida Hajiya A'isha gida yace to, "alokaci guda suka fita daga dakin gaba dayansu.

**************
Abdul-jabbar yaji sauki sosai,jikinsa yamarje yakara wani irin kyau idan kagashi baka taba cewa shine yai wannan rashin lafiya, sai wani Kuma shine tun bayanda "Mama tabashi labarin ta,

Shikenan Kuma sai yake jin haushi mutane Abinda bayayi da toh" shiyakeyi yanzu wato fada, abu kadan sai yafara, yayinda yake ba Mama kulawa ta musamman fiye da tunani mai karatu, data motsa sai yace Mama mekike son, hakan itama tace kula dashi sosai musamman dataji abida likita yafada dan haka batasan "abida zaya bata masa rai,

Ranan wata laraba Abdul-jabbar yafito zayaje gida su Y Y K dakuma yawan da yasaba Na Neman Humaira *nikam Nace tabdi Humeeh kam tana yola*
yana sanye da t shat baka da wandon jims fari kalkal, hannun sa rike Da key" mota tareda wayar sa,' sai kamshi yake zubawa cikin nutsuwa yake tafiya har ya isa bakin mota, zaya bude motar kenan sai yaji wayarsa Na Kara koda yaduba saiyaga sunan Dalter boy, yana dauka sainaji DA karfi yace?.....



💐Lufha Ce💞
💐💐💞💞💞 💞💞💞💐💐
DA SANNU
💐💐💐💞💞 💞💞💞💐💐

page126-130

NA

💞AMEENAT 💐UMAR 💐FARUQ
(MEENAT)

------------------------------
-------

*®PEN WRITERS ASSOCIATION*

*PEN:THE STRONGEST WEAPON*
--------------------------------------

*only exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers*


✍🏽


"Meh kace? sai kuma yacire wayar da sauri daga kunsan shi', sannan yakara volume din wayar, don yaji maganar da kyau, yace banji da kyau ba fa meh kace? Delter boy yace Dan "iska nasan kaji, kanaso ne nasake maimai tawa, toh" nace ne" "anyi posting din mu yola nan da two months zamu tafi,

Cikin karaji Abdul-jabbar yalallayo wani Uban ashar yakwada wa Delter boy, tareda cewa Kai! Uban wanene yai posting dina Wannan garin? Delter boy yace a ah to menene "aiba Shame bane, Dan "anyi posting dinmu Adamawa inace garin kune?

Cikin masifa Abdul-jabbar yace toh" nibana San wannan gari kaji KO"? Cikin mamaki Delter boy yece toh" ikon Allah tunda nake bantaba jin Wanda yake gudun garinsa ba saikai'

yace "eh naji Dalla malam kafada mun Uban wanene yace ayi posting dina wannan garin? cikin jin haushi Delter boy yace Ubana ne, Dan iska tunda idan zasuyi posting din suna tambayan Mutum ne, Kuma wlh saikaje yola nan saboda haka kazauna cikin shiri nan Da wata biyu zamu tafi , yana kainan yakashe wayarsa kit!!!

Abdul-jabbar kam ranshi yabaci fadi yakeyi Don me za'ai posting dinsa wannan garin daya tsana,awani gefen Kuma yafijin haushi Delter boy *nikam nace Toh" aibashi yace ai posting dinka can ba*

Cikin bacin rai Abdul-jabbar yajuya yakoma cikin gida, don "ayanda yakejin bacin rai bazaya "iya driving ba,
Mama kam gaban tane yafadi saka makon gani shi datayi a hargitse, saboda yanzu batason abinda zaya bata masa rai, shiyasa ma take taka tsantsan DA abinda "Doctor yace',
don bata son tarasa Dan tilon DANTA

Da sauri tace meya faru? cikin bacin rai yace mama wai "arasa inda za'ai posting Dina sai YOLA? "Ajiyar zuciya tayi "aranta tace Masha'allah Anzo gurin, lokacin Dana kejira yazo kenan?
Kallon sa tayi tareda cewa zonan,
"Ahankali yazo kusa Da "ita yazauna tareda kwantar Da kansa saman cinyar ta,domin yanzu ya sangarce dayin haka, yayin "ita Kuma saita Dora hannun ta saman kanshi, tana shafa lallausan sumanshi irin na fulanin asali,

tace kwantar DA hankalin ka, aiko" bakaje Adamawa Dan kowa ba kaje Dan Dan'uwana, KO" kamanta dashi' ne?, yace "a ah tace Saboda haka kadaina bata ranka kafa Doctor yace ba'asan kana bata ranka, Saboda bacin ranka tashin ciwon kan Kuma kaga ciwon ka,' ciwone mai hatsari tashin sa komai Na iya faruwa,

Wanda tasanadin haka "Ana "iyarasa ran Mutum KO" kana san' narasa kane?, da sauri yace a ah tace toh" kadai bata ranka kaji KO"? yace toh" saboda haka kar kadamu kataje kayi "aikinka, kawai kaji ko"?

yace toh" Mama "amma dai gaskiya "idan naje "iyakata barikin daza'a "ajiyemu (nasojoji) kawai, tace "ah baza katafi gurin "Mado na ba? shi kadai nefa dan'uwana, "a duniya,

yace toh" gurin sa"kawai zanje ni' baruwana dakowa, tunda basa sanki' toh nima banasan su" ,yakara she maganar Cikin jin haushi, tace "ah suna sona mana "Hajiya tana sona' "Baba genr Da "Baba engr Da su Adda "Uwa duk suna" sona',

yanajin tana tafadan sunayen mutane "amma baiji tafadi sunan "Baban sa da na wannan "Adda Aina'u ba, wato haka yana nufin sune mutanan dasuka fi kuntata mata arayuwa kenan ko?, Mtsww yaja tsaki, "ahankali shiyasa yake jin haushi su" duk dacewa yanajin kaunar "Baban shi acikin zuciyarsa, Amma hakan bai hanashi jin'hau shin abinda ya "aika tawa Mama shin ba, "Ahankali ya mike tareda cewa Mama Bari natafi gidan Y Y k, tace toh" yaushe ne tafiyar naku"?
yace nan da wata biyu ne tace toh " ALLAH yakai mu Lafiya, yace Amin tareda fita

*******************
YOLA
Wani katafare gida Na hango awata hadadde yar unguwa me suna KAREWA GRA ginin gidan upstear ne anyi mashi paint ashes and White colour,

"Tana kwance awani tanfareren gado tana sanye da wani sleeping gown milk colour ce, Rigar tanada dan sirin hannun batada tsawon sosai domin KO iyakarta kwauri, Humaira kenan mutanan YOLA.

A hankali tafurta sorry "yah Himu I can't forget "Him bcos l Love "him so much "where are you my special?....,
Chan kuma saita fashe da kuka me ban tausayi, sai kuma tafara surutai barkatai tankar zararriya, "acikin surutu natane take cewa "yah Himu yace waikai mayaudari ne? Ni' Kuma zuciya ta taki yarda dacewa "kaidin mayaudari, ne Amma kuma meyasa kai Mani haka? Why are you doing this to me (meyasa!!)why!! (meyasa!!)why!!! "Abdul-jabbarrrrrrr?

Haka tacigaba da kuka dakuma surutai har tsawon wani lokaci, saida tayi mai'sarta tukun sannan ta mike Ahankali tanufi (toilet) bayi,

Ko" a toilet dinma tana wanka tana kuka kadan kadan, "ahaka harta gama tadauro towel tafito, agaban mirror ta tsaya tana kallon kanta saida taka rema kanta kallo tukun, sannan tafara Shafa mai kamar bataso harda tagama, tabude wedrof tadauko Riga da siket na'atamfa tanada ratsi ja da fari ajinta, bayan tasane sai tayafa Dan karami mayafi fari, sannan tasa wani flat shoe fari sannan tanufi waje "A hankali take taka steps din tamkar bataso.

Ta "kuntane yasa Umma datake falo tana kallo T.v tadaga Kai ta kalleta,

Sannan tadubi agogon dake manne "afalon yanuna 1:00pm, sannan tamaida dubanta kan Humeeh data zauna kusada ita, fiska ba walwala tace Umma Ina kwana?

Umma tace dayake yanzu kika tashi kam dole kice Ina kwana, kalli "agogo yanzu kafe Nawa?

"A hankali ta kalla tareda dukar dakai kasa sannan tace karfe daya Na Rana,

Umma tace ace" tunda kikai sallar asuba sai yanzu kike fitowa haba "Humaira, nalura dake duk kwana kin nan haka kike, wai me ke damunki ne?

Me makon taba "Umma Amsar tambayar datai mata sai kawai tafashe da kuka,

Umma kam baki tasaki tana kallon ta Cikin matsanancin mamaki tace a ah lafia?

Cikin kuka tace "Umma nima bansan "abunda keda munaba saidai banajin dadi araina,

Umma tai murmushi tace shikenan kuma Dan bakijin dadi aranki saiki zauna kina kuka?...Haba autata, matso kiji,

"A hankali Humeeh tamatsa tareda kwantar da kanta akafadar "Umma,
Umma tasa hannu tana Shafa bayanta tace' idan Mutum yatsici kamshi Cikin wani yanayi dabai sabajiba toh" addu'a yakama tayayi ba kuka ba habah,sai kace ba matar "Malam?... ba tafadi tana murmushi.

itama Humeeh murmushi, tayi tareda turo baki tace toh" Umma "ai "inayi, tace yauwa toh kikara "DA SANNU" komai zaiyi dai dai ne kinjiko? tace Toh" Umma Ina "Abba Na?..., tace Abbanki kam tundazu yafita tunda yayi zaman jiranki baki fitoba, baki ta turo kadan tace toh" Umma shine baki tadani ba?.... baki Umma ta tabe tareda cewa taya Zan tadake" bayan 'kinsan "Abbanki yace "adaina tadake idan kina bacci, abari harsai kin tashi dakanki " Saboda ciwon Kain nan naki nafama, murmushi tayi tareda cewa toh Umma yaushe yace zai dawo?,,,, tace "a ah ni bai fada Mani ba, yanzu dai kitashi kaje kicin kidebo abinci Ciki. toh" tace tareda mikewa tanufi kicin.

***********
*DA MISALIN KARFE 12:30PM*
Yana zaune akatafarin office dinsa" gaba daya attention (hankali) dinsa, yanaga wani babban photo dayake manne ajikin bango, wato irin window size din nan duba guda zakai wa photo kane cewa bana yanzu bane, irin photo nan ne nada wato fari da baki, photo akalla zaikai kimani shekara ashirin da takwas zuwa talatin, macece ajikin photo tana sanye da kayan Fulani hannun reke da kwarya tana dariya,

"Ahankali aka turo kofar office din aka shiga tareda sallama, duba guda zakaiwa mai sallama kagane cewa shi security guard ne (maigadi) "aciki ya "amsa sallamar ba tareda yajuya ba, yace Jabeer sonawa zanfada maka cewa bana San damuwa?....
idan wani Abune aje gurin Dept mana KO" dole saini?

Ahankali Wanda akakira da Jabeer ya russuna tareda cewa, Allah ya huci zuciyar excellecy" bawani Abu bane, damai wani Mutum ne yake son ganin
ka, toh kuma "ace masa yatafi sai anjima yadawo yace "a ah shi yanzu yake san ganin ka,

Cikin daga murya yace wanene shi?...., Jabeer yace "eh toh ranka yadake bansan shi ba,
Saidai yace "ace Alh Mahmoud wai idan baka gane ba "ace maka MADO n! da
sauri yajuyo yace *what*?... (Meh) MADO kace yace?...

Jabeer cikin jin tsoro yace "eh ranka yadade haka yace,'
Da sauri yace OK" jeka shigo dashi yanzun nan, da sauri Jabeer yace toh" tareda fita,

"A hankali aka tura kafar Da sallama aka shiga, ya'amsa sallama tareda zuba masa idanu shima Wanda yashiga kallon sa yake, Ciki sanyi murya yace Mahmoud Ashe Zan sake gani. Ka?... wato hankan yana nufi "DA SANNU" ALLAH zaya baiya nar mun da A'ISHA ta kamar yanda ALLAH ya baiyanar dakai,

"A Hankali Yace kana nufin kace mani har yanzu ba' asan inda Adda A'isha Na take ba kenan?....
Cikin sanyin murya yace have a sit first, bamusu yasamu kujera guda ya zauna, yana duban sa Wanda shidin ma duban nasayeke,
A hankali excellancy
Yace?......





💐LUFHA CE💞
💞💞💞💐💐
💐💐💐💞💞
DA SANNU
💞💞💞💐💐
💐💐💐💞💞

page131-35

NA

💞AMEENAT UMAR💐 FARUQ
OR
(MEENAT)



----------------------------------------
*®PEN WRITERS ASSOCIATION*

*PEN:THE STRONGEST WEAPON*
----------------------------------------

*only exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers.*


✍🏾



"Mene ne yasa tun bayan, da kadawo "aka fada maka abinda yafaru tsakanin Nada "A'isha shine ka tafi, tsawon shekaru masu yawa baka dawowa ba sai yau,

"Anya Mahamud abinda kayi ka kyauta mana kenan,?...kako San "irin tashin hankali da "aka shiga lokaci da "aka nemeka ba'agan kaba?...., muna Cikin jima min rashin A'isha sai Kai kuma katafi, Shin meyasa baka yarda da kaddara ba?.. meyasa bakayi tunani cewa duk abinda yasami bawa da sanin UBANGIJI ba?..., Mahmoud ba baka kyauta ba, Sam, "ahankali yadukar da kai cikin nadama, yace kayi hakuri Hamman Soja, nazauna nayi tunani nage cewa haka danayi sam kyauta ba, shiyasa nakasa tunkarar "Baba gen Da "Hajiya domin "Ina matukar jin kunyarsu,

wani "irin kaya tattace murmushi yayi yace tsawon shekaru masu yawa, nake san naji wannan "sunan musamman daga bakin wacce "tasa mun sunan' Amma banji ba saiyau, Hmmmm...

ya ALLAH Kaine masani abinda yake boye DA baiyane ya UBANGIJINMU "ina rokonka' ka" banyanar mana da wannan baiwa taka "A'isha, tareda abida ta Haifa,"ahankali yace Ameen tareda kwantawa sosai a "irin kujerar nan mai juyawa, idanu yarufe tareda.....jin wani irin kauranar ta yana ratsashi.

*TUNA BAYA*
***********""""********
"Tun Lokacin da Hamman Soja sukai magana da A'isha bai saike kiran taba, "asalima bai dawo gidan ba, saida yayi wata daya sannan yadawo kuma bai isake A'isha agidan ba wani abin mamaki kuma shine Sam baidamu ba, don "a tunanin sa' gida taje domin yasan batada gurin zuwa daya wuce can,

" Tunda A'isha tabar gidan "Aina'u takecin karanta babu babbaka,gida yazama Nata sai yadda taso takeyi KO" dayake tace dama gidanta ne', "akacin Amanarta' Dan haka nema yasa taci alwashin cewa duk Wanda yashiga hurumin ta toh" "DA SANNU" zata fitarda dashi,

********
"A bangaran Hajiya kam hankalin ta yafara tashi,Saboda takira telephone din gidan su A'isha saidai Aina'u ce" ke' dagawa, kuma idan ta tambaye ta "Ina "A'isha sai tace mata "aitana bacci,
toh" itakuma Hajiya Saboda ganin tana dauke da juna biyu
Shiyasa bata cewa "atashe da "ita toh ganin cewa cikin ta yashiga wata Na biyu,

ya kamata tafara zuwa "ana dubata "itada "abinda ke ciki ta, saidan kuma da gabaya "idan ta kira telephone din ba'a dauka, toh shine kuma "abin yafara bata tsoro, gashi shima Magajin kota kira shi bata sabu.

Tana zaune afalo tana tunanin A'isha, sai ga Hamman Soja yashiga da sallama, ajiyar zuciya tayi tareda amsa sallama saida yazauna nesa da'ita kadan sannan yagaida ita, bayan ta amsa sai take tambayar sa ya'u shi yadawo?...

yace dazu, tace yasu A'isha da Aina'u ?.... yai shuerun sannan yace lafiya lau, nan dai tafar yimasa Malabar A'isha har tana cewa yaka mata
tafara zuwa "ana
dubata "inafata dai cikin baya bata" wahala sosai, kasan cikin fari wani saiyai tabashi matsala Saboda rashin sabo,

shikam Hamman Soja gaban sane yake faduwa, saka makon jin abinda Hajiya take fadi, "ahankali yadago dakai yace batana nan ba?.. cikin rashin fahimar abinda yake nufi, tace wakenan fa?...cikin daure fuska yace ita Aishan mana gaskiya Hajiya A'isha bata kyauta Mani ba ni Sam basan haka take ba,

Da sauri tace me "A'isha tayi maka sannan Kuma tana "Ina,?... Don niba tazo nan ba,asalima rabona da ita tunda taje asibiti Na dubata nace tanada juna biyu, Kuma nakira telephone din gidan Kuma sai "Aina'u ce ke dau sai tace mun tana bacci
nan data fada mashi,

Mtsww yaja tsaki yace yafi "mata dama nace", karta kuskura nadawo Na isaketa agidan nan,
Da sauri Hajiya ta mike tareda cewa me kake nufi da hakan?... Cikin bacin rai Yace Hajiya wannan cikin dayake jikin Aisha banawa bane', alima ni bazan tabaq haihuwa ba tunda nasamu matsala lokacin, danai hatsari saboda haka shiyasa nace taje tanemi wan...

Da sauri Hajiya tadafe kirji tareda cewa Na shiga uku ni FATIMA, kace Ciki dake jikin A'isha banaka bane toh" nawaye?.... sannan Kuma bazaka taba haihuwa ba meyasa meka,?....
Yace "eh sabo...maganar ta tsaya saka makon gani Hajiya tafadi Sumammiya...

Da gudu Baba gen ya karasa gurinta'wanda dama tuni yafito daga daki yana tsaye yana sauraran su, daga kanta Baba gen yayi tadora akafar shi yayinda yakata fadin Subhanallahi, Hajiya gabada hankalin sa yatashi ganin KO" motsi batayi,

Da sauri Hamman Soja zaya gurinta,wani mahaukacin tsawa Baba gen yadaka masa, tareda cewa kana zuwa gurin nan zanyi shooting din ka Da wanna bindigan najikin ka,' (nace tab lallai ran tsohon soja ya baci) yace zaka bani ruwa KO sai nayi mugun Saba maka, da saurin Hamman Soja yadauko ruwa, baba gen ya yayyafa mata, wani irin ajiyar zuciya tayi tareda bude idanun, da sauri ta tashi ta dubi Baba gen cikin gigita,

Tace general mafarki nakeyi KO" da gaske ne abinda yaron nan yafada?... Cikin bacin rai tareda duban Hamman Soja Wanda ya dukar da Kai kasa, yace ba mafarki kikeyi ba Docter yakori matarsa daga gidan shi, Saboda yana zargin cewa cikin jikinta bana shiba ne, saboda wai baza taba haihuwa ba,

Cikin daka tsawa Baba gen yace' Dan Ubanka,' waye yace maka bazaka taba haihuwa ba?...
Da saurin yace naje gurin Likita har sau uku, shine yafada min,Hajiya kam kuka tasaki mai ban tausayi, cikin tashin hakali take fadi shikenan yanzu baza ka taba haihuwa ba....?
yace "eh Baba ger Yace toh Maine ne hujjar ka?.. yace takardun suna nan,
Shuru Baba gen yayi yana nazari,

Cikin kuka natashin hankali tace toh yanzu Ina A'isha ta tafi,?....yace niban saniba, tace oh" ni Fatima KO Ina A'isha ta shi ga?..

oho yafada aran shi koma dai inataje ita' tasani, nikam bazan iya zama Da itaba tana cin amanata ba,

Cikin kuka Hajiya tace "a yadda nayima A'isha tarbiyya Sam bazata iya aikata wanna mummunan Aikin ba, haba Magaji zina da aure fa kake nufi?...., general nikam banyarda da "abinda wannan yaron yafada ba, kilama karya yakeyi,

Da sauriyace' ba karya nakeyi ba takardun suna nan, Baba gen yace' jeka dauko Mani takardu nagani toh" yace tareda mikewa yafita.

Cikin minti talatin sai gashi yadawo koda Baba gen yaduba takardun, jikinsa yai sanyi yayinda wani irin zufa ke karyo masa,
Da sauri Hajiya ta karba itama taduba, wani sabon kuka tasaki tana fadin,

shikenan mu kuma haka ALLAH ya kaddara mana, Kai guda muka Haifa Kai kuma bazaka taba haihuwa ba ikon sai ALLAH, toh meyasa ka kori A'isha meyasa baka kawo Mani ita ba nikam, Dana taya ta rungumar kaddara,
Koda yake dama kila kana Neman hayyar dazaya rabuda ita, haka Hajiya taciga da fada tareda surutai, Wanda kai daga jikasan bata Cikin hayyacinta,
Yayin DA Baba gen meta faman lallashinta Wanda shima karfin hali kawai yake.

***************
Cikin lokacin kankani magana takarade family cewa "A'isha tabace' sannan Kuma Hamman Soja bazaya taba haihuwa ba,

hankalin zuriyan Alh Ahmed Dan kwangila yatashi sosai, dajin

Please Login or Register in order to submit comment