Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bayan daya, wanda a nan ta zube sumamiya............





💓


*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




6⃣4⃣

*Nd*
*ND*
*ND*

ALHAMDULILAH

*DUBUN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI GA YAN GUDAN MU, KAINUWA WRITERS ASSOCIATION, FATANA ALLAH YA KARA DANKON ZUMUNCI YA KARE MU YA SHIRYAR DA MU YA KARA HADA KAN MU YA KORE FITINA YA BAMU LAFIYA YA KARA MANA ARZIKI MAI ANFANI, TAKU CE KANWARKU CE YARKU , YAYARKU CE, KAWAR KU CE YAR MUTAN NIGER*




Rikicewa Aunty ta yi tana faman ihun a taimaketa, nan mai aikin gidan ta zo ta kamata domin qbin ya ja baya sosai ba masu aiki da yawa wannan din ma tana tare da su ne dan amana,
Kamata ta yi suka yi daki da ita inda Sarah ta samu waje ta zauna sai susa take hannunta cikin sket dinta kowa na kallon ta

Kamar wasa har yama ta yi ummiey bata farka ba har lokacin da dady ya dawo daga aiki

Yana zuwa ya tarar da tashin hankalin nan,
Nan ya shiga tambayar ba.asi aman da yake ta ga yanda ummiey ta yi sai tsoron fadawa dady ya kamata,

Kanta kawai ta sada tana sharar hawaye inda shi kuwa yace su kamata a je asibiti mana tunda bata farfado ba,
Tashin hankalin da ya tardo ummiey a ciki ne ya hana shi gane hallin da su Aunty ke ciki dan haka suka kamata suka nufi asibiti

Likitoci ma sun rufu a kanta su dai basu ga abinda ya sumar da ita ba, kuma sun yi mata yanda ya dace ace ta farfado aman shiru kake ji malan ya ci shirwa

Lokacin da docter yake fada masu aunty ta dora hannayenta a kai ta rushe ta kuka ta ce" shikenan na cuci kaina, ni ba ga gidan mijin ba, ni ba ga konciyar hankali ba, gashi zan rasa mahaifiyar tawa , wayo mariama ki yafe min abinda ba yi maki a rayuwa na raba ki da iyayen mu dan tsananin kishin irin yanda suka damu da rashin lafiarki gashi tana neman kome mani tun a gidan duniya ina haduwa da abubuwan da suka girmami tunanina, bokan kansa ya mutu wanda na dogara da shi na manta Allahna

Tunda ta ambaci mariama Dady ya zaro ido ya maimaita sunnan a lebensa, kafin ya gama fada ya yanke jiki shima ya fadi nan wajen sumame, wanda sai daga baya wata nurse ta kwala ihun wani ya fadi
Nan mutane sukai kansa shima ana kuma kallon aunty dake ta dumumuwa tana fadin" shima dadyn ya tafi ko? To ai shikennan ni zaku yiwa haka ko? Du ku mace ku barni da duniyar ko? Nima sai na mutu, nima mutuwar zan yi ehe
Aunty dai an fara sakin layi domin magangannunta na wanda baya cikin hayacinsa ne

Docten nan shi ya rufe daman likitan dady ne ya nemi wani baban malami shek ne ya fayace masa abubuwan dake faruwa

Shek din ya nemi da a zo da su dan haka doctern ya samu da kyar aunty ta sa hannun yarjewarta a fita da su ya shiga ya fita ya samu ambulence din asibitin aka saka su ciki aka fita da su sai gidan shek ibrahim

Ana zuwa ya tara almajirai aka shiga karatu, yi suke ba gajiyawa har zuwa wani lokaci ummiey ta fara wani irin abu kafin take amayo wani bakin abu can kuma sai ta shiga sauke ajiyar zuciya......
Dadynma kusan hakan yayi sai dai shi kan yayi aman sai da aka jima sosai har sai da ummiey ta kawo hankali tana kuka tana fadin ina Mariama? Mariamarta,

Gaba daya wajen ba wanda bai tsorata da duniya da abinda ke cikinta ba a lokacin da aunty ke tonawa kanta asiri ba tare da an matse bakinta ko an tilastata ba(sanu sanu bata hana zuwa, hakuri maganin komai) ,
Ummiey ta girgiza ta yi kuka har ta gode Allah, tana yiwa Aunty kallon tsoro ta ce" ina kika kai min ita bayan kin rabani da ita? Ko kasheta kika yi?

Cikin kuka aunty ta ce" ya zan kashe yar uwata ummiey?

Ummiey ta ce" kul da bakinki , kar ki kara wani abin na munafurci, mai halinki idan ba Allah ya kama shi ba, yayi masa muguwar kamu baya daina aikata mugun abu a doron kasa.......

Aunty ta sada kanta, ta ce" tana nan a anguwar yawa, tana tare da mijinta malan ahmad da yayanta biyu, karamar an yi mata aure tana auren Elhaj Sudais Uban masu gida

A tare ake furta ikon Allah, masha Allah,

Ummiey kam mikewa ta yi ta tayar da balin kawai su je su tafi su je


Hakan kuwa aka yi shek ya tayar da mota biyu dayar warda ake masa jigila ne sai wace yake hawa suka shiga Aunty na fadin wajen har suka karasa kofar gidan Malan na da sai dai kamar Aisha katon shago suka tarar da ma.aikata, aman wannan karron malan a kofama yake suna zaune suna kukula goron sadakin Humaira da ya karba a ranar an kawo sadakin naira dubu hamsin da huhun goro biyu suna kulawa ne dan jama.arsu

Tunda Aunty ta fito gabansa ya fadi, Allah yana ganni baya son huldar yan uwan biyu shi ya sa yaki nuna kansa karma ta ga inda suka koma

Sai dai me, idannuwansa suka sauka kansu, duda an manyanta ba zai mace iyayen matarsa

Hajiya ummiey, mace har mace mai isa da takama mai juya ragamar gidanta mai mulki ta tsofe sai dai duda haka da ciwo da tsufa daban take, wannan baiwa ce daga Indallah

Da sauri ya taso ya nufo su, wanda suma suke binsa da kallon mamaki da kuma kunyarsa

Iso kawai yake masu kan su shiga gida su je

Suma ta ciki ya ratsa da su har boyayiyar kofar gidan nasu,

Da mamaki du suke kallon tsarin gidan, motama biyu ce tankama tankama, gidan ya linka na aunty hakama ya fi na su ummiey nesa ba kusa ba, maganar tsaruwa kuwa ya ginu ginnin zamani duda sun ki a baza tils sai farar kasa solsolsol dake share tana mugun daukan ido da dadin takawa


A wannan rana an sha kukan farin ciki, mama ta rasa ina zata tsoma ranta, inda ana haka Aunty ta zame ta tsere, kunya ta hanata zama , zuciyarta ta kasa gaskata mata Mariama ce haka, lale duniya sai Allah , ka ga du ya barsu sun gama hayaniyarsu ya sakawa abin tsari , hakan ya kara karyar mata da zuciya ta sabi hanya a kafa dan komawa gidan ta san abin yi tana matukar jin kunyar iyayenta da wuya ta iya ci gaba da zama tare da su

Mariama ta yi kukan halin da Aunty ta shiga da yarta domin a gidan malan sai da ta fayace masu komai da komai, harma ta ji tana son taimaka mata (🙄),
Bayan kwana biyu
Yau suke dawowa daga tafiya, , a cikin jirgi a jikinsa kawai take hannunsa a saman mararta ta cikin hijabinta

A hankali ya rada mata" Alllah ya sa ki sama min yan hudu Mata, na kagu su fara motsi , na kagu ya kara girma na ganki kina tafiya irin na masu ciki, Mata idan kika haihu zan ta daukan babyna ina kallo, Allah ya nuna min

Bata ce amin a fili ba dan matsananciyar kunyar abin take, wai ira rauda daga aure sai ciki, gara ta dawo daga tafiyar da ba salama sannan ta shigan masu da ciki Ita dai ta godewa Allah, shi kuwa baya jin kunyar hakan yayi ta lagudata kennan yana santin cikin

Ki yi magana mana, na fasa kai ki gannin maman da mun saukan! Ya fada yana hade fuska irin da gaske yake

Ai da sauri ta ce" amen *MIJI*

yayi murmushi

Mota na tsayawa kofar gidan da yace wai su mama na ciki, nan ne gidansu ta bude marfin motar da gudu gudunta zata arce

Wata sufa yayi ya fito a mitar da Samir ya dauko su ya kwala ihun" MATA idan kika yarda kikai gudun nan da cikina sai kin haihu ke da gidan nan

An yi katari Aba ya fito da leda daga cikin gidan, komai a kan kunnansa,

Samir kansa da ya saki baki idannuwansa suka sauka a kan Aba ya kara buda bakinsa ya dora hannayensa a kai

Bai gama tantance komai ba Ya ji Sudais na fadin" idan baka tayar da motar nan mun bar wajen nan ba sai na shake ka Samir

Samir ya zabura ya waigo ya ce" oga ai Aba ne baka gaishe shi ba

Sudais ya ce" SAMIR😤

da sauri samir ya tayar da motar yana dariya a fili ya dan fitar da kansa yana gaishe da Aba a take kuma yana faman yin kwana da motar ABA kam dariya abin ya bashi sosai irin yanda Sudais ya sada kai ba zai iya kallon Aba ba bayan wannan baranbaramar da ya yi.................

Daga nan ya umarci Samir da su je gidan su Humaira

Sun kusa karasawa Samir ya kara kallo sudais akai katari suka hada ido wanda an yi haka ya fi a kirga,,

Sudais ya ce" ka kuma kallona Samir zan saukeka ne a motar nan

Samir ya zaro ido ya ce" oga motana ne fa

Sudais ya ce" to ka sake ka gani

Samir ya yi murmushi ya ce" daman murna nake, kuma ina fatan Allah ya raba lafiya

Sudais ya ringa sakin kasaitacen murmushi yana shafa sajensa a zuciyarsa yana amsawa da amin,

Can bayan sun tsaya cikin gidan su Humaira Sudais ya ce" ka gane ko, ai ita *MATA* yanda ta so kawai hakan ake yi, kai Allah ja da zamanin *Mai Ni*

Dariya kawai Samir ya bushe da ita gannin da gaske Sudais din ne ke haka, lale duniya

Da iyayenta ya gana inda ta labe tana kallonsa ta bayan labule

Sosai sukai godiya tare da fadin yanzu za.a rakata, Allah ya kara shiryar da ita

Cike da jin kunyarsu ya baro gidan,

Yana tafiya Mom da kanta ta saka ta yi wanka suka sakata gaba suka kara yi mata nasiha da fada da alkawarin idan haka ya jara dawo da ita ta san abinda zata tarar

Har kasa ta duka tana mai neman gafarar su kafin suke tafiya mama ta kaita har gidanta ta dawo

(Wannan kennan, )


Tunda ta shigo take faman sai sun yi hira da Aisha aman ta lura sai sada kai take , kunyarta take ji kamar ta mutu.....wai a haka ta je har gidan kanwarta gaban mijinta tana zuba hauka? Wohohi ai ita bata fatan abinda zai saka ta ganta gata ga sudais ba, ba zata iya kallonsa ba dan tsananin jin kunya

Rauda kuwa sai murnar har an fitar da anko din biki take ta kasa zama sai murna take ta je ta zaga shagon Abanta, sam bata san irin abinda mijinta ya yiwa iyayenta kennan ba, wannan lamari ya saka ta kara zage damtsen sai ranar da numfashinta ya bar gangar jikinta zata daina kokarin faranta masa........





Bayan wata tara


Shayar da Umar Faruk take tana kallon yanda Sudais ke sakawa NANA FATUMA pampos
Dariya ce ta kwace mata gannin a baibai ya saka mata,

Humaira ce ta yi salama ta shigo da fida a hannunta ta dafo shi, ta ce" oh my god malan karka jirde min kafar ya mana

Tana fada ne tana kokarin karbe Fatuma a hannunsa

Zama ya yi yana sauke ajiyar zuciya, watan yaran biyu domin a wata takwas ta haife su aman masha Allah jibga jibga da su, nononta mai kyau ne.........., kallon yanda Humaira ke sakawa yake, da dan cikinta na wata biyu abinka da marar jiki har ya fara dan shaida kansa

Rauda ce ta dan rike kujerar da take sama ta rintse idonta, cikinta ke ti mata ciwo kwana biyun nan bata san dalili bA


Humaira ce ta ce" cikin ne Rauda?

Rauda ta lumshe idannuwanta, bata son tace cikin ne ya hana tafiyar domin shiryawa ne suke zasu je fitar da ankon auren Samir da Hafsat

Sudais ya mike ya fita da wayarsa

Ba.a jima ba suka dawo da docter Amina, nan ta tsareta da tambayoyi dan gane ko wani abin ta ci?

Sai dai amsar bata gamsar da ita ba dan haka ta saka ta shiga ta bata fitsarinta

Tana dariya tace" kai docter gashi, ni dai dan aikinki ne da sai nace me kuma za.a yi da fitsarina

Murmushi ta yi itama ta bude abin awon ciki irin na pharmaci mai tsadar nan ta saka kan cikin fitsarin Raudar

Kamar da wasa ya nuna tire biyu

Rauda tace aa a sake ai yana bada ba hakaba

Sudais ne da kansa ke barewa yana sakawa cike da zumudi, Rauda kuwa hawaye har ya fara wanke fuskarta,
Result din dai daya ne, ciki ne da ita wanda daman wancen ma haka yayi ta sakata ciwon mara kafin yake zama da kyau, sai dai basu san ko na sati nawa ba

Kuka ne ta fashe da shi hannayenta saman kanta, Humaira kuwa sai juyi take tana fadin wayo.gidanmu zai cika da babys

Gannin da gaske kuka take ya saka Sudais ya kama hannunta ya nufi dakinta da ita

Suna shiga ya zauna bakin bed ya dorata saman cinyarsa

A hankali ya ce" menene?

Rauda ta dago ta sauke idannuwanta cikin nasa, murya a raunane ta ce" Aban Yara, yaushema na haihun? Abansu na sha wahala sosai, kar kuma a zo ana fadin bani da aiki sai haihuwa

Murmushi yayi ya ce" zabi ya rage naki *Mata*, ki kontar da hankalinki, ki rainar min cikina, ki kara haihuwa , ki bani farin ciki sannan gobe kiyama mazon Allah yayi alfahari da mu domin yace mal.umarsa ta haiyayafa domin gobe kiyama yayi alfari da mu.....

Ban ki ba aban yara,

Katseta yayi ta hanyar dora yatsarsa kan lebenta ya furta" shiiiiit, bana son ki bata min rai a irin wannan lokacin, bana son na ji haushinki dan kin ki taya ni farin ciki.......wannan dai cikina ne, ni na yi abina, ina son abina
Mata ina son ki, ina son kon ki, ina son kasancewa da ke.....tsoronki shirmenku na mata ne kar ki tsofe......mata koda ciki ya mayar da ke wata kala ina son ki a haka......ki daina

Da murmushi ta rungume shi, a hankali ta ce" ka san ba kishi nake ba...juste ina tsoron a kuma shigar min gonata ne dan kasawata ta wani fannin, koda zaka kara bana so dan na kasa sai dan ra.ayinka

Murmushi yayi kawai, ya mayar da ita kasansa ya haye bed din tana ji tana gani aka shiga kwallon....tafiyar da sai
.....m..mm....



*Alhamdulilah*



An gada a nvl, kai a komai ma ya kasance ka batawa wani, wani bai so ba......ku yafe min, Allah ya bani ladan dake cikin nan ya kuma yafe min kurakuran da na tafka......



Daga *YAR MUTAN NIGER, SAJIDA MAMAN LALLA*
Mu hade a *BAK'A CE......IN SHA ALLAH*


Complete by ummu hafeez the writer of 'yan matan amarya and Komai mukaddarine


Bye bye

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment