Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutanan bayin nan ne na Masarautar Daborah musamman kamar yana bibiyar Bahijja ne dan naga yana shawagi tsakanin gidan Saude da masaukin bayin Daborah." wani irin ɓacin raine ya turnike Sarki Baidulƙais dayaji zancen Uwani kallan Bahijja yayi wanda tai saurin sunkuyar dakanta ƙasa wani irin tsoron Baidulƙais ke kara shigar Bahijja sawa yayi aka kamo Bahijja duk ta ruɗe aka gurfanar da ita a gaban shi duk yanda Bahijja taga Ashir hakan baisa ta nuna shiba duk da taga ananeman yimata ƙage akan abun bata da wata masaniya akan shi, sai raba ido takeyi kamar marar gaskia wani mugun kallo Baidulƙais ya jefama Bahijja sannan yace..


"Mike tsananin ki da wannan bawan."? Baki daya can cikin Bahijja sun game bakinta duk ya bushe dan tsoro a ruɗe tace. "Ranka shidade Bahijja batasan wannan mutumin dake magana akaiba asalima bantaɓa ganin shiba, sai a wajen ka daya kawo maka kayan marmari na rantse bansan waye shiba.!"ta ida maganar zuciyar ta na bugawa da sauri dan tasan yanda Baidulƙais kejin haushin ta zai iya yimata lahani akan wannan maganar da ake kokarin dangantata da ita, jitayi yace. "Ni zakima karya ko Bahijja bayan cin mutuncin addinina dakikeyi yanzun kuma ke zaki ha'ince kikawo wani mutun ko, mikike nufi nagane dan ki gudu ko."? A razane Bahijja takalle shi take hawaye masu zafi sukai nasarar wanke mata fuska, shiko Baidulƙais suna haɗa ido da Bahijja yaga ta aka mashi dara daran idanuwan ta sai yaji taimashi kwarjini kuma baiji zai iya cigaba da hukuntata a wannan lokacin, ji yayi tace. "Wa'iya zubillahi kaicona da cin amana taya zan gudu bayan a halin yanzun ko hanyar garinmu bansani ba asalima na manta sunan garin mu..... Baijira cewarta ba yace. "Yimin shiru minene wai'ya mi ko sunan bawan kike so kifaɗa, Sarkin horo, ka kaimin ita gidan kaso saidai bance kadake taba a jeta zuwa nan da ɗan kankanin lokaci tukun." ba Bahijja hatta su Ashir bakaramin tsoro yakama shib ganin za'a kai Bahijja gidan kaso, da yaya niyar fitowa gani yayi kwara yakaima Malik abinda ke faruwa ya ɗauke ta baki ɗaya Masarautar zaifi, danko bayin Daborah har sunfara kuka sunsan Bahijja batada masaniya akan Ashir haka aka kama Bahijja tana kuka eu Zainab da Indo na kuka danko Saude har kanta ke mata ciwo, shi kanshi Baidulƙais din yanajin abun har ranshi dan duk kanshi ya kulle ya rasa mike faruwa haka a baibai, nan aka sallami sauran bayi, yace bayin Daborah su tsaya yasa Sarkin bulala ya dinga dukan su kamar jakai ba'a kyale suba sai dare sannan akace gobe ma da karfe bakwai su gurfana a wannan filin dan cigaba da karbar horo mai tsanani dan basu rasa sanin Ashir, shi kanshi Ashir yasha kuka dan tausan ƴan uwan nashi musamman Bahijja haka ya dawo tsakar dare wajen su Tasi'u yafara basu hakuri....




"Tasi'u kuyi hakuri akan abinda ya faru tabbas nasan zan sakaku cikin tashin hankali musamman Bahijja naso inbayyana kaina abinda yasa ban bayyana kaina ba, nayi tunanin halin da zamu dawwama a ciki nida Bahijja dan haka zantafi domin sanar ma Yarima MalikusSaif abinda ke faruwa da Bahijja." murmushin karfin hali Tasi'u yayi yace. "Haba Ashir kakosan hadarin dake cikin wannan Masarautar miyasa baka gudu ba gudun kada a kamaka, sakon Yarima Malik yafi tsayawar d zakayi domin bamu hakuri har yanzun kasani munakan yima Yarima Malik hidima saboda a dalilin shi harmuka kasance a cikin wannan Masarautar dan haka kaje kafaɗa mashi halin da Bahijja ke ciki dan tafimu bukatar taimako." wani irin tausayi suka bashi, ganin basu damu da duk wani azaba da zasu fuskantaba indai akan Yarima Malik, cikin kulawa yace. "Shikenan yan uwana zan tafi saidai kusani muna taredaku kuyafeman." rungume juna sukayi kowa na hawaye su sunaji kamar su bisu dan duk sub rabu da iyayen su wasu kuma matan su da abokan su, da haka Ashir yai bankwana dasu cikin daren nan yabi ta wata hanya yafita cikin Masarautar Raifasu ga dare yayi tsakiya duk tsoro ya kamashi haka ya isa wani ɗan kauye ya kwana daman ana ya aje dokin shi ya hau yakama hanyar komawa Masarautar Daborah da abubuwa iri iri a zuciyar shi ya saka wannan ya kwance wannan aranshi.....


Itako Bahijja koda aka rufeta a cikin gidan kaso, ba abinda da takeyi sai ka mai tsuma zuciya tarasa wacce irin kaddara ke bibiyar ta na rabuwa da iyayen ta ko kuwa na kwana cikin ƙangin bauta da azaba tana cikin wannan tunani taji an cakwumota da karfi wata katuwar matace tagani ta zare mata idanu tace. ''Ke wacece da zakizo nan gidan kinaima mutane kuka kinsan baki iya kalar wannan rayuwar kika yarda kikazo nan, uban wayasa kikayi laifin da aka kawo ki nan wajen."? Wani irin tsoro ne yakara kama Bahijja cikin disasshar muryarta tace. "Kiyihakuri nayi shiru dan Allah kada ki cutar dani." wani irin kallo taimata tace. "Mikikace."? Rufe baki Bahijja tayi tace. "Kimin aikin rai.... Bata jira cewar Bahijja ba tasa kafa ta halbata sannan tafara dukan Bahijja jin ihun da Bahijja ta saki yasa Sarki gidan yari ya rugo da gudu ya iske wannan matar sai dukan Bahijja takeyi kukan kura yayi ya anshe Bahijja ya datsa mata mari yace. "Bakida hankali kokin san wacece ita Sarki Baidulƙais yace kada asake a daketa shine ke fitsararra zaki duketa, zatayi magana yafara lallasa ta saida ta duku kamar ganga sannan ya sauyama Bahijja waje sai kuka takeyi a haka baccin wahala ya kwashe Bahijja ga wani irin sanyi da zazzaɓi duk ya addabeta.



Itako Jakadiya tana komawa gidan ta sai uban kuka takeyi sai addu'a takema Bahijja fatan ta tafita cikin wannan ukubar da take ciki tarasa dalilin dayasa kowa ya tsani Bahijja musamman gimbiya Yazira dda Uwani uwar bayi ta tabba ba yanda za'ayi Bahijja ta aibata abin bautar su, ita takara yarda da ubangijin Bahijja shine na gaskia ba abinda suke bautamawa ba icce marar anfani ranar haka Jakadiya ta kwana da tausayin Bahijja a cikin zuciyar ta.......



Danko Sarki Baidulƙais bai runtsaba tunanin wannan bawan yake aranshi yana jefama kanshi tambayoyi miya kawo shi miyazo yi sannan miyake bukata sannan miyahaɗa shi da Bahijja ina yasan Bahijja kodai Sarauniya Zulaiƙa ce ta aikoshi dan tafiya da bayinta inhar hakane tun yaushe yake cikin wannan Masarautar tawa lallai dole in hukun ta Sarkin kofa taya zaibar kowa na shigowa a cikin Masarautar shi kamar marar tunani, yana cikin tunani zuciyar shi ta raya mashi anya ba Sarki Lahazu ya aiko shi ba dan ya ɗauki Bahijja tabbas hakane ba ko tantama aiko yacika munafuki wato dan ɗanshi nason Bahijja shine zai bullo ta wannan hanyar lallai sai ya raina mashi hankali kenen shi zaima zamba cikin aminci kenan ranar dai haka Sarki Baidulƙais ya kwana ya saka wannan ya kwance wannan ya rasa matsaya wata zuciyar nacemashi Sarauniya Zulaiƙa ce wata nace mashi Sarki Lahazu ne, daga karshe yace bari a cigaba da bayin Daborah horo har sai sun faɗi abinda suka sane game da wannan bawa Tarib da haka ya kwanta kamar mai bacci



Koda gari ya waye haka gimbiya Yazira takira Uwani tana zuwa ta duka ta gaida gimbiya, sannan ta kalleta tace. "Uwani ya aka kwana akan wannan tsinanniyar yarinyar nan."? "Gurfanai yakara girma ai tana gidan kaso da kanshi Sarkin da take takama dashi yasa aka garƙameta tana can da mugun halinta, dandai abin haushi yace kada a sake a daketa a cigaba da tsarera kadai." shu'umin murmushi yayi yace. " kibarsu Uwani yanzun zan aikeki wajen Sarkin horo kikai mashi wannan sakon." takarda ce taba Uwani ta amsa sannan ta koma cikin daki sai jin dadi takeyi


Kamar yanda aka umurci su Tasi'u haka suka gurfana a cikin filin nan kamar wasu dabbobi Sarkin bulala ne ya fito da tafkekiyar bulalar shi yacigaba da dukan ta kamar zai kashe su haka yaita dukan su yana tambayar su waye wannan bawan da yazo wajen su, duka kamar zasu mutu, ana cikin dukan su saiga Sarki Baidulƙais yazo da sauri hadimai suka aje mashi kujerar zama ya zauna a gaban shi aka cigaba da dukan su ana tambayar su kowa cewa yayi bai sanshi haka ya sake kiran dogarawa sukaci gaba da dukan su tun suna magana har sun fara sikewa ganin zasu mutu wani bawa yace yanada magana, wani irin tsoro da razana suka kama Tasi'u Sarki Baidulƙais ne yace yanajin su cewa yayi. "Ranka shidade tabbas naga wannan bawan saidai bamusan wajen wa yazo ba yazo wajen mu muntaimaka mashi da ruwa yasha wannan shine abinda muka sani ya kalli wani daga cikin su yace. "Ko Lawi."? Shima gyaɗa kai yayi alamar eh wani mugun murmushi Baidulƙais yayi yace. "Kuci gaba da dukan su har safe in sukaki fadar gaskia akashe mani su basu da wani anfani a wajena ko kadan." da haka Baidulƙais yakama hanya ya tafi haka suka koma sashen Sarki Baidulƙais shida Jakadiya



Suna isa ya zauna itakuma Jakadiya ta zauna kasa cikin girmamawa tace. "Ranka shidade niko inasan inbaka wata shawara akan Bahijja."cikin kulawa yace. "Inajinki Jamra minene shawarar taki."? "Yawwa ranka shidade inaganin Bahijja batada masaniya akan wannan bawa Tarib da ake magana akai, sannan sai inga waannan bayi da ake hukuntawa da wahala idan su suka kawo wannan bawan a wannan Masarautar gani nike kawai akwai abinda yazoyi a wannan Masarautar." shiru yayi sannan yace. "Tabbas Jamra zan iya yarda ba ruwan Bahijja kan wannan alamari amman ban aminta da waɗan nan bayin ba da kike magana." "hakane ranka shidade saidai mizai hana bazaka fiddo Bahijja ba tunda kaima kanai kata kyakkyawan tazo."shiru yayi na ƴan dakikai sannan yace. "Bazan fiddotaba Jamra sai bukatar hakan ta taso wannan dalilin yasa nace kada wanda ya duketa."
"Amman ranka shidade....daga mata hannu yayi yaɗa mata yace. "Jamra ma fahimci kina shiga sabgar Bahijja ko miyasa."? "Ranka shidade kasancewar mai karanci shekaru a cikin bayi sannan kuma tanada amana da sanin yakama ta." "ko Jamra ashe kema kinsan halayen Bahijja kenan Zanduba amman ba yanzun ba, sannan karkiyi kokonto tabbas zaki yarda da abinda ake zargin waɗan nan bayin na Daborah kinsan basu da amana ko kadan daga su har Sarauniyar su da wannan wawan Yariman nasu wannan dalilin yasa ban rangwanta masu."



Shiko Ashir yana isa cikin Masarautar Daborah yasamu ya aje dokin shi ya shige turakar bayi bashi ya fitoba saida marece liqis sannan ya fito sallar magrib yayi daga masallaci bai zarce ko inaba sai sashen Yarima Malik iske shi tareda Huzaifa sai Yazid dukawa yayi yakai gaisuwa cikin kulawa ya amsa hakan yasa ya tashi yafara ƴan gyare gyare Huzaifa ne yace. "Ashir kwana biyu na rabu da ganin ka." cikin girmamawa yace. "Banjin dadi ne shiyasa sai yau nadawo bakin aiki." sannu sukayi mashi shidai Malik baice komai ba, basu jimaba sukayi mashi sallama suka tafi, tashi yayi yai wanka ya sake shiryawa sannan yakira Aliya yace. "Tashigo mashi da Ashir, bada jimawaba suka shigo sannan ta fita, kallan shi yayi yace. "Shine kafita daga infito wanka." sunkuyar da kanshi yayi sannan yace. "Allah yataimaki uban gidana ai wannan girman kane dan ka kimtsa shiyasa." murmushi yayi kai karamashi kyau da haiba sannan yace. "Sannun ka da hanya Ashir, bani labari." jiki sanyaye Ashir yace......




_Ƴar Mutan Kankia ❣️_



Share
Comment
And
Vote

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________

*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*


Babi na 33&34


"Ranka shidade kamar yanda kaganni a gaban ka haka naga Bahijja gurfane agaban Sarki Baidulƙais tanai mashi hidima saidai....ɗaga mashi hannu yayi yace. "Kagama kawomani sako mai dadin sauraro Ashir amman inafatan ba wanda yaganka koda kuwa bayin Daborah ne."?


Numfasawa Ashir yayi sannan ya sadda kanshi ƙasa yace. "Ranka shidade ba takaran bayi ba hatta Bahijja taganni ita da uban gidan ta saidai bata ganeni ba kasancewar batai wayon sani ba." cikin rarrabewar kalma Yarima Malik yace. " ban...bane...ta...gan...kaba, kamar yaaa." ya ida maganar yana jan kalma, shi kanshi Ashir yanda yaji Malik yaima shi tambayar saida yaji cikin shi ya juya daurewa yayi yace. "Eh ranka shidade ta ganni." murtuke fuska Malik yayi sannan yace. "Inajinka." "Sarkin bayin Masarautar ne ya aikeni kaima Sarki Baidulƙais kayan marmari nan Bahijja taganni." "bance karka bari aganka ba."?


A daburce yace. "Ranka shidade naso inga Bahijja ne sai na haɗu dashi shine ya aikeni." ɗan karamin tsaki Yarima Malik yaja sannan yace. "Banyi zatan zaka samu matsala akan abinda na umurceka ba, wannan dalilin yasa a cikin amintattun bayina na turaka ko kanada labarin Sarki Baidulƙais zai iya gane kaidin bakon fuska ne a cikin bayin sa koda kuwa sunkai dubu a lokacin."?


Mamaki ne yakama Ashir a ranshi ko cewa yayi lallai kam kamar yasan abinda yafaru kenan nabani yazanyi yanzun cewa yayi. "Eh hakan tafaru ranka shidade." da sauri Malik ya mike tsaye ya goya hannayen shi a bayan shi ya kalli Ashir da wani mugun kallo yace. "Miyafaru."? "Tabbas ankama bayin Masarautar mu ana tuhuman su akan sun sanni duk da naba Sarki Baidulƙais sunana a matsayin Tarib karshe wata uwar bayi cewa tayi ni bakone ga Bahijja taganni ta wajen masaukin bayin wannan Masarautar hakan yasa..."yimin shiru Ashir yimin shiru mizaka kuma ceman ko so kake kunnuwana sucigaba da sauraran banzan zancen ka so kake kacemani ankama Bahijja an bigeta bugun daya wuce misali tunda kagama ɓata komai ko kuwa cewa zakayi baki ɗaya bayin aka kama akaita bugu kamar za'a kashe su."? faɗaman mikake son kafaɗaman dakai nike.!" baki ɗaya jikin Ashir yagama mutuwa shikan shi yasan duk hakurin MalikusSaif dole ya fusata a kiɗime Ashir yace. "Tuba nike ranka shidade tabbas duk abinda ka faɗa haka take anacan ana tuhumar bayin Masarautar mu sannan itama Bahijja ankamata ankaita gidan kaso......bai bari kalaman Ashir sun dai daita ba Yarima Malik ya ɗauke Ashir da wani fitinannan mari saida ya faɗi cikin ɓacin rai ya nuna Ashir da yatsa yace. "Ashe kai wawane bansani ba kaico inama bakai na aika ba yanzun na sakamaka da sharri kagama shan wahalar yimin aiki yanzun gashi na saka maka dda mari, kai kuma kajefa mutane a ukuba ka saka Bahijja cikin bala'i ko kasan irin azabar da kabar Bahijja a ciki kuwa? Miyasa baka baiyana kanka ba."?


Tuni zufa tagama wanke Ashir kamar wanda yayi dambe da zaki danjin marin Malik yakeyi har cikin kwanyar kanshi baki ɗaya ji yayi ganin shi ya dusashe na ƴan dakikai sannan yace. "Kaimin afuwa ranka shidade tabbas nayi babbn kuskure saidai naso inmika kaina a lokacin da aka danganta Bahijja dani, abinda nayi tunani karkajini shiru shiyasa na fasa mika kaina duk da Bahijja taganni hakan baisa ta nunaniba lallai Bahijja ta cika mutun mai yawan halacci duk da batasan waye niba amman hakan baisa ta tunaman asiri ba balle aci zarafi, gaskia ne nagaza nagaza da nakasa bayyana kaina dan fansar Bahijja saidai duk nayi wannan abun dankai uban gidana."


"Aikin banza aikin wofi kayi a banza kwara ka fidda Bahijja cikin ukuba zaifimin dadi akaina ko kasan jin shurin ka shi zai tabbatar min da cewa ba lfy kai kuma daka fidda Bahijja cikin wannan mayuyacin halin amman yanzun naji Bahijja tana cikin Masarautar Raifasu amman tana cikin kalubale da tashin hankali, har yaushe kake tunanin yau ko gobe zanje ɗauko Bahijja bakasan sai nai dubarar barin Masarautar Daborah ba batareda kowa ya saniba, saidaina halin yanzun ka kasheman wannan tsarin nawa dole inje neman Bahijja kota wane hali koda hakan yana nufin ɓacin ran Sarauniya bazan iya bari inaji inagani rayuwar Bahijja ta halaka a sanadiya taba, kabani kunya Ashir kabani mamaki Ashir nayi danasanin aiken wlh blh Ashir badan kana bawana na amana ba da nabada misali akanka don ya zama izina ga sauran bayi da akanka Yarima MalikusSaif zai fara hukunci mai tsanani a cikin bayin Daborah saidai kaci arzikin aikin dakai mani baka cancanci haka, ammn ka buɗe kunnan ka kajini da kyau daga yau kar insake ganin kafar ka a cikin turaka ta koda wasa."

Da sauri Ashir yarike kafafun Yarima Malik yafara bashi hakuri yana kuka da hawayen shi kamar wani karamin yaro, saidai wannan lokacin tsananin tausayin Bahijja sun gama gauraye illahirin ɓargo da jijiyoyin jikin Yarima Malik baiganin kowa kojin komai sai tsananin son ganin Bahijja a tareda iyayen ta danjin shi yakeyi zai iya jayayya da mahaifiyar shi akan ceto rayuwar Bahijja, tureshi Malik yayi yace. "Ɓacemani dagani Ashir kada in illataka a banza da wofi tunkan sauran darajar ka ta zube a idanuna." duk da haka Ashir baikasa a guiwa ba ya sake rike kafar Malik yace. "Kayi hakuri ya shugabana dakayi fushi dani gwara kasa aita dukana koda kuwa za'aimani illah dan fushin ka yafi gwarwa shin wuta zafi a cikin zuciya ta na rokeka kaimin lamani in kai kaina a wajen Sarki Baidulƙais don fansar Bahijja, koda na rasa raina tabbas zanyi alfahari dan na cika umurnin uban gidana sannan ba isar mashi da sakon shi kuma Bahijja zata zama fansassa a wajena da sauran ƴan uwana bayi da suke a kalkashin ikon Sarki Baidulƙais na rokeka Yarima magajin gobe ka dubi shekarun da ba ɗebe ina tareda kai karka juyaman baya ka yafemani.!" duk da maganganun Ashir sun daki zuciyar Malik saidai baiji a lokacin zai iya yafema Ashir duk da ya girme shi amman baiji zai ɗaga mashi a wannan yanayin da yakeji ya tsani komai kuma bai shi'awar komai a dake yace. "Tashi katafi turakar bayi idan na yanke shawara zan nemeka, sannan bance ka kuma cewa komai ba." duk da Ashir bai yarda da abinda Malik yace mashi ba saidai baida zaɓi da ya wuce yabi umurnin uban gidan nashi sallama yai mashi ya tafi yana share kwalla duk ya shiga damuwa mai tarin yawa, Shiko MalikusSaif jiyayi wani kululu ya tsaya mashi a wuya ya rasa yanda zaiyi dashi ba shiri ya kwanta jin juwa na neman kada shi sai juyi yakeyi ga wata uwar yunwa da yakeji lokaci guda ya nemeta ya rasa hakan yasa ya mike kanshi na sarawa ya fita ba inda ya wuce sai gidan waziri nan ya haɗu da gimbiya Zahara'u gaishe shi tayi ko kallo bata ishe shiba balle tasa ran amsawa shigewa yayi a falo ya iske Huzaifa yagama cin abinci yanayin da yaga Malik kaɗai ya tabbatar mashi daba lafiya da sauri ya kama hannun MalikusSaif suka shige cikin ɗakin Huzaifa suka zauna gefen gado cikin kulawa yace "Yarima lafiya miyafaru faɗamani damuwar ka dan Allah." tashi Malik yayi sai dukan hannu shi yakeyi da tafin hannun shi yakasa cewa komai yaje ya dawi yaje ya dawo shima Huzaifa sake mikewa yayi jiki a mace yasake jefoma Yarima Malik tambayoyi iri iri, shi kanshi ya kosa yaji damuwar abokin nashi.

A wajen Bahijja kuwa zaune take duk ta takure ga wani uban cizan sauro duk yafasa mata jiki abinga ga fara duk jini ya kwanta kullin bata abinyi sai kuka da addu'a duk da ba'a bugun ta amman gidan yarin Masarautar Raifasu ya ta'azzara duk da kusan iri ɗaya ne dana Masarautar Daborah, gidan yarine katoton gaske sannan kuma ginin kasane a gidan kasa akayi shi da dama idan aka kai mutun cikin shi ana iya mantawa da rayuwar shi baki ɗaya duk da baikai gidan yarin Masarautar Daborah girma ba, tana cikin tunanin duniya taji ankira sunan ta dagowa tayi Sarkin horo ne tagani ya kirata bayan budemata kofa da yayi daga rufewar da akai mata a wani karamin daki, tana fitowa baijira cewar taba taji ta wanke ta da mari har ukku da sauri ta rike kunci hancin ta ya fara zubda jini tayi mamaki sosai duk da tasan Sarki Baidulƙais yace kar asake a duketa, jitayi yace. "Ke yar iska ko kina shiga dokokin gimbiya Yazira ko, barganin Mai Martaba yace kada a dukeki akan gimbiya Yazira zan iya halakaki sakarai dan haka yau kinma kanki baki ba abinci sai gobe mayya kin wani tsareni da dankwala dankwalan idanun ki." haka Bahijja ta goge kwalla sannan tace. "Kaji tsoron Allah minai maka miya haɗani da gimbiya Yazira sannan dame kakeso inji da wannan kaddarar ko kuwa ta ƙazafi akan lamarin gimbiya Yazira zanji." cikin fushi ya sake wanketa da mari yace. "Wato ke bazakibarwbazakibar wannan addinin naki ba ko? Shine har anan ma zakimana shi da rashin kunya ko? Cikin gadara Bahijja tace. "Koda zaku kashe ni bazan bar addinina ba, dan na fidda rai da rayuwa dan haka ba tsoron mutuwa ko azaba zanjiba."


Ɗauko bulala yayi yafara wankar Bahijja saidai tasama ranta bazatayi kuka ba, haka yaimata bulala talatin sannan ya wurgata a mazaunin ta ya rufeta, ya tafi hawaye ne masu ɗumi suka wankema Bahijja fuska, ta kalli jikin ta, murmushi tayi tace. "Tabbas Bahijja kincika baiwa marar ƴanci da ace a gaban iyayena nike da bawanda ya isa yaimani kalar wannan ukubar danike ciki kwantawa tayi hawaye na zirara a saman fuskar ta.

A Wajen Sarki Baidulƙais kuwa zaune yake a fa'da shida magatakarda yaba shi umurnin ya ruba wasika zuwa ga Sarkin Waisu Humzu cikin kankanin lokaci yagama rubutawa aka tada ɗan aike ya tafi Masarautar Waisu, bayan sun gama ƴan tsubbace tsubbacen su haka suka tashi ba inda ya tsaya sai filin da yasa anaba bayin Daborah horo na musamman koda ya isa ya iskesu sunyi laushi ligib haka yakara tambayar su waye Tarib saidai jiya iyau ba wani sauyi dan amsar su ɗaya ce basu san shiba, wannan karon kau da kanshi ya dukesu sannan ya shaidama Sarkin bulala itace damar su ta karshe muddun sukaki faɗar gaskia yabasu damar su halaka su baki ɗayansu haka ya koma sashen shi rai ɓace koda suka iso ya iske Jakadiya tagama haɗama shi kayan abinci zama yayi zaifara ci kenan saiga gimbiya Yazira itama zama tayi suka gaisa sannan tafara bashi abincin zai ƙarɓa kenan Bahijja ta faɗo mashi a rai, yaji bazai iya ciba yarasa dalilin dayasa yake tausayin Bahijja a zuciyar yasan dai baida burin da ya wuce ya ɗanɗani zumar Bahijja sannan taimashi aikin bauta, sawa yayi Jakadiya takaima Bahijja abinci a gidan kaso hakan ba karamin dadi yaima Jakadiya ba dan tanaso taga ƴar tata,haka ta ɗauka ta tafi gidan yari, itako gimbiya Yazira wani irin bakin ciki ne ya turnike ta afili ta bayyanar da ɓacin ranta tace. "Haba ranka shidade taya zaka ba baiwa wannan abincin mai daraja ina laifi kabarta ta amshi na gidan kaso!." wani irin kallo yaimata sannan ya mike tsaye yace. "Kina nufin inabarta yunwa ta illatata kenan ba haka nike ba duk abinda nikeyi inasane." yana gama faɗa ya shigewar shi daki tanasan shiga tana shakkar abinda zata tarar dan tasan halin mijin nata baida wasa ko kadan.

Itako Jakadiya koda ta isa haka mai kula da kofar gidan yarin ya bude mata gate ta shiga wuce masu laifi taitayi kananan masu laifuka su ba gidan kasa suke ba wata hanya sukabi sannan suka taka wani bene kamar zaka shiga cikin rijiya haka suka dinga bin wannan bene suka shige gidan kasa duk da safiya ce amman kace marece dan ba wani wadataccen haske ke gare shiba nan Sarkin gidan yarin yaimata iso zuwa wajen Bahijja tana isa ta isketa ta buga uban tagumi koda taga Jakadiya da sauri ta mike saidai ba yanda zatayi ta iso wajen Jakadiya sabida rufe kofar dakin Bahijjan take hakan yasa Jakadiya tasa aka bude Bahijja zama wani wuri sukayi sannan Sarkin gidan yari ya basu waje, cikin kulawa Jakadiya ta kalli Bahijja tana taɓa fuskar tace. ", Bahijja lafiya naga fuskar ki duk jini miyasa meki harhaka."?
buɗe baki Bahijja tayi tace.

"Bakomai Baba bugewa nayi da ta'ga,kaina kemin ciwo shine hancina ya buge da ta'ga." kallanta tayi cikeda mamaki tasan Bahijja bata taɓa yimata karyaba saidai bata amince da abinda tagaya mata ba, saidai ta kyaleta, tace. "Ga abinci kici ƴata karki damu zaki fito bada jimawa inafatan ba abinda ke damunki."? "Eh Baba bakomai." bata abinci tayi ta zuba mata kamar mayunwa ciya haka Bahijja takama cin abinci ba ƙauƙautawa wani tausayi Bahijja taɓa Jakadiya

Please Login or Register in order to submit comment