Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakin ciki Da bacin rai.

Domin shikam yasan baici sisin kwabo acikin makudan kudin da suka salwanta ba, saidai kam yana zaton "mataima kinshi, koda yake ance zaton zunubi koda ya kasance gaskiya Amma dai kam yana zarginshi dasa hannun shi acikin lamarin,

Tunda "yanuna baya kaunarshi, tun lokacin Da akarbi matsayin shina manager akaba "Abban su Humaira,toh shikenan ya dauki karanta tsana yadore mishi

shiyasa Abba yayi tunnan KO shine toh kaidai wanene yake da sa hannu acikin wannan lamarin Toh yabarshi DA Allah.


A haka su "Humaira suke Rayuwar Cikin matsananci hali inda hartakai aka kiresu daga school din dasuke, tunda basu biyan kudi dayake su private school baruwan su dazar time yayi Toh abasu kudi.

Dama "Alh Musa kedan taimaka musu toh shima iyalin shi sun'isheshi mata biyu dayara bakwai gashi shima karayar Arziki yasame shi, don hane maya Ko mai yakara jagulewa,

Dole badan sunaso ba suka koma wata government school tunda shi bawani kudi ake biyaba,

A haka har yah Himu ya kammala S.S three din shi da taimakon Malam wato mahaifin Umman su dayake yah Himu yasamu result me kyau, Don haka Malam yasamar mishi Admission a A b u Zaria don yaci gabada karatun shi inda yake level one yanzu haka sunyi hune yana gida ita kuma Humeeh tana S.S two yanzu,

A yau ranace datake sance ranan aiki ga kowani ma'aikacin government Kai harda students wato yan makaranta, ranace wadda Malam bahaushe keyima kirari da cewa KO bature na tsoronki wato Monday.

" Wata yar kyakkyawar matashiyar buduurwace yar kimani shekara goma sha hudu zuwa sha biyar farace Itaba doguwaba ita kuma bagajera ba fuskarta Dan dai dai tana dauke Da manyan idanu Amma ba sosai ba, tanada Dogon hanci da Dan karamin baki Wanda idan tayi dariya kamar kada tarife bakin, badan komai ba saidan open teeth din datake dashi sama Da kasa wanda ya karama fuskarta kyau Da kwarjini, ga kirjinan Nata Kam hmmm! ba'acewa komai domin koh cike yake Da dukiyar Fulani zaka fahimci hakane ta yadda suka dago hijab dinta,

Sanye take Da school uniform riga Da wando Da hijab, rigar da hijab din fararene shikuma wandon me ruwan kasane, Tara taya irin jakarnan da yammatan yanzu suke yiwa lakani da swaga bag ko kuma suce wankan gefe Humaira kenan yamma tan "Umma.

Kallo daya zakai ma kyakkyawar fuskarta kagane cewa da'alama yau bata jin zuwa school din, zakafahimci hakane daga ya nayi yanda take tafiya Ahankali tamkar bata son taka kasa,

A hankali take kokarin shiga kwarda zatafita Da ita bakin titin dazata hau adai dai ta sahu,

Toh kuma a wannan lokacin ne hanci wata mota kiran Honda civic yar karama new model takunno cikin tsautsayi kaji fachauuu daruwan kwataaaa!

Tunda ga kasanta har saman gaba daya school uniform din jikinta yabaci Da ruwan kwata, Allah yasota bada beauty fice din tabah a hankali tadago dakai don taga "waye kedai wannan Aikai- akan?

Dai Dai lokacin da "yafito Cikin mota domin tuni yayi parking gefe yanufo gurinta,

Ta tsura masa ido farine Dogone kuma mikakke yanada tsayayyu kafada masu birgewa ma'abucin faffadan kirji da kakkauran jiki, sai kuma yadan Rankwafa kadan ta yadda zubin halittar shiya bada kirar wani Mutum mai tsararren tsayi mai ban sha'awa,

Kai kace wani bako ne daga karasar Lebanon, gawani saje daya aje wadda takarawa kyakkyawar fuskarshi me dauke da eye balls da Dogon hanci kyau da kwarjini,

shekarun shi bazasu wuce Ashirin da takwas zuwa da taraba yana sanye da Riga t-shart white and wandon jeams black. Abdul-jabbar Ahmed kenan
Mashi saurayi me jini ajika,

Cikin lokaci kankani takare masa kallo Ahankali tadukar Da kanta kasa, A dai dai lokacin da yakarasa gurinta,
Cikin muryarsa me dadin saurare Yace eyya please Am so sorry ban kula dakeba wallahi, ahankali tadaga Kai ta kallesa aiko suka hada ido at the same time jitai gabanta ya fadi shima Abdul-jabbar hakata kasance agaresa, Da sauri ta dukarda kanta kasa tareda cewa it's ok,
Sannan tajuya da sauri
tafara tafia,
Yayi Dan taki kadan ya isa gareta badon komai ba saidan yasake jin daddadan muryanta, ahankali ciki rada yace sorry once again,
Batare Da ta juyoba tace I say it's ok sannan tacigaba da tafiya ya tsurama bayanta ido duk Da cewa tana sanye da hijab hakan be hanashi hango kugunta yana motsawa ba,

Yana tsaye harta shiga wani gida me dakali biyu ahankali yasauke nauyayyan ajiyar zuciya sannan yajuya yanufi inda yai parking motar sa.

Itakam Humeeh kallo daya zakai mata kagane cewa kiris take jira tafashe da kuka,

Aikam tana shiga cikin zauren tafashe Da kuka Wanda kanajisa kasan Na sha'gwaba ne,
"Yah Himu da dakin shi yake cikin zauren yanaji kukanta yafito da Sauri haryana buga tuntube da bakin kofa,domin kuwa idan akwai abunda yatsana to baiwuce kukan Humeeh ba,

Lokaci guda yajero mata tambayoyi kamar haka meyasa meki? me'akai miki? kedaw! Maganar ta tsaya saka makon yadda yaganta,

Da Sauri ya karasa gurinta tareda cewa kut! "wani Dan renin Hankali ne yai miki wannan wulakanci?
Cikin sha'gwaba tace "wani ne yanhhh aibai jira takara Saba ya shuri takalma da sauri yai waje

Cikin zafin nama yah Himu yakara sa gurin Abdul-jabbar dake ko Karin shiga mota sai yaji ance dakata Malam,

Da sauri yajuyo suka hada ido cikin daurewar fuska yah Himu yace haba don Allah Malam wannan wani irin abune haka meyasa idan kuna driving Baku kallon hanya da kyau ne?

Dubi yadda kabata mata school uniform yanzu shikenan Kai mata hasarar zuwa school yau,

Mtsww yaja tsaki sannan yaci gabada dacewa kudama ya yan masu kudin nan haka kuke some time sai kurika daukan yayan talaka abanza,

Abdul-jabbar dayake sauraran shi tunda yafara baice komaiba saida yaga yakai ayah sannan,
Yace Toh" kuyi hakuri bansan tana tahowo ba nikuma nariga nakawo shiyasa,
Yace toh idan bamuyi hakuri ba yaza muyi tunda kariga kagama, yajuya yanufi gida yana gunguni fada.

Shikam Abdul-jabbar bin bayan sayai da kallo harsaida yashiga gida,
sannan ya bude mota yashiga yaja yai tafiyar sa
Wannan shine silar haduwar Abdul-jabbar DA Humaira.




💐LUFHAT ce I Love all FANssss💞
💞💐💞💐
💐💞💐💞💞
DA SANNU

💞💐💞💐💐
💞💐💞💞

💐page36-40💞


NA

💐MEENAT 💞UMAR FARUQ💐



Assalamu'alaikum
Masaoya wannan littafi kuyimun hakuri narashin ganin posting din na jiya saboda banajin dadin jikina, Amma yanzu Alhamdullah. sannan kuyi hakuri
Na chanja tsarin littafin hakan yafaru ne saboda wasu basugane sunan littafin ba, so dafatan hakan bamatsala NAGODE SOSAI.



Wannan page NA sadaukar DA shiga duk Wanda yagane SUNAN WANNAN LITTAFIN nagode kwarai dako karinku nagane sunan book din wato DA SANNU.




edited by Zainuddeen zain

----------------------------------------
®PEN WRITERS ASSOCIATION


PEN:THE STRONGEST WEAPON
----------------------------------------


only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers




✍🏾





Koda Humeeh tashiga cikin gida Umma tana duke bakin fanfo tana wankin kayansu,

saijin sallamar Humeeh tayi" ta amsa tare da mikewa tsaye tace ke kuma lafiya ki kadawo baki tsoron ki Makara?

Tajuya ta kalle ta ganin yadda take ne yasa tace A ah ya'akai kuma hakata faru?

Cikin kukan Sha'gwaba tace bawani" ne yawatsa Mani ruwan kwata ba?

Umma tai murmushi tareda girgiza Kai tace Toh" shine kuma abun kuka?

Ta turo baki tace Umma kalli fa "yanda duk yabada Mani school uniform dina,


Umma tace hmmm "Humaira kenan "toh" yazakiyi da kaddarar Ubangiji?


Tasake turo baki kadan tace "toh" shikenan fa yau barani school ba,

Umma tadan ja tsaki mtsww tareda cewa toh" sai meh? Dama yau bakiyi niyar zuwa makaranta ba ai ina kula dake tunda kika tashi,
Saboda haka sai kicire kayan Na wanke.


Dai dai lokacin da yah Himu ya shigo yana fada, Umma ta kallesa tace Kai kuma fa Kai dawa ne?

Yace Umma nida wannan "guy din nan mana daya watsama Humeeh ruwan kwata Dan renin hankali kawai, yai kwaf"

Umma data zuba masa ido saida yakai Aya, sannan tace yanzu zuwa kayi kukai tashin hankali ko? banasan haka fa

Yace Umma nifa ba tashin hankali natafi mukayi ba, kawai da nafada masa" irin haka dasuke be dace ba ya kamata surika kula.


Ya kalli Humeeh yace tafi kitube kayan kikawo Na wanke maki kinji my sister?

Tace toh tanufi daki don ta tufe,

Shikuma yanufi wurin Umma yana cewa "Umma wanki ki kikeyi Ina daki baki kirani nayi makiba?

Tace eh ai bansan kana nanba, yace Ina nan banfi taba, dai dai lokacin da ya tattare hannun Rikarsa yaduka yafara wankin.



Cikin nitsuwa yake driving zuciyar sa cike da tunani "Humeeh Ahankali ya furta is beauty "she have a Sweet voice sai kuma yasaki lallausan Murmushi tareda Shafa suman kansa sannan yace ko meye
sunan ta?

(Nikam dake gefe nace oho "kaji shi daga ganin Sarkin fawa sai meya tai zaki.?)
Chan kuma sai ya hade fuska sannan yai tsaki mtsww" saboda tuno kalaman "yah Himu,

Yace kai kaji "guy din nan fa? Don yaga wannan motar shine hada wani cewa yayan masu kudi,? toh" nima Arzikinta naci akabani Ni din'ma aidan talaka ne, yai kwaf."

"Yana tafe yana surutu harya karasa unguwar su Y.Y.K yai hon mai gadi "yabude masa get yashiga bayan sun gaisa da "baba maigadi sannan yakarasa ciki,

Bayan yayi parking sai yakashe "motar sannan yanufi cikin gida,

Yai sallama yashiga Y.Y.K suna zaune shida Jamila matar sa ya amsa tareda daga Kai ya kalle sa,

Magani yake ba "Jamila dayake tana dauke da tsohon ciki Haihuwa KO yau KO gobe."

Saida ya zauna a daya daga cikin kushin din falon sannan ya kalli "Jamila cikin sigar zolaya yace sannu tsohuwa!

Ta Dan harare sa kadan tace "wace tsohuwa?

Yace ah "kemana, tace koh dai Kaine tsohon ba?

Yai murmushi yace ah haba
dai ki kalle nifa da kyau yaro dallele Dani kice mani tsoho,

Tace tabdi lallai kam A haka kake kiran "kanka yaro hada wani dallele bayan kakusa zama baba,

Saida yai dariya sannan yace gaskiya kam toh barina Dena kiran kaina yaro tunda yanzu Na kusa zama baba KO?

Tace a"toh da dai yafi kam,

Saidai gaskiya kidena kirana tsoho domin ni aiba tsoho bane,

Wanda zaya kwanke yammatan uku nan gaba shine za'akira da tsoho? yakai karshen maganar dayin dariya"

Tace oho Ashe babu dadi "ni aka kirani da tsohuwa?

Sannan ba "yammata uku zaka wanke ba ko goma ne ba abunda ya dame ni" kuma nima adena kirana tsohuwa,

Yace ah ke "kam ai tsohuwa ce ke bakiga yadda kike zama dakyar tashi dakyar ba,

Sannan karki damu da
"matan daza'a karo Asalima ba'akanki fa zasu zaune ba"

Harara ta watsa masa cikin wasa sannan tace dama ya za'ai "su zauna akaina saidai kam "su zauna kan Wanda "ya daukosu"

Dariya yai yace "toh shikenan tunda kan Wanda ya daukosu zasu zauna,

Itama dariya take tace yasu "Mama da baba Lami?

Yace suna Lafia tace "toh madallah dai dai lokacin datake Ko Karin tashi dakyar,

Yace kin gani ba?
Ance ke tsohuwa ce kince "a ah,

Tai murmushi tace kaidai kasani "Abdul-jabbar nikam nashiga daga cikin in kakoma ina gaidasu "mama.

murmushi yai yace "toh" Uwan biyu zasuji azauna Lafia."

Y.Y.K dariya yake masu sannan ya "kalli Abdul-jabbar yace Nawa kenan
Kadai ya'iya zolayar my "Dear har kagaji,

"Toh ya akai ne"? naganka tunda sassafe I hope dai lafia ko kayi mafarkin My "Dear ta haihune? yakai karshen maganar sa da yin dariya"

Shima Abdul-jabbar dariya yai yace kaidai bari Nawa narasa yadda aikai yau nafito Tunda sassafe haka,

Saidai ga dukkan alama fitowar mai sa'ace domin ko nayi babbar tsintuwa,

Y.Y.k yace babbar tsintuwa ta me kenan?

Nan "yabashi labarin abunda yafaru tsakaninsa da "Humaira,

Yaci gabada dacewa Kai "Nawa gaskiya beben "ta hadu sosai wallahi ya Kai karshen maganar da yin murmushi.


Shikam Y.Y.K ido ya zubama "Abdul-jabbar saboda ganin yadda ya takarkare sai koda "yarinyar yake,

Hannu yasa ya girgiza Y.Y.k yace Nawa Ina ta magana Amma bakace komai ba,

Yai firgigi tareda cewa hmmm Nawa kaine kuwa?

Yace yes I am you Abdul-jabbar Amma me yasa kace ni ne kuwa?


Mamaki nake wai Kane ke koda mace hmmm Amma dai kam gaskiya this girl is Lucky ko wacece domin ga dukkan alama ta tafi da lmanin ka koh?

Dariya yai tareda shafa kyakkyawan sajen yace Kai nawa baka "ganta bane,

Shima dariya yake yace ai zanso kam naganta ko wacece ita,

Yace saidai gaskiya bajin dadin yadda nabata mata school uniform ba" shikenan yau Na "hanata zuwa school kamar yadda yayanta yafada,

Y.Y.k yadan bubbuga kafadar sa tareda cewa kada kadamu
Anjima zamu je mukara "bata hakuri daga nan sai mu kafa gwamnatin mu ko?
Ya kai karshen maganar da yin dariya.

Shima Abdul-jabbar dariya yake,"

Hakan sukaci gabada firarsu har lokacin da Abdul-jabbar ya mike tareda cewa nizan tafi,

Shima Y.Y.K mikewa yai yace tunyanzu?

Yace eh zanbiya ta wurin "M .B daga Chan saina tafi gida,


Har wurin motar sa yaraka sa bayan yatafi sai shikuma yakoma cikin gida don yai shirin tafiya office.

**************

Wanene Y.Y.K?

"Yusuf ya'u Na kaka Dane ga Alh "ya'u Na kaka da Matar sa daya Hajiya karima da yaran su uku

Mata biyu Aunty "Naja'atu Da Aunty "Murjanatu sai namiji daya shine "Yusuf matan duk sun girmi "Yusuf ko wace tana zaune gidan mijinta lafia tare da yaranta"

Alh "ya'u Na kaka hamshaki mai kudi ne kuma dan kasuwa yana zaune a unguwar sarki, yakasance Mutum ne mai tausayin talaka,

Dazaran ya kula kana bukatar taimako "Toh KO baka tambaye saba zai tai makeka,

"Toh balle kaje ka tambaye sa to fa sai inda karfinsa yakare,

Wanda shine yadauki yauyin karatun "Abdul-jabbar tundaga primary secondary har zuwa N.D.A,

yanzu haka ma "Abdul-jabbar yagama N.D.A din sa Zasu tafi America akwai wani kwas da zasuyi Na shekara daya, kuma Alh "ya'u Na kaka ne yadauki nauyin tafiyar",


A hankali Abdul-jabbar yake driving har ya isa gidansu dake unguwar kurmin mashi,


Inda suke zaune shida mahaifiyarsa Hajiya "Aisha wanda shima Alh "ya'u na kaka ne ya mallaka masu kuma shine ya kaita makka,

"Toh wai duk sanadin Abotan dake tsakanin Yusuf DA Abdul-jabbar ne?
A ah shidin dai mai taimakone kawai Toh madallah da kyakkyawar zuciya irin ta "Alh ya'u Na Kaka."


DA sallamar sa yashiga cikin gidan tana zaune afalo kallo take ta amsa masa sallamar tare da daga Kai ta kalle sa,

Dai dai lokacin daya zauna kan kafet tare da cewa ya Allahu, sannun "mama ya gida?

Tace yauwa sannu da zuwa, ina kaje ne tunda sassafe haka? Yace yace naje gidan Y.Y.k tace aw "toh suna lafiya ? yace lafia kalau sunce suna gaida ke, tace Ina amsawa,
Sun Dan taba fira kadan yamike tare da yace cewa Mama "baba Lami bata iso ba tukun ? tace eh wallah bata iso ba" yace toh Allah ya kawota Lafia tace Amin", ni Zan shiga Na kwana,
tace Toh shikenan.


Abdul-jabbar Sai juyi yake a gado shida ya tafi daniyar yai bacci Amma yakasa,tunanin "Humeeh ya addabi kwakwalwar sa,
Daya yarufe idon fuskarta yake gani tareda kyakkyawar surarta, Chan kuma kunnu wansa yana tuna masa daddadan voice nata,

A hankali ya jawo filo ya matsesa a kirjin sa tareda rintse ido wani irin yanayi yakeji Wanda be taba jin irin
Saba,

Dakyar! dakyar!! Abdul-jabbar ya gaya dare saboda tsabar tunanin "Humeeh burinsa kawai yasake gani beauty fice dinta tareda jin sweet voice Nata,

Bayan yai sallar magrib sai yai bude baki kasan cewa yana yin azumin Litinin Da Alhami",

Key motar sa kawai yadauka ya fita,
Ya kokarin shiga mota sai yaji wayar sa tana ringing, koda yaduba saiya ga "NAWA kamar yadda yai save, yai murmushi tareda dagawa,yace ya akai ne?

Daga Chan yace Lafia lau kana Ina ne? Yace gani nan zanzo wurinka, yace bana gida muna asibiti DA Sauri Abdul-jabbar yace Lafia meya faru?
My Dear ce zata haihu,
Kuma wani asibiti ne? Y.Y.K ya fada masa sunan asibiti yace OK gashi nan zuwa,

Don haka dole Abdul-jabbar ya hakura da maganar zuwa wurin Humeeh, ya nufi asibiti,


Koda ya isa asibiti Jamila ta haihu ta haifi yarta mace kyakkyawa DA ita tubara kalla masha'Allah,

Sai misalin karfe10:30pm nadare sannan Yakoma gida saida yashiga cikin gida yafadawa Mama cewa "Jamila ta haihu,

Mama tai murna sosan ta kumayi addu'ar Allah yaraya Bebe yace Amin tareda juyawa yanufi dakin sai.


**********
Washegari da misalin 2:30pm Abdul-jabbar ya isa gidan Y. Y.K ,

Bayan sun gaisa sai Abdul-jabbar yace Ina maijego? Y.Y.K yace tana ciki bacci take,

Y.Y.K yace ya akai ne nawa,?

Abdul-jabbar yace Dan safa kwata miliyon dinsa, yace gaskiya Nawa ina cikin wani yanayi fa,

Y.Y.K Idon yazaro alamar tsoro yace Nawa meya faru? Yace gaskiya tunanin yarinyar nan ya hanani sakat fa, dariya yake masa sosai,

yayinda shi kuma ido yazuba masa sai kuma ya Dan hade fuska tareda cewa bansan fa iskaci wannan wani irin dariya ne haka?

Y.Y.K ya Dan tsaya dayin dariya yace toh aikai Nawa daganinka Ansan cewa you're a new come din Na,yanzu dai tashi mutafi yafada yana mikewa tsaye, shima Abdul-jabbar din mikewa yai suka fita





💞LUFHAT CE💐
💞💞💐💐 💐💐💞💞

DA SANNU
💞💞💐💐
💐💐💞💞

💞Page41-45💐



NA


💐MEENAT
💞UMAR FARUQ💐




edited by Zainuddeen zain

-----------------------------------------
®PEN WRITERS ASSOCIATION


PEN: THE STRONGEST WEAPON
-----------------------------------------


only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers



✍🏾




Tsaye suke suna duban suga ta inda "yaro zaya bullo su'aikesa yakira masu "Humaira,
Y.Y.K ne ya hango wani yaro yanufosu sai yace yauwa gawani yaro zaya biyo tanan bari saimu aikesa yakirata,

Ya sunanta? Abdul-jabbar yai masa kallon nima bansa niba,

Dariya Y.Y.K yai a dai dai lokacin da yaron ya iso wurin su har zaya wuce su,
Da sauri Y.Y.K yace salamu'alaikum, tareda meka masa hannun shima yaro Hannun yamika masa tareda amsa"sallaman,

Dan Allah abokina kashiga gidan Chan kace ana sallama da "maigidan yace toh" yanufi gidan

Da Sauri Abdul-jabbar yamatso wurin Y.Y.K yace Kai Nawa maigidan fa kace?
Yace eh toh" tunda bakasan sunan sabuwar budurwar takaba basai muyi maigaba daya ba?

Yace Nawa banfa ganeba kamar ya maigaba daya?

Yace dadina dakai kenan wallahi sai Kai tayin abu kamar dan fari,

Yace toh ai shidin ne, yai murmushi yace toh" sannu Sarkin yan wauta, abunda Nake nufi shine mufara kamun kafa da Babanta,

Yace da fatan kagane ai Dan fari gilashi? yakarasa maganar da yin dariya.
Shima Abdul-jabbar dariya yai yace eh nagane kanin mata,

Ya watsa masa harara yace waikai baza kadena kirana kanin mata ba ko?

Dariya Abdul-jabbar yake sosai yace baza A denaba din, kaima baka cemani Dan fari ba?

Yace toh"kai badan farin bane? yace ni ne,
Toh kaima ba kanin matan bane? ya langabe Kai tareda cewa toh" yazanyi tunda sun'rigani zuwa ni ne" dariya sukai gaba daya tareda tafawa.

Dai dai lokacin da yaron yadawa yace ace "maigidan baya nan waisu wane ke nemansa? Kodaya kema naji ace wata tazo tagani Kusu wanene? tana nan zuwa.

Y.Y.K yace yauwa abokina mungode ya zaro naira Dari biyu Aljihu sa yami kama yaron,

Yaro yadan russuna tareda sa hannun biyu ya karba yace Nagode yajuya yatafi.

Tunda ga nesa "Abdul-jabbar ya zuba mata ido hankali take tafiya kamar bataso taka kasa sanye take da atamfa brown me ratsin ash Riga da zani ne dinkin tasa hijab mai hannu Ashe colour,

Ta isa wurin su tareda sallama "Y.Y.K ne ya amsa mata fuskarsa dauke da murmushi, tadan russuna kadan ta gaida su Y.Y.K ya amsa mata

Shikam "Abdul-jabbar be amsa ba saidai ido daya zuba "mata ganin yadda take komai cikin sanyi hakanan yasa yaji takara shiga cikin Ransa,

A hankali ya sauke ajiyar zuciya tareda maida hankalin sa wurin su,

Cikin Dan siririn muryarta mai dadin saurare tace kuke Neman maigidan Chan?

Yace eh mune saidai ba "maigidan muke nema ba yar maigidan muke nema"

Da sauri tace kalle sa yai murmushi yace eh wurinki mukazo" ni sunana Yusuf kina iyakirana Y.Y.K shi kuma dan 'uwana sunan sa Abdul-jabbar,

tace Lafiya dai KO? Yace Lafiya lau saidai bamu San sunan Malamar ba?

A hankali ta dukar dakai kasa tana murza zoben dake Dan yatsanta,

Shikam "Abdul-jabbar ido ya zubama zarazaran yatsunta masu kyau da sha'awa sabada adon Jan lalle da bakin da akai masu,

Cikin sanyi tace sunana Aisha Amma Humaira ake kirana yace nice name toh malama Humaira ya "mutanan gida ya kuma school? Tace Lafiya Lau yace toh" madallah,

Yace Malama Humaira nasan dai kingane wannan KO?
Ta kalli wurin da "Abdul-jabbar yake wanda shima din ita yake kallo,

ido suka hada at the same time Abunda taji jiya shita karaji yau saboda haka saitai saurin dukar dakai kasa tareda cewa eh nagane sa,

Yace toh" dama munzo ne mu karabaki hakuri Akan abunda yafaru jiya don Allah a muna afuwa,
Sannan kuma idan ba damuwa munason kulla alaka tsakanin mu dake,
Wato Dan uwana ne yaji kin kwanta masa Arai tun lokacin daya ganki ma'ana yana sonki, saboda haka ne mukazo da kokon bararmu gareki dafatan za'a
Amunta damu.?

Shuru tai ba tareda tace komai ba, Yace mlm Humaira kinyi shuru bakice komai ba?

Tace toh ni mezan ce? yai dariya yace keko keda abuncewa, gaskiya bazan boye makiba dan'uwana yakamu da sonki lokaci daya don haka kinga dole zaiso yasan matsayinsa awurinki KO?

Tace toh kudan bani lokaci nai shawara, Yace kamar yaushe kenan? tace nanda sati biyu, Da sauri yace two weeks fa ki kace!?

Ta kada Kai Wanda ita kanta bata San lokacin da tace two weeks din ba,
Shikam Abdul-jabbar cikin tsoron jin abunda tafada yasahi Kara zaro big eyes dinsa waje, Y.Y.K yace haba Humaira sati biya ai yai yawa A yadda dan'uwana yakejinki aransa ai baza ya'iyayin sati biyu be gankiba,
Tace toh sati daya, Yace a ah inama dai laifin muzo gobe? ya fada yana mirgina kai, a ah ba gobe ba, toh" sai yaushe? tace jibi, yace beyi yawaba? tace a ah beyiba,

Yace toh shikenan ba komai hakama da akai mana mungode kwaraida gaske,
Tace sai anjima Y.Y.K Yace toh a gaida su "Umma da yayan mu yafada yana murmushi itama murmushi tai tace to zasuji tajuya ta tafi.

Abdul-jabbar yabi bayanta da kallo,

Y.Y.K ya zungure sa tareda cewa Kai wannan wani irin kallo ne haka? sai kace Wanda yawarke makanta
Wannan aisai kasa ta buga tuntube tafadi, tun dazu kake kallo ta da wannan kwala-kwalan idon naka kamar na mage kilama Shiya takasa sakin jiki tai magana, yakai karshen maganar dayin dariya.

Shima Abdul-jabbar dariya yake yace Amma dai Nawa da sharri kake, yanzu saboda Allah idona ne kwala- kwala kamar Na mage?

Cikin zayala Yace eh koba haka sukeba? barima Allah yasa idan muka dawo jibin tace bakai mataba, saboda kafaye kato sannan kuma idanun ka kwala-kwala.

Aikam me Abdul-jabbar zaiyi inba dariya ba hada rike ciki yadan tsaya dayin dariya yace ba Amin ba,aizata soni da yaddan Allah kuma "DA SANNU" kuma zata gane irin kaunar danake mata.

Y.Y.K yace bani key kagani najamu kai kam yau naga Happy yacika maka ciki so ba lallai bane ka'iya driving din'mu.

Yajefa masa key tareda cewa ai kaidin ne Wallahi ko mutun beyi niyar dariya ba sai kasa sa,


Yai dariya yace Nawa kenan duk kawani rikicewa datace two weeks,yace aidole Na rikice ba kasan yadda nakejinta araina bane shiyasa.

Yace Hmmm ni mamaki kake bani ban taba zaton zaka mato akan san ya mace ba wallahi, a yadda naga mace bata gabanka kuma komai kyanta Amma sai gashi naga wannan kanata rawar jiki a kanta,

Koda yake gaskiya nayaba da "Humaira kyakkyawar ce gatada nutsuwa da alama tarbiya yaratsata, gata Da sanyin murya kawai dai ka'iya zabe konace kayi dace saidai ace Allah ya tabbatar Da Alkhairi.


Abdul-jabbar dadi yaji

Please Login or Register in order to submit comment