Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inasan insan me yasa wannan Masarautar take fama da abokan gaba tun tasowa ta ake abu daya har zuwa yanzun."? Zamanta ta gyara zuciyar ta na ƙuna wata irin zazzafar gaba na dawo mata sabuwa take idanun ta suka kaɗa sukayi jajir kamar garwashi saidai wani ɓangare na zuciyar ta bata jin zata kasa bawa Malik tarihin wannan gabar da suke fuskan ta a cikin Masarautar Daborah.....ganin halin da mahaifiyar shi take ciki yaji ya shiga damuwa tare da danasin yimata kalar wannan tambayar duk da yana bukatar karin haske a kai,cewa yayi. "Umma bansan tambayar da naimaki zata ɓata maki rai ba kiyi hak.....bai karasa ba Sarauniya Zulaiƙa ta rufe bakin MalikusSaif tareda girgiza mashi kai tace "Aa Malik baka ɓata man rai ba sannan karka manta kaine magajina dole insanar dakai amsar tambayarka kodan kasan inda ka dosa lallai Malik wannan tarihi ne mai tsawon gaske wanda saidai in baka abin da ba arasa ba daga baya ka ida samun wasu amsoshin musamman in kana bibiyar kayan tarihi na wannan Masarautar mai tarin albarka, ina fatan zaka maido hankalin baki dayan shi akai na sannan duk abinda ba faɗa wanda yasaka cikin damuwa ka nemi karin haske ya Malik, tashi tsaye tayi tana zagaye kata faran parlourn sannan tace....


*my real fan's show me ur real love to paid my new book his name BUƊADIYAR SOYAYYA💔*



Share
Comment
Vote


*BAYI MA YA'YYANE*


*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*

```kungiya daya tamkar da dubu, masu aiki da iliminsu```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________

*BASED OF 2021*

*Free book ne📚🖊️*
```amman fa rashin comment dinku zaisa ya koma na kudi, amman idan kuna comment babu chanjin ra'ayi free book ne🥰```


*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*




*Wannan page din nakine Deeymusy(my Dejja) ki sani inayinki sosai kuma ina maki son fissabillah💞*


*Ina masoya kuma makaranta novel do MAGEN NANA CE? Na Sa'adatu rabi'u, ga dama ta samu duk mai karanta novel din to ga link an bude maku yanda zaku samaishi ckin sauki Amman a tabbatar da za'ayi comment 👇*

https://chat.whatsapp.com/FvGEKVbSNBK1qOZccO97Xs






Babi na uku


A salin labarin Masarautar Daborah da abokan gaban ta.

"Malik Masarautar Daborah takasan ce Masarauta mai tarin albarkatu nadaga zinarai lu'u lu'u da jawhar sannan Masarautar mu ta shahara wajen artaba da abokan gaba saidai muna da mayaka masu yawan gaske kuma idan muka tunkari abokan gaba sai munyi galaba akan su....

A zamanin kakata Sarauniya Yahanasu kakata ta bakwai take ba mahaifin kakana wannan labarin da zan baka Malik, lokacin da Sarauniya Yahanasu take a karagar mulkin Daborah suka sunkayi tashin hankali mai rikitar wa suna zaune a fa'da anata fadanci kowa hankalin shi kwance baida wata matsala sai ga Sarkin kofar gabas ya shigo a cikin fa'da yana ta haki kamar wanda aka kwato shi a hannun gawurtaccen zaki hakan ba karamin tada hankalin Sarauniya Yahanasu yayi ba a kiɗime suka fara jefama Sarkin kofa tambayoyi da kyal yace Allah ya taimaki Sarauniya mai dole kurace daga gabas ta tunkaro wannan Masarautar na manyan mayaƙa wanda baka iya hango karshen yawan su.... bai karasa maganar ba Sarauniya ta daka mashi uwar tsawa mai rikitarwa take taje ta dauki kugen yaki da kanta ta buga kuge cikin kankanin lokaci mayaƙa sun fito a hargitse kowa cikin fargaba, da kanta ta hau munbari ta faɗa masu ga magota nan sun kawo ma Masarautar Daborah hari dan yaka kowa ya shirya duk da cikin minti goma zasu iya shigowa cikin Daborah baki daya wajen ya harmutse da hayaniya kowa ya shiga shiri hankalin Sarauniya Yahanasu yayi masifar tashi itama shiga tayi sashen ta tafara shirin tarar abokan gaba, suna cikin shiri ga sarakunan kofuna duk sun rufe kofofi duba da yanda Masarautar takeda kofofi har guda hudu gabas yamma kudu da arewa a cikin mayaƙan dake garemu wasu anturasu fatauci kafin su ankara sukaji ana bugun kofofi da guduma cikin kankanin lokaci suka farma Masarautar nan da sara ba addina da kibiyoyi sarkin yawa yafi sarkin karfi duk da Jaruman mu basu shirya ba amman sun dage akan abokan gaban su, inda sarkin yaki Zaidu da yan tawagar shi suka cimma waɗan nan mayakan da suka shigo ta kofar gabas kowa sai murna sukeyi ashe ko kwata daga cikin wɗan nan mayaƙa ba'a kashe ba haka sukayi shiru saida suka bari Mayaƙan mu sun lafa suka shigo masu ta kofar arewa da kufu duka saka Mayaƙan Daborah tsakiya suka dinga sare masu kai baji ba gani hakan yasa Sarauniya Yahanasu ta fito a cikin shirin ta ta faɗa cikin wannan artaba akaita fafatawa da ita dayake kakata jaruma ce kuma bata shakkar abokan gaba ta dinga sauke kawunan maza suna zuba ƙasa ba abinda ke yawo a cikin wannan filin banda zubar jinin kayaƙa dubawar da Sarauniya zatayi taga wasu mayaƙan masu yawan gaske sun sake tunkaro su gashi Jaruman ta sun kusa karewa duk da haka Sarauniya Yahanasu bata karaya ba haka taciga da kashe maza tareda sauran mayaƙan ta waɗan da suka rage a tare da ita.......



Numfasawa Sarauniya Zulaiƙa tayi wanda idanun ta ke zubda kwalla sannan tace Malik a lokacin nan nafada maka cewa rabi da kwatan Jaruman Daborah sun tafi fatauci, duk da haka sukaci gaba da artaba akan abokan gaba basu karaya ba haka sarkin yaki Huzaifa ya dinga yima maƙiya kisan gillah



Saidai kasan ance Sarkin yawa yafi Sarkin karfi koda su Sarauniya Yahanasu suka ci karfin waɗan nan abokan gaba sake ganin waɗan su sukayi waanda suka doke n farko yawa sun sake haiƙe masu tun da karfin mayaƙan mu haryakai ga karfin hali kawai sukeyi ana cikin hakane wani azzalumin bawa dake cikin tawagar waɗan nan abokan gaba suka sare kan Sarkin yaki Huzaifa gashi ya rike tutar Masarautar Daborah tunda shike jagorantar tafiyar nan haka Sarauniya Yahanasu tayi ta maza ta riko wannan tuta haka sukaci ga da fafatawa da ita akwai wani basamudan bawa tunda ake wannan yaƙi hankalin sa nakan Sarauniya Yahanasu duba da kalar Jaruma tarta aiko yasa kibiya ya harboma Sarauniya a saman ciki haka ta faɗi wannan a kasa amman bata mutimu kuma hannun ta na rike da wannan tutar zamanin kakan kaka na Jabbar yana matashin Saurayi kuma baida lfy a lokacin da aka kawo wannan farmaki a gaban idan sa aka kashe mahaifiyar shi duk da yasan abinda suka kawo su a cikin Masarautar Daborah, hakan yasa wasu daga cikin amintattun Masarautar mu suka bi ta hanyar sirri suka gudu da Yarima Jabbar kasancewar shine magajin Sarauniya Yahanasu, haka sauran mayaƙan sukaci gaba da artaba akan abokan gaba ganin za'a karar dasu baki daya haka yasa suka fara guduwa intakai ce maka tarihin Sarauniya Yahanasu da zamanin ta Malik haka magota suka shiga cikin Daborah suka tunkari cikin Masarautar dan kwasar gani ma ta dukiya koda suka iske Sarkin taska suka kwace makullin taskar sannan suka kashe shi haka suka kama kwasar gani ma kamar wasu mayu saidai abinda basu sani ba karamar taskar Daborah ce suka buɗe koda baban Sarkin taska Ganiyu yaga haka guduwa yayi saidai bai fita ko inaba yana cikin Masarautar Daborah, haka Sarkin su Faihasu yabar ɗansa Ƙaisu da niyar cigaba da mulkin Masarautar Daborah a tunanin su sungama kashe kowa a cikin Daborah saidai bayi waɗan da suka kasan ce a karkashin ikon Sarki Ƙaisu.......hmmmm Malik kana tunanin akwai ranar da takuban mu zasu sauka ƙasa akan abokan gaba? Shima numfasawa yayi cikeda da tausayin Sarauniya Zulaiƙa yace"Umma ba rana ba wata saidai kince an gudu da Yarima Jabbar ya abin ya kasance."? Murmushi manya Sarauniya Zulaiƙa tayi tana shafar fuskar ɗanta cikin so da kauna tace. "kana nufin baka gaji da jin wannan labarin doguwar gabar ba."? Murmushi yayi sannan yace." Hmm Umma kenan taya zangaji bayan na daɗe ina jiran wannan ranar." jin shigowar Dammur ya katse masu hirar su duƙawa yayi ya gaishe da Sarauniya Zulaiƙa kallan ɗaya yai mata ya fahinci damuwar ta kuma koba'a faɗa mashi ba yasan meke damun Sarauniya Zulaiƙa, numfasawa yayi yace."Allah ya huci zuciyar uwar gijiyata tabbas ganin ki cikin ɓacin rai ya bani amsoshin tambayata tabbas Malikussaif duk lokacin da kaga Sarauniya a wannan yanayin yana tuna mata kalar cin amana da magota sukayi ma wannan Masarautar tamu mai albarka." mamaki yakama Malik ganin har Dammur yasan halin da suke ciki murmushin takaici Sarauniya Zulaiƙa tayi sannan tacigaba fa bama Malikussaif amsar tambayar da yai mata.....


```Ikon Allah komai abokan gaba suke nema a cikin Masarautar Daborah masoya sai muzuba kunne muji me Sarauniya Zulaiƙa zata cema Yarima Malik......
```

A lokacin da suka gudu da Yarima Jabbar ba inda suka yadda zango sai wani sansani na Daborah wuri ne na sirri ba kowa yasan wajen ba sai amintattun fadawan Sarauniya Yahanasu suna zama kowa hankalin shi a tashe yake a cikin ga tashin hankali da ya dira a cikin zuciyar Jabbar ba abinda yake tuna wa yanda aka kashe mahaifiyar shi a gaban idon shi, haka sukai ta zama har tsawan kwana bakwai, wakilai suka saka dukkan su sunyi shigar sirri wanda ba kowa ke iya gane suba haka suka dinga zagaye har suka fara ganin Jaruman su sun fara dawo wa haka sukayo dasu a wajen da suka fake, koda sukaga su Jabbar a cikin hali ba karamin tashin hankali suka shiga ba, tambayar su ba'asi sukayi, haka suka kwashe komai suka faɗa masu kowa saida ya girgiza da jin wannan mummunan maganar, shawara suka yanke akan zasu koma dan su kwatar ma kansu, yan'ci umurni Yarima Jabbar yaba yan tawagar su, akan suje dan suga halin da Masarautar mu take ciki, haka sukaje suka iske komai an sauya shi duk bayin mu da sauran mutanan mu basu da iko akan komai na Masatautar mu, bayan sun dawo suka faɗama Yarima Jabbar halin da ake ciki a cikin kwana ukku suka shirya kansu kowa ya ɗauki takubba da kubiyoyi.....ranar wata lahadi da safe su Yarima Jabbar da babban Jarumin Daborah Maishir suka shirya suka tafi cikin Masarautar Daborah wannan karan ta kofar kudu suka shiga cikin Masarautar a hankali suka dinga yima mutanen Sarki Ƙaisar kisan gilla dayake sunsan sirrin Masarautar su haka suka dinga kashe su kamar kiyashi sadda zasu farga har sun shigo cikin tsakiyar Masarautar abu kamar wasa sadda zasu farga sunci galabar su haka a ka dinga fafatawa cikin kankanin lokaci sunyi masu fata fata ana cikin ɗauki ba daɗi suka fille kan Sarki Ƙaisu haka suka cake kansa a saman mashi sannan suka kama Jaruman su, suka maida su bayi, a cikin su suka tada mutun ukku, suka rubuta masu sakon da zasukai ma uban Ƙaisu, Sarki Faihasu cikin tashin hankali suka tafi jiki ba kwari haka kowa yaita murna Masarautar Daborah ta dawo wajen ku nan aka naɗa Yarima Jabbar a matsayin Sarkin Daborah duk da suna cikin farin ciki amman kowa najin alhini na rashin Sarauniya Yahanasu, a hankali mutanen mu suka dinga dawowa cikin Masarautar haka akacigaba da hudɗa kamar kullin amman kowa na cikin shiri a wane ɓangare na Sarki Jabbar yasa aniyar ɗaukar fansa a wajen abokan gabar mu......cikeda kulawa gimbiya Zulaiƙa tacema Yarima Malikussaif haka rayuwa ta kasance a cikin Masarautar Daborah.......


Rude idansa Yarima Malikussaif yayi yana nazarin lamarin Masarautar Deborah sai ynzun yasan dalilin da yasa ake yawan kawoma rayuwar shi farmaki, bude idan shi yayi a hankali wa'anda sika kaɗa sukayi jajir yace."Umma abu biyu ke yawan damu na a cikin zuciya ta na farko menene dalilin dayasa ake yawan kawo ma Masarautar Daborah hari me suke buƙata a wajen mu."? Cewar Malikussaif yaima Sarauniya Zulaiƙa wannan tambayar, shiru tayi naɗan wani lokaci sannan tace"kayi tambaya mai anfani saidai zanso ka jinkirta neman wannan dalilin duk da yanada anfani a gareka Malikussaif saidai ka sani a halin yanzun bashi nike son ka fuskanta nafi son ka maida hankalin ka a fagen mulki kodan ka kara tabbatar da nasabar ka sannan kaine magajina wanda zai gaji kujerar alfarma ta Sarautar Daborah....... Saidai kafin nan zan kara faɗakar da kai ban lamunta da ka dinga sakin jiki da kowa ba, kuma kasan hannun ka Malikussaif hakan yana da anfani a gareka." Shidai tunda ta fara magana yake kallan ta gyada mata kai yayi cikin gamsuwa, saidai wannan karon yayi mata tambaya a takai ce, "Allah yataimaki Sarauniyar Daborah, da Sarki Jabbar ya amshi Mulkin Daborah ko ya ɗauki fansar kisan da akaima Sarauniya Yahanasu."? Kallan juna sukayi ita da Dammur duk da sunji dadin tambayar Yarima Malikussaif,hakan yasa ta sake maida hankalin ta ga ɗan nata sannan tace"ƙwarai kuwa ya ɗauki fansa mai girman gaske saida ya saka masu tsoro da razana a cikin zuciyar su da shakkar Masarautar Daborah saidai ba yau zan ida faɗamaka wannan tarihin ba, inka sake samun lokaci kazo in karasa baka ko kuma ka tambayi Sarkin adana tarihi na wannan Masarauta, ina fatan zaka dauki abubuwa masu matukar mahimmanci a cikin wannan labari da na baka, akan gaggarumar gabar dake tsakanin mu da Masarautar Waisu.......Yarima Malikussaif zaiyi magana kenan sai ga Jakadiyya ta shigo dukawa tayi ta gaishe su, sannan ta sanar uwar gijiyar ta manyan bakin da sukayi a fa'da........

*A gsky idan baku comment zan daina yi ne fa😢, dan banjin dadin abinda kuke man gaskiya*


*Yar Mutan Kankia ce❣️*

*Muje zuwa....🖤*

Share
Comment
Vote

*BAYI MA YA'YYANE*
*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________

https://chat.whatsapp.com/H5RHfKhkR2eCXckRXP2SLr
_Ga link nan ku shiga domin samunshi daga farko kuma ku dunga samun update kan lokaci, dan banjin dadin yanda kuke tmbyata daga farko fa, pls ki shiga kuma kisan zakiyi comment 💞_

*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*


Babi na huɗu


Bayan wasu kwana ki Yarima Malik ne a cikin ɗakin shi kwance, ya rufe idan shi kamar mai bacci a zahiri, saidai ba baccin yakeba ba abinda yake tunawa sai halin da Bahijja take ciki shidai har a zuciyar shi yarasa dalilin da yasa yake jin tausan su, kuma baisan yanda akayi ba yake yawan tunawa da jinjiran nan ba, duk da yabata Bahijja saidai baida tabbacin ko iyayen nata zasu amince da sunan da ya zaɓa mata, yana cikin wannan tunanin baiwar shi mai gyara ɗakin shi ta shigo da sallama duƙawa tayi ta gaida shi, duk da idan shi na rufe hakan bai hana shi amsawa ba ciki ciki shiru ne ya biyo baya tanasan ta fara aiki kuma bata san ta takura mashi ganin bai tashi daga gadon ba komawa tayi gefe ta zauna kusan minti sha biyar hakan yasa ya zauna ya zuba mata manyan idanun shi masu firgitar wa ganin kallan da yake mata ne yasata jikin ta yin sanyi duk ta tsargu, kauda kanshi yayi kamar wanda akaima laifi, hakan yasa ta fara neman afuwa"Allah ya huci zuciyar magajin gobe bansan shigowar da nayi ba naɓata maka rai ba, kaimin aikin gafara." Shi mamaki ta bashi ganin sai ahi take yi bayan yasan ba abinda taimashi mikewa yayi yasa ta haɗa mashi ruwan wanka bayan ta gama haɗa mashi, yafara magana kamar wanda baisan maganar "kije turakar bayi ki anso mani Bahijja."saidai Mairo ta waiga ta tabbatar da shi yayi maganar tayi mamaki ganin yanda baidamu da kowa ba amman har yake son ganin Bahijja shi kanshi yaga tsantsan mamakin ta asaman fuskar ta, shigewa yayi toilet ita kuma tashi tayi ta tafi sai al'ajabi takeyi koda ta isa turakar bayi sashen Binta ta wuce ta fada mata sakon Yarima MalikusSauf, tunawa tayi da alkawalin da sukayi a fa'da wajen Sarauniya Zulaiƙa zasu dinga kai mashi Bahijja tana gaida shi, abinda yasa bata kai taba batasan su sake shiga cikin wani mawuyacin halin, maganar da Mairo tayi mata shi ya dawo da Binta a duniyar tunani, mika mata Bahijja tayi badan ta soba, tafiya sukayi lokacin da ta isa wajen Yarima MalikusSaif iske shi tayi zaune a saman kafat yana cin kayan marmari koda Mairo ta shigo da Bahijja kallan ta kawai yakeyi ganin yanda taketa wasan ta cikin farin ciki tana wasa, tana isa ta duka ta gaishe shi sannan ta mika mashi Bahijja, ansar ta yayi yana mai jin tausan ta a cikin zuciyar bare in ya tuna da kalar rayuwar da zatayi a matsayin ta na baiwa, saidai ya kuduri bazai taɓa bari Bahijja ta shiga cikin ƙuncin rayuwa ba kamar yanda iyayen ta suke ciki, haka Mairo taci gaba da aikin ta shiko MalikusSaif sai murmushi yakeyi yana kara yabawa da kyawun Bahijja duk da ba zata wuce shekara daya ba wasa ta kamayi da yatsun shi shima wasan yake mata sai dariya takeyi shima baisan ya ɓuge da dariyar ba itako Mairo dake aiki sai mamakin kalar kaunar da Yarima Malik kema Bahijja kamar kanwar shi ta jini haka ya dinga bata dafafar madara tana sha, shiko saijin dadi yakeyi tana kara shiga cikin ranshi "Bahijja Allah ya rayamin ke Allah yatsaremin ke Bahijja gashi kinzo a baiwa, zaki shiga cikin wata kalar rayuwa saidai kisa a ranki Bahijja kin samu ɗan uwan da kula dake Bahijja ta." itako da batasan me yake nufi ba sai dariya takeyi yana bata madara har Mairo ta kammala aikin ta, ji yayi kamar karya rabu da Bahijja saidai ba yanda ya iya haka ya mika mata ita da wata babbar leda godiya tai mashi sannan ta tafi har cikin ɗakin uwar bayi itada su ladi ta iske su haka taba ta Bahijja da ledar da yaba Bahjja suna buɗewa kayane masu kyau sai kaya makula she na yara sai murna sukeyi, suna mamakin kalar kula da kaunar da Yarima MalikusSaif kema Bahijjah..........



Yau ta kama asabar Sarauniya Zulaiƙa tana fa'da Magatakarda ke rubuta adadin abincin da zasuyi amfani dashi na wannan shekarar fa'da ta natsu anata budget, da an rubuta sai a mikama Malikussaif takaddun shi ke ajewa suna cikin haka saiga Sarkin fa'da ya shigo da wani bawa da ka ganshi kasan ba lafiya baki ɗaya hankalin su ya koma wajen su, kallan tuhuma Sarauniya Zulaiƙa tayima Sarkin fa'da daman gashi ya makara baizo da wuri ba, baki dayan su suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa, Sarkin zagi yace "Sarauniya ta amsa Sarkin fa'da meke tafe daku."? Cikin inƙina yara magana shi kanshi tsoro ya cika zuciyar shi, "Ranki shi dade wannan azzalumin bawa ne kuma maci amanar Masarautar Daborah nakama shi, tareda magotan mu, sunna maganar yanda za'ayi a halaka jama'ar mu, har wasiƙa naga zai basu aiko nai masu dirar mikiya nidasu kokowa Allah ya jefomani Barden Kudu ya taimaka mani na gurfanar dashi a gaban ki,Allah yakara girma."wani irin taƙaici ya kama Sarauniya Zulaiƙa kallan Magatakarda tayi ya ƙarɓi takardar ya karanta kamar haka


_Daga bawan ku Jamir zuwa ga Masarautar Waisu inasan in sanar daku cewa ku hanzarta zuwa Masarautar Daborah dan cimma su, sun sakankance yanzun kuke da damar da zaku shammace su bissalam...._

Duk wanda ke wajen nan saida yai mamaki banda Sarauniya Zulaiƙa tana zargin bayin basu da amana shiyasa bata ɗauke su a bakin komai ba tayi alkawali saita yi yaƙi da bayi kamar yanda kakanta Sarki Jawwar yayi tunda Masarautar Waisu ta taɓa mulkar Daborah bayin su suka gurɓace dan haka ta saka a ranta bayin su ba zasu taɓa samun yan'ci ba a kowane fanni, cikin gadara tace."ina Barden fa'da? Da Sarkin horo."? Mikewa sukayi tsaye suka"Ranki shidade gamu a gaban ki umurnin ki muke saurari." murmushi tayi wanda da tayi shi kwara ta zauna a yanda suka santa, dan sun san duk randa Sarauniya tayi murmushi to ranar zata yanke hukunci mai tsanani mai muni kuma, cewa tayi."Ku tafi da wannan maci amanan bawan kuje ku filleman kanshi sannan ku cake shi jikin mashi ku tada ɗan aike zuwa Masarautar Waisu ku haɗa masu da wasiƙa, muddin baku cika umurnina ba ni Sarauniya Zulaiƙa nayi alkawalin sai na fille kawunan ku da hannaye na tsani maci amana kowa ye sani." haka suka faɗi kasa jiki na kyarma suka cakumi Jamir sai ahi yake yana neman afuwa amman ko inda yake bata kalla ba ganin abanza yakeyi yafara kiran sunan Malikussaif rufe idan shi kawai yayi shima baiji dadin yanda aka yarda da Jamir ba amman yaci amana, rufe idan da MalikusSaif yayi Sarauniya Zulaiƙa ji tayi kamar ta datsa mashi mari acewar ta badan ita ta haifi MalikusSaif ba da saita koya mashi hankali saboda baida kishi har zaidinga jin tausan bayi kuma maciya amanar su, maganar Jamir ce ta katse mata tunanin ta"Kataimakeni MalikusSaif karka bari a kasheni dan Allah MalikusSaif na rokeka, dan adalcin ka Malik...... Uwar tsawa Sarauniya Zulaiƙa daka masu Barde danko Jamir baisan fitsari ya kubce mashi Magatakarda ya mikama Barde wasiƙa suka tafi dashi rai ɓace Sarauniya Zulaiƙa ta bar fa'da tareda dogarawan ta rai ɓace, koda Malik yaga ran mahaifiyar shi a ɓace bin bayan ta yayi ya isketa sai haki take bayi da hadiman ta, suka bar wajen takasa zama tayi nan tayi can a wani ɓangare na zuciyar ta tana jin haushin MalikusSaif, dafata yayi sannan yace. "Allah ya huci zuciyarki Sarauniyar Daborah kidaina damuwa akan wannan abun tun......ai Malik bai karasa ba ta daka mashi tsawa karo na farko da Sarauniya Zulaiƙa ta daka ma Malik tsawa shi kanshi ya tsorata da yanayin ta, ta nuna shi da hannu ta fara magana........



*Uhmmm! Komai Sarauniya Zulaiƙa zata cema MalikusSaif 🤔, Sai mu haɗa next page*


*Yar Mutan Kankia ce❣️*




Share
Comment
Vote

*BAYI MA YA'YYANE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
__________________

https://chat.whatsapp.com/H5RHfKhkR2eCXckRXP2SLr
_Ga link nan ku shiga domin samunshi daga farko kuma ku dunga samun update kan lokaci, dan banjin dadin yanda kuke tmbyata daga farko fa, pls ki shiga kuma kisan zakiyi comment 💞_


*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

*wannan page din naku ne BAYI MA YA'YYANE FAN'S 1,2,3,4,ku cigaba da bani ruwan comment dan haka yana man dadi sosai, son fissabillah💓*


Babi na biyar


"Karka kuskura kace zakayi man wata Magana Malik baka da anfani tunda baka kishin uwar ka ahaka zaka zama Sarkin wannan Masarautar ammn baka da kishi kai tausayi ko? Kai mai imani harkake tausan wance wulakantattan bawan Jamir duk wanda zai mutunta Jamir bayana yake ni Zulaiƙa kaf bayi na hatta uban bayi ban dauki yarda na bashi ba kamar Jamir! da ka rufe ido kana tausan sa kuka zakaima shi? Malik banda kaine mafi soyuwa a gareni ba da sai nasa kayi nadama, ka saurareni da kyau kaji me zance maka natsani bayi kuma ban kaunar su, sai na yaƙi duk wani bawa na munafuki na! kasa a ranka ran mahaifi na Abduljabbar fansa ne, Malik." ta ida maganar cikin tsawa dan MalikusSaif ya ɓata mata rai sosai, Sororo yayi idan shi sun kaɗa ya rasa yanda zaiyi ya fahimtar da mahaifiyar shi ba wai tausan su, ya rinjayi kishin Masarautar shi akan suba, baisan ya zaiyi ba yasan dai wake ɗaya shike ɓata miya amman har yanzun akwai masu gaskia a cikin bayin su, amman da sannu zai nunama mahaifiyar shi gaskia, zaunar da ita yayi sannan yace "Umma kiyi hakuri ba haka nike nufi kuma zan iya komai akan Masarauta ta, saidai Umma kisani bayin nan fa Ƴaƴane kuma ba kowannan su ke basu da amana ba, umm......"yiman shiru Malik zan saɓa maka ni zaka dinga cewa bayi ƴaƴane? ni a wajena kwara dabbobi dasu, sannan ni banga amana a wajen bayi ba, in takaice maka Malik dole kasama zuciyar ka tsanar bayi tun kan dare yai maka matukar ni Zulaiƙa na haifeka, ɓace man dagani shashasha me kalar halin uban sa." ta ida maganar tana nuna mashi kofar fita, Ya rasa yanda zaiyi da mahaifiyar shi, ya kagara mahaifin shi ya dawo ko ya huta da matsalar Umman shi, tafiya yayi rai ɓace duk baijin dadin yanda mahaifiyar shi ta ɗauki aƙidar kakan nin shi na wulakanta bayi yarasa ta inda zai bullowa wannan matsalar, ita kanta bayan Malik ya tafi wani irin tausayin ɗanta taji bata so ta ɗaga murya akan shi saidai dole ta faɗa mashi aƙidar Masarautar Daborah.



Bayan wata biyar

Please Login or Register in order to submit comment