Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata amanar Bahijja cikin murna ta ƙarɓa daman tun farkon ganin ta da Bahijja taji taimata kuma tanasan ta ɗanyi mata wasu yan tambayoyi na gaba kaɗan da haka ta cigaba da aikin ta, ita kuma Jakadiya ta tafi, bacci yasake ɗaukar Bahijja uwar bayi ce ta shigo dakin matar zata kara kwarama Bahijja ruwa ta hanata tace Jakadiya tace abarta tayi bacci ta huta kar atasheta cikin bacin rai Uwani tace......






*Yar Mutan Kankia ce❣️*



Share
Comment
Vote


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________


*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



Babi na 18




"Kai amman dai anyi tsinannar rayinya anya bata tareda sihiri baiyanan ne, Sarki Baidulƙais yakaita kusa dashi, ga Jakadiya tana bata kulawa, anya ba tsafi tayiba shiyasa kowa ke sonta, gaskia saina kassarama ƴar nan rayuwa ga ƴaƴanmu amman itakadai ce abar so." itadai Saude kallan Uwani kawai takeyi tana mamakin hassada irin tata, duk da itama tanada zuria amman ba abinda ya shafeta da Bahijja inbaka taimaketa baka kassarata ba, cikin jin haushi tace. "Kika kafeni da idanu wato ke bazaki ɗauki matakin ba kenan akan wannan ƴar kwikwiwon yarinyar ba ko."? cewa tayi"haba shugaba kece fa uwar bayi yakamata ace kaf bayi da bako da ɗan gidana sun zama cikakkun ƴaƴanki menene riba dan kinsaka ido akan jikar ki Bahijja."
"Karki rainaman hankali anyi ita Bahijja ba bil Adama bace? dan kawai tanada kyaunki rabu dani ina ganin girmanki matsayin ki na mataimakiya ta baccin haka da na raina maki hankali sai kinsha mamakina sakarai." tabar ɗakin sai sababi takeyi itako Saude kallan Bahijja tayi dake bacci duk tausan ta yakamata tasan duk wanda uwar bayi ta tsana saiya sha ukuba dukko girman mace da haka ta cigaba da hidimar ta.



_~DABORAH~_




Malik ne zaune wajen Dawud Yauma sun gama duba littafin da suke nema basu samu ba hakan yasa Dawud yace suje wajen Lawal mai kula da manyan litattafan tarihi musamman na tsafi cikin gamsuwa Malik yace. "Shikena bari mutafi saidai kace zaka faɗamana abinda kasani dan gane da Sarrilƙus."
"Eh kwarai kuwa munyi hakan daku saidai yanzun bari mukoma wajen wancan iccen inmana shinfiɗa sai in fadama ka kilan kasamu wani ɗan ilimi dangane da Sarrilƙus." haka suka tashi yai masu shinfiɗa kowa ya zauna shima ya zauna yana kallan Malik yace. "Kamaido hankalin kaji Labarin Sarrilƙus da yanda akaita artaba dashi musamman Masarautar Daborah wanda har yanzun ake ciki dayin ta."




LABARI




A shekaru dubu biyu da suka gabata zamanin Sarauniya Maimoon ƴar Sarki Khamil jikanya ga Jabbar ɗan Sarauniya Yahanasu ta II anyi hatsabibin boka da tsafin sa ya karaɗe nahiyar Gambia a lokacin ba addini a cikin Masarautar Daborah, wata rana Sarauniya Maimoon tana gudanar da mulkin ta a fa'da saiga wani bakin mutun marar kyawun fasali ya kawo mata magani yace taba mahaifin ta Khamil saboda baida lfy har anfidda rai wannan dalilin yasa ta cigaba da rike sarautar mahaifin ta, koda wannan mutumin ya fadama Maimoon kudurin shi bata kawo komai aranta ba ta karɓa saboda anmaida tsafi ado kuma abin tunkaho bayan aiyima Sarki Khamil magani bayan kwana biyu kamar ya warke ashe an turo mashi bakin aljani ya dinga zukar jini Khamil har ya mutu, lallai mutuwar Khamil ta ɗaga ma Sarauniya Maimoon hankali har andanga na bayan wata daya aka naɗata a matsayin Sarauniya Daborah.



Bayan shekara ɗaya da kafuwar daular mulkin Maimoon sako ya bayyana a cikin fa'da ta hanyar halboshi da mashi ya kafe a bangon fa'da kowa saida hankalin shi yai mummunan tashi musamman Sarauniya Maimoon.


Shiru ne ya biyo baya sannan Sarauniya Maimoon taba magatakarda umurnin ɗauko sakon, fizogo kibiyar yayiya zare takarda dukawa yayi yaba Sarauniya Maimoon ta bashi umurnin karanta sakon dake jikin takardar.


_Sarauniya Maimoon ina hankalin ki yatafi da zaki ɗauki magani kiba Khamil bayan tsafin sake jikin shi yai sanadiyar mutuwar Sarki Khamil dan haka kasani da sannu sai mun karar da tsatsan ku a doran ƙasa, sannan kijira guguwar yakina daga mutane harda aljanu nine Sarrilƙus saina lalata Masarautar Daborah da abinda kuka taka dake da bokan ka Ƙuduru sain karar daku sannan in ɗauki wakur Barri inkaita Masarautar Raifasu hhhhhhh!"_



Da sauri Sarauniya Maimoon ta mike tana alajabin yaudarar da akaimasu tabbas dole saita ɗauki mummunan mataki akan Sarrilƙus saidai abinda baka sani ba Malik bakaramin mataki Sarauniya Maimoon ta ɗauka ba akan Sarrilƙus!"

Ɗan nazari Malik yayi sannan yace. "Amman ina mamakin wannan mutumin daman haka ya share shekaru masu yawa a doran duniya kodai aljani ne."?

Murmushi Dawud yayi yace. "Sarrilƙus mutun ne ba aljani ba sai dai kasani ba ainihin sunan sa kenan ba, Sarrilƙus wani zoben tsafi ne da ya shafe saman da shekaru dubu biyar tunkan a kafa daular mulkin Daborah yake, ainahin bokan sunan shi Gamki duk wanda yake anfani da zoben shine ake kira da Sarrilƙus shi kuma dajin gamki saboda bokan yasa ake kiran dajin da gamki shi kuma sunan dajin zusu, lokacin da gamki ya kama dajin da aljanu sai suka hana kowa huɗɗa da dajin sai su kadai shiyasa ake cewa dajin gamki, shi kuma bokan zobe na tsatsubar kukar saman dutse ake kiran shi da Sarrilƙus, yanada yara matsafan gaske, duk wanda ya mutu sai su naɗa sabo abashi wannan zoben ana kiran shi da Sarrilƙus, kaji takaitaccen tarihin Sarrilƙus."


Numfasawa Yarima Malik yayi cikin gamsuwa yace. "Amman naji sai dai shi wannan bokan menene ainahin sunan shi."?

"Eh gaskia kayi tambaya mai anfani ainahin sunan shi Ƙibbu sannan shine boka na casa'in dake mulkin dajin gamki kuma zoben Sarrilƙus na hannun shi duk da akwai aljanin dake kula da wannan zoben shida rundunar aljanu, har yanzun dajin gamki da kake gani Malik inakaje da rana kamar dare yake tsabar tsafi abinda baka sani ba Malik zuwa dajin gamki ba riba saboda aljanu sunyi tasiri a cikin shi saidai ban tunanin akwai mahalukin dake rayuwa a cikin shi saidai matsafa da sauran aljanu kuma duk a ƙalkashin ikon boka Sarrilƙus yake."



Yazid ne yace . "amma taya zamu samu damar yakar wannan hatsabibin bokan."? wata dariya Dawud yayi yanai masu kallan yara manyan gobe yace. "Yazid kenan faɗa da aljani ba dadi kuma duk wanda yataka wuta bazai kuma waiwayar taba, kaga yaki da Sarrilƙus tamkar baraza da rayuwa ne dan haka bansan ta yanda zaku bullowa wannan bokan ba saidai bari inbaku taƙaitaccen tarihin yaki da Sarauniya Maimoon tayi da Sarrilƙus akan fansar ran mahaifin ta Khamil ɗan Sarki Jabbar."



Gyara zama sukayi sannan Huzaifa yace "munajinka ya Dawud." cigaba da magana yayi. "Kamar yanda nafaɗa maku sakon da Sarrilƙus yasa aljanu suka halboma Sarauniya Maimoon tunda ga ranar Maimoon ta shiga cikin damuwa kullin kudurin taya zata kawo karshen Sarrilƙus haka ta tara bokaye nadaga sassa daban daban na kasar Gambia duk wanda yazo yayi yan dube duben shi sai yace bazai iya tunkarar Sarrilƙus ba dan yafisu aljanu da tsafi mai girma daga cikin wannan bokaye da Sarauniya Maimoon ta tara haka suka gama tsafe tsafen su suka tafi ta sallame su amman a banza a wofi, saidai abin mamaki washe gari haka aka tashi a alajabi da tsoro cikin ƴaƴan Sarauniya Maimoon, Jumal aka wayi gari ankashe shi batareda wukaba, jikin shi aka zana Sarrilƙus sannan aka duba kirjin Yarima Jumal ba zuciyar shi da harshen shi tabbas faɗamaku kalar tashin hankalin da Maimoon da sauran yan Masarautar Daborah suka shiga ɗaukar lokaci haka ta rungume Jumal tana ta kuka mai tsuma zuciya tana birkita shi taga takarda anrubutata da jini tana karanta wa ta sume ba rai dan firgici."


Waziri Shuzab ya ɗauka ya karanta wasikar wanda mamaki ya gama bayyana a fuskar waziri yakara maimaitawa yayi a gaban kowa.



_Kina mamakin ganin gawar ɗanki ko? Ba abin mamaki bane yanzun haka Maimoon zuciyar ɗanki da harshen sa anba aljani ɗan tsitu dan ya wargaza alkadarin ku sannan kuyi gaggawar mika wukar Barri wajen Sarki Gursu na Raifasu in bahaka ba zamuyi maku dirar mikiya sai munkarar da kowa da komai naku nasan komai zai burgeki kina ganin jinin ɗanki rubuce a takarda ko.? Ina sauraranku keda kazamin bokayen ku, duk tsafin da zasuyi a banka innaga dama lokaci daya zan halakansu dake kanki Maimoon ki kiyaye! Sarrilƙus ke magana._


Baki daya aka shiga ruɗani aka binne Jumal sannan aka fara ba Maimoon kulawa takai sati ko magana batayi a cikin Masarautar Daborah, da yake ƴaƴan Sarauniya Maimoon huɗu ukku maza ɗaya mace, haka akaita bata jike jike har ta hakura saidai Maimoon bata daina yunkurin yakar Sarrilƙus ba, bayan wata bakwai komai lfy ba wata damuwa aka wayi gari ba takobin Barri a cikin gidan tarihi take Sarauniya Maimoon ta fille kan Sarkin tarihi ta haɗa gangamin yaki mararsa iyaka ta tunkari Masarautar Raifasu taimasu dirar mikiya anyi musu asara marar kyawun gani haka yasa Sarkin Raifasu ya murza wani zobe take aljani ya bayyana nan ya fada mashi abinda ke faruwa, cikin kankanin lokaci rundunar yaki ta karu harda aljanu kasan yanda lamarin iska yake duk da ankashe rabi ta kwata da jaruman Raifasu amman daga baya aka fara yima Jaruman Daborah ɗauki ɗai ɗai duk da ba'a ganin masu yakin da aka fahimci da jinni haka yasa. Sarauniya Maimoon taba wazirin ta wukar Barri da ta anso wajen yariman Masarautar na lokacin har ta kashe shi, daman sunzo da bokan su, hakan yasa ya ɓace shida waziri sukabar wajen ta hanyar ɗauke takobin Barri Sarauniya Maimoon ta gama kufula shiga tayi wajen Sarki suka fara fafatawa sai sarrafa wannan zoben yakeyi yaki na kamari danko saida yaima Sarauniya Maimoon kaca kaca harya ɗauka ta mutu yana cigaba da sarrafa zoben shi tasa takobi ta datse ma Sarki hannu ya faɗi kasa take wajen ya ɗauki kuwa marar dadin sauraro abokan artabar tasu suka dinga bacewa yan sauran jaruman Raifasu suka dinga guduwa dan tsira da ransu, duk da haka ba laifi akwai sauran Jarumai fa yawa na Daborah duk da ankashe da yawa haka aka dinga neman Sarauniya Maimoon har cikin fa'da a kwance aka sameta cikin jini ga Sarki Gursu akwance da hannu ɗaya yana shirin mutuwa dai jini ke zuba cikin sauri aka ɗauki Sarauniya Maimoon nan ta tace a zare zoben a taho dashi Masarautar Daborah, sai kuwa Sarki Gursu yakeyi yana nuna kada su taɓa wannan zoben amman haka aka tafi dashi sai zafi ke fita a jikin shi har cikin Masarautar Daborah aka ajiye zoben kowa yaita murna anci yaki gwanin dadi saidai abin da baku sani ba Malik ɗaukar wannan zoben da akayi saida ya jazama Masarautar Daborah da abinda ke cikin fitina da baku tunani dan itace ainahin durkushe war Masarautar Daborah har izuwa yanzun."

''Kowa ya gama karaya da lamarin Sarrilƙus cikin jimami Yarima yace miya faru har haka."? cikin tausayi da jimami harda saukar kwalla a idan Dawud yace....




*Yar Mutan Kankia ce❣️*

Share
Comment

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________


*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*




Babi na 19

"Sarauniya Maimoon tana zaune a cikin fa'da tareda manyan fadawan ta suna shawarwarin yanda zasu ɓullowa lamarn Sarrilƙus kawai sukaji fa'da ta ɗauki rawa da kuiwa ga wani irin hasken wuta da ya hargitse wajen tare da da guguwa mai duhun gaske wadda baka iya ganin gaban ka dan tsoro kowa ya gama fita hayyacn shi wannan guguwar ta ɗauki lokaci mai tsawo tana zagaye fa'da sannan wani katon bakin aljani ya bayyana a sifar mutun marar kyaun gani da fasali, koda mutanen mu hankalin su yadawo jikin su suka fara gane mutane hakan yasa da sauri suka mike tsaye dan firgitar ganin bakin mutumin dake tareda su, itako Sarauniya Maimoon take ta mike tayi wajen wannan aljani a daƙile duk da ta tsorata amman hakan bai hana ta nuna ita shugaba bace, koda Sarauniya ta isa wajen bakin mutumin ta tsaya gaban shi tace.

"Miya kawo ka cikin fa'da ta mi kake nema."? maimakon yaba Maimoon amsar tambayar ta sai ya fashe da wata irin mahaukaciyar dariya saida kowa ya duke tsabar kaɗuwa da tsoro yakai minti goma sannan ya dakata, duk da haka Sarauniya Maimoon bata fasa kallan shiba ido cikin ido, miko mata hannu yayi sannan yace. "Ki azamani zoben da kika ƙarba a hannun Sarki Gursu nine bawan zoben inba haka ba komi ya biyo baya kuka jama kanku ya Maimoon."

Cikin fushi tace. "Kai bawa marar yanci ba zan bada zobe ba kayi abinda kaga dama inhar ka isa tunda kace kaine shugaba mai kula da wannan zoben." ba tareda ya jinkirtaba ya ɓace ya tafi, kowa yayi mamaki sunyi tsammani sai ya ɗauki mataki marar kyau haka sukaci gaba da shawarwari kan lamarin har suka kammala Sarauniya Maimoon takoma sashen ta ita da hadiman ta, har dare yayi ba wani abun da ya biyo baya saidai banan gizo ke sakar ba, Sarauniya Maimoon na tareda da ɗanta Muntazir saiga baiwar gimbiya Hunaisa ta shigo a firgice ta zube a gaban Sarauniya Maimoon tana garxa uban kuka, a tare suka mike tana tambayar ta ko lfy, cikin shassheƙar kuka duk muryarta ta dakushe tace. "ki gafarceni ya Sarauniya ta, na nemi uwar dakina banganta ba, bata cikin wannan Masarautar tuba nike." wani uban duka Maimoon takaima isa ta rushe da kuka mai cin zuciya Yarima Muntanzir ne ya fita ya sanar da sarkin gida cikin kankanin lokaci kowa yasan da ɓatan gimbiya Hunaisa aka baza jarumai a cikin daren nan ba inda ba a duba gimbiya Hunaisa ba amman ba amo ba labari ta ɓata har gari ya waye ba wanda ya runtsa a cikin Masarautar Daborah.


Haka Sarauniya Maimoon taita kuka baci basha har aka wuni cur, danko Jaruman mu tunda suka bazu neman gimbiya Hunaisa basu dawo ba saida rana ta faɗi duk inda ake sa ran ganin ta ba aganta ba ko kaɗan, lamari ya ta'azzara ga Sarauniya Maimoon duk ta lalace ta rame a yini biyu kaɗai kulawa hadiman ta sukaci gaba da bata, suna cikin jimamin ɓatan gimbiya Hunaisa saiga sako an harbo shi ta hanyar mashi ya soke a saman gadon Sarauniya Maimoon, danko bakaramin tsoro ya kama kowa ba, banda Sarauniya Maimoon dan ta shirya zuwan wannan lokacin, zaro mashin tayi ta fiddo wasikar dake jiki ta karanta.



_Maimoon dama kindai na wahalar sa jama'arki akan nekan Hunaisa tana hannuna ki rike zobe ni kuma in rike ta, dan haka kisa a ranki bazan taɓa bada taba saidai gawar ta sannn ki saurari zuwana cikin kankanin lokaci._

Mikewa Sarauniya Maimoon tayi tafito waje tasa sarkin shela ya tara mata Jarumai ta sanar dasu sakon boka Sarrilƙus,tasa a haɗa mata gangamin yaki suka tunkari dajin gamki, dan karɓo gimbiya Hunaisa, kamar dai yanda kuke shirin yi Ya Malik abin mamaki suna tunkarar wannan dajin ba alamun shi sai wani uban fili duk rairaye masu yawan gaske, duk irin subbace subbacen bokan wannan lokaci bai iya gano alkadarin dajin gamki ba, haka suka gaji suka dawo gida, ko awa ɗaya basu kulla ba sukaji ana kaɗa kugen yaki a cikin Masarautar Daborah, kowa ya shiga alhini suma Jaruman mu fita sukayi a shiga sahun yaki duk da Jaruman da sukazo yakar Daborah basu kai namu yawa ba kuma da alama Jaruman Masarautar Raifasu ne, Sarki Gursu yafara magana.
"Sarauniya Maimoon kinsan fansar ƴarki ko? Wannan dalilin yasa kukakai hari dajin gamki yanzun munsame ku tareda jama'ar wannan zoben da kuke renawa yanzun mizaki iyayi ya Maimoon."?

Kallan kallo akafara tsakanin Sarauniya Maimoon da Sarki Gursu batace komai ba, hakan yaba Sarki Gursu damar sawa aka buga kugen yaki, akafara fafatawa tsakanin Sarauniya Maimoon da Sarki Gursu kowa yana kokarin yaga bayan ɗan uwan shi, baki daya jinin Jarumai kan hakaifa yake duba da yarjejeniyar dake tsakanin Masarautun guda biyu duk wanda aka kashe Sarkin su, sun zama bayin wannan Masarautar, ba karamin kokari Sarauniya Maimoon takeyi ba lokacin ji take ranta fansa ne akan kwato yar ta, koda fafawar tasu tai tsamari hakan yasa Sarauniya Maimoon tasamu nasarar wullar da wukar hannun Sarki Gursu ta faɗi kasa hakan yasa ta taɗe shi ya faɗi ta ɗaura mashi wukatar a wuya take Jaruman Masarautar su suka duka kasa sukaima Sarauniya Maimoon biyayya, tace. "Kai Gursu matsiyaci dakai kaskantattace me zakace ga macen da taci galaba akan ka ko zaka iya bada izini a fiddo mani ƴata a matsayin ka na bawa na ko saina fille kanka a gaban bayinka kuma Jaruman Masarautar ka."?

Cikin kyarma yace ."za'a bada gimbiya Hunaisa amman da sharadi sai ta barshi shida Jaruman shi a matsayin ƴantattu sunkoma Masarautar su." take za'a basu gimbiya Hunaisa hakan yasa ta amince a lokacin burinta taga ƴarta mafi sowa a gareta, magana aka fara ba tareda sunga kowa ba. "Maimoon kisake shi kuma kibar kowa ya tafi Masarautar shi ga ƴarki can cikin fa'dar Daborah kin amincewa da umurnin mu shi zaisa ki rasa ƴarki baki ɗaya da komai naki." cikin kaduwa ta saki Sarki Gursu ta kama hanyar tafiya fa'da saidai kash basuda amana, tana isa ta iske ba Hunaisa a cikin fa'da hakan yasa da sauri Sarauniya Maimoon ta shiga sashen ta ba inda ta wuce sai cikin ɗakin ta, a hankali ta fara kallan kasan ɗakin jini ne ta gani duk ya ɓata wajen bakaramin firgita Sarauniya Maimoon tayi ba, har tuntuɓe takeyi dan sauri ta isa saman gadon ta ganin ƴarta shimfiɗe cikin jini yai bala'in ɗaga mata hankali saurin ɗago gimbiya Hunaisa tayi ta kwalla uwar kara mai firgitar wa tace."Hunaisa kitashi ki tabbatar mani da cewa ba mutuwa kikayi ba karki barni ina kaunar ki, Hunaisa ki karyata zatona akan abinda zuciya ta ke rawaita mani na rokeki Hunaisa."

Cikin ɗacin rai Sarauniya Maimoon ta ida maganar ta sake fashewa da malalacin kukan da ba hawaye dan azaba, koda Yarima Muntazir ya karaso cikin ɗakin jiki na ɓari ya rungumo ta a jikin shi ba irin girgizawar da basuma gimbiya Hunaisa amma ko motsi batayi shima ƙin amincewa da mutuwar ta yayi cikin kankanin lokaci waziri da Sarkin gida suka shigo cikin ɗakin jin ihun da Yarima Muntazir ya saki cirko cirko sukayi ganin yanda Sarauniya Maimoon taki yarda da mutwar ƴarta yasa suka tabbatar mata da mutuwar gimbiya Hunaisa a kiɗime ta zaro takobi tace duk wanda yakara cewa gimbiya Hunaisa ta mutu tabbas saitayi ajalin shi kowaye shi kallan kallo aka shiga yi sakanin Sarkin gida da waziri kowa nasan yin magana amman sun kasa hakan yasa ɗaya bayan ɗaya suka zare suna jimamin halin da uwar gijiyar tasu ta shiga.


a lokacin da suka fito daga sashen Sarauniya Maimoon tamkam suka iske ƴan fa'da kowa da kalar tambayar da yake masu sun kasa amsa tambayar da akaimasu shiko Yarima Haris yana tunkaro sashen mahaifiyar tashiya iske cinci rindon mutane tsaitsaye kowa yai jugum a hankali ya iso Wajen yana kallan su ɗaya bayan ɗaya ganin yanda idanun Sarkin gida suka kaɗa hakan ya tabbatar mashi ba lafiya da sauri ya karasa jiki a mace ya tambaye shi ba'asi ba yanda zaiyi haka ya zayyanewa Yarima Haris duk abinda ke faruwa, kowa hankalin shi ya gama tashi danko mata da kananan yara suka hau kuwa da kuka jin labarin mutuwar gimbiya Hunaisa a ruɗe Yarima Haris ya faɗa cikin ɗakin Sarauniya Maimoon yanda ya iske su ya tabbatar da basu cikin hayyacin su musamman Yarima Muntazir saboda abokin ta gwaicin gimbiya Hunaisa ne shiyasa shakuwar su tayi yawa tafiya yakeyi kamar kasa bata iya ɗaukar shi, yana isa ya ɗauki zanin gado ya janye mahaifiyar tasu akan ta ya rufe fuskar gimbiya Hunaisa ya koma gefe ko kuka ya kasayi dan firgita da ganin irin kisan gillar da akaima kanwar shi da kallo Sarauniya Maimoon tabi Haris gyaɗa mata kai yayi alamar dagaske mutuwa tayi ba mafarki suke ba, dan ya fahimci basu gasgata mutuwar gimbiya ba, jin yanda aka shaki wuyan shi ya dawo dashi dogon tunanin shi kallan Sarauniya Maimoon ya tsaya yi ganin kamar ta haukace ta rasa tunanin ta "karya ne Haris ƴata bata mutuba ka tabbatar mani sa haka, kace Sarrilƙus bai galaba akaina ba ka tabbatar ma mahaifiyar ka da hakan karkace ƴar uwar ka ta mutu." wasu zafafan hawaye suka fara sintiri a idon shi, ganin halin da ta shiga a hankali ya janye ta suka bar ɗakin ya kaita wani yana lallashin ta sawa yayi akai mashi kiran Jakadiyya tana isowa ta zube yabata umurnin kulawa da Sarauniya Maimoon, sannan ya koma haka aka ɗauki gawar gimbiya Hunaisa aka tafi binneta danko rabata da Yarima Muntazir bakaramin artaba akasha ba, lallai Masarautar Daborah tayi rashin gimbiya mai adalci a wancan zamanin kowa na kaunar ta.


Yarima Malik ne ya kalli Dawud sannan yace. "Ya aka kare da Sarauniya Maimoon kuma wane mataki ta ɗauka da a wajen Sarrilƙus."?

Numfasawa yayi sannan yace. "Kwarai kuwa Malik abunda nike shakkar sanar maku kenan dan akwai taɓa zuwa a cikin lamarin amman zan faɗa maku abinda nasani dan ku kiyaye sannan kusan hanyar da zakubi wajen karɓo Bahijja."


Saida aka kwashe sama da wata ɗaya sannan aka samu hayyacin Sarauniya Maimoon, bayan ta dawo cikin tunanin ta tafara haɗa jaruman Masarautar ta suka fara shirin tunkarar Masarautar Raifasu dan sun san danjin gamki yafi karfin tunanin su, saida suka ɗauki sati guda cur suna shirin yaki kafin nan suka kama hanyar tafiya Raifasu kwanan su biyu suka isa tareda turama Sarki Gursu sakon Sarauniya Maimoon, wannan karon ba karamin rikiɗa yayi ba da ganin rundunar mayakan Sarauniya Maimoon,da sauri ya tada gangamin yaki ba wata yar jejeniya data shiga tsakanin su aka kaure da yaki baji bagani dan Sarauniya Maimoon da tawwagar ta a wannan lokacin zukatan su a bushe yake dan ɗaukar fansar ran gimbiya Hunaisa da sukazo ɗauka a Masarautar Raifasu kuma sun san dole boka Sarrilƙus zai ɗauki mataki a kansu, kunsan miyafaru a wajen yakin." Huzaifa ne yace. "Aaa bamu sani ba ya Dawud." cewa yayi....




*Yar Mutan Kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*




Babi na 20



"A lokacin da suka shiga cikin Masarautar Raifasu, aka fara fafatawa tsakanin jaruman su, baji ba gani yaki yayi yaki Yarima Muntazir da Yarima Haris su sukaja tawagar jaruman Daborah, haka sukaita shiga cikin rundunar Raifasu sunai masu kisan gillah kamar ba gobe daman can Yarima Hasir barde ne na yaki gashi baida tsoro, suna cikin wannan yakin Sarki Gursu ya fahimci Yarima Hasir na neman karar mashi da Jarumai inya shiga cikin da'ga yana iya karar da rabi dan jarumta baiji bai gani danko Sarauniya Maimoon tana gefe ita da hadiman ta kura tai kura yaki yai yaki baka ganin kowa banda ƙura sai karar takubba da masu, sai sauke kan maza akeyi, ana cikin haka Yarima Hasir ya fille kan ɗan Sarki Gursu yasa mashi ya soke shi ya ɗaga shi sama yayi magana mai karar gaske, duk wanda ke wajen saida ya dakata dan firgita dajin amon maganar Yarima Hasir yana cewa. "Kai matsiyacin Sarki asararre kana ina ko zaka iya shaida wannan kan waye? Ko baku fahimci wannan kan na jahilin ɗanka bane wai shi Jarumi ko har kake tunanin zai iya haɗa kafaɗa da Yarima Hasir na sare kansa kuma na soke shi ko kana da abinyi a halin yanzun ban faɗa maku ran gimbiya Hunaisa fansa bane a garemu toh yanzun wasan zai fara." yana gama faɗa yayi wurgi da kan Yarima Busru ba inda ya tsaya sai gaban Sarki Gursu jikin shi na kyarma ya duka ya ɗauki gundun kan yana mamakin irin cin kashin da Yarima Hasir yaima ɗansa, wata gigitattar ƙara ya saki yana buga ihu duk wanda ke wajen yakin nan saida ya girgiza daga Jaruman shi harna Daborah har girgiza kasar wajen keyi ga wata irin siraci da hayaki na fita daga bakin shi da gudu yayo kan Yarima Hasir suka game baki daya wajen ya sake harkewa da kurar yaƙi sukaita fafatawa

Please Login or Register in order to submit comment