Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*BAYI MA YA'YYANE*


*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*

```kungiya daya tamkar da dubu, masu aiki da iliminsu```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________

*BEST OF 2021*



*Wannan labarin ƙagengen labarine, ban yi shi dan wani ko wata ba, inda labarin yazo dai dai da rayuwarka akasi ne*




*Free book ne📚🖊️*
```amman fa rashin comment dinku zaisa ya koma na kudi, amman idan kuna comment babu chanjin ra'ayi free book ne🥰```

*My books👇*
*Nana jawaheer*
*Gimbiya hakima*
*sanadin link*
*izzah ko mulki*
*a gidan haya*
*Sadaukin burhaan*
*ɓarawo ne*
*a sanadin soyayyar minti*
And know
*bayi ma ƴa'ƴane*


*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



Babi na 1/2



Masarautar Daborah masarauta ce dake can cikin kasar Gambia, yankin Afrika ta gabas masarautar ta shahara a fagen Sarauta wadda ta share sama da shekara Dubu Ukku da kafuwa a cikin duniya ba inda ba'asan labarin Masarautar ba, a cikin kasar Gambia harma da kewayenta.

Masarautar kwata kwata basu san kima ko darajar bayin su ba, sun maidasu kamar wasu dabbobi wani bima har kwara dabbobi sun fisu ƙima a cikin masarautar Daborah, kuma sunyi suna wajen tarar abokan gaba daga ko ina a cikin sassan duniya, wanda suke da tarin makayaka masu karfin gaske, labarin su ya karade kaf nahiyar wannan dalilin yasa ake shayin haye masu wannan kenan.



Duke take tana ta famar naƙuda kamar zata mutu duk tagama fita hayyacin ta, duk yan uwanta sun zagaye kofar saboda gudun kar labarin naƙudar Binta tafita a cikin masarautar, kowa jininshi akan hakaifa yake, sai uban zufa suke ketawa karma ace mijinta Abdulmajid hakan bakaramin tada mashi hankali yakeba, itako Binta baiwar Allah sai addu'a su Jummai ke mata ciki ikon Allah ta surbuɗo kyakkyawar yarta santaleliya jajir da ita gwanin ban shi'awa, godiya taima Allah duk da tasha wahala hakan baisa hankalin ta ya gushe yabar jikin taba, kukan da jaririyar keya hakan yasa ya fita har waje da sauri Abdulmajid ya shigo ya dauke diyar ya boyeta, sannan yasa su Jummai suka shirya su, duk baki daya hankalin su yaki kwanciya.



Ladidi ce ta shigo sai haki take a cikin Turakar bayi ta shigo dakin su Binta duk sun raina gaskiar su, kowa yabita da kallan tuhuma ko lfy? Bude baki tayi tafara magana cike da tsoro duk ya mamaye ta tace."kin bani Binta wayace ki haihu a cikin wannan Masarautar? Ko kinsan kalar hadarin da kika jefa kanki?Kin manta da matsayinki a cikin wannan masarautar?Amman kikayi wannan gangancin."!? Duk a cikin tsoro tayi wannan tambayar maida kallonta tayi ga Abdulmajid tace. "yanzun kai Abdulmajid a matsayinka na uban bayi ya zakayi da wannan matsalar."!? Kowa ya kasa magana danko su jummai kuka kawai sukeyi sunajin tausayin Binta, karma ace yar jinjirar da batasan komai ba, zuwan ta kenan a cikin duniyar ga baki dayanta ma, kukan da yar tasu takeyi shi yakara jefasu cikin tashin hankali hakan yasa Binta daukar diyarta tafara bata nono kila tasamu kodan jinkai ne a wajen yarta bayan rasa su, magana Abdulmajid ya fara cikin damuwa yana cewa."Ladidi ko kinsan me kike fada, taya zamu kawar da abinda Allah ya kaddara mana, karfa kimanta munkai sama da shekaru Arba'in da aure muna neman haihuwar nan amman bamu samuba sai yanzun Allah yajikan mu yabamu sai mu yarda muce bamu so? mukasan ko wacece wannan yarinyar nan gaba? kisani ni Abdulmajid koda za'a sare kaina bazan taba wofintar da kyautar da ubangijina yaimani ba, bayan na bata sama da shekaru masu yawa ina nema kawai dan ina bawa sai in wulakanta wannan ni'imar mai girman gaske."? Yayi ma ladadi tambayar yana kallon kwayar idonta, girgiza kai tayi sannan tace. "Aa uban bayi ba nufina kenan ba nidai fatana Allah ya tsaremu daga sharrin makiya kuma yakare mana yar'mu." baki ɗayansu suka amsa da. "Ameen."


ita dai Binta ita kadai tasan halin da take ciki sai kuka takeyi tana addu'a Allah ya tsaremata yar'ta koda ace ba tare zasu rayuwa ba.

*∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆*

*FA'DA*


zaune take a saman karagar mulkin ta alfarma wadda tasha ado da ruwan gwal da arzurfa ta hakince sai takama takeyi da gadara sai fiffita ake mata cikeda izzah take kada yan yatsunta wa'anda suka sha gwala gwala saman kyakkyawn wuyanta shima yasha ado mai ban mamaki ta gyara gashin kanta da aka daura mashi crown sai shaining takeyi taji gwal baki daya farfajiyar fadar fadawa ne zaune a saman kujeran su a suka kewaye fa'dar sai tsakiyar fa'dar katon kafat ne wanda ya gaji da tsaruwa kujerar Sarauniyar ce a tsakiya sai sauran yan fa'da suka kewayeta inda akabari in anzo kowa zai duka saman kafat dinnan yakai gaisuwa wajen Sarauniya inta zauna sannan kowa zai zauna.


Ba abinda yaimata zafi ko magana ba tayi sai kaɗa kafar ta takeyi a hankali cikeda kasaita, jin Sarkin kofar ya shigo cikin fa'da yana dakatar da wata baiwa a cikin amintattun bayin ta, hakan yasa ta kalli wani dogari dake gefenta kallan sa kawai da tayi yasa shi tafiya da sauri yacema Sarkin kofa da ya budema wannan baiwar gate din shigowa cikin fa'da jikin shi na rawa ya bude mata ta shigo faduwa tayi saman tsakiyar kafat din fa'da takai gaisuwa wajen Sarauniya takai wajen minti biyar sannan Sarkin Zagi yace mata Sarauniya ta amsa, kanta a kasa a jin maganar Sarkin Zagi yabata ikon dagowa ta kalli Sarauniya tace."Allah yataimaki inane man izinin zanyi wata muhimmiyar magana mai mahimmanci aimin a fuwa tuba nike Allah yakara girma." a dakile ta daga mata hannu, sarkin zagi yace."an gaisheki Mero Sarauniya tabaki damar magana." ƙara duƙawa Mero tayi sannan tace."Godiya nike Allah yataimaki Sarauniyar Daborah ina tafe da wani labari mai girman gaske lallai yau antashi da alhini a cikin wannan Masarautar mai tarin albarka, yau a cikin Turakar bayi antashi da firgicin gaske yau dinnan Uwar bayi Binta ta haifi kyakkyawar yar'ta mace hakan yasa nace bari in hanzarta fada maki, Allah ya huci zuciyar ki yakara daukaka."



Miƙewa tayi cike da gadara tana kaɗa kai cikin izzah da isa sannan ta bude baki tafara magana, tana cewa."Sarkin fa'da kaida Sarkin horo ku hanzarta zuwa ku kamomin dasu baki dayan su harda yar da iyayen baki daya kuma nabaku nan da minti ukku." tashi sukayi suna cewa. "Allah yakara nisan kwana angama yanzun nan kuwa."fita sukayi da sauri duk cikin su ya duri ruwa, itako sai kai lawo takeyi cikeda da kasaita.


*∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆*



dauke suke dashi a saman wani gado daya gaji da kayatuwa bayine guda hudu suke dauke da wannan gadon mai dauke da kayan ado na jauhar da lu'u lu'u, sai daukar ido yakeyi ga dogarawa sai dukan wadannan bayin sukeyi hakan yasa wani matashin Saurayi yayi magana a hankali yana saman gadon duk da bazai wuce shekara goma sha biyar ba a duniya ba, ba karamin bacin rai bane ya kama shi ba, suko wadannan dogarawan sai ahi sukeyi suna neman tuba kallonsu yayi sannan yace. "daga yau karku sake ku kara dukan su me sukai maku da zaku dinga zalintar su? ga aiki sunayi ga duka dame kuke son suji."? Ya ida magana cikin saukin rai, cewa sukayi. " Allah yahuci magajin gobe tuba mukeyi Allah yakara maka lafiya." haka sukaci gaba da tafiya dashi sai a lokacin bayin nan suka samu sukuni ba inda suka isa sai bakin kofar shiga fa'da, da sauri Sarkin kofa yafara koda wannan kyakkyawan Saurayin mai farin jini ga alumma Masarautar, a hankali yake tafiya har ya isa wajen zaman shi, nan ya gaishe da Sarauniya sannan ya zauna a gefen ta saman tashi kujerar duk danya fahimci ran ta a bace yake sai dai baiyi magana ba, ba dan yana san zuwa fa'da ba yasan ba yanda zaiyi dole yazo, gani yayi dogarawa nata dukan wasu bayi, kamar zasu kashe su ga jinjira a hannun su bakaramin taba ransa hakan yai ba, ba inda suka gurfana sai gaban Sarauniya kowa yakawo gaisuwa jikin su sai uban ɓari yakeyi duk sungama tsorata Abdulmajid ya duƙa duk da bugun da suke mashi, amman sai da yace. "Allah yataimakeki kiranki ya samemu kimana aikin rai." ya ida maganar hawaye suna tsiyaya a idonshi, tahowa tayi kusa dashi ta wasga mashi wani kalar masifaffan mari mai rudarwa,dafe wajen yayi yana jin ciwon abunda Sarauniya tayi mashi, sake cewa tayi."tuba mukeyi Allah ya kara girma." zagaye fa'dar ta kamayi tana ciwon yatsa, dawo tayi tana kallonshi sannan tace. "Uban me yasa kuna bayina zaku sake jiki har ku haihu a cikin masarauta ta? Har yaushe kukeda wannan yanci? Ku kuka ka fara karyaman dokata, kuma manyan bayi lallai kun raina dokar Sarauniya Zulaiƙha kenan."?



Cikin dakiya da tsoro yace. "kiyi mana aikin rai haka Allah ya kaddara....wani kalar wawan kallo ta aika masu dashi, wanda yasa kowa yayi kasa da kanshi cike da tsoro, ya kasa karasa maganar da yayi niyar gaya mata.



Sarauniya Zulaiƙha kenan wadda ta kasance ya ɗaya tilo a wajen Sarki Abduljabar wadda ta gaji mulki mai girman gaske a cikin masarautar Daborah itace Sarauniya ta talatin dake gabatar da mulki a cikin masarautar Daborah, wannan shine kadan daga cikin nasabar Sarauniya Zulaiƙha.


kowa ya nutsu kamar ba dan adam a wajen danko Binta ko magana takasa jitake kamar tayi fitsari tsabar firgita ga tana fama da raunin haihuwa, jin maganar Sarauniya Zukaiƙha ya dawo da ita cikin hayyacin ta. "Sarkin horo anshe waccen jinjirai kaje ka yanka ta sannan ka binne mani gawar ta, su kuma ka kaimin su gidan kaso aita dukan su sannan ajefe su har sai sun mutu." ba Abdulmajid ba duk wanda ke fa'dar nan saida gaban shi yai mummunar faduwa, haka Sarkin horo yazo ya kama jaririyar nan uwar ta rike daura mata mari yayi, hakan yasa ta saki sai kuka takeyi da sauri wannan dan Saurayin ya tashi yafara magana, jin maganar shi yasa Sarkin horo tsayawa, cikin sanyin jiki yace dan baiji dadin abunda mahaifiyarshi tayi ba, cewa yayi. "Allah yahuci zuciyar Sarauniyar Daborah, kiyi masu aikin gafara haka Allah yaso karki zartar da wannan hukuncin akan jinjirar da bata san me akeba na rokeki kiyimasu afuwa." ba karamin mamaki ya kama taba ace dan' data haifa shikejin tausayin bayi har haka, kallonshi tayi cikin mamaki dan abun ya bala'in bata mamaki ace ɗan da ta haifa yake tausayin bayi har haka cewa tayi. "Yanzun ace jinina ɗa'na ace kai zakaji tausayin wadannan kaskantattun mutanen wadan da basu da wani anfani ko daraja suna bayin wulakantattu abin yarwa, karka manta bayi fane."?
Murmushi yayi wanda ya ƙara mashi kyau sannnan yace. "Allah ya baki hakuri Umma, amman kiyi masu lamani ki yafe masu, kuma koda suke bayi, AI BAYIMA ƳA'ƳANE ki yafe masu."



Yarima Abdulmalik kenan ɗa'tilo ga Sarauniya Zulaiƙha ta dauki son duniya ta daura mashi, batasan abinda zai same shi ko kadan hakan yasa tasa ake koya mashi dabi'un Sarauta duk da bai anfani da kalar abinda takeso yafiye tausayi shiyasa take cewa ubansa ya gada, mahaifin sa Saifullahil islam Sulaiman, shi kuma babban dan kasuwa ne mai fa'da a ji cikin kasar Gambia harma da kewaye matarsa daya sai dan'sa Abdulmalik wanda suke kiran shi da MalikusSaifil islam ko suce mashi Malik wasu kuma sunai mashi inkiya da sunan mahaifin sa MalikusSaif, duk da ya tashi cikin gata hakan baisa ya dauki duniya da zafi ba, ya gaji da haduwa kyakkyawa ne ajin farko ya gaji da haduwa saidai farine kuma dogo ne jayant, duk da kyawunsa bai gama fita kasancewar yanzun yake girma bazai wuce shekara goma sha biyar ba a duniya.

Kallonshi tayi sannan tace."Malik? Kasan me kake cewa? dan bayi na ƴa'ƴa bashi zai nuna suki bin dokata ba." matsawa yayi kusa da ita dan ya lura rainta ya ɓaci sosai cewa yayi. "Umma karki manta bantaɓa neman alfarma ba bakimin ba, dan Allah kiyi hakuri kibar wannan yarinyar kinga daman banda kanwa kibari su kula da ita inta girma sai ta dinga yimin hidima kitai maka mani." ya ƙarasa maganar yana kwantar da kanshi bisa kafaɗarta, dan tunani tayi sannan tafara magana cike da gadara batasan Malik ya tambaye ta alfarma ba tai mashi itaba ko da zata rasa komai nata cewa tayi. "Shikenan da'na na kyaleta amman meyasa duk bayin nan dake cikin masarautar nan karasa wadda zatai maka hidima sai wannan jinjirai."? Murmushi yayi daman yasan zata bar mashi ida tunda ya nemi alfarma ta farko a wajenta cewa yayi. "Aaa Umma insha Allah zata girma kuma inasan a sakamata suna BAHIJJAH, shine sunan da nafi so Umma." kasa matso Sarauniya Zulaiƙha tayi tsabar mamaki wai MalikusSaif shike zaɓama bawa suna, bama ita ɗaya ba Kowa mamakin Yarima MalikusSaif sukeyi duk da yanada tausayi amman ya nuna damuwar shi akan bayin nan sosai, daurewa Sarauniya Zulaiƙha tayi sannan tace. "Sarkin horo bata yarta, su kula da ita, amman kaje dasu a cikin Turakar bayi kaima kowan nan su bulala tamanin tamanin dan yazama izina ga kowane bawa, sunci darajar da'na MalikusSaif, lallai da yau dinnan sai nasa an hala kaku, sannan kunji abinda da'na Malik yace yana san asaka mata suna Bahijjah, inasan kullin ku dinga kawota tana gaida Malik safe da dare tunda yace yana sonta, kuma kuci gaba da koya mata taka tsantsan akan lamuran MalikusSaif, har girmanta zata zama baiwar MalikusSaif in kunne yaji."?



Duk da baiji dadin dukan da tasa za'ayi masu ba, amman yasan hakan ma ba karamin adalci tai masu ba, godiya sukai mata suka tashi Sarkin horo ya tisa su gaba, sannan Malik ya rike hannun mahaifiyar shi yai mata murmushin karfin hali yaimata godiya, shafa ƙanshi tayi sannan tace."Malik ba abinda bazan iyaba akanka da'na komai naka ne." Suko su Binta haka aka dire masu bulalai a gaban yan uwan su bayi gata da danye jiki azube aka barsu bayine suka daukesu suka shiga dasu cikin gida cike da tausayin su saida kowa ya tsorata ganin abinda ta faru da iyayen bayi inaga su.



Share
Comment
And
Vote

*BAYI MA ƳAƳANE*


*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*


```kungiya daya tamkar da dubu, masu aiki da iliminsu```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________


*BEST OF 2021*



*Free book ne📚🖊️*



*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

*naji dadin comment dinku gaskiya, kuma naji dadin yanda BAYI MA ƳA'ƳANE hakan yayi man sugar sosai wlh, inayinku son fissabilillah ❣️*


Babi na biyu



Koda aka maida Binta cikin dakin su ba abinda take banda kukan azaba ga jikin ta duk ya tulbe jini yana zuba ko zama ya gagareta lamarin gwanin ban tausayi, mijinta Abdulmajid shine yayi karfin hali duk da shima yana jin jiki amman haka ya daure ya rike matar shi yana bata baki har ya samu baccin wahala ya dauketa ga yunwa yana ji bai auneba yaji yar su nata kwalla uban kuka haka Binta ta tashi a galabaice ta fara bata nono duk da ba komai a cikin cikin ta, amman ba yanda ta iya gwanin tausayi haka Abdulmajid ya dinga jin tausayin iyalinsa karma ace yar jinjirar yar su wanda baisa kalar rayuwar da zata fuskanta ba anan gaba yasan tana cikin barazana mai girman gaske a cikin Masarautar Daborah.


Tunda Yarima MalikusSaif ya koma katafaren sashen shi ba abinda ke mashi yawo a cikin zuciya kamar tausayin bayin nan musamman yanda yaga kalar tozarcin da akaima waɗan dattawan a cikin fa'da yarasa yanda zai ɓulloma kalar wannan aƙidar ta mahaifiyar shi yana cikin wannan tunanin ne baiwar shi Shamsiyya ta shigo da hadimai kawo mashi abinci, sallama sukayi baki dayan su, duƙawa sukayi suka kwashi gaisuwa duk da Masarautar su ba'asan darajar bayi ba amman hakan bai hana Yarima MalikusSaif sakarma bayin nan fuska ba, "ranka shidade ga abincin da kace a girka maka nan, Allah yakara maka girma angaishe da Yariman Daborah." Cewar Shamsiyya mai kula da abincin Yarima MalikusSaif, cikin sakin fuska ya gyaɗa masu kai duk da bai fiya san magana ba amman yana da kyakkyawar alaƙa da bayin Masarautar su, zuba mashi abincin Shamsiyya tafarayi tana cikin zubawa ya dakatar da ita sannan yai masu izinin tafiya.



A wajen Sarauniya Zulaiƙa kuwa ranta ne yai masifar ɓaci bare in ta tuna karya mata doka da bayin nan sukayi sannan a wani ɓagaren a zuciyar ta tana mamakin meyasa Yarima MalikusSaif ya kubutar da bayin nan a kan hukuncin da tai niyar yimasu bayan ba yau ta saba kayan ke hukuncin akan bayi da talakawan ta ba, sannan meyasa yace dole sai wannan ficiciyar jinjirai zaice yana so ta zama hadimar sa, saidai tasan ɗanta bai damu da shiga a sabgar bayi ba shiyasa tunda ta fahimci yanda yakeda da tausayi bata bari yana yawan hudda da bayi.


Tayi nisa a cikin tunani mai zurfin gaske saiga Jakadiya ta shigo dauke da katan ture tareda bayi suna take mata baya, baki dayan su suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa amman ko inda suke bata kalla ba, balle su saka ran zata amsa masu gashi su dukan su kansu kasa ko haɗa ido basuyi da ita kowa jikin shi sai kyarma yakeyi kamar wasu munafukai, sunkai sama da minti goma a haka sannan ta buɗa baki cikeda gadara tace."Jakadiya."jikin Jakadiya ne ya hau kyarma da sauri ta amsa tana neman ahi wajen Sarauniya. "Allah yakara miki karfin iko umurnin ki abin tunkaho a gareni Allah ya huci zuciyar surkulle mai wuyar fassara turmin tsakar gida sha lugudan mahassada anbuga dake anbarki Sarauniya Zulaiƙa Masarautar Daborah da abin dake cikin a karkashin ikon ki take Allah yakara maki girma ina sauraran umurnin ki." duk wannan kirari da Jakadiya tayi ma Sarauniya Zulaiƙa bai sa tayi murmushi ba ko kuma ta nuna jindadin kirarin da tayi ma sai ma ƙara tamke fuska da tayi cikin izza tace."Ina fatan kina ba Yarima MalikusSaif kulawa ta musamman sannan kin tabbatar da tsaran sashen Yarima."? Ƙara ɗukawa tayi sannan tace."Allah ya kara maki girma ban tunanin akwai inda akeba tsaro kamar sashen Yarima MalikusSaif." cewar Jakadiya, cikeda gamsuwa Sarauniya Zulaiƙa ta gyaɗa kai dan a halin yanzun ba abinda ta ɗaurama buri kamar Malikussaif bare in ta tuna da yanda take da abokan gaba daga sassa daban daban a duniya wanda ma bata san da zaman wasu ba, wannan dalilin yasa Sarauniya Zulaiƙa bata bari wani ya raɓi Malik dan tasan shine rayuwar ta.



Bayan sati ɗaya Yarima MalikusSaif ne a saman wani bene wanda akayishi da ginin jan gargari yana ta nazarin rayuwa duk lamarin duniya ya sha mashi kai ga yana tambayoyin da yake so yaima mahaifiyar shi amman baisan yanda zata ɗauki maganar ba, sannan a dayan gefen shi Jarumai ne keta faman wasanni da wuƙaƙe suna ta gwaji saboda Masarautar suna da Jarumai wanda basu san iyakar su ba kullin suna cikin shiri kodan farmakin abokan gaba, kallan su yake suna bashi shi'awa Sarkin yaki ne yazo wajen Yarima MalikusSaif ya gaishe shi cikin sakin fuska ya amsa"Allah yataimaki Yarima MalikusSaif yakamata ka sakko kayi training kaga ka kwana biyu bakayi gwaji ba."cikin gansuwa Yarima MalikusSaif yace. "Eh hakane sai dai bazan samu damar yin gwaji ba yanzun, amman wani lokacin zanyi ina bukatar hutu." rissinawa Sarkin yaki yayi sannan yace'' Hakane yaka mata ka kara samun hutu saidai Jarumai na bukatar ganin ka a cikin su kodan kara samun kwarin guiwa dan ganin sun samu gwaji mai inganci Allah yataimaki magajin gobe." cikin jindadi Yarima MalikusSaif yayi murmushin dake kara bayyanar da kyawunsa duk da kasancewar shi baƙi amman hakan bazai hana bayyanar kyakkyawar surar shi ba, Yarima MalikusSaif kyakkyawa ne ajin farko ya kasance mai sanyin hali wanda kowa ke kauna a cikin Masarautar Daborah, saidai shi dogo ne yanada manyan idanu masu daukar hankali sannan kwata kwata shekarar shi shabiyar a duniya,wannan kenan..


Koda Sarkin yaki yatafi, hakan yasa Yarima MalikusSaif ya tafi sashen mahaifiyar shi, inda bayi ke take mashi baya har ya isa wajen mahaifiyar tashi.


Yana isa bayi ne keta hidima duk inda zai wuce sai sun duƙa sun gaishe shi, basu waje sukayi, cikin jindadi Sarauniya Zulaiƙa ta kalli ɗan ta, saidai ta fahimci yana cikin damuwa tashi tayi daga kishingiɗar da tayi ta zuba mashi ido gaida ta yayi cikin kulawa ta kama hannun shi sannan ta fara magana...


"Abdulmalik." a hankali ya kalli fuskar mahaifiyar shi cikin murmushi mai karama shi kwarjini,sake cewa tayi."Mike damunka."? Numfasawa yayi sannan ya ce"ranki shidade inatare da matsananciyar damuwa a cikin zuciya na daɗe ina neman amsoshi masu yawa saidai ban san taya zan fara ba." Mamaki yakama Sarauniya Zulaiƙa tana ayyanawa aranta daman akwai abin da zai damu Malik har haka bata sani ba? ina hankalinta da tunanin ta ya tafi har tabar ɗanta a cikin damuwa, ta tabbata inda Safulislam nanan bazai taɓa barin ɗansa cikin damuwa ba amman zata samu ta ɗebemasa damuwa kafin mahaifin sa ya dawo daga fatauci, sake kallan shi tayi tace"Haba Malik wannan wane irin abune da zai takura ka har haka? Fadaman shi duk duniya baka da wadda ta fini sannan karka manta duk abinda ka gani a cikin Daborah ikon ka ne, fadaman damuwar ka."? Duk da yasan mahaifiyar shi bata haɗa shi da komai ba saidai yana shakkar yimata waɗan nan tambayoyin, jin ta sake rike mashi hannu yadawo dashi daga tunanin da yatafi, ajiyar zuciya ya sauke sannan yace"Umma

Please Login or Register in order to submit comment