Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

itace itace

Mama ta yi saurin matsawa kusan malan, murya kasa kasa ta ce" walahi ina tune da ranar, ta shigo tare da yayanta kwaya biyu ta nemi da mu taimaka mata aman sai Aisha ta wulakantata ta kore ta, bayan ta fita ne Rauda ta kwashi wasu suturunta ta bi matar ni dai ban san ya sukai da ita ba da ta dawo ta jima kagin take cewa mama abin mamaki matar nan sunana ta kira , ni kuwa nace da ita to ai ba mamaki domin tana fita a waje ma sai ta ji sunanki da haka muka ci gaba da shagulgulan gabanmu

Da kyar aka samu ta barta bayan ta maimaita ba wani nisa zatai ba domin irin masu halayan Aisha take nema dan ita jininsu ne abincinta

Daga wannan ranar Aisha ta kuma dawowa wata shiru shiru da ita sosai, bata yawan magana, sannan abu kadan sai ka ga tana hawaye ko ta tsorata,
Hakan ya kara tayarwa da mama hankali ta shiga adu.a tana nemawa Aisha sauki wajen Allah

Tsohon Saurayin Aisha dai Fahad ne ya dawo yake nacin zuwa wajenta, wani lokacin mama ta fatataketa ta fita wani lokacin ta fashewa mama da kuka wai ita walahi tsoro take ji yana da mata fa, sam ba dan rainin abin hannunsa ba sai dan tsoron matarsa
Mama takan ji tausayinta a ranta aman a fili ta nuna ai mai matan shine daidai ita me take tunani? Tana jiran saurayi santali ya fito mata ne? Ai wannan ma Allah ne ya ji kanta ya turo mata da shi dan haka ta karba kawai ta yi hamdallah......

Rayuwar Sudais da Rauda a kasar saudiya

Rayuwa ne mai cike da tsari, dumbin kulawa, Rauda na samu wajen mijinta haka shima yana samun tarin soyaya, kulawa, uwa uba nutsuwa a tare da yarinyar da ta yiwa zuciyarsa dirar mikiya sannan ta shayar da shi mamakin yar shila ma mace ce😂

Zaune take ta tsurawa windows ido, filfilfil iskarnan mai dadi mai saka nutsuwa na hurawa, dadin garin manzo ni.ima daga nan ta fito,
Hadarin da bai yi shawara ba cida ba komai ne ya fara sakin ruwa, sai garin fiyayaen halita garin gagara gasa garin masoyina 😌,

A hankali ta mike ta je ta rufe windows din ta dawo ta zauna zuru da ita

Ya jima yana kallonta kafin wayarsa ta dauki ruri ya nufeta

Mom shine abinda ya gani dan haka ya daga da salama

Bayan sun gaisa Mom ta ce" watanku nawa son ? Ba zaka zo na ganka ba ko?

Sudais ya yi murmushi, Mom kennan, wai ya zo ta ganshi, so dai take ya zo ta kara kakaba masa yarinyar nan ya dawo yana ta fama tamakar wani yaro karami kulun bakinsa yana haiga idan ya tarota ta nan sai ta bule ta can

Sai da suka gama wayar ya ajiye ya dauki uar karamar ta ma.aikata ya yi kiran wani balarashe imran sukai magana suka gama kafin yake karasowa a hankali wajen Rauda da wata wayar a hannunsa

Yana zuwa ya zauna inda ske facing din juna,
Yar doguwar riga baka ce a jikinta, gashin kanta ya yi mata luwaiwai sai hannunta na hagu da wani dan abin hannu siriri ta daura shi shikenan sai kanshin da take bazawa
Rauda ta zama wata fresh da ita, fatar jikinta ta zama wata mai sulbin gaske sannan ta kara haske, hutu ya bayana ta ko.ina a jikinta koda yaushe cikin gyaran kanta take bata yarda dan sun yi wata biyu da kwana goma sha hudu da shi ba tace wai sun saba, a kulun takan tashi da niyar wannan bakona ne, wanda nake son na birge, na ja ra.ayinsa, na yarda da kalmar tsoka daya ne a miya kowa wawa yake kai masa, dan haka nima ba kowa bace dan ya nuna yana sona ba hakan zai bani damar na zubar da makaman yakin yakar zuciyarsa ba, domin kuwa zama wahe daya ya kori komai,
Hakan da ta sakawa ranta ya saka take binsa da dukan matsayinsa na miji a wajenta, tanai masa biyaya ne mudin ranta, sannan tana kokarin bashi hakinsa a duk lokacin da ya nema kai harma kokari take ita kanta ta nema dan ya jita a ransa
Tako taka rawa ya yaba harba yayi kari, domin salolinta sun zo masa a yanda yake so,
A ranar da cikin baci ya jita tana kai masa hari.....wato tana nuna bukatarta a gare shi , ya ji shi tamkar wani sarki....cike da nustsuwa ya amsa gayatarta harda yayi dare a wajen, tun daga lokacin ya kara sarawa ya sake komai kawai Yar shila ta gama da shi (🤣)

Habarta ya saka hannunsa na dama ya dago, kafin yake kashe mata ido daya ya ce" ni wai shashare nin na menene?

Bakinta ta turo ta juya masa baya tana dan alamun kuka zatai

Juyo da ita yayi, ya shagwabe fuska kamar yanda ta yi ya ce" a sasautawa Sudais yana neman kansa

Rauda ta yi walwal da idannuwanta kafin ta ce" sire, a gaskiya ina kishin mijina.....ta ya za.a ce wai ministan wannan gingirmemen garin yana nemawa yarsa aiki a ma.aikatarka sannan a matsayin secretariarka? Aa, ni fa ba yarinya karama bace na san magana idan aka yi, mu koma gida ni gida nake so

Ta karashe tana fashewa da kuka bilhaki

Ajiyar zuciya ya sauke yana taping din bayanta, har wata zufa ya ji tana karyo masa ta tashin hankali

Murya a rine ya ce" ki yi hakuri Mata, yanzu ya kike so a yi?

Sasauta rigimar ta yi tana kallonsa ta ce" idan har dole sai ka dauki mace a matsayin secretaria ka dauki matanka aunty da ni mu kasance a kusa da kai

Dariya ya fashe mata da shi har yana dan rike ciki kafin yake tsagaitawa ya dan nunota da yatsarsa karama ya ce" ko ku kori du macen da ta zo siyaya wajen mijinku ba, bayan sana.ar dan almajin du yawanci harkar kayan matan ne....shikenan sai mu yi tsawa mu dawo gida abinmu

Raudama ta yi murmushi ta fada kirjinsa murya kasa kasa ta ce" koda mijina ya shekara goma a gabannnan a zaune bana tunanin wani zai gane cewar baya aiki domin Allah ya rufa masa asiri fiye da tunaninsa,
Farin cikina ina kishin mijina domin ina sonsa

Ajiyar zuciya ya sauke ya bata wata runguma mai zafi,
A kunnanta itama ya kawo lebensa, a hankali ya ciro harshensa ya lashi gefen kunnen nata, ya kai bakinsa sosai ya ce" kin san meye an fasa daukan nata, sai dai zuciyata ba zata iya harbawa ba in dai tana tunanin kina can waje wajen da wani gardi na iya ganinki, Rauda zan haukace idan na ji labarin kin taba son wani a duniya, zan shiga mugun hali idan na ga wani na kallon min mata........yanzu kuwa duniya ta ki gaskiya, mutane sun lalace......rudin duniya na halakar da bayi, mazonmu ba zai ji dadin wannan lamari ba duda ya san da zuwan zamanin, al.umarsa tana ta manta dumbin alkhairinsa a gareta tana tafka tsiya a doron kasa bayan ta manta wanda ya yita ya fita gannin kanta......ba zan iya barinki ki fita aiki ba, ki yi hakuri Mata

Kankame shi ta yi ta shiga kai masa farmaki, yana zuwa da zafi zafinta wanda basu iya tashi sun karasa bed ba sai nan kan lalausan kafet din falon suka baje koli.......🤦‍♀

Haba dady, dan Allah ka yi hakuri ban gansu bane da na hada har su

Dady ya watsa mata harara ya juya ya fice abinsa
Mahaifiyarta dake zaune tana danna waya ta ce" ke idan kin gama wankin na babanki ki maida hankali ki dora girki mana

Mikewa Humaira ta yi tana sharar kwallah ta nufi kayan ta kwashe ta je wajen yin wankin inda mahaifiyarta ta bita da kallo,
Gaba daya jikinta ya yi wani tabo tabo
Wani wajen tamkar an kona,
Fuskarta kuwa ta yi wani mahaukacin baki ta yi mata tsaba tsaba tambar jikin tsaka
Humaira dai ta dawo sai kace zarara ita kadai ma magana take idan tana zaune, somin har mafarkin khairath take tsabar ta sakata a ranta fadi take alhakin Khairath da Sudais ne ke binta , khairath bata duniya bale ta yafe mata sudais yana duniyarma aman ta tabata ko tsafi take ba zata iya kai kanta inda yake ba
Kuka ne aikinta ba dare ba rana, sai tana susar fatarta tamkar ta yageta ta huta, ta dawo wata kala da ita, abin sai adu.a, takan saka abinci gaba sai ta fashe da kuka, tun bata iya girkawa ba har ta iya wasu abubuwan , aman sam ita bata jin dandannon su a bakinta
Sama ta kalla bayan ta gama wankin ta ce" khairath, ina kike? Ke mutuwa kikai........ki godewa allah idan har Allah ya cida ke kin huta, mijinki ne ya wanke ki yana hawaye, cikin nutsuwa ya suturtata ki sannan shi ya raka ki har gidanki na gaskiya, shi ya saka ki yana mai binki a hankali tamkar kwai, yana taisaya maki yana jinki har ransa ya rabu da ke, yana ji yana gani ya dawo ya baro ki a wajen wanda ya halice ki wanda ya fi shi son ki, khairath Allah ya jadada rahama gare ki, ya jikanki
Rana gama fada ta fashe da kuka ta duke nan domin wani jiri ne ya kwasheta

Mamanta ta mike da sauri ta fada dakin su domin ba zata iya ba, cikin haihuwa ba zai barta ta yi shiru bata lalabi Humaira a wannan yannayin ba
Dadynta kuwa murmushi yayi, ya tayar da mota,
Dadi yake ji idan ya ga irin haka, yana so ya kara yarda da nutauwarta kafin ya makata islamiya kafin elhajin ya dawo ya je da kansa dan ya ji a matsayin da take idan ya saketa ne sai a yi hakuri a yi fatam samun wani mijin na gari.......

Sarah ki daina bina, Sarah bana son ganninki kwata kwata a rayuwa, bana iya buda idannuwanna na gan ki ba tare da na aibata ki ba ki fice sarah
Ta karashe tana karajin da ya saka sarah rukunkume jikinta tana kyarma

Ta dora hannunta a kai ta rasa inama zata nufa ne? Sarah na dauke da cutar kanjamau, a haka suna cikin wannan tashin hankalin Elhaj ya biyo dare ya rufe dakinta ya afka mata (wa.iyazubillah), har fadi yake dan ubanki da kare kawai bakya yi shima dan baki san ya da zaki yi yayi da ke ba aman ni ubanki ki hana min, ko ki yarda ko na kashe ki na kashe uwarki na bi ta baya sai kun kunbura kun fashe za.a ji warinku mu je mu birne banzaye masu son abin duniya
A wannan rana sarah ta ga balaki gannin idannuwanta, daman da yan kuraje dake tsatsafo mata a gabanta wa.inda har wani wari suke tamkar muse haka Abanta ya ringa gugarsu yana darzarsu ya gama da ita ya makawa mahaifiyarta saki yana ikirarin tarbiya ai ta uwa ce dan haka ya saki uwar saki uku sai a je a bi layin karuwanci
Tafe dai ne kawai aunty take, aman bata san inda take jefa kafafuwanta ba, zuciyarta ta yi mata nauyi, gidansu suka nufa wanda sai da dan adaidaitar ya ajiye au ya bi su karbo kudinsa

Tunda aunty ta shigo ta riko hannun mamanta gam, kallonta take tana hawaye tana tuna irin tarin cutar da ta yiwa iyayenta da kanwarta dan son kanta, kamar yanda bokanta ya fada in dai suka ji sunnan Mama toh zasu tuno da ita ne da muguwar soyayarta a ruhinsu hakan ya sa ta kafe mahaifiyarsu da ido ta ce" ummey, ina MARIAMA take

Tamkar bugawar guduma haka sunnan ya shiga kwakwaluwar Ummiey daya bayan daya, wanda a nan ta zube sumamiya............

*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*

Na: *SAJIDA*

*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

6⃣3⃣

Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une
Shine abinda suke ta maimaitawa bayan malamin da yayi ta yiwa Aisha Rukiya kwana da kwanaki kafin ake samu ta yi magana, da sai dai zuru sai kuma ta yi ta ihu tana nuna waje tana gatannan ta dawo itace itace

Tamkar bugawar guduma haka sunnan ya shiga kwakwaluwar Ummiey daya

Please Login or Register in order to submit comment