Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa rike da wata firar leda saida ya zauna sannan yamika mata ledar,

Mamaki ne yakamasa saboda kin karban ledan datai ya kalleta yace A ah ungo mana,

Ahankali tasa hannun biyu ta karba tace na meye? batareda ya kalleta ba yace kiduba mana,

Koda "taduba sai taga kwalin Waya Tecno yace kiduba akwai Sim card aciki nasa number ta saida gaskiya banyarda kisaka number kowa acikin ba musamman ma ta namiji saidai ta yah "Himu kawai sai kuma nasu "Hanah da "Haleeh,

Ya kalli agogon hannunsa yaga 60:30pm yamike tsaye tare da cewa zantafi itama tamike tsaye tace nagode Allah yasaka da Alkhairi ina gaida "Mama da baba "Lami yace OK zasuji,

Saida taga tafiyar sa sannan tashiga gida zuciyar ta cike Da kaunar special dinta....




๐Ÿ’LUFHAT Luv your All FAN๐Ÿ’ž
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

Page51-55


NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)



edited by Zainuddeen zain


------------------------------------------
ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION


PEN:THE STRONGEST WEAPON
------------------------------------------


only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers




โœ๐Ÿพ




Koda Humeeh tashiga gida ta iske Umma bakin murhu ta nayi masu girkin dare,
Dakin tashiga tacire hijab dinta tareda ajiye wayar sannan tafito don ta taya Umma Aiki.

Bayan sallah magrib suna zaune abinci sukeci akwano guda Humeeh itada Ummanta, bayan sungama ne sai Humeeh ta tattara kwanoni takai su kicin ta'ajiye. bayan tadawo sai tashiga daki tadauko wayar da "Abdul-jabbar yabata bayan ta zauna ne saita mikawa Umma wayar tareda yimata bayani....

Shuru Umma tai tareda jujjuwa wayar sannan tace toh" Humaira nifa bana san karbe-kaben kayan samari, tsayama dai tukun na inafata dai ba rokon sa ki kayiba?

Da sauri Humaira tace a ah Umma niban rokesa" ba, Umma tace ah toh" domin ni gaskiya banason roko saboda yana zubarda kima da darajar ya'mace a idon samari.
Allah Umma ni barokonsa naiba shi yabani dakansa,
Toh" shikenan yanzu abinda nakeso dake shine kibari yayan kin" yazo saimusan yadda za'ai kinji KO?

Murmushi Humeeh tayi tace toh" Ummana yanda duk kikace haka za'ai,

haka suka cigaba da hira har aka kira sallar isha'i suka tafi yin sallah.


*****************
Koda yah Himu yazo week Umma tayi masa bayanin kan wayar Da "Abdul-jabbar yaba Humeeh, baice komai ba... saidai yace abata tayi amfani dashi saidai takula dakainta tatsare mutuncinta.

Toh tunda ga wannan lokacin kuma sai soyayyar su itada "Abdul-jabbar yakara karfi,

Koda yaushe suna makale awaya KO Abdul-jabbar baige gidansu Humeeh toh" za'asha soyayya tawaya,
Sun shakuda juna sosai har sunajin idan daya yarasa daya tofa sai a slow,

Ah soyayya sukeyi kamar bagobe suna tsaka da Soyayyarsu kwatsan sai wani lamari ya shiga masu.

Wata Rana Abdul-jabbar yaje gurin Humeeh bayan sun sha hirarsu Wanda aran nan hada Hanah akayi hirar kasan cewar sunzo, saida ita Haleeh ta tafi gida dawuri saboda Hajiyar ta tace takoma gida dawuri zatayi mata aiki saboda haka sai bata dadeba ta tafi don hakane ma bataga Abdul-jabbar din ba. sai Hanah ce kawai tagansa"
Suna cikin hira sai Hannah tace zata tafi gida bayan tafiyar "Hannah da dan mituna kadan sai shima Abdul-jabbar yatafi,


Yana kulle kofar mota sai yaji wata murya abayansa tamkar ta mashaya tace ya kake? Bai juyaba saboda a tunanin sa ba dashi akeba,

Jiyayi ansake fadar ya kake? saboda haka sai yajuya don yaga wakeda wannan murya haka irin ta mayashaya,

Aikam yayi arbada wata yarinya tana sanye da wata Riga body hook da kuma minin siket kafarta sanye Da wani high shoe tarataya kwankan gefe, kanta yaci uban atterch jiki shaya belicin yagaji ga farce zaro-zaro sun sha janfarce fuskar nanko tasha makeup ba kyan kallo. Amma ita kam agurin ta tahadu batada wani fasali sai kace sandar sunuka.

Bayan yakare mata kallo sai kuma yafara tunani aransa wannan kuma wacece haka?

Katse masa tunanin tayi dacewa baka ganeni bane?

Ya kalleta fuskarsa ayamutse yace inafa naganeki,
keh' nibanma taba ganin ki ba sai yau,

Tace Lah kodai kamanta dani? yace eh toh' da alama Na manta dake kam.

Tayi wani yake wanshi dariya tace yoh nice fa Lariya,

Ya tabe baki tareda kauda kai gefe yace toh" Lariya ta'ina kenan?

Dariya tasake yin tace Lah! Kai Abdul-jabbar haryanzu baka tunaniba ?

(Aransa yace ai mutanan kwarar ake tunawa ba'irin kuba), afilikuma cikin kosawa da maganar Yace Ayyah ban tunakiba?


Tace yoh nice" fa Lariya yar Hajiya "Jumma.

Yace oh! Allah sarki toh"sannu fa ya Hajiyar taki take?

Tace Lafiya lau i tacema tace nazo nagaida Hajiya A'i,

Yace toh" Sannu da kokari ki gaisheta, yafada yana kokarin shiga cikin gida.

tace Abdul-jabbar yajuyo batare da ya" amsa, takarasa wurin sa har jikinta yana kokarin gogar nasa jikin.

Dasauri yaja baya domin kuwa wani irin Kari yaji tanayi,

Dariya tayi tareda cewa Abdul-jabbar kanada kyau fa, hannun ta mika danufin shafo kyakkyawan shajansa tace Inason irin wannan abun yanada kya!

Wani uban tsawa yadaka mata Wanda yasatai sauri sauke hannun ta, harara ya watsa mata cikin takaici Yace keh! dalla gafara meye haka?
Batace komai ba saidai ido data tsura masa.

Harara yasake watsa mata tareada jan dogon tsaki mtsww.

sannan ya juyawa yanufi gida cikin takaici domin gaba daya tabasa haushi,cikin rai sakuma yace dafa da wannan kazamin Hannun nata" zata tabani Kai! Amma da tacuceni, yayi kwaf dai-dai lokacin yake bude kofar dakin sa.

Wayarsa ce tayi kara dasauri yaduba sunan daya ganine yasa yai lallausan murmushi. bariyai saida ta katse sannan yakira tareda bude sifika A hankali ya lumshe ido yace my cool yakike?
Cikin zazzakar voice dinta tace Lafiya lau dama Inason naji yaka isa gida?

Yace Lafiya lau Na isa kingama yanzu Na shiga daki.
Tace toh ka huta lafiya ka kuma gaida "Mama da baba "Lami,
Yace ai bazan fadaba. dasuri tace why?
yace kullun fa cewa kike Na gaida su" ya sassauta murya yace please My cool kizo kidai dasu mana dakanki kinji?

A hankali tace nifa kunya nakeji Amma dai zanzo.
Da sauri yace yaushe zakizo?

Tace zanzo very soon Amma dai yanzu kace in gaida su.
yace toh" zasuji tunda kin kizuwa nima kigaidamun da "Ummata tace toh" zataji, sanna sukai sallama ya kashe wayar tareda jefata saman gado sannan yanufi Cikin gida.


Tundaga zaure Lariya take kukan Sangarta tana shiga Cikin gida sai tafara jifa da jakarta da kuma takalmanta, sannan tayi zaman yan'bori a tsakar gida sai kuma tasaki wani kuka Mara dadin saurare.

Da sauri Mahaifiyarta Hajiya jumma tafito daga daki, hartana buga tun-tube da bakin kofa zani a hannun dankwali a hannun.

Da sauri tanufi gurin yartata tadafa kafadarta Cikin tashi hankali tace Lariri ta maiyasa meki? mai akai maki ?
Taya mutsa fuska tareda tura hannun ta Cikin wannan danbanzan gashin dokin tana yamutawa (nabakin tsofaffi ) sannan tace Hajiya ni aure nakeso.

Ajiyar Zuciya Hajiya Jumma tasauke, tace haba Lariri aini Na dauka wani abun akai maki.

Sai kuma
tawashe dafaffun hakoranta wai ita adole dariya take tace A ah abu mai sauki aini nan daki kagan'ni kullum fatana baiwuce naga auran kiba.

Taso zonan kafada Mani kinsamu Wanda kikesone?

Saman wani banci suka zauna Hajiya jumma ido ta tsurama yartata tana neman Karin bayani, Lariya tace eh nasamu.

Tace toh"- toh" wanene shi? tace Abdul ne, tace wani Abdul din? tace Abdul-jabbar Dan wajan Hajiya A'i.

Aikam tasake washe bakin tace A ah kice tuwona maina za'ai kenan KO?
ta daga Kai alamar eh, tace toh" shiyace yana sanki? tace eh Ai mun kwana biyu muna Soyayya bandai fada maki bane saboda inajin kunya.

Nikam saboda Tsabar mamakin jin Abunda Lariya tafada harsaida birona yakusa fadiwa kasa, DA sauri narike tareda tsura mata ido ganin yadda take kauda kai gefe ita adole kunyar takeji

Tabdi sunan wani waishi "zubairu(ah ita" kam wannan zubairace)

Hajiya Jumma ta washe baki tareada dukanta" kadan akafada tace yar'nema kunyar me? shakuru minki indai "Abdul-jabbar ne kamar kin auresa' gobe zanje nasamu Hajiya A'i sai mutsara yadda za'ai kinji KO? tace toh"


Nasan dai mai karatu zayaso yasan WACECE Hajiya Jumma tare DA yarta LARIYA, Hajiya Jumma mutumiyar Buruku ce tanan Cikin garin Kaduna Hajiya Jumma macece mai zaman kanta saboda San abun duniya yasa tabaro garin iyayanta Buruku tadawo nan Cikin kaduna dazama.

Hajiya Jumma irin matan nan ne masu auren Mutum badan Allah ba saidan Abun hannun shi batada wani kyau, asalima bakace sosai gata batada hanci saidai kam tanada dirin Allah yaimata Kira mai kyau.

Wanda dashi take cutar duk Wanda yace yana sonta dazar kace kana sonta toh" shikenan saitabi boka DA Malam ta aure ka bayan ta aure ka idan kanada iyali sai tarabaka DA iyalinka, sannan ta mallakeka ta kuma rabaka da Abunda ka mallaka daga karshe kuma taraba ka da rainka Hajiya Jumma kenan muguwar mace ce ta iya shiga bokaye da Malamai sosai

A hakanan ta mallaki dukiya mai tarin yawa tasayi gida tasayi adai-dai tasahu har guda uku take bada haya ana kawo mata kudi,

kuma tana zuwa kano saro kaya su atanfofi dasu lesissika dadai sauransu.

don haka Cikin lokacin kankani tayi kudi hartaje makka inda acan'ne suka hadu da Hajiya A'i mahaifiyar Abdul-jabbar suka kulla aminta.

bayan sun dawo makka ne sai Hajiya Jumma taci gabada kasuwancin ta inda Allah ya hadata dawani Mutum mai suna Labaran, yanuna yana santa wani abun mamaki shine itama Allah ya jarabe tada navigate sanshi cikin lokaci kankanidon haka ba'adauki wani lokaci ba aka saura masu aure.

Bayan kwana biyu da yin aure sai Labara yazoma Hajiya Jumma da Labarin cewa anche Lagos tafi kano saukin kaya, saboda haka takawo kudi yaje yaraso mata kaya acan aikam saikace wadda yaima asiri(dayake yafahimci cewa itadin gurin kudi batada sauki)

aikon tawashi kudin ta tabashi harda sayarda adai-dai sahunta guda biyu duk tahada kudin tabashi yatafi.

Aure da Albarka
Bayan tafiya Labaran da sati uku sai Hajiya Jumma tafamci cewa tanada Ciki,
Saboda haka murna kamar ya kasheta.

Tunda duk aure-auren datayi bata taba haihuwa ba sai wannan, saboda haka saita maida hankalin ta gurin kulada Cikin ta.

Har Cikin ta yakai wata hudu ba Labaran ba labarinsa,
(Hmmm Abunda Hajiya Jumma bata saniba shine Labaran rikakken Dan cacane kuma mane min matane,
don haka koda yaje Legos Abunda yai tayi kenan da kudin.

Saida Cikin ta yakai wata biyar sannan sai gashi yadawo, dawasu yankaya wayanda KO Rabin-rabin kudin daya yaje dasu basu Kai ba.

Aikam sun kwashi yan'Kallo domin kuwa mutane ta tara masa tana taimashi masifa akan sai yafito mata da kudin ta tunda bai saro mata kayan ba, sai faman masifa take bata kodamu DA Cikin dake jikinta ba.

Shikam dayake tantirin Dan duniya ne sai ya kalalla meta dace mata aikayan yana siya yana sayar wane acan kuma anasamun riba sosai.

yanzu hakama yasiya yabarma abokinsa yakula masa dashi. yanzu ma Abunda yasa yazo saboda yanata tunanin ta dakuma mafarkinta shiyasa yazo don yaganta shine acikin kayan yataho mata da wannan.

Aikom sai tashiga washe baki ita adole miji yadamu da'ita, bayan kwana biyu yakoma.

Besake dawowa ba harta haihu inda tasamu ya"mace mai Kama DA babanta tasamata suna LARIYA" tasha wahala sosai godiyan ta guda adai- dai sahun da'akeyi mata haya Ana kawo mata kudi.

Saidai Lariya tashe Kara biyar sannan Labaran yadawo batare dakomai ba DA gashi sai kayan jikinsa, duk yacinye mata dukiya.Hajiya Jumma taimasa tarba mai kyau kamar babu komai aranta abun yabashi mamaki sosai.

A wannan lokacin kuma tuni Hajiya Jumma tasangarta Lariya sosai
Ta dauki San duniya tadora akan Lariya tareda wani buri marar amfani tana kula da'ita sosai irin kulawan nan Wanda bakomai acikin sa sai zallar rashin tarbiyya.


Tunda ko makaranta taje idan tai badai-daiba akai mata fada sai Hajiya Jumma take har makaranta tai ta masifa wai saboda meza'a takurama yarta,

Su kam malamai dasu kagaji sai suka koreta a makaranta.
Hajiya Jumma tace yoh sai me don sun koreki yi zaman ki nima uwarki ai banyi karatu ba kuma gashi Ina rayuwa ta kamar kowa.


Bayan kwana biyu da dawowan Labaran sai Hajiya Jumma ta fahimci Labaran yana matukar kaunar yar tashi duk Abunda yasamo toh" Na Lariya, ne kuma har zuwa wannan lokacin batace masa komai ba akan dukiyar ta da yacinye.

Akwai wata Rana yadawo sai yakira Lariya bayan ta zauna sai yamika mata kunshin Laida Ashe tsirene aciki aikom sai tabude tafaraci,
tana Cikinci sai Hajiya Jumma ta kallesu sai tayi murmushi tace Laririta zonan,
Aiko sai ta tashi yanufi gurinta,ta dorata acinyarta tare da daukar guda tasaka abakinta sannan ta kalli Labaran Wanda shima suyake kallo ita DA yarta ta.
Hajiya Jumma tahade girar sama da kasa ma'ana tabata fuska kamar bata tabayin dariya ba,
Cikin daga murya tace...?




๐Ÿ’žLufhat Ce๐Ÿ’
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page 56-60

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’FARUQ
OR
(MEENAT)


edited by Zainuddeen zain


------------------------------------------
ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION


PEN:THE STRONGEST WEAPON
------------------------------------------


only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers



โœ๐Ÿพ



LABARAN! wai kana nufin dukiya ta dakaje kacinye kaci banza kenan? bai bata amsa tambayer taba, saidai jajayeb idosa daya tsurama ta yayida yaji kirjinsa yafara dakan Uku-uku, Ahankali yace Ashe ranan zatazo?

Nikam dake gefe nace tabdi Labaran ai dole wannan ranan tazo domin kuwa KO kudin Uwarka kacinye sai tayi maka magana toh" ballantana matarka.

Wani killer smile Hajiya Jumma tayi Wanda yasa kirjin Labaran ya cigaba da matsananci bugawa, domin tunda yake da ita bai taba ganin tayi irin wannan murmushi ba,
Saikuma yagata daure fuska tace nasan bakada amsar bani tunda kana ganin kacinye Mani kudi kaci banza kana nufin nadauki hakuri ko? tabdi
Toh wallahi baka'isaba bazan dauki hakuri ba "Ai Hajiya Jumma ba'ai mata Abu tayefe Ina Labaran kayi kuskure idan har kayi tunani cewa zan yafe maka a ah, bana yafiya, kowa yaimani kankara toh" ni sainai masa Na itace yanzu kam nasan konace kabiyani kudi Na nasan baka dasu, saboda haka kaga wannan? tanuna Lariya dake kanciyarta sai cin nama take ba Abunda yada meta,
tace yarka ita ne madadin kudina da kacinye,
Cikin karfin hali yace aikema yarkice tunda ke keka haifeta, tayi dariya tace tabbas ya'tace saidai kabar tunani cewa Nina haifeta, saboda ninan daka ganni gurin KUDI banida mutunci saboda haka babu Abunda bazan iyayi ba indai akan kudi ne.
Cikin tsoro dajin kalamanta yace toh"Zaki siyar da'itane KO" me zakiyi da'ita?
Tai shewa tare da dariyar mugunta tace Allah nadawo inji Dan cirani Labaran Uban Lariya mai kakeci nabaka nazuba Bini Ahankali DA SANNU zakaga Abunda zanyi da yarta ka,

Ta tashi tare da tajan Hannu Lariya suka nufi daki tabarshi nan cike da tsoro da kuma tunani Abunda zata'aikata da Lariya din.


SANNU ahankali rayuwa tai ta tafiya Lariya tazama cikakkiya Budurwa a wannan lokacin kuma tuni tazama tantiriya yar'iska bin maza take bihakki DA gaskiya Wanda hakan ya farune Da taimakon Uwarta,
Wanda Labaran yayi fada yayi zagi hada su duka Amma duk abanza.
(Allah yasa wake Amin).

Nikam nace toh"ai dama Kama titdina tidan duk abunda Kai sai Anyi maka
(Allah yasa

Sanadiyar hakane yasa Labaran kwantawa mummunan rashin Lafiya Wanda har saida yakai shi dabarin duniya,

ko" bayan mutuwar sa baisa Hajiya Jumma itada yarta Lariya sun saduda ba, saima Abunda yai gaba sai azo har gida adauki Lariya saitayi kwana DA kwanaki sannan, tadawo ma Hajiya Jumma da kudi sosai, shikam ciki gurin zubar dashi tuni ta zama customer.
Wannan shine takai tattace tarihin Hajiya Jumma da yarta Lariya,

Yanzu gama yawace-yawacen ta aure takeso kuma ba wanda take so sai Abdul-jabbar, tabdijam toh" bari mugani abun zayayuyu kuwa?

Washegari tun misalin karfe goma Na safe Hajiya Jumma ta isa gidan Hajiya A'i,da sallamar ta tashiga parlor Mama na zaune ta kallo atashar MBC Bollywood,

Sai jin sallama tayi Ahankali ta amsa tare da dagakai sai taga Hajiya jumma, hakanan kawai sai Mama ta tsinci kanta dajin faduwar gaba saka makon ganin Hajiya jumma, Amma kuma sai bata nuna mata ba,

Saidai tace a a" yau Hajiya Jumma ce agidan namu? yayi dariya tace kedai nice fa, dai-dai Lokacin data zauna
Bayan sun gaisa sai Hajiya Jumma tace "ke dai kinganni tunda sassafe "KO? Mama tayi murmushi tace "eh "ai jiyama Lariya tazo tai gaida ni aina gode Allah dai yabar zumunci,

Hajiya Jumma tayi murmushi tace "ai kedai bari gawani zumunci ma zaya kara kulluwa,
Mama tace toh" daga ina kuma?

Tace Hmm Ashe yaran nan Suna San junan su bamu saniba"?
Cikin rashin fahimta Mama tace wasu yara "kenan fa?
Dariya tayi tace Abdul-jabbar mana shida Lariya,
ita kam Mama jin maganar tayi tamkar Almara sai tace toh" lallai kam nibansani ba,

Ta washe baki tace "eh KO" nima bansaniba sai yau Ashe ma hada alkawarin aure sukai ma junansu", Mama tace toh" kice magana ta girma?
Tace Hmmm kedai bari "ai abun yayi dadi kinga shikenan sai "ai tuwona maina,

Mama tace kinga nikuma banga alamar faruwar hakan ba,

Da sauri Haj jumma tace saboda me? yasa ki kace haka Haj A'i?

Saboda tarbiyyarsu tasha ban-ban ke kanki kinsa cewa " "Lariya batada ce da shiba, ba wannan ba kinsani sarai cewa "Lariya batada tarbiyya duk kin bata yarinya Sam ba kiyi mata tarbiyyan kwarai, ba jifa jiya yadda tazo gidan nan kamar ba diyar muslmai ba, gaskiya Yaron nan bazaya auri Lariya ba.

Ita kam Haj Jumma idan ranta yakai dubu toh"yabaci DA jin kalaman Mama,

Sai ta kalleta rai abace tace Haj A'i yanzu Abunda zakice Mani kenan? tace " aike kinsa abunda nafada gaskiya ne,

Tace toh" "ai shikenan bakomai nagode nizan tafi tafada ranta bace tare da mikewa tsaye,

Itama" Mama mikewa tsaye tayi tareda cewa a a" har Zaki tafi kenan?
Tace Ummh dai-dai Lokacin da takai bakin kofar fita,

Mama tace toh"sai anjima ki" gaida gida, bayan ta" koma tazauna sai tace "ai "shikum zata shigo yasameni idan bayada ahankali ne toh" "ai nagani,

Duk yan'matan cikin garin nan yarasa wadda zayayi Soyayya da ita sai "Lariya, ko"me yagani ajikinta" daya birgesa Rashin tarbiyya? ko" kuma rashin Kamun kai? "oho masa.

Sai misalin karfe 11:15 Am sannan Abdul-jabbar yashiga cikin gida, yana sanye da Riga T.shat white da wandon jeans black hannun rige da key mata sai zuba kamshin yake,

Saida ya zauna ya Lankwashe kafafu sannan yace Mama Ina kwana?
Ta amsa rai bace da Lafiya lau,
idanu tsura mata domin yaga ranta kamar abace,
Saboda haka sai yace Mama meya faru naga kamar ranki yabaci?

Tace "ai ba Kama bane raina abace yake sosai, yanzu saboda Allah duk yan'matan garin nan karasa wadda zakai Soyayya sai "Lariya
Kai KO" mekagani ajinta" daya birgeka?

Big eyes dinsa yazaro,Wanda har saida yasa taji faduwar gaba saka makon tuno mata wani Abunda idanun sa yayi, ga kuma wani irin kwarjini da sukai mata.

Don haka DA sauri takauda idonta daga barin kallon sa,

yace Mama "Lariya fa ki kace? Cikin jin haushi tace wannan wani irin abune haka Ina tambayar "ka kana tambaya ta?
Ko" baka game "Lariya yar gurin Haj "Jumma ba?
ba harda alkawarin aure Kai mata ba?

Yace kiyi hakuri Mama nagane ta" jin abun'nayi kamar Almara, niko" me zaya birgeni ajikin "Lariya da zayasa nayi Soyayya DA ita,"har nayi mata alkawarin aure?

Hmmm Mama ke dagajin wannan Magana kinsan ba gaskiya ba ne,
Haba dai tabdi
God for forbid nayi Soyayya da "Lariya har nai mata Alkawarin aure,

Yarinya DA batada kamun Kai kowa yatashi sai yakwashe ta, sai Dan banzan yawo wato
Yanzu tagama yawace-yawacen ta zatai aure sai nikuma nakwasa, tunda banida kowa KO"? toh" bawai hakan yana nufin nakai kaina ga halaka bane,
Yaja dogon tsaki mtsww
Kai amma dai yarinyar nan taraina ma kanta"hankali
Toh"nima ida baji dana ganta ba a kofar gida nan harna manta dawata "Lariya yai kwaf,

itakam mamaki abun yabata don haka,sai tace kana nufin kace Kai bakata ba zuwa gurinta ba?

Cikin takaici Yace haba Mama me zanjeyi gurinta? ke kanji kinsan bata dace Dani ba ,ya kuma Jan tsaki mtsww sannan yace Allah Maya hadani da'ita sai naci mutuncinta.

Tace a a" karabu dasu duk abinda suke nufi ya kare Kansu, ya mike tare da cewa nizan fita, tace toh" sai kadawo.

Shuru Mama tayi tana nazarin maganar da Haj "Jumma tazo mata dashi,
Jitayi gabanta yafadi saka makon tunawa da tayi kowacece Haj "Jumma,

Ahankali tafara tunani wani lokaci da "Haj Jumma tazo gidan ta bayan sun gaisa,
Sai tace ke KO" Haj A'i meyasa bazaki auri Alh ya'u nakaka ba? gashi acikin Bari anata maganar yana sanki sosai,

Mama tace saboda bana ra'ayin aure,
Haj Jumma tace
Kinga idanice ke KO"? wallahi auransa zanyi, Mutum mai kudi irin "Alh ya'u nakaka tabdi "ai bazan barsaba, kinga idan kina tsoron matarsa ne toh" kisha kuruminki", ninan daki kagani nasan bokaye da malamai Kala-Kala saboda haka kizo muje nakai ki" gurin boka yan miki maganin ta",
ke" bama ita kadai ba har dashi" Alh ya'u Na kakan sai boka ya asirce mikisu, Ke koma kashesu" kikeso ayi boka zata iya.

Da sauri Haj A'i tace "a ah Haj Jumma kisafa kikace?

Tace eyi "yoh toh" meye? tace gaskiya nibana zan iya kashe mutum ba,shiko" harka Da boka Da malam ban iyasaba kuma banason Na iyashi har abada, bama haka ba ni aure ma baya gabana saboda hakanan mubar wannan maganan.

ajiyar zuciya tayi tareda dawowa daga dogon tunani datake,
tace toh" ni bansa Abunda "Haj Jumma take nufiba da tace "Lariya suna Soyayya DA wannan yaron ba toh" me hakan yake nufi?


Itako Haj Jumma rai abace ta isa gida Lariya ta tambaye ta yadda sukai da Haj "A'i ? nan tafada mata komai "aiko Lariya sai tasaki kukan sangarta tace itakam wallahi idan ba "Abdul-jabbar bazata auri kowa ba,

Haj Jumma tace kwantar da Hankalin ki indai "Abdul-jabbar ne sai kin aure sa kota halin kaka, badai Abunda Haj A'i tace Mani kenan ba? toh" sai tazo gidan nan daka farta taro keni ki auri danta, da alama ta tamanta KO" wacece Haj Jumma toh" Amma zantuna mata,
tashi kitafi abunki.


****************

Bayan kwana biyu
Abdul-jabbar ne zaune Shida Humeeh firarsu suke ta masoya, sai ya kalleta Cikin So da kauna Yace my cool idan muka tafi zanyi kewarki sosai fa.

DA sauri ta kallesa tace Ina kuma zaka tafi? yace kin manta nafada miki cewa zamuje America yin wani cos? tace "eh natuna yaushe zaku tafi? yace nanda three weeks,
tace Amma dai baza kodade ba KO"? ummh one year ne kawai, DA sauri tace shekara daya ne kawai? tafadi haka ne kamar zatai kuka.

Ahankali yace my cool idan akwai raida lafiya shekara daya a gurin Allah kamar yaune,
saboda haka karki damu very soon Zaki ga mundawo insha'Allahu,

Ke nimafa don tafiyar tazama dole ne, idan badan haka ba dasai nayi zamana muyita Soyayyar mu KO"? yakai karshen maganar sa dayi murmushi,

itama murmushi tayi tare Da rufe fuskarta Da hannun alamar kunya, hakan sukaci gabada fira har tsawon wani lokaci sannan yatafi gida.


Mama ce keta faman safa da marwa a tsakiyar parlor, kallo daya zakai mata kafahimci cewa hankalin ta atashe yake,

Koda Abdul-jabbar yashiga ya isketa Cikin wannan halin,

Ya kalleta tare da cewa Mama Lafiya?
Cikin tashin hankali tace sonake yanzun nan Kai maza-maza katafi gidan "Haj Jumma kudai-daita juna kaida "Lariya,

DA karfi Abdul-jabbar yace eyeeee?



๐Ÿ’žLufhat ce๐Ÿ’
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

Page61-66

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’FARUQ
OR
(MEENAT)

edited by Zainuddeen zain

------------------------------------------
ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION

PEN:THE
STRONGEST WEAPON
------------------------------------------

only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers



โœ๐Ÿพ



Shidin ne" bayada Uba? Haj Jumma tade fuska tace "eh "shidin mana, yoh yanada ubane idan kuma kince yana dashi toh" yana ina" Uban NASA"?

Mama tace haba Hajiya yazakice bayada Uba wallahi yanada uban sa kamar KO wani da dakikasani,


Tace Hmmm Haj A'i kenan inada labarin kifa kaf, tunda kikazo garin nan yau kimani shekaru kusan talati Amma baki taba zuwa gida ba,
sannan kuma wani dan'uwan ki be taba zuwa gurin ki ba kinga hakan yana nufin kinyi abun kunya ne, shiyasa ki kabaro garinku ki kadawo nan dazama KO?

Itakam Mama komai ya kwance mata saboda haka sai tarasa abunda zatace,
tabbas a Cikin

Please Login or Register in order to submit comment