Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar tayi mata kuka haka taji,cikin kulawa tace. "Ƴata rabanki da kici abinci tun yaushe ko ba'a baki abinci, lemor abincin da Bahijja ta ɗauko yasa ta dakata sannan tace. "Baba ko yaufa saida akabani abinci kawai dai wannan abincin da kika girkomani akwai dadi yayi kama dana sarakai." takarasa maganar tana cigaba dacin abincin ta, kallan Bahijja tayi fuskarta ɗauke da murmushi sannan tace. "Eh abincin Sarakai ne Mai Martaba ne zaici sai yafasa yace akawo maki kici." ɗebe hannun ta Bahijja tayi take fuskarta ta sauya ture kwanan abincin tayi tace. "Baba da ace tun farko kinsanar dani daga inda abincin nan yazo da bazanciba, duk Masarautar nan dake kadai na amince Baba ke ke kaunata, kece Mahaifiya ta." tagama maganar kwalla ba zirara a idanunta itama Jakadiyar kwalla ta share sannan tace. "Ƴata ki aje duk wata kiyayya da ake maki baki da wani zaɓi daya wuce ki amshi duk abinda yazo daga gareki koda a hannun makiyinki ne Bahijja ba wanda zai cutar dake, saidai kada ki amince da gimbiya Yazira, amman Sarki Baidulƙais bazai cutar dake ba, saidai zai iya cika burin shi akanki, ta wannan fannin karki amince dashi azzalumi ne ki rike wannan a ranki ƴata." gyaɗa mata kai Bahijja tayi sannan ta rungume Jakadiya suna cikin magana Sarkin yari yazo yace ma Jakadiya lokaci yayi, da toh ta amsa sannan taba Bahijja ruwa tasha, kallan abincin gaban Bahijja yayi hakan ba karamin ɓatama Sarkin yari rai yaiba daurewa kawai yayi, sannan tayi sallama da Bahijja ta tafi, kallan Bahijja yayi yace. "Waya baki izinin cin abinci yau bana ce bazakici komaiba sai tace. "Daga Mai Martaba ne." komawa tayi cikin dakin ta yasa kwaɗo ya garkameta da mugun kuduri aranshi iri iri.


Koda Jakadiya ta dawo ba inda ta wuce sai madafa takai kwanuka sannan ta faɗi abinda za'a girma Sarki Baidulƙais na dare, haka takoma wajen Sarki koda yaga Jakadiya da kallo yabita na kindad, cewa tayi. "Ranka shidade koda nadawo daga wajen Bahijja na wuce madafa dan sanar da uwar tuwo abinda zakaci da dare." "sannu da kokari Jamra, ya kikabar Bahijja a wane hali take."? shiru Jakadiya tayi kamar mai nazari sai tace. "Ranka shidade ban amince da yanayin da naga Bahijja saidai dana tamabayeta damuwar ta tace mani bakomai." murmushi yayi yace. "Shikenan Jamra kin kyauta saidai kidaina takurata akan abinda take ɓoyewa a ranta, zaki iya tafiya kije ku huta kafin anjima." godiya taima Sarki sannan ta tafi, shiko a ranshi shima bai yarda da abinda Bahijja tafaɗama Jakadiya ba yanaji akwai abinda akemata yasan bazata faɗa ba dan rashin galihu da ƴanci bazai bari ta faɗa saidai yasan yanda zai bullowa lamarin da haka ya tashi ya shiga daki ya cigaba da yan tsafe tsafen sa da yasa ba.



Daborah


Yarima Malik yaka makura wajen zirga zirga har Huzaifa yagama saka rai da sanin damuwar MalikusSaif, suna cikin haka kowa yayi shiru wani uban ajiyar zuciya Yarima Malik ya saki sannan ya kalli Huzaifa yace. "Mezakace ga baiwar da batasan hawaba batasan sauka ba ake azabtar da ita akan wani dalili wanda bata da ilimi akanshi."? Take jikin Huzaifa yai sanyi yasan tabbas Umman Bahijja na cikin ukuba kenan to miyafaru har haka kallan Yarima Malik yayi sannan yace. "Gaskia anzalince ta sannan zata kasance cikin tashin hankali koda kuwa zata kashe kanta tabbas gaskiar ta abin korarwa ne saboda baiwace marar ƴanci da galihu."
"Ko zaka iya taimakonta."? Cikin mamaki yace. "Kwarai kuwa musamman yanda batasan komai ba, saidai wacece wannan baiwar da ta ɗaga hankalin Yariman Daborah har haka."? "Wakake tunanin zai ɗaga mani hankali ya hanani sukuni injishi tamkar jinin jiki banda Bahijja!" da sauri Huzaifa ya kalli MalikusSaif yace. "Inakasamu labarin Bahijja kana nufin tana Masarautar Raifasu."? "Kwarai kuwa Huzaifa hakan yasa goben nan nikeso ka kashirya zamu tunakari Masarautar Raifasu dan ɗauko Bahijja!" bakin Huzaifa na haɗe haruffa yace. "Tayaya kakeganin zamu tafi."? "Ko bazakaje ba intafi da Yazid."? Murmushi yayi sannan yace. "Allah ya huci zuciyar magajin gobe ina nufin ya zamuyi da Sarauniya."? ''Koda hakan ya nufi yafeni saina ceto rayuwar Bahijja." "Aaa MalikusSaif kada kabari tausayin Bahijja yayi rinjaye akan ka karabu da Mahaifiyar ka, kasan ta hanyar da zaka bi, mutafi." "kaga Huzaifa ko kasan cewa a halin yanzun Bahijja na gidan kaso a garkame." "subhanalilah agarin yaya."? Hmmm cewar Malik sannan yace "ta hanyar wannan shasha shan Ashir nasaka shi aikin dubomani idan Bahijja na Masarautar Raifasu hakan yasa ta shiga cikin ukuba dan anganshi wajen masaukin su ba ita da sauran bayin da muka bashi kaga dole inje incire Bahijja cikin wannan musibar duk fa akaina ta shiga wannan halin.

Wani irin tausayin Yarima Malik ya kama Huzaifa dan shi a halin yanzun abokin nashi yake jima tausayi ganin yanda ya damu da baiwa kamar Bahijja marar daraja a cikin Masarautar Daborah tabbas akwai wani baban almari shi yafara tunanin abokin shi bawai tausayin Bahijja kadai yake yiba harda so saidai yasan baisan yana son taba abinda yasani tausayin ra yakeyi itada iyayen ta, jin shirun yai yawa yasa MalikusSaif ya kalli Huzaifa yace. "Ko baka da abin cewa shiyasa karakani da idanu har haka."? "Hmm Malik kenan akwai babban lamari da nike hange tsakanin ka da Bahijja, amman gaskia abinda ya kamata kafara tunkarar Abbuh akan wannan maganar." "kaga Huzaifa shima bakin shi ɗaya da Sarauniya kawai dai shi yanajin tausayin su, saidai son shi a gareni bazai barshi ya banni inje ɗauko Bahijja ba a ewar shi baisan insaka rayuwata a cikin haɗari kaga dayake ni ɗane ita kuma Bahijja ba ƴa' bace baiwa ce." "Aaa Yarima karka faɗi munanan kalamai akan iyayen ka, abinda yafi kamar yanda nace kaje ma Abbuh da wannan maganar abinda yace sai munema kanmu mafita zuwa gobe sa safe ina ganin hakan zaifi." cikin gamsuwa Yarima Malik ya amince da shawarar abokin nashi tashi yayi yace bari yaje wajen Mahaifin nashi dan baison lamarin ya wuce safiya baije wajen. Bahijja ba.


Koda ɗan aiken Sarki Baidulƙais ya isa Masarautar Waisu yana zuwa Sarkin gida yaimashi iso zuwa wajen Sarki Humzu, yana zaune saman wata shimfiɗa ta alfarma shida ɗanshi Yarima Haishir sai matar gimbiya Ƙamariya, yana zuwa suka zube suka kwashi gaisuwa, cikin kulawa suka amsa Sarkin gidane ya faɗa mashi dalilin zuwan bakon nashi ɗagama Sarkin gida hannu yayi a lamar ya tafi dan ko ba'a faɗa mashi ba daga ganin wannan yadin yasan kayan bayin Raifasu ne, kallan Yarima Haishir yayi hakan yasa ya karɓi takardar dake hannun wannan bawan budewa Yarima Haishir yayi sannan yafara karantawa.


_Bayin mamakin cin amanata dakayi ba Humzu ni naɗaukeka amini kuma ɗan uwa amman kai saɓanjn haka dan haka kasani bawan ka daka turo dan ya sace Bahijja haƙar ka bata cimma ruwa ba dan kana so kaba danka Haishir auren ta shine zaka biyo ta wannan hanyar ta kasani duk abinda zakayi Baidulƙais yana ankare dakai dan haka Bahijja tawace malakina kuyi gaggawar rufe babin Bahijja tunkan ayi baku daga Sarkin Raifasu zuwa ga Sarkin Waisu....._


Wani irin huci Haishir ya furzar kallan baka da wayo Sarki Humzu yaima Haishir sannan ya kalli wannan ɗan aiken duk da agaban shi aka karanta sakon yace ya tashi ya tafi sannan inyaje ya gaishe da Sarkin su, ba Haishir ba hatta ɗan aiken da gimbiya Ƙamariya saidsaida sukayi mamakin jin amsar da Sarki Humzu yace aba abokin nashi haka ya tashi ya tafi zuwa Masarautar Raifasu, yana tafiya Yarima Haishir yace." haba Baba taya zaka bada wannan amsar ga abokin gaba tunda a halin yanzun ya tashi daga masoyi."


Hmmm murmushin girma Sarki Humzu yayi sannan yace. "Yaro yarone hakan bakaramin ciwo zaima Baidulƙais ba, ba'a nuna ɓacin rai a gaban abokin gaba yanzun ba zargin mu yake ba akan kaima baiwa Bahijja farmaki ba, ni nafi zaton Sarauniya Zulaiƙa keson ɗaukar baiwar ta kasan itace fansa akan Yarima HusbarulƘais dan haka tunda harya jefomani wannan mummunan kalaman saina rabashi da Bahijja cikin kankanin lokaci."dariya Yarima Haishir yayi yace "shiyasa nike alfahari dakai Babana kanada hikima shikenan Bahijja zata dawo gareni inyi yanda nike so da ita." gimbiya Ƙamariya ce tace. "Kaji wawa inakai ina baiwa kana ɗan Sarkin Waisu magajin gobe." ɓata rai Yarima Haishir yayi yace. "Umma da acekinga Bahijja ina tunanin a wannan duniyar da muke ciki ba wata ƴa mace da takaita kyau, kina tunani abune mai sauki Sarki Baidulƙais zai tsaya yana gargaɗi akai kema kinsan Bahijja abice mai matukar daraja akowace Masarauta tasamu baiwa kamar ta, ta cancanta ta zama cikakar gimbiya kodan ta zama abun tunkaho a cikin duniya da wannan kasar tamu ta Gambia mai albarka


Yanda Sarki Humzu yaga yanayin Haishir ya tabbatar dacewa yai nisa ga son Bahijja dan haka zai iya kokarin sa dan ansota dan haka dole ya nunama Yarima Haishir cewa Bahijja fa baiwa ce mai cikeda rikici sarkakiyawa da kalubale ya tabbata Sarki Baidulƙais bazai bar Bahijja kodan yanda yake fasiƙi sannan shima Haishir ko wane lokaci burin shi Bahijja tazama mamora a gareshi koda ba auren ta yaiba, sannan uwa uba yasan muddin MalikusSaif yana numfashi sai ya kwace Bahijja ta koma kalkashin ikon mulkin su kodan addinin ta, da haka yaita sake sake sannan yace ma Haishir. "Ɗana kabi asannu lamarin Bahijja akwai ruɗarwa karka zira jikin akanta saidai kasa aranka gab muke da kwato Bahijja a cikin wannan Masarautar tamu ta Waisu kodan incusama Baidulƙais bakin ciki a cikin zuciyar shi.


Shiko Yarima MalikusSaif yana isa wajen Saifulislam ya iske Mahaifiyar shi ta fito daga cikin ɗakin mahaifin nashi daga ganin zataje fa'da yanda yaga tayi shirin gaidata yayi yana mai ɓoye damuwar shi a kan fuskar shi, duk da haka saida Sarauniya Zulaiƙa taji ranta yabata ɗan nata na cikin damuwa rike hannun shi tayi cikin nata sannan tace. "Yariman Daborah kamar akwai abinda kedamunka, faɗaman mike faruwa.?" kirkiro murmushin karfin hali yayi sannan yace. "Ummu bakomai kawai kaina naimani ciwo ne kuma nasha magani." cikin kulawa tace. "Sannu ɗan albarka ya kamata ka huta gaskia shiyasa naga karabu da zuwa fa'da kenan."? Da eh ya amsa Mahaifiyar tashi, cikin kulawa tayi bankwana da ɗan nata baki ɗaya hankalin ta yanakan Yarima Malik hakadai ta tafi fa'da, shiko yana isa ɗakinll Mahaifin nashi yai sallama ya iske shi kan sallaya, da murmushi ɗauke a fuskar shi ya amsa cikin so da kauna sannan yace. "Yarima daganin ka kana cikin damuwa kuma akwai abinda kake ɓoyema Abbuhn ka kuma abokin shawarar ka faɗaman damuwar ka ɗana."?


"Abbuh Bahijja itace damuwa ta kuma matsala ta.!" wani mummunan faɗuwar gaba ta riski Saifulislam, aran shi ko cewa yayi anya ɗan nan yanada hankali miyakawo maganar Bahijja daman Malik bai cire Bahijja aran shi ba duk da bata cancanci hakan daga garemu ba amman rigimar dake tareda Bahijja ba karama bace, Allah dai yasa Malik ba wani abu yake ji dangane da Bahijja koda yake baiwa ce fa kuma hadimar shi, Aaa bata yuyuwa ko Mahaifiyar shima bazata lamunce da hakan ba, wata zuciyar tashi tace. "Kai ko Saifulislam miyakawo wannan maganar da bata da tushe mtsw daman haka zuciya take a zahiri kuwa cewa yayi. "Dana miyakawo maganar Bahijja." "haba Abbuh baka ganin halin da take ciki antabbatar mani cewa tana cikin hali yanzun haka tana gidan kaso kaga dole mutaimaketa Abbuh." Cikin kulawa Saifulislam ya kalli ɗan nashi sannan yace.....




*Ƴar Mutan Kankia ce❣️*


Share
Comment
And
Vote


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________


*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



Not Edited



🔚🔚🔚 of Book One


Babi na 35&36



*Wannan page din nakine kiyi yanda kikeso dashi Pharteemarh knk inaimaki fatan alkhairy ta wajena🥰*



~Kusani inayinku irin sosai din nan Bayima Ƴaƴane Comments Group kusani inajin dadin yanda kuke mani ruwan Comments Allah yabar so da kauna inai maku fatan alkhairy da duk wani masoyina wanda nasani da wanda bansani ba duk ina maku son fisabilillah Allah yabar kauna 🤝🏻~




"Tabbas Malik yakamata ace zuwa yanzun Bahijja tadawo wajen iyayen ta saidai nayi mamakin yanda har kasan tana cikin wannan mawuyacin halin saidai wannan ba abun la'akari bane, mafita itace yanda za'ayi a anso ƴar mutane tabbas Baidulƙais yaci amana bayyanan niyar wanda da wahala muyafe mashi ita, saidai mahaifiyar ka tasan da wannan zacen. "? Cikin daburcewa Yarima Malik yace. "Kullin abinda take gargaɗina kenan in mance da rayuwar Bahijja hakan yasa na yanke shawarar dakaina zanje ansar Bahijja Abbuh ba faɗamaka dan insamu albarka da adduarka agareni."


"Hakane fatan alkhairy Saidai inaso kasanar da mahaifiyarka wannan zacen." "shikenan Abbuh naji dadin addu'arka Allah yakara girma da ɗaukaka." "Ameen ya Allah, saidai abinda zan faɗamaka kasani cewa,ban yarjemaka kabar Masarautar nan ba, kai kaɗai zan haɗaka da jarumai da zasu kasance dakai." da sauri ya kalli mahaifin nashi yace. "Abbuh kayi hakuri bansan tafiya da wasu jarumai ni kaɗai zan tafi."
"Shikenan saidai karka manta ka tabbatar ka gayama mahaifiyarka kafin kayi wannan tafiyar." da toh ya amsa mashi sannan yaimashi sallama ya fita, sashen shi ya wuce ya zauna dan yasan tana fa'da sai 'yan sake sake yakeyi yanaso yaje wajen mahaifiyar shi amman yana tsoron abinda zai iske wajen shi yasan zata amince da kudurin shi.



A wajen su Yarima Haishir kuwa yana gama shiryawa ya wuto wajen mahaifin shi yace. "Abba zantafi Raifasu dan cika umurnin ka kasamani albarka." fuskar shi ɗauke da murmushi yace. "Gamji ya shiga lamarin ka sannan ka kiyaye karka bari a samu matsala ɗana." toh Abba,da haka suka hau dawakan su shida bayin shi guda ukku.



_Masarautar Raifasu_



Bayin daborah ne aketa ganama azaba kamar ba mutane ba daga cikin bayin wani bawa ne da ake cema Nulwa yacema Sarkin bulala ya tsaya zai faɗi abinda yasani duk wanda ke wajen saida sukaji wani mugun faɗuwar gaba, kallan bayin yayi yace. "Inajinka." "Ranka shidade nasan wannan bawan da kuke tuhumar mu akan shi, wato Tarib, ba sunan shi Tarib ba sunan shi Ashir daga cikin mu yake yazo daga Masarautar Daborah wannan shine gaskiar abinda nasani kataimakeni karka kashemu muntuba."
Cikin ɓacin rai yace. "Daman kusan da wannan zancen kukayi shiru.!" jiki na kyarma Nulwa yace. "Aaa daman zamu faɗa." daga hannu Sarkin bulala yayi ya watsama Nulwa mari, yaci gaba da faɗa da dukan su, ji sukayi Sarki Baidulƙais yace. "Dakata da dukan su." zama yayi saman wata kujera ta alfarma yace. "Nulwa kace kasan bawan nan."? Da sauri ya ɗaga kai yace. "Eh daga wajen mu yake sunan shi Ashir."
Kallan shi yasake yi yace. "Miyakawo shi a wannan Masarautar."? Raba idanu Nulwa yayi ya kalli Tasi'u duk ya raina gaskiar shi wani mugun kallo ya watsama Nulwa, sauke kanshi yayi kasa yace. "Yazo dan ya duba idan Bahijja na cikin wannan Masarautar." shiru yayi yana nazari duk kanshi ya kulle jikin shi yai sanyi yace. "Waya turoshi."? Da sauri Tasi'u yace. "Ranka shidade ba wanda ya turoshi kawai dai hanya ce ta biyo dashi shine ya shigo." da sauri Nulwa yace. "Bahaka bane Yarima Malik ne yazm turoshi.!"


Mikewa Sarki Baidulƙais yayi yace. "Koda naji ainasan daman kune munafukan." dan haka aita bugun su kar a raga masu sannan a kaiman su gidan kaso a rufe mani su, bance abasu abinci ba ko kadan dan haka duk wanda ya nemi yaimaku taurin zuciya ku kashe shi." da sauri Nulwa ya rike hannun shi yace. "Karufamana Sarki Baidulƙais yace. "Kaga wannan bawan kasare mani kanshi sannan ka kawo mani shi a cikin fa'da ta." take cikin Nulwa ya duri ruwa haka aka tisa keyar su har cikin gidan yari sai kuka sukeyi......



Koda aka isa dasu gidan kaso haka aka dinga jibgarsu kamar jakai sannan Sarkin horo ya sauke kan Nulwa da kanshi yakaima Sarki Baidulƙais, fa'da ce tamkan da mutanen koda ya iso da kan Nulwa ya aje gaban Sarki Baidulƙais yace. "Ranka shidade angama cika umurnin ka." kallan magatakarda yayi yace. "Rubutama Sarauniya Zulaiƙa wasika kaba bawa yakaimata sannan asaka kan wannan bawan cikin buhu a haɗa mata dashi, yanzun yanzun." sannan ya kalli Sarkin horo yace. "Je kacigaba da abinda ba saka bance a ragama wa'annan bayin ba saidai karka daki Bahijja." haka ya tashi ya tafi......



A Masarautar Daborah kuwa Yarima Malik ne yaje wajen Sarauniya Zulaiƙa iske ta yayi kwance a saman makeken gadon ta na alfarma yana shigowa bayin dake dakin suka zube suka kwashi gaisuwa ɗaga masu hannu yayi alamar amsawa baki dayansu suka fita, zama tayi gefen gado tana kallan ɗan nata, a hankali ya iso wajen ta daka ganshi kaga mai damuwa, shima zaman yayi gefen ta sannan ya gaidata cikin girmamawa, kallan shi tayi tana nazarin ɗan nata sannan tace. "Yarima mike damunka."? Shiru yayi yarasa dame zai fara, ganin shirun yayi yawa yasa ta sake jefo mashi tambaya akaro na biyu, a hankali ya buɗe bakin shi kamar baisan magana yace. "Ummu kimin aikin gafara bansan yanda zaki ɗauki wannan maganar ba.!" murmushin manya tayi sannan tace. "Kaɗama mahaifiyarka abinda ke zuciyarka dan ita kadai yafi cancan ta kasanar mawa Yarima." cikeda gamsuwa yace. "Ummu inasan zuwa Masarautar Daborah domin anso Bahijja." da sauri Sarauniya Zulaiƙa ta mike tace. "Banhaneka maganar wannan baiwar ba miyasa ka takura kanka akanta? Ko bakasan minike yawan faɗa maka ba Malik."?


A zuciyar shi kuwa cewa yayi, gaskia Ummu saidai kiyi hakuri dan ba abinda zai hanani ceton rayuwar Bahijja, amman a zahiri sake marairaicewa yayi yace. "Ummu koda tana cikin musiba."? "Koda zata rasa ranta koda hakan na nufin rayuwar ta zata lalace ta tarwatse koda hakan ya na nufin daina numfashin ta, wai ko kamanta itadin baiwa ce? Ko manta itadin marar daraja ce? dan haka kada insakejin bakin ya ambaci kalmar Bahijja."


Wani mummunan faɗuwar gaba ta riski Malik kallan mahaifiyar shi yayi sannan ya duka ya rike kafarta cikin sanyin murya yace. "Ummu Malik dan Allah kitausaya mani kibari inceto rayuwar Bahijja karki manta alkhairyn da taimani a rayuwa.!" "yimin shiru, yimin shiru Malik wlh badan bansan inga bacin ranka ba dakasha mamaki, inka kuskura bakin ma yakara furta kalmar Bahijja saina wanke ka da mummunan mari sha sha sha, ɓacemani dagani.!'' a hankali MalikusSaif ya mike jiki sage kamar wanda kwai ya fashemawa a ciki, duk da haka bai kasa a guiwa ba ya faraba mahaifiyar shi hakuri yace. "Ummu kiyi hakuri Allah ya huci zuciyarki sannan duk abinda kikaji game dani na ɓacin rai ki tausaya ki yafemani sannan kisama ɗanki albarka Ummu." baijira cewarta ba ya fita ranshi nai mashi ƙuna, ba inda ya wuce sai sashen shi ya fara shirin barin Masarautar Daborah a sirrance bayan kiran Huzaifa da yasa akai mashi.


A wajen Bahijja kuwa Jakadiya ce zaune a gefen ta suke magana kasa kasa saidai dagani kamar sirri sukeyi Jakadiya ce tafara magana. "Bahijja inasan inmaki wata magana tabbas ƴata tunda naganki naji kiyimani har cikin zuciyata sannan kuma addinin ki yaimani dan haka a yau nikeson inshiga cikin wannan addinin naki ƴata." cikin farin ciki marar misaltuwa Bahijja ta kalli Jakadiya ta rungume ta tace. "Babata naji dadi marar misaltuwa da naji wannan batun daga gareki dan haka addinina abune mai kyau da jinkai ga tausayi dan mahaifina yasha faɗamani hakan, yanzun duk abinda nace ki faɗa." cikin jin dadi Jakadiya tace. "Toh ƴata." Bahijja ce tayi shiru tana ɗan tunani da alama wani abun take tunawa tace. "Kice Ash hadu alla ilaha ilallahu wa ash hadu anna muhammadar rasulillahi." haka Jakadiya ta maimata rungume ta Bahijja tayi tace. "Wannan shine makullin shiga addinina, ma'anar kuwa shine kince kin shaida babu abin bautawa da gaskia sai Allah kuma annabi Muhammadu baiwan Allah ne kuma manzon sane, daga yau kinzama cikakkar musulma Baba, saidai banda ilimi sosai a cikin addini na,duba da yanda aka rabani da iyayena, amman kibari idan Allah yasa na fita wannan gidan zan nemi Tasi'u shi zai kara koya maki komai dangane da addinin mu." sake rungume juna sukayi suna hawaye cikin so da kauna.


gimbiya Yazira ce da kanta taje gidan yari ta harɗe kafa saman kafa tasa Sarkin horo yana ganama Bahijja azaba bugun ta yaci gaba dayi itako Bahijja ta dukar da kanta kasa tana kwalla, ga zaginta gimbiya Yazira nayi kowa hankalin shi yayi wajen mugunta itako Bahijja azaba ta isheta ji sukayi ance. "Mi zangani haka wannan wane sakarci ne."? Cewar Sarki Baidulƙais atake gimbiya Yazira ta ruɗe danko Sarkin horo zubewa yayi kasa yana neman afuwa, danko Sarki Baidulƙais yagama kulewa ranshi yai mugun ɓaci baisan sadda ya wankama Sarkin horo mari ba, itako Uwani sai kyarma takeyi kiran Sarkin bulala yayi yasa shi yaima su Uwani dukan tsiya sannan yasa aka garkame su gidan kaso ita da Sarkin horo, isa danko gimbiya Yazira gumini yagama wanke mata jiki sai kyarma takeyi jiki sake tafara magana. "Ranka shidade daman abinda yasa kaga nazo gidan....wata irin tsawa ya dakama gimbiya Yazira sannan ya wanketa da maruka har ukku cikin fushi yace. "Daman na lura kintsani Bahijja baki kaunar ta na fahimci haushin ta kikeji daman sharri kike mata akan gurfane nasan bazata aika abinda ake tuhumar ta dashi ba, dan haka yau ba sai gobe ba nakara ganin kin shiga sabgar Bahijja bani bake sannan naimaki katangar karfe da Bahijja dan haka maza kiɓaceman dagani! " yakarasa maganar ranshi ɓace, itako da wani marayan kuka ta fashe tafara ba Sarki Baidulƙais hakuri, baki ɗaya wani irin tsanar gimbiya Yazira yaji wanda baitaɓa jin irin shiba"kayimani halacci kayafemani karka rabu dani Abban Husbarul kai kadai gareni da rabuwa da ɗana zanji ko kuwa da juyaman baya da zakayi ka yafemani.!" shiru yayi kamar mai nazari sannan yace. "Baki san wannan ba, ita Bahijjar me taimaki kika tsaneta dan haka baki ba Bahijja, sannan Uwani daga yau na fiddata a uwar bayi kuma na yanke mata hukuncin gidan kaso na wata shidda munafukai."kallan Bahijja yayi wadda tunda Sarki Baidulƙais yafara magana ko kallan shi bataiba saboda ta tsane shi bata san kallan fuskar shi, sawa yayi aka kaita sashen shi.



_Daborah_



Koda Huzaifa yazo wajen Yarima Malik ya iske shi yagama shiri kallan Huzaifa yayi yace. "Huzaifa kaje kashirya cikin daren nan zamubar Masarautar nan." cikin gamsuwa Huzaifa yace. "Ranka shidade aituni nagama shiri na baka da damuwa saidai kabari kafar mutane ta ɗauke sai mutafi." murmushin jin dadi Yarima Malik yaima Huzaifa sannan yace. "Yawwa na wajena naji dadi kamar wane lokaci kake ganin zamu tafi."? "Ranka shidade idan naga dama tabada zanzo da kaina in gayamaka saidai ince ka tsaya cikin shiri, fata Allah yasa muyi wannan tafiyar cikin sa'a." da Amin Yarima Malik ya amsa yana cigaba da abinda yakeyi shima Huzaifa fita yayi.


Koda aka kai Bahijja sashen Sarki Baidulƙais sawa yayi aka kira mashi Jakadiya yace, takai Bahijja wajen Saude dan bata kulawa ta musamman, tashi Jakadiya tayi daga dukiyar da tayi suka fita da Bahijja suka tafi taskar bayi, ranar haka su Zainab sukaita murna Bahijja ta dawo garesu, nan aka haɗa mata ruwan wanka ta shiga tayi sannan ta kwanta koda dare yayi Bahijja ce tafito ta tafi wajen Jakadiya tadata tayi tace. "Baba yazamuyi idan aka gane kin karɓi addinina kuma kinga anka su Tasi'u bare ya koyar dake komai yaza'ayi."? "Haba Bahijja kada ki damu kema kinsan yanda zaki ɓoye addinin ki kina kankanuwar ki bare kuma ni kada ki damu kanki ki sani zan kiyaye kuma na aminta da addinin ki shine na gaskia." wani irin dadi Bahijja taji ta rungume Jakadiya tana kuka wanda batasan ko na mene ba, hakuri Jakadiya tafara ba Bahijja sannan tace. "Yawwa ƴata koyaman abinda kika sani a cikin addinin musulinci nan Bahijja taimata bayanin sallah dai dai gwargwado, harta nuna mata, ba ita ta koma wajen Saude ba sai cikin dare.


A Wajen Malik kuwa ko bacci yakasa burin shi yaga Huzaifa ya shigo bai ida tunanin da yake ba saiga Huzaifa haka suka kama hanya suka fita a sirrince kowa ya hai saman dawakai suka kama hanyar tafiya Masarautar Raifasu.


Tunda Baidulƙais ya tashi ya fito zuwa falo yana fitowa yasamu Jakadiya zaune tana jiran fitowar uban

Please Login or Register in order to submit comment