Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uwar kara da hayaniya na tashi gwanin tsoro amman haka Saifulislam suka cigaba da tafiya cikin dajin ko tsoro basuji wani uban wulgi suka gani ya wuce ta gaban su, cikin gafin nama Sarauniya Zulaiƙa ta kai uwar sara da takobi, take takobin ta lauye ji sukayi baki ɗaya anɗago su sama daga saman doki anyi wurgi dasu saman katan icce Sarauniya Zulaiƙa ta faɗa tashi tayi da sauri ta ɗauko lauyayyar wuƙar duk wani irin bakin jini daskararre, taɓeta akayi ta faɗi kasa akadinga janta kasa gashi bata ga mai jantaba, da sauri Saifulislam ya tasu yai saiti ɗana kibiya a saitin da akejan Sarauniya Zulaiƙa da wani uban ihu yaji ankwaɗa sannan ya rungumo Zulaiƙa sai addua yakeyi itama binshi takeyi sai wulge wulge da ihu ake masu, duk tsoro ya kama zuciyar su, wata uwar dariya suka tsinkaya ankai minti talatin ana abu guda sannan sukaga wani irin ingarman zaki a gaban su, a gigice Saifulislam ya zaro takobi ya wullama wannan zakin ya sameshi a kafa wata irin kuwwa da gurnani zakin nan yayi ya tunkaro Saifulislam, cikin gafin nama Sarauniya Zulaiƙa ta ɗauko takobi tayi saitin wuyan zakin nan ta ɗana a saman makoshin shi rigijib ya faɗi sai shure shure yakeyi wani tankameman mutun sukaga zakin ya koma cikin kankanin lokaci ya ɓace, rike hannun Saifulislam Sarauniya Zulaiƙa tayi ta rufe idanta da sauri suka ɗauki takobin suka fara gudu zasu fita cikin dajin Gamki sake wurgi akayi dasu suka gansu wajen wani ruwa ga maganganu marar sa dadi anayi cikin kausassar murya akace. "Zulaiƙa kinyi wauta dahar kafarki ta tako Masarauta ta batare da Malikussaif ba kinzo ne dan ki ɗauki fansa to yau dinnan saikin san kinzo turakar Sarrilkus Hhhhhhh aljani ɗan tsitu aikin ka yanzun zai fara." kankame juna sukayi itada Saifulislam sukaita addua kamar ba gobe koda aljani ɗan tsitu yayo kan su Saifulislam, jisukayi guguwar ta lafa komai na dajin yai shiru buɗe ido sukayi sukaita addua ji sukayi magana a firgice. " zasu ƙonani ya Sarrilkus kataimake ni nakasa shan jinin su, ihuhu wulakantattu ne kaimani rai inbisu har masaukin su dan kashe su."

Take wata guguwa ta turnike kamar me duk sun ruɗe da kyal Saifulislam ya lalubo takobi ya rike a hannun shi ji sukayi kamar suna sararin subhana cikin kaftawar ido suka gansu a zubdasu saman wani yayi ga uban haske rufe idanun su sukayi sai hasken wuta ketashi ji sukayi ance. "Badai a dajin Gamki zaku dinga yimana addua ba, da kanmu zamu halaka ku dan haka ku shirya zuwan tawwagar Sarrilkus sai munga bayan ku, hhhhhhh.'' take sukaga wannan hasken wutar ya ɓace cikin tsoro Sarauniya Zulaiƙa takara rungume Saifulislam addua yai tayi ɗaukar wukar da suka yanki wulgin da akai masu yayi sukaita tafiya mai nisa sannan suka hangi dawakan su, hawa sukayi duk zazzaɓi ya rufe Sarauniya Zulaiƙa haka suka tunkari Masarautar Raifasu cikin kaɗuwa da shakku fatan su susamu ɗansu Yarima Malik cikin aminci.

Suna isa cikin Masarautar suka wuce dakin da Malikussaif ke kwance su Yazid ne atareda shi sai Bahijja dakema Malik tausan kafafu zuwa yanzun kam takai shekara bakwai a duniya yanda sukaga su Saifulislam, saida suka tsorota jikin su duk jini kowa tashi yayi akai gaisuwa sannan malamin dakema MalikusSaif magani yace. "Ko andace da jinin ko wane halitta ne na dajin Gamki."?

Jikin Sarauniya Zulaiƙa ba kyarma tace."andace."....."Malan andace sai dai bamusan ko andace da dai dai ba gadai takobin nan hannuna." cewar Saifulislam ya mikama malamin takobin karɓa yayi yasata cikin wata ruwa sannan ya tofa addua ya ɗauko ta sai hayaki takeyi ya buɗe sukar da akaima Malik a ciki ya zuba wannan ruwan dake ɗiga take wajen yayi baki sai halbe halbe Malik yakeyi yana fidda kumfa a bakin shi ga hayaki na fita baki ɗaya hankalin kowa ya tashi tsabar kaɗuwa hatta malamin da sauri Zulaiƙa ta rungumo MalikusSaif jikin ta shiko Saifulislam ɗauko Malik yayi yana tayi mashi addu'a ji sukayi cak bugun kirjin Malik ya tsaya ko numfashi baiyi, da karfi Sarauniya Zulaiƙa ta girgiza MalikusSaif wadda zufa ya gama wanketa dan tsoro da fargaba, ganin yanda su Yazid ke kwalla yasa Bahijja ta kama hannun MalikusSaif tana kuka tana kiran. "Ya Malik katashi kada kabarmu." itako Zulaiƙa ta gama kiɗimewa da ganin halin da Malik yashiga kamar matattace sake girgiza shi tayi ta fasa uban kuka tana cewa.......


*Salon kuyi man kuka haka labarina yazo sai kuyi hakuri dan koni Yar'mutan kankia mutuwa zanyi balle MalikusSaif 👹🌚*



*Yar Mutan Kankia ce❣️*


Share
Comment
Vote


*BAYI MA 'YA'YANE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
__________________


*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

*Sakon ta'aziya zuwa ga yar'uwa kuma ƙawata dan kin wuce na kira da suna Fan sai da yar'uwata Yar'gatan Momyn sultan, Allah ya jikan Baba yasa mutuwa ta zamo hutu a gareshi, ya jikan dukan al'umar musulmai Amin🙏*


Babi na 14





"Malik kaitaimaki rayuwata kaine farin cikina karka barni Ya Malik kaine gatan Masarauta Daborah na shiga ukku." wani mugun tari Malik yayi ba kaukautawa baki ɗaya bayin Masarautar su suka zagaye su sai kuka sukeyi masu Addu'a nayi kowa da abinda ke damunsa shiru ne ya biyo baya duk wanda kagani a cikin su kasan yana cikin matsanan cin damuwa Sarkin yaki Baru ne yafita wajen Baidulƙais yaje yana zuwa ya shako shi ya kawo shi wajen MalikusSaif take Jarumai suka zagaje Baidulƙais da takubba magana Sarkin yaki yafara a fusace. "Ya Baidulƙais nasan kanada sirrinkan ganin Sarrilƙus dan haka ka kirawo shi zuwa ga yarima mai adalci mai kishin bayi da sauran talakawa karkayi anfani da wannan damar dan cimma burin ka saidai kasani karya wannan sihirin shi zaisa ka koma da mulkin Masarautar Raifasu kamar yanda kadimul islam ya faɗa."cikin girman kai da gadara yayi dariya mai sauti kamar wani mahaukaci ya kalli Zulaiƙa tana jikin Malik sai hakin kuka takeyi wanda gwara gawa da Malik a halin yanzun, saida ya gama dariya mai isar sa sannan yayi tafi da hannun shi yace. "Zulaiƙa harkin saduda kenan ya kikaga ni ainafaɗa maki da inrayu da inmutu duk ɗaya naimaki alkawali yanda narasa Farin ciki kema kinyi bankwana dashi koda kuwa yarima Malik yarayu ya kikagani Zulaiƙa ina baki Shawara kibi shawarata tunkan dare yaimaki dan haka barganin kunci galaba akaina Zulaiƙa kiyi tunanin dole in miki biyayya aaa kinyi kuskure a halin yanzun ke kenema a wajena dan haka imhar kunasan yarima MalikusSaif ya rayu sai kunbi sharuddana sannan."


Cikin gamsuwa da garaje Safulislam yace. "Mun amince nidai rayuwar ɗana nike bukata tafiyemani komai kafaɗi ko minene zan baka ya Baidulƙais." tafiya yakeyi cikin gadara yaje kusa da Malikussaif ya shafi fuskar shi sannan yace. "MalikusSaif kenan ya kagani gwara matacce dakai ko? Naji abunda kace inason fansar ran ɗana Husbarul shine bukatata da farko inhar kunji zakuyi mani ita Shikenan ko yau din an Sarrilƙus yana iya zuwa saidai kuma dole ku tabbatar dani a kan mulkina da Masarauta ta, sannan inada bukatar bayi daga cikin Masarautar ku shikenan kungama mani komai ya kuka ga bukatar tawa saidai karku manta ku danganta ta da rayuwar ɗanku MalikusSaif da kuma bukatar tawa." shiru ne ya biyo baya duk da kowa yasan bukatar tasu mai wahala ce amman hakam baisa sunyi kasa a guiwa ba cewa Zulaiƙa tayi. "Sai dai kasani za'ai maka fansar danka amman bazan baka bayina ba sai dai za'a fanso maka konawa ake saida bayi a kasuwa in haka yaimaka shikenan."

Murmushin raini Baidulƙais yayi sannan ga girgiza kai. "Zulaiƙa banda bukatar wani bawa akasuwa daki bani bawa dari a waje gwara kubani bawa goma a cikin rundunar bayin ki,amman inkina ganin bukatata tafi rayuwar ɗanki mahaimmanci shikenan saiki zaɓa Zulaiƙa, zan iya tafiya kafin kiyi tunanin da zai anfanar dake."


Juyawa yayi zai fita Safulislam yace. "Karka tafi Baidulƙais ai bukatar ka tafi komai sauki a cikin bukatar da kanema sai dai bayi kamar nawa kake so."? wata irin shu'umin murmushi yayi sannan yakara kusa da Safulislam yace. "Naji dadin abunda kace sai dai a wannan fagen so nike inba Sarauniya Zulaiƙa umurnina tabi ya Abu Malik."

Kamar Zulaiƙa bazatayi magana ba tace. "Abinda mijina yace shine zaɓina dan haka kafada bayi nawa kake so." dariyar iskanci yayi mai sauti sannan ya kuma cewa. "Kina kyautawa kanki da kikabi umurnina Zulaiƙa bayima goma sun isheni, saidai inasan ki haɗaman da amintattun bayin ku guda biyu saidai banyarda kici amana taba yanzun nan zakiga Sarrilƙus yazo har wajen Malik ya kikace Zulaiƙa."


Cikin gansuwa ta amince take Sarauniya Zulaiƙa tasa Sarkin taska ya dibo kudi masu yawa wanda basu iya ƙayyadece su taba Baidulƙais sannan taba Sarkin bayi Abdulmajid umurnin bashi bayi goma haka ya lissafo cikin rundunar bayin su, yaba Baidulƙais sai dai ya nuna guda a cikin su yace baimai ba, cikeda da kosawa Sarauniya Zulaiƙa tace ya canza da kanshi abin mamaki take Baidulƙais ya nuna BAHIJJA, dake gefen kafar Malik dan kamar ita ke jinyar Yarima Malik, duk yanda Sarauniya Zulaiƙa ta tsani Bahijja saida taki amincewa da rabuwa da BAHIJJA musamman Safulislam danko Binta kuka tafarayi mai cinrai ganin za'a rabata da ƴarta duk wanda ke wajen saida ya girgiza banda Bahijja da batasan inda maganar ta dosa ba, Sarauniya Zulaiƙa tace. "Kacanza da wata amman banda Bahijja." cikin mugunta yace shifa da Bahijja zai tafi kuka wuwi Binta keyi take Sarauniya Zulaiƙa tafara jin tausan Binta a rayuwar ta ganin yanda za'a rabata da ƴarta saboda ta ɗanɗani ɗacin rabuwa da ɗa ganin zata rabu da ɗanta, cikin tausayi Zulaiƙa tace. "Gaskia muddin zaka ɗauki Bahijja saidai kahaɗa da mahaifiyar ta Binta katafi dasu." duk wanda. Ke wajen saida ya gamsu hatta Abdulmajid, maganar da Baidulƙais yayi shiya dawo dasu a cikin tunanin su. "Bansan mahaifiyar ta kurike ita nike bukatan koda ace zaku hanani kudin fansar ran ɗana, a sanyaye Sarauniya Zulaiƙa tace. "Binta duk da kasancewar ki baiwa ta wadda nafi tsana saboda wasu dalilai kinji abinda Baidulƙais yace, amman ba zan yake hukunci ba har sai abunda kike ce shi za'ayi dan ba zanso na rabaki da yar'ki ba." cikin sanyin murya Binta tace. "Haba ya uwar dakina wannan shike nuna rabani da ya'ta har abada kenan ya zanyi inama banzo abaiwa ba inama mutuwa nayi na huta inama banga wannan ranar ba saidai banda zaɓi sai abunda kukayi lallai Bahijja tun jinjirarki ajali ke bibiyar ki Bahijja ga mai tausanki bai lafiya bare ya baki kulawa ta musamman Allah yazama gatanki marainiyar Allah gashi anrabaki da iyayenki Bahijja tabbas har yanzun nakasa yarda da maganar da Yarima MalikusSaif keyi na bayima 'ƴa'ƴane tabbas banga ranar da bayi zasu zama 'ƴa'ƴaba." ta karashe maganar tana kwalla da takaici sannan ta rungume ƴarta sai kuka sukeyi.

Bayan kwana biyu, aka tashi lamarin Malik yakara ta'azzara hankalin kowa yagama tashi musamman Sarauniya Zulaiƙa da tagama fidda rai da rayuwar ɗanta Malik tashi yayi yana ta aman jini bakin kirin kamar gawayi ga numfashin shi yana ta ɗaukewa kamar zai mutu baki daya sun zagaye Malik cikin kankani lokaci banda kuka ba abinda Binta keyi ita da Bahijja ga Sarauniya Zulaiƙa tsoro da fargaba sun sa tafara suma danko Saifulislam yana rungume da Malik da yagama sheɗewa dan wahala kowa yagama sadudu da lamarin ana cikin haka Binta tafita da gudu zuwa wajen Baidulƙais tana isa ta zube sai uban kuka takeyi cikin gadara yace. "Baiwa mike tafe dake har haka."? cikin sarkewar murya Binta tace. "Na'amince da Bahijja tazama baiwarka kataimake mu karmu rasa MalikusSaif a halin yanzun yana bukatar mu sadaukar da duk wani farin cikin mu." cikin jindadi yayi dariya yace. "Tabbas baiwa sai dai muje inji ta bakin Sarauniyar ki." haka suka tafi yana gaba tana biye har ɗakin da Malikussaif yake kwance lokacin Sarauniya Zulaiƙa tagama galabaita ta suma yafi ukku da kyal ta farfado sama da awa ukku sannan ta buɗe idonta ta azasu akan Baidulƙais da sauri ta mike kamar wata zakanya ta cakumi wuyan Baidulƙais takai mashi wani wahalalan duka takara dunkulo wani Saifulislam ya rike ta sannan tace. "Uban wa yakawo ka wajen ɗana kazo danka karasa mani shi."!? cikin sauri Binta tace "ya shugaba ta ni nataho dashi dan ceto ran MalikusSaif fansa ga ƴata *BAHIJJA* kodan kulawar da yake mata sannan rayuwar Malik arziki ce ga kowa Allah kaɗai yasan wanda zai taimaka nan gaba ciki ma yake sai dai ina fargabar makomar addinin ƴata, ammn na amince ya ɗauki Bahijjaa matsayin baiwar shi." takarashe maganar tana kuka mai tsuma zuciya, mikewa Sarauniya Zulaiƙa tayi ta matso kusa da Baidulƙais tace. "Zamubaka Bahijja saidai kasani inada sharuɗɗan da zan gindaya maka sune na ɗaya karkayi anfani da damar daka samu a wajen mu wajen sauyama Bahijja addini ko kuma laalcewar mutuncin ta, sannan karka manta da yanda ka anshi Bahijja bayan fansar ta da zanyi da bayi dubu akan ta amman ka nace sai ita dole kabata wannan damar da nagindaya maka mutuncin ta da addinin ta, kaikayi naka itama tayi nata inhar ka amince ni Zulaiƙa zan cika maka alkawali."


Shu'umin murmushi yayi cikin gamsuwa yace "na amince fatana Bahijja ta dawo a karkashin ikon Masarautar Raifasu hakan zaisa zuciya ta daina yin ƙuna akan rashin ɗana duk da fansar shi da zakuyi."

Saifulislam yace. "Ni ban amince ba da fansar Bahijja a baiwa ba, akan Malik duka duka nawa Bahijja take da za'a rabata da mahaifiyar ta dan haka kafaɗi ko nawane ni Saifulislam nayi alkawali zan baka fatana abar Bahijja wajen mahaifiyar ta." wani kallo Baidulƙais yayi ma Saifulislam na baka da hankali inada burin nawa zan rabu da Bahijja baku da wayau a zahiri cewa yayi. "Aaaa ban bukatar dukiya ita nike bukata ta zama hadimata duk da naga ba shekarune da itaba amman ai zatayi anfani inhar baku shirya ba shikenan ku rike ɗanku da baiwar ku ni kuma inrike damata."


Da sauri Binta tace "Allah yataimaki shugaba na kayi hakuri kabar wannan maganar kome zai wuce inda har Allah yakawo Bahijja a baiwa ba ko shakka tana cikin kalubale ka rabu da ita da sannu zata saba da rashin iyaye zan mata addua dacewa akoda yaushe kamar yanda mahaifin keyi mata, kabari a ceci rayuwar Yarima MalikusSaif narokeka."


Saifulislam baikuma cewa komai ba sai goge kwalla da yayi da tausan Bahijja a cikin zuciyar shi, nan Saifulislam yasa aka ɗauko wata jikkar kudi akaba Baidulƙais sannan aka yarje mashi Bahijja sai kuka su Yazid sukeyi shiko sai jindadi yakeyi mikama bawan shi jikar kudin yayi sannan yace. "Inada sharadina akan ku matukar kuka samu maganin cutar Malik ina gargaɗar kuda kuyi gaggawar barin Masarauta ta, sannan karku taɓaman mutane na da bayin ku da kuka bani guda tara duk da Bahijja goma in kun amince yanzun boka Sarrilkus zai bayyana a gabanku." take Sarauniya Zulaiƙa ta amimce ganin yanda jikin Malik yakara tsanani, wani zobe ya ɗebe a hannun shi bakikkirin ya murza take wajen ya hargitse sai wata uwar ƙara ke tashi kayayyakin ɗakin suna ta fashe wa suna komawa toka kowa ya gama hargitse wa dan tsoro wata uwar guguwa da walkiyar tsafi ta turnike wajen Baidulƙais ne cikin tsoro da ya kiɗime mashi jiki yace........






*Yar Mutan Kankia ce❣️*




Share
Comment
Vote



*BAYI MA 'YA'YA'NE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________
*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



Babi na 15


Baidulƙais yace."Sarrilƙus Danzir aljanni ɗansitu bayyanarku agareni dace ku nike jira hhhhhhh ihuhuhuhhhhh ni Baidulƙais."
Wata uwar tsawa aka saki mai razanarwa sannan wani katon toron giwa ya bayyana cikin kankanin lokaci ya rikiɗe ga koma tafkeken gadangare bayan shi da wasu manya manya mutane bakake guguwar takai minti talatin sannan wannan kadangaren ya koma wani basamudan mutun kowa saida ya tsorata sannan wata walkiyar tsafi ta taso ya ɗauki Bahijja da Baidulƙais su kuma sauran matsafan suka ɗauke bayin da akaba shi da Haishir wata magana ce aka fara mai ruɗarwa akace. "Sarauniya Zulaiƙa kin cika alkawali dan haka ga maganin ciwon MalikusSaif nan dan haka kusan yanda zakuyi anfani dashi muddin kuka samu matsala Malik zai iya mutuwa dan haka nan da awa ukku, ku gudu daga Masarautar Raifasu ko in turo maku rundunar aljanu hahhhhhh saini Sirrilƙus hhhhhhhh."

Take ya ɓace sannan aka saki maganin ya faɗo a saman MalikusSaif da gudu Sarauniya Zulaiƙa tabi wannan walkiyar har sun ɓace, take Binta ta faɗi a sume ba rai dan fargaba Abdulmajid ya rungume matarsa ya saki marayan kuka sannan suka ɗauki maganin a daburce Sarauniya Zulaiƙa ta mikama malamin dake ba Malik maganin lokacin hankalin Malik yagama futa daga jikin shi kowa yayi kanshi aka farayi mashi maganin cikin fargaba.

koda su Baidulƙais suka ɓace ba inda suka sauka sai cikin ƙurgunmin dajin Gamki sai walkiya wajen keyi ga tartsatsin wuta yana tarwatsa,danko Bahijja tagama suma dan fargaba da tsoro baki daya jikin ta yayi sanyi ganin wata halitta da tayi agaban ta yasa ta kankame jikin ta tafara kuka tace. "Kumai dani wajen Umman ta tsoro nikeji!." fashewa da kuka tayi tsawa Baidulƙais yayi mata duk tsoro da fargaba ya gama kama ta sai ƙyarma takeyi ganin wata halitta tayi agabanta ita ba mage ba kuma ba kare ba addu'a Bahijja tafara a cikin zuciya tsabar firgita yasa tafara fita waje bata sani ba, wata irin razanan nar tsawa Sarrilƙus ya dakama Bahijja har fitsari ya fara zubo mata a wando dan tsoro jin wata muguwar tsawa da magana mai kaushi tafara magana. "Ke yarinya kibar yi mana wannan abun naku inba hakaba yanzun nan zan maidaki ƙura abin shekarwa kinaji na."

Da sauri ta ɗaga kai alamar eh haka taita kukan zuci ga tsoro ya kama zuciyar ta da fargaba, a wajen su Malik kuwa maimagani tsoro ya hana saka ma Malik a jiki gudun kadda a samu matsala a rasa shi addu'a yafara yana tofawa sannan ya rufe ido ya saka maganin wata uwar tsawace ta karaɗe ɗakin gwinin tsoro cikin jikin Malik hayaki ne baki ke fita sannan wani zare baki ya fita yayi sama ya ɓace sai haki yakeyi ga zufa tagama rufe MalikusSaif wata irin kyarma ya kama Malik kamar zai mutu, rufe shi Sarauniya Zulaiƙa tayi sukaita yimata addu'a kowa da abin da yake saƙawa a cikin zuciyar shi.


Bayan wasu awanni Yarima Malik ne yayi ajiyar zuciya mai karfin gaske tareda salati abakin shi ya buɗe ido yana ta kallan mutane kamar wani baƙo can yace. "Umma ina nike mi nikeyi anan wajen."?


Cikin farin ciki Sarauniya Zulaiƙa ta rungume Malik, shima Saifulislam cikin farin ciki ya rungume ɗan nashi sai murna yakeyi haka kowa yaita murna kamar ba gobe, dan murna haka malamin nan yasa akayi addu'a aka godema Allah, kuɗi Sarauniya Zulaiƙa ta mikama wannan malamin sai godiya sukema mashi haka ya tafi shiko Malik ruwa su Yazid suka haɗa mashi yayi wanka ya sake kaya, Binta ta shigo gaishe da Malik cikin sakin fuska ya amsa sannan yace. "Umman Bahijja ya fama da jama'a ina Bahijja batazo duba yayan nata ba."? Cikin kulawa tace. "Nabarota wajen Baban ta, daman ta gaji."

"Gaskia ai kwara ta huta ina ruwan Bahijja ai tana kokari." murmushi Binta tayi sannan ta tashi zata fita tsaya taga Sarauniya Zulaiƙa a bakin daki, cikin sakin fuska Binta ta gaisheta ta amsa karasowa tayi cikin ɗakin tareda ta dafa Malik sannan tace ya ɗauki abinda yake bukata zasu wuce gida, cikin jin dadi yace. "Yaww Umma yakamata mu koma masarautar mu hakanan."

Labari sukaci gaba dayi cikin so da kauna da misalin karfe biyu kowa ya shirya harda bayin su, suka fito suka ɗauki hanyar tafiya Daborah ko tsinke basu ɗauka ba da sunan ganimar yaki, itako Binta daurewa kawai takeyi hankalin ta na wajen ƴarta fatan ta Sarki Baidulƙais ya dawo da ƴarta a cikin Raifasu tasan insha Allah zata samu abinda takeso tsoro takeyi kar a halakar mata ƴa da wannan tunanin ne suka fita Masarautar Raifasu zuwa Masarautar Daborah.


tafiya sukayi mai nisan zango sannan suka isa Masarautar Daborah Sarkin kofa ya buɗe masu suka shiga kowa ya nufi sashen su bayan aje dawakan su da sukayi, itako Binta da Abdulmajid turakar bayi suka wuce su dasu ladidi da sauran bayin da akai tafiya dasu, jikin su a sage duk guiwowin su sunyi sanyi musammn da suga shiga ɗakin su sukaga ba Bahijja kuka Binta ta fasa maicin rai sai lallashin ta Abdulmajid keyi su Ladidi ne suka shigo sukaci gaba da ba Binta hakuri kayan wasan da Malik ya taɓa sayama Bahijja ta ɗauko tana kallo sai kewar ƴarta takeyi ga zuciyar ta na dukan tara tara magana tafara cikin tashin hankali "Kaicona ni Binta nayi asarar bada ƴata da nayi munɓata lokuta masu nisan gaske wajen tanadama Bahijja farin ciki ashe a banza tunda mungaza tsayawa mu jajirce mu nunama duniya itama ƴace kamar kowa amman mungaza tabbas Bahijja bazata taɓa yafemana ba batayi dacen iyaye ba, kaicona."
Cikin kosawa ga bakin cikin rabuwa da ƴarsa Abdulmajid yace. "Haba Binta me kike faɗi anya kina cikin hankalin ki da tunani kuwa kinsan abinda kikeyi? Menene a cikin dan munbada ƴarmu zatayi bautar baiwa a wata Masarauta karfa kimanta Bahijja baiwa ce, Malik fa? Ko kin manta mu dukan mu a kalkashin ikon Sarauniya Zulaiƙa muke, karfa ki manta mu bayine kuma bamuda ƴanci, ina laifi dan munbada Bahijja akan fansar Malik karki manta yaron nan da ya fanshi ƴarki a lokacin da gaf take da mutuwa sannan ya fanshi iyayen ta duk dan farin cikinta damu kanmu kodan haka ba mun sadaukar da Bahijja ba akan Malikussaif ba, dan Allah kidaina wannan maganar sai indinga yimaki kallan butulu, kisan me yadace kifaɗa matata addu'a itace gatan Bahijja kuma da yardar Allah saita dawo cikin Masarautar Daborah."


Cikin jindadi da samun kwarin guiwa Binta tayi murmushi sannan tace. "Maraba da samun miji haziƙi jajirtacce kuma fasihi lallai Baban Bahijja kacika kutun harda rabin mutun yanzun nakarajin tafiyar Bahijja akwai nasara tunda Yarima Malik ya tashi sai addua zumuyi ma yarmu Bahijja tabbas ina jinjina mijina."


Rungume ta yayi yana shafar bayan ta sannan su Ladiyo suka zauna akai ta ƴar fira dasu kowa na faɗin albarkacin bakin shi har dare yayi kowa yayi sallama da junan su, suka tafi makwanci kafin zuwa asuba su koma bakin aiki kamar kullun...


Bayan kwana ukku, dajin Gamki ne yayi tsit bakajin kukan komai sai tsuntsaye ga duhu saidai duhun bai hana kaga na kusa dakai ba, Bahijja ce zaune saman wata itaciya ta maƙure waje ɗaya duk da ta daina jin tsoron dajin sosai ganin ba abinda ke cutar da lafiyar ta, wani bakin mutun ne ya kawo mata wani kalar abinci ba kyaun gani ya aje mata, ko magana bai mata ba ya juya ya tafi tana kallan abincin nan ta rufe ido sai hawaye takeyi shiko Baidulƙais yana tareda da boka Sarrilƙus suna magana a saman tabirin dutsen kuka cema boka yayi. "Gurfanai ya taimakeka uban gidana yakamata ace yau nakoma Masarauta ta dan cigaba da gabatar da mulkina tareda sauran bayin nan, dan samun bayin Zulaiƙa bakaramin nasara bane a wajen mu munsamu babbar dama da zamu cimma burin mu akan Sarauniya Zulaiƙa ta Yarima Malik."
Shiru Sarrilƙus yayi sannan yace."Kwarai kuwa shiyasa nace ka anshi wannan yarinyar amatsayin baiwa cikon ta goma akwai nasarori da yawa a tareda ita sannan taimaka aikin bauta na baiwa itada sauran bayin ka, yanzun zansa amaidaka Masarautar ka kai dasu komi kenan zan turo maka aljani ɗantsitu inkana bukatar taimako ina tareda kai, sannan duk da sunbaka fansar ran ɗanka Hasburu karsuyi tunanin angama da hannun ka zaka kashe Malik kaidai ku cigaba da yima Gurfanai biyayya akan ikona, hhhhhhh."

Shima Baidulƙais ɗin dariya yayibcikin jindadi, wani magani Sarrilƙus ya busa saiga wani bakin aljani ɗankarami ya bayyana a gaban Sarrilƙus cikin bada umurni ya nuna mashi Baidulƙais, kafin kaftawar ido suka ɓace harda bayin nashi ba inda suka ɓulla sai tsakiyar fa'da nan ɗantsitu ya diresu

Please Login or Register in order to submit comment