Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gunki? Ita ta ji ana cewa maza ihu suke harda kuka aman kawai Sudais sai dai ya wani yi mata shiru ga shegen nacin.....abin nan🤣

Da sauri ta ja ta ce" kar ka taba ni, kar ka taba ni ni, baka yi wanka ba , ka je ka wanke datin da ta kwaso, karamar yarinya har ka iya tausheta haka? Ni kar ka taba ni ka koma kawai ka waye a dakin nata

Cike da takaici Sudais ya ce" ke ki daina yi min magangannun shirme mana, idan ma hakan ne ba matata bace? Ko kin taba jin an ce na dane wasa ba tawan ba? Bare ma ni ba abinda ya shiga tsakanina da ita, wannan karamar yarinyar zan jewa? Ba sai na halakata ba? Ke kanki kin san irin matan da nake iya zuwar ma, dan haka kar ki yarda ki caja min kwakwaluwa rainon matata nake

Da sauri Rauda ta koma ta rufe dakin ta nufi tsakar dakinta
Kai kawo ta shiga yi, "wannan yarinyar zan jewa?
"Ba abinda ya shiga tsakanina da ita
"Ke kin san irin matan da nake zuwarma


Kishiyata yake fadawa ba abinda ya shiga tsakanina da shi?
Ya Allah, me hakan? Rainona yake?

I.m 22 old, aman ya kiraye ni da wannan yarinyar? Shi din menen girman nan nasa? Anya kuwa ? Ni ba mahaukaciya bace koda ban je university gidan kowa ba na je islamiya, Ohk shi nan sai na girma kennan zai san matarsa nake? Shi ya sa ya kula kawance da ni? *zan gani sire ni da kai wa za.a rainan*


A yau Aisha ta yi shirin komawa yar uwarta bayan ta yi bincike ta gane gidanta,
Sannan sarah ta sauko harda ara mata kaya dan su je tare domin aunty ta kashe kudi sosai dan karkata hankalin Sudqis daga Rauda ya saketa ya tsaneta ya karkato kan Sarah ko sa samu damar wanke goma su tsoma biyar





*BAK'A CE*

*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




5⃣2⃣



*BAK'A CE*........... NA NAN TAFE I.A







Tana shiryawa da daridari ne, dan kuwa ko a jiyan da dare sai da suka tsigeta bayan nan ne ta shaidawa aunty ta samo gidan Rauda tana son zuwa gobe da yama abinka da marar kunya a nan suka shiga nuna mata soyaya

Har nan nema sarah ta fauko mata wata rigar atampa da ta sha mahaukacin dinkin zamani ta bata cewar ta saka wannan dan kar su je a hana masu shiga


Bayan ta gama shiryawa Sarah ma ta gama hadewa cikin wani material dan ubansu tana ta kallon Aisha, a gaskiya Aisha ta hadu ... haka take ayannawa a kasan zuciyarta sai dai kuma banza ce sam ba yar gayu bace yanzu zaka nuna mata ta yi maka ta kawo maka hauka

Haka suka fito Aunty ta ba sarah wani turare a kwalba ta yi mata signe da ido
Har sun fita Sarah ta ce tana zuwa ta yi mantuwa ta koma wajen Aunty

Aunty ta ce" kin ga turaren nan? Ki tabatar ya shaki kanshinsa idan kika fesa, kar ki fesan ma sai yana wajen, ku like mata ki tabatar kin bugo mana shi fa Sarah kin ga uban gidan abanki ne yau ya kasance ya zo gidan nan neman auren ki hango min ci da cinyewa .... shikenan mun haye

Sarah ta saki murmushi ta ce" karki damu mom zaki samu abinda kike so
Ta cusa kwalbar a cikin breziyarta ta fito ta shiga motar ta tayar suka harba bakin titi

A yau Rauda ta farka da damuwa domin kuwa tsaf ta kwana tana tunanin irin abinnan da Sudais ya yi,, ya zai cewa kishiyarta wai wani yarinya ce ita ba abinda ya shiga tsakaninsa da ita?

A hankali ta mike ta je wajen Hafsat, bayan sun gaisa ta ce" sister kina da data ne?

Hafsat ta yi murmushi ta ce" hajiata Wifi ne ai a gidan naki baki ga sai shanawa nake ina hawa kyauta ba?

Murmushi Rauda ta yi ta zauna gefen bed din kadan ta ce" ina son dogon aiki da dayar wayarki, ina iya aronta wunin yau?

Hafsat ta mike tana dariya ta ce" ban san ya aka yi har yanzu oga bai baki waya ba, aman na san da dalilinsa, gata ki je har adadin da kike so danma kin fi karfin rike irinta da na baki kyauta

Rauda ta dan jujuya katuwar wayar kirar samsung s8 ta yi murmushi, bata ce komai ba
Kunawa ta yi ta shiga cikin uc browser, ta rasa ina zata shiga dan haka ta koma ta zauna ta ce" na ji aunty na fadin a cikin nan akan iya samun ap na komai ko?

Hafsat ta karba ta zauna sosai ta ce" kin ga, idan kina son shiga wajen harkar vidios, ko wace iri ce hausa turanci yare daban daban, sannan ko me kike son gani a ciki ki shiga youtube, idan kuwa ap kike so a nan saman wajen zaki rubuta sunansa zai baki
Haka dai ta nununawa Rauda abu uwa sosai a wayar kafin take yin godiya ta mike ta fita ta nufi dakinta tana turo baki a ranta ta ayanna gabjeje du kibar nan sai ya kara cin karfe , ta kebe bakinta ta fada saman bed dinta


Zama ta yi, ta yi shiru, ita dai bata da mutumin da zata tambaya yaya ake tarairayar miji, wannan abin kuwa dole sai an koya ba karamin abu bane...,

Ta jima tana nazari kafin take sakin murmushi,

Wanka ta salo, ta dawo ta saka doguwar riga marar nauyi kawai ta fesa turarukanta ta zauna ta jawo wayar ta shiga YouTube dan samun haske a abubuwan dake duhu a gareta, ta dauko vidios masu dama, wasun har rufe ido take idan tana sauraro wai kunya sai kuma ta saki murmushi ita daya

Haushi haushi yake kallon su a kofar gidan a tsaye suna ta yiwa sojawan wajen magiyar su bar su su shiga

Banban sojan nw ya fito fuskarsa a hade da yar karamar waya a hanunsa,
Yarensa na ganinsa suka sara masa sannan sukai shiru dan sun san in dai shi ne ya fi su hauka zai yi fata data da su ne,

Wa kuke nema? Wajen wa kuka zo?
Ya jero masu tambayoyin fuskarsa na nuni da zaku ci ubanku ne

Kallon juna suka yi, a hankali Sarah ta matsa kusa da Aisha domin sarai ta san su waye , ta san me suke iya yi, kurma suke kiransu a cikin gari domin basu da mutunci, wani bariki budurwa ba zai hana su ci ubanta ba

Aisha ce ta shiga inda inda ta ce" wawa wajen Rauda muka zo

Ke ba.a kama sunayen matan gidan gatsal haka! Ta san da zuwanku ne? Ya fada muryarsa na amo tamkar muryar Sudais

Kifta ido ta shiga yi , sai ga wayar hannun nasa ta yi kira
Dagawa ya yo ya ce" oga barka da safiya

Sudais ya amsa ya yi shiru, so yayo da ya bada umarnin a yi masu lulusar fitar hayaci , sai dai wani abu yace masa ya bar su su shigo ya ga ya zata dauke su? Ya zasu kaya

Murya a dake ya ce" su shigo

Yana gama fada ya kashe,
Sojan ya ce da su" mu je!

Yana gaba yana tafe irin na kakarfan mazan nan su kuwa suna biye da shi a dan guje guje domin ba zasu iya tafiyarsa da yanga ba

Gaba dayansu kansu ya daure, gidan nan a garin nan? Basu taba kawowa ransu tsaruwarsa ya kai haka ba, yanzu Rauda ce ke rayuwa a gidan nan a matsayin matar gidan? Rauda mafi kaskanci a cikinsu wace ko kwaliya bata iya ba? Ko wanka bata iya ba?

Suna wannan tunanin suka karasa kofar baban falon

Falo mai abin mamaki, falo mai tsari tsari mai daukan hankali
Yana bude masu ya juya ya koma

Sudais dake zaune ya umarci Hafsat da ta je ta kirayo Rauda, ta fada mata ko su waye kafin ta fito sannan tana fitowa ta basu waje

A hankali ya daidaita camerar falon da son (kara) yanda zai iya jin me suke fada (akoyta fa sai dai tsada)

Sun kusan minti ashirin a zaune, an gabatar masu da du wani dan abin motsa baki ga sanyin ac ga katuwar tv na hasko kasashen larabawa

Cike da nutsuwa take takowa bayan ta riki adu.a.o.i a bakinta a matsayin makaman da zasu kareta da dukan fitinar da auntynta ta zo da ita

Tana zuwa ta saki fuskarta ta yi masu salama

A tare suka waigo wajenta, rigar nan ce dai ta dasu mai ruwan hoda sai ta daura dan karamin dan kwali a samn kanta ta yi dauri kawai dan rufe kai ba dan kwaliya ba, sannan rigar kananuwan hanaye ne da ita, sai wayar wajen Hafsat da ta ara ta fito da ita domin tana tsakan karanta wata ap ne na yanda mutun za yana kara kula da jikinsa da sauransu

Fara.a ta bayana a fuskarta ta kara yi masu salama

Sai a sannan suka farga,

Aisha ta ce" eh lale Rauda, hajia kika zama shi ya sa kika shanya mu a nan ? Mun fi awa muna zaune hakama kafin a bar mu mu shigo wajen ki sai da mukai ta magiya ? Kennan ke ba zaki yi zumunci ba ko?

Rauda ta yi murmushi tana mai nemawa kanta wajen zama kusa da su ta ce" lah aunty ai ban san kuna zuwa yau ba, tsarin mai gidan ne hakan

Sarah ta gyada kai a ranta take ayanna zaki ci ubanki sai ganninsa ya yi maki wuya nan gaba

Aisha ma ta yatsina fuska ta ce" ka ji masu gida, ke yanzu kina rayuwa a gidan nan, kin ci kin tayar da kai aman iyayenki na gidan laka? Da mariga ta yi shikenan su da gannin haske?

Rauda ta sauke kanta kasa, ta dan jima kafin take dagowa tarrrrr ta ce" *ALLAH YA SAN DA ZAMAN SU*

Sarah ta kama baki ta ce" kai kai kai, ke zumunci fa ya kawo mu wajen ki ba neman wani abin ba, ya zakina sakar mana magangannu haka sai kace wa.inda muka zo yaki? Waima ina mijin *namu* yake ne ya fito mu gaisa mana?

Rauda ta tsaida kallonta kan Sarah, itafa yarinyar nan tunda take magana mai tsayi haks bata taba hada su ba, kai ita bata ma yarda da ita ba kwata kwata,
Idan Rauda ta baiwa Sarah amsa, to lale bangon dakinma ya yi magana, share maganarta ta yi tamkar bata yi ba wanda hakan kuwa ya bakanta mata rai sosai

Aisha kanta ta dan ga canji sai dai ta danganta hakan da yau yan rashin maganar ne a kan Rauda dan haka ta matsa kusanta ta kamo hannunta na dama ta ce" Lallana,

Rauda ta dago ta bata hankalinta gaba daya, ta amsa da" na.am

Aisha ta ce" kina tune ranar da na san Elhaj Uban Masu Gida kike aure da kina kukan nan kin ce" *Aunty kar ki yi fushi da ni, ni zan nemi ya sake ni sai ya aure ki* an yi haka ko ba.a yi ba?

Rauda dake kallon ta ba ko kifta ido ta ce" Eh haka an yi

Aisha ta kara matsawa sosai ta ce" na zo ne kan hakan Rauda, ke kin fi kowa sannin irin yanda nake son sa ko? Ke nake baiwa labarin idan na aurw ahi ga yanda zan tafiyar da rayuwar mu ko? Ke dai ke zaki baiwa labarin bana hada soyayarsa da na kowa

Rauda da gabanta ke faduwa ta gyadawa Aisha kai ta ce" eh

Aisha ta ce" ki cika min mafarkina, ki tabatar min da hakan na iya yiwuwa , na tabata tunda kika furta kalmar ya sake ki ya aurw ni ba abinda ya shiga tsakaninku, ina fatan har yanzu zaman doya da man ja kuke

Rauda ta tsareta da ido, ikon Allah haka ta furta a kasan zuciyarta,

Ki bani amsa mana Lallana, Aisha ta fada tana kara kallon ta

Zara zaran gashin idannuwanta ta lumshe, a hankali ta bude ta ce" aunty me kike son sani takamai?

Aisha ta ce" ki fada min wani abu ya shiga tsakaninku ne?

Rauda ta ce" aunty ai wannan siri ne mai girma wanda idan na bayana shi Allah zai kama ni gobe kiyama, insha Allah zan rike sirin mudin raina

Ido Sarah ta zaro ta ce" ta faru ta kare

Aisha ta ce" kinga Sarah ba abinda ya faru na san kanwata fiye da komai, Raudana ba zata aminta ta bakanta min ba,

Na san kin ki fada min ne dan tsoron Allah Raudana, aman ina mai neman wannan alfarmar a wajen ki , ki kashe auren nan ya aure ni, ni zan fitar da mu daga kangin talauci, ni zan kawo mana sabuwar rayuwa , kema na biya maki karatu kasashen waje ki je ki cika burinki na zama hamshakiyar yar kasuwa, abanmu ya daina faskare kin ji?

Rauda ta ce" ko?

Aisha ta ce" Eh mana ,

Rauda ta yi murmushi ta ce" tohm

Aisha ta yi murmushi itama, abin ya zo mata da sauki ma, Allah ya taimaketa har yanzu ba abinda ya shiga tsakaninsu ga dukan alamu

Aisha ta waiga ta ce" ina tsinaniyar kishiyar taki ne?

Rauda bata ce komai ba kawai kallon su take da mamaki, haka wai dama sukai rayuwa? Aisha banda son kanta da kin tsoron Allah bata ajiye komai ba

AISHA ta ci gaba da fadin" zata gane kurenta ne idan na shigo tana ji tana gani Elhaj zai gagareta, domin soyaya idan muka fara baje kolinta ba shegen da ya isa ya raben min shi

Rauda ji take wani abu na taso mata, mijinta na suna ne auntynta ke furuci haka kansa, idannuwanta ta lumshe ta ci gaba da jan carbinta tun karfinta rana neman natsuwa a wajen indalah


Haka sukai ta tsara mata yanda zata kashe aurenta kuma su suna ikirarin ya auri Aishar, sai kuma abinfa ya tsaye mata irin yanda sarah ke ta faman wai yana ina ta yan shi, har ta fara cicira maganar ya ki zuwa ya gaishe su a matsayin su na yayunta

Da ido kawai take binsu tamkar sabon kamu, sai kuma zuciyarta ta shaida mata *SUDAIS FA NAMA DAYA NE KWAL A CIKIN MIYA, MIJINTA*

suna gamawa suka mike da niyar tafiya

Wajen Hafsat ta je ta fada mata zasu tafi

Hafsat ta fito tana waya da yayan su ya shaida mata kar Rauda ta saki ta fita, sannan ya umarci Hafsar da ta yi masu kyauta wada zata gigita su

...................wannan kennan......



*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




5⃣3⃣


*ina mika godiyata ga mumbers Idan ka raina inda ka ke, ina jin dadin comment din ku fiye da tunanin ku, fatana na yi ta faranta maku kamar yanda kuke faranta min........*



Fuska daure Hafsat ta miko masu envelope tana tir da Sarah, daman bata da mutunci har ta so yin kawance da ita?

Sarah tana sakin wani malalacin murmushi ta ce" kawata ni kamar baki gane ni ba?

Hafsat ta kaleta da kyau, ta juya ta ce" yana jiran ki zai raka ku kofa ,

Aisha ta kuga muryarta ta ce" aa, to ina Raudan?

Hafsat ta yi masu banza ta shigewarta dakinta

Sun dan jima nan tsaye sai gani suka yi kofar banban falon ta bude,
Sojan nan ne ya bayana dan haka da sauri suka yi waje ya yi masu rakiya...........


Rauda tana komawa dakinta ta zauna saman kujera mai zaman mutun daya, waje daya ta kurawa ido, magangannun Aisha ke dawo mata" ki kashe auren nan ya aure ni, .....

Na kashe aurena ? Auren da iyayena sukai min hudubar na yi biyaya ? Mijin da ta aureni ya aure ki? Ikon Allah, Aunty ai ana barin halal ko dan kunya, ke yayata wada muka konta ciki daya kece ke furtan kalaman nan? Takamarki ke kika fara son sa kin fi ni son sa? Kin manta ni kuwa ni ce *ZABIN DA ALLAH YA YI MASA?* ohk na bakanta ran kowa, uwa uba na sabawa Allahna dan na faranta maki wanda inada tabacin ba zaki taba gode min ba?

Kanta ta girgiza ta dauko wayar ta tatara damuwar tunanin auntynta ta watsar a kondon shara tana furta a fili cewar" AUNTY ki yafe ni domin ba zan maki biyaya ba, HUMAIRA ki gafarceni domin ina son sannin ni kaina wai banzar ce ko kuwa? Sire, ka shiryi zuwa dan na dauki makamin tarwatsa du wani kudurinka .....ina son ganewa ina son sannin yar shila ta isa yanka kuwa? (🤔)

Takarda ta dauko da alkalami ta zauna ta shiga rubuta dukan abubuwan da take bukata, tana yi tana murmushi domin abubuwa.ne na gyaran jiki na jiko, wanda ya rubuta abin ya ce ba lale budurwa ta sha ba aman ko ta sha ba wata damuwa du cikin gyara ne

Tana gamawa ta mike ta ajiye ta fito ta nufi dakinsa kai tsaye

Tana zuwa ta nemi izinin shiga

Ya fito daga bayi ne ya saka kayansa yana kokarin shafa dan mai marar maski dan ya saba komai zafi sai ya shafa mansa mai kara gyara masa fata

Karasawa ta yi tana masa murmushi ta ce" hi freind

Tsareta ya yi da ido, kafin yake miko mata hannunsa na dama ya ce" asalamu alaiki freind

Hannun nasa ta cafke tanai masa dan murmushi kafin take neman waje ta zauna kusa da shi sosai

Yana gamawa ta dauko tea ta zuba ruwan zafi ta hada masa a dan kofi lipton da ananas ta mika masa
Karba ya yi yana mai gode mata da idannuwansa

Sai da ya gama sha , ya amsa kiran Samir a waya dan jin karfe nawa zasu je wajen daurin auren wani ma.aikacinsa

Yana ajiyewa ya zo kusa da ita ya zauna ya ce" menene labari Hajiata?

Ta kallo shi da kyau, a ranta ta ayanna haka fa , hajiarka bayan a ranka kanai min kallon yar shila ne

Ta lumshe idannuwanta ta bude ta sauke saman kansa ta dan yi wasa da su kafin ta ce" freind, plz mana ina son zuwa saloon

Kallonta ya yi da dan sauri, a ransa ya ayanna saloon kuma? Kai ina ba zai yiwu ba , a saloon din fa akoy maza, ko ba maza a ciki akoy masu yawo haka kawai a kale min mata? Ni mai yasa ma ban yi saloon a gidan nan ba? Yanzu da kawai sai dai ta leka a wanke mata kan a cikin gida hankalina konce


Gannin ya yi shiru ya sa Rauda ta matsa ta dan shiga jikinsa ta ce" plz mana Freind, ina so ne na gyara gashina kuma tare da Hafsat zamu tafi ka amince min ka ji?
Ta karasa tana mai tsare shi da ido tana marairaicewa tana dan kara shiga jikinsa

Jin lunfashinsa yayi ya dan fara canzawa sakamakon hada jikinta da nasa da ta yi, a hankali ya samu ya janyeta daga jikinsa, ji kawai ya yi yana amsa mata da " to ku shirya idan an dan jima sai ku je

Da sauri ta mike tana murna ta kara rungume shin kana ta juya da gudu gudu ta yi dakin Hafsat dan fada mata

Baki sake ya bi bayanta da kallo, a fili ya furta" kai, ya aka yi haka na amin e mata fita zuwa saloon?
Baya baya ya yi ya dafe goshinsa ya afka tunani, fadi yake ka ga Sudais ka farga daga rungumarka ka amin e mata fita?
( han ...)

Shiryawa suka yi cikin abayoyi bakake
Kamar yanda Hafsat ta yane kanta da dankwalin rigar haka ma Rauda ya kasance fuskokinsu kawai ake gani domin tsayi ne da ita hakama hannayen vudadu ne sosai

Fitowa suka yi suna dan hirar su suna dariya kasa kasa,

Sudais Da Samir ne zaune a falo an kawo masu jus da dan abin taba baki suna tataunawa suna jira lokaci ya yi su je wajen daurin aure

Kanshin turarensu ya isar masu da zuwansu

A hankali Sudais ya dago gabansa na dan faduwa ya ayanna what? Ita da zata fita me ya hadata da turare?

Tsare fuskarta ya yi da kallo, batai kwaliya ko kadan ba, kwalinma tun na asuba ne da ta saka (wannan na daya daga cikin hudubar ma.aiki ga yarsa mafi soyuwa a gare shi wato nana Fadima cewa" du abinda kike kar ki bari mijinki ya ga idonki ba kwali😌 ( gyara ba laifi) )

A kasan zuciyarsa ya ayanna" MATA kina da tsararen kyau wanda idan kowa a duniya ke ganinsa zan ji haushi, bana son ki gane halin da nake ciki mata,

A hankali ya dan dukar da kansa ya canza harshe wanda sun iso aman basa jin me yake fadawa Samir domin basu iya yaren ba kamar ruwa ruwa wato larabci, ya ce" Samir, zaka kai su saloon

Samir ya dago yana kallon sa, ya ce" aman oga kafa yiwa mutumin nan alkawarin zamu je

Sudais ya ce" eh zamu je mana aman sai an kai su na ga dawowar su kafin mu je

Samir ya ce" idan aka daura auren fa

Sudais ya hade rai ya ce" kai malan, idan na je nine alwalinsa ne? Ka ga ka yi min abinda zan samu nutsuwa, ba zan lamunci Hafsat ta tukasu haka sake ba kuma ba zan yarda wani garjejen direba ya ja min mata ba, dan haka kumu je tare mu kaisu

Samir kam abin ya girmami tunaninsa dan haka sai ya amsa da kai kawai ya mike yana satar kallon Hafsat a ransa ya ayanna" ita harda su jan baki, idan na yi magana tace ai ita a kasuwa take, na saya na saya aman ta ki, kai gwara ma mu kaisun hankalina zai fi konciya ni din ma

Hakan kuwa aka yi, Hafsat ce ta nuna saloon din da zasu je, suna zuwa Sudais cikin hade fuska ya ce" zamu je anguwa da mun dawo zamu biyo mu tafi gida

Da toh suka amsa bayan sun yi godiya suka fice suka shiga saloon din

Katon litafi mai dauke da kalolin gyaran gashi tun daga coiffure da kitso kala daban daban aka miko masu ,
Nan mai saloon din ta fada masu cewa ana gyaran jiki ana wankin kafa ana dilka da kurkum ana gashi idan suna so

Kallon juna suka yi kafin Rauda ta dan saki murmushi ta ce" sis, ina gannin ko zaki je ki sayo mana sauran kayayakin nan ne ? Kin ga idan na je kar ya zama damuwa

Hafsat ta karba tana karantawa, ta kali hajia mai saloon ta mika mata ta ce" hajia wannan kuwa a ina zamu samu?

Hajiar na amsa tana karantawa ta ce" ai ina da su, sai dai nawa na kirki ne akoy tsada

Hafsat ta yi murmushi tana zama ta ce" wannan ba damuwa bane, yanzu abinda muke so muna son dilka da kurkum, muna so a gyara mana kanmu, a yi mata turare harda wankin kafa

Hajia tana murmushi ta ce" kawai ki ce a yi mata gyaran amarya

Hafsat ta ce" yawa Hajia , sosai fa , ki baje komai kawai ki yi mana bilan

Hajia ta kirayi biyu daga cikin yaranta suma matan ne masu kyau da su ta fada masu aikin da zasu kama mata
Hajia datijuwa ce mai gyaran amare da saloon , ta kware a aikinta bata da dar ko wa zai zo ta san yanda zata tarbe shi

Please Login or Register in order to submit comment