Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikinta ke ciwo sakamakon dukan da Aisha ta yi mata, dan kuwa ta daketa kamar da wasa ta ce " a kulun fada maki nake ba kowa ya san darajar na gaba da shi ba, ba lale ne ki ce ke dole sai an mutunta maki iyayenki, ke ba karfin da zaki tari abin ne da ke ba, dole a wannan zamanin ka yi hakuri da rayuwa a yanda ta zo maka, haba Rauda haba Raudana

Tausayinta ne ya ji ya mugun kama shi, harma ya ji kamar ya juya ya shaidawa Elhaj wannan bukata da wuya ta yiyu , bai taba ganninta cikin rashin tudun dafawa irin na yau ba,
Daman zata yi sanyi haka?
Cijewa ya yi ya shigo gidan nasa da salama, wanda jin muryarsa ya sa Aisha ta yarda icen dake hannunta ta yi gagawar nutsuwa domin tunda abinnan ya faru wato auren da ya daurawa Rauda take shayinsa, ......

Malan AHMAD KENNAN
..



*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




2⃣8⃣

*WANNAN PAGE NAKI NE NA SIS LADEEFA ALKHAIRIN ALLAH YA TABATA A GARE KI*

kuna da yawa fa, walahi sosai kuna da yawa, na gode da kulawarku jiki yayi sauki alhamdulilah💓💓💓💓💓💓💓





Salamar malan ta saka Mariama juyowa da dan saurinta, ganninsa ya sa ta saki ajiyar zuciya domin ta san dai ko menene malan zai tare mata

Kallon su ya yi gaba dayan su , bai ce komai ba ya juya ya shige dakin su

Murna fal zuciyar Mariama domin rabonsa da ya shiga dakin su tun ranar da abin ya faru,

Hannun Rauda ta kamo ta tsayar da ita kofar dakin ta shiga ciki dan gudun kar Aisha ta kuma dukanta

Malan Ina yini

Kalonta ya dan yi ya amsa ciki ciki wanda hakan ya sa gwuiwarta ta dan sace

Neman guri ya yi ya zauna, ya ce" na dawo kan maganar auren yata , wace na isa da ita

Da sauri Nana Mariama ta sada kanta , bata ce komai ba,har ta tuna masa zamanin amarcin su

Ya ci gaba da fadin" na yi mata aure sannan mijinta ya shirya tarewarta domin ya ce yana so ta tare karshen satin nan

Da sauri ta kalo wajen sa, murya na dan rawa ta ce" malan karshen satinnan fa ka ce? Malan ai mu bamu shirya ba, mai muka ajiye? Mai zamu kai mata kayan daki, kayan kicin, gara? Sannan malan ai bai yi mata kaya ba kamar yanda ake yiwa kowa koda bazawa ce

Malan ya ce" haka ne, zancen kaya bai dame ni ba, ya yi bai yi ba tsakannin su ne, aman maganar kaya kin manta ajiyar da nake wajen liman? Duda sun nuna kar a yi mata komai aa, sai nai mata du abinda Allah ya hore min

Mariama ta ce" kar a yi mata komai? Me hakan ke nufi malan? Ko mai hali ne mijin nata?

Da san mamaki yake kallonta, ya tabata ba dan abin ya bata mamaki bane , bata dai bar maganar mai kudin ba, dan haka ya ce" aure na yiwa yata, ban nema mata mai kudi ba ko marar shi, fatana inda zan kaita ya zamto alkhairi a gare ta, bana son wani taro, idan lokaci ya yi kawai zan kaita da kaina

Da mamaki ta bi shi da kallo bayan ya gama ya mike ya shiga canza jalabiyarsa ya dauko wata a cikin jakarsa kano ta yi zahi ya canza ya dauki wanda ya cire da dan klin dinsa ya fice ya barta a gurfane tamkar mai neman gafara

Yana fitowa ya ga Rauda tsugune a nan, da yannayin tausayi ya bita da kallo, yana matukar son ya rarasheta aman baya so ta ga fuskar da zatai masa koke koke ko wani abin

Kamar da wasa yau alhamis, ya kama sauran kwana uku Rauda ta tare,
Malan ya siyo mata gado da armoire mai gida biyu kawai, ya sa akai mata kujerar roba biyu, ya sayo mata kwanon shinkafa bakwai, makaroni leda gom sha uku kaloli, magi kananuwa leda guda, mai littre hudu, su dangin dadawa, kayan yaji, tumatiri da sauransu daidai aljihunsa

Sai bayan ya kawo kayan gadon Aisha cike da shakiyanci ta fitar da kudi dubu hamsin ta ce a cikin kudinki na dauki sauran saura wannan

Mariama ta karba, bata iya ce mata komai ba domin kwatakwata ta dawo wata so silence, yannayin malan na damunta, ga irin yanda take gannin Rauda, bata cewa kowa komai sai dai ta zauna


Daman ita ba wata fitinaniya ba, idan abu ya dameta sosai takan yi ta kuka ne, aman akoy barancin fadin abinda ke cikin zuciyarta....sai dai wannan ba dama, malan ya ki ya saurareta haka ma Mariamar dan kar ta sakota gaba da kuka, aman har.yanzu Mariama a wai take gannin lamarin, aure fa ba wasa ba, danma wulakanci mijin har yanzu bai tako gidan da sunnan gannin matar ba ko gaishe da iyayen

Ajiyar zuciya ta sauke, ta je wajen malan da kudin ta mika masa tanai masa bayani

Kallonta ya yi ya ce" kirawo min su

Zuwa sukai Rauda Da Aisha suka tsuguna bayan sun yi salama

Malan ya amsa yana bin su da kallo, RAUDA ta rame, ta rame sosai ana gannin ramarta, ya dan girgiza kai ya ce" wani irin aiki ne kuke haka har aka baku albashi dubun hamsin?

Rauda bata iya cewa komai ba sai sada kanta da ta yi,

Aisha ta ce" Aba.ai mune masu karamin albashin ma, ai dubu dari da hamsin hamsin ne

Ya dago ya kaleta ya ce ya aka yi ya dawo dubu hamsin? Ke kuwa ina naki?

Aisha ba tare da wani dar ba, domin ita a ganninta ai hakan ba laifi bane ta ce" kudin makarantar nawa na hada da dubu darin Rauda da darin wajena na kai na zuba, sai ya rage dubu dari shine na raba na bata kasonta ni kuwa na sayo atampopi da mayafai sauran dubu goma sha biyar zan kai dinki

Da mamaki.yake kalonta, aa, Aisha wai ko dai bata da hankali basu sani ba suna daukan mumunan halaya ne da ita? Me ke damunta haka? Idan ita batai niyar duba halin da suke ciki ba ai sai ta tausayawa na kanwarta, atampopi, a tunaninsa ta kai wajen da zata yi tunanin daidai da abinda ba daidai ba
Wani tausayin Raudar ya kara lulube shi, ya ce" Aisha dauko min atampopin

Mikewa ta yi ta je ta kwaso sayayar da ta yowa kanta, ba tare da ta sayo kwarar shinkafa ba, ba damuwarta bane sun ci ko basu ci ba ita dai ta san du rintsi dole mahaifin su ya basu koda garin kwaki ne, idan kuwa cikinta ya dauka koda me ta ci bata da damuwa ita dai damuwarta ta saka mai kyau a yi cudanya da ita cikin yayan manya

Dadaga atamfofin ya yi, wajen kala goma sha daya ne manya guda takwas sai kananu guda uku,
Cikin nutsuwa ya kasa biyu, dayar da ta hayo ya ware gefe, ya dauki mayafan ya kasa suma biyu wato hudu hudu
Da kansa ya zabarwa Rauda kashi gudan ya turawa Aisha guda wace ta yi kasakai tana jiran karin bayani
Gannin bai ce da ita komai ba ya sa ta ce" Aba, kayana ne fa?

Idannuwansa ya dago a hade, ya ce" Eh sai na raba maku da kanwarki ba, ai kudinta naki ne, abinta naki ne kamar yanda yake naki nata ne

Ranta a matukar bace ta mike ta bar kayan a nan ta shige wajen mamansu ta fashe mata da kuka tana fada mata wai Aba ne ya kwace mata kayanta ya baiwa Rauda bayan ita an yi mata aure ko yaya dai mijinta ai zai yi mata sutura komin talaucinsa

Muryar Malan ce ta katse ta ya ce" Aisha, Aisha, ina miki tsoron rayuwa, ke ko kunya bakya ji? Kin kama kudinta kin kashe ke mai son kanki dan na raba abinda kika sayo shine zaki zo kina daga murya? Aisha kayan nan gaba daya ba zaki saka ba sai ki je gidan da kika san za.a hukunta ni ki fada, kuma wannnan dubu hamsin din zan mayar da gadon nan daman dubu ashirin na sayo mata shi sai na cika gaba daya a bata na gani na fada ke kuwa mu zuba ni da ke da du wanda ya daure maki!


Yana gama fada ya fice ya bar Mariama da sakin baki tana mamakin su malan harda habaici aka koya? Shi dai bai mata kirikirin da ita yake ba aman kuma bai boye nufinsa ba, Aisha kuwa kara volume din kukanta ta yi tana rantse rantsen idan ya dawo da dinkunnan sai ta kwashe abinta ai ita ta yi aikinta ba wani ba

Ranar asabar mota yar kurkura ta kwashi kayan Rauda aka loda ta kai ta dawo ta kuma kwasa an yi kaiwa uku kafin ake kwashe komai, direban nan dai kurmanta ya yi jigilar nan, yana gamawa ya dawo ya kai Mariama ita da Aisha dan gyarawa Rauda daki bisa umarnin Malan

ELHAJ SUDAIS kennan, dan karamin gidan Samir ya sa samir ya kama masa, daki biyu ne kwal, da bayi a cikin kowani daki sannan dakunnan ba wasu tafka tafka bane,
Tsakar dakin da dan fadin sa sai kicin a tsakar gidan

Hankalin Mariama ne ya dan kwonta, duda bata so yarta ta auri mai dan hali ba aman irin wannan ginnin ma ba kowa ke samu ba, dan kuwa ya isheka zaman duniya

Aisha kuwa dariya ta ringa yi ta ce" mama, wannan gidan da gidan mu mai ya raba su? Abinda ya raba kawai gidan mu ginnin laka ne wannan kuwa na suminti ne aman kin ga gida kukub shima tamkar akurkuki? Kai Allah kai damo ga harawa mama, aurena da Elhaj ya tabata zaku sha kallo, yan uwanki sai sun dawo suna baki hakuri dan su sami wajen zama

Mariama ta yi murmushi ta ce" Allah yarda Aishana

Aisha dake buga labule da kusa ta ce" yama yarda tunda ya kaini aiki kampaninsa

Mama ta ce" aa, wai kin tabata ba za.a kore ku a ma.aikatar nan ba kuwa?

Aisha ta ce" ai ba ni na mare shi ba, Rauda ce, sai na fada masa ya yiwa girman Allah ya barni na yi aikina wace ta yi masa wannan aikin an yi mata auren dole an hadata da talaka irintA!

Mariama ta dan girgiza kai ta ce" da alama halayenki daya da aunty , yanda kike kin jinnin talaka tamkar ita ta haife ki, ni kuwa soyaya bata barni na ga aibun abanku ba a lokacin

Aisha ta sauko ta kamawa Mariama shinfida tabarmar ledar ta ce" hum Mama, ai walahi ba zan boye maki ba kin cuce mu! Da kika auri aba, ni fa kunya nake ji a nuna shi a matsayin mahaifina, kaf anguwar mu mune karshen talakawa shi yasa ko zaka aka fitar sai dai ki ga yayan manyan nan sun kwala salama daga kofa an miko mana zaka, ga nakasasu ko? Wa.inda basu da komai....


Mariama ta girgiza kai ta ce" aa kar ki ce haka, kowa da irin destin dinsa Aisha

Destin? Mama destin, ai mutun na iya juya destin dinsa ya dawo masa yanda yake son ganninsa

Mariama ta ce" lalalalla, ko daya, rubutu ne Aisha, du yanda Allah ya tsara maka haka yake zuwar maka, a gaskiya bana fatan irin rayuwar babun da nayi yayana m su yi, ina muku adu.ar samun nutsuwar rayuwa, shi kuwa farin ciki konciyar hankali shi ne gaba da komai

Aisha da ta ajiye kujeru hudu , kennan an saka labulaye an sa kujeru, an sa dan prm mai sunnan Allah guda biyu, sai tulu daga can gefe dakin ya gama haduwa da iya abubuwan nan ta shiga tsakiya ta nunawa mahaifiyarta ta ce" mama , farin ciki? Konciyar hankali a nan? A nan ai ba konciyar hankali, ba maganar wasa da dariya, ba maganar samun nutsuwa, talauci? Ai talauci bai yi ba, baki ga yanda talaka ke bacin rai ba? Ai yanda aljihunsa yake ba annuri haka zuciyarsa take, mama, ke dai kawai a yi rayuwa aman ni? Ba zan auri talaka ba!

Girgiza kai Mariama ta yi, ta lura in dai kan wannan maganar ne Aisha ba zata taba sauraronta ba dan haba kawai sai ta yi gaba ta kyaleta, ita kam dakin Rauda ba laifi, daidai talaucin su sun yi kokari sannan gadonta an samu da setinsa komai ya yi kyau sosai

Haka suka gama suka share ko.ina suka kara wanke bayin suka fice

Ba kunshi, ba kitso Rauda? Ban ji kina neman mai kunshi ba yar gidan Abanta
Malan ne ke tambayar rauda da yama bayan ya dawo ya tarda ita ta yi wujiga wujiga da ita sai kallon waje guda,

Murya a raunane ta dago ta kali Abanta ta ce" Abana, ka yafe min Abana
Sai hawaye sharsharshar

Waje ya samu ya zauna kusa da ita , a hankali ya kamo hannayenta biyu hakan ya sa ya ji jikinta zafi rau,
Zuciyarsa ce ta karaya, ya ji idannuwansa sun cika da hawaye, murya da alamar rarashi ya ce" kin kasance mai yi min biyaya, kin kasance mai yi min godiya a dukan abinda Allah ya nufe ni da samu kin kasance mai karfafa min gwuiwa, LALLA RAUDA albarka ita ce a kulun nake saka maki, Rauda ba zaki wulakanta a duniya ba, ki kadara komai ya same ki rubutacen al.amari ne ba wanda ya isa ya ja da hakan!
Ki kontar da hankalin ki, na san rashin gannin wanda na aura maki na damun ki da rashin sannin ko waye, mahaifinsa ya gabatar da maganar ya zo ku gana sai dai wata fitina da ta bilo a nan gidan wace sai bayan daurin auren nan na fahimci komai ya sa na kiyewa maganar zuwansa, sunnan mijin ki *SUDAIS MUHAMMAD*
Dumdum ta ji gabanta ya fadi aman kuma sunnan yayi mata taushi a harshenta, sai ta tsinci kanta da maimaita sunnan a kasan zuciyarta tana mai adu.ar Allah ya sa mai tausayi ne

Malan ya ci gaba da fadin" kar ki yarda rudin duniya da mugayan mashawarta su saka ki canza halayen ki na kirki, ki kasance mai yawan adu.a da hakuri sannan ki yi masa biyaya, na tabata koda da wata manufa ya karbi auren ki Allah zai hana shi wulakanta ki

A gaskiya ta ji maganar mahaifinta ta sanyaya mata zuciya, ta ji zuciyarta ta samu nutsuwa, a hankali ta dora kanta saman hannunsa daidai nan mai kunshin da Aisha ta je nema ta shigo

Lale ta zanawa Rauda dan kadan, bashi da wani yawa ta kuma zanawa Aisha kafa da hannu itama kuma jan lale ne yayi masu kyau sosai

Malan dake zaune saman tabarma , sosai fuskarsa take cikin annuri ya kali Mariama ya ce" Mariam

Da dan sauri ta kalo wajen sa, rabonsa da ya kirayeta da sunnan nan har ta manta,
Kalonsa ta yi sosai ta amsa tana rike da hannun Rauda guda dan kar na yatsutsan su hade,

Malan ya dan yi murmushi ya ce" kema a zana maki mana kunshin

Da mai kunshi da Rauda suka sa yar dariya, somin yanda Malan ya yi maganar abin sai ya mugun baka dariya, haka Rauda ta ji zuciyarta wasai domin Mariama ma biye masa ta yi ta mika hannunta bayan an gama yiwa Aisha aka zana mata

Mai kunshin dai itama ba wata mai shi din bace, malan ya zare har dari bakwai ya bata ta tafi tana ta godiya

Ba yanda Mariama batai ba dan Malan ya amince a dan yi taro aman ya kiya,

Rauda kam ta dawo kuma sai ido, gashinta batai masa komai ba kiyawa ta yi a yi mata kitso sai kawai dan shirye shirye da ake yi a cikin gidaan nasu

Da kyar Mariama ta roki malan ya baiwa Aisha 2 complet a cikin kayan nan aman ta ki karba dan haka da haushi ya karbe ya hadewa Rauda a sabuwar jakarta kano ta yi zahi, dinkunnan kuwa sun mugu mugun yin kyau domin telan yan mata ya kaiwa ya bashi abinda gare shi shi kuwa ya yi mata dinkunna ba laifi

Rana bata karya sai dai uwar diya ta ji kunya,
Ranar lahadi ranar *tarewar Rauda*



...........mu je zuwa......



*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




2⃣9⃣













A yau ranar lahadi, yau ne ranar tarewar Rauda

Tunda safe take konce a dakin su, ta yi shiru ta afka tunani..... a zuciyarta sai kokowa take da tunanin kwakwaluwarta fadi take"
Aure ne aka yi min, tunda aka aura min mutumin ban taba ganninsa ba , shima hakanan duba da wasikarsa ta farko,
Ban san halayarsa ba sai sunnansa kawai da Aba ya fada min ,
*SUDAIS* wanene kai? Shin bawa ne mai son kusanci da Allah mai burin tashi a kusa da ma.aikin Allah salalahu alaihi wa salam, mai son tashi ne babu shanyayen jiki? Shin ka kasance mai aure aure ne ya sa ka karbi aurena ba tare da ka yi tunanin komai ba irin ni wacece, halaya na, tarbiyana, mai tausayi ce, na iya tatalin rayuwa? Sai kawai ka aure ni........
SUDAIS ni dai *BANI DA ZABI* a yanda rayuwa na zata kasance..
SUDAIS ina fata ka zamto min *ZABIN ALLAH*

Muryar Sarah ne ta karade gidan tana rafka salama daga bakin kofa

Da murnarta Mariama ta fito ta saka sabuwar atamparta ta tarbi auntynta

Kallon sama da kasa take binta da shi, Sarah kuwa ta dare saman kujerar malan ta roba ta dage kafafuwanta sai yatsina fuska take dan har cikin zuciyarta kyankyamin yan uwan momynta take

Aisha ce ta gaishe su itama ta zauna tana sauraron yanda mamanta ke baiwa yar uwarta labarin yanda auren ya kasance

Aunty ta ce" lalle kin bari Ahmad ya ga damarki fiye da tunnanin mu, yanzu in ba wulakanci ba daga wannan yar maganar shikenan sai cibi ya zama kari? Daman da niyarsa in kin ga haka Mariam, mai yiwuwa mutumen mai abin hannunsa ne

Aisha ta yi carab ta ce" aa aa, talaka ne tukuf, talaka ne na sosai baki ga yanda gidan da ya kama mata yake ba kuma da ganni ba malakinsa bane gidan haya ne

Sarah ta yi wata irin dariya ta ce" ba dole ba, ai sai takama da kyau ita bata gannin talaucin dake gidinta sai shegen girman kai tana dadagawa mutane kafada wancen lokacin kinga yanda take hararan mom dan ta fadi mahaifinku talaka ne? Ita fa bata zuwa gidanmu ko da aike wai ita mai son uba kar a zagar mata ubanta

Aisha ma dariyar ta yi ta ce" kai , ai ba.a kwana biyu bata sha marin mama ba, dan kuwa daga an aibata aba shikennan sai ta buga ta tare

Sarah ta yatsina fuska ta ce" sai kace wani mai biya mata bukatunta na yau da kulun, ni dai da ace Mom ta auri talaka da ta janyowa kanta masifa wly,


Aisha ta yatsina fuska ta ce " haka dole muke zaune, aman ni wly idan abana talaka ne ba zan auri talaka ba, yanzu haka tana ji tana gani za.a kaita kamar wani auren tsohuwar bazawara marar galihu ko dan taro baza.a yi ba

Rauda dake daki tana jin du abinda suke fada ta kara gyara konciyarta tana tir da wannan halaya nasu, su nan har sun sami abin jifanta da shi, ai ita alhamdulilah an ga nata auren su su kuka da kansu ba burin zabo mai kudin ba duniyar nan da ta rikice haka sai a slow

Zaman Mariama da aunty a wunin nan ba wani zaman an zo tayata murna bane, zama ne ta yi ko ruwan gidan bata sha ba sannan ta wuni ne tana yi mata gore gore da abubuwa dai mararsa dadi hakan ya sa ta kara tsurewa du ta shiga tunanin rayuwar da Raudanta zata je ta yi

Da yama sukai tafiyarsu bayan aminci ya kulu tsakanin AISHA da Sarah abinka da halaya daya

Bayan salar magarib, Aba ya fito tsakar gida ya tarar da yayansa da matarsa suna zaune sun yi jigum jigum suna jiran dawowarsa daga masalaci domin ya fada cewar da ya dawo za.a tafi
Daidai wannan lokacin baraka makociyar su ta kawo turaran wuta da humarar da mama ta bada dubu guda da dari uku aka kawowa Rauda,
Mama ta karba ta saka a jakar Rauda tana yiwa Baraka godiya wace ta bisu da kallo tsegumi cike da cikinta wai an yiwa Rauda Aure, wa ya aureta? A ina aka daura auren? Ya aka yi basu yi taron tarewarta ba ? Duda akoy halin babu a tare da su aman babun bata kai nan ba gaskiya haka dai ta juya ta tafi ba dan ta so ba sai dan bata samu fuskar tambaya ba

Malan ya shigo, sabuwar doguwar fara jalabiya ce a jikinsa, ya kafa hularsa harda turare ya fesa masha Allah malan ya fito das da shi

Da kallo ya bi su inda ya tsayar da kallon sa kan Rauda,
Bakin dogon hijabi ne ta dora kan riga da zaninta na atampa, ba walwala ko daya a tare da ita sai ma lagadab da ta yi

Dan girgiza kansa ya yi ya dauki babar jakarta ya fita ya dawo ya dauki kondon kayan sabulunta da kayan kwaliyar da ya dan tsintsinto mata ya kai ya dawo
Shi kam bai san mai zai fada masu ba, ya yi mata nasiha a jiya har shiga baci yanai mata nasiha dan haka ya umarceta da ta mike su tafi

Gabanta ne ya fadi, zuciyarta ta karye, ta mike a hankali ta dan fara takawa
Mariama dake tsaye ta rungume hannunta na dama saman kirjinta, ta bi yarta da kallo,
Ji ta yi wanni irin kuka ya zo mata wanda ta kasa rike shi
Tun karfinta ta sake shi ta furta sunnan RAUDA da dan karfin da ya sa Rauda ta tsaya cak daidai kofa kusan Abanta

Da sauri mariama ta karasa ta rungume Rauda a jikinta wace itama ta saki kukan zuciyarta na tsale tana jin kamar ta shige cikin mamanta ta huta da wannan tashin hankalin
Murya a raunane Mariama ke san bubuga bayan Rauda ta ce" its ohk Lallana, kin san me na tabata ba zaki sha wahalar rayuwa ba domin kin kasance mai biyaya
Kina iya kokarinki dan gannin kin fita hakina ni magaifiyar ki, kin fita hakin mahaifin ki, sai na yar uwarki,
Rauda ina sane da dukan abinda ke faruwa, ina sane da dumbin hakurin da kikai ,
Wannan aure da yardar Allah sai ya zame maki alkhairi, ki yi hakuri da jarabawar rayuwa kowa da irin tasa, kuma indai bawa ya cika mai imani sai Allah ya jarabce shi

Ajiyar zuciya Malan ya sauke yana kallon Mariama, ya ji dadin kalamanta wa Rauda, a kasan zuciyarsa ya furta" Mariamana kennan mai hali kala daban daban , wataran ta yi halaya mai kyau da nagarta wataran kuwa ta tsula tsiya😁

Haka ta rako Rauda har bakin mota,
Mota ce baka yar madaidaiciya da direba kurma a ciki
Haka suka shiga suka dauki hanya wanda suna tafe Aba na kara yi mata nasiha kasa kasa

Suna karasowa kofar gidan Aba ya ce" yaro makulin gidan a wajenka ne?

Kurman direba ya dan juyo saitin Aba ya ce" Aa Aba ai an zo an bude gidan an kuna inji

Da mugun mamaki take kallon sa harda sakin baki ta ce" kai Aba daman wannan yana magana?

Aba ya

Please Login or Register in order to submit comment