Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

RAHIM*


Babi na 8/9



Yarima MalikusSaif ne zaune a falon sashen shi yana nazarin sakon yaƙin da aka aiko masu, yayi nisa a cikin tunani, har Sarkin yaƙi Baru yasa kai mashi iso zuwa wajen Yarima MalikusSaif, tunda baiwar shi mai kula da masu shiga da ficen sashen ta fara magana, MalikusSaif baisan tana yiba saboda yayi nisa saida tayi ma MalikusSaif magana takai ukku, sannan ya dawo a cikin tunanin shi kallan ta yayi da alamar ko lfy sake dukawa tayi sosai kanta ƙasa sannan tace. "Ranka shidade Sarkin yaƙi Baru ne yace in mashi iso zaigana dakai." sake kallan ta yayi ko magana baiba yai mata alamar da ya shigo.



Koda Sarkin yaƙi Baru ya shigo gaishe da Yarima MalikusSaif yayi yaimashi nuni da wajen zama bayan ɗan shiru da ya biyo baya sannan Sarki Yaƙi yace. "Allah ya taimaki shugaba, nazone akan maganar wannan yakin da za'ayi ya kamata a shirya dabaru na yaƙi gudun samun matsala sannan jarumai nacan filin barr suna ansar gwajin da ya dace kai kawai muke sauraro, Allah yakara girma da ɗaukaka."cewar Baru wanda ya karashe maganar kanshi a ƙasa.



Numfasawa Yarima MalikusSaif yayi sannan yace. "Hakane Baru tabbas abinda nike ciki kenan, ina ta tunanin yanda zamu ɓullowa wannan lamarin saidai ku me kuka shirya."? Cikin jin dadi Sarkin yaƙi yace.



"Allah ya taimaki adalim Yarima Sarkin Jarumai na Daborah Allah yakara maka lfy, tabbas mun kasa Jaruman mu gida hudu zamu tafi da kashi biyu a cikin filin daga suma zasu rabu kashi hudu su tsare kowa ce kofa ta gabas da yamma, zamu fara fafatawa da abokan gaba, yanda yaƙi yayi shikenan in sunga muke da nasara basai sun shigo cikin filin yaki ba sauran kashi biyun, in kuma sunga muna neman karaya, za'a turo mamu kashi ɗaya su shigo cikin mu, saidai kowa ce kungiya za'a naɗa mata shugaba saidai kaine shugaban kowa ce ƙungiya, a shawarce bazamu bari Yariman Masarautar Daborah yafara hayema abokan gaba ba, saidai ka kasance a cikin kashi na karshe in an kusa gama yaƙi kaji abinda muka shirya ko hakan yayi."?




Nazari Yarima Malik yayi sannan yace. "Eh hakan yayi saidai ni bazan lamince ba ace ina cikin sahun karshe ni zan ja goranci kashin farko da na biyu a matsayina Yarima Malikussaif wanda sunana ya kareɗe kasar nan ace na kansace a cikin sahu ƙarshe ai nasaba tace zata faɗi kabari in tunkari abokan gabar da suka daɗe suna farautar Malikussaif wannan shine ƙimata da martaba ta koda za'a kasheni a cikin filin daga."



Sarkin yaƙi Baru zaiyi magana kenan Yarima MalikusSaif ya ɗaga mashi hannu alamar ya isa, sannan yace. "Kitashi mutafi filin gwaji musan abinda ya kama ta ayi, shine abinda ya dace." haka suka kama hanya suka tafi duk inda zasu wuce sai an duƙa angaishe su haka suka tafi har cikin filin Barr wanda Jarumai keta faman gwada Jarumtar shi.
*(a can na hango Bayi ma yaƴane comments group suma suna ta ansar gwajin wajen Momyn Sultan da My Dejja gami da Autar Safana, Suna ta kokari su ga sun iya komai kafin ranar yaƙi tazo😝🥺🌚)*


Sarkin shela yafara sanar da isowar Yarima MalikusSaif baki ɗayan su suka dakata daga gwajin da sukeyi, magana Yarima MalikusSaif yafara cewa. "Yanda nasame ku, kuna wannan gwajin ya burgeni dan haka inasan ku rabu kashi biyar. Cikin kankanin lokaci suka rabu nan Yarima MalikusSaif yaja kashi daya hakama Sarkin yaƙi Baru shima ya ɗauki ɗaya cikin kankanin lokaci suka fara artaba da Yarima Malik kowa yan kokarin nuna jaruntar shi akan ɗan uwan shi, wani irin shura Yarima MalikusSaif yaima Sarkin yaƙin yaji shi akasa Yarima Malik yasa mashi takobi a wuya cikin kankanin lokaci suka ɗauki ihun murna Yarima MalikusSaif yayi wining din Sarkin yaƙi duk abin nan Sarauniya Zulaiƙa na kallan su sai jindadi takeyi tana mamakin kalar jarumtar ɗan nata haka suka dinga gwaji har marece kowa ya tafi cikin nishaɗi suka cigaba da shirin tafiya yaƙi.....



Da marece Sarauniya Zulaiƙa na zaune ita da yan fa'dar ta a cikin sashen shi suna shawara akan yanda zasu ɓulowa lamarin yaƙin da zasu tafi, kowa na bada shawara akan yaƙin Sarkin yaƙi ya mikama Malikussaif katuwar taswirar katon filin Barri wanda ya kunshi duwatsu da manyan tsauni sai rairariya suka fara nuna ma Sarauniya Zulaiƙa yanda za'a raba mayakan su yarima MalikusSaif ne yace. "Allah yataimaki Sarauniyar Daborah wannan bakin layin da kika gani a kanshi mutanan mu zasu tsaya sai wancan dutsen na Faisi nan ne kashi biyu na jama'ar mu zasu ɓuyo wasu daga ciki zasu fito ta gabas, sai ni zanja waɗan nan rindunar zan tunkari Yarima Ƙaru na Masatautar Raifasu da tawagar shi inda Sarkin Yaƙi zai kula da sauran tawagar ya kukaga wannan shirin."? cikin jindadi Sarauniya Zulaiƙa ta rike hannun ɗan nata tana shafa gashin kanshi sai jindadi kowa keyi haka suka gama tsare tsaren su kuma kowa ta aminta da shawarar da Yarima MalikusSaif ya bada a matsayin shi na shugaban jarumai na Masarautar Daborah.



Saidai ance banan gizo ke sakaba a cikin waɗan nan Jaruman nasu akwai wani azzalumin mutun wanda yake kai sirrikan Masarautar Daborah wajen abokan gabar su, saida aka gama komai dashi sannan ya saci hanya ya tafi Masarautar Raifasu dan ya gaya masu halin da Masarautar Daborah take ciki haka ya kama hanya saman doki saida yayi tafiya mai nisan gaske sannan ya isa da yake sun san shi bude mashi gate din Masarautar akayi akai mashi iso wajen Sarki Baidulƙais lokacin suna tare da Jaruman Masarautar ta Raifasu suna ta shawarwari saiga Jairulfaz ya shigi zubewa yayi a gaban Sarki Baidulƙais kowa saida yaji dadin ganin shi dan sunsan akwai labari a wajen shi, Yariman Masarautar Husbarul Baidulƙais ya fara tambayar Jairulfaz halin da Masarautar Daborah ke ciki haka ya kwashe daga farko har karshe ya faɗa masu cikin jin dadi Sarki Baidulƙais ya mika mashi kuɗade masu yawan gaske, sannan ya kama gaban shi take suka canza shiri sai jindadi sukeyi inda suka aikama Sarkin Ƙaisu abinda ke faruwa da masarautar Waisu kowa ya shirya haka sukai ta mugun shiri ga Masarautar Daborah sun saka a zuciyar su sai sun dirkake Masarautar sannan sun kafa sabuwar Masarauta da kansu....



Bayan sati ɗaya yau aka tashi da murna a cikin Masarautar Daborah, marar misaltuwa musamman a wajen Sarauniya Zulaiƙa da Malikussaif, wasu mutane ne masu yawan gaske suke shigowa a cikin Masarautar Daborah,fadawa ne suka taro wane babban mutun mai arziki da ka ganshi kasan dattijo ne mai shekaru sannan yanada kamala Sarkin zagi da yan fa'da ne suka taro shi suna kiran. "Barka da zuwa ranka shidade sannu da dawowa Masarautar Daborah angaishe da Saifulislam miji ga Sarauniya Zulaiƙa angaishe da mahaifi ga Malikussaif Masarautar Daborah da mutanen cikin ta nai maka barka dawowa wannan Masarauta." haka ya mika masu hannu sukayi musabaha sai murna yan Masarautar keyi musamman bayi da talakawa kowa so yake ya gaisa da Safulislam haka suka iso gar wani katafaren sashe na Sarauniya Zulaiƙa, dai dai nan Malikussaif yafito saijin dadi yakeyi yana murna haka ma mahaifin shi yana jin dadin ganin tilon ɗan nashi rungume juna sukayi haka itama Sarauniya Zulaiƙa ta fito cikin shigar alfarma ta Sarakai ta tari mijin nata sai jindaɗi takeyi baki ɗaya su suka ɗunguma zasu tafi sashen shi, bayi ne keta zuwa suna gaida shi har ƙasa hakama Abdulmajid yazo da bayi suka kawo gaisuwa sai ɗaga masu hannu yakeyi har ya shiga cikin sashen shi tareda mutanen shi, wani irin katafaren falo ne da yagaji da kayan alatu, bayin dake ciki sun gyara ko ina, suma gaishe shi sukayi sannan suka bar wajen suma sauran yan fa'da suka gaishe da Saifulislam, suka tafi cikin jindadi.....



Riko hannun MalikusSaif yayi yana kallan ɗan shi, gani yayi yakara mashi girma sosai cikin farin ciki Safulislam yace. "Sarauniya ta ya naga Malik ya zama babba masha Allah, wace irin kulawa ake ba ɗan nawa."? Murmushi Sarauniya Zulaiƙa tayi tace ma mijin nata. "Allah yataima Kangiwa ai Malik bani ba duk wanda ke cikin wannan Masarautar yana ba Yarima Malik kulawa ta musamman." cikin sakin fuska Safulislam yace. "Malik ɗana me kake buƙata."? Kwantowa yayi aka faɗar mahaifin nashi yana kara jin son shi da kaunar shi a zuciyar shi, yace. "Abba ina kewar ka Abba bansan kasake yimin nisa Abba." cikin kulawa ya kalli ɗanshi yace. "Malik duk wannan fataucin da kaga inayi saboda kaine ɗana ba abinda bazan yiba saboda kai, kullin fatana kazama cikin farin ciki a koda yaushe kuma naji daɗi yanda na iske ka baka cikin damuwa, dan haka dole inma mahaifiyar ka gaggarumar kyauta nasan daga gare tane."



Cikeda farin ciki Sarauniya Zulaiƙa tace. "Haba mijina dan nakula da Malik har saikaimin kyauta."? Kallonta yayi sannan yace. "Kwarai kuwa Sarauniya ta, kin cancanta fatana kici gaba da faranta ma Malik duk abinda yake so ai mashi shikenan angama wanke mani zuciya ta." Malik ne yace. "Abba ai duk abinda nike so anai mani kuma ina samun kulawa ta musamman , numfasawa." Sarauniya Zulaiƙa tayi sannan tace. "Ya kamata abar wannan fira kaci abinci ka huta kaga ka kwaso gajiya."


Fuska sake yayi murmushi inda ta fara zuba ma mijin nata abinci da kanta cikin kankanin lokaci hadimai suka kaima mutanen sa abinci a wajen masaukin baki, shiko Saifulislam da kanshi ya dinga ba Malik abinci sai jindadi yakeyi itako Sarauniya Zulaiƙa sai sababi takeyi wai sun haɗe mata kai har suka kammala cin abincin su cikin so da kauna, sallamar uwar bayi ce Binta ta katse masu firar su, dukawa tayi kanta ƙasa tace. "Allah yataimaki Kangiwa barka da hanya sannu da dawowa gida lfy." cikin jin dadi ya amsa. Sake dukawa Binta tayi tace. "Ranki shidade Allah yataimaki Sarauniyar Daborah barka da hutawa, Yarima Malik barka da marece fatan kuna cikin aminci." amsata Malik yayi sai murmushi yakeyi musamman da yaga Bahijja a gefen Binta itako Sarauniya Zulaiƙa ko kallan inda su Binta suke batayi ba, maganar da Saifulislam yayi shiyasa ta kalle su.



"Binta ina kika samu ƙankanuwar yarinya har haka."? Kallan kallo aka fara yima juna tsakanin Binta da Sarauniya Zulaiƙa inda Malikussaif ya kafe Bahijja da ido, itako Binta jikinta sai ɓari yakeyi tana shakkar amsar da zata ba Saifulislam, sake cewa yayi. "Gaskia yarinyar nan ta burgeni matuka dagani zatayi fikira mene sunan ta? kuma ina kisamu karamar yarinya Binta."? Kallan banza Sarauniya Zulaiƙa tayi mata almar kin san sauran itako Binta ganin kallan da Saifulislam yaima ta alamar ke nike sauraro yasa ta sadda kanta ƙasa tace......




*Yar Mutan Kankia ce❣️*




Share
Comment
Vote

*BAYI MA YA'YYANE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________


*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



Babi na goma


*wannan page din naki ne FILLO YAR'MAMA, kiyi yanda yanda kike so dashi🤗*


"Allah yakarama ɗaukaka ranka shidade wannan yarinyar ƴata ce wadda na haifa sunan ta Bahijja." mamaki bayya ne a fuskar Saifulislam yace. "Ƴarki ashe da rabon Abdulmajid yaga zuri'ar sa Allah ya rayata."



"Ameen Ranka shidade bari mu koma bakin aiki marece nayi, Bahijja mutafi ko."? Shiko Malik sai jindadi yakeyi yaga Bahijja baisan abinda yasa ba yake jin ta tamkar wata ƴar uwar shi ta jini, shiko Saifulislam cema Sarauniya Zulaiƙa yayi. "Kinga Binta gaskia yarta ta birgeni gata ubaiwa ya kamata ace mun riketa dan ta samu inga tacciyar rayuwa umai kyau." wani kallo taima mijin nata sannan tace. "Haba Abban Malik yina mu ina riƙon baiwa karfa ka manta ita baiwar muce." girgiza kai yayi, dan baiyi mamakin jin haka daga matar tashi ba yace "Haba Fulani minene dan mun riƙeta karfa kimanta suma bayi ƴaƴane kamar kowa wai ke sai yaushe zaki daina tsanar bayi da zuri'ar Abdulmajid ki ɗabe aƙidar iyaye da kakan ni tunda basu sukaci amanar ku ba, ya kamata bayi su zama ƴantattun ƴaƴa a cikin wannan Masarautar Daborah haba banjin dadin haka kefa mace ce kuma ansan ku da tausayi."


Cikeda mamaki Sarauniya Zulaiƙa tace. "Haba Saifulislam akan bayi zaka dinga tada jijiyar wuya ba ruwana da wani bayi ƴaƴa ne dan haka ba amana ko dangantaka tsakanina da bayi ko wani abu da ake kira rangwa me."


"Haka kike ce? Toh nidai a matsayina na mijinki na faɗamaki gaskia yanda kikaga ya dace haka zakici gaba da gudanar da mulki a cikin Daborah sai dai ki sani yanzun mun samu ilimin addini dai dai gwargwado ba kamar da ba da kakannin mu suka dinga mulkin zalinci ba kama hannun yaro ya kamata ace tunda Masarautar nan tamu mun karɓi addini munsan shari'a dai dai gwargwado muyi koyi da gaskia kibar aƙidar iyaye tabbas kinada iko akan kowa ne bawa a karkashin ikon ki yake sai dai kisani bai kamata a dinga wulakanta suba anacin zarafin su, dan haka ni zan shiga daga ciki in huta kiyi nazari Ummu Malik." yana gama faɗa ya shiga bedroom din shi, sai furzar da iska mai zafi takeyi shikan shi Malik baisan yaga ana cutar da bayi ko kadan amman ba yanda zaiyi yasan laifin wani baya shafar wani kuma sun hukunta wannan Jafar din ya dace komai ya wuce, gani yayi mahaifiyar shi tafita a fusace, duk inda zata wuce bayi ne keta darewa a tsorace har tashiga sashen ta, shima nashi ɓangaren ya tafi jiki sanyaye......



Sarauniya Zulaiƙa ta kwalawa Jakadiyya kira a ɗimauce ta shigo ɗakin Sarauniya Zulaiƙa tana kwance saman gado da kaganta zakasan tana cikin ɓacin rai, sawa tayi akira mata Binta, cikin rawar jiki ta tafi tasa aka kira Binta, tana cikin shara wata baiwa tazo ta gaya mata sakon Sarauniya Zulaiƙa saida taji mummunar faduwar gaba, duk jikin ta yai sanyi, cema Bahijja tayi tazauna wajen su Mairo haka ta tafi cikin sashen Sarauniya, koda ta shiga falo Jakadiyya ta iske kallan da taimata kaɗai yasa uwar bayi sake karaya, tare sukaje Jakadiyya ta shiga ta sanar da Sarauniya Zulaiƙa isowar Binta lokacin mai kula da shirin ta na tayata shiryawa saƙa mata sarkar wuya tayi sannan ta ɗaura bakar alqabba ta fito cikin izzah da gadara koda ta fito Binta naganin fitowar Sarauniya Zulaiƙa zubewa tayi ƙasa tana kwasar gaisuwa, amman saboda rashin daraja ta mutu haka Sarauniya Zulaiƙa ta taka Binta da ƙafa ta wuce ta kanta bayi da Jakadiyya suka take mata baya har ta zauna saman wata irin kujera ta alfarma, bayan Binta kamar ya buɗe haka ta iso wajen Sarauniya Zulaiƙa ta duƙa kiran ta tayi da yatsa ta kara matsawa kusa da Sarauniya Zulaiƙa ta ɗaura kafar ta akan kafaɗar Binta duk bayin nan kansu ƙasa suna karajin tausan Binta duk da suma ba wani ƴanci ke gare suba, hadima keta mata fiffita wasu na mata tausa sannan kafar ta a saman Binta sai fidda iska takeyi tana nuna izzah da gadara cikin isa ta fara magana. "Ke Binta." Jikin Binta na ɓari ta amsa. "Allah yataimaki uwar dakina Sarauniya mai adalci tuba nike Binta ta amsa na'am. "



Cikin gadara tace. "Waya baki damar kawo gaisuwa wajen Saifulislam bana hana ki kusanto zuri'ata ba da wannan wulakantatrar baiwar ba."? Tunda Binta taji abinda Sarauniya Zulaiƙa take kiran Bahijja bakaramin ɗaci maganar tai mata ba sai dai tasan basu da wani zaɓi ko yan'ci tunda suka zo a bayi marassa galihu take takara jin tausan ƴartata, tace. "Tuba nike ranki shidade rigima ce kawai ta yaro amman bazan kuma yawo da Bahijja kimin aikin gafara muntuba."



cikin kaskanci Sarauniya Zulaiƙa tasa aka kira mata Sarkin bulala yaima Binta bulala talatin ana cikin dukan ta Yarima MalikusSaif ya shigo wajen mahaifiyar tashi sai dai bai jidadin abunda akaima Binta saida aka gama dukanta sannan ya karaso ya gaida ya zauna tareda gaida mahaifiyar tashi, sauran bayin wajen ne suka gaida shi, itama Binta dake goge kwalla gaida shi tayi, amsawa yayi cike da tausayama ta, magana Sarauniya Zulaiƙa tayi bayan ta kori dukkan bayin dake wajen banda Binta tace mata.



"Daga yau kada insake ganin kin kusanto wannan jakar ƴarta ki, a wajena ko mijina uwa uba ɗana Yarima Malik in kunne yaji."? Baiwar Allah Binta cikin sauri tace. "Allah ya huci zuciyarki bazan kuma ba ko cikin gidan nan bazata kuma zuwa ba, zata tsaya a turakar bayi da sauran dangin ta muntuba Allah yakara girma." Cikin kosawa Sarauniya Zulaiƙa tace. "Ɓaceman da gani kuma kije kuci gaba da aikin da kuka saba sauran inga wani bai abinda aka saka shi ina fatan kin gane."? Saurin ɗaga kanta tayi ta amsa da "eh." nan Binta ta koma wajen su Mairo suna ganin ta sukasan ba lfy, amman ba damar da zatayi masu wani bayani saboda aikin da sukeyi ba dare ba rana, tana iso Sarkin horo ya lafta mata bulala taci gaba da aiki sai dukan su akeyi kamar wasu jakuna hatta Bahijja itama aikin take duk da bazata wuce shekara biyar ba a duniya wannan kenan......




A Masarautar Waisu kuwa ba abinda sukeyi sai shirin yaki dan kullin training suke ma Jaruman su shiyasa ma suka kaima sauran Masarautu tayin hadin guiwa da Masarautar Raifasu da Masarautar Ƙaisar Yarima Haishir shine yake jagorantar Masarautar Waisu kullin burin shi taya zai yaki Yarima MalikusSaif wani masassaƙi yasa aka kira mashi yasa ya ƙera mashi mashi mai kaifin gaske haka yasa boka yayi mashi mugun sihiri aka zuba guba a jikin mashin boka Sarrilkus yace muddin Yarima Haishir ya soki Malikussaif da wannan mashin tabbas bashi ba kwana duniya, ba karamin dadi yakama Yarima Haishir sai kara shiri yakeyi yau ya kama sauran kwana biyu ayi yaƙi........



Ana gobe za'a hadu filin daga, a wajen Binta zaune take Mairo nagasa mata jikin ta dake zubda jini inda Bahijja ke kwalla duk da Bahijja bata da wani wayon kirki amman harta fara gane in mahaifiyar ta tana cikin damuwa, tunda Binta ta fahimci yarta tafara hankali tana shiga damuwa intaga bata walwala ta fara ɓoye damuwar ta, Abdulmajid ne ya shigo gidan yanda yaga matar shi cikin damuwa yasan abinda ke faruwa saidai yasan basu da rabon sa'a a rayuwar su haka zasu ƙarata a matsayin bayi marassa ƴanci ko galihu a cikin Masarautar Daborah share kwallan idon shi yayi yazo yaba matar shi hakuri, jikin shi na kyarma ya tafi wajen Sarkin dawakai yasan muddin ya isa sai an mashi bulala talatin da safe hakama da yamma inzai dawo gida sai amma shi wata talatin ɗin harma ya saba da wannan wahalar da yake kwasa, shafa kan Bahijja yayi yace.


"Ƴata kiɗauki kaddara da juriya tabbas kinzo a matsayin baiwa marar ƴanci, gashi kinfito a Masarautar da ba'a san darajar ɗan Adam balle bawa wanda ke kuma kin zama ƙasƙantatta sai dai ki sani Bahijja insha Allahu zaki zama mai gata wadda duk duniya za'a yi mamakin baiwa ta zama mai daraja Allah yaimaki albarka ƴata." murmushi tayi ma mahaifin nata tace. "Ameen Baba saika dawo kayoman tsaraba." tunda Bahijja tafaɗi kalmar tsaraba saida hankalin Abdulmajid yai matukar tashi karfin hali kawai yayi ya fita, shidai yasan yana iya yini baici komai ba saboda wajen aikin shi ko abinci ba'a basu, sai in Binta tayi aiki take kullo mashi sauran girkin da aka rage a leda wani bima ƴarsu zasu ba su kwana da ƴunwa ta ina zaiga tsaraba!? Itama Binta tashi tayi zata tafi wajen aikin ta tahaɗama Sarauniya Zulaiƙa karin kumallo, tana tashi Bahijja tafara kuka saitabi mahaifiyar ta, da kyal ta lallashe ta takaita wajen wata baiwa marar lfy wadda ta rasa idon ta sakama kon duka da akayi mata wai ankama ta zata zubama Yarima Malik guba a cikin abinci haka Sarauniya Zulaiƙa tasa akai mata lahani tanaji tana gani akai mata ƙage, wajen Goggo Ma'u takai Bahijja itama dattijuwar baiwa ce tana da zuri'a samari da yan mata duk bayi dan dai mijin ta ya rasu, da safiya tayi zasu tafi wajen aikin wahala, ɗaya daga cikin su wanda ake kira da Adam shike kula da Malikussaif yana sashen shi, koda Binta taje wajen Ma'u gaisawa sukayi sannan ta kora mata bayani ta yarda nan Bahijja ta zauna tana gani mahaifiyar ta tafi kuma bazata dawo ba sai dare, gashi bata barma mata ko kwayar zarra ba da sunan abinci haka ta tafi da tausan ƴarta a cikin zuciyar ta.....




Washe gari da safe shiri aketa yi za'a tafi wajen yaƙi tunda Saifulislam ya dawo aka shaida mashi da sakon da magauta suka aiko yace shima zaije a fafata dashi ba yanda Sarauniya Zulaiƙa batai ba yace sai yaje haka suka shirya kowa yasa kayan jarumai hakama Malik sannan ya ɗaura da kayan Sarakai itama Sarauniya Zulaiƙa ta shirya zatayi rakiya har cikin filin Barri, Sarkin yaki da Waziri Dammur da sauran Jarumai kowa yahau dawakai, Malikussaif da sauran jarumai suka kama hanyar tafiya wajen da za'ayi yakin, itama Zulaiƙa da mijin ta sai wazirin ta da sauran bayin da za'a tafi dasu suka shiga ayari akai ta tafiya mai tsayin gaske har suka isa makeken fili mai ban tsoro Jarumai ne iya ganin ka na Masarautar Raifasu sunja sahu sahu sai commender din su a tsakiyar su, suma su Yarima Malik sahu suka ja suna facing abokan gabar su, saidai kamar yanda suka tsara kashi ɗaya ne suka shigo cikin filin Barri, Sarkin Masarautar Raifasu da Sarauniya Zulaiƙa suke ma juna kallan kallo Sarki Baidulƙais cikin hassala yace.





*Yar Mutan Kankia ce❣️*




Share
Comment
Vote


*BAYI MA YA'YYANE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________


*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



Babi na goma sha ɗaya





"Ke Zulaiƙa kisaka aranki yaune ranar karshen ki a duniya keda tawagar ki sannan sai na fille kan ɗanki Malik na sokeshi a jikin takobi na cinye antarsa ɗanya a gaban ki sannan kema in fille kanki abin wulakantar wa ingaje mulkin Masatautar Daborah in mai bayin ki bayi ne daga karshe in malleke duk wata dukiya da kuke tunkaho da ita kuma takobin Bairu zata zama a kalkashin ikona ni Sarki Baidulƙais bin Zadair hhhhh matsiya ta maza a gabanki ya Zulaiƙa."



Murmushi Sarauniya Zulaiƙa tayi ko ajikin ta duk da taga yawan mayaƙan da Sarki Baidulƙais ya tara dan yawa sai dai basu firgita Sarauniya Zulaiƙa ba ko kaɗan, Sarkin shela ne buga kugen yaƙi cikin kankanin lokaci Jaruman Masarautar Raifasu suka tunkaro su Malikussaif, saman dawakai suka taho da gudun gaske, koda MalikusSaif yaga sun tunkaro su hannun shi ya juya koda Jaruman Daborah sukaga abinda Malik yaima su take masu takubba suka koma baya masu kibiyoyi suka dawo farko saida MalikusSaif yaga sunyi rabi ya bada order aka fara yimasu ruwan kibiyoyi sai bazar da Jaruman Raifasu sukeyi, haka sukaita yimasu ruwan kibau kamar ba gobe, danko Malikussaif da yaja kibiya sai sama da talatin tafita haka sukaita kisan su kamar wasu kiyashi koda MalikusSaif yaga sun kusa isowa wajen su take ya sake juya hannun shi masu takubba suka dawo farko masu kibaua suka koma baya kowa ya tsaya cikin shiri cikin kankanin lokaci Jaruman suka hade karab jikake anata kabtama juna takubba dan ko MalikusSaif tsakiyar fili ya shiga shida Saifulislam suka dinga filli kawunan maza suma wa'ancan haka suka dinga kashe Jaruman Masarautar Daborah danko Malikussaif wani irin sabon karfi yake ji wani uban tsalle ya doka ya sauk kan wani mugun bawa na Masarautar Raifasu danko Sarki Baidulƙais jiyake kamar yai hauka tsabar bakin ciki burin shi yaga kan MalikusSaif a ƙasa yaki yai yaƙi baka ganin komai kasa sai jini ga kawunan mutane birgir kamar ruwa, saida su Yarima MalikusSaif suka kusa karar da tagwar Sarki Baidulƙais sannan sukaga an turo masu wasu rundunar bakaramin tashi hankalin Sarauniya Zulaiƙa yayi ba ganin Jaruman Masarautar Waisu ne, a cikin ranta ko tana mamakin yanda akai masu zanba cikin aminci saboda basu san akwai wasu Jarumai na bayan na Masatautar Raifasu yaki yakara turnike wa danko Malikussaif wani sabon karfi yaji ya taso

Please Login or Register in order to submit comment