Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasa sai garza uban ihu da kuka takeyi, ganin taki sakin shi yasa ya banbaro hannun ta daga rikon da taima shi ya fara tsula mata ita a jiki sake fasa kara tayi mai ruɗarwa, hakan yasa Yarima Haishir zai tafi wajen Sarki Baidulƙais ya hango Sarkin bulala nata dukan wata yarinya tana sakin ihu da sauri ya iso wajen su ganin yanda Bahijja keta zille zille tana kuka hakan yasa ya dukama Sarkin bulala tsawa rai ɓace yace. "Sakarta baka da hankali ne zakaimata wannan uban dukan baka ganin yarinya ce."?


Zubewa kasa Sarkin bulala yayi yana neman afuwa. "Ranka shidade tuba nike kaiman afuwa umurni daga Gimbiya Yasira." rai ɓace Yarima Haishir yace. "Daman tace ka duketa ne ko kuwa ita kadai ka raina da zakai mata irin wannan ukubar har haka."? "Aaa ranka shidade aiki za'a sakasu a taskar bayi zasu gyara wajen Gamji tun da safe basu fara aikin ba har yanzun shiyasa aka dakesu."....."yimin shiru wannan sakarci muddin baka duka kanemi afuwar taba ni kadai nasan abinda zan maka." jiki na rawa ya duka har kasa yana neman afuwar Bahijja, itako daman duk ta ruɗe dan taji dukan da akai mata duk da bada yawa aka bugeta ba, batasan sadda ta tace ta yafe mashi ba, hakan yasa Yarima Haishir yace su tashi su tafi haka kowa ya watse, itako Bahijja banda garzar kuka ba abinda takeyi ga sheshekar kuka tanayi Yarima Haishir yace ta tashi ya fara bata hakuri, godiya taimashi haka su Zainab suka kamata suka koma cikin taskar bayi.

Suna shiga cikin taskar bayi ɗakin su suka nufa da ita, sai shashsheka takeyi alamun taci kuka tagaji da godewa Allah, Zainab ce ta dafa kafaɗar Bahijja tace. "Haba kawata kibar wannan kukan inaga ke akaima wannan dukan ai kilan mutuwa zakiyi ko, dole ki ɗauki dangana inda har kikazo a baiwa ba yanda zaki iya." share kwallan da suka taho mata tayi ta kalle Zainab tace. "Zainab kenan da ace kinji irin kuncin da nikeji a zuciya ta dabaki faɗi hakaba, tabbas ina cikin tashin hankali anrabani da Masarautar mu da iyayena da masu kaunata nan inma ina cikin tashin hankali marar misaltuwa da zaki buɗa kirjina tabbas da kinsha mamaki yanda zuciya ke dokuwa kamar ta fito." cikeda tausayin bahijja Indo tace. "Keko wane hali kike ciki har haka."?


"Hmmm kunga zan kwanta jikina baimin dadi anjima zanje inma gimbiya Yazira wanki kar in makara." cikin rashin yarda Indo tace. "Kawai bakisan kifaɗamana damuwar ki kilan baki daukemu yanda muka ɗauke kiba." murmushin karfin hali Bahijja tayi tace. "Ba haka bane kawai dai nagajine kuma ba wani hali bane irin yanda ake gallazamana azaba duk da karancin shekarun mu, dan haka karku damu ba komai."

Zainab ce tai saurin cewa. "Eh kam dole ashiga cikin hali fata dai gamji ya fidda mu a halin nan." ganin Indo zata kara wata maganar yasa Zainab ta riko hannun ta suka mike tareda yima Bahijja bankwana suma suka shiga gidanjen su, cike da rashin jindadin abinda Zainab tai mata suna fita Indo tace. "Haba Zainab ya zaki fiddoni bayan nasan ba abinda Bahijja kesan faɗa bane kawai dai ta boyemana damuwar tane." "Hmmm hakane sai dai zakiji mutuwar Sarki a bakin Zainabu ba kije ki tambayi Umman ki, kilan tasan abinda Bahijja ke boyewa kinga shiga ta gida indan huta kafin mufara aikin bautar kamar jakuna." bata jira cewar Indo ba ta faɗa dan karamin gidan su mai daki biyu, wanda kusan haka gidajen bayin suke kufai kufai wani gidan ma mutun biyu ke ciki har ukku, dayaki taskar bayi tana da girma dan dai bata kai turakar bayin Daborah girma ba.

Washe gari da marece Sarki Baidulkais ne da Sarki Lahazu zaune a saman wata kilisa ta alfarma tasha kayan marmari jere suna fira a cikin lambu gwanin dadi sai Sarki Lahazu ya kalli aminin nashi yace. "Abokina daman insan insanar dakai wata magana." cikin kulawa ya kalli Sarki Lahazu yace. "Inajinka menene." "daman akan maganar da nace zamuyine shekaranjiya ɗanka Haishir yaga yarinya yanaso kuma yana kaunarta da zummar aure shine nace bari infada maka amatsayin ka na uba." duk da yasamu faɗuwar gaba amman sai ya samu kanshi da murmusawa yace. "Kai gaskia naji dadi gamji ya dafa a ina yaga yarinyar."?


Numfasawa Sarki Lahazu yayi yana cewa. "A cikin Masarautar ka yaganta kuma na fahimci yayi nisa akan son ta gaskia." ɗan shiru Baidulkais yayi yana nazari shima Lahazun shi yake kallo yana nazartar wani abu ga abokin nashi kafin yace. "A Masarauta ta.? Wacece wannan."? dan ɗaga kafaɗa Sarki Lahazu yayi yace. "Wata baiwa ce....baijira ya ida maganar shiba yace. "Baiwa fa kace kamar Yarima Haishir inashi ina auren baiwa."? kallan raini Lahazu yaima Baidulkais sannan yace. "Ai wannan baiwar ko aya tazo ya cancanta asota kodan kyawunta usulin ta da ɗabiarta kaga ba wani abu bane idan aka ƴan tata Shikenan kaga ya samu mata uwa uba takoma Masarauta ta sai naso sannan za'asan ba cikakkiyar ƴa bace baiwa ce ya kaga wannan salon abokina."?

Shiru yayi yanda yaga Lahazu yana yaba kyawun surar baiwar ba abinda ke idanun shi ke hakaito mashi sai surar Bahijja da kyaunta dan danan yaji kirjin shi na dukan tara tara dakewa yayi yace. "Hakane saidai ya faɗa maka sunan baiwar kuwa."? da eh ya amsa ma Sarki Baidulkais a kagare yace. "Wacece ita."? "Bahijja sunan ta wata yarinya bazata wuce shekara sha biyu ba a duniya." da sauri Baidulƙais ya mike yanajin wata irin juwa na dibar shi dakewa yayi bakin shi na rawa yace. "Bahijja baiwa ce ta amana inama ba itace Yarima keso ba danaba..... "Kaga abokina menene da kabamu baiwar amana aimu ƴan tata zamuyi kuma ta auri yariman Waisu dan haka saidai in akwai wata kwantacciya a kasa ban saniba." murmushi yayi mai ban takaici yace. "Hmmm bazaka ganeba Lahazu."
"Inba komai kabawa ɗana Bahijja yana sonta."
"Yanzun dai kaga yarinya bata sani ba kuma kaga..."kaga baiwa harwani ra'ayine da ita anya nakasa gane manufar ka akan Bahijjan nan da kake ta kumfar baki akanta." baisan sadda yace. "Sonta nike." baki ɗayan su suka kalli juna danko Lahazu tufa ke hannun shi baisan ya saketa ba, da sauri baidulƙais ya dawo hayyacin shi yace. "Ina nufin matsayin baiwa ta hadimata ban shirin rabuwa da Bahijja a halin yanzun kodan kankacin shekarun ta amman..."Hmmm kasanni nasanka kasan abinda zan'iya haka kaima kardai ace ba abinda nike zato bane ke tsakanin ka da ƴar cikin ka Bahijja inko har zargin da nikeyi ba haka bane to kafansar ma ɗana baiwar ka Bahijja ko nawa ne ni Lahazu zan biya." cikin fushi baidulƙais yace. "Karka faɗamun magana abinda kake zato sam ba haka bane, Bahijja sunan ba ni nahaifeta dan haka wannan itace maganata ta karshe kabar zancen Bahijja zanyi tunani akai, komai kenan zakaji." "Amman yaza kace haka inaganin....ɗaga mashi hannu Badulƙais yayi zuciyar shi na dukan tara tara jiyake kamar ya shake Lahazu musamman da ya fahimci yana zargin sa akan neman Bahijja kamar yanda haka yake a zahiri sai dai shima baiji zai iya sadaukar ma Haishir Bahijja yana sonta kuma ya ɗauki aniyar sai ya ɗandani zumarta mai tsannin zaƙi.


Murmushin gefen baki lahazu yayi sannna yace."Shikenan yanda kace ina sauraran ka, kuma zan sanar ma Haishir halin da ake ciki sannan kasani kamar yanda kace haka ina jiran tsammani dan haka zuwa gobe zamu koma gida dan jiran sakamako, nabarka lfy." yana ida faɗar haka yai tafiyar shi yana fidda iska mai zafin gaske, shima zama yayi rigijib jiki sake yana jin wasu kwalla masu zafin sun taho mashi a kirjin shi na duka a haka yayi shiru yana saƙa abubuwa kala kala a ranshi.


Wajen karfe shidda Bahijja ce ta fito sashen gimbiya Yazira rike da wasu kaya a hannun ta sai sauri takeyi ta tafi sashen Jakadiya, tana shiga wata hanya taji anrike mata hannu, wani irin faɗuwar gaba taji ya kamata, zatayi ihu taji an doɗe mata baki, baki ɗaya idanun suka fito kamar zasu faɗi kasa idanu kawai ta zuba mashi tana kallan shi, wani irin kwarjinin ta yaji yakamashi baisan sadda ya cire hannun shi daga bakin taba, yana so ya faɗa mata son da yake mata amman ya kasa da sauri ta anshe hannun ta, jikin ta na rawa tace. "Ranka shidade barka da marece, damn Jakadiya ta aikeni zan wuce." kamar wanka gele ya bata hanya ta wuce duk jikin shi yayi sanyi yana jin wani abu gami da Bahijja, itako sai sauri takeyi tanajin kafar ta na harde mata harta shige gidan Jakadiya, shiko inda tabarshi yakasa ko motsi da kyal yaja kafa ya tafi, masaukin su, yana shiga ya iske mahaifin shi yaje ya dawo ya kasa ko zama tambayar shi damuwar shi ya fara bai iya cema shi komai sai yace. "Kashirya gobe zamu koma gida." wani mummunan faduwar gaba yaji yace. "Abba taya zan tafi ba Bahijja."?
"Karabu da ita." dukawa yayi yace. "Na rantse da Gamji zan iya mutuwa inba Bahijja." kallan sakarai yaimashi cikin kosawa yace. "Haka nace karabu da ita ai munci ribar zuwan da mukayi nasamu abinda nazo nema, dan haka gobe zamu tafi mubashi lokaci yayi tunani akan Bahijja kafin mu ɗauki matakin da yadace akan shi kaga iyakar abinda nace kenan bansan musu." badan yaji hankalin shi ya kwanta ba yabar maganar ya shiga daki sai tunanin Bahijja yakeyi a cikin zuciyar shi.

Masarautar Daborah, Yarima Malik ne kwance baisan bacci yai awan gaba dashi yana cikin bacci ya fara mafarkin waiga wata yarinya nan tana ta gudu a cikin daji wasu mutane sun biyota da gudu ta boye bayan wani katan icce ta leken mutanen da suka biyota, sai taji ankamata ance mun kamata dan haka yau sai mun kasheta suna ta dariya itako sai kuka takeyi tana wul kafafu tana cewa Ya Malik kataimakeni zasu kasheni......ji yayi ya tashi kamar an kwara mashi ruwa dan zufa yana son ya tuna abinda ya faru amman ya kasa sai muryar yarinyar yakeji akunnen shi tana cewa ya taimake ta baki daya kanshi ya kulle, daren ranar Malik bai koma bacci ba sai yafara nafilfili har asuba saida ya dawo sallar asuba sannan ya kwanta bacci wahalalle ya ɗauke shi, bai tashi ba sai goma na safe lokacin har Ashir ya gama shiri yana jiran uban gidan nashi ya fito ba Malik ya fitoba sai wajen sha ɗaya cikin shigar alfarma ya fito na milk din kaya da ratsin kofi riga da wondo na ƴan india ne a jikin shi sai hula, koda ya fito falo gaishe shi Ashir yayi kallan da Malik yaimai ya tabbatar da yagama shirin tafiya Masarautar Raifasu, zaman yayi saman wata kujera ta alfarma sannan ya amsa da. "Lfy, yanzun zaka tafi kenan, anshi wannan kayi guzuri Allah ya tsare hanya.cikin jin dadi Ashir ya amsa yana godiya sannan yaima Malik sallama ya tafi, bai jima da fita baiwar shi Aliya ta shigo tafara gabatar mashi da kayan karin kumallo sannan ta shiga tafara gyara mashi daki, yafara kalaci kenan yaji ana sanar da shigowar Saifulislam yana shigowa Malik ya mike yana rungume mahaifin shi sannan suka zauna atare suka yi karin kumallo sannan suka cigaba da fira ta ɗa da mahaifi yana tambayar dan nashi damuwar shi.


A Masarautar Raifasu kuwa Sarki Lahazu da Yarima Haishir har sun gama shirin su tsaf su da bayin su, ba dan Sarki Baidlƙais yaso ba yaje sukayi ban kwana duk yanda Yarima Haishir yaso ya sake ganin kyakkyawar fuskar Bahijja ta gagare badan yaso ba suka tafi zuciyar shi cike take da kaunar Bahijja har aka buɗe masu gate suka kama hanyar tafiya zuwa Masarautar Waisu.




Sarki Baidlƙais ne zaune a sashen shi yakasa zama yaje ya dawo har Jakadiya tazo baisan da zuwan ta saida ta sake gaidashi karo na huɗu sannan ya kalleta a firgice ko amsa gaisuwar ta baiba yace. "Ina Bahijja turomani ita yanzun Jakadiya." tana san tayi magana tana shakka, haka ta tafi sashen gimbiya Yazira ta isketa tana wanki kamar kullin faɗa mata sakon Sarki Baidlƙais tayi dai dai nan uwar bayi Uwani ta fito da sauri ta koma ta gayama gimbiya Yazira kiran da Sarki kema Bahijja, batasan ta iso wajen su Jakadiya ba tace aiki tasa Bahijja, dukawa sukayi ta gayamata kiran da Sarki kema Bahijja, cikin izzah tace. "Shikenan ke kuma nabaki minti biyar kije ki dawo." da sauri Bahijja ta amsa da toh, itako gimbiya Yazira tana komawa daki alqabba ta saka tana dakon zuwa sashen mijin nata dan bata yarda da kiran da yaima Bahijja ba, itako Bahijja jiki a mace ta tafi Jakadiya na kwantar mata da hankali ta tafi, a falo ta same shi ya kafeta da mayun idanun shi itako sai wasa take da hannun ta harta shigo ta gaida shi ta duka kasa ta raɓe kamar wata mage, kallan ta yayi yace.....




*Ƴar Mutan Kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote.



*BAYI MA 'YA'YANE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
__________________


*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



Babi na 27&28




"Miyahanaki zuwa wajen aiki ko kina nufin kindaina yima uban gidan ki hidima!"? Yanda Bahijja taga yai maganar ba alamun wasa a fuskar shi shiyasa Bahijja takara shiga taitayin ta, kanta a kasa tace. "Tuba nike ranka shidade ina aikin uwar ɗakina ne gimbiya Yazi.... ba tareda ta karasa sunan ba ya daka mata uwar tsawa ƴan hanjin ta ne suka juya dan tsoro yace. "Daga yau baki da aikin kowa ko bautama kowa da sunan wahala saini daga ban amince ki kara aikin wani ko wata ba daya wuce nawa ni Baidlƙais inba hakaba kiyi kuka da kanki dan saina maki hukunci mai tsauri kinajina!"? Da sauri tace. "Eh ranka shidade naji kaimin afuwa basan sake ba." basuyi aune b sukaji ana sanar da zuwan gimbiya Yazira tana zama gefen mijin ta tagaida shi, a dakile ta amsa kallam Bahijja tayi tace. "Ke tashi kibamu waje!" a hankali Bahijja ta tashi zata tafi jitayi yace. "Bahijja." juyowa tayi a sanyaye ta taho baijira ta karaso ba yace. "Je kigyaraman daki na."


Wani mugun kallo gimbiya Yazira ta aika mata sannan tace. "Ranka shidade nasaka ta aiki kuma ai Bahijja tayi ƙankanta da gyaran ɗaki." kallan da bankaɗa mata ne yasa ta haɗiye sauran kalaman ra sannan yace. "Ban umurce ta datayima kowa aiki ba da ya wuce nawa dan haka daga yau na haramta mata yima kowa aiki a cikin Masarautar Raifasu sai nawa kaɗai kuma ba ruwanki da girman ta ko ƙanƙan tarta umurni nane da fatan kinfahimta."?



A sanyaye gimbiya Yazira ta ɗaga mashi kai itadai Jakadiya tana jin duk abinda ke faruwa nata ido duk da tasan ba karamin musifa yake jefa Bahijja ba duk da mugun kudurin shi akan ta......




A turakar bayi kuwa Binta ce dasu ladidi keta share share kamar ba gobe duk da kasancewar Binta uwar bayin Daborah hakan bai hanata aiki ba kuma ba ruwan ta da zalintar kananan bayi acewar ta dui daya suke ba wanda yafi wani a cikin su, suna cikin aikine duk sun gaji suka zauna gefen wata bishiya Ladidi ce ta kalli Binta tace uwar bayi ya kamata ace izuwa yanzun munsan halin da ƴarmu Bahijja ke ciki tunkan ta manta da suwaye iyayen ta kinga akalla ta ɗauki lokaci mai tsayin gaske a Masarautar Raifasu."



"Hmm Ladidi kenan kina bani mamaki yanzun mu harmuna da wani gata ko galihu da zamu iya dawowa da Bahijja a hannun mu aini inaji araina kilan muda Bahijja sai darussalam na fiddata araina saidai munaima Bahijja fatan alkhairy akowane hali take munai mata fatan nasara Allah ya jibinci lamarin ta." " Ameen saidai duk da haka bansan kina fadar haka kisa aranki ƴarki zata dawo gareki." "Hmmm Ladidi kenan Allah yasa, ko yanzun ina tsoron abinda kaje yadawo shiyasa bansan ana zancen nan." "kinjiki taya za'a hanaki maganar ƴarki, kuma shi Yarima Malik baice komai ba bayan akan shi kuka rasa yarku." mikewa Binta tayi tana takaicin kalaman Ladidi, tace. "Mubar maganar nan Ladidi Yarima Malikussaif yaimana komai tunda yana tausan halin da ƴarmu ke ciki." tayaya cewar Mairo wadda tunda aka fara maganar takasa cewa komai dan mamaki halin Binta taga batasan laifin Yarima Malik ko kadan. "Hakane duk da hakan bazai anfanemu ba saidai Yarima ya tambayeni inda Bahijja take kuma nasanar dashi abinda nasani, saidai tsoro na ɗaya hukuncin da Saraunya Zulaiƙa zata ɗauka akaina kasancewar ta kama mu muna maganar dan Allah kusama zuciyar ku hakuri muyima Bahijja addu'a kowane hali ta tsinci kanta ta ɗauki dangana da hakuri kunji inda na tsaya a lamarin Bahijja, saidai kusani inasan ƴata tilo a duniyar nan da muke ciki saidai ba yanda muka iya kaddara ta riga fata!." ta karashe maganar tana share kwalla a idan ta suma gogewa sukayi kowa ya kasa cewa uffan basuyi aune ba sukaji an rufesu da duka haka suka mike sunaci gaba da aiki basu jimaba da cigaba da aiki ba saiga wata baiwa wadda ake cema Hamziya tace ma Binta Saraunya Zulaiƙa nasan ganin take taji jikin ta yai sanyi suma su Mairo duk sun shiga ruɗani haka ta tafi tana mai addua a cikin zuciyar ta batasan me zata iske ba a yau kuma......




tana isa wajen Saraunya Zulaiƙa ta isketa ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tana shakar kamshi duk hadimai masu mata fiffita suna tayi masu tausa nayi haka Binta ta isa wajen Saraunya Zulaiƙa takai gaisuwa shiru ne ya biyo baya na dakikai sannan taimata kallan kaskanci tace. "Sai yanzun kikaga damar zuwa kiran nawa."?


Jitayi jikinta ya tsinke ta sake kallan Saraunya murya na rawa tace. "Allah yataimaki uwar marayu yanzun kiranki ya riskeni ko sakan ban karaba na taho amsa kiranki saidai wanda nayi a hanya kimin aikin gafara Binta na tuba.!"
A watse ta tsirta yawu akan fuskar Binta sannan tace. "Basai na fada maki abinda zakiyi ba amman bansan ko kanki na rabawa ba!" godiya Binta tayi ta mike tafara daddan nama Saraunya Zulaiƙa takafaɗa a hankali, shiru ne ya biyo baya, itako Binta ganin yanda Saraunya Zulaiƙa ta ƙaskantata yasata tafara kwalla wanda batasan tanayin suba sannan tasa hannu tana share miyan da Saraunya Zulaiƙa ta watsa mata a kan fuska, jin da tayi Binta ta daina yimata tausa na dakikai yasa dakama Binta tsawa tace. "Baki da hankali insaki aiki ki tsaya kina haukane kinkosan agaban wa kike!"? Baiwar Allah Binta batasan sadda ta duka kasaba tana neman afuwa, haka Saraunya Zulaiƙa ta ɗauke Binta da maruka har ukku dai dai nan Saifulislam ya shigo ta tsaya ko motsi ya kasayi itako Binta rike kuncin ta tayi tana maiba uwar dakin tata hakuri duk ta ruɗe dan ta maru wanda harta fara sabawa da azabar Saraunya Zulaiƙa akanta tace. "Uwar gijiyata kiyi hakuri Binta nagodiya ina tuba Allah ya huci zuciyar Saraunyar Daborah girman kine!." buɗe baki Saraunya Zulaiƙa tayi zatayi magana kenan taga Saifulislam wanda mamaki ya gama kamashi hakan yasa tace. "Ɓace mani da gani shasha sha kuma gobe kizo aiki da wuri kinajina." "angama ranki shidade uwar marayu mahaifiya ga adalin Yariman Daborah Allah yakara girma nabarki lfy." haka Binta ta tafi zata wuce ta duka harkasa tagaida Saifulislam, cikeda sa tausayin ta ya amsa sannan ta tafi shi kuma ya karaso cikin falon Saraunya Zulaiƙa, sauran bayin na ganin haka kowa ya bar falon daga shi sai ita ya rage, itako Saraunya Zulaiƙa tana ganin ya zauna ta zauna gefen shi tanai mashi barka da shigowa a takaice ya amsa take taga sauyi akan fuskar mijin nata cikin kulawa tace. "Abu Malik miyasame ka bansaba ganin wannan fuskar taka mai cike da haiba a cikin ɓacin raiba ko fushi lfy ka faɗaman damuwar ka."? Da bainiyar cewa komai ba sai kuma yace. "Bakomai ina murna zanzo ingana da farin cikina sai kuma nazo naga saɓanin hakan kardai ace har yanzun baki wofintar da al'adar kaka da kakanni akan wa'annan bayin ba."?
Shiru tayi daman tasan sai ya tanka itadai ta kasa gane halin Saifulislam shidai komai tausayi shiyasa take yima Malik uzuri, amman a zahiri sai tace. "Aaa bahaka bane narasa gane mugun halin Binta taya zata... "Kinga Ummu Malik basai kince komai ba nasan wacece Binta kema kinsan hakan, saidai kash bai kamata muzama masu butulci akan iyalan Abdulmajid ba duka da yanda suka sadaukar da ƴarsu ɗaya tilo akan ɗanmu ɗaya tilo Malik duk da itama ƴace kamar shi amman hakan baisa sun sota ba sai sukaso namu ɗan, hakan bai nuna maki darajar suba da kimaba agaremu."? "Haba Abu Malik kadai danganta wannan baiwar yarinyar Bahijja da ɗana Malik jinin sarauta kaka da kakanni karka manta itafa baiwa ce yar gado akan bauta da bayi haba mijina baiwar!"? Cikeda takaici ya kalli Saraunya Zulaiƙa yace. "Hakane Bahijja baiwa ce saidai kisani daga malicci ɗaya suke kilama tafi Malik daraja sannan kisaka a ranki kamar kullin kuma ba zan fasa faɗamaki ba Bayima Ƴaƴane kamar kowa kuma suma suna tasu darajar ki gyara shawara nike baki a matsayin ki na mata agareni mafi soyuwa a cikin zuciya ta.!"


Shiru tayi tana karajin tsanar Binta da ƴarta nakara ruruwa a cikin zuciyar ta kamar kara hura wutar ta akeyi zatayi magana sukaji shigowar Malik wanda tunda suka fara maganar su Bahijja yanajin su ganin kar maganar tayi tsayi asamu saɓani tsakanin iyayen nashi wanda bai fatar hakan yasa shi saurin shigowa gaidasu yayi cikin girmamawa, haka mahaifin nashi ya amsa yana mai jin dadin ganin ɗan nashi itako Saraunya tana hake dashi a ciki ciki ta amsa wanda hakan yasa Malik baiji dadi ba basu jimaba suna fira d mahaifin nashi wanda Saraunya ta zama ƴar kallo hakan yasa Saifulislam yaimasu sallama yatafi shi kuma Malik ya koma wajen mahaifiyar shi ya yafara fadanci yana bata hakuri da tausassan lafazi da takiyin magana jin yanda ya dage yana koɗata sai kace ba Malik dinta yasa ta sakkowa daga fushin da takeyi dashi tace.....




"Haba Malik yakakeso inyi taya zan zuba ido kana magajina amman kana sakin jikin ka da kaskantattun mutane kabani mamaki abinda naji kuna cewa da Binta akan wannan banzar baiwar Bahijja." duk baijin dadin yanda mahaifiyar shi ke wulakanta mutane amman sai ya boye damuwar shi yace. "Kiyi hakuri Ummu kema kinsan ina tareda ke, dan haka indai akan Bahijja ne kisa a ranki namanta da ita bankara zancen ta farin cikin ki shinawa Ummu na!" yakarasa maganar shi yana kwantawa a saman cinyar ta itama shafa sumar kanshi takeyi wadda tai kwance tayi luf da ita, tace. "Kaji dan halak kagama wankemani zuciya ta Allah yaimaka albarka."
"Ameen Ummu na." cewa tayi. "Yanzun damuwa ta ɗaya shine yanda mahaifinka ya fita yana fushi dani akan wannan lalatattar baiwar Binta." da sauri Malik ya tashi zaune yana mai boye damuwar shi ga mahaifiyar shi yace. "Haba Ummu kidaina damuwar kanki akan Binta itafa baiwar kice kibarta da abinda kr damuntama na bauta, amman ki kwantar da hankalin yau zanje gun Abbuh zan bashi hakuri komai zai wuce." cikin jindadi tace. "Yauwa masoyina abin alfaharina Allah yatsareman kai farin cikina." da amin ya amsa a ranshi yana misalta son zuciya irin na mahaifiyar shi tana addu'a Allah ya tsare shi batasan taga ya cutu, amman ga ƴar wasu can na cutuwa ko ajikin ta dayake ita baiwa ce, da haka yaimata sallama ya tafi sashen shi, itako tana da kwarin guiwar cewa Saifulislam zaidaina fushi da ita dan tasan ba abinda Malik zai nema wajen mahaifin sa ya rasa da haka ta shiga daki dan hutawa.

Itako Bahijja lamarin Masarautar Raifasu yakara ƙamari a gareta kullin cikin tsangwama take a wajen gimbiya Yazira ba dare ba rana hakama idan ta dawo taskar bayi ba abinda ya sauya cikin tashin hankali take kwana dan Uwani uwar bayi kullun dare sai ta shiɗema Bahijja bulala talatin haka take kwanciya jikin ta a fashe wani bima bacci gagararta yakeyi kuma gari na waye haka zata tashi ko karin kumallo batayi zata tafi sashen Sarki Baidulƙais kamar yanda ya umurceta

Please Login or Register in order to submit comment