Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

furta" Mata, ban so dawowa nigeria nan kusa ba aman bani da zabin da ya huce na zo dan na ga alamar kin rantse sai kin yiwa wani aiki ......

Farin ciki na neman kauracewa yan matan nan biyu da mahaifansu dan kuwa damuwar Aisha ta tsananta wanda take jin haushin kanwarta dan ta nuna ta daina zurfafa soyaya da kiyaya dan ba kyau hakan ya saka bata sakewa kowa tana fushi da kowa, hakan ya shafi walwalar iyayen

Zaune take tana kada miyar yauki, gefenta radionta ne tana sauraron shirin mu tatauna, ana tsaka da shirin aka dakatar dan gabatar da sanarwa mai mahinmanci wanda Farida Alkali ke gabatar da
Cike da zazakar muryarta ta fara sanarwar kamar haka" *KANFANIN ABAYA AND GOLD* na *ELHAJ SUDAIS MALALE* suna bada sanarwar neman ma.aikata masu takardun shedar sun karanci kasuwanci daga ranar litinin zuwa asabar za.a rufe dauka bisa albashi naira dubu dari hudu du wata! Allah ya baiwa mai rabo sa.a

Butar dake hannunta ta saki cike da murna, da sauri ta karaso wajen mahaifiyarsu ta ce" mama, kina ji kuwa? Kanfanin Sudais ne

Cike da tausayawa mahaifiyarta ke kallonta ta ce "....






*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*



8⃣



Na: *SAJIDA*





Cike da tausayawa mahaifiyarta ke kalonta, dan kuwa ta fahimci halin da yar tata ke ciki sai adu.a dan a ina zata samu abinda take so? Aishanta mai gayu da kyau du ta rame dalilin tunani da ta sakawa zuciyarta na mutumin da yayi mata zara ta ce" eh kina ji ma.aika zai dauka aman ai ku takardunku basunkai inda ake bukata ba ko?

Rauda dake wanke tufafinta ta ce" mama, ai basu fadi girman takarda ba , ko zuwa muke mai yiwuwa mu dace

Da sauri Aishar dake fushi da Ita ta ce" yawa sister, kin ga gama wankin mu je mu canzo envelop mu fara shiri tun yau idan Aba ya zo ya tofe mana su da adu.a ko Allah ya sa mu dace

Murmushi ta yi har cikin zuciyarta tana son gannin hakoran yayarta tana farin ciki, a ranta ta yi adu.a cewa" Ya Allah wannan soyaya da yar uwata ke yiwa wannan bawa naka kar ka jarabeta da shi, ya Allah idan har mutumin arziki ne mutumin mutunci ne ka karkato da tunaninsa wajen yar uwata ka sa ya ganta da kansa ya sota ya aureta, idan kuwa ba malamuncinta bane Allah ka cire mata wannan zazafar soyaya ka saka mata ta malamuncinta ya ubangiji


Hakan kuwa aka yi, sun yi shiga na mutunci atampa da hijabi har kasa mai hannu , suka shiga adaidaita , idan ka kali fuskokinsu zaka karanci abu biyu ne, Rauda fuskarta na nuna tsantsar zulumi ita kuwa Aisha tsantsar fsrin ciki

A gaskiya Rauda ta sare, hankalinta ya tashi irin yanda ta hango tsaruwar ginnin wannan Kanfani, ko ina camera ne da jami.an tsaro, sannan yan mata tsala tsala sun bayana da samari kowa da takarda a hannunsa na neman aikin nan,
Da wuya ka ga wani a wajen napep ta sauke du yawanci da motocinsu, wasu da mashin dadaya ne Ake ajiyewa a juya mutanen fa da dan yawansu

Da sauri Aisha ta damki hannunta suka zo shiga suka mikawa masu tsaron kofar envelop dinsu sai dai abinda ya basu mamaki mata ne suka duba takardun suka basu suka shige

Tafe suke suna bin hanyar da aka rubuta nan ne wajen daukan ma.aikatan har suka karaso kofar wani gun da suka ga mutane a zazaune layi ne dan haka suma suka bi layin

Sun dan jima a zaune, kusa da wani namiji suke zaune ya ishe su da yawan magana sai ga wata mata ta fito da irin kayan securitie a jikinta ta nufo wajensu

Abin mamaki tana karasowa ta yi nuni da su Rauda ta ce" ku mu je ko?

Kallonta suka yi kafin suke kallon juna, da mamaki suka kuma kallonta da idannuwanta ta yi masu signa kafin ta juya

Da sauri aisha ta damko hannun rauda suka mike suka nufi kofar

Kafin ka shiga sai an caje ka da irin abin nan na caje mutane sai dai abin mamaki waje kawai mutumin ya basu ko kalonsu bai ba suka shige

Gabansu ne ya yanke ya fadi sakamakon gannin tsaruwar wannan waje, cike da tsoro Rauda ta damke hannun Aisha ta fara kokarin janta da su koma domin har ga Allah ita fa ta tsorata da irin dukiyar wajen nan, haba dole a saka tsaro irin haka dan kuwa abin ba na wasa bane

Tirjewa Aisha ta yi ta ki bata goyon bayan su juyan, a hankali ta ce" Rauda ki natsu mana kina ganni mu suke kallo

Dago da idannuwanta ta yi, hakan ne kuwa su suke kallo! Mata ne guda uku .. ba bahausa a ciki, larabawa biyu da baturiya guda

A hankali suka karasa suka mika takardun su wa macen ta farko

Buda takardun ta yi, cike da mamaki ta dago tana kalon su, abin nan na bata mamaki, to aman wa.innan yan matan mai din oga ne da ya umarci a dauke su aiki ko tambaya kar a yi masu?
Angelina da take matsayin mai kula da bangaren gold tana kara tace karkonsu ta kali Basma cikin yaren turanci ta ce" aman suna da kyau yan matan nan, daman a nan kano ma akoy yan mata masu kyau haka?

Kafin ta bata amsa dan ecouteur din dake kunnayensu a markaye wanda aka hada su magana da Sudais ya dauki amon muryarsa cikin wannan maganar nasa marar taushi ya ce" ba abinda na saka ku kennan ba, na saka ku ne ku dauke su ba tare da kun yi masu wani dogon magana ba dan haka ita ramaman nan sosai ku saka ta a matsayin mai kula da harkar takardu ta kawo office dina, ita kuwa dayar ku kaita wajen su Basma

Yana kai aya yayi shiru ransa na tafarfasa ya ji haushin angelina, shi fa a gaskiya idan ya ga abin nasu hauka ne kan *MATA* sai ya dakatar da su aikin nan baya ce masa komai ya kawo gaba daya mata musulmai sannan ya saka tsaro a cikin sun ma domin yanzu duniya ta ki gaskiya mata kansu neman mata suke

Cikin gagawa aka bi umarninsa aka tafi da su kowace aka nuna mata wajen da zatana aiki sannan aka fada masu tun gobe zasu fara....

Farin cikin da suka shiga ya hana su tsayuwa mamakin wannan sa.a tasu ta yau harma su dasa ayar tambaya a hakan, aman abinda suka sani shine Allah ne ya tsaya masu ko tambayoyi ba.ai masu ba du kuwa da irin kannantar takardunsu bayan wa.inda ke tare da su du sun fi su da yannayin girman takardu da komai

Da matukar farin ciki suka dawo gida, da gudu suka shige suna masu shaidawa mahaifiyarsu cewar an dace

Cike da farin ciki ta rungume su tana yiwa Allah godiya, har ta hangota ta warke duda basu sani ba aikin mai jimawa ne ko na dan lokaci, ita kam tana fatan mai jimawar ne

Yana ajiye wayar ya kashe computersa, ya jingina da kujerar office dinsa yana sauke ajiyar zuciya, tunani ya afka na irin taurin kan *Mata*, a fili ya Furta" *YA ALLAH KA SA TA FURTAN KALMAR SO , ITA KAM BA ZAN WULAKANTATA BA ZAN KARBI SOYAYARTA DA GAGAWA, ZAN ADANNATA A MUHALIN DA SOYAYAR WATA BATA TABA SHIGA BA, MATA KODA BAKI IYA GIRKI BA NI INA SONKI A HAKA SAI DAI BA ZAN TABA IYA FURTA MAKI BA DOMIN HAKAN BAYA CIKIN TSARIN RAYUWANA*

yana gama tunaninsa ya mike ya fito ya shiga acenseur ya sauko kasa , a kafa ya shiga takawa yana mai jinsa cikin nishadi domin ko ba komai ya san ya karakiusanto kansa da *Mata*

Yana shiga vila dinsa ya dauki mashin cikin mashinan masu tsaron kofar gidansa ya hau ya karasa domin ko a saudiya ginnin gidan Sudais ba na wassan yaro bane

Khairat ce zaune saman kujera irin mai juyawar nan tana shan madara da ta yiwa kauri kitif

Salama yayi mata, ta juyo tana amsawa ta saki murmushin da ya saka kumatunta girgiza domin khairat yar lukuta ce sosai, ga zaman guri daya ga cin dadi ga gari mai ni.ima mai tarin albarka hakan ya kara mata gudunmuwa wajen kara busuwa jikinta ya kara yin luwaiwai

Yana karasowa ta mike ta karaso wajensa ta rungume shi ta ce" welcom habibi!

Murmushi ya saki ya ja hancinta ya ce" Khairat, zabin Mahaifiyata, Allah dayib

Itama murmushin ta yi ta bi bayansa suka nufi dakinsa domin yau aikinta ne ta taimaka masa ya shirya suka fito dan cin abincin rana duda har yama ta yi

Suna gama cin abinci masu aiki suka kwashe suka shiga kimtsa wahen su kuwa suka koma baban falon gidan suka zauna suka shiga hira

Humaira sarkin kishi, kai zuciyarta take nesa duda ita a ganninta ta fi Khairat komai aman tana jin haushi idan ta ga baya banbance tsakaninsu

Can cikin hira ya ce" ina son zan shiga nigeria cikin satin nan na gaba, na baku zabi wace take son zuwa gannin gida sai mu tafi domin ina kyautata zaton wannan karon zan dan jima a nigeria

Cike da mamaki Humaira ke kallonsa, a saninta Sudais baya son zaman nigeria dan kuwa al.adun mutanen saudiya ta daye zuciyarsa aman abin mamaki a wannan shekarar yana yawan maganar nigeria ko dai kuma hankalinsa ya karkata can ne? Kai aman ita gaskiya ba zata so hakan ba dan kuwa kasar nan ita ce daidai da wajen ta yi rayuwa
A hankali ta ce" aa, nigeria da alama ta fara kwato incinta domin tana son dawo da elhajin kasarta cikinta ni ko dai can zamu koma da zama ne

Sudais ya dan jima yana auna maganar Humaira, lale gaskiya fa ta fada..., kamar yana kara kaunar kasarsa fiye da da, kalonta yayi ya ce" ai ba abin mamaki bane dan dan kasa ya koma kasarsa, may be daman bai tsaya ya tantance dadin kasar nasa da wata kasar ba

Tamkar ba ta bakinsa maganar ta fito ba, inda Ya juya wajen Khairath ya shafa cikinta dake ture tamkar mai ciki ya ce" Khairath, ko dai na yi ajiya a nan ne?

Khairath ta dago tana kalonsa sannan ta bi hannunsa sa kalo ta kakalo murmushi domin kuwa ita kanta tana kokonton ko ciki ne da ita dan kuwa ta cika kwadayi kwanakin nan sannan bata ga period dinta ba

Cike da nuna farin ciki ta ce" ya Allah amen ya rab

Da sauri Humaira ta kaleta, bata san lokacin da ta mike ba ta yi bangarenta kar zuciyarta ta buga
(Wannaan kennan)


Konci tashi yau har satin su Rauda bibiyu da fara aiki a karkashin kampanin Abaya and Gold na Haj Sudais,

Yau ya kama litinin kamar kulun sun shirya da wuri, yau koko kawai suka samu da mama ta karbo a gidan lami bata riga ta fara tuyar kosan ba

Da gagawa suka tari bos domin kudin wajensu ba zai ishe su zuwa a napep ba
Suna zuwa wajen magama hudu bos ta sauke su suka taka a kafa har wajen aikinsu suna tafe suna dan zantawa

Wannan kalon kan nasa ya fi a kirga da ya yi, domin kuwa jalabiyar da ya saka bugagiyar jalabiya ce mai shegen tsada ruwan fara kar, ya daura agogo ruwan ash color yA saka safa ash color ya saka takalminsa sau ciki

A hankali ya saka dan macaji ya gyara kansa ya nadidiye shi ya dauko hiraminsa ya dora shi

Yana gamawa balarabe sak ya bayana a gaban mirrow din, a hankali ya lumshe idannuwansa yana mai rokon allah allah ya sa yana haduwa da *MATA* komai ya zo masa da sauki dan kuwa a irin yanda yake jinta a zuciyarsa kamar ya cire ya huta, daman haka soyayar yake?



To fa wacece *MAYAR* NAN? Yanda yake hasashe zai samu ne?





*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*



9⃣



Na: *SAJIDA*




Murmushi ya kuma saki ya fito ya zauna ya rubutawa matansa chek, domin kowace ta roki arzikin zuwa ta ga iyayenta ba zai hana su ba domin shi mutun ne mai adalci

Yana gamawa ya fito kamar yanda ya saba ya shishiga ya gaisar da iyayensa da kakaninsa su hafsa kuwa har sun tafi makaranta dan haka ya zo wajen motocinsa ya shiga suka daga

Tun daga bakin kofa ya ga yanda du suke ta kazar kazar kowa yana aikinsa ba sanya domin kuwa oga na gari shi kuwa baya son wasa

A hankali ya bude motarsa ya fito daga motar ya tsaya yana kallon yanda ma.aikatansa suke gaishe shi ya shiga daga masu hannu dan kuwa idan ya ce amsawa zai yi to fa har yayi.ciwon baki

Cike da iza yake takawa yana kutsawa har ya zo bakin koridor din da zai sada shi da office dinsa
Kamar ba sadauki ba ya ji gabansa ya yanke ya fadi, ajiyar zuciya ya saki dan kuwa ya tabata hakan baya rasa nasaba da dan zai hadu da *MATA* ne

Kofar office din su Basma ya kafawa ido, wato wajen da suke zama wajen da nan suke wuni idan mai son harhar gold ya zo su tafi su nuna masa ya zabi wanda yake so

A hankali ya nufi kofar, du takunsa daya sai gabansa ya fadi dan bai san ko tana wajen ko bata nan ba,
Har ya dora hannunsa a kan kofar ya ja ya tsaya, ya jinginar da kansa a jikin kofar yana sauraron yanda zuciyarsa ke bugawa tamkar ta dira ta fito daga kirjinsa, a hankali ya furta" ya Allah, mai ke shirin faruwa da ni ne? Mai ke damuna ne? Menene hakan ne? Wai zan shiga wajen nan ne dan na ga MACE , macen da bata san me nake ciki ba, yarinyar da nake matsayin uban gidanta a wannan waje, yarinyar da na tabata na girmeta nesa ba kusa ba, na ce mata me? Ni ba taba shiga na yi wajen nan ba idan suka ganni a yanzu ai dole su yiwa kansu tambaya, ya Allah, du na zama wani kala dalilin wannan damuwa tawa🤦🏻‍♂

Da sauri ya sauke hannunsa, ya juyo ya ga guard dinsa na tsaye inda ya barshi da wayoyinsa

Juyawa yayi ya nufi bangaren office dinsa yana mai jin kasala na kara rufe masa ilahirin jikinsa

Yana zuwa guard dinsa ya bude masa kofar glass din dake ta walwali ta sha guga ,
Ajiyar zuciya ya sauke ya lumshe idannuwansa yayi adu.arsa kamar yanda ya saba kafin ya saka kafarsa waje koda dakinsa ne sai yayi adu.a yake shiga

Kafarsa na dama ya saka tare da lumshe ido ya bude tar a kan dadayku manyan ma.aikatansa da du suka juyo suna kalonsa kafin suke fara miko masa gaisuwarsu daya bayan daya yana amsawa hankalinsa konce domin kuwa manyan mutane ne , manyan ma.aikata ne na kasa daban daban da na nigeria du wanda ke wajen nan gagarumin mai ilimi ne dan gayu na bugawa a jarida


Coridor din da zai sada shi da ainahin offishin nasa ya nufa wanda a cikin coridor din office din Aisha da na wani mai suna Abdul majid wanda ke kula da computer wajen

Tunda ya tunkaro wajen yake jin dariya kasa kasa wace ta saka shi daskarewa waje guda, da kyar ya ja numfashinsa ya sauke ajiyar zuciya a zuciyarsa yake fadin ke baki isa ba haba, ta ya ke macen ki ringa saka ni faduwar gaba bayan nine namijin ni ya dace na ringa saka ki jin hakan *MATA* ,

Cijewa yayi ya gyara tsayuwarsa ya doshi office dinsa kai tsaye sai dai me yana karasowa suna fitowa

Ja yayi ya tsaya ya shiga yiwa zuciyarsa fada cewa" ki nutsu ki kama kanki, kar ki manta sai mata ta fara furta maki kalmar so kafin ki karbeta, karki manta ke din ta daban ce, ke din ba zaki iya tunkarar wa.innan yan matan zamanin masu halayar rashin kamun kai ki furta masu kalmar so ba dan kwatakwata hakan bai dace da ke ba, ki nutsu fa!

Duda yanda yake gayato jarumta ji yayi yana neman gazawa, lumfashinsa na neman gagararsa
A hankali ya kai hannunsa na dama ya bale boturan da ya saka na wuyansa wanda yake ji kamar ya shake masa wuya a yanzu ya saka hannun yana dan shafa wuyan nasa

Da sauri guard din nasa ya matso cikin harshen turanci ya ce" sir lafiya? ?

Yana kokarin yin magana suka juyo wajensa a tare

Aisha cike da mamaki da farin ciki take kalonsa da wani irin yannayi mai wuyar fasara,
Alkawarin da ta yiwa kanta, abinda ta jima tana jira kennan, wannan rana ta jima tana tsara yanda take so ta zo mata sannan irin abinda zata yi a ranar

Sakin hannun Rauda ta yi wace itama ta yi mutuwar tsaye da gannin ogansu mutumin da ya haukata zuciyar yayarta tsaye a gabansu tamkar a naso shi

Aisha ta daga kafarta tana nufar Sudais, wanda hakan ya hadasa masu faduwar gaba gaba dayansu,
Shi yana mai faduwar gaban ganninsu gashi ga su a karo na uku, Aisha na faduwar gaban abinda ta yi niyar zuwa ta sanar masa wanda ke hanata baci da sukuni, Rauda na faduwar gaban abinda Aisha zata aikata dan karfin hali wa mutumin da ya fi karfinsu wanda hakan na iya sakawa ta jaza masu hasarar aikinsu (idan abin ya tsaya iya aikin ma ai da kyau)

Ja ta yi ta tsaya a gabansa, ta kafeshi da wa.innan idannuwan na mahaifiyarsu masu fizga dan tsananin tsarinsu da girmansu da kyansu, ittafa a yau a yanzu ba sai an jima ba zata amayar masa da sirin dake ranta koda kuwa zai raba gangar jikinta da numfashinta ne

Cikin siriryar muryarta ta ce" welcom *SUDAIS*!

Gabansa ne ya yanke ya fadi da gannin abinda ke shirin faruwa, bai kai karshen tunaninsa ba ta ce" Sudais, *My Sudais* sunana *AISHA AHMAD* ina tsananin farin cikin dawowarka a wannan lokacin, Sudais ba zan iya ci gaba da rike damuwana ba,
Tayi tsai tana sauke ajiyar zuciya ta ci gaba cikin sasarfa ta ce" koda gizo ne kake yi min ba kai bane zan fadawa fatalwanka, Sudais Ka tambayi Rauda, kanwana ce bana iya baci, bana cin abinci bani da sukuni SuDais
Ta kuma kiran sunansa wannan karon cikin sanyin jiki ta ce" *Sudais* wanda yayi daidai da jin bugun zuciyarsa na karuwa

Da sauri ya dago jajayen idannuwansa ya sauke su a fuskarta, ji yake tamkar ya tsayar da ita , ji yake kamar yayi da baya da baya ya koma ya kasance bai bayana a wannan waje a wannan lokaci sannan a gaban *MATA* ba

Katse masa tunaninsa ta yi, ta katse masa lumfashinsa na wucin gadi sanadiyar maganar da ta furta, cike da tabacin abinda take ambata ta ce" *SUDAIS I LOVE U SUDAIS* ka so ni koda bai kai rabin rabin son da nake maka ba, ta hade hannayenta tana kokarin ci gaba da magana
Cike da tashin hankali SuDais ya dora hannayensa biyu a kansa, ji yayi wata irin juwa na neman yarda shi,
Taga taga ya yi ya kusan zubewa da sauri guard dinsa yayi kokarin tare shi yana ambatar subahannalah sai dai Sudais ya daga masa hannu ya dafe bango da hannunsa na hagu
Ji yayi ba zai iya furtawa Aisha komai ba, a daidai wannan lokacin bukatarsa shine ya gansa a gida ya kauracewa kowa da komai ya samu yayi tunani,

Saurin juyawa yayi yana kokarin komawa hanyar da ya fito sai dai kafin ya tabuka wani abin Aisha ta rike masa gefen jalabiyarsa, muryarta na rawa ta ci gaba da magiya kan ya saurareta kar ya tafi ya barta a wannan halin da take ciki dan bata san irin abinda zao iya samunta ba😭


Cikin zafin nama ya juyo ya janye hannunsa kafin ta tantance wani abin ya dauketa da gigitacen marin da ya saka Rauda da Guard dinsa mugun zabura

Cike da tashin hankalo Rauda ta tako da gudugudu ta tare Aisha ta fado jikinta ta riketa sosai sosai ,
Da wani mugun kallon tsana ta dago ta sauke idannuwanta kan fuskarsa wanda ya kusan saka zuciyarsa bugawa dan kuwa da wannan kallon da ta yi masa sai ya gwamace dama mari ta wanka masa

Aisha ta cukuikuye hijabin Rauda ta riko hannun Rauda jikinta na mugun bari, hankalinta a tashe,

Har wata kwallah ce ta tarunma Rauda a idannuwanta, a hankali ta rikw hannun yayar tata murya kasa kasa ta ce" mai ya kai ki kallon wannan mutumin da baya gannin mutuncin wanda ya rabe shi furta masa irin wannan kalma? Aunty ki yi hakuri da wannan soyaya domin bata da anfani

Aisha ta ce" Rauda aa, Rauda ki yi shiru

Shirun kuwa ta yi ta samu da kyar ta kama Aishar suka mike ta kamo hannunta da niyar ratsa ta gefensa su yi tafiyarsu

Idannuwansa ya zaro, domin gaban goshinta gashinta ya fito sosai sanadiyar cukuikuyeta da Aisha ta yi,
A shigowarsa kuwa ya tarar da maza sosai , ba tare da wani dogon tunani ba ya yi gaba da sauri ya fice su yayi waje

Harara rauda ta raka shi da shi sannan ta tsaya tana kara baiwa yar uwarta hakuri


Suna cikin haka Basma ta shigo wajensu , sai ta nuna bata ma san abinda ya faru ba ta ja su cikin office din Aishar, nan ta jawa Rauda hijabinta ya rufe mata gaban goshinta da kyau suka zauna suna tataunawa inda wayarta ta yi ta ringin sai mikewa ta yi ta kara ba tare da ta yi magana ba

Muryarsa a dagule ya ce" bata fito gashinta a fili ba dai ko?

Basma ta amsa sa da " eh na dawo da su office gaba dayansu na rufe masu kansu

Ajiyar zuciya ya sauke ya datse kiran ya kurawa hanya ido inda direba ya sake baiwa motar wuta

A hankali ya ce" Ya Rab, ba itaba, Allahna ba itaba, *MATA* dan me kina tsaye kina kalo hakan ya faru? Mai ya sa baki hana faruwan hakan ba,

Idannuwansa yayi gagawar rufewa dan a lokacin hararar tsanar da ta jefo masa ta kuma fado masa a idannuwansa , da sauri ya dafe kansa yana ta maimaita innalilahi wa.ina ilaihi raj.une.......................



Comment ko?🤧



*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*



1⃣0⃣



Na: *SAJIDA*


Haba sis ba zan dawo ba, ba zan dawo ba aikin nan mun bar shi daga yau ! Rauda ke fada cike da bacin rai da kunyar abinda yar uwarta ta aikata yanzun

Rauda Ta ci gaba da fadin" a matsayinki na mace aunty, mace da aka sani da kunya da jan aji, mace da aka sani da tarbiya da wayo da dabara, haka kawai ki tarbi gaban wannan garjejen katon ki furta masa kalmar so? Aunty ko mazan a yanzu sun daina irin yanda kika yi, su kan yi dabara ne su jewa mutun ta inda zasu samu gamsashiyar amsa ba wai kawai daga shigowarsa ki tare shi ki furta masa kalamai haka sannan ki yi tunanin zai saurareki, kin ga mu yi tafiyarmu sannan mu yi hakuri da aikin da karatunma gaba daya aunty dan kuwa koda bamu yi tafiyarmu ba shi zai kore mu ne!

Da mamakinta Aisha sai ta saki murmushi harda dan sautin dariyarta mai kayatarwa ta ce" lallana, menene? Wannan abin ne ya daga maki hankali kike kai kawo har kike ikirarin mu bar aiki? Idan muka bar aiki ya zamu yi da cikar burikanmu? A ina zaki samo kudin karatun da kike mafarkin yi dan ki talafawa DAD?
Ta dan tsagaita sannan ta dafe daidai zuciyarta ta ce" ni kuwa ta ina nawa mafarkin zai cika na samun muradin zuciyata? Wannan ai ba komai bane lallana, wannan abin da kika gani somin tabi ne, wannan marin da yayi min sister ai farkon sanina ne, sau nawa kika ga an yi haka an ci riba? Na

Please Login or Register in order to submit comment