Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idannuwansa a fuskata,
Ta lumshe idannuwanta ta ce" Namijin duniya kallonka mai tafe da harara.......

Allahu Allahu La ushirika bihi shai.a.... shine adu.ar da Sudais yayi ta nanatawa a wannan koncin bayan korar su Rauda da yayi,
Gefensa Samir ne zaune a kujerar nan mai juyin mutun guda, ya zubawa abincin da aka kawo wa Sudais aman ya ki ci..
Tunani ne ya sako shi gaba, ya rasa ta ina zai kamo wannan lamari, wai dama *AISHA* ke son ogansa? Shi kuwa ogansa ga dukan Alamu ba Aisha ce ke jan ragamar zuciyarsa ba

Ajiyar zuciya ya sauke ya juyo wajen Sudais ya ce" Elhaj,
Sannin ba zai amsa masa ba, ya ci gaba da maganarsa dan kuwa ya san in dai ya ji koda bai bashi amsa ba ba zai yi masa karya ba, Ogansa baya shakun magana da kowa kai tsaye ya fada masa gaskiya

Samir ya ce" oga mai zai hana ka tunkari matsalar nan da kanka ne? Ina nufin ka tunkareta ka fada mata damuwarka?

Sudais ya dan bude idannuwansa ya jima yana kallon ac din dake daidai kansa , kamar ba zai yi magana ba kuma can ya ce" mai kake nufi?

Samir ya bayar da hankalinsa sosai ya ce" ina nufin oga damuwar nan tunda har ta fara kawo ka haka mai zai hana kawai a fada mata ta amince a yi komai a gama ko hankalinka zai dawo waje guda? Idan ka yi duba da wannan rashin lafiyar da ta fado, da irin yanda harkoki suke sanya, Elhaj baka taba zuwa gari ba ka shigo kampani baka yi zagaye ba sai wannan karin, kar ma.aikata su ankara su fara kokarin kawo sanya a harkar neman nan
Dan tsagaitawa yayi da maganarsa yana adu.ar Allah ya sa bai bata masa rai ba, kai koda ya bata masa sai dai yayi hakuri domin bai ga wa zai fada masa ba, shi kam yana mamaki mutun kamar Sudais yana tsoron mace? Tsoron mace mana sai dai yana labewa a bayan kar ta raina shi da wasu kudiririkansa nasa, harma abin na kokarin jan dama dan kuwa yana hango rigima yana tsoron ka ja na ja ne za.a yi a wannan lamarin

Jin shiru ya sa Sudais ba tare da ya dago da kansa ba ya ce" ci gaba

Samir ya dan daburce, can dai ya ce" daman oga bana son abinda zai saka ka yi kasa ne, aman ka yi hakuri

Sudais ya yi dan murmushi, ya sauko kafafuwansa kan takalminsa ya tsurawa Samir ido, a ransa yake fadin" kennan har ana gannin feeling dina a kan wannan yarinyar haka? Har an gane halin da nake ciki? Ko da yake shi ai shi na saka aikin ya bibiyar min ita dole ya fahimci halin da nake ciki...., sai dai kash koda zan zube sau dari ne saboda damuwarta ba zan yarda na barar da kaina kamar yanda kake so Samir ba, naki din, ba zan amince da shawararka ba

Aman a fili ya ce" a dukan jawaban da kake kana nufin ina son yarinyar nan ne ko me? Shin Samir na taba yi maka maganar ina sonta ne?

Samir ya dago da sauri da mamaki shinfife a fuskarsa, lale ma ogansa yana kokarin ya take maganar kenan, a hankali ya girgiza kai

Sudais yayi murmushin gefen baki ya ci gaba da fadin" a iya sanina nakan kirata da *MATA* ne kawai, mata kuwa yana da ma.ana biyu mata kamar yanda ake fadi sai kuma mata ana nufin *Matata*
Iya nazarin hangena ban bambance maka wane nake nufi ba
_rashin lafiya kuwa Allah ne ya kawota ba wai wata damuwa ba🤦🏻‍♂
_a kadan mun yi shekara biyar da kai, ina tunanin kai ne wanda ya fi sannin sirina bayan yan gidanmu dan kuwa koda a jarida na boye wani kai kam na fada maka duka dan ka natsu ka daina gannin ka tashi a gidan masu kudi ka ce zaka yi wasa da damarka har chance dinka ta kubuce maka
Ya kuma yin murmushi ya ce" ban ce aa ba, kuma ban ce eh ba, ban ce na isa ba kuma ban ce ba zan iya yakiceta a lamurana ba, ban ce da kai ina sonta ba, kuma ban ce da kai na tsaneta ba, ina so daga yanzu a daidaita su da sauran ma.aikatana, ina so yanda za.a hukunta kowa a hukunta su idan suka taka dokokin ma.aikatata, ina so a yiwa Babar gargadi na kirki kan abinda ta aikata na taran gabana ta firtan banzar maganarta kan idan ta kuma za.a koreta, ina so na karyata abinda ya faru da ni a yau sannan ya zamo sirri, zan yi zagaye ranar litinin karfe bakwai da rabi ina so kowa ya halarta a farfajiyar ma.aikatana banda masu tsaro kawai, Samir kar ka manta wanda Maciji ya sara koda ya ga igiya yakan tsorata ne, kana iya tafiya!

Samir ya mike, cike da jin dadin ogansa zai dawo yanda yake (🤣) ya juya har zai fita sudais ya ce" SAMIR
Ya ja ya juyo,
Sudais ya ce" *SAMIR INA SON TA!, Aman hakan in sha Allah ba zai kayar da ni ba!*

Ido Samir ya zaro na mamaki ya ce"""






*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*




1⃣3⃣




Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kasa_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



Bai barshi yayi maganar ba sanadiyar hade girarsa da yayi
Da sauri samir ya juya yana magana da zuciyarsa yana tsananin mamakin lamarin Sudais

Mikewa ya yi ya karasa gaban table din yana dan langi domin har zuwa lokacin bugun zuciyarsa ba wani daidaita ta yi ba

Agogon hannunsa na azurfa da suka konce ya dauko ya daura a hannunsa na hagu, ya konce hiraminsa ya shaki iska ya sauke ajiyar zuciya a ransa ya ce" soyayarki a cikin zuciyata gaskiya ce, tashin hankali wa wannan soyaya wajibi ne, abinda yake kila wa kala kankaruwar soyayar taki daga zuciyana, wannan shi ne nake tunanin zai yiwu kuwa? Sai dai na fahimci karfina isata wayona ba zai bani wannan dama ba, aman zan fadawa Allah ya cire min wannan bakon lamari dan kuwa ya girmami tunanina *Mata*, ina so Allah ya sa kar wannan soyaya ta taba lafiyata harma ta sa na shiga hakin mutanen da nake tare da su,
Zan yi hulda da ke ne kamar yanda zan yi da sauran, *Mata* zan cinye wasan ta wajen daina son ki
Ya karashe maganar yana mai sakin dan guntun murmushi kafin yake zama kan kujerarsa ya jawo takardun da ya dace ya duba tun safe ya shiga aikace aikace bilhaki ( agogo kennan sarkin aiki )


Eyah, *Jarina* ya jikin nasa yanzu?
Nana Mariama ke tambayar Aisha dake zaune tana fada mata irin rashin lafiyar da yayi yau a office

Aisha ta ce" uhum, mama na tsorata, na ji tsoron kar a je ya mutu *burina ya kasa cika*

Da sauri Rauda ta kalo wajenta, bata san lokacin da bakinta ya furta" aa🤔, Aunty daman kukan nan da kike rusawa ba na soyayar nasa bane?

Aisha ta kalota ta yi murmushi harda juya ido, ta ce" kina da matsala Lalla,, kin ga ai yaro da kudi akewa kirari ba wai gardi ba, ina son SUDAIS sai dai da kudinsa na fi son sa!

Rauda ta ci gaba da ninke kayansu tana sauraron hiraraki har suka zo inda ya kore su irin tsoron da Rauda ta ji
Nana Mariama ta yi ta dariya tana kallonta ta ce" oo, Rauda Allah ya shirye ki ke kam

Itama murmushi ta yi tana kara hango fuskarsa da irin hararen da ya zabga masu du dan kawai sun yi masa sanu a ranta ta furta" ina tsananin tausayin mutanen da yake mu.amala da su, ina tausayin kowa ciki harda matarsa shi yasa nake tausaya maki auntyna

Tana gamawa suka shiga shirin dora tukunya dan kuwa weekend ne, aman kowace a kasan zuciyarta tana zulumin abinda zai faru ranar litinin da aka ce za.a hadu a tsakar ma.aikatar cikin shukoki


Yau lahadi, tunda yama yake bangaren Hajiya kaka, sun sha hira kamar kulun har lokacin bacinsa ya kusa dan haka ya mike yayi tafiyarsa aman ya manta wayarsa a nan

Hafsat dake zaune ta dauka cike da murnar zata turi kudi yau ta shiga ta tura, bayan ta gama sai ta yi sha.awar shiga hotuna dan ta yi kallo

Kalo take sha du yawanci na kalolin kayayakin da yake siyarwa ne irin wa.inda da an bugo sabin kala ake turo masa a yanzu da ya taho daga saudiyar da kuma idan baban harka ta samu ta gold da ake turo masa hoto dan ya fara gani kafin a je a auna

Ta shagalta kayayakin sun birgeta sosai sai kuma ta fito ta shiga wani dossier din wanda a cikinsa kuwa hotunan yara ne, kyawawan yara yaran larabawa, yaran hausawanmu, yaran turawa bulbul da su , haka kawai ta ji tausayin yayan nata ya darsun mata a zuciya
Ta fita sai ta ga wani dossier shi kuwa an rubuta *MATA*
Maimaita sunnan ta yi, sai hakan ya bata a kwakwalwarta mata ko kayan mata ne irin sana.arsa
Ba tare da tunanin komai ba ta shiga,
Mamaki ne ya kasheta a zaune, ido ta shiga tsurawa hotunnan nan, wani waje yarinyar ta fito daga aji, wani waje ta tsayar da adaidaita, wani wajen zata shiga wani gida, wani wajen tana hira da yar uwarta suna shan dariya irin ta yi murmushi
Mamaki ne ya kashe hafsa a zaune, ta yi tsai tana kallonsu, fuskokin nan nasu kamar ta sani aman a ina ta san su? Sannan mai ya hada hotunan nan da yayanta? Mai kalmar *MATA* take nufi?

Kanshin turarensa ya isar mata da sakon zuwansa wajen da take, dan haka da gagawa ta fita a wajen tana kokarin bude wani wajen ta dan dago ta saci kalonsa

Tsaye yake ya harde hannayensa yana kallon kanwar tasa, a ransa yana mamakin irin yanda bata tsoronsa take aikata abubuwan da ya hana,
Hannunsa ya mika mata kawai ta sako masa wayar ya juya yayi tafiyarsa

Ajiyar zuciya ta sauke ta mike tana tunani, a kasan zuciyarta tana fatan All3 ya sa haka ne, da kuwa ta fi kowa murna yayanta ya kamu da so ko menene?

. Ranar monday

Rana ce da aka tashi da lumshin hadari, safiya ce mai cike da ni.ina
Lunlumin nan ya saka du ake gannin tamkar safiyar bata gama wayewa ba ,

Karfe bakwai da rabi du wani ma.aikaci ya halarta a harabar jardin din da zasu yi meeting

Aisha na tsaye kanta a kasa, du irin gyaran fuskar da ta sha ta goge shi da ruwan hawaye sakamakon kiranta da aka yi da zuwansu aka wanketa tas tare da kwakwaran kashedin idan ta kuma aikata abinda ta aikata za.a koreta a ma.aikatar tare da fita hakinta na iya adadin aikin da ta yi masu a ma.aikatar sannan aka canza mata waje tare da fadin bata cancanci wannan waje ba

Rauda na kusanta tana tambayarta lafiya? Kasa kasa aman Aisha ta yi shiru ta kasa bata amsa

Wajen kuwa ya cika da tsararun ma.aikata, yan mata sai gwali ake an sha kyau sosai da sosai,
Samarin ma du sun sha cost matan aure sun sha lulubinsu masha Allah, wajen ya hadu da dan duhun hadarin nan yana bayar da dan gumi gumi sanadiyar daurewar da hadari yayi sai kanshin turaruka kala daban daban ba wari a al.amarin

Salif kuwa da sun hada ido da Rauda zai sakar mata mirmushi ne mai sanyi ita kuwa sai ta sada kanta kasa tana dan murguda bakinta tana fadan kallon yayi yawa


Suna haka ya fito ta kofar dake kallonsu, a yau yayi shigar hausawa ne, ya saka shada kalar ruwan baki ya dora hula ruwan zaren da aka yi masa aikin shadar sai takalmi kafa sau ciki baki na fata

Gaba daya da kallo suka bi shi, ya hasko wajen dalilin kalar fatarsa da ta yi luwai luwai tamkar ba rana a kasar

Yana tsayuwa guard dinsa biyu suka tsaya a bayansa wanda daya ne kawai ake iya hangowa sayan kuwa fafadan kafadun Sudais sun kare shi kwatkwatA

Da sauri adjoin dinsa ya mika masa farar takarda doguwa bayan ya risina

Karba yayi ya dan duba, ya dago ya cire dan siririn bakin gilas din dake idannuwansa

Murya kasakasa, ya furta " ASALAMU ALAIKUM"
Da ba dan yar lasifikar😌 dake sakale a kunansa ba da ba wanda zai iya jiyo shi domin yawan mutanen da kuma yar tazarar dake tsakaninsu

Ci gaba yayi da magana kamar haka" du wani ma.aikaci na gidan ya san rules din mu, du wani ma.aikaci kafin a dauke shi sai an bashi takardar yarjejeniya ta kulawa da aikin da ya kawo shi idan kuwa ya taka mana dokoki da irin hukuncin da ya dace da shi

An gina Abaya nd Gold kampani ne bisa abu daya! Shi ne *NEMAN KUDI*

A cikin rules din gidan nan wace zan kuma nanata maku shi ne ba sani ba sabo, idan kana da damuwa ka zo ka tarar da ni, idan barin aiki ne da ni zaka yi magana, ko wata iri ce damuwarka ni zaka zo ka gani
Ya karashe da nuna kansa wanda hakan ya baiwa sauran damar dagowa suka kuma kalonsa dalilin kwarjinninsa da haibarsa ya sa suka furta *MASHA ALLAH*

ya ci gaba da fadin......
















*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




1⃣4⃣



Ya ci gaba da fadin" an samu canje canjen poste da aiki, domin an tace an tantance kowa irin aikin da zai yi dan haka du wanda aka ba aikinsa sai ya bada hima ko ya rasa dan ba zamu yi sanya da aiki ba kampani ya samu matsala

Ya jima da yin shiru ya ce" du mai matsala da hakan yana iya samuna ni ba mataimaki ba wani ba,
Ma.asalam

Yana gamawa ya ajiye takardar da aka rubuto bai karanta komai ba, guard dinsa daya ya dauka suka bi bayansa

Yana shigrwa kowa ya ksma gabansa ya nufi ma.aikatarsa

Su Rauda na zuwa suka shiga aikinsu suna hira tsakaninsu cikin raha da mutunci

Shigowa mataimakin Sudais ya yi , bahaushe ne bakin mutun dogo mai sunna sidik, yana zuwa suka gaishe shi

Amsawa ya yi da yar fara.a dan kuwa akoy fahimtar junna a tsakaninsu
Takarda ya mikawa Rauda ya ce" ki saka hannu a nan na kaiki wajen da aka canza maki

Ido ta zaro , su basma kansu nan da nan suka hade rai suna kallon juna domin kuwa sun yi sabo harda na mamaki, dan kuwa suna zaune ne da fahimtar juna ana mutunta juna a yi wasa da dariya

Jiki a mace ta dauko pos dinta ta mimika masu hannu tamkar ba zasu kuma haduwa basma ta dan rumgumeta irin gaisuwar larabawa sukai salama kan sai sun hadu lokacin cin abinci ta bi bayan Sidik

Yana gaba tana biye da shi a baya, abin mamaki sai gasu a office din Aisha, da sauri ta kale shi da alamun karin bayani

Ya ce" nan ne sabon office din ki, sai ki maida hankali a aikinki banda wasa idan kika yi wasa da damar nan za.a canza maki ne dan kuwa wace t fita ta yi wasa da damarta ne so be careful

Tana kallonsa tamkar sakara har ya fice bayan ya gabatar mata da litafin program din aikinta daga litinin har juma.a
Sai can ta yi firgigit ta zazaro idannuwanta waje, hannayenta biyu ta dora a kanta ta furta" ina ba zai yiwu ba, nan fa office din aunty ne, aman ina take ita auntyn? Ina aka mayar da ita, mai ta yi? Ko shi ne sanadiyar fushinta? Ya Allah ka shige min gaba ka fi kowa sannin aikin nan dan me nake yin sa, ka fi ni sannin abinda ya dace da rayuwa ya Allah kar ka bar wata fitinar ta kunno tsakanina da aunty a sanadin wannan waje , ka sa wajen da aka kai ta ya fi yi mata dadibkan nan

Ta jima kafin take daukan litafin, dan kai kawo ta shiga yi tana karanta abubuwan da suka zama wajibi ta yi a kulun
Ajiyar zuciya ta sauke ta kai dubanta wajen takardun da sai ta bi daya bayan daya na office office ta duduba rubutun da aka yi ta karanta sannan ta kai office din oga ya sa hannu ta dawo ta bi office office ta rarabawa kowa, haka zatana yi ko wace safiya kafin ta dawo amsa kiran masu bugowa dan yin magana da oga idan ya zama wajibi su yi magana ta kai masa idan kuwa bai zama wajibi ba ta karbi bukatar mutun ta bayar da order a yi, aikin Rauda dai baban aiki ne wanda mafi akasarin masu malakar wajen nan sai sun karanci abin, sannan sai mai hazaka da hakuri

Cikin gagawa ta shiga dubawa sai dai du gagawanta bata samu ta dube gaba daya takardun ba gannin ta dora lokaci sosai ya sa ta saka farar takarda a tsakiyarsu ta mike ta gyara zaman hijabinta ta dauka ta yi office din Sudais

Zaune yake yana amsa kira a waya, magana suke da mahaifiyarsa ya bada nutsuwarsa gaba daya

Rauda kam tana zuwa ta dan yi knocking ,

Tsai yayi ya zuba mata ido ta cikin computer, har sai da mamansa ta maimaita kana ji na kuwa?

Sudais ya sauke ajiyar zuciya ya ce" eh mommy , yanzu du yanda kike so a yi a yi kawai

Ta yi murmushi tana fadin daman na fadawa abanka baka da gardama kan wannan tsarin ba zaka fara ba

Tana gama fadar hakan ta kashe wayar shi kuwa ya mika hannunsa ya dana abinda ke saman table dinsa wanda ke aiki da kofar wanda sai ya danna shi kofar ke buduwa

Da salama ta shigo kanta kas, tana matukar jin tsoronsa da kwarjininsa haka kawai bata iya sakewa da shi har mamakin karfin halin yayarta take ganni da ta iya tunkararsa da kalmar "SO

Tana zuwa ta gaishe shi da turanci ta gabatar masa da takardun

Sai da ya duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa na hagu ya dago fuskarsa a hade bai ce komai ba ya amshi takardun ya shiga saka hannu
Yana tsaka da sakawar ya zo daidai farar takarda, ya dauka ya shiga jujuyawa ya dago yana kallonta , har zuwa lokacin bai furta mata kalma ko kwaya daya ba

Idannuwansa da suka sauka a fuskarta suka saka ta shiga halin daburcewa dan kuwa sai ta shiga dan sosa goshinta da yatsutsanta na dama har wani dan gumi ya fara karyo mata

Inda indar da bata san tana da ita bace ta same ta lokaci guda ta ce" am am am.....daman su na kasan nan ban karanta ba domin ina tsaka da karatun na ga lokaci ya kure kar na yi laifi shi ne na kawo maka su haka dan na san ai ba zaka saka hannu a iya karatuna kawai ba

Tunda ta fara magana ya tsare lebenta da kalo, wanda idan har ba tsayawa ka yi ka kare masa kalo ba ba zaka fahimci shi din yake kallo ba, tamkar mai hararan fuskar nata, da zuciyarsa yake kokowa yanai wa idannuwansa fada kan ba kyau irin kallon nan aman ya kasa kauce idannuwansa,

Dago da idannuwanta ta yi a dan tsorace jin yayi shiru, sai ta ga harararta ne yake ashe, da sauri ta kuma sada kanta ta hade hannayenta tana wasa da su

Da kyar ya aro jarumta tunawa da yayi abinda yake son yi wato yakice ta a ransa, cikin dakakiyar mirya ya ce " kin san mai ya kawo ki wannan ma.aikata kuwa?

Da sauri ta daga kanta gabanta na faduwa tana tsoron ya kore ta,

Ya ci gaba da fadin a wani waje kika yi stage ne? (Sarai ya san bata yi ba)

Da sauri ta dago, hankalinta ya fara tashi , bakinta ya shiga rawa dan kuwa ita ba karya zatai masa ba aman kuma tana tsoron gaskiyar ta haifar mata da matsala, shi kuwa yayi shiru da dukan alamu sai ta bashi amsar zai saurara mata

A hankali ta ce" ban yi stage ba

What ? Ya fada da dan karfi yana mai dan fitar da idannuwansa, ya dafe goshinsa da yannayin takaici ya ce" ki saurare ni da kyau, nan ba wajen ki zo ki koyi aiki ba ne, wajen ki zuba basirarki ne ki yi aiki tukuru, takardun nan ki koma ki karance su , ma.anar ki fara karantawa dan koda da wani abinda bai dace ya karaso wajena ba ki cire idan kuwa baki fito da niyar aiki ba sai ki kara gaba

Sauraron tsagwaron rashin mutuncin wannan bawan Allah take, mamaki fal zuciyarta to aman meye laifi dan bata iya aiki an koya mata ba?

Cikin sauri ta shiga tatarewa hannunta na rawa ta juya da sauri ta koma office dinta, wato dai lokacin da ya dace ta je ta ci abinci sai ya kasance ta kare shi a aiki


A wannan ranar bata gama aiki ba sai da ta yi yama sosai ta fito a office din inda ta ga sai yan tsiraku

Neman Aisha ta yi bata ganta ba ta juya ta kama hanya ita kadai

Tana shigowa gida magariba na kawo kai, ta shigo da muguwar gajiya har juwa take gani sai dai kafin ta rufe bakinta da salamar da ta yi sai ji ta yi an dauketa da mari

Da sauri ta kallo mai marin, Mamaki shinfide a fuskarta, Muryar mahaifinsu ce ta katse mata mamakinta yana cewa" Aisha, Aisha ina yi maki hani da saurin hannu, tabas kece yayar Rauda aman ki kiyaye saurin bugu sannan yanzu na gama fadar ki yi hakuri ta zo na ji ko?

Murya a raunane Rauda ta ce" Aba me na yi?

Mahaifinsu ya ce" Rauda, ya aka yi kika amince da wajen da yar uwarki take so bayan kina da zabin kin karbar aikin?

Cike da mamaki take kallon Aisha, dama saboda wannan aikin ta zabga mata mari haka?
Bata gama tunaninta ba Aisha ta ce" ta fada min daman tana daya daga cikin masu bakin cikin wannan waje nawa ko me? Daman idan na hau abu na sauka zaki hau shi Rauda? Mai na yi maki da zaki yarda ki yi aiki a kusa da shi, a tunanina koda korarki za.a yi ba sai dai a kore ki ba? Shi ne aka kai ki wajen da nake aka kawo ni wajen da kika bari cikin matan da suke tunanin kanmu daya da su? Du sai na sa ya kore su daya bayan daya, sai na zame masu barazana a aikin su, domin ni na fi karfin su !

Tana gama fadar haka ta juya ta shige ranta a bace, mahaifiyarsu kuwa ko kanzil bata ce ba alamu dai itama tana goyon bayan abin

Murmushi mai ciwo Rauda ta saki, ta kali mahaifinta ta ce" ka yi hakuri Aba , insha Allahu gobe zan je na ajiye aikin dan samun farin cikin kowa a gidan nan


To readers shin ta ajiye aikin ne???





*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation






Please Login or Register in order to submit comment