Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin kaushin murya yace. "Baidulƙais na cika umurnin shugaba na sai dai kasani inada sharuɗɗan da zanginda yamaka, anjima da dare ayanka akuya mai gajeren bindi sannan ta kasance kai ido ɗaya ce ku yanka ta, a tsakiyar duhun dare shine kariyar mulkin ka, dan haka kakiyaye."

Yana gama faɗar haka ya ɓace bat, tashi Baidulƙais yayi ya hau saman karagar mulkin sa yana rufe ido da hannu ya nuna Bahijja alamar tazo tasowa tayi duk tsoro ya kamata duk da basujin maganar da aljani ɗantsitu yayi da Baidulƙais sudai sun gansu wani wajen na daban amman tana zargin Masarautar Raifasu ce, koda ta isa dukawa tayi ta gaidashi ɗaukar kafar shi yayi ya ɗora saman kafaɗar Bahijja yaimata nuni da ido duk da ba wani sanin aikin bauta tayi ba, amman taga Umman ta naima Sarauniya Zulaiƙa haka, itama cigaba da danna kafar Sarki Baidulƙais tayi haka taitamashi tausa, mikewa yayi zaitafi baki daya bayin dake wajen suka baje ya takasu ya dinga yi har ya fita suma tashi sukayi ya haɗasu da Sarkin bayin Masarautar shi suka ya basu masauki da ayyukan su......

*∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆*

A Masarautar Daborah kuwa Yarima MalikusSaif ne ya shirya cikin wasu kayan saki na alfarma, fitowa yayi cikin haiba da kwarjini ya tafi sashen Saifulislam iske mahaifin nashi yayi zaune saman sallaya da alama sallah ya gama bayan ya zauna ya gaishe da mahaifin nashi cikin kulawa ya kalli ɗan nashi yace. "Malik ya karfin jikin naka."?....."da sauki."ya amsa mahaifin nashi sannan yace. "Abbuh daman inasan kanemani alfarma wajen Umma inasan Bahijja ta fara yiman hidima."


Sake kallan MalikusSaif yayi sannan yace. "Malik dole sai Bahijja zatayi maka hidima ɗana."? Murmushi yayi sannan yace. "Aaa Abbuh saidai nafi jin hankalina zaifi kwanciya akan sauran bayin."shima Saifulislam murmushi yayi sannan yace."Hakane sai dai kasani kasama ranka hakuri da Bahijj." a razane Malik ya kalli mahaifin nashi sannan yace!!!!



*Yar Mutan Kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote

*BAYI MA 'YA'YA'NE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________


*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*


Babi na 16


Cikin lailashi MalikusSaif yace. "Abbuh miyasa inasan inba Bahijja kulawa dan Allah kaima karkace haka, kataimaka mani inasan intaimaketa." Kallon ɗa'n nashi Saifulislam yayi sannan yace."Nafahimce ka Malik nikaina banki na rike Bahijja a matsayin ƴata ba sai dai kasani bamu da zaɓi dole muhakura da kaddarar dake bibiyr mu." cikin mamaki MalikusSaif yace. "Abbuh wace kalar kaddara ce har haka? Take neman shigowa rayuwarmu."!? Ya ida maganar cikin tsoro dan rainshi ya fara bashi babu lafiya.

Kama hannun MalikuSaif yayi sannan yace."Kwarai kuwa na rashin Bahijja ko kasan Bahijja ce ita fansa akan ka? har aka samu maganin ciwon ka? tana hannun Sarki Baidulƙais kasan ba lallai tana Masarautar Raifasu ba, muna kyautata zatan tana hannun boka Sarriƙus wanna dalilin yasa nace kafidda rai da samun Bahijja a hadimar ka tunda ba a kalkashin mulkin Masarautar daborah take ba."

Wasu hawaye masu zafi suka wanke mashi fuska yace. "yanzun shikenan ba rana ba lokacin da Bahijja zata zama ƴantatar ƴa? shikenan Abbuh sabida bukatar ku dan kuga ɗanku ya rayu a matsayin mutun zaku bada Bahijja dan tana baiwa hakan shine adalci ya mahaifiyar ta zatayi."?

Cikin tausasa murya ya ƙara rike hannun Malik yace. "ɗana bamu matsama Binta dan tabada ƴarta ba da kanta ta zabi rabuwa da ƴarta da fansar ranka."
"Abbuh duk da haka tayi ne domin darajar ku a matsayin ku na iyayen
ɗakin ta kuma baiwar ku dole tayi hakuri har ta ɗauki Bahijja."
"tabbas Malik kayi gaskia sai dai kasani ni kaina kan Bahijja sai inda karfina ya kare." cewa yayi. "Abbuh yanzun zan tafi Masarautar Raifasu zandawo da Bahijja a tare dani koda zan rasa raina alkawali."


_Wata sabuwa gadai abinda Malik ya faɗa koya lamarin zai kasance muje zuwa_

Saifulislam yace. "Aaa ɗana kada kafaɗi haka Masarautat Raifasu akwai sihiri da tsafi a cikin ta bayyananne kabari sai munsami illimin tunkaran Masarautat ta hanyar wargaza boka Sarrrilƙus saboda shike iko da Masarautar Raifasu, kaga dole munemi limin tarihi dan haka kayi hakuri muga yanda lamuran zasu kasance, sai mu tunkare su."


Hawaye keta zirara a idon Malik yana jin tausan Bahijja a zuciyar shi ko cewa yayi har abada bawa bawane baida wani ƴanci ko galihu, goge mashi kwallan idonshi Saifulislam yayi, nan yakama jan Malik da fira saidai baki ɗaya hankalin Malik na wajen Bahijja....

*∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆*

Masarautar Raifasu bayine keta aiki kamar ba gobe ga uban dukan su anayi da bulalai kamar jakai haka suketa kwasar duwatsu suna kaiwa cikin wani katon waje ba abinda kake gani sai tarin rairayi a cikin shi, duk wanda ya ɗauki dutsen zai ɗaura shi saman kirjin shi dogawara rike da zabga zabgan bulalai suna dukan su, danko jikin su duk ya fashe sai jini ke zuba ga uwar rana amman ba'a ɗaga masu ba ko abinci basu tsayawa suci, ranar haka bayin Raifasu sukayini sunayi wasu har suma sukeyi dan azaba da wahala, haka za'aita dukan su harsai sun farfaɗo suci gaba da aiki, a wajen Bahijja kuwa tsaye take a gefen Sarki Baidulƙais inda wata baiwar shi takawo mashi abinci yaba Bahijja umurni ta zuba mashi ta tsugunna ta bashi a abinci kallan banza yaimata yaki ƙarɓa itako cewa tayi. "Ya shugabana tuba nikeyi ga abincin ka nan ya karaso kaci gurfanai ya taimakeka."


Ko kallo bata ishe Baidulƙais ba saima kishingiɗawa da yayi itako ganin yaki ansa ta ɗauka bai bukata haka ta juye abincin cikin kular da aka kawoma Baidulƙais abinci, ta koma gefe ta tsugunna, abinda Bahijja tayi ba karamin ɗagama sauran bayin wajen hankali yai ba, itako ko ajikin ta hakan yasa Sarki Baidulƙais ya fusata kiran ta yayi ta hanyar hannu yai mata yafice hakan yasa ta gane kiranta yakeyi, tashi tayi taje gaban Baidulƙais ta tsugunna tace. "Ranka shidade gani.....wani wawan mari ya kwashe Bahijja dashi take tasaki wani razanannn kuka duk ta ruɗe kara ɗaura mata wani gigitaccen mari yayi, take Bahijja ta fara sakin fitsri dan azaba, nan ya kira uwar bayi, itama ya wanketa da maruka har ukku yaimata nuni da ta fita da Bahijja dan bata gwaji akan sharuɗɗan shi, "tuba mukeyi Sarki mai dole gurfanai yaja girman ka." cewar uwar bayi takama hannun Bahijja da tagaji da kukan zuci suka fita ba inda ta wuce da ita sai taskar bayi suka shiga ɗakin ta suna shiga ta kara kifawa Bahijja mari sannan tace."Ke dan ubanki ni zaki jazama bala'i wajen Sarki baki da hankali zaki mika mashi abinci ke zaki dinga bashi da hannun ki har sai ya koshi kina jina? sannan kuma daga yau duk wani motsin Sarki a kalkashin ki zaki dinga kulawa shashasha dake mai mugun hali ɓaceman dagani kar in ɓallaki."

Dasauri Bahijja ta fita ta shiga masaukin su tana kuka tana tuna Umman ta da Baban ta, Yarima Malik ne ya faɗo mata arai a zahiri tace. "Ya Malik da kana nan ba wanda zai cutar dani, Allah yabaka lafiya yarima mai adalci mai kishin bayi da talakawa."ji tayi ance. "Kwanciyar uban me kikeyi bazaki je kici gaba da aiki ba ko saina zaneki a wajen nan."? cewar uwar bayi, cikin kyarma Bahijja tafita tana bata hakuri sannan takoma wajen Sarki Baidulƙais ta tsugunna ta ɗibi a abincin tafara bashi yana karɓa yana yaguna yana kuma kin karɓa har hannun ta saiya sage sannan zai karɓa haka har ya koshi yana cikin abincin karshe ya firzama Bahijja a fuska rufe idon ta tayi sannan ta goge tace. "Tuba nike ya shugabana biyayya a gareni shine gatana girma yakara shiga a wajen ka inagodiya shugabana."

Haka rayuwa takasance a wajen Bahijja kullun cikin fuskantar wulakanci takeyi a wajen Sarki Baidulƙais ba dare ba rana wani lokacin indare yayi haka uwar bayi zata kwara mata botikim ruwa a jiki ta sakata wankin kayanta ba karamim tsanar Bahijja tayi acewar ta dan Baidulƙais ya zaɓeta matsayin hadimar shi, wannan dalilin yasa ta hana Bahijja sakat a cikin Masarautar Raifasu, kullin cikin zulumi take kwana take tashi.


Bayan wata huɗu zuwa yanzun Bahijja takara girma sosai, zaune suke a fa'da ta duka wajen Sarki Baidulƙais ya ɗaura kafar shi a saman kafaɗar Bahijja tana mashi tausa, anata fadanci banda maganar tsafi ba abinda ake gudanar wa a cikin Masarautar Raifasu, Baidulƙais ne yace. "Sarkin gida aje taskar bayi a ɗauko mani bayi ukku daga cikin bayin Daborah aljani ɗantsitu zaiyi anfani dasu."

Koda Bahijja taji abinda Sarki Baidulƙais yace hakan ba karamin tsorata ta yai ba shiru kawai tayi ga zullumi bata gama tunina ba aka kawo bayin ukku maza biyu mace daya a gaban idan ta aka yanke hannun wata akasamu wata ƴar kwalba akasaka jinin a ciki zobe Baidulƙais ya murza cikin kankanin lokaci wajen ya haɗe da guguwa take aka bace da waɗan nan bayi hakan yasa tun Bahijja na guntse kukan ta har ya kuɓuce mata tasan bala'in dake wajen boka Sarrilƙus, shiko Sarki Baidulƙais sawa yayi akaima Bahijja bulalai akan tayi mashi kuka a cikin fa'da sannan yasa aka tafi da ita wajen horon bayi.

*∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆*

A wajen Yarima Malik kuwa baida magana saita Bahijja yau tunda ya tashi ya sama kanshi niyar fara binciken tarihin Sarrilƙus dan yasan ta hanyar da zaibi wajen yakar su ya amso Bahijja dan yana ji Bahijja akwai babban alamari a tareda ita, shida Huzaifa sai Yazid suka tafi har cikin gidan tarihin Daborah,suna isa maigidan tarihin ya gaishe dasu suka shiga suka tambaye shi litattafan tsafi da tarihin Masarautu na Gambia ya nuna masu ɗauko litattafan sukayi wajen ukku suka fara dubawa inda kowa ke nema ko zadu dace da samin tarihin Masarautar Raifasu da boka Sarrilƙus....

Suna cikin dubawa Yazid yaga wani littafi na tsafi da aka rubuta shi sama da shekaru dubu huɗu a duniya kuma yafi karfi a Masarautu haka sukaita dubawa suna ganin kayan ban mamaki ranar har yamma basu dace da litattafan tsafin da zasu samu sirrin boka ba, hakan yasa Malik fadama Sarkin gidan tarihi dalilin zuwan shi, bakaramin mamaki Dawud yaiba saidai yananin da yaga Malik bazai iya musu dashi ba hakan yasa yace. "Naji abinda kace magajin gobe saidai kasani kuje ku dawo zuwa nan sa sati ɗaya zan duba maku, in ban samu ba kuzo zanbaku kadan daga cikin abinda nasani akan Sarrilƙus da dajin gamki."

Cikin fushi da garaji Malik yace. "Sati yaimani nisa dan kallan shekara nike mashi saidai na baka nan da jibi zan dawo dafatan zaka taimaka yanda ya kamata."...."na amince Allah yakara girma Allah yakaimu jibin lafiya." cewar Dawud, haka suka tafi sashen Yarima Malik ko abinci ya gagari Malik kullin hankalin shi na wajen Bahijja.

Sarauniya Zulaiƙa ce zaune a saman kilisar ta ana mata tausa ga hadiman ta sai fiffita suke mata wasu kuma suna ta aiki, ɗan aike ne tareda Jakadiya tai mashi isu har gaban Sarauniya Zulaiƙa dukawa sukayi kowa ya kai gaisuwa wajen Sarauniya, ɗaga masu hannu tayi sannan ta kalli Jakadiya da alamar tambaya, kanta kasa tace. "Ranki shidade kinyi bako daga Masarautar Waisu, Allah yataimakeki shiyasa na kawo shi gareki Allah yakarama Sarauniya lafiya da nisan kwana." kallan shi Sarauniya Zulaiƙa takarayi duk da baibari ta haɗa ido dashi ba amman bata aminta da bokon ba, "daga ina ɗan saurayi."?
Kallan sakare yaima Sarauniya Zulaiƙa yace. "Daga Masarautar Waisu uban gidana yace inbaki wannan sakon." kallan tsaf Sarauniya Zulaiƙa taimashi na sakanni taba Jakadiya umurnin ansar wasikat ta hanyar kallo, amsa tayi ta duka tamikawa Sarauniya Zulaiƙa, budewa tayi dafara karantawa.

_Nasan zakiyi mamakin jin wannan sakon daga gareni to ba abin mamaki bane duk da fuskar ki ta bayyana hakan a zahiri, dalilin kuwa shine kinsan ba wata alaƙa tsakanin makiya kuma abokan gaba guda biyu na zauna nayi nazari naga dacen da yake a cikin tarayyata dake dan haka ina mubaya'a a wajen ya Sarauniya mai adalci ina sauraranki daga Sarkin Waisu zuwa ga Sarauniyar Daborah_


Kallan bawan nan tayi sannan tace. "Inakaje kabashi wannan sakon sannan kace mashi Sarauniya Zulaiƙa taji sakon shi ammn kudurin shi abin korarwa ne a wajena dan haka zaka iya tafiya."

Magana bawan nan zaiyi Sarauniya Zulaiƙa ta ɗaga mashi hannu haka ya haɗe maganar shi ya tashi ya fita ba inda yaima tsinke sai Masarautar Waisu yana zuwa ya wuce fa'da ana ta fadanco koda Sarki ya yagan shi baki ɗayan su suka mike Yarima Haishir ne ya tareshi tareda da jefomashi tambayoyi kala kala yace. "Sunbu ko andace? Ina fatan zako mana da labari mai daɗi? Kuma a wane yanayi kabaro Sarauniya Zulaiƙa."!?

Kallan shi Sunbu yayi sannan ya gilgiza kai mikama Sarki sakon wani jikka da ta bashi sannan yace.!!!




*Yar Mutan Kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________


*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*





Babi na 17




"Ina mai bakin cikin sanar dakai kin amincewar Sarauniya Zulaiƙa akan kudurin mu, sannan tace lamarin ka kurarreni a gareta kuma abin watsar wa saidai tabani wannan jikkar bansan meki ciki ba ya shugabana Gamji ya taimakeka ina tuba."

Girgiza kai Humzu yayi cikin bakin ciki marar misaltuwa yace. "Naji abinda tace saidai ba nan gizo ke sakar ba yazama dole mu sauya wata hanya da zamu jawo Zulaiƙa a jikin mu dan mu ha'inceta dan haka Yarima Haishir ya zama dole ka ƙulla abota da Malikussaif kuma ka nuna kanasan shi da zuciya ɗaya ta hakane kawai zaisa Zulaiƙa ta baka mahimmanci tunda kana son ɗanta harda amince dani daga karshe fa marmasu mu darkake su kamar yanda sukayi ga kakan mu Sarki Faihasu inafatan kun fahimta."?

Cikin gamsuwa Yarima Haishir yace. "Ranka shidade munji abinda kace saidai ya zamuyi da gammayar da mukayi da Masarautar Raifasu da Ƙaisu bayan haɗin guiwa kai karfi da mukayi dasu baka ganin hakan tamkar cin amana ne a wajen su."? tashi Sarki Humzu ya tashi daga saman karagar mulkin shi ya iso gaban ɗan nashi ya tallabo fuskar shi yan shafawa cikin so da kauna yace. "Ɗana kenan rabu da maganar Sarki Baidulƙais da rundunar shi tareda Sarkin Ƙaisu a halin yanzun batasu nike ba saboda sun gaza, ta Zulaiƙa nikeyi gata mace amman kullin saitasa gaban maza ya faɗi naso ace Malikussaif ya mutu amman kwatakwalan ci irin na Baidulƙais yasa yakasa harda basu magani wannan dalilin yasa ko Masarautar shi ban kara waiwaya ba, kaima kamanta dasu nasan bada jimawa ba zaizo ya sameni da wata bukatar zai gane waye Humzu kuma me nataka intakamar shi boka Sarrilƙus nikuma takama ta Bokanya Zuruka kaga banda wata damuwa ɗana gamu da tarin mayaka danma nabashi wasu saidai sakaci irin na Baidulƙais yasa anhalakamani jama'ata, kaidai ka kiyaye abinda nace maka yanada kyau ka samu lokaci kaje Daborah wajen Malikussaif dan gaida shi."


Murmushi ɗauke a fuskar Haishir ya rungume mahaifin shi sannan ya ɗauki jikar da Sarauniya Zulaiƙa tabada ya buɗe bakomai bane sai dalleliyar takobi da sauri ya fiddota duk ta haske masu ido saidai ashe ta Masarautar suce, takobin Sarki Faihasu kowa saida yai mamaki duk da bata ce komai aman yagane manufar Zulaiƙa mikama Sarkin fa'da yayi yace akaima Sarkin gidan tarihin Masarautar ya aje a wajen adana makamai na tarihi sai fidda iska da huci Sarki Humzu yakeyi a haka kowa yabar fa'da bai kuma cewa komai ba yana tunanin yanda zai bullowa lamarin Sarauniya Zulaiƙa

*∆∆∆∆∆∆∆∆*

Masarautar Raifasu kuwa tunda Sarki Baidulƙais yasa wawan Sarki hukunta wasu bayi ba abinda akeyi musu banda azaba dan ankamasu da laifin guduwa ciki kuwa harda Bahijja itako Bahijja Baidulƙais yasa akaima ta bulala hamsin yasa aka kaita wani ɗakin duhu aka rufe ta, danko matar Sarki Baidulƙais gimbiya Yazira sawa tayi aka dinga watsama Bahijja ruwan zafi abinka ga fara duk jikin ta yayi jajir jini ya tashi saman fatar ta, suko sauran bayin shanyasu akai a rana aka azamasu duwatsu a saman kirji ana dukan su, ana ɗiga masu narkarka dalma afata sai ihu sukeyi ba dare ba rana cikin azaba suke, a gadarance Baidulƙais yasa aka kawo mashi Bahijja a turakar shi wanda yasa bayin dake wajen suka fita kallan ta yayi duk da bata hada shekara goma ba amman akwai halitta dan inka ganta zakayi zatan takai shekara shabiyar a duniya dan kirar jikin ta duk ta fara bayyana ga gashi samn baya kwance inbakasan Bahijja ba tabbas zakayi tsammani balarabiya ce da kyawunta da dirin ta, koda aka wulla Bahijja cikin ɗakin Baidulƙais ya rufe kofa, ya kafeta mayyun idanun shi tafiya yayi gabanta yana shafa jikin ta duk karancin shekarun Bahijja hakan baisan takasa gani abinda yake shirin aikatawa da ita ba, tunawa tayi da huɗubar mahaifiyar ta tace mata koda Ya Malik dinta ne kada tabari ya taɓa mata jiki mutuwa zatayi, baki daya takara tsorata jin bakin shi a nata ya danneta jikin bango yana sumbar ta ko motsi batayi na dangin ta da suka fara fitowa yafara dirza, kwalla ihu tayi ta gartsa mashi uban cizo jin zai halaka ta ba shiri ya saketa duk ya rikice sai kuka takeyi takama ja da baya baya zuciyar ta kamar zata faɗo kasa dan tsoro da fargaba, shiko ta fasa mashi hannu ya duƙe sai zugi yake mashi gadan gadan yayi kan Bahijja itako ganin haka yasa ta faɗa bathroom din ɗakin shi ta saka kuba sai garza kuka takeyi tana addu'a tarasa dalilin dayasa zai hukunta ta hanyar cutar ta yana mintsilinta harda kama mata baki, tasan yau saita mutu tunda har ya taɓata tunda ba babanta bane tana cikin kukan bacci yai gaba da Bahijja can cikin bacci taji yana ta gamrar kofar yana mata barazana shiko dafe yake da mara yagama kwaɗaituwa da Bahijja kuma ya sama ranshi kota wane hali saiya kashe kishir ruwar da ta dame shi akan Bahijja tun fara ganin shi da ita, itako kururuwa ta shiga yi dai dai da gimbiya Yazira tayo hanyar ɗakin mijin ta, da sauri taji ihun mace dakin mijin ta da karfi ta banka kofar ɗakin ta shiga tsaye ta iske shi daga shi sai wando ya rike ciki, da sauri ya waigo ya ganta harara ya watsa mata, ya cigaba da bugun bathroom din tabbas tasan mijin ta nabin mata amman banda bayi tayi mamakin wacece cikin kewaye takowa tayi duk ta tsorata da yanayin shi, ta fara magana tace. "Ki buɗe kofar kinji ba abinda zai maki." itako Bahijja jin muryar mace tasan bai wuce gimbiya yasa ta buɗe kofar da sauri ta koma bayan Yazira da karfi ya fizogata ya manna a jikin yace ta barmashi ɗaki ai baiwar shi ce kuma mallakin shi zai iya komai da ita, dubara ta faɗo mata a rai, tace. "Haba kamarka mai dole Sarkin Raifasu ba girman ka bane a ji kaima ficiciyar yarinya kamar Bahijja fyaɗe tabbas girman ka zai zube ga idan duniya shawarar da zanbaka me zai hana kabari takara girma sai ka maidata kayan hutawar ka, nasan lokacin zata fi maka anfani."



A fusace kamar zaki ya kara haɗe bakin shi dana Bahijja kamar ƴar baby take a hannun Baidulƙais sannan ya jefar da ita ya kalli Yazira "kin kyauta da kika fahimtar dani wannan shine abinda ya dace." banzan kallo ta watsa mashi sannan ta fidda Bahijja waje ta dawo tana bashi baki tana shafar shi, kamar mai jira ya fara sarrafa Yazira ranar akanta ya kare, itako Bahijja komawa tayi taskar bayi ta kwanta duk zazzaɓi ya kamata sai kyakyarwa takeyi, bacci ya ɗauketa tana cikin bacci taji an kyarama ta ruwa asaman fuska a firgice ta mike uwar bayice tace taje gimbiya Yazira na kiran ta shashen ta duk da batasan me zatayi mata ba saida taji cikin ta ya juya, kakkaɓe ruwan kunnan ta tayi ta tafi, a wani katan ɗaki ta isketa tanacin tufa, dukawa Bahijja yayi ta gaida ta, watsama dubzar tuffa tayi a saman fuskar ta dukar da kanta tayi ta goge sannan tace. "Godiya nike uwar dakina Bahijja natuba gurfanai ya huci ranki."

Jitayi ta watsa mata yatsu a cikin ido ta ɗaureta da mari cikin fushi tace. "Ke baiwa harkin isa shiga ɗakin mijina wato ke mazinaciya ko."? Mamaki ya ishe zuciyar Bahijja da ta kasa gane mitake nufi da mazinaciya jitayi ta kara kifamata mari da sauri ta dawo tunanin ta hakuri tafara bata kamar me amman sai kifa mata maruka takeyi take fuskar Bahijja ta kumbura har ta fasa mata baki, kuka ta fashe dashi nan takira uwar bayi tace akaita cikin taskar bayi aimata dukan tsiya haka akaja Bahijja kasa tanata ba gimbiya Yazira hakuri itako Uwani uwar bayi daman ta tsani Bahijja ko tambayar ta dalilin laifin ta batai ba da kanta taita sakarma Bahijja mari saida ta sauke mata bulala hamsin take jikinta yakara tsanan ta da zafi na zazzaɓi, sannan tasaka wanki, haka ta jibgi aiki tana cikin aiki Jakadiya ta aiko wata baiwa sa'ar Bahijja taje tana kiranta, a gajiye tace aiki takeyi jin abinda tace yasa uwar bayi jiki na rawa tace ta tafi, haka suka tafi har ta faɗa tayi baki tana isa ta riketa suka isa wajen Sarki Baidulƙais tun shigowa Bahijja yake haɗe yawo ya kafeta da ido itako tsoran shi takeyi taki ta. kalle shi dukawa tayi ta gaidashi sai tanɗe baki yakeyi ganin abinda yakema Bahijja yasa Jakadiya taji jikinta ya mutu tasan manufar sa, itako tana tausan Bahijja dan kaf bayi itace karama mai karancin shekaru, haka ta basu waje ya kara tanɗe baki yana shafa fuskar ta zuwa wuyanta kara matsowa yayi yafara sunsuna ta da sauri taja baya maganar gimbiya Yazira ta faɗo mata arai tace aranta ko abinda Baidulƙais ke mata shine zinar ji tayi yace. "Bahijja bani abinci."


Jikinta na rawa tafara bashi da hannun ta sai kama mata hannu yakeyi da harshe yana tsotsa itako sai kwalla ke yawo a fuskar ta tana neman tsarin Allah daga kaidin Baidulƙais harya gama yace taci tace ta koshi kamota yayi ya kara mannata a jikin shi yana wasa da yatsun ta ya shafi dogon wuyanta mai tafiya da ranshi yaji jikinta kamat garwashi, yace. "Baki lfy ne."?


Zamewa tayi a jikin sa ta zauna kasa duk ta tsorata da abinda gimbiya Yazira taimata tace mashi ."eh."cikin kulawa ya kira mai kula da maganin shi ya miko mashi wani jiko na maganin hausa ya mika mata ba musu ta ansa tasha sannan yace akira mashi da Jakadiya tana shigowa ta gaida shi yace tamaida Bahijja gida bata lfy haka ta kamata suka tafi sai magana Jakadiya kema Bahijja saidai tai nisa a tunani samun wata inuwa tayi ta zaunar da Bahijja tace. "Bahijja bakiji inata magana miyai maki."?


A tsorace tace. "Ranki shidade bakomai abinci." nabashi takarasa maganar kwalla na zarya a fuskar ta, cikin rashin yarda tace "ƴata kada kiboyeman ba abinda zan maki kuma bazan fadama kowa b." sannan Bahijja tace. "Shafa mani jikina yakeyi kuma yama tsotsan baki na gimbiya Yazira takamani dashi lokacin na ɓuya a ban ɗaki hakan yasa ta kubutar dani daga mintsina dayayi a nan ta gwada mata kirjin ta da hannu na koma dakin mu, sai ga uwar bayi tai kirana ina zuwa gimbiya taita mari na sannan tasa akaimani dukan tsiya tace mani ni mazinaciya ce dan Allah Umma me mazinaciya ke nufi inajin tsoro." banda kwalla ba abinda Bahijja keyo tausan ta yakara kama Jakadiya cikin kulawa tace. "Saboda kina bari mijin ta na wasa da jikin ki shiyasa tace maki mazinaciya sannan karki kara bari yana taɓa maki jiki, kinaso ki mutu."?


A rude Bahijja tace" Aaa Umma."...'' inhar hakane kada ku kara bari ko hannun ki ya rike." cewa tayi "to Umma daman haka Umma na take cemani ba bani ni Bahijja shikenan mutwa zanyi yanzun."guntse dariyar da takama Jakadiya tayi ganin yanda ta ɗaura hannu akai tana gabza kuka duk ta rikice da ka ganta kaga yarinya sharaf, cewa tayi. "Ai yanzun bazaki mutuba saboda mutuwa tabaki bashi saidai kada ki kara kinji gurfanai ya kiyaye gaba tashi.' mutafi haka Jakadiya takaita har ɗakin ta sannan ta samu wata baiwa dattijuwa Saude ta

Please Login or Register in order to submit comment