Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mashi sake ƙutsa kai yayi cikin rundunar Jarumai sai sauke kan maza yakeyi baki daya mamakin Jaruman tar MalikusSaif ta addabi Sarki Baidulƙais turo wani mugun bawa yayi don ya sauke mashi kan MalikusSaif sai fafatawa da maza Malik yakeyi ko kadan baiga aibun wannan bawan ba, Zaidu ne yagan shi zai sokama Malik mashi a baya daga nesa ya halbo kibiya biyar suka kashe wannan babban bawan na Sarki Baidulƙais


Turniki yai turniki baka ganin kowa tsabar ƙura saida karar takubba da kakeji ankai minti talatin ahaka sannan kura ta ɗan lafa kaɗan kana hangen na kusa dakai ba lallai kagane na nesa dakai ba Saifulislam ne ya sare kan babban bafadan Sarkin Waisu Gabzur duk wani Jarumi dake Masarautar Waisu saida hankalin shi yai matukar tashi hakan yasa sukayi kan Saifulislam inda Malikussaif da Zaidu da sauran manyan Jaruman Daborah suka tare Saifulislam shima yaci gaba da gabzawa da magauta, shiko Sarkin yaƙi bairu koda yaga Jaruman Daborah sunja baya take ya naɗa commender a cikin kashi na biyu na Jaruman su da suka rabu gida hudu, yaba Yazid tuta, sannan da kanshi suka tunkaro inda Malikussaif yake koda Sarki Baidulƙais yaga sauran tawagar su Malikussaif, saida gaban shi ya faɗi duk a tunanin sa sunkare sai yaga harta linka ta farko yawa, afakawa sukayi ba abinda Sarkin Yaƙi yakeyi sai sauke kan maza kamar kiyashi duk wa'annan da karun da suka dirarma Saifulislam sun karar dasu kaf dan baka ganin uniform din Jaruman Masarautar Raifasu sai yan kaɗan hakan yasa suka gudu suka koma wajen layin da akaja wanda ya raba Masarautar su da tasu MalikusSaif da zasu bisu Malik ya hanasu duk jikin Malik ya ɓaci da jini tsabar fatali da kawunan mutane da yayi Sarki Baidulƙais ne ya anshi mayik yafara magana a fusace.



"Sarauniya Zulaiƙa tabbas kinzo da sihiri baiynanne keda tagawar ki har kuka ja da rundunar mutane na dan haka yanzun zan kara farmaku da ɗimbin mutanen da baku tanajesu ba wa'anda suka linka naki linkim ba ninki yau sai nasha ruwa da ƙoƙon kanki." cikin fushi ya ida maganar dan yayi mamaki sosai yanda aka kashe mashi jaruman Masarauta.



Itako Sarauniya Zulaiƙa cikin gadara da izzah ta kaɗai kai tareda shu'umin murmushin rainin wayo bata ce komai ba hakan ba karamin sosama Baidulƙais rai yaiba, fitowa Sarkin yaƙi yayi saiga wasu uwayen runduna sun bayya na suka shiga sahu iya ganin ka danko mutanen dake bayan su Malikussaif, basu wuce dari ukku suko sunkai dubu biyu tsabar yawa daga cikin rindunar Baidulƙais harda ɗanshi Yarima Haishir dan Sarkin Waisu sai Yarima Husbarul Baidulƙais duk sun shirya fuskar su a turnike danko Yarima Haishir jikin shi wani mugun mashi ne da yaji tsafi so ake ya soki. Malikussaif dashi, duk sune a cikin sahun gaba baki daya rundunar su, kallan kallo aka dinga yima juna cikin kankanin lokaci aka buga kuge aka sake haduwa sai barin ta kubba akeyi wajen ya yamutse Sarkin yaki da Saifulislam sai zubda kan maza sukayi shiko MalikusSaif kibiya yake ta halbawa yana kashe maza kamar kiyashi.


Tund Yarima Husbarul Ƙais ya shigo filin da'ga yake kashe Jaruman Masarautar Daborah kamar me, burin shi ya isa wajen MalikusSaif dan cika kudurin shi na ɗaukar fansar kakan sa akan MalikusSaif, shima Husbarul ƙais haka yaita kasar maza yaƙi ya dauki zafi wanda su Yarima Malik sun zubda maza sama da dari biyar kasa suma ankashe masu mutane sosai koda Yazid yaga mutanan su sun rage cikin kashi ukkun da suka boye ya tado tawaga ɗaya sukai ɗari biyar shiya jagorance su inda ya naɗa sabon commender ya barshi da sauran tawagar yaba Lurwan, haka suka taho gadan gadan saida su Husbarul Ƙais suka tsorata, tsakiya suka saka su sai kisar su sukeyi koda Hasburulƙais ya fahimci ankusan karar dasu da alama basu da nasara a cikin wannan yaƙin da gudu yahau doki ya fiddo wannan mashin da yake ɓoyo yayi kan MalikusSaif kowa yaki yai yaƙi ba wanda yagani shima MalikusSaif yayi nisa sai kisa yakeyi can Sarauniya Zulaiƙa ta hango Hasburul ƙais yayi kan ɗanta.



gadan gadan da mashi, da sauri Sarauniya Zulaiƙa ta zari takobi a kugun bafadan ta tashiga cikin filin yaƙi tafara kashe Jarumai shima Sarki Baidulƙais yana ganin tashiga ya shiga yaci gaba da kashe Jaruman ta, tafiya takeyi tana kisar maza burin ta ta isa wajen bawan nan dake neman rayuwar ɗanta, MalikusSaif najuyowa jin karar da Sarauniya Zulaiƙa tayi ganin za'a saukama yarima Malik mashi sai yaji an soka mashi, mashi a cikin ciki baki daya yafara ganin juwa koda Sarauniya Zulaiƙa taga ya caka mashi a ciki zaro kibiya tayi ta saita tsakiyar kan bawan nan ta ɗana mashi take ya mutu, Sarki Baidulƙais naganin ankashe mashi babban bawan shi gadan gadan yayi kan Sarauniya Zulaiƙa shiko Malik jini ne yafara ɗibar shi jinin har ya koma baƙi dan azaba amman a haka Malik ya daure yaci gaba da yaƙi danko Saifulislam yana ganin halin da ɗanshi yake ciki ya haukace takan mai uwa da wabi Yarima Haishir ne ya nufo Malik ganin karfin shi yafara karewa su Huzaifa da Sarkin yaƙi Baru suke tare mashi baya koda Hasburulƙais ya iso wajen Malik ɗaga katuwar takobin tsafi yayi zai sare kan Malik kamar mai jinni haka Malik ya buga uban tsalle ya kaɓe takobin Yarima Husbarul ƙais take ya sauke kanshi ƙasa ko shurawa baiba wata irin gigitattar tsawa Sarki Baidulƙais yayi saida kowa ya firgita tsabr ruɗewa da tsoro take ya sararma Sarauniya Zulaiƙa hannu aiko jini ya balle danma Allah yasa feɗarta yayi ita kuma ta soka mashi wuƙa a kafar shi ya faɗi kasa tasa takobi zata sare mashi kai ta kefata a ƙasa baki ɗaya yaƙi ya lafa ganin Sarkin su aƙasa ga gangar jikin Yarima Husbarul Ƙais ƙasa take yan Masarautar Raifasu da magoya bayan ta suka aje makaman su ƙasa sukayi surrender hatta Yarima Haishir yayi surrender yakara tsorata da lamarin Masarautar Daborah jikin tsawa mai ruɗarwa Sarauniya Zulaiƙa tace.




"Kai Baidulƙais nafaɗa maka sai nayi ajalin ka yanzun ya kagani mace mai kamar maza kallabi tsakanin rauwuna ya kagani yanzun ga kan ɗanka Husbarul Ƙais a kasa a wulakance ɗana ya kashe wawa ko kanada ja, gashi duk aran mayakan da kukayi Masarauta ta taci galaba akan ku, ko kana san in gwada maka yawan jarumai na gashi ka nuna ɗawaga da gadara duk mun karar daku." take Jaruman Daborah sukai ta fitowa kamar ba gobe dan yawa, sake a karaya sukayi.



Taci gaba da cewa. "Dan haka yau dinnan kun zama karkashin ikon Masarautar Daborah sai yanda naga dama daku duk da mulkin ku baida mu Sarauniya Zulaiƙa ba ko wata dukiyar ku, Baru sokoman kan Yarima Husbarul Ƙais ka kawo mani shi nan." cikin kankanin lokaci aka kawo kan Yarima Husbarul Ƙais a gaban Sarauniya Zulaiƙa tasa kafa ta murje kan ta zuba mashi yawo take Sarki Baidulƙais ya rufe idon sa gashi kasa wanwar mace na mashi barazana lallai ya tabbata ya gama jin kunya haka ta wurga mashi kan ɗanshi sannan ta riko hannun Yarima MalikusSaif wanda ya kusa fita hayyacin shi, ta ɗaga hannun shi sama tace. "Ina alfahari dakai Malikussaif ina takama a matsayin ka na ɗana kuma ɗan Jarumai dan haka ina yabama kaf Jarumai na da hazikin mijina Saifulislam dan haka a sa bayi su gyara mana Masarautar Raifasu dan mu huta sannan duk asa igiyoyi ya ɗaure bayin su harda Sarkin su sai abunda muka yanke zamu aiwatar akan ku, lusarin namijin sakarai ja jiki mata a gaban ka tuf." haka ta sake tofa ma Sarki Baidulƙais yawu a fuska tabi ta kanshi ta taka ta wuce duk aka kama mutanen shi harda Yariman Waisu aka kulle da Sarki Baidulƙais suko suka shiga cikin Masarautar shi suka yada zango take Sarauniya Zulaiƙa ta umurci bayin ta suka fara hada abinci harda uwar bayi da ƴarta Bahijja tazo da ita, danko Malik ana kawo shi wani ɗaki Sarkin yaƙi Baru yasa wuka ya farke rigar Malik jini ke zuba bakikƙirin koda aka kira wani malami yace guba ce aka saka a jikin mashin kuma zai iya mutuwa Sarauniya Zulaiƙa tasa aka kira mata Sarki Baidulƙais tasa mashi wuka a wuya ta fara tuhumar shi wayai masu tsafi ga mashin da aka soki Malik sai raba ido yakeyi itako Bahijja koda Binta da sauran bayin da aka zo dashi ta kawo ruwan zafin da za'a gogema Malik ciwo ai Bahijja na ganin shi cikin hali ta faɗa saman shi tana kiran "ya Malik karka mutu kabarni mai mutunci katashi." kowa ido yasa yana kallan Bahijja musamman Sarauniya Zulaiƙa da take maimaita kalmar Yaya a bakin ta, hannu Binta tasa ta ciro Bahijja a jikin Malik shiko yayi nisa, kauda kai Sarauniya Zulaiƙa tayi taima Binta nuni da hanyar fita taci gaba da magana.



"Ba zakayi magana ba ko kana bukatar iske danka wajen da ba'a dawowa."?
Cikin kyarma ya girgiza kai ya gama tsorata bazai so ya mutu ba kodan ɗaukar fansar ɗanshi mafi soyuwa a gare shi, sake daka mashi tsawa tayi tare da sara mashi wuka a hannu aiko jini ya ɓalle, ya rike wajen tana zaro idanu tace. "Zan iya kasheka akan Malik dan haka minti ukku ya rage maka da ka fanshi ranka, ko ni Zulaiƙa yanzun nan zan sauke kanka."


Shiko Saifulislam ya ruɗe ko magana yakasa ji yake inama ciwon Malik ya dawo kanshi dan har yafara fidda rai ga samuwar ɗanshi a ranshi, sake dakama Sarki Baidulƙais tsawa tayi har motsi wajen yakeyi ta ɗaga takobi zaka kashe shi yace.



"Tsaya tsaya Zulaiƙa zan fada maki komai ki barni inji da abunda ke damuna zan faɗa."


A ɗimauce ta sauke takobi saman cinyar shi sannan tace inajinka yakai Baidulƙais faɗa mani." jikin shi yai sanyi yace.......







*Yar Mutan Kankia ce❣️*




Share
Comment
Vote

*BAYI MA YA'YYANE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*


Babi na 12

*Sis jameey ki godema Allah, Allah yayi maki baiwar iya tsara labari ko wane irine walau na saurata zuwa na soyayya da kuma ban tausayi, wai dan Allah BAYI MA YA'YANE na yaƙi ne ko na soyayya dan na kasa gane na maiye dan yana son yafi IZZAH KO MULKI ma💃*


_Allaj sarki haka akeyi man wannan question din wai bayi ma ƴaƴane na yaƙi🤣, ae ba abunda bai kunsa ba ya ƙunshi yaƙi da zallar mulki da kuma soyayyar infact komai ma ya kushi fa, , sai dai ku sani nidai har yanzun nafi ganin dadin Izzah ko mulki ko kun mata da Sadaukin Burhaan shida zubainarshi da kuma Asma'u sannan ga Safiyya ina godiya sosai ina maki son fissabilillah 💓_



Banda raba ido ba'abinda Baidulƙais keyi ga zufa duk tagama wanke shi tsabar firgita da tsoro yace. "Tabbas mashin da aka tsoki Malikussaif ko shakka babu zai'iya rasa ranshi mashi ne na bakin karfen tsatsuba kuma bokan kuka shiyayi tsafin dan haka banda tabbacin ɗanki Malikussaif zai rayu yake Zulaiƙa wannan shine abinda nasani game da mashin da aka soki ɗanki Malik.!"

Cikin matsanan ciyar tsawa da Sarauniya Zulaiƙa tayi sai da wajen ya ruɗe hatta MalikusSaif da bai cikin hankalin shi saida ya bude ido sannan ya rufe tace. "Tabbas Baidulƙais yanzun wannan takobin zata sauke kanka in tumurmusa shi kasa injef gangar jikin ka dabbobi suyi fatali dashi umurni nike baka ya sunan bokan da yai wannan tsafin."? Ta ida maganar cikin tsawa da fushi, ganin yanda Sarauniya Zulaiƙa tai fushi yasa cikin tsoro Baidulƙais yace. "Bokan saman kukane dake dajin Gamki sunan shi boka Sarrilkus matsanancin tsababibin bokane dan haka bansan yanda za'ai yazo nan wajen ba abinda nasani kilan saidai ki same shi can." a fusace Zulaiƙa ta kwaɗawa Sarki Baidulƙais wata irin razanannar ƙara ya kwaɗa saida bayin shi da jaruman shi wa'anda aka kama amatsayin ganimar yaki suka tsorata cikin bada umurni tasa aka kawo mata yariman Waisu Haishir tace atafi dashi sai su Yazid da Sarkin yaki Baru akawo mata boka Sarrilkus gabanta dawakai suka hau suka tunkari bakin dajin gamki dake karkashin masarautar Raifasu banda kwankwamai da aljanu ba abinda ke ɗawainiya da dajin haka suka dinga tafiya mai nisan gaske sannan suka fara kutsa kai cikin wannan masifaffan dajin saida kowa ya tsorata daganin dajin gashi ranace amman kaman dare tsabar duhu dajin da kayan firgicin dake ɗawainiya da dajin.


wani uban ihu mai razanarwa ake kwaɗawa a cikin dajin, haka sukaci gaba da tafiya a tsorace kowa najin mugun tsoro a cikin zuciyar shi sai kutsa kai sukayi har suka shiga tsakiyar dajin wulgin wani bakin abu suka kagani ya sake firgita su sai kyarma sukeyi can kuma suka karajin angibtasu ga wata irin bakar guguwa data tunkaro su ko gabansu basu hange dukawa sukayi kasa suna buɗe idon su bayan ta lafa suka gansu wajen wani katon jan dutse da wata irin katuwar kuka sai wani bakin abu a gaban su shiba mutun ba kuma ba aljani dan fitsitsi bakin shi duk jini kuma yanada bindi, cikin kaɗuwa suka sadda kansu ƙasa bayan minti biyar suka tsinkayi wata irin kara mai gigirwa da tarwatsin wuta ta dunkule sai juyi takeyi takai minti biyar saiga wani wargajejen mutun bakin kirin ya bayyana da ido ɗaya tare da wasu kattin mutane marassa kyau sai surutai sukeyi take yarima Haishir ya zube kasa suko sukayi tsaye sai mamaki sukeyi ji sukayi an taɗesu basuga kowa ba suka faɗi kasa wata magana sukaji mai razanarwa ance. "Ku yan matasa harkun isa kuzo wajen bokan saman kuka kuki dukawa yanzun zamusa aljani ɗan tsitu yasha jinin ku tunda baku da biyayya hahhhhhha."sai waige waige sukeyi basu ga mai magana ba, can sukaji wata uwar kara ta tunkaro su a tsorace suka fara addua can boka Sarrilkus ya ɗaga hannu wannan guguwar ta dakata, cikin dakakkiyar murya mesa dajin girgiza yace. "Shine jankunne agareku karku kuma zuwa wajen na ba ɗa'a sannan ku koma kucema Sarauniya Zulaiƙa ba'aima Sarrilkus wargi inhar tanason ɗanta Malik ya rayu sai dai akawo a cikin Masarauta ta sannan sai yayi sati a cikin bakin dajin Gamki, inba hakaba daman aljani Darus gaf yake da fara zuƙar jinin Malik danma shidin Jarumi da take ya mutu dan haka kuɓaceman dagani tunkan dare yai maku sannan karwanda ya fita a cikin dajin nan ta gaba sai ta baya badan ku yan aike bane lallai dana kashe ku, ku zaman tarihi Hhhhhhhhhahhh."take ya bace sai wannan wuta dake juyi ga kura kowa ya kasa motsi cikin firgita suka fara tafiyar baya baya sai ganin abubuwan tsoro sukayi har da zakuna kamar zasu cinye su, sai su rufe ido sai addua sukeyi can wata guguwa tazo ta shuresu sai suk gansu wajen wani katon icce suka tafiya mai nisa sannan sukaga dawakan su, sai kyarma sukeyi suka hau bamai magana suka kama hanyar Masarautar Raifasu.


*Niko nace muna daga gefe nida my fidos yar'mama da Autar safana gami da My Dejja, muna kallon yanda Momyn sultan take gudu tana sakin abun a wando saboda ita ba jaruma bace🌚 👹*

*dan ko Nennerh da Ummun Nana sai Asma'u magari da phatermarh kankia boye wa sukayi bayana😎*

Tafiya sukayi mai nisan zango sannan suka isa cikin Masarautar Raifasu, har cikin fa'da suka shiga suka iske Sarauniya Zulaiƙa tana ganin su ta mike ta taresu tareda jefa masu tambayoyi. "Baru ya andace kuwa ya nike ganin ku, a sanyaye."!? Ta ida maganar cikin tsoro dan duk hankalin ta baya jikinta karfin hali kawai take.



Dukawa sukayi suka gaida Sarauniya Zulaiƙa sannan Sarkin Yaki yace. "Ranki shidade tabbas mungaza wajen tahowa da wannan hatsabibin bokan ko magana bata haɗamu ba yace bazai zoba saidai akai mashi Malik acan dutsen kuka." yana gama magana ya dukar da kanshi kasa, cikin gadara Sarauniya Zulaiƙa ta iso wajen Baru tana zagaye shi tace. "Meyasa baku kawo mani kanshi ba."?



Shiru sukayi duk sun kasa magana tsawar data daka masu yasa Yazid yin magana. "Allah yataimakeki girma da izzar Sarrilkus ya girmi tunaninmu......wani irin gigitaccen mari ta ɗauke Yazid dashi duk wanda ke wajen nan saida ya girgiza cikin fushi tace. "Badan kana jarumi naba abin tunkaho dana sauke kanka kasa, Sarrilkus din banza da wofi ni Zulaiƙa sainayi maganin shi muddin ɗana Malik ya mutu tabbas saina kashe Baidulƙais sannan insare kan yarima Haishir inga duk duniya wanda ya isa yayi jayayya da Zulaiƙa." tarin da Malik keyi kamar zai sheƙe yasa Sarauniya Zulaiƙa ta isa wajen shi da sauri ta rungumo shi jikin ta tana kiran sunan shi. "Malik mene haka dan Allah kayi hakuri zaka samu lfy insha Allah bazaka mutu ba." cikin shaƙewar murya yace. "Umma kitaimaka ki yafeman cikina keman ciwo bazan tashi ba dan Allah,Umma ina Bahijja dan Allah kitaimaka kirike Bahijja a matsayin ƴarki, inna mutu Abba kayafeman dan Allah."


Rike shi sukayi suna hawaye Sarauniya Zulaiƙa ta tace. "kadaina fadan haka Malik zaka warke." bakaramin tashin hankali Sarauniya Zulaiƙa tashiga ba, fita tayi taje wajen bayin Masarautar Raifasu tasa akaita dukan su sannan aka samu katon dutse aka ɗaura saman kirjin Sarki Baidulƙais shiko yarima Haishir takobi tasa ta daɓa mashi sannan ta samu takarda ta rubuta wasika taba Lurwan yakai Masarautar Waisu.....


Tana dawowa tasa Sarkin Yaki Baru suka ɗauki Malik suka shiga dashi wajen wani ɗaki sannan aka kira wani malami yafara ba Malikussaif magani da addu'oi yayi mashi sannan yasha kullin haka wannan malamin keba Malik rubutu yana sha jikin shi ke fidda hayaki danko yana jin jiki sosai, a wajen Lurwan kuwa yana isa Masarautar Waisu akaima mashi iso wajen Sarkin su, yana zuwa fa'da yakai gaisuwa kallan tuhuma Sarki yai mashi sannan yakai gaisuwa yace. "Inagaisuwa ga Sarki mai dole ni ɗan aikene daga Masarautar Raifasu ta hanyar Sarauniya Zulaiƙa, wani mugun faɗuwar gaba ta riski Sarkin dan yasan wasa ya kubcema maza dagaji ba sa'a a cikin lamarin Sarki Baidulƙais gashi ya bada aron Jaruman shi harda ɗanshi mafi soyuwa a gareshi da kanshi ya mashi wasikar ya karanta.




```Nasan ko bance komai ba tabbas sakona yasa ka girgiza yau ina taron Jaruman ka dakake tunkaho dashi ina ɗanka mafi soyuwa a gareka shin ko kasan da jinin waye nayi maka wannan wasikar ba nakowa bane sai jinin ɗanka Haishir dan haka kayi gaggawar zuwa ka ceci danka ina nan Masarautar Raifasu ta zama kalkashin ikona harda aminin naka wawa da Sarauniya Zulaiƙa kake magana ina sauraran ka nan da awa huɗu."```



Yana gama karatun ya saki takarda yana keto zufa a zahiri ɗagama Lurwan hannu yayi alamin yatafi yana fita ya tashi yafara bala'i. "Ni za'a cima mutunci ɗana za'a wulakanta a rubutoman wasika da jinin ɗana lallai Zulaiƙa wuyanki ya isa yanka, ko kunsan Zulaiƙa tayi nasara a Masarautar Raifasu tabbas dole mutashi tsaye nafahimci tana son tayi abinda kakarta Sarauniya Yahanasu taimana dole mudakile wannan yarinyar da rundunar mu, kuma dole in halaka MalikusSaif da hannuna dan haka yau zanje Raifasu zanmika wuya insamu in amso ɗana tunkan inrashi inyaso daga baya zan masu dirar mikiya in wargaza duk wata zuria da shiri na Sarauniya Zulaiƙa da hannuna zan kacakaca da Zulaiƙa saidai a halin yanzun tashiga gaban mu, naso in halaka ɗan aikenta nabarshi ne sabida jinin ɗana Haishir ina kira ga Sarkin Yaki kashirya anjima zamutafi wajen Sarauniya Zulaiƙa."


*wata sabuwa kuma fa, gadai MalikusSaif can rai hannu ga Allah, ya yarima Haishir shima babu tabbas😂dan Sarauniya Zulaiƙa naga bata da niyar kyaleshi, ga boka Sarrilkus yana jiran a kawo mashi MalikusSaif a faɗarshi ko kuma aljani ya ida shaye jininshi 😭, Abunda dai sai addu'a fa😎*



*ina godiya da comment dinku gami da shirhinku musamman ma BAYI MA YA'YANE COMMENT GROUP, ku sani comment dinku kawai ya isheni balle ma na sauran💞💓*


*Yar Mutan Kankia❣️*






Share
Comment
Vote

*BAYI MA YA'YYANE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*




Babi na 13




Sarauniya Zulaiƙa keta yawo tarasa abinda ke mata ɗadi a duniya har yanzun jikin Malik hayaki yakeyi ga wani irin zafi da yayi kamar wuta, fita Sarauniya Zulaiƙa ce tafita itada Saifulislam sukaje wajen Sarki Baidulƙais, iske shi sukayi zaune shida jamaar shi a wulakance kamar wani bawa Sarauniya Zulaiƙa ce ta tsugunno a gaban Baidulƙais tace. "Kashirya kare rayuwar ka.? Koko kana san kabi ɗanka cikin gaggawa."


Wani kallo yaima Zulaiƙa yace. "Tabbas bakiyi karya ba tun yaushe Baidulƙais ya sallama rayuwa kwara in mutu zaifi kinga muddin kika kasheni tabbas ɗanki shima zai mutu cikin wahala da bala'i ya kikagani ya Zulaiƙa ko nawa salan ya birgeki dan haka ni ban shakkar mutuwa." ya ida maganar yana mata kallon zaki gane kuranki gami da Murmushin mugunta.


Cikin tsawa Zulaiƙa ta ɗaga takobi zata sare kanshi Saifulislam ya rike hannun ta, dukawa yayi yace. "Baidulƙais miyasa kake faɗar haka tabbas dole bazaka ji tsoron kisa ba saidai kasani bazaka so ka cigaba da mulkin Raifasu inko har hakane ni Saifulislam naimaka alkawalin cigaba da mulkin Masarautar ka amman da sharadi sai in zaka sa Boka Sarrilkus zuwa wajen mu dan karya wannan bakin tsafin, dan haka ban bukatar kace komai kayi tunani zuwa gobe ina sauraranka." yana idawa yakama hannun Zulaiƙa da tagaji da hasala suka tafi wata uwar dariya ya saki bayan tafiyar su sannan yace. "anzo wajen."

_Inkon Allah kunji abinda Sarki Baidulƙais yace ko minene burin shi kudai kubiyoni muji yanda zata kaya a cikin wannan ƙayataccen labarin na bayima ƴaƴane_

Bawan shi Jazbir yace. "Ranka shidade yakake gani zamuyi da wannan azzalumar Sarauniyar dan ɗaukar fansar ɗanka? kuma magajin gobe yanzun haka zamu zauna a cikin Masarautar mu muzama bayi marassa ƴanci? amman gaskia Gurfanai baikyau ta mana ba a wannan zubda kima da daraja ne na Masarautar Raifasu ace mace ta maidamu bayi ya kamata musan abinyi Gurfanai yabaka nasara."

Nazari Baidulƙais yayi duk da yanajin maganar Jazbir har cikin zuciyar shi saidai a wajen shi yana takaicin yanda har musulmai zasuci galaba akan su, lallai kam sun gaza wajen Gurfanai tabbas sunji kunya."

Kamar yanda kuka sani Masarautar Raifasu masarauta ce data shahara wajen gabatar da sarauta sai dai Masarautar ba a daular musulunci suke ba suna bautar wani katon icce dake cikin Masarautar baki ɗayan su, shiyasa suke rayuwa yanda suka ga dama, sannan ba abinda suka tsana irin addinin musulunci wannan dalilin yasa suka ɗauki tsana da karan batta akan Masarautar Daborah tunda suka anshi musulunci musamman Saifulislam da Malikussaif acewar su ta hanyar mahaifin shi har daular musulunci takafu a babbar Masarautar su ta nahiyar su ta kasar Gambia, wannan kenan.

Sai dai Masarautar tanada mayaƙa duk da sunsamu naƙasu akan artabar da sukayi da Sarki Jabbar na III wannan dalilin yasa suka kara tuso Masarautar Daborah a gaba suna san suga bayanta musamman yarima MalikusSaif.


```wannan kaɗan daga cikin tarihin Masarautar Raifasu da kudurin su ga Masarautar Daborah kuma ga yarima MalikusSaif ya kashe yarima Husbarulƙais ɗan Sarkin Baidulƙais bari muga kalar cakwakiyar da zata wakana a tsakankanin waɗan nan Masarautu da suka tuso Masarautar Daborah a gaba muje zuwa```

Sarki Baidulƙais yace. "Tabbas Jazbir kafaɗi gaskia dole muɗauki mataki ga wannan jakar Zulaiƙar saina maida Zulaiƙa ta zama baiwata kuma saita zama abin tausayi yanzun abinda baku sani ba dole sai Zulaiƙa tazo tanemi inmata hanyar da boka Sarrilkus zaizo gareta kodan rayuwar ɗanta nan ne wasan zaifara dan haka karka damu dani take zancen itafa macace dole inmaida hankalin ta kamar na kifi ko kaza na rantse da girman Gurfanai saina halaka Zulaiƙa da hannuna tabbas ku rubuta ku'aje da Baidulƙais take magana." ya ida maganar yana wata irin dariya da mugunta da ƙeta.



A ɓangaren Zulaiƙa kuwa fitowa tayi tahau saman doki ta warci takobi ita da Saifulislam gudu kawai suke shekawa kamar ba gobe fita sukayi cikin Masarautar Raifasu suka tunkari bakin dajin Gamki suna shiga cikin kurgunmin dajin ba abinda suke gani sai tsabagen duhu ga wata

Please Login or Register in order to submit comment