Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin Bahijja ta shiga shekara biyu, a duniya uwar bayi ce tazo da ita a sashen Sarauniya Zulaiƙa tana aikin ta na share share da goge goge ita kuma Bahijja sai wasan ta takeyi hankali kwance, mahaifiyar ta sai jin dadi takeyi idan taga yarta na cikin nishaɗi, sallamar da Malikussaif yayi shiya katsema Binta aikin ta dukawa tayi ta gaida MalikusSaif cike da sakin fuska ya amsa yana tambayar ta Bahijja lokacin ma baigan ta, ita kuma tana cin abinci a cikin leda duk ta ɓata hannun ta tana ganin MalikusSaif ta rugo da gudu ta faɗa jikin shi ta rike shi, sai murmushi takeyi tana jin dadi dukawa yayi ya rike hannun ta duk ta ɓata mashi kaya amman bai damu ba yasan yarinya ce bata da wayau, aiko Binta duk ta rude ganin Bahijja ta ɓatawa Yarima Malik kaya kakkaɓe mashi tafara yi tana bashi hakuri da mamakin ta sai yace." haba Umman Bahijja karki damu ba komai ai yarinya ce."dai dai nan Sarauniya Zulaiƙa ta fito falo zatayi, kalaci tsayawa tayi tana kallan shi duk mamaki ya gama kama ta ganin yanda MalikusSaif ya rike Bahijja, suna haɗa ido da Binta ta watsa mata mugun kallo, jiki ba kwari Binta ta zube kasa ta gaida Sarauniya Zulaiƙa, shi kanshi MalikusSaif saida yaji wani iri aje Bahijja yayi ya tafi wajen mahaifiyar shi, yana murmushi ya gaida ta ko amsawa batayi ba, ta zauna bayi nata kai gaisuwa saidai ta ɗaga masu hannu, a sanyaye Binta ta rike hannun Bahijja zata cigaba da aikin ta amman abin mamaki kuka Bahijja tasa ita dole sai taje wajen MalikusSaif aiko kukan ta ya fara damun Sarauniya Zulaiƙa, cikin ɓacin rai ta kira Binta tana zuwa ta duƙa aiko ta wanke ta da mari, wanda hakan saida ya taɓa ran MalikusSaif ganin shekarun Binta amman mahaifiyar shi bata girmama taba,cikin taƙama tace "kina da hankali kuwa zaki zoman aiki da wannan kaskantattar yarinyar tazo tana sawa mutane ciwon ka? ko kina haukane, Malik kanin uwar tane ko na uban ta jibi yanda ta ɓatama shi kaya."kallan da Sarauniya Zulaiƙa zataima Malik taga Bahijja ta makalkale MalikusSaif duk tsoro ya kamata aiko ta sake dakawa Bahijja tsawa saida tayi fitsari a ruɗe Binta ta riko Bahijja jikinta har rawa yake ta debo ruwa ta goge wajen batasan ta fara kuka ba tana neman afuwa wajen Sarauniya Zulaiƙa tace. "kimin aikin gafara na tuba bansan yanda aikai Bahijja ta saba da MalikusSaif ba, kayi hakuri Yarima MalikusSaif hakan bazai sake faruwa ba, Allah ya huci zuciyar ki uwar dakina bazan kara zuwa da Bahijja wajen aiki ba." tana kuka ta ida maganar, sake darka ka mata tsawa ta kara yi tace ta ɓace mata daga gani tun kan tai maganin ta, a sabule ta tafi jiki ba kwari sai hawaye takeyi, shiko Malik dake zaune gefen mahaifiyar shi, duk ran shi ya ɓaci boyema ta ɓacin ranshi, yayi yabata hakuri, bai jima ba ya tafi sashen shi ya kwanta sai juyi yakeyi yana tuna kalar cin mutun cin da Sarauniya taima Binta dan a haife zata haifi mahaifiyar tashi, baisan kwalla sun zubo mashi a kunci ba ya share kwallan idan shi yasan bazai kara ganin Bahijja ba kuma bazai jure rashin ganin Bahijja ba jinta yake kamar wata yar uwar shi ta jini.



A wajen Binta kuwa ta kwashe komai ta fadama Abdulmajid mahaifin Bahijja shiyasa ya yanke hukuncin barin ta a cikin gida duk da ba wayan kirki ne da ita ba, amman bazai juri ganin irin wannan wulakancin ba koda Bahijja ke baiwa marar gata da yan'ci yasan ba abinda ɗanta MalikusSaif zai nuna mata saidai gata amman suna san yar'su so mai girman gaske wanda basu tunanin akwai wanda yakaita samun wannan gatan haka sukaita ta'ajjabi a zukatan su haka Ladiyo da Mairo suka tadda su, duk labari ya karaɗe turakar bayi akan abinda Sarauniya Zulaiƙa tayi ma Binta koda suka zo basu nunama su Mairo damuwar suba, haka suka ce zasu dinga barin ta a wajen junan su idan basu da aiki a lokaci ɗaya, suna cikin wannan tunanin saiga dogarawa sun shigo suka hausu da bugu da zagi kowa ya fita waje haka aka tara bayi kamar ba gobe, sai yawo sukeyi da wasu manyan manyan bulalai suna dukan su, kamar wasu jakkai basu san hawa basu san sauka ba haka akai masu ruddubu ta ko ina , koda Bahijja bata da wayau amman ganin yanda mahaifiyar ta ke kuka da sauran bayi hakn yasa taje ta kwanta saman bayanta sai gwaranci takema mai dukan Umman ta tsayawa yayi yana dariyar mugunta baisan sadda ya daga bulala ba ya shauɗama Bahijja yasa kafa ya halbata a sume Bahijja ta faɗi kuma sun hana kowa ya kama ta dai dai lokacin MalikusSaif sun fito shida su Huzaifa zasu je wajen gwaji idonsa ya gane mashi da sauri yayi kan Bahijja ya dauke ta kanta ya fashe sai jini yakeyi hankalin shi tashe ya fara mata fififita tuni ciki ya ɗuri ruwa ganin yanda idanun MalikusSaif suka ƙanƙance suka kaɗa tsabar bacin rai.....


Suma abokan tafiyar tashi tada bayin sukayi duk da basu damu da duk wani hukunci da za'ai ma bayi ba amman sunji ciwo ganin yanda aka zalinci yarinya karama tashi Binta tayi ta shiga gida da sauri ta dauko ruwa aka sama Bahijja sunkai minti goma sannan ta farko da wani marayan kuka, shi kanshi MalikusSaif jiyake kamar ya taya Bahijja kukan, saida ya tabbatar da hankalin ta ya dawo jikin ta yana jin bugun zuciyar Bahijja sannan ya mikama Binta yana tashi ya dauke wannan dogarin da zafafan maruka har guda huɗu saida ya fadi ƙasa, bayin dake wajen na ganin haka suka bar wajen tunda MalikusSaif ya wanke shi da mari sauran abokan zalin cin nashi suka faɗi kasa duk sungama tsorata karon farko da MalikusSaif ya daga hannu da sunan hukunta wani a cikin Masarautar Daborah, magana yafara azafafe saiga Sarauniya Zulaiƙa zata tafi fa'da cikin mamaki take kallam Malik daya gama fita hayyacin shi, yana zanzaga rashin mutunci dan an hukunta marar sa yanci Bayi....





*Yar Mutan Kankia ce❣️*




Share
Comment
Vote


*BAYI MA YA'YYANE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________


*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



Babi na shidda




"Baka da hankali zaka doki wannan yar karamar yarinyar kai mahaukacin ina ne, akan Bahijja zan iya halakaka yanzun bakaji kunya ba ka bigi yarinya karama, kawai dan tana baiwa, kafisu ne yanda kake mutun haka itama take mutun kuma tana da iyaye sunsan ciwon ta da anyi magana sai kuce ai su bayi ne bari kaji koda suke bayi ai bayima ƴaƴane, daga yau ku bude kunnuwan ku kujini da kyau duk uban da ya sake ko kallan banza yaima Bahijja sai yasha mamaki! Kai kiramin Sarkin horo zo."? kowa jikinshi yayi sanyi haka Sarkin horo yazo Yarima Malikussaif yasa aka saukema kowa bulala hamsin ranshi a ɓace duk wanda ke wajen nan saida sukayi mamakin kalar hukuncin da MalikusSaif yayi akan dogarawa saboda Bahijja, karma ace Sarauniya Zulaiƙa da tagaji da mamaki ganin yanda ɗanta ke kumfar baki kawai dan anbigi baiwa haka yakama gaban shi yabar su Huzaifa sai mamaki sukeyi danko dogarawan nan a kunyace suka bar wajen wanda zuciyar su ke cike da tsanar Bahijja danko Malikussaif idon shi ya rufe ko Sarauniya Zulaiƙa bai gani ba ta gefen ta yabi ya tafi sashen shi yana fidda huci da iska mai zafin gaske hakan yasa Sarauniya Zulaiƙa bin MalikusSaif yana isa yace mai kula da sashen shi kar abar kowa ya shigo wajen shi koda taga yanayin Malikussaif yake hakan ba karamin tada mata hankali yaiba, ko minti talatin baiyi da shiga ɗaki ba saiga Sarauniya Zulaiƙa, zubewa bayin Malikussaif sukayi suka gaida ta kai tsaye ta shiga cikin ɗakin shi, iske shi tayi idan shi sun kaɗa kamar ba shiba, zama tayi kusa dashi sannan ta kira sunan shi, "Malik." a sanyaye ya dago kai ya kalleta da rinanun idanun shi,yana kallonta ya kauda kai cewa tayi. "yanzun dan an bigi baiwa shine zaka dinga kumfar baki har da daukar mataki, wai me ka ɗauki Bahijja ne a wajen ka? Nasa dan kana bukatar taimaka hidima ne shiyasa, ka bukaci in barsu duk da amana da iyayen ta sukaci man Malik, kadawo hayyacin ka mana meke faruwa dakai wai."? Da disasar muryar shi yace"Haba Umma kawai dan Bahijja na baiwa bashi ke nuna a wulakan tata ba, baki ganin karancin shekarun taya zan saka ido a wulakanta Bahijja." ɗaga mashi hannu tayi sannam tace. "Kai Malik inma bacci kake yakamata ka farka Bahijja ba kowa bace illah baiwa, ban lamunci ace Bahijja zatai maka hidima ba Malik dan tausan da kake mata yayi yawa."



A firgice ya kalli Sarauniya Zulaiƙa, sannan ya kama hannunta yace. "haba Umma kefa kikaiman alkawali Bahijja zataiman hidima meyasa zaki sauya alkawali."!?ya ida maganar cikin tsoro dan yasan halin Sarauniya sosai, yasan tsab zata hana Bahijja yi mashi hidima idan ta girma, shiyasa ya sauko daga fushin da yake dan ya samu ya shawo kanta, cewa Sarauniya Zulaiƙa tayi. "Kwarai kuwa ni nace amman yanzun na fasa bazan yarda ka zauna da Bahijja a matsayin hadimar kaba bayan tausan ta da ya ratsa maka zuciya ni nasan abinda nikeyi dan haka idan zaka manta da rayuwar wata Bahijja tun wuri ka manta ga bayi nan manya wanda zasu iya yimaka hidima ba dole sai Bahijja ba dan haka kaga tafiya kuma duk abinda kakeyi yauda marece kaje fa'da kuma gobe mahaifin ka ke dawo." bata jira cewar shi ba tai tafiyar ta, kanshi ke saramashi kamar ya mutu haka ya kwanta yana mamakin hukuncin da Umman shi ta yanke mashi.


Zuwa yayi wajen waziri Dammur da isar shi ya iske shi kishingiɗe tareda ƴarsa gimbiya Zahara'u sai labari takeyi da mahaifin ta jin isowar Yarima Malik yasata sai jindadi takeyi hatta mahaifin ta ya fahimci irin jin dadin da ƴarsa takeyi yana shigowa gimbiya Zahara'u ta gaida shi, ciki ciki ya amsa ta, sannan ta basu waje kallan shi Dammur yayi cikin kulawa sannan ya fara magana bayan sun gama gaisawa da Malikussaif "koba kace komai ba tabbas kana cikin damuwa Yarima."? ɗan shiru yayi na yan mintoci sannan yace"Kwarai kuwa waziri yau raina ya sosu kuma gashi mahaifiya ta tace Bahijja bazata bari Bahijja taimin hidima ba, gaskia inasan inga Bahijja naimani hidima dan matsayin kanwa na ɗauki Bahijja inasan ka shawo man kan Sarauniya ta amince karta karya alkawali." ya ida maganar cikin damuwa, yasan idan ba waziri ba, to ba wanda zai iya shawo kan Sarauniya shiyasa yazo wajenshi da wuri.


Numfasawa Waziri yayi dan yasan halin Sarauniya Zulaiƙa sarai yasan ba wanda ta tsana kamar zuriar Abdulmajid a cikin bayin Daborah, sai dai baisan sadda zata daina tsanar su ba, amman a zahiri sai yace "haba ɗaba Malik kada kadamu kanka zan shawo kanta saidai ka dinga bin ra'ayin mahaifiyar ka ko yayane saboda wasu dalilai." gyara zamanshi yayi yana kallon Waziri sannan yace. "Amman wane dalilai ne wannan."? cewar Malik, kallan yaro man kaza waziri Dammur yaimashi sannan yace"Malik zan sanar dakai sai nan gaba kaɗan inka kara sanin kanka sannan." "mene ne wannan abin kafaɗa mun karka boyeman."!?cike da da damuwa Yarima Malik yayi tambayar, cewa Waziri yayi "naji abinda kace Yarima sai dai kasani karka manta da tambayar da kayi akan Sarki Jabbar da dalilin da yasa maƙiya ke kawo ma wannan Masarautar tamu hari wannan dalilin shi yakamata kasani a matsayin ka na Sarkin gobe na wannan Masarautar ta Daborah." Wani irin kallo Yarima Malik yaima waziri Dammur yana ganin yasan tambayar da yai mashi shine mafi anfani akan abinda yake san ya sani, cewa yayi "da dai zaka faɗa mani tambayar da naimaka da zaifi mani." murmushi manya waziri yayi sannan yace."Hmm Malik kenan bazaka gane ba sai kaji wannan tarihin zaka fahimci manufa ta duk abinda zaka sani anan zaka fahimta Yarima Malik amman inka shirya sanin dalilin ina sauraran ka." ɗan nazari Yarima Malik yayi sannan ya kalli waziri Dammur alamar ina sauraran ka, gyara zama yayi ya rike hannun Yarima Malik sannan yace......



_Continuation on historical story_


"Malik a lokacin da Sarki Jabbar ya anshi mulkin Daborah banyan wasu watanni ya haɗa gangami na mayaƙa masu tarin yawa kullin shiri sukayi ta yanda zasu tarwatsa Masarautar Waisu ba dare ba rana haka suka dinga shiri kayan yaki suka dinga haɗawa kamar ba gobe, kusan kullin Jaruman Masarautar Daborah suna ta shiri jiran umurnin Sarki Jabbar kawai sukeyi, ana gobe zasu kaima Masarautar Waisu hari kowa yana shiri ba dare ba rana abinda baka sani ba Masarautar Waisu, Masarautar tace data shahara a fagen mulki saidai karamar Masarauta ce tunda bata cikin jerin ukku da sukai shura a cikin wannan kasar tamu ta Gambia, amman ba laifi suma suna da mayaƙa dai dai gwalgwado, dalilin da yasa Masarautar Waisu suke son su kawo mamu hari dan gabar dake tsakanin Sarki Hamidu na wannan Masarautar tamu, haka suka dinga yaƙi da junan su, saboda dukiya da kuma wuƙar *BAIRU* kullin mafarkin su kenan suga sun mallaki wannan wuƙar da dukiyar Daborah duba da yanda Masarautar tamu ta shahara a fagen arziƙi, saidai abinda baka sani ba shine Malik da gari ya waye haka Sarki Jabbar da sauran jaruman Masarautar nan haka suka tunkari Masarautar Waisu gadan gadan suka tunkare ta saidai kasan abinda baka sani ba."? Kallan Dammur yayi yace. "Aaa ban sani ba." Murmushi mai ciwo waziri yayi sannna ya cigaba da cewa. "sadda Sarki Jabbar zasu isa har Jaruman Masarautar Waisu sun tare kofar shiga Masarautar su, ba karamin mamaki ya kama Sarki Jabbar ganin har labari ya isoma Sarki Faihasu cikin kankanin lokaci aka fara gabza yaƙi baji ba gani ba abinda kake hange sai kura da jini ke yawo, danko Sarki Jabbar shiga yayi yaita kashe Jaruman Masarautar Waisu cikin kankanin lokaci Jaruman Masarautar Daborah sun kusa ƙarar da Jaruman Masarautar Waisu koda suka fahimci an kusa kashe su haka suka dinga ja da baya suna neman guduwa, haka Sarki Jabbar ya tunkari Sarki Faihasu ya daura mashi takobi a wuya yana huci yace ma Faihasu bazan kasheka ba sai dai zan barka bakin ciki yayi ajalin ka Faihasu na kashe ɗanka fansar ran mahaifiya ta, sannan ina sauraran martanin ku, saidai kusani ku matsiya tane mu ba dukiya ta kawo mu wajen kuba kuma ba mulkin Masatautar ku muke so ba, kawai ɗaukar fansa mukayi akan ku Faihasu sai na kayi nadama ni Jabbar Haris na tsaneku tsana mafi muni a cikin zuciya ta, shiko banda kyarma ba abinda yakeyi kamar zai mutu dan bakin ciki ganin yanda akaima Masarautar su fata fata duk da sun san da zuwan Sarki Jabbar baki daya Jaruman mu suka tafi Masarautar Daborah, abinda baka sani ba Malik sadda kowa ya dawo ƙura ya lafa aka nemi Sarkin bayi na wannan lokacin ba'a ganshi ba, anyi mamaki saidai da Sarkin gidan tarihi ya duba baiga takobin *BAIRU* ba saida hankalin kowa ya tashi musamman Sarki Jabbar, kamo Sarkin tarihi yayi aka fara tuhumar shi kamar ɓarawo haka Sarki Jabbar ya tura yan leken asiri a sirrince suka koma Masarautar Waisu abin mamaki sai suka ga uban bayin Daborah rike da takobin *BAIRU* a gaban Sarki Faihasu sai kyalkyala dariya sukeyi shida Sarki Faihasu cikin farin ciki Sarki Faihasu yafara magana......



```Komi Sarki Faihasu yake cewa kuma me yahada uban bayi Jafar da takobin bairu a gaban Sarki Faihasu, muje zuwa muga yanda zata kaya a cikin wannan labari na bayima ƴaƴane kar kuman dai👆```





*Yar Mutan Kankia ce ❣️*




Share
Comment
Vote


*BAYI MA YA'YYANE*


*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
__________________

*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*




Babi na bakwai




Sarki Faihasu keta kyalkyala dariya kamar wani. Mahaukaci sannan yace. "Jafar ka kyauta mani da ka kawo mani wannan takobin ta BAIRU dan haka a yau na tabbatar da Masarautar Waisu ta cika cikakkar Masarauta, kasan wani abu Jafar baki ɗaya nahiyar Gambia babu Masarautar ta dakai ta Daborah saidai yanzun mun nakasa ta tunda mun rabasu da wannan takobin da kake gani dan haka Jafar tunda ba wanda ya ganka ka maida hankali ka kwasofirma iyalan ka kadawo dasu wannan Masarautar zan baka mikami mai girma da daraja ka maida hankali ka dawo Masarauta ta."


Harkasa Jafar ya duƙa yayi godiya sannnan ya koma ya zauna da nufin in dare yayi ya koma Masarautar Daborah ya kwashe iyalin sa su gudu, Murmushi waziri Dammur yayi sannan yace. "kaji cin amanar farko da bayi sukai ma Masatautar Daborah ko Malik."


Cikin mamaki Yarima Malik Yace. "Hakane ranka shidade saidai Jafar shine yaci amanar wannan Masarautar tamu, saidai me akai ka Jafar din."?


Mamaki ya kama waziri Dammur ganin yanda Yarima Malikussaif bai ɗauki laifin Jafar ba ya ɗaura ma dukkan bayi ba musamman na zuri'ar sa da suka rage a cikin Masarautar Daborah, cewa yayi. "Kwarai kuwa Malik Jafar shine yaci amanar mu a wancan zamanin saidai da sannu da zaka fahimci komai, koda dare yayi haka Jafar ya shigo Daborah daman Sarki Jabbar yasa anzagaye gidan Jafar da dogarawa da Jarumai saida suka bari ya kwaso iyalan sa, suka damke shi, akwai wata ƙatuwar bishi a cikin Turakar bayi aka ɗaure shi su kuma matan aka tsare su, nan aka sa wawan Sarki da sauran dogarawa sukai ta dukan Jafar har safiya tayi, da gari ya waye haka Sarki Jabbar ya bada umurnin aka tuhumi Jafar saidai ance ka guji mutin sai ya karyata da yasha wahala tuni ya bada labarin komai har ɗaukar wannan takobi da yayi yakai ta Masarautar waisu, cikin ɓacin rai Sarki Jabbar ya zare shafceciyar wuƙar dake hannun Barde Labiru ya sauke kan Jafar, haka aka kwance shi aka haɗa da kan aka yarda a cikin kogin danzir dake nan bayan Masarautar Daborah, sannan yasa Magatakarda yasa alqalami ya ɗibi jinin Jafar ya rubuta wasiƙa dashi zuwa ga Masarautar Waisu, yana shaida masu duk abin da sukeyi ya basu nan da awa ukku su hanzarta dawo da takobin Bairu in ba haka ba cikin awa shidda zai karar da tarihin Masatautar baki ɗayan ta, a cikin iyalin Jafar ya aika wani da wasikar kuma ya shaida masu da jinin Jafar a jikin wannan wasiƙa, sauran iyalan Jafar aka ware masu wani wuri na musamman a cikin Turakar bayi aka hana su fita ko ina, kaji hukuncin da akaima Jafar Malik."


Wani irin nauyayyan numfashi ya sauke ya sake cewa. "gaskia kam anyi rayuwa da abokan gaba, amman tunda an hukunta Jafar meyasa za'a dinga cin zarafin bayi har yanzun."?


Murmushi yayi sannan yace. "Hmmm Malik kenan waya faɗa maka iya nan cin amanar bayi ta tsaya? ai har yanzun ba abinda ya sauya saidai bayin da sunfi na yazun munafunci ina baka labarin Jafar sama ra shekaru dubu kenan, abinda baka sani dama tambaya ta kayi sun maido takobin Bairu ko kuwa basu bada ba."


"Gaskia ne waziri, sun maido da takobin."?


"Kwarai kuwa ko awa ukku basu yiba Sarki Faihasu ya tado da wazirin Laisu ya kawo takobi, a ranar aka maida ta a gidan tarihi, ashe abunda basu sani ba an tsafe takobin muddin aka maida ta gidan adana tarihi za'a cigaba da zubda jini cikin Masarautar Daborah sannan abokan gaba zasu kara saka ido a cikin wannan Masarauta, kuma za'a kara ƙuntata ta wannan silar ne akaima Sarki Jabbar sihiri mai tsanani baifi shekara ba ya mutu, saboda ganin ya kasance Sarki mai zafi gaske kuma Jarumi kaji labarin Sarki Jabbar."




Bayan wata daya aka naɗa ɗansa Yarima Khamil a matsayin Sarkin Daborah saidai abin da baka sani ba shine bayan an naɗa Sarki Khamil Masarautar Daborah bata ƙara samun matsalar hari ba ankai wajen shekara biyar ba'ai wani yaƙi ba, haka akai ta hudɗa daga sasssa daban daban na cikin Masarautar Daborah da sauran sassan kasar Gambia, bayan shekara goma da kafa Sarautar Khamil aka kawo wani fitinan hari marar kyaun gani amman saidai ba Masarautar waisu bace kaɗai ba a cikin tafiyar harda Masarautar Ƙairu da Masarautar Raifasu sai ta waisu da Jaruman su sukayi hadin gwiwar yaƙar Masarautar Daborah lokacin Sarauniya Maimoon tana budurwa ita kuma diya ce ga Sarki Khamil sannan itace Sarauniya ta ashirin da biyar a cikin jerin Sarauniyoyin Daborah." amman abinda zai sa bazan gaya maka wannan tarihin yakin da akayi ba a cikin wannan Masarautar baida kyawun fasali Malik saidai lokaci bazai bari in faɗa maka ba, kana iya neman karin baya ni wajen Sarki lawal mai kula da gidan tarihi na Daborah."



Shima numfasawa yayi yace. "gaskia ina cikin damuwa marar iyaka Masarautar nan tana cikin kalubale sosai na rayuwa, wanda har yanzun ba agama wannan arta bar ba, lokacin sallah yayi na ɗauki abubuwa masu yawan gaske, nabarka lfy waziri ka fitar dani daga kashi ukku cikin goma na duhu. "


"Shikenan Yarima Malik ka huta lfy shawara ta itace kada kasa damuwa a zuciyar ka kuma ka nisan ta kanka daga bayi har sai bukatar hakan ta tashi." "ba damuwa zantafi yau mahaifina ke dawo wa kuma Sarauniya ta umurce ni da inje fa'da."cikeda farin ciki waziri Dammur yace. "Kwarai kuwa zuwan ka yanada mahimmanci, nima zanje zuwa anjima, sai mun haɗu ɗana fatan alkhairy." ya samu sassaucin damuwar da yake ciki, haka ya koma sashen shi yayi sallah ya shirya Sarauniya Zulaiƙa da kanta ta biya ta wajen Malik suka tafi cikin fa'da hannu cikin hannu suka tafi,har cikin fa'da......


Koda suka isa fa'da gaisuwa kowa ya kawo wajen Sarauniya Zulaiƙa saida ta zauna sannan kowa ya zauna, kowa yayi shiru ba mai magana sunkai minti goma a haka sannan Sarauniya Zulaiƙa ta fara magana.


"Dalilin dayasa na taraku anan inasan in sanar daku cewa labari ya sameni har cikin sashena Masarautar Raifasu ta aiko ma wannan Masarautar, tamu da takardar hari a babban filin gabas dake yankin ƙairu suna tuhumar masarautar mu da ɗaukar fansar ran Sarkin Darwan tun zamanin Sarauniya Maimoon sai yanzun iyalin ta suka tado da wannan zancen na ɗaukar fansa dan haka ina umurtar ku da ku shirya gangamin yaƙi wanda baku taɓa yin shiba dan tunkarar abokan gaba duk da sunce a Ƙairu za'a yi shi na naɗa wannan ragamar yaƙin a hannun ɗana Yarima Malikussaif sai ku fita bamu da wani isasshen lokaci ku cigaba da shiri nan da sati mai zuwa zamu isa!."


Mamaki yagama kama Yarima MalikusSaif ɗazun waziri yafara bashi labarin Masarautar Raifasu da Ƙairu dan dai baisan yanda lamarin ya kasan ce ba sannn me yasa har yanzun basu daina tinanin daukar fansa ba a Masarautar suba, magana yafara. "Ranki shidade miyasa suke tunanin daukar fansa garemu sannan a karkashin Sarki Lukman hakan ke faruwa.? Jinjina kai tayi tana ma MalikusSaif kallan ganganci tace. "Hakane Malik saidai kasani ba hari zasu kawo mana ba tunda sun sanar damu dan haka kowa ya shirya sannan maganar ɗaukar fansa ba abin mamaki bane tunda Sarauniya Maimoon ta darkake zamanin su yanzun ne Sarki Lukman zai ɗaga darajar su bayan rasata da sukayi sama da shekaru ɗari ukku da suka wuce tun zamanin Sarauniya Maimoon Sarauniya ta Ashirin da biyar a cikin Masarautar Daborah, tsakanina da ita Sarauniya hudu ce nice cikon ta talatin amman in baki ɗaya mulkin da aka gabatar ne tsakanin Sarakuna sha biyar ne duk da mahaifina Sarki Abduljabar na III har zuwa yanzun dan haka kowa ya tafi ya shirya bamu da lokacin da zamu ɓata."haka kowa ya tafi da abinda yake ayyanawa a cikin zuciyar shi.......



*Wata sabuwa kuma🤣, An aiko ma Masarautar Daborah wasikar yaki my guy ku cigaba da bina kuna bani ruwan comment hakan yana man dadi fa💃*

*Yar Mutan Kankia ce❣️*





Share
Comment
Vote


*BAYI MA YA'YYANE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________




*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR

Please Login or Register in order to submit comment