Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakin takara turowa tareda cewa toh" bakai bane kace naje yawo,

Yace toh' yi hakuri aibasan gidan su new besty mu kikaje ba, Kuma ni aiwasa mana nakeyi nasan my Cool bazata ringa zuwa yawoba, kodan kar wasu surinka kalle Mani beautiful face dinta KO? toh" Dan Saki fuskar mana yafadi yana Murmushi, itama Murmushi tayi Wanda har saida wushiryar ta tabaiyyana.

A dai dai lokacin da Dalter boy yakaraso kasan cewar taresu kazo, nan dai tashiga gaba suka bita abaya zuwa falo Bayan sun zazzauna sannan suka gaisa,

Abdul-jabbar yace Abba fa?.. tace' yafita yece OK aikilan kafin mutafi yadawo tace "eh Ina sa ran haka insha'allahu,
Dalter boy yace wa Abdul-jabbar shi Sam bagane Humaira ba wai yaga takara kyau da kiba, ita kam kunya yaka mata, don haka ta tashi tareda cewa tana zuwa tanufi sama.

Bayan tafita sai Dalter boy ya kalli Abdul-jabbar yace J boy, dama suma Humaira mutanan Yola ne kamar ka?.. Kafada yadaga yace I think KO" Kuma aiki yakawo Abbansu nan ba,

Dalter boy yace may be haka ne KO, aiki ya kwoshi KO Kuma "asalin kararsu kenan, dai-dai lokacin da Humeeh tadawo itada Umma,

Da sauri suka sauka daga kan kushin suka tsuguna suka gaida Umma, ta amsa fuskarta sake har tana tambayar su ya Aiki?. sukace' Lafiya lau tace toh madallah sannan ta koma sama,

Yayin Da Humeeh tashiga jera masu Delusion's din data shirya masa, bayan ta zuzzu bamasu', sai ta mike zata tafi da sauri Abdul-jabbar yace inazaki Kuma?

Cikin jin kunya tace Zan shiga daga cikine har kugama, yace "ah 'ai idan baki kusa Dani abincin bazaya tafiba, amma Idan ina kallon beautiful face dinki sai nakusan ciyen wannan garar batareda nasani ba KO bahaka ba?.. Dalter boy?.. yace ummh dai-dai lokacin daya Cika bakin sa, da farfesun kayan ciki daya sha kayan yaji sai kamshi katashi.

Yace yauwa toh kinji so come and sit here yanuna mata kusada shi, kasan cewar a three site suka zauna Dan haka sai ta zauna dan'nisa dashi kadan,

Sunacin abinci suna zuba santi daga Abdul-jabbar din har Dalter boy, tana tayimusu dariya harsuka gama sannan ta kwashe kayan takai kicin,

Bayan tadawo sannan Kuma suka cigaba da fira harda Dalter boy din, sundan taba fira sannan Dalter boy ya kalli agogon hannun sa, sannan yamike

yace'
J boy yakamata mutafi haka nan yanzu fa 3:40Pm kasan akwai aiki agaban mu, Humaira mun gode sai kuma gani Na biyu tace nikeda godiya, sai anjima yace OK sannan yafita yabarsu.

Abdul-jabbar yace my Cool gashi har yanzu Abba baidawo ba gashi Kuma muza mutafi Saboda akwai Abunda zamuyi tace toh shikenan, yace ba damuwa kinfa San yace' yana San magana dani..

Tace "eh haka yace so kutafi kawai idan yadawo sai nafada mashi kazo, yace toh' idan yadawo kitambayar mani shi lokacin dayake gida ya free sainazo KO?
tace toh" shikenan.

Suna tafiya zata rakashi, tace' af my Special aina mata nafada maka, yace" me kenan fa?.. tace yau agidan su my besty Sarah kasan mena gani?.. yace "a ah saikin 'fada, my Cool,

Tace wlh Daddy su my besty kamar kudaya dashi, jiyayi gabansa yafadi amma saiya basar yace' ah habadai?

Da sauri tace ALLAH dakai dashi kamar irin identical twins din'nan saida shi yafika kiba kadan, yace ikon Allah, tace ai inata mamaki harnace kilama Dan' uwanka ne shi? yace' a ah bansan shiba nida nake bako agarin, ke Kama ce ba kawai, tace haka nefa,Kuma fa shine governor garin nan,

Yace ALLAH sarki dai-dai Lokacin Da suka isa gurin motar, saida taga tafiyar su sannan takoma Cikin gida.

Daga yadda yake Driving zaka fahimci gaba daya ransa abace yake, Saboda wani irin mugun gudu yakeyi akan titin kamar zaya tashi sama,

Ganin hakane yasa
Dalter boy yawaiga ya kalleshi tareda cewa master duk wannan gudun dakakeyi iyakarmu fa Gibson barrack,

Juyowa yayin shima ya watsa mashi idanun sa dasuka kada sunayi jajir, yace I know sannan yamaida hakalinsa ga driving, Cikin bacin rai yace' kajiko yanada mata dayara hakan yana nufin wato gaba daya yamanta damu",
yashafemu "ababin RAYUWAR SA" Saboda baya kaunarmu ko? saidai kuma "DA SANNU" zayayi NADAMAR "Abunda ya'aikata agaremu,

Dalter boy yace' master nifa ban fahimce kaba domin gaba daya maganar adunkule kayita, don haka bansan inda kado saba, batareda daya kalleshi ba yace' aiba zaka gane ba ahaka harsuka isa barrack din.

*************
Yau Monday don haka Humeeh yau sai 4:00pm zasu dada makaranta Saboda sunada lectures kuma zasuyi practical, zaune suke itada Sarah fitiwarsu kenan daga masallaci sunyi sallah azahar,

Sarah tace Kai! Kai!! kai!!! besty tashi mutafi ga mutunki nan Chan ya iso, muyi sauri kafin yashiga kinsan shiba sauki, Humeeh tace hakane fa dai-dai lokacin da suka nufi cikin holl din'da zasuyi lecture din,

Sarah tace I hopo kinyi switch off din phone naki? Kinsan shi Dan ka'idane, Humeeh tace tundazu, dai-dai lokacin da suka shige cikin holl din.

Abdul-jabbar ne agaban Abba kasan cewar sunyi wayada Humeeh tace" masa Abba yana gida don hakane yaje,

Tun bayan dasuka gaisa da Abba kanshi ke kasa Saboda wani irin kunyar Abba yakeji, shikam Abba kallon Abdul-jabbar yake yayinda yake mamakin irin wannan Kama komai irin guda haka, hatta da kunbar hannun irin dayane.

Saida yagama nazarin sannan yace samari ya sunanka kace'?...Cikin jin nauyi yace Abdul-jabbar, "ance daga Kaduna akaturoka nan kayi kos KO? yace "eh,

Abba yace "Ok shin wanene mahaifinka "a Kaduna?.. Abdul-jabbar jiyayi gabana yafadi yayinda yaji nutsuwar shi tana Neman kubce masa,

Shi Sam baiyi tsammani wannan tambayar Abba zayayi masa ba, saida ya tattara natsuwarsa sannan yaba Abba amsa da cewa?..



๐Ÿ’Lufhat Ce๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page183-187

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)

----------------------------------------
*_ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN:THE STRONGEST WEAPON_*
----------------------------------------

*_only exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_.*


โœ๐Ÿพ



"Alh ya'u nakaka shine mahaifina, kuri Abba yayiwa Abdul-jabbar da idanu yana kallon shi cikin matsananci mamaki, yace' kace' sunan ka Abdul-jabbar KO?.

Cikin jin nauyi yace "eh Abba sunana kenan, Abba yace toh" Abdul-jabbar "Inaso kafada Mani ainihin gaskiya wanene mahaifinka "a cikin Kaduna?..

"A hankali Abdul-jabbar yasake cewa Alh ya'u nakaka shine mahaifina, Abba yace bashi bane mahaifika, gaban Abdul-jabbar ne yafadi yayi da yaji zufa tana karyomasa kai yadukar batareda yace' komai ba, Abba yace nasan Alh ya'u nakaka dan'shi daya ne Yusuf, Amma meyasa zakayi mani karya Abdul-jabbar?.

Cikin sanyi murya yace Abba kayi hakuri wlh duk fadin Kaduna banida Ubanda yawuce Alh ya'u nakaka domin shi nasani,

Abba yace OK" toh" wacece Mahaifiyar ka?.. yace sunanta Hajiya A'isha, yace' bata fada maka ko wanene mahaifin kaba?.. Da sauri yadago dakai yakalli Abba Wanda shima din kallon shi yake, dukar dakai kasa yayi batareda cewa komai ba,

Abba yace shin Abdul-jabbar baka San "mahaifinka bane?.., sannan Kuma "mahaifiyar ka' bata fadamaka kowane shiba?.., Cikin karfin hali Abdul-jabbar yace Abba tafada mani saidai banasan nasan shi dama can bansan shiba don haka ko yanzu ma banasan nasanshi

Shuru Abba yayi domin yanzu kam zargin dayakeyi akanshi yazama gaskiya, dama Abba tun ranan farko daya ga Abdul-jabbar yagane kosha waye, jiyayi wani irin Sanshi tareda matsananci tausayi shi, yaka mashi,

"A hankali Abba yace Abdul-jabbar meyasa baka San kasan shi waishin bakasan cewa kowani Da' da' uba yake adoba?.. shi bakasan cewa duk matsayin mutun duk mulkinsa dazan akace yau bashida UBA toh" darajarshi fa ragewa take a gurin mutane ,

Shin meyasa bakanan kasa kowaney mahaifinka?
"A hankali Abdul-jabbar yabude baki daniyar yayi magana, saikuma yakasa saka makon wani irin zafi dayaji ZUCIYAR shi nayi,
Kai yadago tareda yazubawa Abba idanu shi dasuka kada sukayi jajir,

Sai Kuma yasaki kuka tamkar karamin yaro kamar kuma ba SOJA ba, SOJAN ma wanda yake sanye uniform ajikinsa kuka yake mai ban tausayi, Wanda kanajinshi kasan 'andade "anasan ayishi ba'asamu damaba sai wannan lokaci,

Cikin kuku yace Abba tunban San kainaba nake san ganinshi, ZUCIYATA tarayu da KAUNAR shi saboda tunani nasan shi harsaida nakamuda CIWON ZUCIYA, wanda haryanzu inashan magani, Amma meyasa shi baya sona meyasa tun Ina cikin mahaifiya ta yatsaneni?

Abba shiyasa nima yanzu bana San ganin shi tunda shima baya sona, pls Abba Ina son Humaira kar kace bazaka bani auren ta ba Saboda naka sance banida mahaifi sai Uban riko,

"Ahankali Abba tadaga hannu sama yanatafan kwarara Addu'a, saida yayi Addu'a sosan sannan yasauke hannu tareda karasa dafadin ALLAH Kaine maji rokon bayinka ALLAH mun gode maka daka amsa Addu'a mu,

Cikin sanyi murya yace zonan kusa dani Abdul-jabbar "aikam da sassarfa Abdul-jabbar yakarasa gurin sa, Abba yace haba SOJA sukutun yake kuka haka kamar MACE ayya kuwa SOJAN NE?.. Kai SOJAN NEFA tunda gashinan harda kakinsu Ajikin shi,

Cikin zalaya Abba yaci gaba da cewa
Kai Kuma fa shi din JARUMI NE KO sunan shi kawai abun kallo ne, toh" koya manta da hakan ne"?.hmm Lallai nasan "DA SANNU" zaya gane cewa shinefa
ABDUL-JABBAR jikan "ABDUL-JABBAR Da "ABDUL-JALAL Daga "AHMED DA A'ISHA" Addan MAHAMUD Angon "AISHA HUMAIRA insha'allahu,

Cikin mamaki Abdul-jabbar yasaki bakida hanci yana kallon Abba, dayake tafaman doka masa murmushi, cikin rada Abba yace kayi sauri kashare hawayen nan kafin Humaira tazo tagani,

tace tafasa auran tunda kaidin RAggo ne kana sanye da kakin SOJA amma kana kuka kamar mace, Abba yakarashe maganar tareda rike haba,

Da sauri yashare hawayen tareda yin murmushi sannan ya dagoda Kai yatsurawa Abba idanu, shisai yanzu ma yagano kamar DA sukeyi DA Mama wani irin dadine yaji yaratsashi,

"Ahankali Abdul-jabbar yace KAWU NA Mahamud Abba yace na'am ABDUL-JABBAR da sauri yamike ya rungume Abba shima rungume shi yayi cikin tsananin farin cikin Abdul-jabbar yace Abba ya'aikai kaganeni?..

Abba yace' haba Abdul-jabber "ai tun ranan farko danaganka gane cewa Kaidin jinina ne, balle kuma ko makaho yalalubaka zaya gane kokai Dan waye, baki Abdul-jabber yaturo kamar karamin yaro yace Abba toh" nidin Dan waye?..

Dariya Abba yayi yace' Abdul-jabbar kenan "ai kobaka taba sanin shiba nasan kaji Labarin shi gurin Maman ka Kuma aikaji dazu nafadi sunan shi akirarin danai maka KO?..

yace Abba toh nikam bashi bane "Babana, DA sauri yace kul naji kasake jin kalman nan tafito daga bakin ka, toh" idan bashi bane "Babanka toh" wanene Baban Ka?.. cikin sanyin murya yace' Abba toh" Ai shidin ne baya SONA Abba yace Waya fada maka baya son ko?.

Nan dai Abba yafada masa duk "abinda yafaru Wanda "Aina'u ce duk keda sahannu 'afaruwar komai, jiyayi SON mahaifinsa yasake kamashi amma fa duk da hakanan yanajin Dan haushin Sa kadan, narashin BIN CIKEN da baiyi ba kawai ya yanke hukunci.

Abba ya kalli Abdul-jabbar yace toh" yanzu fada mani Address "inda Adda ta take dama yau zantafi Kaduna Saboda wasu kayana dasuka fito tacan, Saboda haka yau agidan Adda ta Zan sauka insha'allahu,

dariya Abdul-jabbar yayi yace Abba Ka tsaya mana nakara ganinka da kyau,
Shima dariya yayi yace "a ah aikai kagan'ni Adda ta yarage tagani, naganta Kuma yaudin nan zamu haduda izinin Allah,

Yamike yana cewa Bari nakira Umman taku kugaisa KO?... Abdul-jabbar yace toh" Abba yana gaba Umma tabiye da shi'abaya, tana fadin ikon Allah Ashema shin din Dan gida ne nan dai suka gaisa Da Umma, yayida Abdul-jabbar yasaki jikin shi da sun har suka danyi fira kadan,

Sannan yace zaya koma gurin aiki Abba yace toh" shikenan, shima kamar yadda yafada masa insha'Allahu idan ma yasamu yadda yakeso zaya taho da Addan, yace toh" shikenan sai yadawo nan dai sukai Sallama yatafi.

Yau sai karfe 4:00Pm su Humeeh suka tashi daga school don haka agajiye ta isa gida, koda taleka dakin Umma tana Sallah don haka itama sai tashiga wanka tayi sallah sannan tanufi kichin don wata irin yinwa takeji,

Saida taci abinci tayi nak sannan tanufi dakin Umma tana cewa sannu da gida Ummata, tace yauwa ake za'ayiwa sannu sai yanzu kuka tashi? Tace' Hmm kedai Umma sai yanzu fa, toh" Sannun Ku' yauwa Umma Ina Abba Na?

Abbanki kam yana Kaduna da sauri Tace' Kaduna Kuma? Umma Lafiya tace' Lafiya lau nan dai tafada mata komai gameda Abdul-jabbar, cikin mamaki tace Umma yanzu Abdul-jabbar Dan Uwanane?.. tace' najini kuwa,

Wani irin dadi taji yaratsata da sauri ta tashi tanufi dakin ta, yayinda Umma tabi bayan ta DA kallo tana murmushi, koda ta isa daki wayar ta taciro ajaka takunna wadda ta kasheta tun lokacin da zasu shiga lecture,

Kiran Abdul-jabbar ne first Da yafara shigowa dariya tayi Sannan tadaga tareda sa wayar a handsfreen, jinai yace' haba my cool wannan wani irin "abune haka yaza'ai ki kashi waya tun dazu inata faman nema layinki wai switch off Lafiya?..

tace ah Malam aikai Zan tambaya Lafiya kakirani sai faman yimani ihu kakeyi, alhalin ni bansan komai wanene ba Kai wannan number warron number ce', don niban mataba ganinta ba sai yau Saboda haka sai anjim,

Da sauri yakatse tada cewa ke! Ninefa Abdul-jabbar fuska tayamutse kamar yana ganinta tace' waye Kuma haka nan?.. jitayi Ciki sarkewar murya yace' Special dinki nefa, harza tace Oho sai tafasa sai Kuma ta kyalkyace da dariya,

"Ahankali yasake ajiyar zuciya tareda cewa haba my Cool wannan aisaikisa ZUCIYAR ta tarwatse, ke bakisan haryanzu akwai sauran gyanbo acikinta ba?.. cikin dariya tace Sorry my Special one banyi niyar bata maka rai ba,

tace kasa meye yace a ah saikin fada tace' wannan shine karona farka arayuwata danai wasada abokin wasana, yace "OK toh" ni abokin wasanki ne? tace "eh mana, yace eyyee lallai ma yarinyar nan waya fada maki?.. tace' ah tun yaushe naji komai, yace haka ne Abunda kikaji, Kai no wonder nafaye Son ki dayawa Ashe kedin jininace,

Tace toh" ainima "inason kadayawa harfada zazzabi saida nayi,
yace Hmmm Son Danake yimuku kedai Daddy yayi yawa sosai tunda har saida ya haifarmani DA ciwon ZUCIYA,

tace toh" Amma meyasa danace ko kasan Daddy su my besty sai kace Kai baka sanshi ba, yace toh" mezan ce maki my Cool bakisan Abunda mutumin nan yai mana bane shiyasa,

Da sauri tace kodai meyayi maka shi din dai ne mahaifinka
Don haka Ka gyara kalaman ka, so fadin munanan kalamai ga iyaye badabi'abace me kyau ga mutumin kirki irin ka, shi lamari duniya DA kagani idan Mutum yabi ahankali toh" "DA SANNU" Allah zaya warware masa komai,

Nan dai tayi tamasa magana gani masu ratsa zuciya Wanda yaji kaunarta takarashiga aranshi, Daga nan Kuma sai sukacigaba da tsokanar junansu me cikeda Soyayya.

*Kaduna*
*************
Alh ya'u nakaka ya kalli Abba bayan sun gama gaisawa sai yace" bawan Allah ban bangane kaba fa, Abba yai murmushi tareda cewa ainasan baka ganeni ba Amma dai aikasan Haj A'isha Mahaifiyar Abdul-jabbar KO?
Cikin mamaki yace'



๐Ÿ’žLufhat Ce๐Ÿ’
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page188-192

Second to the last
page
NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)

_*Slm Masoya wannan littafin kuyi hakuri da sunan shi za yakare Ina nufin "DA SANNU" zamuga karshen shi Lafiya Dani daku insha'Allahu nagode sosai da kawar Ku*._


----------------------------------------
*_ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN:THE STRONGEST WEAPON_*
----------------------------------------

*_only exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_.*


โœ๐Ÿพ



"Niko nasan ta inafata dai lafiya?.. Abba yace'l lafiya lau, sunana Alh Mahamud ni mutumin Yola ne "amma na taba zama agarin nan idan tabayin manager Bank a G T ada, amma yanzu banayi nakoma can Yola,

kuma ni kanine "agurin Hajiya "A'isha mundade muna Neman ta, Allah baisa mungan taba sai yaune cikin gudurar ubangiji mukasamu Labarin inda take agurin danta, Abdul-jabbar toh" shine nazo natafi da ita idan bada muwa?..

Tunda Abba yafara magana Alh ya'u nakaka yake Murmushi farin ciki najin wannan daddadan labari, yace ikon Allah dama duk abunda kaga yayi farko toh" idan akayi hakuri "DA SANNU" za'aga karshen shi,

Abba yace'wannan haka yake nan dai Abba yabashi labari "abunda yafito da Mama gida, Alh ya'u yace kai wasu matan sai "ahankali kaji irin wannan makirci haka, kai Allah kayi mana tsari da shaidanun mata, ameen

Abba yace Ameen nan dai shima Alh ya'un yabashi Labarin tun lokacin daya hadu dasu har zuwa yanzu, Abba yaita godiya Alh ya'u yace bakomai aiyiwa kai sannan yakira Hajiya karima matar shi suka gaisa,

Bayan komai yalafa sai Alh ya'u yakira Y Y K awaya yace' masa yajeya dauko masa "Mama yakawo ta nan gidan shi yanasan ganin da, Y Y k yace' toh".

Dagan suka cigaba cigaba da fira har lokacin da Y Y k shida Mama suka iso da Sallama suka shiga falon, bayan sun gaisa sai Mama tace" Alh gani yusufa yace kana son ganina nace toh" Allah yasa Lafiya?..

Yace" lafiya lau dama wannan bawan ALLAH ne yazo gurin ki, yafada yananu namata inda Abba yake zaune yana tafaman doka Murmushi, kuri tayi mashi da idanu tabbas baza taba manta wa da wannan kyakkyawa Murmushi ga fuskar dan'uwanta duk dadai yanzu yazama babban Mutum.

da sauri ta tanufi inda yake dai-dai shima yataso Hannun shi tareke tareda cewa wannan MADO name, yace" nine ADDA rungume juna sukayi suna farin cikin ganin juna, Mama kam harda kuka tayi najin dadin ganin dan'uwanta, yace' Adda na ashe Zan sake ganin ki?..

Tace mado Na gashi Allah ya hada mu yace' haka ne toh" Allah mungode maka, tace Allah "abun godiya kallon shi take cike da mamaki tace madona kazama babban Mutum,

dariya yayi yace' Addana kenan niko sainaga kamar bake kika haifi wannan santalelen saurayin nan Abdul-jabbar ba,
tace hmmm kana nandai yadda nasanka da tsokana bakasan yanzu kagirma bako?..

Dariya yayi tareda sake rike Hannun ta yace" a ah idan Ina kusadake nidin yarone harma dai idan kince MADO na, yakara she magana yana dariya itama dariyar takeyi, nan dai sukan taba fira yaushe gamo sannan Abba yace yanason yatafida Mama gidan Malam su gaisa.

Alh ya'u yace idan bada muwa shima zayaje sugai sa, Abba yace badamuwa, nandai suka dunguma sai gidan Malam, bayan "angama gaggaiwa sai Abba yaiwa Mlm bayanin komai tareda nunamasa Mama,

Sosai Mlm yayi Fari Ciki tareda sawa Alh ya'u nakaka Albarka dagan kuma sai aka ajiye maganar lafiya Yola gobe insha'Allahu.

********""""*********
Washe gari karfe goma nasafe jirgin su yatashi zuwa Yola, Abba Alh ya'u nakaka Mlm Hajiya karima gwaggo da Y Y k, Abba da Alh ya'u nakaka sune suka dauki nauyin lafiyar , dan Kari kaji masu abida abunsu kurada kallabin kitse,

_*To mukan saidai muce "asauka Lafiya*._

๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
Sun isa Yola lafiya Abba ne yakira bala direba yazo yadauke su, direct gidan Baba gen yace" bala yakaisu, bayan yasauke su sai yace yaje yadauko Umma da Humeeh kasan cewar yau basuda lecture,

Labari Abdul-jabbar dan"uwanta kuwa ne tuni ta fadawa mutanan ta, watoh Hannah da Haleeh
Sarah kuwa tace sai sun hadu gidan baba gen,

*GIDAN BABA GENR*
Baba gen da Hajiya Binta suna zaune a tamfareren falonsu" suna fira sai jin Sallama sukai,

Abba yana rikeda hannun Mama suka shiga falon ahankali ya karasa gurinsu gaba daya dashida Mama suka tsugunna gabansu, yayinda sukuma kallon sukawai suke fukarsu cikeda mamaki, Abba yace' Baba Hajiya yau ga Adda A'isha Allah ya baiyyana mana ita,

Da sauri Baba gen yace Masha'allah Allah mungode maka, yayinda ita kuma Hajiya Binta ta rungume ta tareda sakin kukan farin Cikin tana cewa Allah nagode maka, daka baiyyana Mani Amanar daka bani dama "ance mahakurci mawadaci, gashi damukayi hakuri muka barwa Allah komai gashi "DA SANNU" Allah ya baiyyana ta.

Nan dai akai ta farin Ciki harda Baba engr da Matarsa kasan cewar Baba gen yace akira shi, sai da
komai yalafa sannan Abba yagabatar da Alh ya'u nakaka da matar sa tareda dan shi Yusuf, sune suka taimakawa Mama tareda danta Abdul-jabbar, sannan yagatarda Malam Garba da gwaggo sune sarakan shi.

Aikam nan su Baba engr sukai tazuba godiya tareda samashi Albarka, Alh ya'u wlh bakomai ai anzama daya, bayan komai yalafa sai matar Baba engr tace' A'isha toh" Inashi maigidan nawa banga shiba?..

shuru tayi tareda dukarda kai kasa Saboda kunya irin ta fulani, Abba yayi dariya tareda cewa Hajiya aikam Santalelen maigida yana nan SOJA amma sai kin bada toshi Zaki ganshi, tace au haka ne?.. Cikin wasa yace' "eh Saboda haka kawo nikuma yanzu naje nataho dashi.

Da sauri Baba engr yace Masha'allah Mahamud yimaza kaje kataho Mani da ABOKINA, Abba yace toh" yayinda matar Baba engr ta sake cewa yauwa jeka tahodashi, idan naga yayi Mani kagasai nabada toshi dakyau idan kuma baiyimaniba sai akai kasuwa, tafada tana dariya gabadaya falonma dariya akayi, yayinda Abba yamike tanufi hanyar fita yana cewa sosai kuwa zayayi maki kilama kibar Baba engr ki dauke shi.

Yana fita sai gasu Humeeh sun iso key ya amsa Hannun bala direban yace' su shiga Ciki zayaje yatahoda Abdul-jabbar, sukace toh tareda shiga Cikin gidan.

Abba bai tsaya ko'inaba sai Gibson barrack, bai samu matsalaba gurin tahowada Abdul-jabbar, suna tafiya suna fira yayinda Abdul-jabbar kejansu Abba kuma yana gefen shi yayinda Dalter boy yake baya kasan cewar harda shi.

Abba yana fadawa Abdul-jabbar cewa?.. tareda su "Alh ya'u nakaka suka zo, harda abokin shi "Y Y K, Abdul-jabbar yaji dadin cewa harda Y Y k akazo, yace Abba duk family sun hadune?..

Basu naduba tukun amma zasu hadun idan ka'isa, yace shi kam nasan yazo KO?.. Abba yace waye shikuma?...baki yaturo tareda cewa shi din mana Daddy su" bata rai Abba yayi yace ayya Abdul-jabbar yanzu Daddy nakane shi Ku.a Daddy wasu, Ai kafin yazama Daddy wasu" Daddy ka yafara zama, yace' Abba toh" aisu" yakeso nibaya sona shiyasa nace sh....

Kasa karasa wa yayi saka makon kallon Da Abba ya watsa masa tareda cewa baza kadaina bako?.. da sauri yace' yi hakuri Abba na daina, kyale shi Abba yayi baice komai, can sai yace Abba kafada Mani yadda "Baba gen da "Baba eng suka banbanta,

Saboda "Mama tace mun "sunyi Kama dajuna sosai wai harkaya irin daya suke sakawa, Saboda tsananin kamar su bakowa yake gane su ba, haryanzu mada suka tsufa kaya iri daya suke sakawa.?..

Gaskiya nikuma sona ke nagane su", dakaina batareda "annuna munsu ba.
Dariya Abba yayi tareda cewa?...



๐Ÿ’žLufhat ce๐Ÿ’
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page193-200

END

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)

Alhamdullah!
Alhamdullah!!
Alhamdullah!!! nagode ALLAH daya bani ikon fara littafin nan lafiya, ya kuma bani ikon gamashi lafiya Allah kabani Ladan Abunda Na rubuta,tareda wayanda suka karanta inda kumanayi kuskure kayafe Mani, tareda wayanda suka karanta Ameen.

----------------------------------------
*_ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN:THE STRONGEST WEAPON_*
----------------------------------------

*_only exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_.*


โœ๐Ÿพ


"Tabbas har yanzu ma kaya iri daya su" kesawa, don haka Bari nafada maka yadda zaka gane su kaga "Baba gen baya dariya saidai yanada yawan murmushi, kuma bayada yawan magana,

Shikuma Baba engr yanada magana sosai sannan yanada yawan dariya, nan dai Abba yai tafada mashi yadda suke har suka isa gidan da taimakon Abba tunda baisa gida ba.

Abdul-jabbar yanata Mamaki wannan tangamemen gida haka kusan unguwa guda, haka dai suka shiga Cikin gidan security kuwa gasu nan birjek, bai tashi tsinkewa ba saida suka shiga tamfatsetsen falon dayaji kayan more rayuwa wai ran kashi aljannar duniya kenan.

Cike falon yake Da mutane kasan cewar bayan tafiyar Abba sai Baba engr yasa Waya, yana takiran ya'ya'da jikoki suzo akwai family mitin Saboda haka falon cike yake wasu mabasu isoba tukun,

Abun Mamaki shine saida Baba engr yagama kiran kowa Sannan yakira Daddy, yace yazo shida iyalinsa yanason ganin su yanzu-yanzu.

Shikam Abdul-jabbar gaba daya daburcewa yayi Saboda ganin yawan mutane haka, gashi kuma duk ahankalin su' yana gurinshi.

gurin Y Y k yanufa ya zauna tareda cewa Kai Nawa irin wannan kollo "aisaina buga tuntube nafadi, kallesu fa duk nikadai suke kallo, Cikin rada yace' ka kallesu" da kyau mana meka gani acikin kwayar idanun su?...

"Ahankali ya kalle su" ba'abunda yagani akwayar idanunsu" sai zallar kaunarshi gawani lallausan Murmushi dayake tashi "a fuskokinsu", jikin shi ne yai sanyi "aranshi kuwa fadi yake duk wayannan di yan'uwana ne?.. Oh ashe ni Abdul-jabbar dandangine haka, jiyayi wani irin kaunarsu yadarsu a zuciyar shi Cikin kan-kai lokaci.

"Ahankali yamaida kallon shi gasu" Baba engr aikam sai yaga Baba gen yanata Murmushi fuskarsa cikeda farinciki naganin wannan santalele Saurayi wai jikansa ne, kuma magajin shi

Please Login or Register in order to submit comment