Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kunan nan hardakai aka bada."? Mamaki bayyane a fuskar Tasi'u yace. "Eh Ashir munanan muna fama da ƙangin bauta da wahala." "ina sauran mutanen mu."? Numfasawa yayi sannan yace. "Sabi'u Hashim da Kudur duk an kashe su da mashi a gaban kowa aka kashe su." cikin firgici yace. "Kisa misukayi har haka."? "Hmmm yunkurin guduwa sukayi shine akai masu wannan ukubar." "yanzun dai saura ku bakwai ina sauran suke."? "Kaga Ashir ni kaina ina iya kwana ukku banga ɗan uwana ba a cikin su, ba'asan aga muna huɗɗa da junanmu shiyasa ma kaga muna nisantar junan mu, yau kwana ukku daga Hudu sun gaisa da Mahadu ranar dukan da Sarkin horo yaimasu banyi zatan zasu rayuba, kaga nima nan da kake ganina atareda kai zan iya rasa raina bari intafi bakin aiki na." rike shi Ashir yayi yace. "Kai tsaya akwai aikin da Yarima Malik ya aikoni anan Masarautar bari intambayeka wani abu." cikin mamaki Tasi'u yace. "Minene wane aiki ne."? "Ina Bahijja tana cikin Masarautar Raifasu kuwa."? "Kwarai kuwa Bahijja ta nan cikin taskar bayi sannan itace hadimar Sarki Baidulƙais dan haka ni kaina ganin Bahijja wahala yake mani." murmushi Ashir yayi sannan yace. "Kana nufin Bahijja tana Masarautar nan kenan."
"Shiyasa na tabbatar maka da hakan saidai banda hanyar da zaka iya ganin ta, sannan kasani duk cikin babu wanda yakai Bahijja fuskantar kalubale da wahala a cikin wannan Masarauta, acewar wasu daga cikin bayi wai Baidulƙais son Bahijja yakeyi yana son cika burin shi, wannan dalilin yasa gimbiya Yazira take takura Bahijja da duk wasu mabiyanta kaji kaɗan daga cikin abinda nasani da Bahijja dan raban da inga Bahijja nakai sati biyu koda na ganta ba abinda zan iya yimata saidai fatan alkhairy."

Jikin Ashir ba karamin mutuwa yaiba yace. "Tasi'u duk da ka tabbatar mani cewa Bahijja na nan saidai kasani bazan iya komawa uban gidana ahaka ba batareda naga Bahijja ido da ido ba, dan haka kasani zan zauna zuwa gobe ne." "shikenan zan baka masauki amman kasani ni dakai muna cikin haɗari saidai akan aikin Yarima Malik zan iya bada raina kyauta adalin Yarima." "naji dadi insha Allah ba abinda zai samemu yanzun katafi wajen aikinka zuwa anjima munyi magana."
"A ina zaka ganni." "nan zamu haɗu wajen magariba." gyaɗa mashi kai alamar toh haka Tasi'u yatafi Ashir najin tausan su a ranshi duk da yasan ko Daborah bayi bawani jin dadi sukeyi ba ammn in Masarautar ku ba laifi kanada ƴanci ba kamar inda ba Masarautar kuba da haka ya shige cikin bayi yana cigaba da nazartar su.


A wajen Bahijja kuwa kamar kullin yauma tagama aikin ta baki ɗaya hakan yasa ta fito bayan gida itada Indo suna firar su, kasancewar yau Sarki Baidulƙais tunda yagama karin kumallo ya tafi fa'da kuma ya shaidama Jakadiya bazai dawoba sai faɗuwar rana shiyasa yau Bahijja ketajin dadi, sauran bayi ko masuyimata hassada sai haushin ta sukeji ga ba damar su duketa dan duk labari ya karaɗe taskar bayi da kewayen ta Bahijja ta mari Labuda hakan yasa kowa ya shiga taitayin shi akan hayema Bahijja shiyasa suka kara yarda Baidulƙais son Bahijja yakeyi, suna cikin firarsu Indo tacema Bahijja. "Kawata niko nazo maki da wata gulma da nikeji anata yi a cikin taskar bayi." cikeda mamaki Bahijja tace. "Wane labari ne wannan kinsan ni ban cika son ƴan tsugunne tsugunne ba musamman idan abu bai shafeni ba." cikin ɓacin rai Indo tace. "Ke matsalata dake gwalisa tunda nike dake na taɓa kawo maki zancen wasu."? "Aaa Indo karki ɗauka cin zarafi ne da ankama mutun yana gulmar wasu musamman ta gidan Sarauta yanzin an kama mutun aci zarafin sa ko kuma akasheka abanza ko duka kingan ninan shiyasa ban saka kaina cikin matsala da damuwa, amman inajinki minene." "shikenan kinsan a kewaye Masarautar nan ana cewa Sarki Baidulƙais yana sonki shiyasa yasa kika mari Labuda dan kawai taimaki faɗa." da sauri Bahijja ta ɗaura dara daran idanuwan masu ɗaukar hankali akan Indo tace. "Kinga Indo zantambayeki." "inajinki." "minene matsayin ki a cikin wannan Masarautar."?
Kallan kin rainani Indo taima Bahijja sannan tace. "Bawai kuma ƴar matemakiyr Uwar bayi." murmushi Bahijja tayi sannan tace. "Toh tsaya kiji idan baki daina ɗaukar jita jitaba wlh ko Sarkin bayi ya haifeki zaki iya rasa ranki, dan haka ni Baidulƙais baitaɓa yiman wata magana da ta danganci so ba, duk da ni bansan ma mi ake kira da sonba ammn kamar yanda kika faɗa daga lamari ne mai girma dan haka ni Bahijja na karyata wannan zancen banza ne."
"Amman Bahijja baikamata ace kina boye abinda kika saniba." cikin mamaki Bahijja ke kallan Indo tana nazari kamar ya so ko abinda Baba ke fadamani kar in saki jikina dashi shine son, toh inko har hakane tabbas indai ya nunamani wannan son zan iya mutuwa kenan tabb aiko zan iya guduwa bari anjima intabayi Baba asalin Masarautar mu bazan iya zamaba in mutu nabani Allah dai yasa wannan mugun mutumin ba son zai nuna manba da nashiga ukku! tana cikin wannan tunani taji Indo ta taɓata a firgice ta kalleta tace. "Kinga Indo tashi mukoma bakin aikin mu."? "tayaya bayan baki tabbatar mani da zargin da ake maki ba." dayake Indo ta girmi Bahijja nesa bakusa ba zatakai shekara sha takwas itako Bahijja bata wuce shekara sha ukku ba, shiyasa tafita sanin abubuwa, cewa tayi. "Bansan komai ba bansan kina karyatani nidai natafi wajen aikina sai anjima." haka tabar Indo cikeda mamki aranta......




Shiko Ashir koda ya dawo wajen wannan bishiyar zama yayi yana jiran isowar Tasi'u baijima ba saiga shi ya iso, tashi yayi suka dunguma cikin masaukin su koda suka isa zama sukayi ga wata irin yunwa Ashir naji amman ba abinda zasu samu suci kallan Tasi'u yayi yaga duk ya galabaita ga wahala kuma ga yunwa tashi Ashir yayi ya duba yaga kudin da Yarima Malik yaba shi dan yayi guzuri ya fiddo ya kalli Tasi'u yace. "Kaga inazamu samu abinci kaima yunwa kakeji kafin sauran yan uwa su dawo suma nasan da yunwa zasu dawo." kalan shi Tasi'u yayi cikin jimami yace. "Kaiko dai Ashir kana bani mamaki da dariya wayagaya maka munada ƴanci da zamuje kasuwa musayi abinci? ai sai ainahin ƴan wannan Masarautar sukeda wannan damar suma a sati sau ukku suke cin kasuwa muko bamu da wannan gatan karma kasa mu shiga cikin hali." a kiɗime Ashir yace. "Wai baku da damar da zakuyi komai kamar sauran bayin Masarautar Raifasu? aina ɗauka bawa bawane ba wanda yafi wani kuma sunan su ɗaya." "Aaa kayi kuskure sunan akwai nuna kabilanci, Sarauniya Zulaiƙa itace ta maida bawa bawane a wajen ta kuma ba'a bakin komai yake ba, shi Sarki Baidulƙais bawa ba ɗaya bane, sannan a wajen wahala yafi tausan nashi bayin saboda basuyin aikin wahalar damu keyi kuma akwai ranaku ukku a sati daya ware masu ta ƴanci bayi dan su sama damar wanke suturar su da kayan bukatu mufa? Kaga ko anan kasan yafi Sarauniyar mu, kishin bayin sa duk da baimasu da wasa yana zalintar su, saidai akwai lokacin da suke hutawa kuma a ranakun da rana kowa ke tashi aiki dan yin tasu bukatar, saidai mu bamu tashi sai marece saboda tsabar kiyayar da sukema Masarautar Daborah da nuna kabilanci." take jikin Ashir yakara sanyi dafa kafaɗar Tasi'u yayi sannan yace. "Gaskia kam kuna cikin hali duk da ko a Masarautar Daborah kuke ba abinda da zai sauya saidai Sarauniya Zulaiƙa bata yarda bawan ta ya kwana bai ciba kuma tana bada lokacin da kowa zai samu ya shirya, amman a sati sau ɗaya sabanin nan da bayi suka fimu ƴanci dan dai nuna kabilanci, yanzun ina sauran bayin mu suke."?
"Hmmm Ashir kenan basu gama aikiba har yanzun." "kamar yaaah....yanda Ashir yaja maganar shiya tabbatarma Tasi'u maganar taba Ashir mamaki da tsoro ƴar dariya yayi marar sauti dan baida karfin jikin da zaiyi mai sauti yace. "Eh suna aikin bauta basu dawoba nima dan nagama sannan uban gidan nawa yana da saukin kai ba laifi." "ikon Allah yanzun isha'i tayi so ake suyi aikin tsakar dare komai ake nufi? ko sallah ba wanda yayi a cikin hattani." kallan bakada aikinyi Tasi'u yaima Ashir yace. "Kaga malam sallah da kake gani ba kullin mutun zai samu yayi taba idan har aka kama mutun nayi kashe shi zasuyi shiyasa sai dare ya raba muke tashi muyi dukan su wani bima daga zaune zakayi basaja kayi kamar mai gyangyaɗi dan haka kaima ka boye kanka kayi sallar ka nan wajen."
"Naji alwalla fa." "idan aka hanamu dibar ruwa mukanyi taimama muyita." ikon Allah cewar Ashir sannan yace. "Idan kuka bukaci shan ruwa fa."? "Hakuri maganin zaman duniya saidai akwi wata makobciyar ku nan Saude wanibi itake sammana ruwa, dan na fahimci tanada tausayi, sannan wasu lokutan idn Allah yasa zamu hadu da Bahijja sai in Allah yasa taje gidan ta gaskia tanaima Bahijja mutunci."



Cikin jin dadi, Ashir yace. "Yanzun ka sanar dani labari mai dadin sauraro, tabbas yanzun nasan zamu hadu da Bahijja a cikin Masarautar Raifasu, kaga inajin kishin ruwa kuma naga dakin naku ba ruwa yaza'ayi."? "Eh wannan mai sauki ne zamu iya zuwa rafi can gefen lambu amman cikin Masarauta ne idan munci sa'a abarmu ku dibi ruwan." daukar batiki sukayi zasu fita saiga su Laminu sun shigo a wahalacce kallan kallo sukadinga yima Ashir duk mamaki yagama kamasu kamar a mafarki haka suke kallan Ashir rungume shi sukayi kowa fuskar shi cikeda mamaki ganin kallan da suke mashi yasa Ashir cewa. "Kuke mani kallan tuhuma yanzun dai ku huta bari muje mudawo ɗebo ruwa anjima mungaisa." gyaɗa masu kai sukayi sannan suka fita duk da dare yayi amman kana gane mutane, haka suka fita har suka isa wajen ɗibar ruwa suka ɗebo kan hanyar dawowa ne suka haɗu da Zainab itada Indo suma sun ɗebo ruwa a hanya suna labarin Bahijja Indo ke cewa. "Zainab nifa gani nikeyi akwai abinda Bahijja ke boye mana akan Sarki Baidulƙais nidai ban yarda da hidimar da take mashi ba." ɗan karamin tsaki Zainab taja sannan tace. "Kinga Indo kirabu da zancen Bahijja daman ai kowa yasan Sarki son Bahijja yakeyi." ji sukayi ance ƴan mata,har kundawo ɗebo ruwan kenan, sai ina zuwa har haka."? A daburce Zainab ta kalli Indo sukace. "Eh mundawo." ji sukayi ance. "Ina Bahijja nagan ku, ku biyu." duk Indo tasha jinin jikin ta Zainab nason taga mai masu wannan tambayar amman sun kasa ganin fuskar shi, cewa sukayi. "tana gidan Baba Saude can mukaga ta shiga." Tasi'u ne yace. "Hakane daman sakon Jakadiya zamu bata amman da safe munbata."duk yanda Zainab taso taga abinda akeson aba Bahijja ya gagareta karshe ma suka neme su ko sama ko kasa basu gansu ba, sai abun ya zamar masu kamar a mafarki, suko su Ashir suna dawowa sukayi salla sannan suka dinga fira kowa dandai yace masu zuwa jibi zai koma gida da haka kowa ya kwanta a gajiye, itako Bahijja tana gama sallah tafara fira da Baba Saude rabi na iyayenta ne cema Saude tayi. "Baba Saude niko inasan inkoma wajen iyeyena da yaya Malik dan har ya fara shige mani, saida yanada mutunci sosai abin damuwar ko nace zantafi bansan inda zan samu garin muba, tunda na manta sunan shi." itako Saude murmushi tayi duk da ba addinin su ɗaya da Bahijja amman tana son ɗabi'un ta, "haba ƴata dakin bar wannan zancen ni kaina gashi bansan ko ina aka sameki ba da nafada maki amman daga yau karki kara yin wannan maganar a gaban mutane za'a iya cutar dake." cikin gamsuwa Bahijja tace toh, da haka sukayi bacci.



Washe gari da safe Bahijja ce tagama shiri zata tafi wajen aikin ta tunda gari ya waye Ashir ya sake ɓadda kama yana kallan mai shige da fice itako Bahijja sallama taima Saude ta fito tacigaba da tafiya baki ɗaya hankalin ta nakan hanyar ta, jitayi Zainab ta kwalla mata kira, tsyawa tayi tajirata tana isowa suka tafi, tunda kunna Ashir suka jiyo kiran da akaima Bahijja ya fito waje ko zaigan ta yaga babu kowa hanya yabi yana dubawa can ya hangi wulgin ƴan mata biyu sadda zaikai wajen su har sun shige wajen aikin su da alama gidan Sarauta ne suka shiga, haka ya jiyo zai koma cikin taskar bayi, jiyayi ance kai ɗan Saurayi daga ina......




*Ƴar Mutan Kankia ce❣️*


Share
Comment
And
Vote

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



Babi na 31&32


Cikin sarkewar murya Ashir yace. "Am daman daman nazo...."kaga anshi wannan kwandon ka kaima Mai Martaba yanzun nan." baijira abinda zai ceba, Sarkin bayi ya juya yatafi wata irin ajiyar Zuciya ta sauke jiki sanyaye ya shige cikin sashen Sarki Baidulƙais yana shiga ya taddashi zaune saman wata irin kayatacciyar shimfiɗa, dukawa yayi yakai gaisuwa wajen Sarki Baidulƙais, kallan shi yayi cikeda kulawa sannan yace. "Bawa waya aikoka da wannan kwandon."?
Shiru Ashir yayi yakasa magana yarasa mizaicema Sarki Baidulƙais dan baisan sunan wanda yaba shi sako ba, zaiyi magana kenan sukaji ance. "Ranka shidade nagama haɗa ruwan." da sauri Ashir ya ɗago idanun shi ya azasu a fuskar Bahijja wani mummunan faɗuwar aba yaji, ga wani irin girma da kyau taimashi ganin irin kallan da yaga Baidulƙais naima Bahijja shiyasa yace. "Ranka shidade...."ɗaga mashi hannu yayi yace. "Kije madafa kice ahada mani farfesun ƴanciki ki tahomani dashi." cikin sarkewa murya tace. "Angama Ranka shidade gurfanai ya taimakeka." mikewa tayi zata tafi karab suka haɗa ido da Ashir hakanan taji faduwar gaba ya kamata, sake kallan shi tayi shima kallan nata yakeyi ya sakar mata da murmushi, tafiya tayi tana mamakin wannan wane kalar bawane itada bata taɓa ganin shi ba a cikin Masarautar Raifasu koda yake ai bayin ne dayawa daman ba kowa zaka saniba da wannan zancen ta tunkari madafa dan cika umurnin Sarki.

Shiko Baidulƙais sake kallan Ashir yayi yace. "Bawa wane aiki kakeyi."? Jiyayi gaban shi ya faɗi karfin hali yayi yace. "Ranka shidade ina kula da wajen dawakai ne da basu ruwa." ya ida maganar yana sosa keya duk ya takure, cikeda mamaki yace. "Daman an sauya Gunzar daga kula da dawakai bansani ba? Nayi mamaki koda yake kilan yanzun tsufa yafara ka mashi, ko kaima ɗansa ne." a daburce yace "eh aaa daman ba...."ya kake magana a daburce kamarya eh aa." buɗa bakin Ashir keda wuya saiga Jakadiya ta shigo itama zubewa tayi takwashi gaisuwa sannan tace. "Ranka shidade Sarkin dawakai Gunzar yace insanr dakai ana bukatar sauya wasu dawakan asamu matasa." cikin mamki Sarki Baidulƙais ya kalli Ashir yace. "Amman yanzun wannan bawn ke faɗaman cewa Gunzar ya aje aiki, kuma saigaki da wannan sakon ya abin yake Jamra."?
Kallan shi Jakadiya tayi tasan bata taɓa ganin wannan fuskar ba kuma ba laifi tasan rabi da kwatan bayin Masarautar Raifasu ganjn yanda Ashir ya raina gaskiar shi hakan yasa take Jakadiya tagane akwai abinda ke tafe dashi saidai bata nuna hakan bka a fuskar taba saboda batasan tai sanadiyar shigar wani a matsalata a zahiri sai tace. "Ranka shidade kasan tsufa na Gunzar inaga ya shafa'a kuma kasan sai anayi ana kara daura yara a hanya, shiyasa kaga hakan." shiko Ashir ka shine kawai baiba dan tsoro da yagama cika mashi ciki harya hango ankashe shi ganin abinda Jakadiya tace yai saurin cewa. "Kwarai kuwa ranki shidade hakane kam, bari inje bakin aikina kahuta lfy uban gidana." dakatar dashi Sarki Baidulƙais yayi ta hanyar daga mashi hannu sannan yace. "Inkaje kacema Gunzar nabada izinin hakan amman ya nemi Sarkin yaki, daga nan kukara kulawa da dakai sosai yanda yakamata, saidai minene sunan bawan."? Jiyayi kamar ya ruga ya rasa mizaicema Sarki Baidulƙais dabara ta faɗo mashi yace. "Tarib." gilgiza kai Sarki Baidulƙais yayi alamun gamsuwa hakanan yaji Ashir ya kwanta mashi a zuciya aranshi ko yace ya kamata kazoma mai kulawa da al'amurana dan dagani zakayi Jarumta amman a zahiri bashi izinin tafiya yayi, sannan ya kalli Jakadiya yace. "Jamra daman kinsan wannan bawan."? Gilgiza kai tayi tace. "Gurfanai ya taimakeka bansan wannan bawan ba yau nafara ganin shi."
"Shikenan idan kin fita kibiya wajen Gunzar kice inasan ganin shi." da toh Jakadiya ta amsa sannan ta tafi madafa dan ganin wainar da ake toyawa.

Shiko Ashir koda yafita bakaramin ajiyar Zuciya yayi ba dan ya bala'in tsorata tunowa yayi da abinda Yarima Malik ya cemashi kada yabari kowa ya ganshi a cikin Masarautar Raifasu kawai ya dubo in Bahijja na nan, amman gashi har magana da Sarki Baidulƙais yayi addu'a yafara Allah yasa kada ya shiga damuwa ba inda ya koma sai cikin taskar bayi yaje masaukin su Tasi'u ya kwanta ganin kwanciyar bazata yimashi yasa shi fitowa ya shiga gidan Saude isketa yayi kwance da alama bacci takeyi tunani yayi mizaice mata da yazo wajen ta hakan yasa ya fita yana fitowa suka haɗe da juna ganin zai wuce ta yasa tace. "Kai baka ganin mutane ne da baka bada hakuri." wani irin mugun kallo ya watsa mata nakinyi kadan zaiyi magana yaga wasu bayi zasu wuce sun gaida Uwani cikin girmamawa hakan ya tabbatar ma Ashir cewa wannan tanada wani matsayin na daban waya zuciyar cemashi tayi kodai itace Uwar bayin su dagani ma kodan kayan dake jikin tama, hakuri yabata zaitafi tace. "Kai Saurayi daga ina."? "Nan nike Baba inaga kilan baki kuladani bane shiyasa." yakarasa maganar cikin garaje dan ya kosa yabar wajen, zatayi magana ya tafi duk mamaki ya gama kama Uwani tana mamakin waya haife wannan bawan mai nagarta inki har siyoshi akayi ina masaukin shi da bata taɓa ganin shi ba sai yau, da wannan tunanin ta shige gidan Saude tana ta bacci tadata Uwar bayi tayi....



Shiko Ashir ya ɗaukarma ranshi gobe zaibar Masarautar dan yaganema kanshi komai da yakeso ya gani, itako Bahijja kamar yanda Sarki Baidulƙais ya umurce haka ta kawo mashi farfesun yan ciki da kanta ta bashi sannan yace ta cinye sauran haka takoma gefe taci abincin ta sannan ta ajema Jakadiya itama taci ta rage sauran ta juye a leda da niyar kaima Baba Saude dan tasan da wahala idan yau ta karya, koda marece yayi tashi tayi taima Sarki bankwana ta koma taskar bayi itako Jakadiya gidanta ta wuce tana isa ta iske Uwani a wajen Saude gaidasu tayi sannan ta zauna hakan yasa Uwani ta aiki Bahijja wajen gimbiya Yazira duk yanda taso ta faɗamata abinda Sarki Baidulƙais yace amman Uwani taki ta saurari Bahijja, haka ta tafi da wasu kaya a hannun ta, haka ta tafi har bakin kofar shiga sashen gimbiya Yazira saidai takasa shiga koda ta shiga ba kowa sai bayi ƴan kaɗan ta iske dubawa tayi falo batanan hakan yasa ta tambayi wata baiwa tace tana aikin dakin ta, komawa tayi gefe shiru ba gimbiya Yazira hakan yasa ta shiga gudun kada Baidulƙais ya shigo ya sameta a cikin sashen gimbiya Yazira, tana tura kofa ita kuma gimbiya Yazira ba shirin fitowa bangeje juna sukayi turaren dake hannun gimbiya Yazira ya fashe fadi kasa ya fashe ita kuma Bahijja duk kayan da Uwani tabata sun ɓaci tsoro yakara kama Bahijja batasan tace, inalillahi wa'inna ilahir raji'un ba, wani mugun kallo gimbiya Yazira ta watsa ma Bahijja take ta kifa mata wani marayan mari tasake kifa mata wani har sau ukku saida Bahijja ta faɗi wata baiwa tasa takira mata Sarkin bulala haka tasa akaita jibgar Bahijja tun tana kuka harta kasa saida yagama gibgarta sannan tasa yakaita taskar bayi ya ɗaure ta jikin bishiya yaci gaba da dukanta, sannan tace zagar masu gurfanai tayi koda yaji haka bai ko ɗaga kafa ba wajen dukan Bahijja ba haka yakaita taskar bayi ya ɗaureta da bishiyar kusa da gidan Saude yaita duka Tasi'u ne yadawo wajen aikin shi ya tadda wannan aika aika da sauri ya shige wajen ya shaidama su Ashir kafin kace me wajen ya cika da bayi itako Bahijja harta canza kamanni dan duka ga azaba tana sha, duk wanda Sarkin bulala yafada mashi abinda Bahijja ta aikata sai ace daman akasheta itako sai kalmar inalillahi wa'inna ilahir raji'un take ambata da karfin gaske koda su Ashir suka fito baisan yaima Bahijja kwalla ba dan tausayi ranar anma Bahijja bulala tafi ɗari a jikinta labari ya bazu har cikin fa'da, hakan yasa Sarki Baidulƙais yaji, ranar Bahijja haka ta kwana ɗaure a wulakance tunda uwar safiya Sarki Baidulƙais yasa aka taho da Bahijja, koda ta isa wanke ta da mummunan mari yayi daman gimbiya Yazira tagama gayama Sarki Baidulƙais karya, cikin fushi yace. "Wato ke Bahijja dankinga mahimmancin dana baki shine zaki fara zagin gurfanai ko, dan nabaki damar kiyi addinin ki bashi ke nuna kici zarafin nawa addinin ba dan haka yau zaki ɗandani kudarki shine kikaje wajen iyalina dan cin fuska." baiwar Allah Bahijja ko magana ta kasa haka Sarki Baidulƙais yasa aka kara dukanta sannan aka bata aikin wahala ranar haka ta yini tana aikin wahala itako gimbiya Yazira sai murna takeyi tasamu damar data raba Bahijja da mijin ta a saukake ranar Jakadiya da kyal tai bacci dan tausayin Bahijja hakma su Ashir



Sarkin dawaki tsugunne a gaban Sarki Baidulƙais yana kwasar gaisuwa sannan yace. "Gurfanai yakara girma kiranka ya sameni." cikin kulawa yace. "Gunzar daman ka ajiye aikine bansani ba."? Cikeda mamaki yace. "Ranka shidade ai bantaɓa fashin aiki ba saidai lalura mai tsanani. " mamaki fal a fuskar Sarki Baidulƙais yace. "Amman jiya wani matashi yace mani daga cikin zuriar kane ka aje aiki sannan kuma sunan shi Tarib nayi mamaki dan banyi tsammanin kana da ɗa kamar wannan ba." duk kan Gunzar yagama kullewa cewa yayi. "Ranka shidade kaima kasan ƴaƴana matane sannan namijin bai wuce shekara sha ukku a duniya Gaksia banda masaniya akan wannan bawan dakake magana akai." "lallai kam anyi wasa da hankalina kenan, kuma bai baka sako naba." "eh banga kowaba duk jiya sai Jakadiya kuma nina bata sako zuwa wajen ka."
Cikeda da bacin rai Sarki Baidulƙais yace. "Shikenan na yarje kuje a sauya dawakai sannan kuma kuje da Sarkin yaki sannan abasu kulawa ta musamman yana gama fada yaba Gunzar damar tafiya sannan yace ya turo mashi uban bayi, mamaki sosai ya addabi Baidulƙais aranshi ko yana mamakin wanda yaimashi wasa da tunani har haka yana cikin al'ajabi ya tsunkayi maganar Sarkin bayi dukawa yayi yagaida Mai Martaba sannan yace. "Humtu inasan kasa ataramani bayin Raifasu kaf a babban fili dakaina zanzo akwai wanda nike nema." da sauri yace. "Angama kashi lafiya." yana tafiya ba inda ya sauka sai cikin taskar bayi



Kowa ya gama hallara a wani katan fili dake wajen taskar bayi kowa sai alajabi yakeyi jin kiran da akace Sarki naimasu hatta Bahijja dogarwa basu bari ba duk da batajin dadin dan ta bugu akan sharrin da gimbiya Yazira tai mata, bayan sun fito su Tasi'u ne suka fito koda Ashir yaga Sarki Baidulƙais yataho cikin filin shida Jakadiya take ya raina gaskiar shi kowa ya maida hankalin shi wajen Sarki Baidulƙais hakan yasa Ashir yabi wajen wani katon icce ya boye yana hangen abinda akeyi, take Sarki yafara duba bayin daya bayan daya amman ba Ashir ba alamin shi nan Sarki Baidulƙais yafadi dalilin tarasu, kowa yai mamaki musamman su Tasi'u da suka nemi Ashir sama ko kasa basu san ya zille ba, take Uwar bayi ta tuna da bawan da bugeta daman bata amince dashi ba, hakama Sarkin bayi ya tuna yaba wani bawa kwandon kayan marmari yakai ma Sarki Baidulƙais, duk kansu ya kulle itako Jakadiya tana ganin shi tagane bako ne taki fadane gudun kada Sarki Baidulƙais yasa a cutar dashi, take wutar Bahijja ta ɗauke tabbas ta ganshi wajen Sarki shekaran jiya saidai tarasa ina tasan wannan bawan kowa da abinda yake sakawa a ranshi ɗago kan da Bahijja zatayi sukayi ido hudu da Ashir bayan wani katon icce saidai batajin zata iya tonashi tasan basu da imani, bata gama wannan tunanin ba taji Uwar bayi tace. "Ranka shidade tabbas koni naga wannan bawan kuma banyarda dashi ba raina nabani kamar akwai abinda yazoyi nafi zargin ko

Please Login or Register in order to submit comment