Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




3⃣3⃣

Kabewa a dafata ta dafe a murjeta sosai ta yi kitib a hadata da madara peak da karankafi a saka a firij ya yi sanyi a sha da safe kafin lokacin zuwa turaka , kana iya sha ko ba sanyi zabinka ne🚪🚪🚪🚪🚪🥰🥰🥰🥰








Gabanta ne ta ji ya mugun faduwa, wanda har ta saki dayan hannun zanin da sauri ta raruma ta daura haka kuma jikinta ya dauki rawa domin ba hijab a jikinta danma Allah ya taimaketa dinkin Aba da ya kai gaba daya manyan dinkuna ne akai mata du idan ta saka zubul take yawo a ciki aman wuyanta da yake a bude sai tana jin tamkar ana gannin sauran sashin jikinta

Kalo irin na kurulah ne ya kafeta da shi wanda shi kansa bai san ya shagalta da kalonta haka ba, so yake sai ya karanto abinda ke saka shi afkawa a soyayarta har haka , yanzu ma wannan kayan na jikinta tamkar ta aro sun mugun yi mata yawa baka iya tantance ainahin tsarin jikinta

Ya kai sau uku tana dan dago idannuwanta tana satar kallon sa sai ta ga ya tsura mata ido tamkar yana hararanta

Kanta ta sada a karo na ba hudu tana dan murza yatsunta

Ajiyar zuciya ya sauke, a kasan zuciyarsa yake ayana" inama wannan sabanin bai shiga tsakanin mu ba, inama kin fahimci irin macewar da na yi a kanki kin fito kin furtan kalmar so kin amshi tarairayana, Rauda sonki kawai nake

Takawa yayi har zuwa daidai inda take ya ja ya tsaya, ya hade girrar sama da ta kasa ya ce" fatan kin shigo gidan aure dan bautar aurenki ba dan hutu ba

Bata iya cewa komai ba sai zuciyarta dake ingizata kan ta nemi sakinta tun kafin tafiya ta yi tafiya,

Sudais ya ci gaba" ina so idan ina magana a ringa bani amsa

Kanta ta dan dago sai ta ga kusancin nasu yayi yawa dan haka ta dan ja da baya sannan bata bashi amsar da yake jira ba

Kankance idannuwansa ya yi ya ce" ko baki ji abinda na fada ba?

Kanta ta daga irin ta amsa shi, itafa a kasan zuciyarta bata ma yarda cewar shi din ne mijinta ba, me hakan ke nufi? Abanna ko bai san wanda ya aura min ba

Hum ya ce , ya taka ya karasa wajen armoire
Bouton ya mika hanu ya dana gaba daya suka bude, tsai ya yi yana bi da kallo kamar yanda ya umarta ne kuwa? Wato tufafin da ya umarta a zuba masu tun daga abaya , lesh, shada, atampa, kananun kaya, su bra komai an zuba yanda yake so masha Allah, ya juyo ya kuma kallonta, murya a dake ya ce" idan dai kina cikin gidana ya zame maki tilas ki yi anfani da suturar da na tanadar maki da kuma abincin gidana,
Ya zama tilas ya kasance kina fita falo koda baci ne ki yi a can domin bana son ana yawan kunshe kunshe a daki
Da safe karfe bakwai du abinda kike ya kasance idan ranar da .... ya yi shiru yana kallonta domin sai ya ji nauyi ce mata ranar da take da shi, haka gabzaza a gabanta a tsaye har zai ce mata wani ranar da take da shi? Ta ce me kennan? Wannan karamar yarinyar ai hankalinta ba zai dauka ba danma may be a islamiya an karantar da ita ko a makaranta an dan fada mata wani abin...., yatsina fuska ya kuma yi gannin ta dan dago jin yayi shiru, ya kawar da fuskarsa ya ci gaba" idan har ya kasance ranar aikinki ne, shayi da towel da ruwa mai dumi kin tanade su kafin lokacin, zaki kawo min dakin motsa jikina na gama ki tayani shiryawa

Da sauri ta kuma dago kanta ta sauke idannuwanta a kansa, mamakinsa ya cikata , na taya shi shiryawa? Me yake tunani ne da ni?

Kar ki yi wani tunani ko ki fasara ni a wata fuskar, ba dan wani abin ya sa na sako ki a layin matana ba sai dan na san hakokin Aure!, ba dan ina son ki ba, lalalalallalalalla ,....... Sudais ya fada yana dago mata dan yatsansa na kusan babar yatsarsa alamun maganarsa hakan take, sannan haushin kansa du ya tornike shi, ya haka sai kace wani redio ya sakata gaba sai zuba yake tamkar wani sauna ya kasa yin shiru du dan ta yi magana ya ji muryarta aman dan isa sai dai ta dago ta wani kale shi , kai da abinda take ayanawa a cikin zuciyarta sam ban yarda da wannan shirun da wannan kallon rainin da take yi min ba, waima ni ina tawa isar? Ni Sudais da idan magana ne sai ina iya yin minti ashirin kafin na tofa maka a yau na zazaga mata Magangannun da ina iya yinsu a tsayin wuni ba tare da na kara wani abin ba yarinyar nan ta kasa furtan wani abin, ta kasa yi min magana da muryarta na ji muryarta, rabona da muryarta tun dazu da Samir ya kawota ta waya idan ta dan yi masa magana, ya salam ni kuwa bana so na cika yi mata magangannun da zata raina ni """ Sudais ke ta fafatawa da zuciyarsa

Gannin ba zata tanka ba ya saka shi juyawa da niyar tafiya

A daidai wannan lokacin kuwa Rauda ta gama yanke shawararta, to ai ta fadi gidan sauki, shi baya sonta itama bata son sa, sai ya sawake mata kawai ta kara gaba , rigingimun dake tare da shi sun fi karfinta

Murya kasa kasa cikin zazakar muryarta da yannayin sanyi kamar yanda ta saba ta ce" sire

Ja yayi ya tsaya, ya saki ajiyar zuciyar da bai shirya ba, haka kuma ya tsinci iska na taba lebensa kennan harda murmushi ya saki , ya dan yi jim ya saita kansa kafin ya juyo ya dawo kusa da ita

A hankali ta matsa kusa da bed din dakin ta ja ta tsaya , kanta ta sada kasa ta rike gefen rigarta dan samun kwarin guiwa,
Tamkar ba zatai magana ba ta ce" ka yafe min, ka yafe min..., na aikata maka kuskuren da na yi nadama daga baya,
Auntyna ta kasance tana kaunarka tun ba yau ba , sai haka ta faru... Sire tunda ya kasance ba wani abin da zai sa mu jure tashin hankalin da ya hada mu, *BA SOYAYA* , aure yinsa halal ne haka ma barinsa Abannnnn

Shut up! Shu...u...shuppppppppppp! Sudais ya daka mata tsawar da hanjin cikinta ya hautsine
Taku ya yi ya tsaya a daidai inda take,
Bata san isowarsa ba haka kuma bata ankara ba sai ji ta yi ya saka hannunsa daidai wuyanta ya turata da karfin da ya bata mamaki wai haka ma bai yi mata da dukan karfinsa ba

Kafarsa ya saka kadan ta bayan kafarta ya kaita saman bed din ya kasance ta fada rairan kafafuwanta a kasa daga daidai tsatsonta har kanta saman bed
Kafarsa ya dago da takalmin kafarsa da komai ya dora gefen cinyarta wato ya raba kafafuwansa ya saka nata tsakiya,
Nan da nan idannuwansa sun canza kala, kamanunsa sun zame mata abin tsoro,

Kansa ya dafe wanda ya shiga sara masa , ta rigarsa kuwa kana iya gannin yanda kirjinsa ke dokawa zuciyarsa ta kara bugu

Dan kwalin kanta ya fadi tun wajen faduwar da ta yi ta rinrintse ido gaba daya jiran duka take jikinta sai mugun rawa yake,

Muryarsa a matukar dake tamkar ta zaki ya nunota da yatsa daya ya ce" *KE CE TA FARKO A WANNAN SASHIN, KUMA IN SHA ALLAHU KE CE TA KARSHE! KAMAR YANDA NA SAN ZUFATA TAWA CE HAKA NA SAN KE KIN SHIGO RAYUWANA, NA CIRE KADARAR UBANGIJI IKON ALLAH YAWA NE DA SHI KO MUTUWA, AMAN KI SANI BANA AUREN MACE NA SAKETA KE KODA KADARA TA SHIGO NA SAKE KI ZAKI ZAUNA NE HAKA DOMIN SIRINA MAWA NE!*

hannayensa ya dora ya sakata a tsakiya, a hankali ta bi hannayen da kallo wanda tsoro ya sa ta shiga rawar jiki, girman hannayensa sun tsoratar da ita, sannan magangannunsa sun sakata a duhu, wai ma me magangannunsa ke nufi? Ita da bata kai karshen maganarta ba ya hazurka haka ina da ta kai karshen maganarta, me ke damun Uban gidanta ne, ya Allah wannan mutumin haka yake gabjeje da shi, sannan kanshin turaransa da ya doro hannunsa sai take ji ya cika mata hanci tamkar ita ta fesa

Tar ta sauke kwayar idannuwanta cikin nasa dan gannin mai zai yi mata da ya kawo hannayensa haka?

Gannin sosai fuskarsa ta kusanto tata ya saka ta rintse ido bugun zuciyarta ya ninku, sai da ya kawo fuskarsa daf da tata, ya zuki numfashinta ya sakar mata nasa itama ta zuka domin ba yanda zata yi ta kawar da fuskarta aman ta rufe idannuwanta ruf dan tsoro,
A hankali ya kai bakinsa daidai kunanta ya sirinta muryarsa ya ce" *HUKUNCIN IRIN WANNAN FURUCIN MAI TSAURI NE MATA,*
irin yanda ya yi maganar, irin yanda ya sakar mata numfashi a kunenta, yanda ya yi salon maganar nasa sai da ta ji wani irin yamyamyam gaba daya jikinta ya dauka, kan ta ankara ya fice ya barta nan konce tamkar wace ta yi dambe sai shesheka take tana sauke ajiyar zuciya ta rasa me zata yi ta ina zata fara






🤔🤔🤔




*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




3⃣4⃣










A hankali ta mike daga koncen tana bin jikinta da kallo, kanshin turaransa ba wani taba jikinta ya yi iya wuyanta ne kawai ya taba aman jinsa take sosai a jikinta sannan tana jin dadin kanshin a ranta
A hankali ta mike ta gyara zanin bed din ta dauko alkur.aninta ta koma saman salaya ta gabatar da salah ta zauna tana karatu har dare ya raba sannan ta konta a nan din dai ta yi baci

Duk rintsi sai na kori yarinyar nan daga gidan nan mama, dalilinta yake min ihu a ka, mama kashedi ya yi min me hakan ke nufi? Shin sonta yake ko me?

Haba Humaira, wai ke dai haka kulun damuwarki kennan kishiya kishiya kishiya? Ke ba zaki yi kokari mijin naki ya kasance kin zama sarauniyar zuciyarsa ba? Maman Humaira ta fada

Humaira ta ce" mama, na rabaki da mutun mai kushe mutun, Elhaj fa ya kasance shi a komai sai ya nunan bai dace ba, ki duba fa ki ganni wai na tsayar da shafa mai, idan na tsayar fatana ba sai ta yi tamkar na kone ba wly sai ta dawo abin kyankyami ni kaina na sani aman wai shi Elhaj ya dage kai da fata sai na tsayar da shafa mai, kin ga yanzu yarinyar da ya auro din? Talaka tilis, sannan wly idan aka jeramu farina ya zarce nata nesa ba kusa ba sai ma ace yar aikina ce

Mama ta ce cikin gagawar magana irin ranta ya baci" fari dai fari dai fari dai! Ke yaushe zaki yi hankali ki gane inda na nefa? Humaira da alama sai kin saka na fito fili na yi maki kwadokwado na marar kunya ko? To bara ki ji:

Ku dai matan zamani yan mata da matan aure da yawanku burinku kyau, ki yi fari far ki yi dinki ki saka ki ringa kwarkwasa shikennan kyau ya kare kuma a tunaninki takamarki kyanki ya isa ya kaiki du inda kike so, ya isa ya ja maki soyayar miji ko waye, ya isa ya ja maki kulawar miji da sauransu,
Ke kin san yau da gobe kuwa? Kin san kwana tare tashi tare kuwa? Uhum ke kin ga kanenki na yaba kaynki kulun? Ko a cikin gidanku kin ga ana raga maki dan kyanki? Ke ko a ma.aikata ya kasance an saba an san juna kulun kin ga ana daga maki kafa dan kyanki? Kina zaune ke mai kyau, mai aji, kina takama wata yar shila mumuna zatai maki shigar wuri ta raba ki da abinda kike takamar
Ke idan baki kasance mai biyaya, hakuri, kawar da kai , tsafta, iya girki, iya zaman duniya da dukan wanda Allah ya hada ki da shi ta sanadiyar mijin nan naki...uwa uba sannin asalin waye shi mijin naki iya tafiyar da shi kofa a shinfidarku ne tofa a kulun kina cikin damuwa! Humaira mazan zamaninku da namu ba daya bane, ko a zamanin mu idan mace ta kasance baka gamsu da ita ba kana kara aure bale zamanin ku da matan ke harin mazan tun karfin su suna warto su suna nuna masu abinda suka kasa samu a wajen matar su ko ke ce mace ba dole ki kali wannan dadin ba? Ke Humaira idan fa shi mijin naki baya ra.ayin farar macen, bata bashi sha.awa kwatakwata baya jinta a cikin zuciyarsa sai ya kasance ke a hasken da Allah ya yi maki baki gode ba sai da kika kara kuma karawarma ta hauka Humaira har karni fa kike? Shi sakarai ne? Kina sairaron redio kina kallon tv kuwa? Kin ga yanda mijinki yake da daraja ya yi sunna a duniya kuwa? A zee aflan na ga talar shagonsa na chocolate, Humaira mijinki baban mutun ne wanda ya nema Allah ya yarje masa ya samu, mata ba kalar wace baya gani, ke har ya fito ya sanar maki ga abinda yake so aman ke sai ki yi masa kunnan uwar shegu? Ke ba zaki bi umarninsa ba sai kin jangwalowa kanki fitina ki dawo kina haikar baki tamkar wata mahaukaciya? Kina fa kallo irin yanda ake zaman auren a gidaje casa.in cikin dari, mijin ya auro macen ya sakata a gidan du dare ya dareta ya daneta ya biya bukatunsa da safe ya mike ya barta ba ci ba sha ga tarin yaya yau ba makarantar boko ba ta islamiya da kyar ta harhada ta samu jari ta dorawa yayan tallah idan sun saido sun kawo ta sayi kwaki ta kwada masu ya dawo ya cinye ya sha ruwa ya mike ya shirga baci dankareren kato idan ta raya masa ko abi kadan ya shiga tsakaninsu ya jibgeta a gaban yayanta ita kuwa ta yi ta kurma masa zagi ko ta yi ta hada shi da Allah ya isa yana kara lalacewa haka haka y'ay'an ma su taso sai idan Allah yataimake su wasu su dan kama sana.a wasun kuwa sai adu.a kawai haka suke fama kai da fata dan su samu idan dai ya fita ya dawo ya tarar da su sannan kar ya kauracewa shinfidar su, aman ke Allah ya yi maki gata ya wanke ya baki maimakun ki zagine ki dage ya kasance ke din wata ce a fadar zuciyarsa aa kina nan kina cafka bleating fata ta saka maki tamkar tsohuwa saman ido ya yakune maki gurbin ido yayi maki jajajir ya kode tamkar tsohuwar da ta kai shekara tamanin marar gata, ke daman abu ba abu ba kina fama da cikon nono da na mazaunai hannaye sun yi maki tauri tsabar masifar shafa mai ido du sun mutun maki jijiyoyin jiki sun firfito maki tamkar wata fatalwa gashin kai du atach ya cinye shi ya ja baya ya zama dan tsugul da shi a haka kike so ya zo yana sinsinarki? Ke hakuri ma ne da shi, yana da hakuri sosai. Humaira ke fa ba yarinya bace, shekara talatin da daya a duniya ya dace ace yanzu kin san abinda kike yi , kin zo da farkon auren ku kin garkama alura har ta shekara kina zuwa anai maki wai dan ko baya son haihuwa yanzu tun daga lokacin gashi sai nemanta muke kamar mu mutu babu maimakun ki yi fama da abinda ke gabanki aa ke kina tambayana yanda zaki yi ki kori matar da ya auro? Ki yi ta kanki ki haifa masa magaji mana sai ki taka da karfinki Humaira, ni dai fada maki nake a kulun idan kika kashe aurenki ba ke kafai ba mu kanmu kin yi mana bakin cikin rayuwar gata!


Du wannan jawabin da mahaifiyar Humaira ke yi mata gajiya ta yi da sauraronta ta ajiye wayar ta sakata a handsfree ta dora wayar saman abin bed dinta kawai ta afka tunanin inda zata bi ta adabi rayuwar Rauda, bata da burin da ya zarce ta fice mata a gida ko ta sakata a uku


Bayan sati guda

A cikin wannan satin da aka yi ba wani canji da Rauda ta yi, ya kasance ma tana lure da wanda ya tunkaro dakinta sai ta konta ta shiga baci ko ta tayar da sallah ko kuwa ta yi bayi, harta Hafsat ta kasa sake mata ita kawai gani take ai sam sun fi karfinta ba zatai wata mu.amala da dayansu ba, du ta bi ta takura kanta ko abinci ya kasance ba wani sosai take ci ba domin hafsat ke kawo mata dakinta ta ajiye

Abin duniya ya ishi sudais, a da yafi ganninta fiye da yanzu da take kusa da shi, yana cikin matsi da bukatar abincin ruhinsa,

Yau karshen kwannan Humaira a dakinsa wanda ta caza shi ta kasa biya masa bukatunsa sai yake jinsa tamkar yayi tsere an fesa masa ruwa a iya fuskarsa kawai, sai jan ido yake yana muzurai gashi yau alhamis ne ranar kasuwa

Tunda ya fito daga masalaci ya zo saka kayan training dinsa

Iya kayan ya saka kamar yanda ya saba sai dai ina a yau fa sai ya yi dabarun maza

Komawa ya yi ya saka wasu kananuwan kayan daga ciki ya dauko kayan training din ya saka iya wandon kawai mai ruwan Ash kala mai rubutun Adidas a jikinsa da bakaken harufa ya dauki rigar ya rataya a jikinsa ba tare da ya saka karama ko daya ba daga shi sai wandon dake jikinsa ya fito ya nufi wajen training

Wayar da bata san da ita a dakin ba ta hau ruri dan haka ta zabura tana neman inda take, fitowarta kennan a wanka ta saka dogon wando jins ta saka riga fara kar mai kananuwan hannu domin ta san indai za.a shigo zata sani ne ta ajiye hijab a kusa da ita kiran ya shigo
Rauda akoy son saka kananuwan kaya rashi ya sa take anfani da na gonjonta idan ta samu ta daya a dakinsu sai ta saka abinta ta sha iska ta yi karatunta ta sha bacinta da abinda, a yanzu da ya lamunce mata sakawar sai take taba kananun kayan har zumudi take ta saka ta yi ta murmushi domin tana son su halin yau da gobe ne sai a slow

Tana daga wayar ta ji miryar sa haka kawai idan ta ji gabanta ke faduwa ya ce" idan baki cika umarnin da na baki ba a yau kina cikin fushin Allah

Yana gama fada ya kashe yana ta kumbura ya ajiye rigarsa ya hau mashine ya danna ya shiga training

Ta jima tana tunzura baki, bata son haka, sam bata son kusancinta da kowa Har ta bar gidan

Kicin hudu ce a baban falon gidan kuma su biyun kowace da ky din nata dan haka ta dauki ky din ta dauko wani zumbulelen hijab baki sidik kakaura ta saka ya zo mata har daidai kafarta gashin kanta ya dan dago da hijab din yayi mata tamkar acuci maza
Silifas ta saka ta fito ta yi saurin shigewa kicin din

Baki ta hangame, ko.ina glas ne kana kallon kanka , zuwa ta yo ta taba sai ta ji ba glass bane bangon kicin din ne mai baka damar gannin kanka tamkar madubi

Sai tsarin kicin din shi kansa ya kusan zautar da ita,
Ajiyar zuciya ta sauke a fili ta furta" haka, aunty zata more 🙄


Kayan shayi ta harhada ta kuna gaz ta dora
Ta dauko flask na inox ta kara daurayewa ta dauko papier ta goge sosai ta ajiye ruwan shayin tatare suka gama da ruwan gumin ta jujuye ta dora saman tire na inox sabo fil mai shegen kyau ta dora da kofofi tamkar shan mutun da yawa, tana yi tana ayanna dole na guji fushin ubangiji kafin mu fahimci juna ka sake ni!

Kamar barauniya take sando kar matar gidan ta ganta ta wajen training din wanda daga sama aka rubuta shi din ma kofar dai iri daya ne

Dana open ta yi ta tura Da hannunta na hagu ta shiga
Tana shiga ta dan dakata tana raraba idon inda zata ganshi

Saman wani tapi ta ganshi yana ta abdomino yana dagawa yana komawa muscle dinsa sun firfito, hannayensa tamkar na dan dambe yana yi

A fili ta furta" tap! Tana zaro ido wanda bata san ta fito ba sai da ya dakata ya juyo da sauri gefen da take tsaye

Tun daga yan yatsutsanta dake fili ya bita da kallo har fuskarta, ta sada kanta ita bata karaso ba ita bata juya ba ita bata ajiye kayan ba

A ransa ya ayanna aa, yarinyar nan waima me take boyewa da take fama da hijabi tamkar wata mai takaba, daga ni sai ke a waje ki wani zumbulan hijabi to ko tubewa kikai kin isa ki girgizani ne?

A dan harzuke yayi tima ya mike tsaye ya karaso inda take
Ba tare da ya yi magana ba ya mika hannu ya karbi tiren ya ajiye nan gefe

A hankali ya saka hannayensa biyu ya kama hijabin nata tun daga kasa ya shiga kokarin cire mata

Idannuwanta ta kwalalo cike da tsoro ta yi saurin dafe hijabin ta shiga jujuya ido tamkar zata sume tana kokarin yi masa magiya tana jujuya kanta irin kar ya cire

Nuna mata ya yi bai san yarenta ba, gannin tana ta kicikicin ya matso sosai daf da ita ya dage hijabin har wajen wuyanta ya furta" *ke, ki daina tunanin shirme mana, duniya sai ta nuna nake shanta!*

Yana maganar ne yana idasa cire mata hijabin wanda dan karfin da ya saka ya sa ya biyo da ribom din da ta daure gashinta da shi, ta yo luuu zata fado masa ya ta yi saurin rike kanta ta ja da baya ta juya masa baya jikinta na rawa ta saki kuka mai karamin sauti ta tsugune jikinta na wani irin rawa

OGA ELHAJ SUDAIS dai bai gane komai cikin mutuwa ya yi ko sumewa ya yo a tsaye a wajen ba,
Wani irin zaro ido yayi ya sauke daradaran idannuwansa a kan halitar Rauda,
Rauda ta kasance irin matan na masu diri, tamkar yar gwari haka duwaiwanta suke manya da su , tsatsonta kuwa dan firit sannan mamarta su ba manyan nan ba su ba kannanuwa ba a tsakatsaki suke ,
Gaba daya halitar jikinta sun yi daidai da tsayinta sun yi mata das sai idan tana tafiya ne jikinta rawa rawa yake tamkar iska na kada saka

Yana nan tsaye tamkar bashi da jini ta rarumi hijabinta ta saka ta juya da gudu ta fice a wajen training din wanda fitarta kawai ya gani ya zabura ya.......





🤣🤣🤣🤣🤣🤣


*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼

Please Login or Register in order to submit comment