Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ban Da ban.

Ganin cewa da gaske kuka suke sosai sunki sakin juna, sai Kuma suka basu Abdul-jabbar tausayi. Ahankali Doctor ya isa gurinsu cikin sigar lallashi yace haba _Lovely friends_kukan mekuke?...

OK" nagane kuna kukan rabuwa da junane KO?...da Sauri suka daga Kai alamar "eh yace toh" "anfada Ku "idan daya "yayi aure shikenan "an'rabu?...
toh" ba'arabu ba "ai wannan lokacin ne zaku Kara dankon zuminci ku, bawai Ku tsaya kuna kuka kamar irin little-little childrens din'nan ba.

Kuba kusan cewa yanzu they're bigs girls ba?... cikin zolaya yace bani wayarki nakira Humaira ko dariya tayi maku

Cikin shagwaba Hannah tace gashi, yace "au nakira tadin?... tace "eh. nan danan yayi Dialling number Humeeh tareda sa Wayar "ahandsfree, saiko tadaga, saidai cikin sheshshakar kuka zukaji tace Hello waye?...kasan cewar bata tsaya duba waba, cikin matsananci Mamaki Doctor yace Humeeh tace na'am yace meyasa meki naji kamar kina kuka ko?..

_*Allah sarki Humeeh" tana can tana kuka mai kunshe da Abu biyu", daya kewar su Hannah da Haleeh daya Kuma na SON Abdul-jabbar, wanda ganishi yatayar mata da tsohon mikin dake zuciyar ta. domin kuwa jitayi SON Abdul-jabbar yadawo mata sabo fil "ayanda takeji yanzuma haryafi Nada saidai tunawa datayi cewa yanzu Abdul-jabbar banata bane yasa take kukan tausayin kanta*._

"Don haka cikin cikin kukan Shagwaba tace ummh! I Miss my Hannah and Haleeh I lot.

Dariya ce takwace wa Doctor shidasu Abdul-jabbar, da sauri Humeeh tace waye Kai?... yace l am Doctor Ibrahim "Angon Hannatun Humeeh DA Haleeh, hakane?... Tace eh, yace ayya
No wonder ashe kema kina can kina kukan'ne, shiyasa suma suke nan sunayi.
"ALLAH sarki three heart's in one place,

Toh ku "Inbanda "abunku ai "idan kaji kewar dan'uwanka bazama zakayi kana kuka ba, just dauki Waya kakira shi saikaji lafiyarsa' Shima sai yaji taka za'a
Ko?....
Bahaka bane friends suka ce" hakane.

Yayinda sukaji tausayinsu" yaka masu" tawani bangaren kuma kawancansu yana birgesu. Haleeh tace Doctor "Ina Hannah DA Haleeh yace gasunan sai kuka suke faman yi,
Humeeh tace My Hannah,
Cikin Shagwaba Hannah tace Na'ma
toh" my Humeeh Shinefa yace my Haleeh ta tafi ba,

yace toh" ai abinda yasa nace ta tafi Saboda kinga gida ba'asan zata kwana ba shiyasa,

Humeeh tace pls Doctor kabari my Haleeh ta kwana mana?...kaga saita taya my Hannah hira. yace Humeeh bai Kamata Haleeh ta kwana ba tunda gida ba'asan zata kwana ba, kinga kwanan ta anan zaya'iyazama damuwa "azo ana nemanta "amma kunsame ?.. girgiza Kai sukayi alamar "a ah yace l promise yours gobe dakaina Zanje har gidana dauko maki Haleeh tazo tawuni maki hardare, wani "abinda Mamaki shine DA Sauri suka hada baki harda Humeeh, sukace da gaske?... yace insha'allahu

Dariya sukayi gaba dayan su" tareda cewa "eh mana", nandan Doctor cikin hikima irin ta maza ya lallashesu", sannan suka tafi "akasauke Haleeh gida sannan Y Y k yakai M B gida yakai Kuma Abdul-jabbar sannan shima yanufi gida, dayake da motar shi Y Y k din sukaje gurin Dinner.

*American university Yola*
*****************
Da misalin karfe goma Na safe, Humeeh ce' zaune saman wani dotse "akarkashin wata bishiyar fulawa, sanye take cikin rigada siket na'atamfa mairuwan toka, tanada ratsin ja tasaka hijab shima ja.
tana rataye da jaka mairuwan toka shima takalmin kalarshi kenan.

fuskarta bawani kwalliya saidai powder kawai data Shafa, sai Kuma man baki kadan data shafa alebenta. Gaskiya dress din yai mata kyau musamman data man'na wani Dan siririn glass "afuskarta.

Wasu littafiai naga tana dubawa, can Kuma sai naga tabude Jakarta tafito da wayarta, Dailling Number Hannah naga tayi tareda bude hands free din wayar sannan ta ajiyeta "akan littafai.
Daga can Hannah tadauka tareda yin Sallama, cikin zalaya Humeeh ta amsa dacewa Amarya kinsha mai yamike?

Dan tsaki mtsww! tayi tareda cewa nasha mai kona sha wahala,
Dariya Humeeh tayi, yayinda Hannah tace "au dariya ma kike Mani?... tace toh" kedince' wlh "inbanda abinki meya hada Amarya Da shan wahala?... Wadda akace' yar'sha galice "ita komai a kasamu ita "akaba ta karashe maganar tana dariya. tsaki mtsww tayi tace "aiko meye idan kikayi "aure zakisani yar'rainin sense kawai.

DA Sauri tace wani?... tab.. nikam bazanyi aure nabar Umma taba. tace "au Allah?... tace ummh, (Murmushi tayi data tuna cewa Abdul-jabbar yana nan zuwa gareta Wanda Kuma tabbas da maganar aure zaije) Dan haka sai tace toh "ashikena saiki zauna kiyi tayiwa "Umma gadin daki,
tace "aidama yarinya kobaki fadaba, tace toh "Aisaiki tattake nidai yakike?..

Tace lafiya lau toh" ya school din?... tace lafiya toh" Allah ya bada sa'a Ameen, nan dai suka Dan taba fira sannan ta kashe wayar, yayinda tacigaba DA duba littafai.

Assalamu'alaikum shine Abunda taji amfada cikin wata siririyar murya,
A hankali ta "amsa tareda daga Kai ta kalli maiyin Sallamar wata budurwar tagani yar kimani shekara goma sha biyar, kyakkyawa tana sanye da "Abaya baka.
tayaye kanta da mayafin abayar fuskarta tasha kwalliya, yayinda ta man'nawa idonta irin glass din'nan DA "akekira no respect.

Cikin yar siririr murya tace Don Allah zan'iya zama nan wurin?...tana Nina kusada Humeeh, yayinda Humeeh tace Lah! bakomai kizauna mana. tace OK ta zauna tareda cewa thanks, Humeeh tace no problem. Can sai tace sunana *SARAH "AHMED ABDUL-JABBAR* kefe?...,wani irin yarrrrrr! Humeeh taji "ajikinta saka makon jin sunan "Abdul-jabbar, Murmushi tayi sannan tace *A'ISHA "MAHAMUD IBRAHIM,* tace OK wani department kike?.. tace Medicine. Da sauri tace Wow! nice to meet you wlh, dai-dai lokacin datake mika mata hannu tace nima can nake.

"Itama hannun ta mika mata tana dariya tace Allah sarki, tace kinga nifa banyi copying times table ba koda yake "ance sai 12:00 mukeda lecturer KO?... Humeeh tace "eh hakane toh" ganawa basai kiyi copy din ba, tace "OK toh" nagode takarba tana rubutawa. bayan tagama sai kuma sukafara fira kamar sun dade dasanin juna, har zuwa Lokacin lecture yayi suka nufi Class din.


*BAYAN SATI DAYA*
*****************
Da misalin karfe 2:30 pm Humeeh ce" kwance tana Waya da Sarah sabuwar kawarta. kasan cewar yau tun 2:00pm suka tashi daga school. Dan haka take hutawar ta'abinta, wadda Kuma "acikin sati dayan nan sun shaku sosai dajuna itada SARAH "idan kagansu" sai karantse dama can tare suke" wanda har tasan "Haleeh DA "Hannah kasan cewar Humeeh tabata Labarin su harsun gaisa "AWaya"

Hira suke tazu bawa kamar bayanzu suka rabu makaranta ba, Sarah ce' keyiwa Humeeh korafi cewa ya kamata tazo gidansu. Kasan cewar "ita Sarah taje gidansu" Humeeh har sau biyu, dariya Humeeh tayi sannan cikin zolaya tace
Sorry my Saratutu aizanzo.

_(Dayake tasan bata son akirata Saratu saidai_*SARAH*)

Da sauri tace Kut! Amma dai my Humeeh kinci abinci hada wani Saratutu KO?... kuma kinsa I don't like it faaa! Cikin dariya tace Sorry nadaina. tace "OK toh" fada Mani yaushe zakizo?... kinga sisters Dina sun'matsu suganki.

Tace Ummh! dama "Abunda yasa kikaga banzo ba saboda "Abba baya nan ne shiyasa toh" Amma kinsan me?.. tace "a ah saikin fada, tace "Abba yadawo da sauri tace da gaske yaushe?... tace Allah koda nadawo gida Na iske shi' dama shizan fada miki, So kinga gobe zanzo insha'Allahu. tace toh Allah ya kaimu tace Ameen, "Ina gaida "Umma shima "Abba ina gaida shida dawowa sukai Sallama.


Tana cikin chatting Da mutanan ta "Hannah da "Haleeh sai bacci ya kwashi ta, cikin baccin taji Wayar Na Kara, dauka tayi tasa "akun'ne batareda taduba ba. cikin murya bacci tace Assalamu'alaikum,

Zumbur naga tamike tamkar wadda "aka tsikarawa Allura tareda zaro beauty eyes dinta waje cikin hada kalmomi naji tana cewa?...





๐Ÿ’Lufhat Ce๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page166-170

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)

----------------------------------------
*_ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN:THE STRONGEST WEAPON_*
----------------------------------------


_*Pls masoya wannan littafin kuyi Mani afuwa narashin ganin posting Dina, akan lokaci. abubuwa wanne sai a slowly Amma insha'Allahu komai zayazo normal nagode.*_





*_only exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_.*


โœ๐Ÿพ



"W..a..n..e..ne..?.. Sai Kuma naga tasauke wayar tareda tsura wa number idanu, yayinda jikinta yaketa rawa "a handsfreen tasa wayar, da'alama tanaso ne' ta tabbatar da gaske muryar shi" din'ne, KO kuwa kunnan tane yake mata gizo kamar yanda yasaba.

Saidai ga Mamakin ta saitaji Cikin Zazzakar muryarshi dabaza ta taba mantawa da'ita ba, yace Hello my Cool kenan, nasan kinajina sannan kuma kamar yadda *SONKI da KAUNAR KI' kE DA KOMAI NAKI*bazaya taba gushewa acikin Kwakwalwa taba, toh" kema nasan haka *KOMAI NAWA* bazaya taba gushewa acikin Kwakwalwarki ba.

Domin *SO DAYA NE* saboda haka gani "A harabar gidanku, kizo kiyi Mani jagora domin kinsan bai dace Na shiga gidan mutane, batareda *IZINI* ba so l am wanting for *U my Cool*" sannan yakashe wayar.

"Idanu nagata tsurama wayar tabbas shine jitayi kirjinta yaci gaba da bugawa, saka makon tunawa datayi yace' yana harabar gidan. don haka da sauri tamike tareda jawo mayafin "abayarta dama shike jikinta Dan haka saita yafashi,

Tareda shuran flat shoes dinta tasaka sannan tafito waje, da sauri take saukowa daga matattakalar benan, Da sauri tawuce Umma dake zaune "afalo, yayinda Umma tabi bayan ta Da kallo Cikin mamakin "aranta tace toh "ina kuma wannan lafiya "inazata haka Da sauri?..

Humeeh kam tana fita Sai tafara waige-waige aikam saita hango shi, tsaye ya jingina ajikin wata dan kareriyar mota ya rungume hannu akirji, yana sanye da uniform din,su" na SOJOJI.

_*Kut shine abinda nace saka makon ganin ABDUL-JABBAR turkashi toh faaaa*!_

Tsaye tayi Chak! tana kallon shi fuskarta cike da mamaki, yayinda shima yake kallon ta yana takowa "Ahankali Cikin tafiyar kasaita, irin Nasu" na Sojojin masuji da'isa da takama.

Sai Murmushi yake sakar mata ganin yakusa isketa yasa tafara tafiya, "ahankali da baya da ba yayinda shikuma yake binta ahankali-"Ahakali,

Harsuka isa bakin kofar falon tadaga kafa daniyar zata shiga falon kenan, Saita tafisuuuuu! zata fadi tabaya.

Cikin Zafin nama irin Na SOJOJI yarike mata hannun, tareda tallabo kugunta. yayinda hannun ta guda Cikin nashi hannun, gudan Kuma tadafa kafadar shi yaza mana suna jiyo bugun zuciyar su tareda jin'numfashi
Juna.

Kallon juna suke sosai yayinda kamshin turaransa yahadu danata, Sai yabada wani irin ni'imantaccen kamshi mai dadin gaske, yayinda sukaji wani irin kasala yaka masu "alokaci guda.

"A hankali yakai bakin sa gurin kun'nanta Cikin rada yace wayace maki ana tafiya da baya da baya bakisan hakan bayada kyau Ummh?..


"Itakam Umma dataji Humeeh shiru bata shigoba, Saita tashi tanufo hanyar waje don taga KO lafiya,
Saidai abinda tahango talabulen yasata tsayawa, kasan cewar labulen falon irin mai ragan'nan ne
Don haka da sauri tace Humaira...

Cikin tsoro tareda rawar murya Humeeh tace N..a.n.a na'am Um..mah gani, "Ahankali Abdul-jabbar yadaga ta yayinda yaketa sakar mata lallausan Murmushin sa mai kashe mata jiki.

Da sauri tajuya tanufi Cikin falon jikinta Sai rawa yake, bin bayanta yayi yana dariya bakinsa dauke da Sallama yashiga cikin falo, Umma ta amsa yayinda ya tsugun'na har kasa yace sannu Umma "Inayini da fatan munsa meku lafiya?.. cikin jin kunya tace lafiya ya Aiki yakuma mutane nan gida?...yace lafiya, tace toh" madallah sannan tanufi kitchen kasan cewar dama tana girkin'ne,

Humeeh tana ganin "Umma tanufi kitchen Sai ita Kuma tanufi dakinta, yayin da Abdul-jabbar yabi bayanta da kallo, da dan gudu-gudu take taka steps din tana shiga dakin tarufo kofa. tareda jingina bayanta "a kofar idanun ta rufe, sai sauke nufashi take sai kace wacce tayi gudun tsere.

"A hankali Abdul-jabbar yamike' daga tsugun'nin,yayinda yatura hannun wanshi dukka biyu 'acikin aljihun, tunani yake arashi kuma fadi yake meyasa my "Cool ta tafi kodai batayi farin Cikin ganinsa bane?...

Zama yayi "a daya daga Cikin kushindin falon yafara kallon t.v, kusan 30 mints shuru ba Humeeh ba dalilin ta. Yayinda kallo daya zakaiwa Abdul-jabbar ka' fahimci cewa kallon kawai yake ba tareda yana fahimtar abinda "akeyi acikin t.v ba.

Domin kusan duk hankalin sa yanaga hanyar da Humeeh tabi, yayinda jafi-jafi yana kallon agogon hannun shi ki'la yanada wani uzirine.

Umma ce' tafito daga kitchen zata hausama sai taga Abdul-jabbar zaune shikadai. Kallon sa tayi tace "a ah Kai kadai ne ina ita "Humaira take'? Cikin jin kunya tareda Sosa Kai yace "eh tunda tashiga Ciki bata fitoba,

Tace" a ah toh" inazuwa, yace toh" dai-dai Lokacin datake hawa steps din.

"Abangaren Humeeh kuwa bayan tagama tsayuwa, saita koma gefen gado ta zauna tareda zuba Uban tagumi, sai kace wadda akayiwa mutuwa.

Sai kuma tafara tambayar kanta take Waya ba Abdul-jabbar number ta?.. sannan Kuma Waya fada mashi cewan tadawo Yola bayan haka Kuma me yazo yi gurinta?...

_domin batayi tunanin cewa Hannah KO Haleeh zasu bashi no taba_

Toh Waya bashi no ta?..toh kodai wanene tabbas agurin bikin Hannah yasamu toh" kodai Doc... turo kofar Umma ne' yakatse mata tunani.

'Da sauri tamike tana kallon Umma, itama Umman kallon ta take', cikin mamakin domin taga tsoro karara 'afuskar ta. saboda haka sai tace "a ah waike yau Lafiyar ki' kalau kuwa?... Humeeh tace Lafiya lau.

Umma Tace toh" Lafiya lau kike shine kika bar "mututum, shikadai "afalo ko' ruwa baki'kai masaba. baki ta turo tareda cewa Umma *ABDUL-JABBAR* nefa.. Da sauri Umma tace' "Abdul-jabbar fakikace'?.. tace "eh Umma shine, tace "ikon Allah nikam 'aiban'ma ganeshi" ba dama nan garin yake aiki?.

Humeeh tace "Oho niban saniba, toh" yanzu Kuma meya zoyi gurin ki?. toh" waima Waya fadamasa mundawo nan garin?.

tace Umma nimafa "abinda nake tunayi kenan, kawai nidai yakira ni yace wai "infito gashi nan "aharabar gidan mu, toh" shinefa kikaga nafita da sauri toh" Kuma kodanaje sai kawai naganshi'.

Umma tace toh" aisai kije kiji da meyazo Kuma, tace Umma nidai gaskiya ba.. Umma ta katse ta dacewa wuce kitafi nace' kije kiji da meyazo, hakan Humeeh tawuce' tana gun-guni.

_Nikam nace um-umhum su Humeeh anaso ana kawai market (kasuwa)_

Kitchen tanufa tire Da Cup tadauka, tareda bude fridge taciro lemon juice da ever water masu sanyi, tajera "afarantin sannan tanufi gurinsa fuskarta ba walwala
yayinda kirjinta keta dukan uku-uku.

"A hankali tayi sallama Cikin yar siririyar murya ta, idanunshi na'akanta ya amsa sallaman, a hankali tajawo Dan karamin table gabanshi tadora faranti, sannan takoma nesada shi kadan ta zauna.

Batareda ta kalleshi' ba tace inawuni, shuru bai amsa ba tasake cewa inawuni nan ma shuru bai amsa ba, Dan haka sai tajuyo dasaurin do taga meyasa yaki amsa bai suwarta.

Caraf suka hada idanu dashi' tsawon yan mintoci suna kallon juna, can sai ta kauda Kai gefe tace bismillah kasha ruwa.

Cikin sanyin yace pls ataimaka azuba mani, "ahankali ta tashi tajeta zuba mashi Lemon juice din ta miki masa batareda ta kalle shiba,yayinda shi Kuma idanu shi suna kanta.

Bayan tamika mashi saita komawa ta zauna, yayinda taketa cika tana batsewa fuskar nan nata babu walwala, ganin hakane yasa gaba daya Abdul-jabbar yadaburce yarasa ta iyazai fara..

Har yagama shan lemon idanu shi nakanta' yayinda ita Kuma KO kallon inda yake batayi ba.

Wata dabarace tafado mashi wayar shi naga yaciro, yayi dailling number Mama tareda sata a handsfreen, yayi Sallama Mata amsa yace Mama nakira wayar ki' dazu Amma baki dagaba Lafiya?..

Tace" eh Lafiya lau bana kusada wayar ne,"ainagani toh" Kuma Dana kirana sai ban sameka ba, yace
Kila "inata gurin da ba
Network. tace Oho" toh" yanzu ankaiku gurin daza kuyi "aiki?.. yace eh ankaimu Gibson jalo Barrack, shuru tayi batace' komai ba, (da'alama ta tuna wani abune) yace hello Mama naji kinyi shuru l hope dai Lafiya?..

Tace' a ah bakomai nadai tuna wani "Abune,' Da sauri yace' inafata dai abinda kika tuna baisa kinji ranki yabaci ba?.. kinsa bana
san bacin ranki yanasa naji duk hankali Na yatashi.

Tace a ah bakomai don haka ka kwantar DA hankalika, ALLAH yabada sa'an abuda "akaje nema, yace Ameen tace yaushe zakaje kidansu takwara ta?..

_*kasan cewar tasan DA maganar zuwa wansa gurin Humaira*_

Yace Mama gani "agidansu"My Cool, tace masha'allah kasa mesu lafiya?..
yace Lafiya lau suke", saidai kinsan wani abu?.. tace "a ah sai kafada yace' Mama My Cool tana fushi dani sosai ko" magana batayi maniba, saboda hakane yasa narasa ta "ina zanfara bata Hakuri. Kingani ma hada hararana takeyi pls Mama kiyi wani abun kinji?
Yakara she maganar cikeda shagwaba.

Cikin Mamaki jin 'abunda yafada Humeeh take kallon shi, yayinda shidin'ma idanun sa suna "akanta yana sakar mata Murmushi, aranta kuma take fadin ji yadda yake' magana kamar wani karamin yaro.

Murmushi Mama tayi har saida sauti shi yafito tacikin wayar, (Allah sarki Mama yanzu kam tuni tasaba da shangartar Abdul-jabbar, domin kuwa tun bayada yaji sauki shikenan sai yake zuba mata shagwaba "iya san ranshi yayinda ita Kuma take biye mashi)

Tace toh" yanzu kaba takwarar tawa wayar,yace toh" tareda mikawa Humeeh wayar, idon shi cikin Nata takarba, yayinda take sakar masa' harara Wanda narasa gane kona meye..

"A hankali tace Mama 'inayi, Tace Lafiya lau takwarata ya "Ummanki' da yayanki" ya kuma karatu?..tace duk Lafiya lau, tace toh" madallah. nan dai Mama tafada mata duk Abunda yafaru, tun daga yanda akai "aurenshi Da Lariya har zuwa rashin Lafiyar dayayi.

Takara da cewa don ALLAH kiyi Hakuri kinji takwarata, duk wannan abun da yafaru nice' natilasta mashi Wanda ni kaina bansan yadda akai hakan tafaru ba

Saidaga baya nagane cewa harda makircin Haj Jumma, kinga dayake "abun ba Saboda ALLAH akayi shiba sai gashi "DA SANNU" Allah yawarware komai.

Don haka "inasan kimance Da duk "abunda yafaru "abaya, domin nasan dake dashi kuna SON junanku" saboda haka Ku manta da baya Kufuskanci gaba, Allah ya tabbatar Da Alkhairi tsakanin ku'
Kinji KO"?..

tace toh" Mama Insha'Allahu komai yawuce, tace toh" nagode ALLAH yaimuku Albarka
tace' ameen sai anjima sannan tamika mashi wayar.

Yakarba tareda cewa Mama "Ina SONKI' sosai ga kewarki tada meni dayawa, dariya tayi tace Kai kam shiriri tarka tayi yawa, daga jiya zuwa yau shine kayi kewata dayawa?..

Yace' Allah kuwa Mama sainaji kamar nashekara bana kusa dake", shiyasa nake rokon Allah yabarni da Mamanta, Murmushi tayi tace' ka kulada kanka sannan Karin ga shan maganin ka'
"Akan lokaci, saboda nasan halinka sarai baka San shan magani.

Yace zanyi yadda kikace insha'allahu kice" ina gaida Baba Lami Tace toh" sai anjima ka gaida abokinka yace toh tareda kashe wayar.

Ya kalli Humeeh itama shi take kallo, sannan tace' kaci *DARAJAR* Mama, Amma badan hakaba hmmm?... Yace ainasan dayau sunana SORRY KO?.. Kilama KO wannan ruwan da juice Umma ce' tasa kika kawo Mani Ko?..

Bata bashi amsa ba saidai tace' Waya baka number Wayata, Waya fada maka mun dawo nan Yola than Waya baka Address Dina?..

Murmushi yayi yace duk wannan questions din ni kadai?.. Kai tadaga alamar "eh, yace "aikam yanzu kuwa zanbaki "amsar tambayar ki'.
Nan dai yafada mata duk abunda yafaru, harda gani ta dayayi yakara da cewa Dr I S g
"Abokina ne Kuma shine Dr na.

Murmushi tayi tace'
Nima ainagan ka, idanu yazaro Cikin Mamaki yace' shine kika kyaleni?.. tace' toh" mezance' maka?.. yace hmm My cool "inda kinsan halin Dana shiga adalilin SONKI' dabaki guje maniba.

Tace toh" aikain...da sauri ya katseta dacewa Shhhh! don't say anything, just we do what Mama say.
Aikam Cikin lokaci kankani suka balle Da firar Soyayya, tareda tambayar bayan rabuwa nan dai kowa yafadi wa Dan uwansa, halin da yashiga dalilin rashin dan'uwan sa.

Sun'nutsun sosai acikin firar Soyayya harbasu" San lokaci yajasosai ba, saidai kawai sukaji "ana kiran sallar La'asar
Kallon juna sukai suna dariya.

Ya mike tareda kallon agogon hannun shi yace", kinga har lokaci yaja bansaniba bari natafi kar'anemeni

Itama tamike tareda cewa toh" ya kalleta Cikin So da kauna yace' Kai my Cool bako cewa sai anjima KO sai yaushe?.. kodai kindai SO Na sosai ne?..

Fuska tarufe da hannun ta tace' ah nikam aibanki kazauna muyita firaba, ya matsa kusada ita kadan yace' da gaske My Cool?. kaita daga alamar eh.

Murmushi yayi yayinda yakejin Sonta yan karuwa acikin Zuciyar shi, yace nima zanso haka saidai yanayi aikin'mune sai a Slow, amma karki damu insha'Allahu "DA SANNU"
zamu kasance tare, har abada kedai kiyi mana Addu'a kinji me SANYI TA?..

tace toh" insha'Allahu zanyi. yace' yauwa toh"muje kirakani,
Har gurin mata tarakashi sannan takoma Cikin gida,
Zuciyar ta cike DA farin Ciki yaugata ga Special dinta.

Umma ta kalleta tace' sai yanzu yatafi?. Cikin farin Ciki tace' "eh yatafi yace" yana gaida ke' tace' "Ina 'amsawa toh" meke tafedashi kuma?..

Nan tafada mata duk yanda sukai harda wayan Da sukai Da Mama, tace' Umma Bari naje nayi sallah,
batajira amsar Umma ba tanufi hanyar toilet.

Yayinda Umma tabi bayan "tada kallo tace Hmmm yaro" mankaza, Humaira ainasan haryanzu kinsan Yaron nan toh" Allah ya tabbatar Da Alkhairi tsakanin nace'
Toh Ameen.


Dai-dai lokacin da Abdul-jabbar yake kokari fitadaga harabar gidan, toh" Kuma alokaci ne Abba ya kun'no hancin motar shi.

Da sauri Abdul-jabbar yasauke glass din motar shi, domin KO Ba'a fada masaba yasan cewa Abban' su" Humeeh Saboda Kama daya hango.

Shima Abba yasauke glass din motar yayi tareda tsurama Abdul-jabbar idanu, Cikin ladabi ya gaida Abba ya'amsa tareda cewa?..



๐Ÿ’Lufhat Ce๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
DA SANNU
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

page178-182

NA

๐Ÿ’žAMEENAT UMAR๐Ÿ’ FARUQ
OR
(MEENAT)


*GAREKI MASOYIYAR "DA SANNU"*
*Wannan page naki ne ke kadai kiyi yadda kikeso dashi, MY HABITY SALMA USMAN gital group novel, inayi dake kamar yadda kikeyi Dani NAGODE SOSAI DA KAUNARKI AGARENI ALLAH YABAR ZUMINCI "DA SANNU" ALLAH ZAYA HADA FUSKOKIN MU LOVE U SO MUCH*๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹


----------------------------------------
*_ยฎPEN WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN:THE STRONGEST WEAPON_*
----------------------------------------

*_only exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_.*


โœ๐Ÿพ



Wanene wannan?. SARAH tayi Murmushi tareda cewa Lah my besty shinefa "Daddy mu,

Tace sorry My besty ban fada maki koni wacece bako?. toh kamar yadda kika sani sunana SARAH AHMED ABDUL-JABBAR,

wayan nan najikin picture din sune' mahaifana wannan itace Mom dina Hajiya Maryam, wannan mahaifina Kuma shine governor jahar nan ayanzu dai nice babba agidan nan sai kan'nan Na gasunan,
wannan itace Esha baby wannan Kuma Zarah Mama,

SARAH tayi dariya tace besty I hope kin gamsu, Cikin karfin hali Humeeh tace "eh Amma kinsan ban taba sanin cewa Dad dinku shine governor jahar nan ba?

Idanu SARAH tarazo Cikin mamaki tace Kai besty kina Cikin garin Yola kice bakisan governor kuba?.. Humeeh tace Allah ban sanshi ba saiyau dana ganshi ahoton, kinsan nafada maki bamu Dade Da dawowa nan garin ba,

SARAH tace' eh haka nefa, nan dai suka Esha baby da Zarah Mama suka gaida ita, dagan kuma suka nufi danning don cin Delusions din Da aka hadawa Humeeh,

Bayan su gama sai suka koma falo suka baje kolin fira, yayinda rabin ahankali ta yana kan wannan hoton, suna cikin fira sai Mom tafito Humeeh ta gaida ita harta tambaye ta ya Umman ta da Abban ta tace Lafiya lau suke,
Sai bayan tayi sallah azahar sannan tayi shirin tafiya gida,

Mom tayi mata kwatar abaya da turaruka DA mansha fawa masu asalin kyau da tsada, ta Kuma bata wasu turare da lifaya takaiwa Ummanta, tace toh ta godiya.

Har gurin mota suka rakata saida sukaga fitarsu sannan suka koma Cikin gida.

"A cikin mota kam Humeeh Sai tunani take tareda mamakin hoton datagani agidan su "Sarah, Wanda Sarah tace shine Daddy su"

Caf aida badan da "Sarah tace' Daddy su ba tabbas datace' shidin Special dinta ne,

Hakadai take ta tunani DA Kuma mamaki, can dai wata zuciya tace toh waike mamakin mekike shin kin manta dacewa "anakama?

Da karfi tace' "eh hakane Kuma fa,
har saida Bala drive yajuyo yace ranki yadade kina magana ne? dasauri tace' a ah,

A ranta kuwa take fadino "Oh ni A'isha tunda nake aduniya bantaba ganin Kama irin haka ba, irin wannan kama haka sai kace irin identical twins, haka take tasake sake harsuka isa gida.

Suna shiga motar su Abdul-jabbar tana shigowa, Bayan Bala drive yayi parking sannan tafito tanufi cikin gida Cikin nutsuwa take takawa, har takusan shiga falon sataji ance Aminci Allah ya tabbata ga mai sanyin ZUCIYA ta.

Ahankali tajuyo suka hada idanu tareda sakarwa juna Murmushi, yauma sanye yake da kakinsu Na SOJOJI, ahankali yakaraso gurinta saikuma yadan hade fuska yace' yawo kigaje ko?

Kai ta girgiza alamar "a ah, yace toh' idan bayawo kikaje ba toh Ina kikaje saida ta turo Dan mitsitsin bakinta sannan tace Kai Special gidansu my besty Sarah fanaje shine naje yawo?

Dariya tabashi ganin yadda ta turo Dan bakin hada wani bata fuska, sai yace toh" shine Kuma hada su fushi?

Please Login or Register in order to submit comment