Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakan alamar gargaɗi yai maita duk da ta fahimta zama yayi tufa ya ɗauka yana san ci amman ya gagara ga yunwa na addabar shi gashi yafison yaga Bahijja na bashi abinci da kanta.....



Itako Balki ba inda tasha sai wajen Uwar bayi ta kwashe komai ta faɗama ta, aiko da sauri ta isa wajen Gimbiya Yazira ta nasar mata komai, jitayi kamar zata sike dan kaɗuwa wannn karon sawa tayi a ɗauko mata Bahijja akawo mata ita wajen ta........



_WAISU_


Yarima Haishir ne keta shiri shida hadiman sa zasu tafi Masarautar Raifasu ba inda ya wuce sai wajen Mahaifin sa yana shiga ya same shi zaune yana karya kumallo shima zama yayi gefen shi bayan sungama gaisawa ya hau karyawa saida suka gama sannan mahaifin nashi yace. "Inafatan kagama shiryawa."? eh nagama ranka shidade." shima mikewa yayi yana gyara jikin shi sannn suka fito tare ba inda suka wuce sai wajen dawakai kowa ya hau da bayinsu guda hudu suka tunkari Masarautar Raifasu.

*∆∆∆∆∆∆∆*

Binta ce zaune a ɗakin ta tana ƴar fira da mijin ta cikin so da kauna rabi duk akan ƴarsu Bahijja sukeyin ta sunajin kewar ta nakara ratsa su, suna cikin fira Binta tafara kwalla da ta tuna da abinda Sarauniya Zulaiƙa tai mata, duk da bata Abdulmajid labarin abinda ya faru gudun karta jefashi cikin damuwa gani yayi tana goge kwallan idanun ta yafara tambayarta damuwar tace bakomai saidai bai aminta da abin da matar tashi ta faɗa mashi ba amman saidai baisan ya nuna mata bai amince ba, suna cikin jimami kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyar shi, saiga wata matashiyar baiwa tazo ta faɗama Binta sakon Yarima Malik hakan taji faɗuwar gaba, tashi tayi ta tafi kiran Malik a falon sashen shi ta zauna kasa bayan minti biyar da zuwan ta hadimar shi ta sanar dashi zuwan Binta baijima ba ya fito a zaune ya taddata kasa ta dukar da kai kasa, sallamar shi taji hakn yasa ta ɗago kai tana amsa sallamar shi zama yayi saman kujera gaidashi tayi cikin girmamawa shima amsawa yayi yana mai tambayarta Abdulmajid yana lfy ta amsa, shiru ne ya biyo baya na dakikai, murya na rawa tace. "Ranka shidade aikan ka ya riskeni Allah yasa lafiya ba wani laifin nayi ba!" Shiru yayi kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace. "Daman akan maganar Bahijja ne inasan kisanar dani inda Bahijja take a halin yanzun"?


Jitayi kwalla sun ziraromata a fuska ta goge sannan tace. "Ranka shidade nikaina basan inda Bahijja takeba a iya sanin da mukayi munba Baidulƙais amanar Bahijja saidai a ranar muka nemesu muka rasa sun ɓace wanda hakan ya bala'in ɗaga mana hankali saidai bamu da tabbacin Bahijja tana wajen Baidulƙais ne ko kuma Sarrilƙus gaskia bansan abinda zance ba akan wannan lamarin ba." kanshi ne yai bala'in kulewa dajin batun Binta ashema ba'asan inda Bahijja takeba takamai mai shine Ummu tahana shi zuwa neman ta!!! a zahiri ko cewa yayi "Kuma bamai tabbacin inda Bahijja take baku taɓa yunkurin neman agaji ba koda wajen Abbuh ne."? A tsorace Binta tace. "Karufamn asiri Yarima kabar maganar Bahijja karka saka kanka cikin hatsari ina mai mata addua ko wane hali take bazata tozar taba da yardar Allah." "hakane saidai ni nace kibari insha Allah duk inda Bahijja take sai na nemota sannan zan fansheta da duk abinda na mallaka a hannun Sarki Baidulƙais tunda shi aka sani da amanar Bahijja." ji sukayi ana tafi da hannu kamshin turaren da yaji shi ya tabbatar mashi da mai tafin, itako Binta kamar ta buɗe kasa ta ɓoye dan tsoro da shakka duk sun dabai bayeta, Sarauniya Zulaiƙa ce kemasu kallan mamaki musamman Malik dake ikirarin zai salwantar da komai akan Bahijja, cikin dakakkiyar murya mai amo tace. "Zaka salwantar da komai naka akan Bahijja ko? Ke kuma kina kukan munafunci shine kike karyama ɗana zuciya ko? Dan yaji tausn ko, wai mike haɗaki da ɗana miya haɗa biri da gada karfa kimanta Malik magajin Masarautar nan ne keda ƴarki bayi ne, nafahimci Binta kina karya dokoki na dana gindaya dan haka ni nasan maganin taurin kai irin naki ɓace mani dagani." hakuri Binta takama ba Sarauniya Zulaiƙa har kuka takeyi shiko Malik al'ajabi ya hana shi magana, shu'umin murmushi tayi tace. "tashi Binta kukan me kikeyi share hawayen ki keda ga ɗanki yayan Bahijja karki damu jeki gida." mamki ya gama kama Malik ganin yanda mahaifiyar shi ta koma kamar ba itaba, ajiyar zuciya ya sauke yana godema Allah ganin mahaifiyar shi tafara jin tausan bayi, tashi Binta tayi taima Sarauniya Zulaiƙa godiya sannan ta tafi jiki sake, kallan Malik tayi cikin kulawa tace. "Sannu Jarumi mai tausai yayan Bahijja saika maida hankali wajen ɗauko kanwar taka." tana gama faɗa takama gabanta Allah kaɗai yasan abinda ta saƙa a cikin zuciyar ta, danko Malik ko motsi ya kasayi dan tsoro musamman magnar da Sarauniya tayi mashi ta karshe, sai tufka da warwara yakeyi a cikin zuciyar shi..


Sarki Lahazu ne tareda mutanen shi suka isa Masarautar RAIFASU ba inda suka tsaya sai wajen Sarki Kofa yana ganin su ya zube yana karɓar gaisuwa cikin girmamawa, Sarkin gida ne ya iso shima gaisuwar yakai wajen Sarki Lahazu sannan yaimasu iso zuwa cikin fa'da suna shiga Baidulƙais ya mike yana tarar abokin nashi cikin mutunci ya basu waje suka zauna yana tsokanar Yarima Haishir dan inyana ganin shi sai yaga kamar yana ganin ɗan shi Yarima Hisbaru ji yayi wasu kwalla sun taho mashi yai saurin maidasu yana kallan Haishir yace. "Ɗana ankara girma yakamata ace zuwa yanzun ka aje iyali kullun kara manyan ta kakeyi." murmushi yayi irin yanajin kunyar abinda Sarki Baidulƙais ke faɗa mashi yace. " gamji yakara girma nakusa ranka shidade!" kallan shi Sarki Lahazu yayi yana shafa kanshi sannan yace. "Kagan shi nan baida ma yarinyar da zaace gata zai aura saidai shiririta amman tunda ya faɗi haka a rana bata karya." dariya suka saka baki ɗayan su nan Sarki Baidulƙais ya rike hannun Hisbaru suka mike sukayi ɓangaren shi daga haka fa'dar ta watse, suna isa suka zauna saman wani irin ƙayataccen kafat da sha kayan alfarma zama sukayi sukaci gaba da labarin bayan rabuwa Jakadiya ce ta shigo ta kawo gaisuwa, nan Baidulƙais yabata izinin gabatar da abinci ga bakin shi tafiya tayi ba da jimawa ba saiga bayi ɗauke da kayan abinci iri iri,aka ajiye a gaban su, wata baiwa ce ta duka zata zuba masu abinci ya dakatar da ita yana kallan Jakadiya duk da tagane nufin Baidulƙais amman saita basar. "Aikomin da Bahijja tazo ta zuba ma baki abinci."

Wani irin bakin ciki ya turnike Jakadiya sam batasan taga Baidulƙais yana raɓar Bahijja haka ta tafi ta kira Bahijja saida tasha da'ga sannan ta taho dan ta tabbatar mata da baki yake bazai mata komai ba hakan yasa ta taho jiki sanyaye take magana kamar wadda kwai ya fashema wa a cikin ciki, tare suka shigo ɗagowa Baidulƙais yayi ya kafeta da idanun shi, ko kaftawa baiyi, suna isowa suka tsugunwa muryar Bahijja ita ta maido Haishir daga tunanin da yakeyi na dalilin zuwan su Masarautar Raifasu da kudurin mahaifinsa, sauke shanyayyun idanun shi yayi saman fuskar Bahijja take idanun su ya sarke dana juna ta sauke nata kasa, maganar Baidulƙais ce ta katse masu tunani yace. "Yau baki shigo aiki da wuri ba, zuba mana abinci." ɗaukar filat tayi tafara zuba masu abincin, saidai duk yanda Baidulƙais yaso ya haɗa ido da Bahijja taki yarda ko alamar annuri babu a fuskar ta ta ɗauki mataki mai girman gaske shi kanshi Haishir mamaki yakeyi ganin irin kyawun Bahijja saidai taimashi kwarjini da yawa ganin yanda ta ɗauki mataki a kyakkyawar fuskar ta, wani irin kaunar ta yaji ta kama shi, har yake ganin zai aje mulki da yake takama dashi dan yaga ya mallaketa a rayuwar shi kota halin ƙaƙa, itako Bahijja tana gama zuba masu ta ajema kowa a gaban shi, sannan ta ɗauki flat ta ajema Yarima Haishir, ta koma gefe ta zauna kallan Baidulƙais keyi amman taki yarda su haɗa ido ganin yanda take cin magani yasa shi yafara cin abinci da kanshi saidai duk baijin dadin abincin baki ɗayan shi, har suka gama da ta ɗago ido saitaga Yarima Haishir ya sakar mata murmushi itako sai ta kara tsuke fuska, suna gamawa ta mike ta tattare kayan abincin, Jakadiya ce tasa wasu bayi suka kai madafa, dukawa Bahijja tayi gaban Baidulƙais tace. "Ranka shidade ina neman alfarmar tafiya banjin dadi sosai." yaso ya hanata tafiya baisan Sarki Lahazu yayi zatan wani abu, bata izini yayi harta kai bakin kofa sukaji Yarima Haishir yace. "Bahijja." kamar bazata juyo dan tasan Baidulƙais ne kuma ta tsani wata alaƙa na haɗata dashi amman sai ga juyo mamaki fal a ranta ya akai wannan bakon yasan sunan ta karasowa tayi ta sake dukawa yace. "Zuboman ruwa kinbamu abinci amman kin manta da ruwa, duk da naga kina sauri." yanda yai maganar kamar wanda akaima dole, Sarki Baidulƙais shima yai mamaki duk da yasan sunji sunan a wajen shi, zubo mashi ruwan tayi ta mika mashi, ansa yayi saidai taji ya riko mata da hannu yana murzawa da sauri ta zame hannun ta sai akan idon Baidulƙais wani irin bakin ciki yaji ya kama shi, basarwa yayi itako garin zame hannun ta ruwan ya zube ya wanke ma Yarima Haishir jiki da sauri ta mike tana bashi hakuri murmushi yayi yace. "Karki damu kyakkyawar baiwa ba laifin ki bane, sake bani kinji." haka ta kuma bashi ya karɓa, tana gamawa Baidulƙais yace. "Zaki iya tafiya Bahijja." da sauri tabar wajen, Sarki Lahazu yace. "Kai abokina wannan kyakkyawar yarinyar ina kasameta kamar tsada."
Saiyaji ya tsani tambayar da abokin nashi yaimashi cewa yayi. " na fanson sune a wajen Sarauniya Zulaiƙa su goma ka ganta can Bahijja kenan, ta daɗe a Masarautar nan tunda mukayi yaƙi dasu, na fanshe su da kudade masu yawa akan ran ɗana Hisbaru kaji yanda akai na samu wannan kyakkyawar baiwar." gilgiza kai yayi yace. "Gaskia kam ta haɗu shikenan sunci bulus akan ɗanka kenan."
"Aaaa akwai tarkon da nike ɗana masu,abokina."

taɓe baki yayi alamar ko ajikin shi sukaci gaba da firar su kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyar shi.....


Gimbiya Yazira tasa aka kawo mata Bahijja aka gurfanar da ita agaban ta, kamar wata ɓarauniya itako duk ta gama karaya tasan kashinta ya bushe, mikewa tayi ta wanke Bahijja da mari sannan tasa ƙafa ta halbata kamar kwallo baya tayi ta buge kanta kasa kara ta saki duk da haka baisa gimbiya Yazira ta ɗagama Bahijja saima cigaba da dukan ta da tayi tun taba nishi har saida ta suma dan duka koda Uwani taga gimbiya Yazira na neman kisan kai batasan sadda ta janye Bahijja ba itako ta gama fita hayyacin ta dan azaba bayi tasa suka ɗauke ta suka kaita taskar bayi sai fiffita su Zainab kema ta amman ba alamar matso kuka suka farayi sun ɗauka Bahijja ta mutu itako Indo tagama fita hankalin ta da gudu ta fita ta tafi wajen Jakadiya da tana zuwa ta zube tana kuka sai shassheƙa takeyi tambayar ta Jakadiya tayi amman ta kasa magana hakan yasa ta kara kulewa ta dakama tsawa da kyal Indo ta tsagaita kukan da takeyi tace "Bahijja.....cigaba da kukan tayi wanda yagama cin karfin ta da sauri Jakadiya ta dafa kafaɗarta tace. "Miyasameta faɗamani"? "ta mutu ta mutu!" gilgiza ta Jakadiya tayi tace. "Wa? Waya mutu Indo!"
"Bahijjahhhh.....ta ida maganar tana jan sunan Bahijja kamar daga sama Sarki Baidulƙais ya iso wajen daga ɗakin shi yaji sakon da ake faɗama Jakadiya, a kiɗime ya jefama Jakadiya tambayoyi wanda takeji kamar kafarta bata iya ɗaukar ta, "waya mutu wanaji kuna cewa."? Bahijja kawai Jakadiya ta iya faɗa wanda tuni sun fice daga falon shiko kamar gunki ko motsi ya kasayi, suna isa wajen Bahijja suka isketa kwance sai fiffita ake mata baki ɗaya Jakadiya tagama ruɗewar batasan ta isa wajen ruwa ba ta ɗibo ta watsama Bahijja ruwa a jiki, a jiyar zuciya mai karfi ta aje tareda sakin kara mai rudarwa tana ganin Jakadiya ta ƙan ƙameta tana kuka a hankali, itama ajiyar zuciyar tayi tana shafa fuskar Bahijja batasan ta fara kwallan ba, tambaya tafarayi miyasameta, Zainab ce ta gayama Jakadiya abinda ya faru daga farko har karshe, wani irin tausayin Bahijja ya kara kama Jakadiya a ranta tace.?, gaba kura baya sayaki tana fama da barazanar Sarki Baidulƙais ga kuma azabar gimbiya Yazira gaskia Bahijja tana cikin bala'i marar misaltuwa ganin kowa yayi zugum yasa Jakadiya tace sukoma bakin aikin su ita kuma ta zauna tare da Bahijja tana kwantar mata da hankali, a hankali tabi jikin ta da kallo batasabmn takara fashewa da kuka ba tace. " Baba kasheni zasuyi jibi jikina duk jini wlh tsoran gimbiya Yazira nikeyi dan Allah kitaimaka mani ingudu in nemi iyayena in koma wajen masu sona!" rufemata baki tayi taba gilgiza kai tace. "Kidaina faɗar haka Bahijja barin Masarautar nan tamkar rasa rayuwar kine dan Baidulƙais bazai raga maki ba da ace nasan kudurin shi akan ki kenan da ban bari a raboki daga Masarautar kiba da kuma iyayenki duk da kasancewar ki baiwa kamar yanda kike a halin yanzun!" kallan ta Bahijja tayi kamar mai tuna wani abu ta sake fashewa da kuka tace. "Baba kibari intafi wajen Ya Malik nasan shi bazai cutar dani ba, nan kasheni zasuyi basu kyaunata ko kaɗan basu tausayi na."


Itadai Jakadiya bata kuma cewa komai ba sai aikin lallashin Bahijja da takeyi zatayi magana sukaji Balki tacema Jakadiya Sarki na nemanta ba yanda ta iya haka ta mike ta tafi wajen Sarki Baidulƙais kamar jira tana zama ko gaisuwa basuyi ba yafara tambayar ta. " miyasameta dagaske ta mutu!" yanda ya ke tambayr ta shine ya kara bama Jakadiya mamaki, amman aitasan kodan ya cimma mugun nufin shi akan Bahijja bazai so ta mutu azahiri tace. " bata mutu ba saidai tana cikin yanayi akalla saita kai sati biyu tana hutawa akafin ta dawo bakin aikin ta." cikin damuwa ya tambaye ta abinda ya sameta, shiru tayi tana tunanin kalar amsar da zata bashi, sai cewa tayi. "faɗuwa tayi ta fashe kai shine ta samu doguwar suma." Shiru tayi kamar mai nazari badan ya yardaba yace. " bakomai amman kibari sai taji sauki ta dawo aiki anjima zan aiko Sarkin gida ya kawo mata magani kije kibata kulawa ta musamman sai kinjini Gamji ya bata sauki."da amin ta amsa ta tafi tana aljabin Baidulƙais duk rashin tausan shi amman yana jin tausan Bahijja koda yake dan ya cimma burin shi, shiyasa yace ta huta da wannan tunanin ta tafi wajen Bahijja




*Ƴar mutan Kankia ce❣️*


Share
Comment
Vote



*BAYI MA 'YA'YA'NE*

*~Touching heart story💔😭~*

_By_
*Jameey Yar'mutan kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*


Babi na 25&26

*Afuwan! Ina neman afuwa ga yan BAYI MA 'YA'YA'NE COMMENT GROUPS🙏, ku sani inajin dadin comment dinku sosai amman ina busy shiyasa bani baku reply ina jindadin shirhin da kuke sai da bani da lokacin da za'ayi firar dani, amman ku sani comment dinku da shirhinku ke sa nike two post a rana nagode ku cigaba da zuba comment din dai😍❣️*

Washe gari da safe Bahijja ce kwance saman cinyar Jakadiya tana bata labari itako sai dariya takeyi zuwa yanzun gani take kamar itace mahaifiyar ta itama haka Jakadiya ta ɗauka a cikin zuciyar ta, bakaramin kulawa take ba Bahijja ba tamkar ƴar da ta haifa da cikin ta, suna cikin firar su Zainab ta shigo ta duba Bahijja da jiki wanda izuwa yanzun ta samu sauki sosai, nan Jakadiya ta ɗan fita zagayawa Zainab ta matso kusa da Bahijja tace. "Bahijja ashe wai da Sarki aka kamaki shiyasa gimbiya Yazira taimaki dukan tsiya ke ko miyajamaki."

Jikin Bahijja ne yai mugun sanyi ta rasa wane munafuki ya faɗama Zainab sauran ta koma mujiya a cikin wannan azzalumar Masarautar. "Ke ina kikaji wannan labarin waya faɗamaki."?
daburcewa Zainab tayi tana rawar murya tace. "Wajen uwar bayi naji tana faɗama Lawisa da su Balki suke maganar kinganni nan ba ruwana."

Hawaye masu zafi suka wanke ma Bahijja fuska tarasa mike mata dadi a rayuwar ta, murmushin karfin hali tayi batace komai ba, duk taji ta tsani rayuwar da ta sameta, koda Jakadiya ta dawo kallan Bahijja kawai tayi tagane tana cikin damuwa zama tayi ta fara tambayarta damuwar ta sai tace bakomai Baba kawai kaina naji yana ɗanyi mani ciwo kallan tuhuma taima Zainab dan bata yarda ba cikin kamun kai Zainab taima Bahijja sallama ta tafi tana godema Allah da Bahijja bata faɗama Jakadiya ba.


Shiko Yarima Haishir tunda ya tashi yake yan kalle kalle ko zaiga kyakkyawar baiwa sunan da yabata kenan, a cikin zuciyar kasan cewar ainahin sunan ta ya ɓace mashi koda aka kawo masu kalaci baici komai ba zuciyar shi ta azazzale shi da san ganin kyakkyawar fuskar ta, mahaifinsa ketayi mashi magana amman baiji shiba hakan yasa ya dafa shi a firgice ya jiyo yana kallan shi, Sarki Lahazu ne ya zauna yana tambayar shi damuwar shi da yai niyar bazai faɗa mashi damuwar shi ba amman saiyaga kwara ya faɗa mashi. "Abba ina cikin damuwa marar misaltuwa, naga abinda raina keso kuma ina son inkasan ce dashi."


Da sauri ya tambayi ɗan nashi abinda yake so. " Abba ina wannan baiwar da tazo tabani ruwa harta kijamani jiki ina sonta kuma auren ta zanyi."


Wani irin shuumin murmushi yayi yana kalan ɗan nashi sannan yace. "Dalilin zuwan mu kenan naga yana boyeman wani sirri nashi ta wannan hanyar ne kadai zan gane daganan zan datse alakar mu dashi, dan haka kasama ranka kasamu kuma zan ƴanta maka ita da karfina sannan in aura maka ita, inasan ka natsu kadaina bin matan banza nikuma zan aura maka ita." dan dadi Yarima Haishir baisan sadda ya makale mahaifinsa ba yana murna a haka Sarki Baidulƙais ya iske su zaunawa yayi yana murmushi yace. "Ɗana wannan irin farin ciki na menene.? Mahaifinsa yai murmushi yace. "Yau zakaji abinda ke damun ɗan naka nasan zakai mashi maganin damuwar shi." cikin gamsuwa yace. "Badamuwa indai dukiya ke badashi zan mashi."

Murmushi mugunta sukayi suna kallan juna suka kashe ido da Yarima Haishir sannan ya fita alamun maijin kunyar iyayen nashi da dariya suka bishi suna mamakin kalar halin ɗan nasu.


Haka rayuwa takanse a cikin Masarautar Raifasu danko Bahijja ta rabu da zuwa wajen Sarki Baidulƙais hankalin ta kwance wani lokacin kuma gimbiya Yazira kesa a kirata ta saka ta aiki saidai duk wannan abun Sarki bai sani ba.


A Masarautar Daborah kuwa Malik ne tafe da hadiman shi sai koɗa shi sukeyi suna kirara shi ba inda suka dosa sai wani ƙayataccen lambu mai matukar daukar hankali da saka nutsuwa yana isa daman n gyara inda zai zauna sai kuɗa shi bawan shi Ashir yakeyi yana. "Zaman ka lfy Yariman Daborah, gaba lfy baya lfy alkhairyn Allah ya tabbata da aminci su lulubeka Yarima Allah yakareka daga murmushin makiya angaishe da Yarima Malikussaif ɗa ga Saifulislam magajin Sarauniya Zulaiƙa yar Abdulhamid Allah yakara girma."


Haka yaita koɗa Malik, shima zama yayi gefen uban gidan nashi, hakan yasa ya ɗagama sauran bayin nashi hannu alamar su bashi waje shida Ashir suka kebe sannn ya fara magana. "Ashir inasan insaka wani aiki amatsayin ka na amintaccen bawana."
Cikin zumuɗi Ashir yace. "Ranka shidade zaman da nike kenan aikin ka shine nasara agareni umurnin ka abun tunkaho a gareni ina sauraron ka magajin gobe." "inasan ka badda kamanni ka shiga Masarautar Raifasu ka tabbatar min idan Bahijja na cikin Masarautar kazo ka faɗamani saidai karka yarda ka faɗama wani inda zakaje sannan karka ce ni na aikeka kaidai kabi ta yanda zaka ɓadda kama ka ziyarci Masarautar Raifasu kome kenan ina sauraran ka."

Shiru Ashir yayi yana mamakin maganganun Malik ya ɗauka anrufe babin Bahijja ganin yanda Sarauniya Zulaiƙa ta shure maganar ta amman shi Malik bai mantata ba gaskia ya cika ɗan halak bai mance halacci ba. "Shikenan ranka shidade, zuwa gobe zan shirya in shiga cikin Raifasu dan tabbatar maka da abinda kakeson gani dan gane da Bahijja saidai fatar mu musameta a can ɗin."? . "kwarai kuwa Ashir fatana kenan." murmushi Ashir yayi yana cigaba daba mai gidan nashi kwarin guiwa sannan yaciga ba da bashi labarai masu dadin gaske basu suka baro lambu ba sai marece likis sannan suka wuce sashen Yarima Malik,yana zama a falo baiwar shi Aliya ta haɗa mashi ruwan wanka ya shiga bathroom shi kuma Ashir ya tsaya cikin falo yana kula da uban gidan shi.


A wajen Yarima Haishir kuwa kwana yayi yana tunanin Bahijja a cikin zuciyar shi ɗan ganin da yaimata yaji ta shiga ranshi fiye da tunanin shi a haka dai har gari ya waye wajen karfe goma ya tashi ya shirya ya fita fa'da, can ya iske mahaifin shi anata fadanci yana zuwa yakai gaisuwa wajen Sarki Baidulƙais sannan ya gaida mahaifin shi, kowa yayi shiru a fa'da kamar ba kowa Sarki Baidulƙais ne yafara magana. "Inasan Sarkin fa'da da Sarkin taska ku zaun aku duba nawa fa'da zata bukata da kuma wannn Masarautar musamman wajen kayan masarufi na yau da gobe." da sauri Sarkin zagi yafara cewa. "Ranka shidade, gyara ginzi toran giwa gaba lfy baya lfy." Sarki Lahazu yace. "Kamar yanda kace hakan yabasa kyau yakamata ace kunduba komai kafin shekara takare tunda za'aci kasuwar Qazub sai kuyi duk abinda yakamata."
Cikin gamsuwa Sarki Baidulƙais ya amince da shawarar da abokin nashi yabashi,haka sukaci gaba da ƴan shawarwari daga karshe Sarki Baidulƙais ya tashi suka tafi sashen shi,a saman hanyar komawa sashen Sarki Baidulƙais, su hango Bahijja ta taho kanta akasa tana wasa da duwatsun dake hannun ta hankalin ta kwance, shiko Yarima Haishir koda ya ganta ya kafeta da shanyayyun idanun sa masu ruɗawar wa, magana Sarki Baidulƙais kemashi kojin shi baiba saida Sarki Lahazu ya taɓo Yarima Haishir sannan yadawo daga dogon tunanin da ya tafi, bin inda yake kallo yayi saiyaga Bahijja ta taho tanata yan wasannin ta, ji tayi ta bangaji mutun ta tafi zat faɗi da sauri Haishir ya rikota tafaɗo jikin shi duk tsoro yagama kamata kirjinta yafara dukan tara tara, shiko Baidulƙais daurewa kawai yayi gudun kada girman shi ya zube a gane akwai wani abu aranshi dangane da Bahijja yasa ya daure yana maijin haushin Haishir a ranshi, da sauri Bahijja ta kwace hannun ta da Hashir ya rike, ta sauke kanta kasa dan bata san suna haɗa ido, dukawa tayi tagaida Sarki Baidulƙais da Lahazu sannan ta tafi jiki a sage duk ta tsargu, shiko Haishir da kallo ya bita, jiyake kamar ya bita, shima bin mahaifin shi yayi suka tafi yana ta tunanin Bahijja a ranshi, itako cikin taskar bayi ta shiga ba inda ta tsaya sai wajen Indo isketa tayi tana wanki suna gaisuwa da umman ta tadawo suna labari da kawar ta rabi duk labarin Yarima Malik take bata danma duk ta manta wasu abubuwan da suka faru, itako tana aiki tana taya Bahijja labaran da take mata har ta gama aikin ta suka wuce wajen Zainab suka dasa sabuwar fira, ji sukayi ana buga karaurawa da sauri suka tashi suka fita waje turus sukayi ganin bayi masu yawa anbaza su cikin rana ana dukan su, ga Bahijja da tsoran bugu dan danan idanun ta suka ciko da kwalla tafara ja dabaya, Sarkin dogarai ne ya daka mata tsawa batasan ta zube ba tana bashi hakuri itama cikin sahu ta shiga a kaci gaba da gana masu ukuba.

Banda bugun su ba abinda akeyi, Sarkin bulala yakama Zainab yafara duka sai ihu takeyi baidaina dukan taba saida ya sauke mata bulala talatin koda Bahijja taga yanda akaima kawarta take ido ya raina fata dan tsoro har saida ta fara sakin fitsari a wando, shiko baki ɗaya ranshi ya gama ganin haka yasa ya ɗauko katuwar bulalar shi zai shauɗama Bahijja ta rike shi kam da karfi ta ɗare saman shi tana kuka kamar ranta zai fita ba yanda baiba dan ya yakice ta daga jikin shi amman ya

Please Login or Register in order to submit comment