Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi idan ina hawaye?

Rauda ta shiga kikifta ido itama tana hawayen a hankali ta ce" ya fi karfin kwatance hawayen mahaifiyata

Mama ta lumshe ido ta ce" ki taya ni kara rokon gafarar abanku, ya yafe min aman ya kara yafe min ya saka min albarka, Rauda du irin girman darajar miji da Allah ya ce *Da zai umarci mutun ya yiwa mutun sujada da ya umarci mace ta yiwa mijinta sujada* , aman na take, na halbe, na dane, na yi ta wasa da shi tamkar birin wasa na,

Sai dai na godewa Allah da ya nusar da ni kafin na koma gare shi a irin wannan rayuwa

Tashin hankalina a yanzu shi ne ku yayana ... bare ke da Allah ya nuna min kin yi auren
Rauda shin a ya kike daukan girman darajar wannan sunna wato *MIJI?*
kina da niyar aiki ko nace kamanta yanda ma.aiki ya koyar da mu dan gannin kin kare hakokin *MIJIN KI?*

Mama ki dakata mama, dan Allah mama ki daina tsoratar da ni! Rauda ta fada tana mai rusa kuka

Mama ta ce" kina tsorata a yau a gabana dan na titsiye ki, ni mahaifiyar ki ina da ranar gobe kiyama idan Allah ya tsayar da ke da litafin rayuwarki ya hasko ki gaban bainar nasi ya kirayi sunan ki ya bayanar da fila fila a aikace aikin da kika aikata a gidan duniya tunva na mijin ki ba ( la haula wala kuwata illa bilah,,,, 😭,,,, ya Allah ka bamu ikon kamantawa, ka bamu ikon yina mazajen mu biyaya mudin ran mu )

Da sauri Rauda ta fada jikib mama ta rungumeta, tana hawaye a hankali har ta samu ta dan tsagaita jin mama ta yi shiru tana taping bayanta dan ta yi shirun itama

Murya a raunane ta ce" mama, tabas dan adam butulu ne, yakan mance duban alkhairin da Allah ya babaye shi da shi rudin duniya ya rude shi,
Wani lokacin tsoro da fargaba da nagatan da basu tsoron Allah kan kai bawa ga aikata laifi mafi muni ga wanda ya yi duniyar da abubuwan cikinta baki daya..... mama ina zamu je? Ya zamu yi? Me muka tanada? Me zamu ce masa?

A hankali mama ta ce" *mu gyara, sai mu samu rabauta domin shi din gafurun rahim ne Raudana*

Mama ta ci gaba" du wace ta ce maki kalau ne, ita mijinta bai taba yin fushi da ita ba, ko bai taba daga mata murya ba, ko ya kasance yan rigingimu na yau da gobe tace ita bata sani ba karya take, ta fada maki haka ne dan gadara da karya sai dai kuwa idan ba a hayacinsa yake ba wato asiri wanda na rantse idan har kika yarda kika yi shi ko a kiyama kar allah ya hada ni da ke Rauda, biyayar nan dai, hakurin nan shi na toke ki da ki yi kar ki yi anfani da abinda na aikata a baya ki yi kokarin gyara naki kema rayuwar idan ransa ya bace ki yi shiru, idan naki ya baci ki tausashi zuciyar ki kar ranki ya bace ki ringa sakin magangannun da ba da.a a ciki

Kanta kawai take gyadawa bata kuma cewa komai ba

Aba ya saki murmushi, ya juya a hankali ya koma dan samo masu koda kosai ne su ci domin kuwa coco sai dai na gobe in da rai,
Yana alfahari da Mariamarsa, yana jin wani irin kuzari har daga kai yake shima ya fito magidanci, matarsa na shayin bata mata domin *Indalahi*


Sai wajen karfe biyar na yama Sudais ya yi salama,

Rauda dake tuka tuwo ta mike tana amsawa kafin ta rage idacen murhun dan kar ya kone ta tako a hankali jikinta du a mace haka ta wuni domin mama batai kasa da gwuiwa ba wuni ta yi tana kara kusantata da ni.imar aure harda yan dabaru da karin jadadawar hakuri shi zai sa ta ci riba

Kallonsa take tamkar ta ga sabuwar halita, a hankali tamkar gidansu ya karasa ya dauko hijabinta ya saka mata, cikin nutsuwa ya kamo hannunta ya ce" *Mata* shiga daga ciki ina zuwa

Juyawa ta yi ta shige ciki bisa umarninsa , shi kuwa ya yiwa samir bip suka shiga shigowa da abinda ya zo da shi dan cin yau kawai






More cmment more pgπŸ˜‰

*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




5⃣0⃣



Page din ki ne *MADAME DAKKWARO* πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“


( *Walahi na tsani sticker, idan kina da damar yi min comment ki yi min plz idan kuwa ba dama ba laifi aman kar ki yi yunkurin sakoni a gaba da na yi typingπŸ˜‰* )


Kallon kayan kawai mama take, kayan abinci ne na cikin carton carton, ga su jus da chocolate
Ita kanta Rauda zuciyarta ta cika da murnar hakan duda ta san hakan ba komai bane a wajensa aman kam tana tare da farin cikin yau mama da aba zasu more da kayan marmari

Haba haba kai kuwa, kayan nan mu je ina da su? Gashi irin na sakawa a frij ne idan ba.a saka ba suna iya lalacewa? Aa ko malan ya dawo ya tarar da abin nan kuma na karba zai saba min ne aa ya dawo su kwashe ka yi hakuri
Mama ta fada tana ta mamakin wannan abin

Sudais ya ji wani abu ya darsun masa a zuciyarsa na kaunar datijuwar wato mahaifiyar abin kaunar sa, aa wai ita ce ko me ya sameta?

Lumshe idannuwansa ya yi bayan lura da ya yi Raufa sai sakin murmushi take , ya ce" mama daman d'a na yiwa iyayensa alkhairi su maido? Ko dai ni din ne ba.a haihuwar da ni? Ya karashe yana shagwabe fuskarsa sosai irin na yara kannanuwan nan

Kunya ce ta kama mama, Rauda kuwa ta zaro ido tana kallon sa ta ce" lah Sire menene haka wai kamar wani baby?

Mama ta zaro ido ta kallota ta ce" ke? Ya ishe ki haka bar shi ya yi bacinsa ai mamansa ya yiwa,

Murmushi ya saki kafin yake yo mata gwalo ita kuwa ta yi gagawar rufe idannuwanta da hannunta tana murmushi wai ta ji kunya

Maama ta yi murmushi kawai ta kawar da kanta, ita soma take ta gudu domin ta lura mijin Rauda ba ya jin kunyar yin wani abin

Suna haka Aba ya dawo kafin suke mikewa dan tafiya
Aba kansa fadan yawan kayan ya yi ya ce sam baya son irin haka ya je ya rike masa yarsa da kirki kadai ya isa ya saka shi farin ciki har karshen rayuwarsa , sannan ya shiga yi masu nasiha kan zaman tare da hakuri ya dora da cewa" idan rai ya baci hankali ke nemo shi, sannan ya zama wajibi ku sani zaman tare na dorewa ne idan ana tataunawa , koda wani abin ya faru tsakanin ku ku yi kokarin gannin kun tatauna a tsakanin ku da yardar Allah zaku samu hanyar samun lumana a tsakannin ku

Sosai Sudais ya ringa jin wata nutsuwa tare da sirikan nansa harma ya dora ayar tambaya a irin kallon da ya yiwa mama da farko (shiryuwa ta yi Sudais)


Shagwagwabe fuska Rauda ta yi kafin take fashewa da kuka tana kallon iyayen nata, tafiya zata kuma yi ta bar su? Kai ina iyaye dadi ne da su komai dadin da kake ciki nesa da su ragage ne (annata😟😟😟😟😭)

Sai da Aba ya yi rarashi kafin take yin shiru mama kuwa hararta kawai take kafin ta girgiza kai, kai Rauda ba wayo

Har sun kama hanya ta dawo murya a raunane gannin har dare ya yi ta ce" mama, Aba wai ina aunty ne? Na yi tunanin ko tana makaranta gashi kuma har yama na yi bata shigo ba? Ko har dare suke kaiwa?

Mama ta kalli Aba , Aba ya kale ta , ta kikifta ido ta ce" ke, ki je mana yana jiran ki zaki dauko wani zance kuma?


Rauda ta yi tsaye tana kallon su, du sun dan daburce ba kamar mama da ta shiga sosa hannunta na hagu tana dan zaro ido , takan yi haka idan ta daburcewa wani abin

Matso su Rauda ta yi da kyau ta ce" me ke faruwa?

Mama ta ce" ba nace ki tafi ba?

Malan ya mika hannunsa ya kamo na Rauda ya ja ta wajen kofa, daidai soro suka tsaya ya kaleta da kyau ya ce" ta zabi tafiya ta bar mahaifanta kan dalilinta, ta yi mumunan fushi da mu ta bar mu

Cike da tashin hankali Rauda ta ce" Aba, ta bar ku? Ta je ina?

Aba ya sada kansa ransa na suya, ya dago ya kali sama ya ce" ta shiga Duniya bayan ta fada mana cewar ta barmu ne zata je ta samawa kanta farin ciki

Tashin hankalinta ya karu ta ce" Abana, dalilin an aura min wannan bawan Allah aunty har abin nata ya girmama ta fita daga gidan nan? Ina zata je ? Wajen wa? Wanene yake tare da mu da zuciya daya sama da iyayen mu? Meke damun aunty?

Aba ya ce" rudin shaidan da son zuciya, sannan ko daya ba dalilinki bane, son abin duniya ne ya rufe mata ido, ni ba zan yi mata baku ba ko kadan sai dai adu.ar Allah ya takaita mata wahalar da zata gani a duniya

Rauda da ta fara hawaye mai yawa ta daga kanta tana kallon sararin samaniya , can ta ce" ta yi mata girma, fadinta da abinda ke cikinta sun fi karfin tunaninta, a bar aunty a iya anguwarnan ma ta fi karfinta bale duniya Abana, ya Allah ka shiryar mana ita, ka shirye mu baki daya , Abannna ku yi mata adu.a in sha Allah zan tambaye shi da izinninsa zan gwada nemanta

Rauda, ki je kawai, zata dawo.....ina mai tabatar maki wajen nan da take yiwa kallon kurkuku sai ya zame mata wajen mangarinta, adu.a kam munai mata sosai fa

Haka Rauda ta fito jiki a sanyaye ta nufi mota sai dai yanzu baya ta shiga domin Samir ne ke jan su

Haka suka biya gidan su Humaira sai dai mamanta ta ce ta tafi

Suna zuwa gida Rauda ta bude dan shigewa cikin gida

Bude gefensa ya yi ya kamo hannunta na hagu dake kusa da shi
Samir na gannin hakan ya fice ya yi nisa da su

A hankali ta dawo ta koma cikin motar ta sada kanta domin ta san magana yake son yi da ita

A hankali ya fito ya dawo bayan shima ya shiga ya rufe motar

Shiru kake ji , ita bata dago ba shi kuwa bai yi magana ba ya tsareta da kallo

Jin shirun ya yi yawa ya saka ta dago da kanta ta kai dubanta wajensa , da sauri ta kawar da idannuwanta tana kokarin mayar da kallonta wani gefe

Idan har kika bari hawayen idannuwanki suka kuma sauka kan fuskarki na yi maki alkawarin hukunci mata

Da sauri ta shiga ajiyar zuciya tana hadiye kukanta bata yarda hawayen sun fito ba dan bata san irin hukuncin da zai yi mata ba

Menene? Sudais ya jefo mata tambaya hankalinsa konce tamkar ba abinda ke damunsa

Tana ajiyar zuciyar ta kallo shi, ta ce" ba.....ba komai

Mama kike so? Ya kuma tambayarta tamkar kana tambayar yaro dan jaririn da baya fahimtar yaren ka

Kai ta kara girgiza masa tana hadiye kukanta

A hankali ya furta" ya Allah

Hannunsa ya kai daidai kirjinsa wajen zuciyarsa tana kallonsa kamar yanda yake kallonta, murya a kasa sosai ya ce" ki daina yawan kuka kin ji? Ki sama min natsuwa


Ita kam takan yi mamakinsa idan yana furta ta sama masa natsuwa, wace irin natsuwa kuma? Kukan nata na hana shi natsuwa ko me?
Sai dai bata iya bashi amsa ba ta gyada masa kai kawai ta shiga kokarin fita a motar domin bata da bukatar da ta fi ta je ta yi wanka ta yi alwallah ta yi ta sallah ta yi ta adu.a ko ta samu sauki, ita kam ta cika rauni du ji take wani iri

Hannunsa dake cike da gashi baki sidik ya miko ya kamo nata da kyau ya rike, ya jima a haka kafin ya ce" Freind?

Kallo shi ta yi, Freind kuma? Da wa? Mijin nata ne ke tambayarta zama abokinta? Shi kam yana zo mata da abubuwan mamaki

Eoooooo? Sudais ya furta yana farkar da ita daga tunanin da ta afka

Kallo shi ta yi kafin take bin hannayen su da kallo, hannunta sai ya zama wani dan firit a cikin nasa, shi kam komansa haka ne gabjeje?

Kin aminta na zama Freind din ki? Irin mu zama abokai na ku da kut.....kina fada min damuwar ki farin cikin ki...da sauran su ... nima haka?

Da mamaki ta saki baki tana kallon sa ta ce" kuma mace da namiji abota? Kuma ma kai katoto ne.......😳 shiru ta yi kafin ta kai hannunta ta rufe bakinta da shi

Ido ya zaro ya ce" kai kai kai, ni ne tulelen? Gabjejen? Dankareren?

Ta yi saurin bude idonta ta ce" kai kai kai aa ba haka nace ba sire

Ya yi murmushi ya ce" kin ga ni ne sirin ki, abota idan na yi da ke bai haramta ba, ina son zama abokin ki ne dan rayuwa ya kasance muna taimakekeniyar juna

Rauda ta tsare shi da kallon da bata san ta yi masa ba, sajensa, lebensa, girarsa, dara daran idannuwansa, sai ma idan yana shagwaba tambar karami, murmushi ta sakar masa ta kai dan yatsanta ta ce" mu kula

Shima murmushin ya yi gannin ta dan saki ranta ya mika mata suka kulla kafin yake yi mata salama ta fice tana waiwayensa tana yi masa bye tana murmushi

Samir ne ya dawo yana dariya kasa kasa ya shiga ya tada mota
Juyowa ya yi ya tsare sudais da kallo kafi ya ce" sai ina oga? Ya fada yana sakin murmushi mai sauti

Sudais ya hade rai ya ce" kai dariyar me kake?

Samir ya shiga tatayinsa ya ce" ba komai

Sudais ya ce' mu je zoo

Ke kina da hankali kuwa? Me ke damun kwakwaluwar ki? Mariama tarbiyar da ta baki kennan? Kazar nan guda daya ce sukutum ke daya na bari a falon nan daga na shiga wanka na fito na tarar kin cire fifike guda ki wani ce ba ke bace? Dan ubanki abincin elhaji ne idan ya dawo ya kike so mu kare da shi? Ohke bakin ciki kike yi min ina zaune a gidan daula ina bin mijina ba kamar uwarki da ta raina mijinta ba? Kin taba gannin na dagawa mijina murya? Ko dai so kike ya sake ni ya aure ki ne? Aunty ta karasa tana daga muryarta sosai

Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Aisha ta fada tana dafe gefen fuskarta da aunty ta yayarfa mata mari , ta kallo wajen Sarah ta ce" Sarah ki fada mata, wly ban dauka ba, bani bace , ni da a nan na bar ku na shiga dan yin sallah?

Sarah ta dago daga danna wayar da take ta ce" ah mu kika bari? Kina nufin ni na dauka dan uwarki da ubanki mai datin hula?
Sarah ta fada tana tasowa a mugun harzuke ta nufo Aisha

Hannun da ta ci naman da shi ta manta ta dago dan kaiwa Aisha duka

Aunty ce ta gani ta dan zaro ido, bata kuma cewa komai ba kawai ta juya dan barin wajen ta je ta sake masa wata kazar dan kuwa ta sani ne idab ya ga kazar nan a haka ko wa yayi mata tsaye sai ya ci mata mutunci ya tsigeta sama da kasa ya tsinewa iyayenta

Da Sauri Aisha t kauce ta ce" ke kar ki sake kin ji? An fada maki ni ganga ce?

Sarah ta yi murmushin yan duniya ta ce" aa, ganga fa mai kawo kudi? Ke ai jaka ce mai cinye abincin mutane banza sakara

Aisha ta ce"""""



*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




5⃣1⃣


( *imanin dayanku ba zai tabata ba har sai ya sowa dan uwansa abinda yake sowa kansa........* )




Aisha ta ce" ni ce jaka sarah???

Sarah ta yi mata kallon tsaf ta ja tsaki ta ce" jakinma ya fi ki daraja.....kafin take juyawa tana ta kokarin juya yan shafafun duwawunta


Nan ta bar Aisha ta zauna ta daga kanta sama, rabonta da ta gane kan mutanen nan tunda ta zo zama cikinsu, wai wani mumunan hali ne da ita da ya sa suke yi mata haka ko me? Aman ai ita yar uwarsu ce ko ba komai ance dan uwanka dan uwanka ne ya fi gaban wulakanci

Wannan kennan


Cike da nutsuwa kamar yanda ta saba ta gabatar da salarta , ta jima saman salaya tana adu.a , bata kai ga shafawa ba ta ga ya shigo, direct wajen salayar ya nufo hannunsa dauke da plat

Da ido ta tsare shi har ya zauna ya yi irin zaman makaranta wato ya tankwashe kafafuwansa ya ajiye plat din a tsakiyar su wanda ta bi shi da kallo pizza ce na ciken

Adu.arta ta kai ta shafa wanda ya daga hannunsa ya shafa shima,

Riga ce a jikinsa mai botira sai dai botiran du a bale suke sai fara daga ciki , da wando dan dogo irin na dari ya kame daga can kasa

Yar yukar ya mika mata da cokali mai yatsutsai ya yi mata nuni da ido cewar ta yanko su ci

Karba ta yi ta shiga dan kokarin yankawa aman tana satar kallon sa ta ga shi hankalinsa konce sai wani dan kakauda kai yake dai

Yankawa take tana mika masa yana karba , shima sai ya yanko ya miko mata
Na farko karba ta yi ta kai bakinta, ta sha jin labarin pizzar nan a wajen yayan masu da shi da yan mata yan gayun ajin su , yau gata ga pizza

Harda lumshe ido ta kai bakinta bayan ta yi bisimillah
Dan bude idannuwanta ta fara a hankali, ta ga dai abin ba mai gyarata bane sai ta bude gaba daya
Yatsina fuskarta ta shiga yi tana kallon sa,
Shima ita yake kallo, a ransa yake ayyana ya haka ko dai bata son ta chiken?

Kokarin hadiyewa take, da kyar ta samu ya shige cikinta ta shiga sauke ajiyar zuciya wata na korar wata

Matsowa ya yi ya ce" lafiya? Me kika hadiya a ciki freind?

Kallo shi ta yi, kunya take ta ce masa ba dadi domin bata san a me zai dauki hakan ba, wata zuciyar
Ta ce da ita ke ya fa san wacece ke , ya ga gidan ku, ya dai san ba kudin shinkafa da dawa za.a saka a sayo maki pizza ba dan haka ba wani abin kunya a dan kin kasa ci

Fuskarta ta kara yatsinawa ta ce" ba dadi

Ido ya zaro ya ce" ba dadi fa? Ko kin fi son na jan nama?

Rauda ta kawar da kanta ta ce" ni abin ne, wani yami yami, manda manda, ni fa ban san me ake so na ji a cikinsa ba

Ido ya zaro, maimakun ta bashi dariya sai ya ji wani sanyi a ransa, bata da kiriniya ya tabata da tana da shi da ko bata ci a wajen kawaye ba zata saka saurayi ya sayo mata

A hankali ya shiga fitar mata da dan nama naman wajen da ya fi naman , ya hada da dan cream din kadan ya yo wajen bakinta,
Ido cikin ido ya ce" ha

Idannuwanta ta shiga kikiftawa ta ki bude bakin domin itafa bata ji dadin abin ba , kai yan gayu suna bata mamaki wani lokacin su kansu suna cin abin ne kawai dan dai su nuna sun isa ko dan vitamine ko meye ma su damiwarsu wai

Make kafadarta ta yi tana turo bakinta

Murmushi ya yi mata har hakoransa suka bayana ya ce" kin ga, ki yarda da ni, ki taba wannan idan ba dadi sai a hakura

Yawu ta hadiye ta bude bakinta da kyar, ya samu ya saka mata yana kallon ta,
Dan taunawa ta fara, nan ta ji wannan din kuma da dan dadi ba kamar inda ta cira dazu bane, sai dai kanshin nan dai nasa ne ita kuwa bai wani yi mata ba,

Da kyar dai suka gama cin abincin ya fitar da game a wayarsa ya saka masu lido suka koma bakin bed suka shiga bugawa

Nan fa gardama ke sarkewa har Rauda ta fada kansa tana titirjewa ita bata yarda ba yana mayar da ita gida da gangan a sake

A haka dai suka zauna har dare ya yi sosai wajen karfe biyu suna shirme basu ankara na sai da ta fara jin idannuwanta sun yi mata nauyi ta kalli agogon dakin nata

Ido ta zaro ta kallo shi ta nuna masa

Shi kansa ya yi mamaki, to ya aka yi lokaci ya yo gudu haka ?

Fuska ya shagwabe ya ce" to ki raka ni, ni tsoro nake ji

Rauda ta zaro ido ta bi shi da kallo ta kalli kanta, bata san lokacin da ta saki dariya mai dan sauti kadan ba, rana yi tana nuna kanta kafin kuma ta nuna shi

Shima dariyar ya yi ya ce" kin ga ki daina gannin girman nan nawa bani da nauyi fa, zo ki ga ki goya ni

Rauda ta kara yin dariya ta ce" idan na goya ka, ina mai tabatar maka na tashi a aiki, tap rabewa zan gida biyu

Shi kam dariyar nata ke burge shi, baya jim zai iya fita ya barta a haka sai dai baya so ta kawo wani abin cikin ranta dan haka ya mike ya dafa kanta ya yi mata adu.a tamkar baby ya shafa mata a hankali yana kallon kwayan idannuwanta ya karasa har saman goshinta ya yi mata kiss da lebensa ya sakar mata muah ya dan shafa gashin kanta ya cafke hannunsa da nata ya ce" ki huta *MATA*

hannunta ta daga masa a hankali itama tanai masa bye, sai dai sam bata so ya fita a wannan tsohon daren duda ta san was yake mata sai dai ta mike a hankali bayan ya dan jima da fita ta bi baya dan gannin ya tafi? Sai dai ba fita zata yi ba bakinta daga nan bakin kofarta

Sudais na fitowa ya ga Humaira zaune saman kujera ta dafe kanta da hannayent bibiyu

A hankali ya karasa wajenta ya tabata ya ce" Humaira lafiya? Me kike har yanzu a waje?

Dago da kanta ta yi da idannuwanta da suka canja launi ta sauke saman kansa, , ranta bace ta ce" dakinta? Me kake a dakinta har wannan lokacin? Samir ya zo yayi ta jira baka fito ba, ka bar wayoyinka a dakin ka, sannan da ka shiga ka saka kofar a blinder yanda ba zaku ji mai kiranku ba koda bugawa za.a yi? Wannan wani irin cin fuska ne da cin zalin? Ka gama da ganga zaka yar da ita ne? Na zama kaya ne har zaka zubar da ni a kondon shara? Me na yi maka haka? Ta karashe tana fashewa da kuka, ta ci gaba da fadin" baka taba fin minti ashirin a dakina ba, baka taba taraya da ni a dakina ba, aman ka duba ka ga

A hankali Sudais ya kai hannunsa zai tabata domin a gaskiya takan bashi tausayi wani lokacin, Humaira ta cika daukan abu da zafi, kiahinta ya yi yawa, haka fa da ran Khalisat har tambayarta take wai idan yana saduwa da itae yake cewa ko irama yakan yi mata shiru ne tamkar

Please Login or Register in order to submit comment