Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saka auren yan mata ukun nan cikin ikon Allah Allah ya fitar masu da miji a tatare wanda da mai shekara goma sha biyar rafi.at, da mai shekara goma sha shida Shafa, sai mai shekara goma sha takwas Bilkissu kowace ta samu mijinta mai mutunci har an saka rana

Bakar rana wace ta zo masu da canje canjen rayuwa ta sanadiyar zamowar Sudais zakara
Aure na sauran kwana biyu , sai shirye shirye ake... daidai karfinsu sun ciru sun kulu sun yiwa yayansu kayan daki daidai gwargwadon iyawarsu
A ranar juma.ar nan suna farkawa Gaba dayansu sun tashi da wani irin yannayi, gidansu kuwa har ya fara cika da dangi da aminan arziki

Rafi.at ce tsugene kusan mahaifiyarsu, ta ce" umana yau baki saka mana albarkar ba fa

Fadimatu ta dago ta yi murmushi ta dan jawo kuncinta ta ce" ai yau du sai na tashi da mutuwar jiki Rafi.at, a kulun nakan saka maku albarka safe da yama, Allah yayi maku Albarka ya yafe maku kurakuranku na jiya da yau da safe da wanda zaku yi nan gaba,

Murmushi ta yi ta ce" umanmu yau zamu tafi

Haka kawai ta ji gabanta ya fadi da maganar rafi.at ta ce" ina??

Rafi.at ta ce" ummah fa, wajen aunty? Da ta ce yau ya kamata mu je mu karbo sakon gaba dayanmu har mun shirya aunty bilki ce take ta jan jiki har yanzu

Mahaifiyarsu ta yi murmushi ta ce" ai fa sarkin nawa, ita kam akoy sanyin jiki ai

Suna tsaka da maganar Shafa ta fito, haka take daukan ido domin itama ta dauko fatar kakanta sosai ga tsayin gashi har baya,
Abaya ce ta saka mai ruwan ash coler sai ta kara haska fatar nata
Itama tsugunnawa ta yi suka saka mahaifiyarsu a tsakiya suka ce umah bara mu yi selfi

Ai kuwa suka dauki hoto,
Suna tsaka da yi sudais ya shigo, da yake gaba dayansu ya fisu tsayi da kakarfan jiki sai ya kasance shine karami aman suna shayinsa, gashi ba sake masu yake ba

Rafi.at ce ta yi kalar tausayi ta ce" broh ka zo mu yi hoto plz

Haka kawai ya ji yana son yayi hoton dan haka ya shiga suka yi su hudun

Wayar Shafa ce ta dauki kara ta daga , bayan ta kashe ta ce" umah mu tafiya zamu yi, kinga sai gagawa ake aman mu muna nan kar su tafi ba.a bamu sakon ba zamu karbo mata nata kawai

Mikewa ta yi tana wani irin sauki ta kama hannun Rafi.at ta ja da wani irin karfi na mamaki tana fadin mu tafi....

Fadimatu tana fadin" baku karbi kudin napep din ba fa aman ina har sun fita kofa
Da sauri ta mike tana fadin" ka ga sudais zo ka karba ka kai masu

Shima mikewa yayi ya bi bayan mahaifiyarsa sai dai me, suna shiga dakin ya ga ta yi wani irin tsayawa ta dafe kirjinta, da sauri ta juyo tana kallon kofar dakin nata

Cikin azama ya karasa yana riketa ya ce" momy, lafiya? Ko kirjin naki ne?

A hankali ta sakar masa nauyin jikinta domin a lokacin ji take tamkar ana zare mata laka gaba daya,
Bakinta ta bude zata yi magana sai dai ji ta yi an fasa kuka ana faman kiran inalilahi wa inna ilaihi raj.une

A hankali ta lumshe idannuwanta sai hawaye suka biyo baya, wani irin karfi ne ya zo mata ta mike ta bi bayan Sudais da yayi gagawar fita dan gannin menene ake shigowa da haka?

Idannuwansa ya rufe yana mai jin zuciyarsa zata fito daga gangar jikinsa sanadiyar arba da yayi da abinda ake shigowa aka dora saman tabarmar da yanzu suka tashi a kai

Da sauri ya juyo dan tare mahaifiyarsa sai dai inna, ture shi ta yi ta karasa kusa da mijinta da ta gani ya dukar da kansa ya fasa kuka

Tana karasowa ta shiga kifta idannuwanta sakamakon jin da ta fara yi sun fara rufewa, ta fara rasa ganninta
Wani irin duhu ne ya rufe idannuwanta sakamakon gannin gawowin yayanta amare biyu cikin jinni a konce basa alamar motsi

A hankali ta kai kasa numfashin nata ya dauke gaba daya

Daga wannan rana wannan family ya afka a rayuwa mai wuyar fasara, ciwo ya zo ya sarki Mahaifiyarsu, Muhammad ya tsayar da zuwa wajen aiki...,
Ciwo yayi ciwo a asibiti aka bukaci dubu dari biyu dan za.a yi mata aiki

Hakan ya sa ya dauki Sudais suka je ma.aikatarsu ya samu ogansu
Nan yake fada masa rasuwar da bukatarsa na a ranta masa wa.innan makudan kudade zai biya a sannu

Kare masa kallo yayi cike da isa ya ce" Wa.inda suka rasu Allah ya jikansu, aman karka manta malan Muhamadu daman muna binka dubu ashirin da muka ranta maka zaka cika ka sayawa yayanka kayan daki, to baka biya wasu ba zamu baka wasu? Gashi ya dace ka dawo bakin aikinka dan ka samu a baka albashinka ka biya mu bashin mu, kai in ba abinka ba Malan Muhamadu shekara nawa ya rage maka ka yi ritaya? Du yawan shekarun ba zasu fi 3 ba, a cikin su zaka iya biyan mu ne?

Cike da mamaki ya dago yana kallonsa ya ce" aman dai elhaj du irin shekarun da na bata ina bauta wa wannan makaranta a yau da bugata madaukakoya ta taso min za.a gagara biya min bayan bashi na nema? kai ka san koda aikina ya tsaya sai na biyaka zan iya samun konciyar hankali

Dakile fuskarsa yayi ya ce" shin kana da wata sana.a ce bayan wannan? A nan fa ka kare da ni ka dogara malan Muhamadu, sai ka yi min aiki na biyaka kake samun na cin abincin gidanka, to ta ina zaka samu irin haka???

Da sauri Sudais ya dago da kansa a karo na barkatai , wasu hawaye ne masu zafi suka zubo masa ya mike ya kama hannun mahaifinsa ya fito da shi , fuskarsa ya kure da kallo sai ya bude baki zai yi magana sai kawai bakinsa ya kwashi rawa sai ya rufe, idannuwansa sun yi jajir, ya kasa aiwatar da wani abu

A hankali mahaifinsa ya dafa kafadarsa ya ce" ka kontar da hankalinka Sudais wannan ai ba komai bane ka ji, ka tashi ka yi jirana

Da sauri sudais ya girgizawa mahifinsa kai, ya saka hannunsa a aljihu ya ciro naira dari biyunsu ta keke napep ya dankawa mahaifinsa, murya na rawa ya ce" Ka koma asibiti Aba,

Har ya fara taku cikin sauri mahaifinsa ya ce" Sudais ina zaka je ne haka?

Ja yayi ya tsaya, ya juyo da sauri ya ce" *ABA, ZAN JE NEMAN INCINA NE DOMIN NI SUDAIS MUHAMMAD NA YI ALKAWARIN BA ZAN YIWA WANI KATO NEMAN KUDI BA*

Tun daga wannan rana, *SUDAIS MUHAMMAD* ya fara neman kudi da jarin dubu ashirin da kakarsa ta siyar da gwal dinta na aure wanda mijinta kulley ya bata a tadar auren *buzaye* ta biya kudin aikin yarta sannan sauran aka yi dukan bukatu ciki ta baiiwa sudais dubu ashirin ya ja jari

Tabas sudais ya sha wahala, rana ta dake fatarsa , ruwa ya dake shi, sanyi ya kare a kansa....
Gari gari yayi ta bi, kasuwanni yake ci na kauyuka, yana saron yadidika yana kaiwa kauyuka, cikin ikon allah kasuwar kara daukaka take, haka ya shiga harkar wayoyi yakan sari kananuwan wayoyi ya siyar har ya fara manyan wayoyi abinda da dukan wanda Allah ya nufa zai yi arziki tofa ko mai ya taba zai yi albarka ne

A haka ya Allah ya dafa masa, ya kasance yana samun daukaka, lungu lungu ba inda kafarsa bata shiga dan neman ci gaba

A cikin shekara goma da suka karu Mahaifiyarsa ta kara samun haihuwar ya mace aka saka mata *Hafsat* wace yake jinta tamkar nama daya a miya, sannan kudi dai mai sunnan kudi Sudais ya fara tara shi sannan halitar jikinsa tana kara bayana kanta sai dai har yanzu shigar Sudais shi ne *doguwar riga da hirami*

Sudais na da shekara ashirin da bakwai mahaifinsa ya sako shi a gaba kan fa sai yayi aure, sai dai abin takaicin shi ne: sudais bashi da wannan lokacin, sannan yana da zabin macen da yake son ta zama abokiyar rayuwarsa, yana son idan zai yi aure ya samu balaraba yar mutunci wace a haduwar farko zata girgiza masa zuciya sannan ta nuna masa tsantsar so har sai ya gamsu ya aureta dan kuwa shi fa ba zai kali yan matan zamanin nan masuhalaya marasa kyau ya furta masu kalmar so ba, koda kuwa yar waye ko yar wace kasa ce bata isa ba!

Zuwa wannan lokaci ya kekara masu gini ya hana mahaifansa aikin komai su dawo sun zama iyayen Uban gida, yayarsa Bilkissu ta haifi yaya hudu kuma duka a gidansa suke wajen mahaifiyarsa, sai kakaninsa suma a bangarensu

A hankali ya fara suna, a kano sanusanu sunansa ya zagaye gari harma da makota
Tashi daya ya biyawa family dinsa haji, wanda a tafiyarsu sai dai su ne suka dawo shi kuwa ya samu wani reshe na kasuwanci wanda ya fara harkar abayoyi da gwal inda rigima ta bale a gida Momy ta samo masa matar aure kuma aba ya samo masa yarinyar abokinsa mai suna Humaira

Karshe dai sai kiran kakarsa ne ya same shi ta shaida masa
Hankalinsa ya tashi matuka da jin wai iyayensa zasu yi masa aure, bai zaci zasu dawo kan maganar ba sannan abin har yana neman kawo masu rigima a tsakaninsu
Bashi da abokin tambaya , hasalima yakanyi shawara da Hafsa ne, aman wannan abin ya girmami tunaninta
Cike da rashin kwarin gwuiwa ya nufo gida sai dai abinda yayi tunani dan samun nasarar su bar maganar sai ma kara daukakata da suka yi Aba ya yanke hukunci a matsayinsa na wanda ya haifi Uban masu gida wato *Elhaj Sudais Malale* sunnan da yan kasuwa da shuwagabani ke kisansa da shi cewar sai dai a wanke masa tsula tsulan yan mata biyu Humaira , da Khairat

Hakan kuwa aka yi a ranar da zasu tare shi kuwa ya kaura sabon gidansa na gra gidan da ya amsa kira, gidan da ya kashe makudan kudi ya tsara shi a tsare, dukan family dinsu da muhalinsa a wannan gida, sannan bangarensa daki biyu kadai ne sai can gefe sauran dakunnan

Bayan haka da sati biyu ya daga da matansa saudiya wanda tunda suka tafi basu dawo ba sai shi ne ke zuwa yayi wata a gida ko satitika ya juya aman a yanzu kuma abinda iyayensa ke so shine ya dawo gida nigeria dan kuwa ba son zamansa a kasar ta dindindin..... WANNAN KENNAN.....

.
......... *CI GABAN LABARI*.................


Ajiyar zuciya hafsat ta sauke tana kallon kakarta ta ce" ina alfahari da Yayana

Ramatu kakar su ta ce" ba ke kadai ba mu kanmu muna takama da UBAN MASU GIDA!


Daidai wannan lokacin mahaifiyar su Aisha ta kawo masu karshen labarin waye sudais a yanda ta karanta jaridar rayuwarsa da kuma yanda take jin sunnansa a kullun a gidan redio....


Cike da bege aisha ke saurare inda Rauda ta ji wani hawaye mai dumi ya biyo gefen fuskarta

Bayan kwana uku
Mamaki ne ya cika masa kwakwalwa, a sunayen da Hafsa ta bashi ba wanda bai dora a page din Facebook du ya ga sauran aman banda wa.innan yan mata biyu, wai da gaske ne bata da waya kamar yanda Hafsat ta fada? Aman a wannan zamanin daman akoy yan mata haka????

A hankali ya jinginar da bayansa jikin kujera yana kallon kiran khairat na shigowa a iphone dinsa aman ya kasa dagawa, a fili ya furta" who are you? Mai yake shirin faruwa da ni ne na damu da sanin wacece ke haka???????


Lumshe idannuwansa yayi yana mai jin yanda kansa ke sarawa, ko daya baya son damuwa ko wace iri ce hakan na saurin hadasa masa ciwon kai........




To fa me ke faruwa ne???




*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*



7⃣



Na: *SAJIDA*




Hotuna ne masu yawa a gabansa, wasun su biyun ne wasu kuwa ita daya, a hankali ya dauko wanda take ita dayan inda ta je gidan redio neman aiki wanda du wanda ta je shi yake kira ya hana a dauketa ba dan takardunda basu yi kyau ba sai dan kawai baya fatan ta je tana aiki a gidan redio ko wani gaula yana jin muryarta, shi kansa yana mamakin irin yanda yake kishinta , sai abin haushin na gaba ya ajiye mata envelope a table dinta na aji, ya ajiye mata a cikin adaidaita ya ajiye mata a zauren gidansu aman gaba daya sai ta dauka ta karanta da kyau ta fahimci mai ake nufi sakonta an rubuta mata sadaka aman sai ta rufe ta ajiye a nan inda ta gani, shi ya rasa ta ina zai bilo mata

A hankali ya dago wani hoton wanda ya saka gabansa faduwa, da sauri ya kalo saurayin da ya ba kongilar bibiyarta du inda take ransa a bace ya ce" ban yi maka gargadi da irin wannan hoton ba??

Da sauri saurayin ya tsurawa hoton ido kadan, shi dai bai ga ba inda hoton ya nuna abubuwan da ya hana, aman kuma ogansa yake fada haka

Ka daina kureta da kallo Samir! Ka gane na fa saka aikin nan ne dan na yarda da kai, karka yarda ka bani kunya a lamuran *Mata* domin idan har wani abin batanci ya bilo a tsakanin abinda na saka ka a dalilin *Mata* ina gudun aikata abinda za.a ji kunya! Ya zaka dauki hotonta gaban gashinta a fili, oya ka bani cameran da ka dauka idan ka fita ka sayi wata sannan ka kiyaye gaba wannan shine kuskure na farko kuma na karshe

Ajiyar zuciya Samir ya sauke gannin ba wani baban laifi bane ya aikata, aman duda haka ya shiga baiwa ogansa hakuri sosai sannan ya mika masa yar karamar camerar da ogan nasa ya bashi daman dan dauko masa yarinyar da ya lakaba mata sunnan *MATA*

Haka ya fito ya bar ogansa na tunanin hanyar da zai bi dan gannin ya kilaceta wa garwaya da maza ko fitar da muryarta har wani saunan ya ji...,

Samir na fitowa ya shiga sauri dan zuwa siyan wani cameran kafin gobe dan kuwa ya tabata a gobe ma sai ta fito dan neman aikin shi kam ya rasa ta ina zai bilo ya hana wannan aikin shi kam yana cikin tsaka mai wuya domin aiki ne mai hatsari sannan mai romo


Zaune take saman tabarma tayi dare dare ta saka mahaifinta a gaba, gefenta aisha ce itama da takardu a envelope sun yi shiru gaba dayansu can mahaifinsu ya nisa ya ce" aa, abin da mamaki domin na kaiwa wannan yaron takardunku salihu takardun nan ya duba ya tabatar min lale takardun sun yi kyau kuna iya samun aiki da su a fannin kasuwanci ko gidan jarida kai harta asibiti gefen ciren takarda sai dai abin mamaki har yanzu an kasa samu koda an dauke ku sai a yi kiranku a baku hakuri ni na rasa inda zan kamo

Ajiyar zuciya Rauda ta sauke ta ce" Aba, ni kaina abin nan na daure min kai, harfa wannan asibitin karami na je na kai takardar nan aman ba.a dauke ni ba ranar Aunty Aisha ta hada ta kai gidan sauki inda ake kasuwanci turawa ne a wajen aman har yanzu shiru ba.a kiraye mu ba, gashi lokaci na kure mana wannan shekarar dole sai da isasun kudi Aba
Ta karashe murya a raunane

Aisha ta dago idannuwanta jajir ta ci kukan takaici ta ce" Aba, dan Allah ka janye rantsuwar nan Mama ta je wajen yar uwar nata ta karbo mana koda rance ne mu je mu zuba Aba idan bamu samu manyan takardu a karatun nan ba wani daukaka zamu samu ba , aman wannan takardar zata bamu damar samun aiki mai tsoka

Sai da ta kai aya Malan Ahmad ya sauke ajiyar zuciya, irin abinnan na damunsa sosai fa har cikin zuciyarsa, wani lokacin har hakan na saka shi tambayar kansa shin yayiwa kansa da iyalinsa adalci kuwa da ya ki karbar tayin aikin da aka masa ya dawo ya bar iyalansa a cikin kunci da talauci? Sai dai wani sashi na zuciyarsa ya sanyaya da ya tuna sabawa Allah ya ki yi, dan haka kasancewarsa a haka Haka Allah ya so ya ganshi, shi bai isa ya canza ba shi kuwa ba zai canza hanya dan kawai ya faranta ran Aisha da Mahaifiyarsu ba, to aman idan basu samu aikin nan sun yi ba sai dai shekarar ta tafi haka? Ba tare da ya kula maganar Aisha ba ya maida hankalinsa kansu ya ce" ba zaku yi kunya a rayuwa ba, ku dai ku ci gaba da adu.a , wani jinkirin alkhairi ne Allah ya kawo maku mazaje na gari hakan shine baban burina domin kuwa shine baban jin dadi da zaku samu duniya da kiyama

Mikewa Aisha ta yi ta fada daki mahaifiyarta na sauraron radio ta je ta konta saman tabarmar leda ta yi lamo ta afka tunanin mutumin da ya zamo mata jiki, a hankali ta lumshe idannuwanta ta furta" idan iyayena ba komai bane basu da komai .... ni zan nemi kudi ko ta halin yaya sannan zaka aure ni *SUDAIS* domin ni ban hango namijin da ya dace da ni na dace da shi sama da kai, sannan da yardar Allah idab na hadu da kai koda a duban jama.a ne sai na furta maka kalmar so

Wasa wasa yau har sauran wata uku a rufe daukan daliban da zasu karanci kasuwanci na shekara biyu kawai wanda da wannan takarda kana da damar shiga ko wani kanfani koda a turai ne ka samu aiki mai tsoka sai dai kudin wannan makaranta masu yawa ne duda promotion ake kafin na yan watannnin nan dan a baiwa yayan talakawa damar samun wannan ci gaba wanda mafi yawancin daliban jami.ar sun fatsama nema dan su samu da yawa sun sami aiki sun fara zubawa yayan masu hannu da shuni har an biya masu wasun kuwa suna cikin paputuka dan gannin sun sami wannan dama

Zaune suke a anfani tun karfe bakwai na safe, sai karfe tara managern ya zo wanda bayan ya shiga suka ci gaba da zaman dan an yi masu iso an ce su dakata zai yi masu magana

Suna nan zaune wani saurayi mai kalar hutu ya zo ya shige cikin office din managern da ido suka raka shi kafin su kuma juyowa su yo zuru suna jira

Da shigar samir wannan office ya zauna yayi introduce dun kansa wa manager sannan ya gabatar masa da dalilin zuwansa wato *ELHAJ SUDAI MALALE* ke son magana da shi

Cike da mamaki da farin ciki manager ya karbi waya bayan Samir ya hada su ya yi salama wa SUDAIS

Kana ji Elhaj tanko Bashir, Akoy wasu yan mata biyu da suka zo neman aiki , ina so kar ka basu aiki idan da hali ka tura secreriarka ta salamesu ba sai ka gansu ba

Cike da mamaki manager ya ce" eh wa.inda suke zaune ba? Ai na ga takardunsu Elhaj sun yi kyau kuma fa

Kansa ya dafe yana saman katon bed dinsa dake saudiya ya mike zaune ya ce " ba dan takardunsu basu yi kyau ba, sai dan hakan shi ne bukatana sannan Samir zai baka tajardar kongilar idan na shigo kasar zamu hadu mu dandance maganar

Ai manager bai tsaya jin karshen maganar ba cike da farin ciki ya amsa da " tototo an gama yalabe, domin kuwa wannan kongila ya jima yana son ya samu a kala za.a kai shekara biyu sai yau Allah ya yi,

Yana mikawa samir wayar ya kirayi secretariarsa ya shaida mata ta salami yan matan nan ba zai dauke su ba ta basu takardunsu

Fitowa ta yi suna zaune zaman jira sai gani suka yi an miko masu takardu cewar su je ba zasu samu aiki a nan ba

Cike da takaicin zaman da suka yi, kudin motar da suka yi talbace talbace, karin da basu yi ba, sannan ga shi ba samun nasara aisha ta fashe da kuka ta zubar da takardun a gabanta ta dora hannayenta a kai tana kallon Rauda da ta hade rai fuskarta ke nuna abinda zuciyarta ke ciki

Tana hawayen ta ce" wai wani irin bakin abu ne ke bin mu haka?

Rauda ta kawar da kanta ta ce" kar ki butulcewa Allah Aisha, ba wani abin kawai mu kara hakuri zamu samu ai da saura

Cike da Haushi Aisha ta dan daga murya wanda hakan ya sa Samir ya kara daukowa mai gidansa maganar da suke fadi ta ce" haka fa zaki ce, ta ya zaki ce wani ba wani abin, ke idan ke bakya ganni ni ina ganni, yaushe zaki ce wani ma samu bayan yau sauran wata uku? Idan muka kara wani watan kin tabata zamu samu aikin da zai ishe mu biyan makarantar???

Rauda ta ce" to idan bamu samu ba ba sai mu yi hakuri ba?

Aisha cike da jin haushi ta ce" walahi a bakinki, karya kike , walahi ba zan hakura ba, haba baki da hankali ne? Abinda zai saka na kara samun kusanci da shi kike yi min bakin ciki? To walahi sai na samu kuma sai na yi dan kuwa a yanda nake sonsa ke ko sata sai na yi dan ba zan iya hakura da shi ba

Wannan karin ranta itama ya baci cike da jin haushi ta ce" to ai sai ki kwata aunty Aisha haba, kan wannan banzan dalilin naki da wuya mu samu biyan bukata , ni ina neman takardar nan ne dan na samu ci gaban da zan karawa mahaifana farin cikin rayuwa ba wai wani abin ba, aman ba komai Allah yayi mana zabin da ya fi zama alkhairi aman ki sani wannan mutumin da ya saka kika kara rikicewa *na tsane shi na tsane shi*!

Dau Aisha ta dauke Rauda da mari a wannan waje wanda har jama.a sun fara tsayawa suna kallon fadan nasu dan kuwa Aisha tana daga muryarta ne, cike da masifa ta nunota da yatsa ta ce" za ki saka na yi maki abinda ban taba tunanin zan yi maki a duniya ba, domin kuwa ina son mai sonsa sannan du wanda ya nuna masa kiyaya ko wanene nima ina kinsa!

A hankali rauda ta juya ta fice a wajen wanda aisha ta tatara takardunsu ta bi bayanta itama cike da fushi

Da sauri ya katse vidio call din da Samir yayi masa ya zauna ya dafe kansa ya da hannu bibiyu ya afka tunanin me ke faruwa haka? Menene kuna wannan?

Yana tsaka da tunanin ya ji danshi danshin ruwa, a hankali ta shiga shafa masa kirjinsa tana kara hade jikinta da nasa, ta mika hannunta ta janye hiramin dake kansa ta cusa hannunta cikin gashin kansa tana sosa masa a hankali sannan tana kokarin hade bakinta da nasa
Jajayen idannuwansa ya dago ya zuba su a fuskar Humaira, ba zai iya ba , a yanda yake jin zuciyarsa ba zai iya sex a wannan yannayin ba duda abinda ya tisoshi gaba kennan aman gannin ran *MATA* a bace shima ya hadasa masa da bacin ran mai tsanani

Cike da rashin kuzari ya saka hannunsa ya dakatar da Humaira ya dorata saman cinyarsa yana dan jan mata yar yololuwar rigar da ta saka

Hannunsa ya mika ya dauki wayarsa bai sauketa a samansa ba ya latso number Mai gidan radio Anfani, yana dagawa ya fada masa bukatarsa ya kashe sannan ya zubawa Humaira idannuwansa,

Humaira yarinya ce yar gayu, farinta har ya zarce na *Mata* , ta hadu karshen haduwa domin ko yannayin halitun jikinta ba laifi
Daidai gwargwado humaira na da biyaya duda ana fadin in dai namiji na da kudi kuma yana saki to fa ya zarce wulakancin mace dan kuwa Humaira dalilin aurenta da Sudais ba ita ba yan gidansu kansu sun huta
A hankali ya shafa gashin kanta ya lumshe mata ido bai iya furta mata komai ba ya mike ya fada wanka dan samun yar nutsuwar da zai iya zuwa shago ya fitar da kayan da zai tura Nigeria
Yana tsaka da saka kayansa yayi tsam ya zurawa girar idannuwansa ido, a hankali ya

Please Login or Register in order to submit comment