Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har tartsatsin wutar takubbai kakeji kamar aradu, itama Sarauniya Maimoon shigowa tayi ganin yaki yana kamari, ranar anyi ɗauki ba dadi jini ya koma kamar ruwa shiko Sarki Gursu ganin bazai iya cin galaba akan Yarima Hasir ga ba zobe a hannun shi balle ya kira rundunar aljanun boka Sarrilƙus ya tallafa mashi ji yayi baki ɗaya jikin shi ya fara kyarma ga gajiya duk ta addabi rayuwar shi wani wawan sara yakawo ma Yarima Hasir ya sare shi a saman kafaɗa take jini ya balle ba kyaun gani ganin haka yasa Sarauniya Maimoon tayo kan Sarki Gursu Yarima Muntazir dake ta fama da abokan gaba ya rike mahaifiyar su ya maida ta wani waje yana bata baki gudun kar wani ya illata ta shiko Yarima Hasir jini ne ya ɗibe shi dukawa yayi ƙasa kamar mai neman sikewa hakan yaba Yarima Hasir dama Sarki Gursu ya rugo da gudu zai sauke kan Yarima Hasir aiko cikin gafin nama Yarima Hasir ya sarema Sarki Gursu kafa take ya faɗi da kafa ɗaya ya sake ɗaga takobi ya fille gudar kafar kwaɗa uwar kara yayi da uban ihu mai ruɗarwa take ya ɓace bat kamar aljani da Jaruman shi sukaga abinda ya faru daman gashi ankusan karar dasu suka fara guduwa suko Jaruman Daborah suka dinga binsu da ruwan kibau waanda suka sha yan kaɗan nan sannan Sarauniya Maimoon tasa aka cinnama kayan tsafin Sarki Gursu wuta ranar saida akaima Masarautar Raifasu kaca kaca, dan ko kaɗan yakin nan baizomasu da dadi ba, saidai abinda baku sani ba koda Sarki Gursu ya ɓace yana hannun boka Sarrilƙus kusan abinda ya biyo baya."? Cikin sauri dasan jin karshen labarin yakin Yarima Malik yace. "Kai muke sauraro ina alajabin bacewar Sarki Gursu ammn nasan da sannu zamuji komai."

Jinjina kai Dawud yayi sannan yace.

"take boka Sarrilƙus ya haɗa gangamin yaki marar kyaun gani ya tunkari Masarautar Daborah suna isa cikin Masarauta kowa bai huta balle ya koma mahallin shi sukaji magana mai tada hankalin mai sauraro ana cewa. "Maimoon kina nufin kunci bulus harkina takama ke jajirtatta ce toh kisani ayau zan shafe babin ki a doran kasa baki ɗaya keda ƴaƴan ki baki ɗaya kashe Yarima Busru kamar lalata komai ne a rayuwar ku." waige waige suka shiga yi amman basu ganin komai basu gama alajabi ba suka ga kan bokan su kasa take kowa ya wartsaka da takubba sai ɗauki guda ake masu ganin abin bana wasa bane alamu sun nuna ma Sarauniya Maimoon da jinni suke faɗa kuma lallai zasu iya karar dasu yasa ta fara magana da karfi cikin fushi tace. "Kai karamin ɗan isa lusari inkai kacika Sarkin tsafi gamki ka bayyana kanka kuma kasa jaruman ka su bayyana mana kansu a fafata taya zakuyi yaki ba'a ganin ku."? a take Sarrilƙus yasa suka bayyana a sifar wasu gawurtattun mutane ba kyaun gani haka aka cigaba da fafatawa saidai basujin sara da duka dan girma da karfi tun suna da karfi har suka saduda ganin abin yana tsamari yasa Yarima Hasir shiga gidan tarihi ya ɗauko wukar Barri ya shigo filin da'ga duk wanda ya sara da wukar sai ya wargaje haka yaita kasar mutanen boka Sarrilƙus duk sara ɗaya da zaiyi sama da goma na iya bacewa shiko Sarrilƙus sai gabza ihu yakeyi kamar shi ake sara ana cikin haka aka kashe Wazirin Daborah



intakai cemaku labarin Sarauniya Maimoon da Sarrilƙus da irin artabar da sukayi haka akaita yaki har dare ba'a gama wannan artabar ba, saida aka kusan karar da jaruman Masarautar Daborah saboda yakine da akeyin shi harda aljanu danma Yarima Haris yana ɗauke da takobin Barri shine saukin Jaruman na Daborah amman abinda baku sani ba yaki da aljani ba dadi ana cikin kafta yakin da saida aka kwana ana abu ɗaya daman dukkan su ba wani addini ke akwai ba a zamanin ba abinda suka sani sai sihiri da tsafi shine adon su haka Sarrilƙus ya kashe Yarima Muntazir wata irin riki tatar tsawa Haris ya saki ganin ankashe mashi dan uwa, wata walikiyar tsafi ce ta gilma ta wajen wani uban tsalle ya doka da takobin Barri ya sari wannan walkiyar tsafin da ya gani take wajen yayi dundum banda kara da ihu ba abinda ke tashi cikin walkiyar bayan komai ya lafa Yarima Haris yayi kan Yarima Muntazir ta dugu shida Sarauniya Maimoon rige rige sukeyi da sauri ya rungumo shi ya fasa malalacin kuka mai sosa zuciya na rashin ɗan uwan shi da yayi, yana cikin kukan wani uban guguwar duhu ta tunkaro su, da sauri ya tashi ya ɗauki takobin Barri ya soketa shida wukar sukayi wanwar ba rai Sarauniya Maimoon ta ɗauki wukar akaci gaba da artaba da ita, saidai nasarar da aka samu ashe wannan walkiyar da ya sara da wuka ya yanki Sarrilƙus, sannan soka wukar da ya sake yi a karo na biyu ya soke shi a wuya wannan dalilin yasa yaƙin ya ɗan lafa na wasu lokuta, itako Sarauniya Maimoon ta kashe mutanen tsafin Sarrilƙus bila adadin tana buga masu takobi suna watsewa kamar kura daman duk na tsafi ne rashin sa'a aka halbo kibiya ta dira a kirjin Sarauniya Maimoon hakan ba karamin tsorata yan Daborah yai ba Ghali Sarkin yaki shi yaci gaba da jan ragamar bayan ɗauke Maimoon da sukayi ita da Haris dan basu kulawa koda Yarima ya farfaɗo yaga mahaifiyar shi rai hannu ga Allah bakaramin kidimewa yayi ba ya rungume ta sai kuka yakeyi ganin ba magani zai mashi ga yaki na kara kamari haka ya fita ya anshi takobi yaci gaba da yaki wutace ta kama gidan tarihi inda aka aje zoben Sarrilƙus ashe ɗauko shi aljani ɗan tsitu yayi daman shine musabbabin yakin da ake fama da shi shiki gamki yana kwance rai yakusa fita cikin fushi Yarima Haris ya ɗauki takobin Barri saida ya datse kan Sarrilƙus daman tunda ya soke shi ya koma mutun daga guguwar da yaima Yarima Haris, ihu dankuwa iri iri su suka cika wajen kafin kace tak, Sarrilƙus ya ɓace ashe tawagar shi ce suka ɗauke shi ganin kisan gilan da Yarima Haris yaima uban gidan su, marar kyaun gani, yan tsiraran Jarumai suka rage mana hakan yasa kowa ya tafi wajen Sarauniya Maimoon rai na neman kubuce mata aka hau bata kulawa ta musamman kaji takaitaccen tunkarar boka gamki Sarrilƙus da Sarauniya Maimoon tayi.


Kallan shi Yarima Malik yayi ya sauke ajiyar zuciya sannan yace. "Lokacin sallah ya gabato saidai inada tambayar da zanmaka."

Cikin gamsuwa Dawud ya kalli Malik yace "Allah yataimaki magajin gobe girman kane inajinka."


"Lokacin da aka kashe Sarrilƙus na wancan zamanin akwai abinda ya sake bullowa sannan a lokacin Sarauniya Maimoon ta mutu kuma ya aka kare da Sarki Gursu bayan rasa sassan jikin shi da yayi, sannan zoben da suka ɗauka anbar masu ko kuwa ankyale su tunda nasu bayan tafka babbar asara da zoben ya janyoma wannan Masarautar."?




"Lallai kayi tambaya mai kyau amman duba da lokacin sallah ya karato bari in takai cemaku wannan tarihi."


Cigaban labari, koda suka ɗauki boka gamki suka binne take aka naɗa sabon shugaba tsabibi ne na gaske wanda haryafi wanda ya mutu hatsabiban ci na gaske, haka aka mallaka zoben a Sarki Gursu kamar yanda kuka sani har yanzun Masarautar Raifasu bata daina aiki da tsafi ba sannan duk wanda yake mulkin Masarautar yana karkashin ikon Sarrilƙus shiyasa ake ba Sarkin zamanin zobe yana anfani dashi duk da babban zoben yana jikin boka Sarrilƙus dashi yake sarrafa komai, koda suka gama binne shi aka naɗa sabo yaci gaba da gudanar da mulki sannan suka ɗauki Gursu duk da yana da nakasa suka maida shi yacigaba da gabatar da sarauta kamar yanda suka tsara, a wajen Yarima Haris kuwa hankalin shi yai matukar tashi bayan sun binne Yarima Muntazir kusa da kabarin gimbiya Hunaisa suka dawo gida ana jinyar Sarauniya Maimoon saidai abinda baku sani ba tabbas tafara samun sauki sai Sarrilƙus ya turo aljani ya shanye mata jini tas, saida ta mutu sannan suka bayyana ma Masarautar Daborah shine ya kashe Sarauniya Maimoon a wannan karon Haris bai yunkurin ɗaukar fansa ba saboda yana son ya dawo da darajar Masarautar Daborah bayan durkushewar da tayi na rashin manyan mayaka da kuma kayan tarihi dan ma Masarautace mai kayan adana tarihi daban daban ba waje ɗaya ba, shiyasa Yarima Haris ya hakura amman yasha wahala kafin ya dangana da rashin mahaifiyar shi da yan uwan shi tundaga Yarima Jumal har zuwa Yarima Muntazir da gimbiya Hunaisa da ya rasa, hakan yasa bayan wani lokaci aka naɗa shi Sarkin Daborah bayan wata biyar komai ya kafa ya ɗauki Jaruman shi na amana guda goma duk dashi sukaje Masarautar Raifasu suka kaima Sarki Gursu hari saida sukai mashi gunduwa gunduwa sannan suka kashe Jaruman shi suka kama bayi sannan suka kone gidan tsafin Raifasu wanda suke kira da gidan tarihi a wajen su, tabbas sun masu asara, sannan ya aje wasika zuwa ga Sarrilƙus kamar haka.


_Daga Sarki Haris nasan zakayi mamakin ganin wannan sakon saidai ba abin mamaki bane duba da wanda ka taɓa Sarki Haris ke magana kuma ka kiyayi shiga hurumin Masarauta ta da jamaata inba haka ba yanzun wasan zaifara_


Haka ya dawo yacigaba da gudanar da mulki kamar yanda ya saba, duk da suna cikin shirin hari akoda yaushe, har aka ɗauki tsawan shekaru goma ba'a sake kawo ko wane hari ba a cikin Masarautar Daborah, har Sarki Haris ya samu haihuwa ƴaƴa ukku, da Maimoon sai Hunaisa inda Muntazir shine babban ɗan Sarki Haris a ranar nan Maimoon ne aka aiko mashi da sakon yaki daga Masarautar Waisu duk da yai mamaki ganin ba dasu yake arta baba, ashe Masarautun sun yi hadin guiwa dan cimma burin su akan Sarki Haris da zuriar sa musamman akan gimbiya Hunaisa da ya ɗauki son duniya ya aza mata.


Murmushi Dawud yayi yace. "Yarima kaji abinda zan iya faɗi akan labarin ko tarihin Sarki Haris na IV da tawagar shi da yanda Sarauniya Maimoon ya tayi artaba da Sarrilƙus."


"Hakane saidai wane buri suka ɗaura akan gimbiya Hunaisa"? Mikewa Dawud yayi ya dafa kafaɗar Malik sannan ya kuma cewa. "Idan mukace zamuci gaba da labarin Sarakuna da Sarauniyoyin da akayi a cikin wannan Masarautar gaskia bazai kareba, saidai wani lokacin ranka shidade." haka Yarima Malikussaif dasu Huzaifa suka mike suma suka tafi cikin al'ajabi da fargabar halin da Bahijja ke ciki.




*Yar Mutan Kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________


*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*


*NO EDITED ❌*

Babi na 21&22




_RAIFASU_




Bahijja keta aiki kamar ba gobe ga wata irin zazzaɓi daya adda beta amman a haka take tayima gimbiya Yazira wanki tun safe take abu ɗaya ta gama wannan aikin za'akaro mata wani tun tanayi cikin jin dadi harta fara sarewa uwar bayi ce tazo ta watsa ma Bahijja kayaiyaki masu yawan gaske ta hauta da masifa. "Ke Bahijja wace irin sakarar yarinya ce ke wai? tun yaushe kike abu ɗaya toh nabaki nan da minti talatin muddin baki karasa ba sai jikin ki ya gayamaki sakara kawai."

Itadai Bahijja batace komai ba haka ta dinga jibgar uban wankin ta, tana kwallah ga ƙudunta nai mata uban ciwo, Zainab ce tazo wajen ta tana kallan ta tana aiki dukawa tayi ta fara tayata da sauri Bahijja ta rike hannun tace. "Kirufaman asiri Zainab kinaso baba Uwani ta dukeni dan Allah kibari nagode." ɓata rai Zainab tayi tana cewa. "wai Bahijja sai yaushe zaki daina yin wannan addinin naki ne inkika bari akajiki za'a iya illataki fa!"



Murmushi tayi tace. "Zainab kowa yai addinin sa kinga kitafi wajen aikin ki kada baba Uwani tazo ta sameki anan wlh inajin tsoro!" shikenan amman kibari ko shanya inmaki." ba yanda Bahijja ta iya haka tabar Zainab tacigaba da yimata shanya suba ƴar fira jefi jefi jin maganar uwar bayi tayi akanta tana cewa. "Ke Bahijja kin raina mutane ko? Ke kuma Zainab uban wa yakawo ki nan ina kikabar aikin naki"? "Baba uwani nagama nawa aikin shiyasa." cikin faɗa uwani tace. "Ɓaceman dagani badab uwarki ba da sainai maki dukan tsiya daga yau idan kika ƙara taya Bahijja aiki sai jikin ki ya gayamaki maza kibani wuri." da sauri ta tafi jikin ta na ɓari, ta juyo kan Bahijja ta fara duka tana dungurin ta "dan ubanki wace irin kidahuma ceke, bance karki bari a tayaki wanki nan ba? sannan kuma banace karki bari lokacin dana ɗibar maki ya cika ba baki gama ba"?


Sai kuka Bahijja keyi tana ba Uwani hakuri amman saida tasa bulala ta gama zanar Bahijja sannan taci gaba da wankin ta, ba ita tagama wankin ba sai marece liƙis tana gamawa ta shiga cikin sashen gimbiya Yazira, ta isketa kwance asaman ƙayatattar shimfidar ta hadimai nai mata fita dukawa tayi tace. "Ranki shidade nagama wankin." a wulakance ta kalli bahijja kamar taga wani kashi ta yatsuna fuska tace. "Yiman tausan kafata." nan Bahijja taci gaba da yimata tausa sai kyakkyarwa jikin ta keyi zazzaɓi ya rufeta ringis kwalla ne suka suɓucema Bahijja sai a saman kafar gimbiya Yazira kallan tuhuma ta fara jifar Bahijja dashi ƴan cikin ta taji sun kaɗa take taji wani irin zawo ya kamata, jikin ta na ɓari tace. " tuba nike ranki shidade ban kula ba.....ai bata ida rufe bakin taba taji saukar mari mai firgutar wa, ta dafe wajen tana cigaba daba gimbiya Yazira hakuri, sake wanke ta da wani marin saida bakinta ya fashe wani irin juwa da ta dinga ɗiban Bahijja takasa ko magana, cike da kyama gimbiya Yazira ta kora Bahijja kamar mai jira haka ta fita sai jiri ke ɗibar ta a daddafe ta tafi waje tana tafiya juwace ta kadata kasa su Zainab da Indo suka tadda Bahijja kwance nan suka ɗauketa suka kaita gida.......





_DABORAH_




Shiko yarima Malik cikin dare yana kwance yana bacci sai yan juye juye yakeyi mafarki yayi, ga Bahijja nan, tana ta kuka dogarawa suna dukan ta da bulalai tana kwara amai, kamar zata fitar da ƴan cikin ta wani shirgegen mutun ya gani ya fisgota yana cewa inbata bata kanta ba zai sare kanta, dai dai nan Malim ya tashi da addua bakin shi, sai uban zufa yake ketawa cikin daren ya tashi yayi wanka sannan ya ɗauro alwalla yayi nafila da addu'oi sannan ya koma ya kwanta yana tunanin halin da Bahijja ke ciki yasakama ranshi zuwa gobe zaije ya nemo Bahijja duk inda ta shiga a cikin kasar Gambia.....



Hakadai Malik ya kwanta rabi bacci har asuba tayi koda ya tafi masallaci bashi ya dawo sashen shiba sai wajen goma wanka kawai ya sake kaya sannan ya karya yatafi wajen Sarauniya Zulaiƙa, koda ya shiga a falo ya sameta itada Jakadiya gaishe shi hadiman ta sukayi samun wuri yayi ya zauna nan Jakadiya ta sallami hadimai aka barshi da Sarauniya Zulaiƙa, kallan shi tayi tsaf take tagane ɗan nata yana cikin damuwa, a hankali cikin disashshar murya ya gaida ta, ta kada daina kallan ɗan nata cikin kulawa tace. "Malik meke damunka."? Shima kallam mahaifiyar tashi yayi ya gilgiza mata kai alamar bakomai, cikin rashin yadda Sarauniya Zulaiƙa tace. "Karya batai maka kyau Malikussaif kafaɗaman ni mahaifiyar kace."?


"Ummu ina cikin damuwa kullin da Bahijja nike kwana ina tashi ina shakkar halin da zata tsinci kanta a wajen miyagun mutanen nan.! " a sheƙe ta kara kalan shi dan ita harta fara mantawa da batun wata Bahijja can, ɗan karamin tsoki tayi wanda saida mmakin hakan ya bayyana a saman fuskar Malik, sannan tace. "Kawani damu da lamarin Bahijja ince ita baiwa ce ko? Mene a cikin dan an sadaukar da rayuwar baiwa akan uban gidan ta, ai naɗauka dakai da kaya duk malakar wuya ne kaga dakabar maganar Bahijjan nan!!!"



Wani irin mummunan faɗuwar gaba ta riski Malik yana mamakin kalar butulci irin na mahaifiyar shi, ko kuma yace wane irin tsana taima Bahijja a duniya, a zahiri sai ya riko hannun ga yace., "Ummu kidaina faɗan haka kiga yanda yarinyar nan iyayenta suka sadaukar da ita akaina!" "yimin shiru Malik saime dan an sadaukar da baiwa akanka ince uwarta ma ana iya sadaukar wa bare ƴar tatsitsiyar baiwar yarinyar nan, dan haka ka manta da rayuwar ta."


Wani irin ciwon kai ya dirar mashi a take bakin shi na rawa yafara magana. "Ummu dan Allah kibari inje in ɗauko Bahijja ina tausayin halin da zata tsinci kanta, kuma kinga iyayen ta zasu damu kodan addinin tama kimin lamani!" fusgi hannun ta tayi "sai me kaga ka fidda aranka ni Zulaiƙa banajin zan iya bari kaje ɗauko wata ƙasƙantattar baiwa a matsayin na magajin Masarautata dan haka daga nan kabar wannan sakaran zancen Bahijja me da zaka damu kanka!"


Dai dai nan Uwar bayi Binta ta ɗauko tiredin abinci zata kawoma Sarauniya Zulaiƙa jin abinda take cawa yasa jikin Binta yahau bari har ta kusa da ɓarar da abinci wani matsiyacin kallo Sarauniya Zulaiƙa ta watsa mata jiki a mace tazo ta aje abinci sannan ta gaida Sarauniya Zulaiƙa da yarima Malik, fuska sake ya amsa yana gaida ta, kallan da Sarauniya taimata kaɗai yasa ta gane nufin ta ɗaukar flat tayi ta zuba mata abincin sannan zata zubama Malik yace mata karta samashi a koshe yake, sake kallan ta Sarauniya Zulaiƙa tayi hakan yasa ta zubo ruwa a kofi ta mikoma Sarauniya Zulaiƙa, ganin uwar hararar data wurgamata yasa kofin hannun ta ya suɓuce mata ya wanke ma Sarauniya Zulaiƙa jiki ba Binta hatta Malik saida yaji gaban shi ya faɗi, ahi Binta tafara tana kwallah amman ko ajikin Zulaiƙa tayi kamar ta yafe mafa tacigaba da yima Malik gargaɗi akan Bahijja ko nauyin Binta bataji, shiko yakasa ko motsi dan kunya data addabi Malik, saida tabari Binta ta kara sakankance wa ta waketa da mari lafiyayyu har guda ukku, wani uban kara ta saki tana bata hakuri sai kyarma takeyi tace. "Allah yahuci zuciyar uwar gijiya ta ban kulaba na jikaki kimin aikin rai Binta na tuba Allah yataimakeki!" ɗaga mata hannu Sarauniya Zulaiƙa tayi cikin gadara tace. "Wato ni zakiyima hauka hankalin ki yana ina zaki zubamani ruwa, jikin kine zai gaya maki dani kike magana!"


Ganin yanda ran mahaifiyar shi ya ɓaci tana wulakanta mutanen da sukayi masu halacci dan kawai suna bayi akan wata hujja tata marar usuli, yasa Yarima Malik yace. "Allah yahuci ran Sarauniya kiyimata aikin rai taba kula ba hakan bazata kuma faruwa." kallan shi kawai tayi sannan tabata umurnin kwashe kwanukan abincin ta tafi, itako Sarauniya Zulaiƙa sai huci take tana kara tsanar Binta da ƴarta a cikin ranta, haka Yarima Malik yagama bata hakuri sannan yaimata sallama ranshi ba daɗi ya tafi sashen shi ya aika wata baiwar shi taima shi kiran Huzaifa.......



Koda Aliya taje wajen Huzaifa iske shi tayi zaune dasu Lurwan a wajen dawakai cikin wata bagala suna fira duƙawa tayi tagaida su, sannan ta sanarma Huzaifa kiran Malik, da sauri ya mike yasan ba lafiya tunda har yaimashi aike, kusan tare suka isa, shiya shiga cikin bedroom din Malik ita kuma taci gaba da ƴan aikace aikacen ta, iske shi yai kwance yana kalan silin alamar mai tunni yakai wajen minti biyar baisan da shigowar Huzaifa ba jin antaɓa shi yadawo dashi a cikin tunanin daya ninkaya, zama yayi gefen abokin nashi cikeda tambayoyi masu tarin yawa yake kalan Malik shima kallan shi yakeyi bakin shi yaimashi nauyi ga wani tuƙuƙi ya tokare mashi ƙahon zuciya Huzaifa yai karfin halin jefoma Malik tambayoyi. "Allah yataimaki yariman Daborah bansaba ganin wannan yalwatattar kyakyawar fuskar taka a cikin damuwa ba irin wannan abokina faɗaman mike faruwa duk jikina yai sanyi mike damunka"?


Take idanun Malik sun canza launi ya kara ɗaura ma Huzaifa su, saida yasa ya gilgiza sake jefomashi tambayar Huzaifa yayi, cikin dakewa Yarima Malik yace. "Mezakace da mutanen da akaima halacci suka sakanta da saɓanin hakan"? ɗan shiru Huzaifa yayi na dakiƙa yana nazartar abokin nashi, ya tabbata koma mene da mahaifiyar shi yake yasan inba ita zata saka Malik a cikin yanayi ba ba wanda ya isa ya jefa Malik cikin wannan yanayin kaf Masarautar Daborah, "Allah yataimaki magajin gobe zan iya saka wannan mutanen a layin masu ajizanci na ɗan Adam."


Wani wawan kallo Malik ya jefama Huzaifa marar kyaun gani sannan yace. "A iya nan kawai zaka saka su."? "Kwarai kuwa abokina sannan zan masi uzuri watakil wani lokacin in zukatan mutanen ya huci suyi halacci ga waanda sukai masu kwatan kwacin hakan." mikewa Malik yayi ya goya hannayen shi a bayan shi yana zagaye ɗakin yakai minti goma yana abu ɗaya sannan ya dafa kafaɗar Huzaifa yace. "Lallai Huzaifa sai yanzun nagane banbancin ka da Yazid a matsayin ka wanda ya tashi a gidan sarauta zaka faɗa mani haka!" bakaramin mamki Huzaifa yaiba da Malik ke wannan maganar, "ban fahimce kaba abokina koda Yazid iyakar abinda zai faɗa maka kenan." ɗaga mashi hannu Malik yayi dan harya gaji da magana, shiko Huzaifa baiyi mamaki sanin halin abokin nashi yanda magana ke mashi wahala aiyai kokarima a wannan lokacin, duk da yana san yasan dalilin dayasa Malik ke wannan tambayoyin, haɗa ido sukayi da Malik, yasan cewa akwai tarin tambayoyi da Huzaifa kesan yimashi dan yaga hakan kwance a saman fuskar shi, "Ummu ta tsani mahaifiyar Bahijja kasan tanani zuwa ɗauko Bahijja bayan tace baiwa ce marar galihu abin wulakantar wa, Huzaifa sai yaushe zan nunama mahaifiya ta illar wulakanta ɗan Adam sai yaushe zatasan darajar bayi shin ita ba uwa bace sai yaushe Ummu zata _gane cewa *BAYIMA* *'ƳA'ƳA'NE*_ kamar kowa"?


Ganin halin da Yarima Malik ke ciki saida yasa Huzaifa ya tausaya mashi badan yasan halin abokin nashi ba nasan taimakon bayi da talakawa dayace son Bahijja yakeyi amman bai fatan hakan ta kasance, dan yasan Malik zai fuskanci kalubale wajen mahaifiyar shi da sauran ƴan fa'da musamman wazirin Daborah wato mahaifin Huzaifa, amman a zahiri numfasawa yayi ya tausasa murya yace. "Kayi hakuri Malik zanma mahaifina magana kodan kusancin dake tsakanin shi da Ummu, nasan zai shawo kan wannan matsalar saidai ya kamata aima Bahijja adalci kodan yanda iyayen ta suka sadaukar da ita akan ceto rayuwar ka, ya kamata Sarauniya takawo karsheb tsanar da tayima iyayen bayi kodan haka, sannan yakamata agane sun zama bayin amana bakamar ba baya ba."
"Abinda nikeso insanar da mahaifiya ta kenan Huzaifa saidai kaje ka nemoma mu mafita bansan mahaifina yaji wannan maganar duk da shima sona ya rufe mashi ido ya manta da rayuwar Bahijja!"

Sake dafa kafaɗar Malik yayi sannan yace. "Allah yakara girma karka saka damuwa a ranka zamu amso Bahijja kodan addinin ta da darajar ta, kuma kasan bamu da ilimi ko dubarar tarar Sarrilƙus kuma kasan hatsarin sa!" wani shu'umin murmushi ya saki duk da baiyi mamakn jin haka daga Huzaifa ba sai ya samu kanshi da bashi amsa" har yanzun na fahimci baka san matsayin Bahijja a cikin zuciya taba ko Huzaifa? Inasan zan samu hutu inka fita kasanar ma Aliya kartabari kowa ya sake zuwa ganina ace ina bacci sai anjima abokina sannan kayi kokarin sama mana mafita." gyaɗa mashi kai kawai yayi ya kama hanyar barin ɗakin harya kama handle din kofa zai fita ya tsinkayi maganar Malik a kunnuwan sa. "Ka kwatanta tarayyar ko dangantakar dake tsakanin da gimbiya ka dan tata da Bahijja akaina, saina jika." murmushi Huzaifa yayi ma Malik sannan ya rufo mashi kofa ya fita yana ba Aliya sakon Yarima Malik ya wuce wajen mahaifin shi..


_Masarautar Waisu_

Yarima Haishir ne zaune awajen mahaifin shi suna magana akan harkar kasuwancin da zasu kulla da Masarautar Ƙaisu. "Haishir inasan kasamu lokaci kaida hadiman ka kukai ziyara wajen Sarki Sibbur kaji yanda harkar kasuwancin mu zaya kasance, sannan inasan inkadawo zamukai ma Sarki Baidulƙais ziyara."


Kallan mamaki Yarima Haishir yaima mahaifin nashi yai mamakin jin yace zasu kaima Sarkin Raifasu ziyara bayan yasan kudurin mahaifin shi akan Masarautar Raifasu....shiko Sarki Lahazu yanda yaga ɗan nashi yai shiru kamar mai nazari yasan yana da tambayoyin da yake son yi mashi hakan yasa yace. "Kana mamakin zamuje wajen Baidulƙais

Please Login or Register in order to submit comment