Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zubar da aji su da kansu zasu fadawa namijin suna son sa, wasun kuwa cikin dabara zasu karlato da hankalin saurayin, wasun kuwa koda soyayar namijin nan zai kashe su ba zasu taba amincewa su sanar masa ba da jan aji da gudun kar namijin ya raina su

Sudais ya zauna da kyau kamar da gaske dauka yake ya ce" to ai ni ba zan rainata ba dan ta furtan kalmar so, ainahi ma shine abinda nake zaman jira a nigeria Samir

Samir ya yi tsam, ya kare yiwa ogan nasa kallo, a ransa yake fadin lale oga bashi da ranar barin kasar nan,
Samir ya ce" aa oga ai kai ya dace ka tunkare ta, ka nuna mata alamar soyaya, ka furta mata kalaman so hakan zai sa ta karbe ka kila wa kala

Sudais ya yi murmushin da bai kai zuci ba ya ce" ya ake yi kennan?

Samir ya dago galala yana kalon sa, wai yanzu yana nufin bai taba yin haka wa matansa ba?
Aman dan gaskatawa ya ce" ai oga yanda kake nunawa Su Gajia

Sudais ya girgiza kansa, ba zai iya furtawa Wani sirrin dake tsakaninsa da matansa ba, ba zai fadi hakan ba, dan haka ya kuma sakin murmushi ya ce" kana dai nufin na shirya, na yi wanka na je kofar gidan su na aika yaro kiranta, idan na ci sa.a ta fito sai na isar mata da sakon zuciyata cikin lalami da roko ko?

Samir ya saki murmushi ya ce" haka nake nufi oga, ka lalabata ka bita zaka ga an dace

Sudais yayi yar dariyar da rabonsa da ita har ya manta, ya tafa hannayen sa biyu ya nuno samir ya ce" SAMIR ai ban san cewa tare da dakiki nake zaune shekara da shekaru ba sai yau! Samir ka tabata karatun sa ka yi ba.a yi maka taimako irin na yayan manya ba? Ina da ja a kararun ka sannan ina da ja a hankalin ka,
Kai yanzu yarinyar mai shekara 22 a duniya ce zan je godai godai da ni na hade hannaye ina neman soyayar ta? Karya take, kaima karya kake Samir, sannan du wani banzan da zai nufeta karya yake! *RAUDA'S MINE* kuma zata nemo SUDAIS dinta da kanta!

Samir galala ya yo tamkar sakarai, wai ashe du sauraron nan nasa da oga ya yi dan ya auna girman shirmen sa ne? Ya salam!

Sudais ya kakausa muryarsa ya ce" abinda nake so da kai ka tashi ka kai ni asibitin na canza mata waje na kaita clinik!

Yana gama fada ya mike ya fice inda Samir ya biyo bayansa da sasarfa a kasan ransa yana tambayar kansa ta yaya kennan hakan zata faru???




👏🏻😊👏🏻



*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




2⃣1⃣



Suna karasowa ya bi assibitin da kallo, ya girgiza kansa a ganninsa a irin albashin Salif ya kare a wannan asibitin?

Sauka ya yi daidai ana kiran salar magariba, kuma asibitin ta fi kusanci da gidan su Rauda domin ta kudi ce kuma a wajensu take

Buta ya dauka ya yi alwallah kamar yanda duban bayi suka yi suka shige masalaci dan gabatar da salar magarib

Suna gamawa yawancin jama.a suka fito inda da yawa suka zauna sai sun yi ta isha.i suke fitowa ciki kuwa harda Sudais da samir

A hankali samir ya dan matso Sudais na jan carbinsa fari kal ya nutsu Samir ya ce" oga ga mahaifin Rauda zai fita

Bai katse adu.arsa ba, bai dago kansa ba ya ci gaba da adu.a yana neman karin kusancinsa da ubangiji

Malan Ahmad ya matsa sosai kusan limamin masalacin ya duka ya sada kansa murya a raunane ya ce" Allah ya kara yawan Rai ina son dan tataunawa yanzu, a yi min afuwa na tabata yanzu daidai lokacin karatu ne aman ina tsoron a gama salah jama.a su watse ni kuwa ina da ciwo a zuciyata

Gama sauraronsa liman ya yi, ya kai aya ya ajiye alkur.anin dake hannunda ya ce" malan Ahmad mai ke faruwa haka? Na tabata baban abu ne

Malan Ahmad ya kuma sada kansa, ya shiga dan fadawa Liman kadan daga cikin abinda yake ciki na iko da matarsa take masa kan yayansa, ya gabatar masa da hujoji ya tunawa liman shi kansa ya taba yi masa fadan ya aka yi bai yiwa yayansa aure ba da an zo neman auren matarsa ta kori mutun baya tsoron sharin mutanen zamani?
Lima ya gyada kai yana sauraron sa

Ya ci gaba da fadin" yarinyar wajena wace du idan ana sauka nakan sakata a adu.ar Allah ya yaye mata irin zafin zazabin dake damunta ya yi mana dalilin da zamu hadu da maganin abin ce ciwon ya tashi

Liman ya ce asha asha subahannalah fatan da sauki

Malan Ahmad ya kuma sada kansa yana hangen agogon masalacin ya ga da saura lokacin sallar isha.i dan haka ya ci gaba da fadin" Alhamdulilah a zuwan da na yi dazu da yama tana zaune har ta ci abinci,
Liman Wato rashin lafiyar nan da ta yi wannan karon da farko abinda ya girgiza min zuciya wai na zo asibiti na tarar da Mahaifiyar tata ta canza mata asibiti
Ina zuwa na tarar an bata daki, kayan ciye ciye da shaye shaye a zuba kai dai abubuwan sun kai jarin wani mai karamin karfin

To da yake na tarar da yayarta ta zo ganninta sai na yi tunanin ko ita ta kawo? Dan haka da nuna fara.a na shiga godiya wa yayar tata na ce

Sai dai ban gama godiyar ba ta katseni da yannayi na matan da suka so su fi karfin mazajen su tana fadin" ai saurayinta ne ya kawo , ainahi ma saurayinta ne ya canza mata asibiti daga ta talakawa zuwa ta masu kudi,
Aka nuna min saurayin yana zaune ya hakimce bai yi tunanin ni mahaifin yarinyar bane aman a tunanina da yana da da.a koda ba kowa bane ni datijo ne
Mahaifiyarta ta ci gaba da fadin" ai kam Rauda ta yi ba zata, ana tunanin ta yi bakin jini ne ashe ita da wanda ke sonta zamu warke da talauci, ka duba ka ga Malan wannan sayaya duka a lokaci guda
Yar uwar tata ta furta" wannan ai ba komai bane, kema lokacin da kike soyaya da Elhaj brah ai kin ga, kaf cikin gidanmu har yanzu kece aka fara baiwa mota kafin auren ki aman kika bige da aurwn soyaya yanzu kike cin soyaya
Malan irin haka na faruwa a kulun kwannan duniya, abinnan na ci min tuwo a kwarya na hana ni sukuni
Yanzu so take Raudar ma daje tausaya min ta juye mata tunani domin yau da gobe sai Allah

Liman ya ci gaba da girgiza kansa, yana al.ajabin halayan wasu matan, a gaskiya a irin samun Malan Ahmad yana matukar kokari da iyalinsa aman rainuwa da raina inda ya ajiye su ya saka a kulun bakin alkhairinsa matarsa ke gani har yarsa baba ta tashi itama da halayen karamar itace ya isa da ita, gashi itama ana kokarin cusa mata wani ra.ayin!

Murya a rausashe Liman ya ce" ka yi hakuri Malan Ahmad, ka kara hakuri, nima ka kara yafe min, domin da farko na yarda da abinda aka zo aka fada min cewar ka sakawa yaya ido suna abinda suke so da matarka a anguwa, sai daga baya na fahimci matsalar, ka kara hakuri malan Ahmad ka daina sakawa a ranka ka ci gaba da rokon Allah ya shirye ta ya shiryi iyalinka baki daya, domin yanzu wasu matan kwadayi na rufe masu idannuwan su har su ringa aikata abubuwa tamkar zararu

Malan Ahmad ya yi murmushi ya ce" liman da na nuna bacin raina, *MARIAMA* ni ta kali kwayar idannuwana a gaban yayana, da yayarta, da yaron da take tunanin watarana ya zama sirikina ta furtan kalamai kamar haka" MALAN wai me ke damunka haka? Kana yiwa iyalinka bakin ciki kiri kiri, zamu canza kalar miyar mu kana jin haushi sai dai mu dawama da tsanwar miya da dadawa da gari ko? To Malan Ahmad baka isa ba, ba abinda ka isa ka yi da wannan lamari kuma, Rauda kamar ta auri Salif ta gama dan ba zan yarda da raina da lafiyata ka nakasa min yarinya kamar yanda ka nakasa ni ba!

Malan in takaita maka a gaban bayin Allahn nan ta rufe ido ta yin fata fata ta gama ikirarin ba abinda na isa na yi a rayuwar Rauda, Liman Yar cikina

Ya karasa yana sada kansa kasa

Liman ya kuma jujuya kansa yana dan waige kar a je wasu na ji, inda Sudais kansa ke sade yana jan carbinsa aman gaba daya abinda Wannan bawan Allahn dake kokarin tarwatsa masa kwakwaluwa na dukan cikin kunnansa domin Allah ya yi masa ji a kasan zuciyarsa har ya tsayar da adu.ar jan carbin kawai yake, kokowa yake da kunnensa aman fafur ya ki bashi damar sarafa shi, ya biyewa umarnin zuciyarsa cewa sai fa ya ji karshen maganar domin magana ce da ta shafi *MATA* a kasan zuciyarsa yake maimaita" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Mata bata samu tarbiya mai kyau ba? Me ke shirin faruwa da rayuwana ne? Shin soyaya zata rufe min ido na auri mata na kawo ta gidana koda kuwa babu rabon haihuwa tsakanina da ita ai tana iya bata min zuri.a,

Kara sada kansa yayi ya ci gaba da sauraron magangannun malan Ahmad domin kowa ma jinsa yake dan kuwa bai sirinta muryarsa sosai ba

Liman ya ce" subannalah, subannalah, abu bai yi dadi ba, Allah ya shirya, Allah ya shiryar mana zuri.ar mu baki daya

Malan Ahmad mahaifin su Rausa ya sauke ajiyar zuciya ya ce" liman ai aikin gama ya gama, domin a yau a yanzu a masalacin nan bana so na fita ba tare da ka daurawa yayana aure ba! A yau zan nunawa Mariam da ahalinta na isa sa yayana, Liman du mai son RAUDA ko AISHA ya fito na karbi sadakinsu da salatin annabi sallalahu alihi wa salam a daura aurensu a yau yau din nan


Dum dum dum gabansa ya fadi, da mugun sauri ya dago da kansa daidai lokacin Ladan ya dauki lasifika ya kwala kiran salar isha.i



To readers, cmment fa ko na tafka tsiyar😊😊😊😊😊😊🤣🤣🤣🤣🤣


Shin yaya Sudais zai yo da wannan cakwakiya? Yau satin matarsa biyu da kwana hudu da rasuwa, a al.adarmu ta hausa shin zai amince da wani tsari daban,? Zai ci gaba kuwa da sonta bayan a jin da yayi RAUDARMA bata da tarbiya! Yaya za.a kare da wannan cakwakiya *AISHA KO RAUDA WACECE MAI RABON?*




*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




2⃣3⃣

*YA ALLAH KA HANE MU SHIGA HAKKIN BAYINKA KA TSARE MU FADAWA HALAKA KA YAFE MANA KURAKURAN MU KA SAKA MU CIKIN BAYINKA MASU YARDARKA KA TSARE MU JIN KUNYAR LAHIRA DA TA DUNIYA AMEN AMEN*





Dady bai dauki wani dogon lokaci ba abinka da dare ba wani go slow sosai domin du jama.a sun yi gida tsiraku ne ke yawonsu a cikin gari

Gaisawa suka yi da jama.ar wajen cikin mutunci wanda sai a nan Sudais ya gabatar masu da kansa da kuma mahaifin sa

A hade ya baiwa dady labarin ko su su waye domin marigayi uban marayu sanane a garin dan ya yi sunna sannan har ya koma ga mahalicinsa ba.a yi masa muguwar shaida ba

Sudais ya mike ya cewa mahaifinsa yana son maganar sirri

Gefe suka koma, Sudais ya sada kansa kasa, muryarsa ya raunana ya ce" Dady, kana tune da alkawarin da ka taba yi min a ranar da kuka sanar da ni kun zaba min matan aure biyu aman hakan ba zai hana ku tauye min hakina ba idan na samu mace ko yar gidan waye zaka shige min gaba ka aura min?

Dady ya ce" kwarai kuwa Son, ba zan manta alkawarin da na daukarwa kaina ba

Sudais ya sauke nanauyar ajiyar zuciya ya kali dady ya ce" dady sai dai ina cike da tsoro, na hadu da yarinyar nan a wajen danja, tun daga ranar dady nake adu.a idan alkhairina ce Allah ya tabatar min idan kuwa ba rabona bace ba alkhairina bace Allah ya nisanta ni da ita
Dady a kulun sai ya zamto kusancina da ita kara karuwa yake aman ita bata san bama abinda nake ciki ( ya boye mata abinda Aisha ke ciki) ya ci gaba da fadin" a yauma zuwa na yi dan dubata ba lafiya zazabi sai kawai na riski wannan lamari...........ya kwashe du yanda aka yi ya fadawa dadinsa domin Sudais bashi da tamkar dady sannan ya tabata abinda zai hango masa shi bai isa ya hango shi ba ko dan ya kasance shi daya cilo ne dansa namiji suna sa kyakyawan fahimta a tsakanninsu suna fadawa juna sirikansu suna rufawa junnan su asiri tamkar wasu aminan juna

Dady kansa ya jinjina abin a cikin ransa, sai dai abubuwa da dama sun daure shi sun hana shi yin gardama wa abin du da irin tarin abubuwan da basu yi masa ba a tatare da yarinyar duba da halayen da mahaifiyarta ke da, da rashin sannin takamaiman itama halayen nata irin hakan ne ko kuwa ? Ga mutuwar Khairath sati uku da kwana hudu ko adu.ar arba.in ba.a yi ba da dai sauran su, aman kuma idan ya yi duba da adinnin musulunci bai hana irin hakan ba, sannan ya tabata sudais ba zai yi masa karya ba, ga girman alkawarin da ya daukarwa dan nasa
Dan haka kunayensu zasu toshe a daura auren sai dai zai nemi alfarma idan har iyayen sun amince tarewar a basu koda sati uku ne a yi adu.ar kwana arba.in din Khairath

Karin shaidu aka samu , cikin ikon Allah aka daura aure, a baban masalacin juma.a, a daren alhamis karfe goma saura bisa mafi darajar sadaki aka gama da karatu aka rufe aka fito

Tunda ya fito suka yo salama da dady kan sai sun hadu a gida ya nufi asibitin Samir na biye da shi a baya yana kallon sa mamakinsa bai gama gushewa a fuskarsa ba, yana mamakin Sudais a tunaninsa zai janye ne zai fasa maganar sonta idan ka yi la.akari da halayen sa na kyamatan yan mata masu baudadan halaya aman ya aure ta ba tare da dar ba

Saurin da yake ne ya sa shima ya daga kafarsa ya fada masa sunnan room din wanda sun kusa karasawa su Salif sun fito da aunty da yarta sarah ta rike hannunsa gabjejiya da ita haka kawai dan ta ga mai dan hannu da shuni har suna ta yi masa da mijin mu😊

Saurin sakatawa ya yi gannin ogansa sannan ya janye hannunsa a rikon da ta yi masa ya yi gagawar zuwa yana dan risinawa yana gaisar da Sudais

Kallonsa kawai yake, sai yanzu ma ya fito daga wajen su kennan? Aman ita fa wannan da yake rike da hannunta kanwarsa ce?

Bai iya amsa shi ba ya yi office din docter inda Salif ya bi Samir da tambayoyin wani ne ba lafiya ba

Samir ya yi masa kalon tausayi kake bani ya girgiza masa kai ya juya shima ya tsaya dan jiran fitowar Sudais

Sudais ya dauki lokaci a wajen docter kafin yake fitowa
Bai ko kali inda dakinta yake ba ya umarci Samir da su tafi

Samir kam bai iya yi masa tambayar komai ba shima ya ja bakinsa ya yi shiru dan baya son abinda zai jaza masa matsala da daren nan


Da safe Docter ya shigo masu da salama ya fada masu cewa Elhaj ya umarta da a ringa zuwa gida ana duba ta

Mamaki ne ya cika Mama dan kuwa ita a tunaninta du Salif ne ya yi wannan kokarin , ta jinjina kanta cike da murna suka shiga harhada kayan su tana fatan Salif ya zo ta yi masa godiya

Rauda kam abin ya girmami tunaninta , ita tambayar kanta ma take a ina suka fara soyaya da wannan mutumin da har ya baiwa kansa damar yi mata wanbab hidindimun? Tana fatan ta koma bakin aikinta ta biya shi dukan kudaden da ya kashe mata dan kuwa ba zata amince kudin saurayi ba dan gudun gobe ya fito mata ta wata hanyar

Mama ta kale ta ta ce" haba Lallana (ta dawo kiranta da lalla tunda ta ga kudi🤦‍♀) shin mai ke damun ki ko bakya so ne mu tafi gida asibitin bai ishe ki ba? Ai ko dan albashin ku ma koma ku je ku karbo ko?

Rauda ta juyar da kanta tana saka hijabinta Aisha ta yatsina fuska bata ce komai ba

Direba ne a kofa a tsaye suna fitowa ya gaishe su ya ce" Elhaji ne ya turo ni na mayar da ku gida

Da mamaki Aisha ke kallon sa, Elhaj kuma? Dama salif haka yake da yayan banki? Aa wannan lamari da dadi yake
Ai kuwa ita ce gaba gaba ta hakimce su Rauda a baya direban ya ja su ba tare da sun zurfafa tunani ba ya kai su har kofar gidan su ba tare da sun yi masa kwatance ba kuma basu yi mamaki ba domin dai salif ba sannin gidansu yayi ba

Malan Ahmad ne zaune saman darduma kasan shukar maina dake cikin gidan da carbi a hannunsa yana ja

Suna shigowa su suka yi daki dan kai kayan su ita kuwa ta nufi inda yake zaune direct ta durkusa har kasa kanta a kas ta shiga gaishe shi

Ido ya tsura mata, tsoro yake har cikin ransa kar a je itama ta koma irin su, hakan ya sa ya kasa buda baki ya amsa mata gaisuwarta

Hankalinta ne ya tashi ta zauna dangalgal a kan farar kasar dake tsakar gidan muryarta na rawa ta ce" abana, ba abinda kake tunani kaina bane, aba ni kaina sun fi karfina ban san lokacin da aka mayar da ni wajen nan ba, hasalima ko asibitin gwanatin bani da damar ki dole na yi biyaya ni da bani da karfin komai,
Ka yafe min wly ni bana wata soyaya da mutumin nan, dan wajen aikin mu hasalima wata magana bata taba hada ni da shi ba, Aba ka yafe min kar ka yi fushi da ni

Ajiyar zuciyar da bai shirya ba ya sauke, sai kuma wani mugun tausayinta ya darsun masa a zuciyar sa, harma ya fara jin kunyar abinda yake son fada mata, ta inda zai bi ya fada mata

Mariama ce ta fito ta nufo inda suke tana fadin" malan lafiya daga dawowar mu yarinya da danyen jiki ka saka ta kuka? Lallana lafiya?

Dago da kansa ya yi yana kalon ta, murmushin takaici ya sakar mata ya sauke ajiyar zuciya ya kali Rauda ya ce" Raudana, a jiya na yi baban laifi, na yanke hukunci cikin fushi duda abin alkhairi ne na aikata aman ina cike da zulumin yanda zaki dauke shi

Gabanta ne ta ji yana dukan tara tara, bata ce komai ba domin kafafuwanta har sun fara rawa dan kuwa a jiya tana tine a harzuke ransa a mugun bace ya fita a asibiti bayan ya yi furucin yau zai nuna ya isa da yayansa

Idannuwansa ya rufe ya kuma budewa ba tare da ya kali Mariama ba ya ce" Rauda , *a jiya na daura maki aure*

Ba rauda da Mariama ba , Aisha kanta sai da ta hantsula daga kan kujeea tayani tsegumi ta mike da mugun gudu ta karaso wajen iyayen nata da Rauda da ta sada kanta kasa ba wanda ya fahimci halin da take ciki

Mariama cikin tashin hankali ta ce" aure! Aure fa kace malan? Kana cikin hayacinka kuwa? Ka ko san abinda ka fada? Wa ka aurawa ya ta? Walahi talahi baka isa ba malan! Walahi baka isa ba a me ka dauke ni? Na dauki cikin yar na raini abina na sha wahalar kayana ka tashi ka nuna min iyakata dan bakar zuciya irin taka? Dan aunty ta yi maganar nan ne zaka wani biye mata? A yanzu da muke murnar Allah ya bilo mana hanyar da zamu ci mai dadi ne ka yi min wannan danyen aikin?

Dago da kansa ya yi ya ce" ki sasauta muryarki Mariama ki daina yi min ihu a kaina

Aisha ta yi saurin zubewa a kasa ta ce" aba, aman ai banda ni ka daurawa airen ko aba?

Da kallon tausayin halayenta ya bi ta, ya so ace a jiya ta samu wanda ya taya ta koda mai hucewa ne da ya daura mata shi , itama cikin kakausar murya ya ce da ita" *Baki samu mai so ba, aman da zarar na samu kema zan aura maki!*

Malan walahi baka isa ba, haka kake so yayan nawa suma ka kaisu gidan da har sai fatar su ta dawo kalar tawa dan wahala? Mai na kashe maka da har ya jaza min wannan wulalancin malan? Me na yo maka a duniya da zafi haka? Wly sai ya saketa ko dan gidan uban wanene!

Su duka basu ga lokacin da ya mike ba, har ya kawo wajen Mariama da take tijara tamkar zata daku da shi ya aikata mata abinda bai taba yi mata ba, abinda bata taba kawowa ranta ba zai iya aikata mata! Abinda ya girgiza yayan su su kansu sukai mutuwar tsaye domin Rauda kanta sai da ta mike tsaye jin saukar marin da Malan Ya shararawa Mariama

Yatsarsa manuniya ya nuno mata , ya kada kai ya fice bayan ya dungurawa Rauda akwati a kusanta ya fice kwata kwata a gidan

A hankali Mariama ta sulale hannunta dafe da kuncinta ta hade bayanta da garu wanda a daidai lokacin da gudu suka rukunkumeta kowace ta saki kuka, Aisha na borin fadin kar ta bari itama ya aura mata Wani bayan ga wanda take so kamar ta mutu
Rauda kuwa kukan abinda ya salamo rayuwarta da irin yanda fitintinu ke bilowa tsakannin iyayenta da tausayin mamanta dan ta san auren su da abanta ba na duka bane auren soyaya ne aure ne na hakuri aman tunda yau har ya yi duka tabas ya daki gawa ne dan mai rai ya ji tsoro, tsoronsa da tsoron hukuncinsa suka cika mata zuciya da tambayar shin wanene mahaifinta ya aura mata?

Mariama kuwa ta kasa lalashin yayanta, tashin hankalin da take ciki ya girmami tunaninta harma ta nemi hawayenta ta ji su a kafe, zuciyarta ce ke mugun buga mata tana yi mata sama da kasa lumfashinta yana fita da gagawa, muryarta na rawa ta ce" *innalilahi wa ina ilaihi raj.une! Na kai malan wajen da ya taba lafiyar jikina, saurin dago yayan nata ta yi daga jikinta murya a matukar raunane ta ce" AISHA RAUDA MALAN DUKANA NE YA YI?*


..........................

*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation






Please Login or Register in order to submit comment