Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta gyara mashi ɗakin shi sannan ta hada mashi ruwan wanka, haka zata koma falo ta takure har sai ya fito ta cikaga ba da yimashi dannar kafafu, idan Jakadiya ta shigo kawo mashi abinci Bahijja ce zata bashi abinci, kullin a takure take duk da yanzun yadaina yunkurin ta ɓamata jiki koda kuwa a ɗaki ya isketa tanai mashi aiki saidai yaita kallan ta hakan kesa Bahijja na shuga damuwa duk ta rude, dan bala'in tsoron Baidulƙais takeyi a rayuwar ta....



Watarana da marece Bahijja ce zaune a cikin taskar bayi tana wanke ƴan kayan ta kafin gobe ta tafi aikin ta kamar yanda ta saba, tana cikin wankin ta, batasan hawa ba batasan sauka ba taji anzabga mata bulala a tsakiyar baya, a zabure ta mike tace. "Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un." tana juyowa taga uwar bayi tsaye tana mata kallan banza sake zabgama Bahijja bulala tayi aiko ta kwalla uwar kara cikin kankanin lokaci duk bayin dake kusa dasu Bahijja suka fito itako Bahijja duk ta gama ruɗewa dan bakaɗan takejin dukan n ratsa taba har kwakwalwar ta dan a zaba, koda Bahijja ta fahimci da gayya Uwani ke dukan ta batasan ta mikeba tafara zabga uban gudu batasan ta fita taskar bayi ba, aiko nan Uwani tasa wasu bayi su kamo mata Bahijja itama bin Bahijjar tayi, itako Bahijja batada burin da ya wuce taga ta isa wajen Jakadiya tasan ita kadai ce mai taimakon ta tana cikin gudu taji ta bangaji mutun tai bayaya ta fadi kasa a ruɗe ta sake mikewa tana mikewa taga gimbiya Yazira tsaye ta rike kugu tanai mata kallan tuhuma, cikin Bahijja ne ya kaɗa take yawun bakin ta ya ɗauke batasan ta fara kuka ba tafara ba gimbiya Yazira hakuri, saiga Uwani ta isa sai haki takeyi koda taga Bahijja tsugun ne agaban gimbiya Yazira tasan kwanan zancen tabbas yau kashin Bahijja ya bushe duk da batasan me taima gimbiya Yazira ba, a gadaran ce gimbiya Yazira tace. "Ke dan ubanki wace kalar mayyar yarinya ce ni zaki banka ki gogaman kashin tsiya!" take Uwani tace "yau naga munafukar yarinya, jamgi ya taimakeki gimbiya ta umurnin ki nike jira." da sauri Bahijja tafara gilgiza kai tace. "Ranki shidade ki rufaman asiri kiyafeman karkisa a dakeni ki taimakaman bankula dake ba kiyi hakri!" kamar jira gimbiya Yazira ta fallama Bahijja mari tace. "Dan ubanki wato baki kulani dani ba kenan dan kinmaidani sakara idaninki a tsakar kai suke da zakice mani haka."?


tunkan Bahijja tayi magana tafarajin saukar bulalai kamar ba gobe a kiɗime Bahijja ta rike bulalar da Uwani ke dukanta ta ita sai rawa jikin Bahijja keyi, sake ɗauketa da mari Uwani tayi tace. "Dan ubanki sake mani bulala kar in lahanaki." itadai bata saki ba tace. "Baba Uwani kiyi hakuri ku hukuntani da hanyar bani aiki mai wahala amman banda duka, ban lafiya." jitayi gimbiya Yazira ta kara wanketa da wani marin tace. "Wato ke ga tsinanniya har saikin zaɓi abinda kikeso aimaki kenan kina baiwar."? bata kara cewa komai ba, itako gimbiya Yazira tunda ta fahimci ba abinda Bahijja tafi tsoro a duniya irin duka tasama ranta kullin saitasa andaki Bahijja koda zata mutu ta ɗauki aniyar duk wannan hasken fatar da take takama sa ita saita maidata baka dan azaba,haka Uwani taci gaba da labtar Bahijja itako sai kwalla takeyi wasa wasa saida akaima Bahijja bulala tafi hamsin duk karfin Bahijja yagama karewa zuwa yanzun ko kukan ma takasayi, ana cikin dukan Bahijja saiga Jakadiya ta fito daga wajen Sarki Baidulƙais zata tafi gida, taga anacin zarafin Bahijja tana isowa ta iske gimbiya Yazira suna haɗa ido gimbiya Yazira ta watsama Jakadiya wani mugun kallo ba shiri ta sauke nata idon, kamar taima Bahijja kuka haka Jakadiya taji tagowar da zatayi ga azaba ta isheta suka haɗa ido da Jakadiya kwallan da take makalewa ne suka zubomata ganin ƴarta Bahijja cikin azaba, zuwa tayi gun gimbiya Yazira taimata magana a hankali wanda bansan metacema gimbiya Yazira ba sainaga ta dakatar da Uwani daga dukan Bahijja cikin tsawa tace. "Daga yau kisake aikata irin wannan kuskuren kuma gobe da safe kizo sashena kisameni kafin kije iskancin da kika saba." godiya Jakadiya taima gimbiya Yazira kmar jira da sauri ta isa wajen Bahijja, itako Uwani takema gimbiya Yazira baya tayi suka tafi sashen ta, itako Jakadiya ɗaga Bahijja tayi ta shiga da ita sashen ta, tana zuwa tafara yimata fita duk t fita hayyacin ta duk jini jikin Bahijja ranar ba Jakadiya tai Bahijja sai tsakar dare saida taba Bahijja kulawa ta musamman harta samu tayi bacci sannan itama ta kwanta cikeda tausayin Bahijja a cikin zuciyar ta........




Masarautar Ƙairu kuwa Sarki Danwar ne zaune anata fadanci ba abinda suke tattaunawa akai sai yanda zasu fuskanci Masarautar Daborah dan ɗauko takobin Bairu duk da sunsan ɗaukar takobin Bairu bakaramin aiki bane a garesu, suna cikin zaman saiga ɗan aike daga Masarautar Waisu yakawo ma Sarki Danwar wasika, koda yazo akai mashi iso wajen Sarki Danwar yana zuwa yakai gaisuwa sannan ya fadi abinda ke tafe dashi yaba Sarki Danwar wasika,yana ansa yaba magatakar dan fa'da ya amsa tareda bashi izinin karanta wasikar.




_Daga Sarki Lahazu zuwa ga Sarki Danwar ina mai sanar dakai zuwa Masarautar Daborah dan kaima Sarauniya Zulaiƙa ziyarar ban girma tareda kasuwanci mai girman gaske, saidai zamuyi tafiya ukku ga wannan watan na Fabrilu, kahuta lfy ina saurarenka daga Masarautar Waisu._


Koda magatakarda ya gama karanta sakon Sarki Lahazu bakaramin mamaki bane ya bayyana a fuskar Sarki Danwar ba yasan ba wata dangantaka dake tsakanin su da Masarautar Daborah banda cin zarafi da kwantacciyar gaba mai karfin gaske amman miyasa Sarki Lahazu keso sukaima Sarauniya Zulaiƙa ziyara baccin yasan basu jituwa, ko Sarki Baidulƙais yasan da wannan ziyar tunda a tare suke, a wani bangare na zuciyar shi kuwa yana mamakin abinda Sarki Lahazu ke shiryawa akan Masarautar Daborah duk da shima yanada nashi mugun nufin akanta, sai kuma ya yake shawarar ansar tayin da Masarautar Waisu tazo mashi dashi duk da shima burin shi yaga ya nakasa Masarautar Daborah ta hanyar rabasu da takobin Bairu da haka ya kalli magatakarda yace. " maida mashi da sako akan na amince da tayin su, gamji yakaimu sannan aba ɗan aiken kudi domin guzuri yana gama faɗar haka ya mike tareda maya mashi baya ya tafi sashen shi domin nazari, shiko magatakarda yana gama rubuta wasikar yamika ma wannan bawan sannan yakama hanyar komawa Masarautar Waisu.....



_Daborah_



Yarima Malikussaif ne zaune a sashen mahaifin shi suna tattaunawa akan lamarin Bahijja duk da mahaifin nashi ya nuna gamsuwa akan maganar da Malik yaje mashi da ita saidai baiji zai barshi ya tunkari Masarautar Raifasu yasan za'a iya salwantar mashi da rayuwar ɗa,Malik ne yayi magana yace.



"Abbu inaneman alfarma agareka kaimin izinin zuwa ɗauko Bahijja ta dawo wajen iyayen ta, bamu san a wane hali take ciki a halin yanzun ba, kodan addinin ta Abbu dan Allah.!" shiru yayi yana nazarin maganar Malik duk da yasan abinda ya faɗa gaskia ne amman baiji zaibar Malik yaje Raifasu, a zahiri ko cewa yayi. "Naji abinda kace saidai kaje zan nemeka idan nayi nazari komai kenan zakaji abinda na yanke akai." "Abbu daman abinda Ummu taimaka kayi hakri kayafe mata." murmushin manya Saifulislam yayi yace. "Ba abinda mahaifiyar ka takeman wanda ke ɓataman rai, saidai ɗabi'un tane banso musamman kan yanda take mu'ammala da talakawan ta duba da itace shugaba a wannan Masarautar." "hakane Abbu insha Allah zata daina." "Allah yasa yanzun kabar wannan maganar zan nemeka." cikin jin dadi Malikussaif yace shikenn Abbu Allah yakara girma." da Ameen ya amsa suna cikin fira Huzaifa da Yazid suka shigo, suka gaida Saifulislam, sannan suka fita tareda Malikussaif ba inda suka dosa sai cikin lambu.....



Koda gari ya waye dakyal Bahijja ta tashi tana tashi ta ɗebi ruwa tayi alwalla tayafa wani zani tagabatar da sallah duk da bawani iya gabatar da addini sosai tayi ba amman ba laifi ta iya duba da ba gaban iyayen ta takeba kuma Masarautar da take ba addinin musulunci sukeyi ba, tana cikin sallah Jakadiya ta shigo dakin tun tanajin haushin yanda Bahijja ke ibadar ta har abin yafara burge Jakadiya, tana idasa sallah tafara addu'a tafara cewa. "Allah ka kawomani ɗauki ka fiddani cikin wannan ukubar danike ciki kamayar dani wajen iyayena ya Allah kasaka baba da alkhairy, Allah karabani da kaidin Sarki Baidulƙais da matar sa da duk wani azzalumi tayi tana hawaye sannan ta shafa a fuskar ta, tana gamawa ta mike taga Jakadiya tsaye saida gaban Bahijja ya fadi amman sai taga taimata murmushi itama maida mata da martani tayi nan tace. "Baba ya gajiyarki kinata ɗawainiya dani Allah yabiyaki Babata." murmushi tayi ta dafa kafadar Bahijja sannan tace. "Ƴata kinaso ki koma wajen iyayen ki ni kuma banji zan iya rayuwa babu ke Bahijja yan shekarun danayi dake banjin zan iya rabuwa dake duk da kinada wayonki kika rabu da iyayen naki ammn ba sosai ba, yanzun zaki iya gane mahaifiyar ki Bahijja."?


Murmushi tayi tace. "Eh Baba zan iya ganesu saidai sunan Masarautar mune ya shigeman a zuciya ta."
" hakane kam kinada shekara tara aka rabaki da iyayen ki Bahijja baici ace kin manta dasu ba, amman yanzun zanje wajen aiki kema kitashi duk da bakijin dadi kije wajen gimbiya Yazira anjima zan baki wani labari ƴata." cikin jin dadi Bahijja tace. "to Baba shikenan sai anjiman Baba zazzaɓi nikeji ina tsoran abinda zan tadda wajen gimbiya Yazira da Uwani." "kiyi hakuri Bahijja tunda harkikazo a baiwa baki da wani ƴanci ko jin dadi haka zakije watarana sai labari ƴata." cikeda gamsuwa suka fita ita Jakadiya ta shiga wajen Sarki Baidulƙais ita kuma Bahijja ta wuce wajen gimbiya Yazira, Jakadiya na shiga ta fara rabama bayi aiki, shiko Baidulƙais tunda ya tashi ba wanda yake son gani kamar Bahijja yana shirin yaga shigowar ta saiga wata baiwa ta shigo dukawa tayi ta gaida shi, sannan tace. "Ranka shidade anturoni dan ingyara maka ɗaki." wani wawan kallo ya jefama baiwar tai saurin sadda kanta ƙasa tace. "tuba nike gamji ya huci zuciyar ka." kofa ya nuna mata hakan yasa taja kafafun tafita jiki a sage, shiko wani irin iska ta fidda mai zafin gaske, bata jima da fitaba saiga Jakadiya ta shigo itama gaida shi tayi sannan tace. " gamji yabaka hakuri naga baiwar dana turo ta fita shine nace.....ɗaga mata hannu yayi yace. "Jamra yaushe kika fara karyamani doka a cikin wannan Masarautar kodan kinga nabaki mahimmanci a matsayinki na Jakadiya ta wadda ta kwashe shekaru masu yawa tanai mani hidima.!"
"Rankashidade...."dakata Jamra ina Bahijja ban hanaki saka kowa yaiman aiki ba inba Bahijja ba."? "tuba nike Bahijja tana wajen gimbiya Yazira sannn kuma ta tashi batajin dadi." baisan sadda ya ɗago ya watsama Jakadiya wani mugun kallo ba yace. "Maza kikiramani Bahijja nan da minti ukku nabaki inbahaka nan ba zaki gamu da fushina!" ai da sauri Jakadiya har tuntube takeyi bata san ta isa wajen gimbiya Yazira ba tana zuwa duk bayin dake wajen suka gaida Jakadiya sannan sukabar wajen itama gaida gimbiya Yazira tayi nan ta faɗa mata sakon Baidulƙais bakaramin haushine ya kama gimbiya Yazira ba ta kalli Jakadiya tace. "Jamra na fahimci hadin bakin ku ɗaya da maimartaba wai mike haɗin ki da wannan munafukar yarinya ko kema dake za'a haɗa bako aci amana ta."? "Haba ranki shidade kinsan ba yanda za'ai inbujirema umarnin maimartaba amman ba yanda za'ayi inci amanarki." "kije tana baya." godiya taima gimbiya Yazira sannan ta tafi, tana zuwa ta iske Bahijja da Indo suna noma cikin lambu duk inda ciyawa suka fito cikin shuke shuke Uwani sai bala'i takema Bahijja tana ganin Jakadiya ta gaidata nan Jakadiya takira Bahijja suka tafi hakan bakaramin taɓama Uwani zuciya yaiba, suna isa suka tadda Baidulƙais zaune falo gaishe sukayi sannan Bahijja ta shiga cikin ɗaki tafara aikin ta......


tana cikin shara taji shigowar Baidulƙais bakaramin tashin hankali Bahijja ta shiga ba, jitayi yace. "Ke baiwa zonan." jikinta ne yafara kyarma tazo wajen Baidulƙais ta tsugunna tace. "Ranka shidade gani." cikin fushi yace. " waya baki ikon zuwa aiki wajen gimbiya Yazira."? murya na rawa Bahijja tace. "Ranka shidade itace tabani umurnin hakan tunjiya."
Sake kallanta yayi a sheƙe sannan yace. "Daga yau inna sake ganin ki, kinje wajen gimbiya Yazira na rantse da rawanin kakana Gursu saina halakaki karkiga ina baki kulawa kina yanda kikaga dama zan iya kasheki kinajina."?
Jiki na rawa tace. "Naji insha Allah bazan kuma baah." ta ida maganar ta a rarrabe da sauri yace.
"Minaji kinacewa."? "Bazan koma ba tuba nike." gyaɗa kai yayi ita kuma tacigaba da aikin ta baki ɗaya jitake kamar ta faɗi kasa dan kafafun ta sunyi sanyi dayawa tarasa wacce irin musuba ce ke bibiyar rayuwar ta yanzun shikenn tasan itama kasheta za'ayi kamar yanda aka kashe mata ƴan uwa dan sunyi yunkurin guduwa tasab tabbas dole gimbiya Yazira saitasa taje wajen ta inba hakaba abanza zatai mata illah da wannan tunanin taji Sarki Baidulƙais yace......




*Ƴar Mutan Kankia ce❣️*


Share
Comment
Vote


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*




Babi na 29&30



"Daga yau da karfe bakwai ki tabbata da kinzo aiki kuma bazaki bar wajen aikin kiba sai shidda na yamma kinajina."? da toh Bahijja ta amsa haka ta ida gyaran dakin sannan ta fita zuwa falo nan ta iske Jakadiya komawa gefe tayi ta zauna tana jiran fitowar uban gidan nata....


Bayan kwana biyu gimbiya Yazira ce zaune a dakin Sarki Baidulƙais ta, sai wannan kisisina takeyi kamar wata karuwa sai nanike mashi takeyi, shiko sai yakice yakeyi daga jikin shi, cikin kissa tace. "Mijina nikeso inasan wata alfarma agareka." batareda da ya kalleta ba yace. "Inajinki."


"Daman inasan wannan baiwar ka koreta ta koma Masarautar su nidai bataimani ba." "wakenan? Ƴar ƙinƙinace tazo mata tana sosa keya tace. "Bahijja mana ban kaunar yarinyar nan ko kadan natsaneta kataima.......daga mata hannu yayi yace. "Kinga wannan wane irin shashanci ne kinada hankali kuwa da zakice wai in maida Bahijja Masarautar su, kinsan wacece ita ko kinsan dalilin dayasa na anshi Bahijja karfa kimanta ɗana na cikina narasa mafi soyuwa agareni, daga yau kar inkarajin kin faɗi wannan maganar.!"


Jiki sanyaye tace. "Wai daman ba haka nike nufiba inason daman...."kinga Yazira kibar wannan zancen karma ki ɓataman rai."

Badan gimbiya Yazira tasoba ta hakura cigaba da bashi labarai tayi har rana ta fito jinanturo kofa yasa baki ɗaya suka maida hankalin su bakin kofa, Bahijja ce ya shigo cikin ɗakin tafara tattara kayan da tagani a ƙasa, gyaran muryar da taji anyi shi ya tabbatar mata da Sarki Baidulƙais yana cikin ɗakin daga kai tayi taga ita suke kallo wani irin mummunan faɗuwar gaba taji ganin irin kallan da gimbiya Yazira ke aika mata, a sanyaye ta duka ta gaidasu, wani ƙayataccen murmushi ya sakarma Bahijja sannan ya amsa itako gimbiya Yazira kallan kyama sa kaskanci ta dinga yima Bahijja a dakile ta amsa dan batasan mijin nata ya ɗauki wani abu a wajen ta, tashi Bahijja tayi zata fita waje Sarki Baidulƙais ya dakatar da ita, jitayi kamar ta saki fitsari a wando dan tsoro, maganar da yaimata shiyadawo da ita a tunanin ta, dawowa tayi ta duka har kasa ta sadda kanta kasa sannan yace. "Fara aikin ki ina zakije."? "Ranka shidade inaso infara wani aikin ne kafin kugama." kamar baiji abinda tace mashi ba yace. "Haɗamani ruwan wanka." ba tareda ta bari sun haɗa ido da gimbiya Yazira ba ta tashi simisimi ta haɗa Sarki Baidulƙais ruwan wanka. a ɗarare tace. "Ranka shidade nagama." takoma gefe a takure ta rakuɓe itako gimbiya Yazira cike da kissa ta kama hannun mijin nata suka shiga bathroom kamar jira Bahijja tayi sauri ta gyara gadon tabar dakin fita falo takoma nan ta iske bayi sai aiki sukeyi tana zama wata baiwa tana shara tafara share Bahijja jitayi ta caka mata tsintsiya akafa da sauri ta tashi tace. "Haba baiwar Allah inkikaiman rauni fa." kamar jira tafara bala'i. "Karki rainamani hankali kebakida tunani miyasa bazaki tashi bakoni zan ɗaukeki."? shiru Bahijja tayi itako sai jaraba takeyi kamar zata mari Bahijja, daman mugun haushin ta takeyi, tana cikin faɗa gimbiya Yazira ta fito tasha ado ta iske sai jaraba takeyi, suna ganin ta suka duka suka kawo gaisuwa."
Kallan tuhuma ta cigaba da yima Bahijja sannan tace. "Waike Bahijja wace irin hatsabibiyar yarinya ceke wai dame kikeji ne."? "Kimin aikin gafara daman...."daman me lallai yarinyar nan bakida hankali, ke Labuda inkin gama kizo kisamani a bangare na." "angama ranki shidade."
tafiya tayi tana sane ta buge kafar Bahijja ta tafi, itako Labuda tacigaba da yima Bahijja masiba tashi tayi ta koma gefe ɗaya nan ma binta tayi tacigaba da bala'i itadai Bahijja batace komai ba tana cikin bala'in ta sukaga Baidulƙais yana kallan su.

Kowa saida yasha jinin jikin shi baki ɗayan su, suka zube ƙasa suna neman afuwa baice masu komai ba wucewa yayi ya koma cikin falon shi ya zauna kafa ɗaya kan ɗaya sannan yasa aka kira mashi su Bahijja suna isowa yaima Labuda wani mugun kallo saida ta firgita jitayi kamar ta saki zawo a wando kallan Bahijja yayi wadda tagama tsorata dan tunda yace zai kasheta intakara yima wani hidima take kara tsoron lamarin Baidulƙais acewar ta ko laifi tayi zai iya kasheta, maganar da taji yayi taji ta dakar mata dodon kunne a ruɗe ta kalle shi, shima kallan ta yayi yace. "Eh Mararta nace." yanda taga fuskar shi ba alamun wasa shiyasa ta mike ta mari Labuda a hankali duk tsoro ya kamata saboda uwar Labuda aminiyar Uwani ce Uwar bayi shiyasa take shakkar taɓa Labuda, tsawa Baidulƙais ya dakama Bahijja aiko duk takara ruɗewa yace. "Ko sai na gwada akan fuskar ki sannan zaki mararta."?


Hannun Bahijja na kyarma ta kwadawa Labuda wani irin masifaffan mari mai ruɗarwa, hatta Bahijja saida ta gigita dan batai tinanin zata iya marin Labuda ba, ji tayi yace karamata, kwalla Bahijja takara dan tsoro haka ta sake wanke ta da wani marin saida yasa taima Labuda mari yakai huɗu sannan yasa aka kira mashi Sarkin bulala saida akaima Labuda bulala talatin danko Bahijja kamar ita ake duka dan tsoro ga wasu kwalla dake sintira asaman kumatunta dan bata fidda rai ga duka ba, aiko saitaji Sarki Baidulƙais yace. "Yimata bulala ashirin." take ciki ya ɗuri ruwa sai mursiku takeyi Sarkin bulala na tunkaro Bahijja ta fasa kara da kuka tana neman ɗanewa jikin shi bakaramin mamaki ya kama Sarki Baidulƙais ba yana mamakin kalar tsoro na Bahijja inaga ita aka daka kila sai ta mutu ganin tana neman cakume Sarkin bulala yasa shi dakatar dashi, yabashi izinin tafiya da wani irin kallo yabi Bahijja duk ta gama fita tinanin ta baki ɗaya sai zabga uwar zufa takeyi ganin yanda duk damuwa ta bayyana a kan fuskar Bahijja yace. "Ke baiwa bata hakuri." haka Labuda taba Bahijja hakuri, sannan yace ta tashi ta tafi, kallan Bahijja yayi sannan yace. "Tashi kije gida, wane irin abune haka ya kamata kirage tsoro kodan lafiyarki." da sauri ta gyaɗa mashi kai ta mike ta tafi shiko da wani irin shu'umin murmushi yabita ganin yanda takeda tsoro ga wata irin masifar shi'awar Bahijja yanayi a wani ɓangare na zuciyar shi yana ganin bari yabari takara kwari sannan ya cimma burin shi.


A Masarautar Waisu kuwa yarima Haishir ne keta zagaye zagaye yakasa zaune yakasa tsaye tunda suka dawo daga Raifasu kullin da Bahijja yake kwana yake tashi a cikin zuciyar shi ganin lamarin na neman yafi tunanin shi hakan yasa ya tafi sashen Mahaifin shi ya iske shi kishingiɗe yana shan kankana yanda yaga Yarima Haishir kaɗai hakan ya tabbatar mashi da ba lfy, cikin kulawa ya kalli dan nashi yace. "Lafiya ka tsaya akaina meke damunka Ya Haishir."?



"Zaman dirshan yayi kamar wani zautacce yace. "Baba daman wannan itace kaunar da kake nuna mani kabarni da son yarinyar nan a zuciya ta ko kasan yanda nike masifar kaunar Bahijja, da ace a wannan Masarautar take da yanzun nagama kashe kishir ruwana akan ta."
Cikin jin haushin maganar Haishir Sarki Lahazu yace. "Ban haneka da neman matan banza ba wato itama wannan yarinyar bada aure kake son taba kenan."? Shiru yayi aranshi ko cewa yayi nidai indai zanjini a tareda ita nayi nasara ai banda damuwa kotaya tazoman dai dai ne, Amman a zahiri cewa yayi. "Gamji ya huci zuciyar ka, amman inaso ka amso mani Bahijja daga wajen wannan wawan sarki Baidulƙais din." cikin gamsuwa yace. "Baka da damuwa ɗana koda zan rasa raina yanzun so nike nan da jibi mutafi Masarautar Daborah dan sanin halin da muke ciki hakan yasa na aika ma Sarkin Ƙaisu da wasika dan bansan Sarauniya Zulaiƙa tayi tunanin kawai wata akasa shiyasa kasanta mace ce mai kaifin tunani da basira uwa uba wannan mijin nata akwai fikira." "shikenan Baba amman kai kaɗai zakaje ko."? "Aaa Haishir dakai zani inasan kasaki jiki da Yarima Malik sannan kayi abota dashi dan cimma burin mu,dan haka ya kamata ka sake tako, ya kamata a halin yanzun kamaida masoyi makiya, sannan makiyin ka kamaida shi masoyin ka ta hakane kaɗai zakayi nasara kan abokan gaba ka hanasu sukuni ka rike wannan ilimin Ya magajina ɗana abun alfaharina kaidai daure kashiga tsara ka koma Jarumi kamar Yarima MalikusSaif shikenan zakayi sunan aduk faɗin duniya da nahiyar mu harma da kasarmu ta Gambia."


Wani irin dadi ne ya rufe Haishir saijin dadi yakeyi yana mamakin kalar fikira da dubara ta Mahaifin nashi......


Washe gari da safe tunda Bahijja ta tashi ta tafi wajen aikin ta, akan hanya suka hadu da Uwani sai maman Labuda da wani mugun kallo suka dinga jifar Bahijja jiki sage ta samu tacigba da aikinta kamar yanda ta saba.....



A Masarautar Daborah kuwa yauma Malik ne zaune a falo ya rasa gane damuwar shi kullin tunanin shi halin da Bahijja ke ciki musamman a ɓagaren addinin ta, tunda ya aiki Ashir kullin tunanin ranar dawowar shi yakeyi dan a halin yanzun harya fara sirin tafiya wajen neman Bahijja batareda kowa yasan kudurin shi ba....



Yau da marece Ashir ya shiga cikin Masarautar Raifasu a sirrince batareda da kowa yasan ya shigo ba haka ya shige cikin bayin Masarautar yayi basaja dan genema idan shi abinda Yarima Malik ya turoshi nema a cikin Masarautar Raifasu, a ranar ya iske wani bawa mai suna Ƙubar yana ansar bakar ukuba a wajen Sarkin bulala dan ya buge kayan gimbiya Yazira ba tareda ya gani ba shine ake gana mashi azaba tun rana har yamma hakan ya ɗagama Ashir hankali duk da yasan ba wani abu bane dan anmasa wannan dukan, saidai a ganin shi wannan ba wani abun da za'ace har anmashi irin wannan ukubar ba, suna cikin kallo ya haɗu da wani bawa Anzir nan yake tambayar Ashir daga ina, a wayance yace nan yake shima baisan Anzir din ba, bakaramin mamaki yayi ba ganin kaf taskar bayi ba wanda baisan shi amman ga Ashir yace baisan shi ahaka suka fara sabawa koda dare yayi tare suka tafi wajen ƴan uwan shi suka kwanta.......




Washe gari da rana haka Ashir ya kara fitowa yana ƴan dube dube ko Allah zaisa yaga Bahijja a cikin Masarautar Raifasu koda cikin taskar bayi ne amman bai ganta ba, hakan yasa ya fito yawo a cikin taskar bayi yana cikin tafiya ya samu wata bishiya ya zauna dan hutawa, itako Bahijja ta gama komai zaune take tamaima Baidulƙais fita yana kishingiɗe sai wannan cika yakeyi yana batsewa, nan Jakadiya ta shigo da bayi kowa ɗauke da abinci haka Bahijja ta zubama Baidulƙais abinci saidai wannan karon Allah yasota da kanshi yaci ita kuma tacigaba da yimashi fita....


Shiko Ashir koda ya zauna gefen wannan bishiya yana cikin tinanin ta inda zaifara duba Bahijja yaji ankira sunan shi a ruɗe ya waiga yana kallan mai kiranshi wanj bawa ne yagani daga cikin bayin su waɗanda akaba Baidulƙais suda Bahijja da sauri ya riko hannun bawan yana mai rufe mashi baki suka zauna gefe cikin ɗimauta Ashir yace.

"Tasi'u daman

Please Login or Register in order to submit comment