Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan ta, yana zama saman ƙayatattar shimfiɗar shi ta gaida shi, amsawa yayi sannan ya kalli Jakadiya yace. "Jamra ya Bahijja ta kwana."? Cikin girmamawa tace da sauki saidai yau ban haɗu da ita ba."ɗaukar ruwa yayi yasha yana ajiyar zuciya yace. "Kije ki karamani Bahijja." "Angama ranka shidade."tafiya tayi ta tafi taskar bayi, itako Bahijja tana zaune da Saude suna fira Saude ke cema Bahijja "niko inasan intambayeki ƴata."? Murmushi ɗauke a fuskar Bahijja tace. "Inajinki Baba Saude."
"Ƴata ya sunan Mahaifin ki."? A bazata tambayar tazoma Bahijja kallan Saude tayi sannan tace. "Abdulmajid sunan shi." gyaɗa kai tayi sannan tace. "Mahaifiyar kifa."? Sake bata amsa tayi da Binta sunan ta cewar Bahijja, shiru Saude tayi tana nazari wasu kwalla ne suka wankema Saude fuska tai saurin gogewa cikin damuwa Bahijja ta fara tambayar Saude damuwar ta ganin tana hawaye, itako Saude kukane yaci karfin ta takasa magana da kyal Bahijja ta lallashi Saude tayi shiru sannan tasake cewa. "Baba Saude miyasaka ki kuka har haka."? Ajiyar zuciya Saude ta sauke sannan tacema Bahijja "ƴata wani babban lamarine na tuna shekaru da daɗewa har yau abin dashi nike kwana nike tashi nakasa mantawa dashi a rayuwa, duk lokacin da kike taredani sai injiki kamar jinina nike jinki ƴata." cikin tausayawa Bahijja tace. "Menene wannan abun kidaina damuwa faɗamani kilan inada taimakon da zan maki."wani irin kaunar Bahijja taji tana fisgarta sannan tace."hakane ƴata saidai ki saurari abinda zan faɗamaki....tafara magana kenan sukaji Jakadiya ta shigo gaidata sukayi sannan Bahijja ta kalli Jakadiya cikin sakin fuska tace Baba ina kwana inata kewarki." itama murmushi taima Bahijja sannan tace. "Ƴata kenan ya karfin jikin naki."? "Da sauki Baba." "yawwa Bahijja kizo Sarki na kiranki." "take duk wata walwalar Bahijja ta kau baki ɗaya yanayin ta ya canza ganin kallan da Jakadiya taimata yasata tashi taima Saude sallam a suka tafi, a hanya Jakadiya ta dinga kwantarma da Bahijja hankali da kalamai masu dadin sauraro koda suka isa jin yanda ta tsargu ya tabbatar mata da Baidulƙais ke kallan ta sake sadda kanta tayi harta iso wajen shi tareda Jakadiya suka gaida shi, sai kallan Bahijja yakeyi sannan ya amsa, itako a takure take a hankali ta saci kallan shi taga ita yake kallo addu'a tafara, ji tayi yace. "Mike maki ciwo Bahijja."? Take taji ta tsani ko wace kulawa daga gareshi, "bakomai." sake kallan ta yayi yace. "Kintabbata dda bakomai."? da eh ta amsa tana wasa da hannun ta, shiru ne ya biyo baya bai fasa kallan Bahijja danji yake kamar ya haɗeta duk ranar da ya kalli Bahijja sai yaji muguwar shi'awarta ta addabi rayuwar shi idanun shi suka sauya kalla yai karfin hali yace. "Kinci abinci kuwa."? Saita samu kanta da cewa. "Eh naci." badan ya yarda ba ya kalli Jakadiya wadda duk abinda ke faruwa tana jin su yace. "Jamra kije madafa ki ansoma Bahijja abinci daga gani ko a gidan kaso ba'a bata abinci." da sauri Bahijja ta kalli Baidulƙais suka haɗa ido, taki sauke nata ji take kamar ra shake shi ta huta dan duk abinda zaiyi baitaɓa burgeta azzalumi ne baida imani ko kadan, jitayi yace. "Bahijja lafiyarki ko baki bukatar abincin ne."? Sake bashi amsa tayi da eh, murmushi yayi yasan karya takeyi dan yasan ba abinda taci, cigaba yayi da hadimar shi kmar baisan ya ajiye Bahijja ba, shiru kowa yayi itadai sai kalan kasa takeyi tana sake sake iri iri Shiko kallanta kawai yakeyi yana mamakin irin girman da take karawa ji sukayi wasu bayi sunzo sun aje abinci da kallo Bahijja ta bisu, badbada jimawa ba Jakadiya ta shigo yasa Bahijja ta zuba abincin sannan yace taci abincin satar kallan shi tayi taga ba alamar wasa haka tafara yagunar abincin kamar anai mata dole har ta gama sannan yace taje gida.


_Daborah_



Washe da safe, Sarauniya Zulaiƙa ce zaune a fa'da anata fadanci ita da ƴan kasuwa ne ana shawara akan yanda za'a gudanar da cin kasuwar shekara da za'ayi a cikin babbar kasuwar Gambia wadda take a kalkashin ikon Masarautar Daborah, kowa yana bada shawarar shi akan yanda yakamata abada tsaro duba da yanda take cika da baki daga kasashen duniya sassa daban daban suna cikin magana saiga Sarkin gida ya shigo fa'da ya zube ya gaida Sarauniya sarkin zagine yace. "Angaisheka Sarkin gida meki tafe dakai."? Sake sunkuyar dakan shi yayi sannan yace. "Ranki shidade kinyi bako daga Masarautar Raifasu yana bakin fa'da." kallan kallo ne ya biyo baya kowa yana mamakin jin sakon, ɗaga kai tayi alamar a shigo da bakon koda Sarkin gida ya fita yaima bawan Sarki Baidulƙais iso har cikin fa'da baki ɗayan su suka sake kai gaisuwa sannan ya fita, Sarauniya Zulaiƙa ce ta kalli bawan da alamar tambaya, yanda yaga ta kalle shi saida yaji gaban shi yai mummunan faduwa dan baiga alamun wasa ba a fuskar shi sake dukar dakai yayi sannan yace. "Ranki shidade sakone daga Sarki Baidulƙais yace inkawo maki wannan wasikar, kallan magatakarda tayi da sauri ya karɓa sannan ya kalleta, ta bashi izinin karanta wasikar kamar haka.



_Inama ace baki yunkurin cin amanata ba Sarauniya Zulaiƙa nizakiyima zamba cikin aminci ki turo bawanki ya sace Bahijja, toh kisani kaidin ki da burin ki bai cimma ruwa ba dan haka ina gargaɗarki da fita harkata sannan kisani inaja dake Zulaiƙa duk abinda kike takama dashi ni Baidulƙais na wuce dake inkunne yaji gangar jiki ya tsira_


Wani irin bakin ciki ya tokare zuciyar Sarauniya Zulaiƙa take tasa aka sallami bawan, idanun ta sun kaɗa jajir kamar garwa shi dan ɓacin rai da har ya fita ya dawo da wani buhu a hannun shi ya duƙa yace. "Ranki shidade na manta yace abaki wannan, da sauri Sarkin fa'da ya karɓa budewa yayi ya fiddo kan Nulwa a cikin buhu ya aje agaban Sarauniya Zulaiƙa koda taga kan Nulwa mikewa tayi tasa kafa ta halba shi sannan tace. "Ni Zulaiƙa ƴa ga Abdulhamid jikanya ga Sarki Haris tattaɓa kunne ga Sarki Khamil ɗan Sarki Jabbar na Sarauniya Yanazu na rantse da Allah wlh blh sainaga bayan wannan wawan Sarkin ni zai aikoma wannan sakon har cikin Masarauta ta a fa'da ta, har an'isa da zai aiko mani da kan wannan jakin bawan har abin mamaki ne dan bayi sunci amanar shi koya manta basu da amana nima kaina amanata sukeci! Nulwa yake kowa dan haka aje akiramn uban shi yazo ya ɗauke mani wannan jakin, sannan ina Sarkin horo."? Da sauri yace. "Ranki shidade gani." "nabaka nan da minti biyar kaje ka tattaro mani kaf bayin Masarautar Daborah." bata jira cewar shiba ta sake halba kan Nulwa ta fita rai ɓace.


A wajen Yarima Haishir kuwa da marece liqis ya isa Masarautar Raifasu saidai bai kaida shiga cikin Masarautar ba, shida bawan shi duk inda zashi tare suke zuwa sai bayin da ya taho dasu, suna isowa wani karamin kauye suka zauna yaba bayin shi kaya harda bawan shi mai mashi hidima haka suka saka kayan bayin Raifasu suka shiga dan sama masu masauki kafin tsakiyar dare su shigo cikin Masarautar.


Itako Bahijja ita da Zainab suka fito shan iska bayan taskar bayi suna fira sai shawagi takeyi ta rasa dalilin dayasa takejin dadin yanayin yau, ba abinda yasha masu kai suka cigaba da labari zama sukayi saman wani dutsi suna cikin firar su, Bahijja tace. "Zainab kinsan mine."? "Aa tace ma Bahijja, murmushi tayi tace. "Inaso nidake aga wanda zaifi gudu a taɓo wancen iccen magoran." takarasa maganar tana murmushi, itama Zainab murmushin tayi tace. "Agwada agani mana nasan ba fiki gudu, aiko suka fara ƴar rere da Bahijja kowa nason ya wuce ɗan uwan shi, suna cikin gudu Zainab ta gabza uban tuntuɓe aiko ta duke tana kuka itako Bahijja batasan tanayi ba sai haki takeyi takai wajen iccen mangaro tana isa ta taɓa iccen tana maida numfashi itayi an rufe mata ido ta kwala uban ihu, itako Zainab jan kafa tayi ta taho tana banyarda saidai acanza gani tayi an ɗauki Bahijja tana ta halbe halbe, anyi daji da ita, da gudu Zainab tabi tana ihu sadda zata iso har sun ɓacemata, komawa tayi taskar bayi tana kuka kamar ranta zai fita tayi gidan Saude....


Cikin kankanin lokaci labari yagama karaɗe Masarautar Raifasu anɗauke Bahijja, koda Jakadiya ta samu labari da gudu ta isa wajen Sarki Baidulƙais tana haki shima mikewa yayi yana jefama Jakadiya tambaya. "Jamra lafiya miyafaru."? "Haki takeyi da kyar tace. "Ranka shidade ansace Bahijja.!" da sauri Baidulƙais ya mike yana jefoma Jakadiya tambaya "waya saceta."? "Ranka shidade bansani ba." kamar ya baki saniba."? "Ranka shidade Zainab ce takawo wannan labarin." baisan sadda ya fita ba Jakadiya nabiye dashi sawa yayi aka kira mashi Zainab ya tambayeta ta faɗa mashi komai, baki ɗaya jikin Baidulƙais yagama mutuwa ko motsin kirki yakasa sai al'ajabin lamarin yakeyi ko magana yakasa baki ɗaya kanshi ya gama kullewa tunanin shi ya tsaya cak yarasa abinyi....


Itako Sarauniya Zulaiƙa angama tara mata bayi kaf sun gurfana, tana zuwa ta kalle su ɗaya bayan ɗaya sannan tace. "Kudai baku da amana a cikin ku har za'a samu wanda zaije Masarautar Raifasu ɗauko Bahijja dan haka Sarkin horo aita dukan su har sai sun bayyana kansu inba haka ni kadai nasan abinda zan masu." bayin Allah haka akaita gana masu azaba itana gefe tanai masu kallan tsana, ana cikin dukan su saiga Ashir shima dukawa yayi nan Sarauniya Zulaiƙa tace. A daka da dukan su, "Sarkin horo kaware mani Sarkin bayi Abdulmajid da Binta kaita dukan su, duk yanda akai su suka aiki wannan bawan da ake nema." wani irin tashin hankaline ya kama Ashir zaiyi magana Sarauniya Zulaiƙa ta ɗaga mashi hannu tace. "Jeka kira mani Yarima MalikusSaif a sashen shi." bayan da Ashir ya iya haka yaje sashen Yarima Malik, yaita sallama shiru hakan yasa ya shiga ɗakin shi nan ma shiru har wajen Huzaifa yaje bashi ba alama hatta Huzaifan akan hanya ya haɗu da Yazid ya faɗa mashi baiga Yarima ba shima cewa yayi daga lambu yake baigan shi haka Ashir ya koma ya zube Wajen Sarauniya Zulaiƙa lokacin anata dukan su Binta kamar za'a kashe su, cikin murya kuka Ashir yace. "Ranki shidade tabbas Yarima Malik bai cikin Masarautar nan ba inda ban duba ba." mikewa tayi ta aza mashi mummunan mari sannan tace. "Aikin banza aikin wofi Sarkin horo daina dukan su, aje a dubaman kaf Masarautar Daborah inda Yarima Malik yake."haka aka bazu bashi ba alamar shi, haka aka dawo aka shida Sarauniya Zulaiƙa bashi ba alamar shi, jikin ta na kyarma tace a zuciyar ta. "Tabbas inko har zargin da nikeyi MalikusSaif ya tafi ɗauko wannan matsiyaciyar yarinyar Bahijja tabbas zaigamu da hushi, cikin ƙaƙƙausar murya Sarauniya Zulaiƙa tace "Sarkin Yaki ka ɗibi jarumai kubi sahun Yarima Malik, bance kai masu komai ba saidai duk Masarautar da kuka samu MalikusSaif ka aiko mani ɗan aike saina shafe babin su musamman Masarautar Raifasu." da angama Sarkin Yaki yafara haɗa jarumai....



Suko su MalikusSaif tafiya sukeyi mai nisan gaske ba inda suka tsaya sai wata inuwa dan hutawa kafin suci gaba da tafiya.
A Wajen Sarki Baidulƙais kuwa ya saka bayin shi da Sarkin gida neman Bahijja a cikin kewayen Masarautar Raifasu dan tabbatar da zargin da yakeyi a cikin zuciyar shi duk da bai bayyanawa kowa kudirin dake cikin zuciyar shiba


Jaruman Sarauniya Zulaiƙa suka gama shiri kowa ya hau saman dawakai, tace. "Daga nan kufara bin hanyar Masarautar Raifasu bance ku ɓata lokacin kuba." haka suka kama hanyar neman Yarima Malik......


_Laifin dadi karewa masoyan na anan nakawo karshen wannan ƙayataccen labari ba Bayima 'Ƴa'ƴane littafi na ɗaya, wanda yake cikeda sarkakiyawa da ban tausayi tsantsar zalinci da tarin ilimantawar wa, badan naso ba zan dakatar da wannan labarin saidan wani uzuri daya tasomani, na komawa Makaranta da zanyi, dan haka ina neman addu'o'in ku, ku sani inai maku son fisabilillah ❣️_




*Sai mun haɗu a Bayima Ƴaƴane ne Book two wanda anan ne zaku samu amsoshi masu yawa da suka shige maku duhu*



⏺️ Shin Yarima Malik zai isa Masarautar Raifasu dan ɗauko Bahijja?

⏺️ An ɗauke Bahijja waya ɗauketa?


⏺️ Jaruman Masarautar Daborah zasu cimma Yarima MalikusSaif?

⏺️ Yarima Haishir zai cimma burin shi a Masarautar Raifasu?


⏺️ Sannan Sarauniya Zulaiƙa zata gane wanda bawan da yaje Masarautar Raifasu?


⏺️ Sannan wane kuduri ne Sarki Baidulƙais ya boye akan sace Bahijja da akayi?


⏺️ Sannan wace badaƙala ce zata wanzu tsakanin Sarki Baidulƙais da Sarauniya Zulaiƙa da Sarki Lahazu?



*Waɗan nan tambayoyin dama wasu zasuzo maku a cikin Bayima Ƴaƴane book two insha Allah.*



```Nagode da yanda kuka nunama wannan book din so da kauna kuka anshe shi hannu bibbiyu, Allah yabar tare inayinku masoyana karda ku manta👇```




_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Comment
And
Like

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment