Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

, itama ya sayota da tsadar gaske sai dai ita ba unique bace akoy irinta a can saudiyar , da ya ga zuciyarsa ta rikice kan sai Rauda ta saka wancen dan yayi adalci itama ya dauko mata wannan aman shine ko ado bata yi masa ya gani ba zata saida.......halayenta kennan mota kanta dan ba wanda zai yi gigin siyan motar da ta fito daga wajen Oga Sudais ne da ta siyar da motocinta ta tabata ba zai barta ba motar hawa ba ,...., kuma du wannan hadamar da take bata yi ginin gidan da za.a kala a ce lale wannan tana auren mai shi aa kudaden sun kare a siyen banza siyen wofi... atash du tsadarta bata gani zata cire ne ta saya ga rashin adano idan ta cire daga kanta sai dai ta zubar

Da mugun tsoro Rauda ta zaro ido, da sauri ta cire sarkar daga wuyanta ta zauna bakin gado tana kallo
Tambayar kanta take mene haka? Me ya sa ya yi mata irin wannan kyautar? Sudais ne Rauda..

Da sauri ta mike ta saka hijabinta ta fito ta nufi dakin Hafsat

Hafsat dake zaune tana yanke akaifunta tana kallon wayarta kira ne ta shigowa sai dai ta yi murmushi ta ki dagawa

Whatsupp ya koma ya rubuto" aa fa, Hafsana a rangontawa zuciyana idan ba haka ba na yi sabko gidan nan sai dai oga ya harbe ni, na zo na gan ki Hafsa, ki yi hakuri ko dan dago hannu ne ki yi min kar zafin ya yi min yawa ga na oga ga naki

Murmushi ta saki bayan ta karanta ta ki yi masa replay, a fili ta furta" lalema yayan nawa ne mai hada maka zafi SAMIR?

Dago kanta ta yi tana amsa salamar Rauda wace ta nufota da dan sauri ta zauna tana miko mata sarkar hannunta ta karkata kai tana ciro yan kunayen ta mikawa Hafsat

Idannuwa Hafsat ta zaro, tabas ta san sarkar nan ,
Dago da kanta ta yi ta kali Rauda ta ce" Sis??

Rauda ta samu waje gefen bed din ta zauna itama, murya a dan raunane ta ce" ana kyauta ne wa masoyi, wannan kyauta ne irin na masoya, sis wace ni ? Na tabata dan ya fita a hakina ya bani sarkar nan dan ya baiwa matarsa, ki yi hakuri yayanki ne aman kuma gaskiya ce... da bakinsa ya furtan kalmar kiyaya,! Ke bama wannan ba dalilina na kin komai nasa mai karfin gaske ne

Hafsat da ta saki baki tana kallon Rauda, a ranta take ayanna anya kuwa rauda zata yi wayo? Tana fadin haka wa ni kanwar mijinta🤔,
Kawar da hakan ta yi ta ce" sister kin san da sarkar nan Gold ne?

Zaro ido Rauda ta yi harda mikewa da sauri tana kallon Hafsat

Murmushi Hafsat ta yi ta kamo hannunta ta zaunar da ita kusa da ita sosai,
Ta ce" wani lokacin ba.a anfani da abinda mutun zai fada Rauda, ki kasance babar mace wace ta san kanta mana, a duk lokacin da yaya zai fada maki mumunar kalma ki yi analysen ta, ki koyi karantar abinda ke zuciyarsa koda yana cikin bacin rai ne Rauda, sannan wannan kyauta mijinki ya yi maki, koda bakya sonsa kamar yanda kike ikirari... koda kina da abinda ya hana ki sakewa da shi wanda kika ki fada min ko menene wannan sarkar taki ce, halalinki ne, ki adana abinki

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" Hafsat, a ina na samu damar karantar abinda ke cikin zuciyar mutumin da yayata ke masifar so tamkar ranta? A kansa Aunty Aisha na ikirarin sai ta halaka mutun, a kansa ta yi rantsuwar sai ta bata da kowa!

Ido Hafsat ta zaro, a fili ta furta" What? Kina nufin yayarki ce ke son Yaya?

Rauda ta yi kiftkift da ido, ta kalli hafsat, lalle ta san ba subutar baki ta yi ba domin Hafsat tana nuna mata kauna ta gaskiya, to aman Aisha kuwa yayarta ce fa, sai dai abu guda da take gannin kamar ta yi saurin yi shi ne irin sabo da shakuwar da ta shiga tsakaninsu da Hafsat ko dan bata samu haka da Aisha ba? Kulun Aisha cikin hantararta take da dizgata

Hafsat ce ta kamo hannayenta ta ce" fada min sister, ko baki yarda da ni bane?

Rauda ta sauke ajiyar zuciya ta ce" tun ranar da muka je gidanku wajen birthday aunty ta kamu da matsananciyar kaunar Elhaj Sudais
Du abinda ya shafe shi bata yi masa rikon Wasa, dalilin an canzata a wajen aiki kusa da shi sai da na ga wulakanci iri iri,
Ban san wannan auren da me zan kwatanta maki yanda ya diro min ba a lokacin da na gane cewar shi abanna ya bani a masalaci, walahi abinda ya hana zuciyata tsayawa kawai nisan kwana ne..... na girgiza a ranar , har yanzu ko baci nake abinnan ya fado min a rai nakan farka ne da mugun zazabi da tsorom kowa
Hafsat ki duba ki ganni da wane zan ji? Da Aunty Aisha? Da matarsa? Ko kuwa da shi din kansa wanda ya kiraye ni da matar sadaka , tsohuwar mace, ya furtan cewa ya tsane ni, da wane zan ji?

Hafsat tana sauraronta tana murmushi a kasan zuciyarta, wato ita nan gani take idan ya saka mata soyayarsa a zuciyarta har ta isa ta kwaci kanta, shima yaya wani abu ne da shi ko mai yasa ya furta mata kalmar kiyaya? Sai kuma abinda ya birgeta maganar yaya ta yi mata ciwo dan kuwa gashi har tana nisawa, hannun Rauda ta kara rikewa ta ce" kina nufin dai ya sawake maki ya auri yayarki?

Rauda ta sada kanta ta yi zuru, can ta dago ta ce" eh, ai ba wani abinda ya......... kuma sai ta yi shiru ta janye hannunta tana dan murzawa

Hafsat a ranta ta ayanna kin makaro matar yaya,
A fili kuwa ta ce" Allah ya zaba abinda ya fi alkhairi

Rauda ta cuno bakinta tana amsawa da amin ta mike da niyar tafiya dakinta

Hafsat ta tsayar da ita ta ce" ga sarkar ki

Rauda ta ce" ki ajiye min a wajenki plz

Hafsat ta zaro ido ta girgiza kai ta ce " ko daya, ki je ki ajiye a wajenki na roke ki, sannan ki tabata kin tashi da wuri dan mu kimtsa abubuwan da zamu tafi gidan su Momy kin ga jibi ne adu.ar 40 din Marigayiya

Rauda ta amsa jiki a sanyaye ta juya ta fice a dakin Hafsat

Washe gari ya kama da dan wuri wuri suka shiga kimtsawa Hafsat ta sakawa Rauda kaya kala biyu a jaka da turare da sauransu,
Da yake kwana aka yi ana saukar alkur.ani a can baban gidan an kawo abincin sadaka da aka yi dan haka Hafsat ta ibar masu suka ci suka fara shirin tafiya a lokacin har karfe uku na yama ya yi

Basu ga wulgin Sudais ba domin tun da safe ya tafi can gidan yana tsaye dan gannin an yi komai yanda ya dace tunba fannin malaman da suka zo gari da gari suna bayar da gudunmuwarsu wa wannan marigayiya da ahalinta (masha Allah, kowa halinsa ke binsa)


Karfe biyar na yama suka gama shiryawa, ba wani kwaliya suka yi ba Rauda ta saka dogon hijabinta ja mai hanaye wanda gaban goshin yana da kamar abin dauri ya kama fuskarta ya yi mata kyau sosai
Ba kwaliya a fuskarta ko kwali bata saka ba hakama hafsat suka fito

Direba musa ne ya zo da sauri ya gyara mota yana gaishe su bayan ya karbi jakar kayansu ya saka a bayan mota suka shiga ya ja Hafsat tana jin haushin Humaira ko tace mata ta tafi , kwata kwata bata yi mata magana wai dan tana kula Rauda

Mota na tsayawa Rauda ta riko hannun Hafsat sanadiyar gabanta da ta ji ya yi wata mahaukaciyar faduwa sakamakon ganinsa da ta yi yana tsaye suna gaisawa da wani baban mutun mai cike da kamala

Gabanta yake mugun bugawa bilhaki, sai da Hafsat ta kaleta da kyau tana tambayarta lafiya kafin take kamo adu.a a zuciyarta har ta fara samun nutsuwa

Yar kwallah ce ta ji ta tarun mata a idannuwanta , a hankali ta bude gefenta ta fito ta tardo Hafsat wace ke nanata mata ta kontar da hankalinta ba abinda zai faru

Ta dan nesa da shi suka zo suka gita wanda ya tsareta da kallon nasa mai sakata ta rikice , tambayar kansa yake ina nikaf dinta ne? Shi hijabinma sai yake gannin kamar ya yi mata kadan , kallon dai du na kishin mazan dake dan zirga zirga kan baki da ma.aikatan gidan da kuma yan uwan marigayiyar

Hafsat ce gaba Rauda a bayanta suka yi salama cikin tankamemen falon Momy wanda ya tara kima kiman baki, tun daga kan mutanen momy , jama.ar marigayiya, yan uwa da abokan arzikin., sai kawayen Humaira suma suna zaune suna yar hirarsu,

Dif falon yayi shiru tamkar an ce su juyo du suka juyo suka zubawa su Rauda ido da kallon da ita ba zata iya fasara irin girman kiyayar da take hangowa a idannuwan mafi yawancin mutanen

Momy ce ta mike rai bace ta nufo su ta....





*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




3⃣9⃣


*SAKON GAISUWA GAREKI MA CHERIE TUN DAGA FRANCE WATO HUWAILA, INA JIN DADIN YANDA KIKE BANI KULAWA HAKA, YARKI NA GAISHE DA KE, PAGE DIN NAN NAKI NE KI YI YANDA KIKE SO DA SHI NA AMINIYAR ARZIKI*




Momy na zuwa hannun Rauda ta damka ta jata ta nufi ciki da ita wanda hakan ya sa da sauri Hafsat ta bi bayansu

Tana shiga dakin Hafsat da ita ta tsayar da ita a nan, kallon tsaf da ake fadi shi Momy ta yiwa Rauda a dan kankanin lokaci kafin take juyawa ta fice a dakin

Rauda sam bata gane abinda ya faru ba, bata iya gaishe da matar ba har ta fita sai da Hafsat ta kama hannunta ta zaunar da ita gefen bed dinta wanda yake gyare tamkar tana gidan ,
Ajiyar zuciya ta sauke kafin take cewa" wannan itace mahaifiyarmu Rauda

Tamkar ta daki idannuwan Rauda irin yanda ta kwalalo su cike da tsoro

Murmushi Hafsat ta yi, ta ce" ki tafi da momy tamkar yanda zaki tafi da mamanki, momy mace ce mai saukin hali ga wanda ya dauketa da mahinmanci, tana da saurin hawa sannan tana da saurin sauka, ki dauki momy da mahinmanci ki kusanta kanki da ita na tabatar maki zaki ji dadinta fiye da tunaninki

Da kai Rauda ke amsawa Hafsat, har ta gama yi mata magana da sakata a hanyar da zata samu sasauci wajen mamansu,

Bayan ta gama ta mike tana mai cewa " ina zuwa

Ficewa Hafsat ta yi ta baya ta bula tsakar gida , nan ta tarar da Yayanta yana ta harkokinsa yana kara karban gaisuwa
Gannin Hafsat ta tsaya daga nesa sosai sannan ta tsare shi da ido ya tabatar masa da tana son yin magana da shi dan haka ya samu ya sulube a hankali ya nufo wajenta

Yana zuwa ba tare da ya jira ta fara magana ba ya ce" ina take? Me take? Ya momy ta karbeta?

Hafsat ta yi murmushi ta ce" tana dakina yaya

Daga haka bata kara komai ba ta yi gaba tana fadin bara na samo mata wani abin motsa baki

Ya dan jima a tsaye kafin yake daga kafarsa ya nufi dakin hafsat

Har yanzu tana zaune inda Hafsat ta barta aman ta tsurawa waje daya ido

A hankali ya turo kofar ya shigo wanda hakan ya sa ta dago dan gannin ko waye

Gabanta ne ya fadi ta yi saurin zamowa kasa kanta a kasa murya na dan rawa ta ce" iiiiiina kwana sire

Bai amsata ba haka ya taho har kusa da ita ya duka ya kama kafadunta da kyau ya mikar da ita ya yi masu masauki gefen bed din wanda take kara yin kasa da kanta cike da tsoronsa
Da kyau ya riketa a bakin bed din kafin murya can kasa ya ce" har yanzu Sire din nake? Bama wannan ba wa ya baki izinnin fitowa da hijabi mai color din da zai kara haskaka fatar ki?

Da dan mamaki ta dago ta zuba masa ido, shi kuwa ya dage mata gira guda wanda hakan ya saka ta ji mugun nauyi ta sada kanta da sauri
So take ta saka dan tazara a tsakaninsu aman fir ya riketa ya ki bata damar hakan

Hafsat ce ta shigo da salama wanda ta ja da sauri zata juya Sudais yayi kiranta

Dawowa ta yi kanta a kasa ya yi mata nuni da ta ajiye kofi mai dauke da shayi

Tana ajiyewa ta juya tana dariya a kasan zuciyar tana taya yayanta adu.ar dacewa da samun soyayar abinda yake so

Dauko shayin yayi, ya kai bakinsa ya surba dan jin zafin,
Murmushi ya yi ya dago habar Rauda ya saka idauuwansa cikin nata, du yanda ta so karta kale shi abin ya gagara haka ta tsinci idannuwanta a cikin nasa, ji tamkar tana iyo ne a cikin idannuwansa sannan wata kwala da take gani a konce a cikin idannuwan nasa su suka saka nata sukai mata nauyi
Lebensa ya motsa a hankali wanda ta yi imanin da bata tsare shi da mugun kallo haka ba da ba zata ji abinda yake fada ba
A hankali ya ce" Ha bakinki ki sha shayin nan kar ki bar mana cikinmu da yinwa

Bata iya musa masa ko yinkurin kuma kwace kanta ba, saima ji ta yi bakinta ya buda ya karbi shayin da ya miko mata sai dai ji ta yi ya mata zafi

Da sauri ta dawo a hayacinta ta shiga hura lebenta da har ya danyi ja na wahala

Da sauri ya dago habarta ya matse mata waje sosai , da bakinsa yake hura mata leben nata wanda har ya fita nuna damuwa
Shi kansa bai san ta ina ba, bai yi masa shawara ba sai gani yayi harshensa ya bi umarnin zuciyarsa , wato ya ciro jarshensa ya kai kan leben Rauda cikin nutsuwa ya shiga lashe wajen da ya kone

Idannuwa ta zaro, ta yi wata irin dan ja da baya wanda ya farkar da shi

Shi da kansa sai da ya ji dan nauyi kadan wanda bai taba ji dan kawai ya dan yi irin haka ba

A hankali ya dan raba jikinsa da nata ya tatara mata hijabinta ya kontar da ita saman bed din,
Kafafuwanta ya dago ya dora mata su comfortable

Dan dukawa yayi sosai kusa da kanta yana dan shafa gaban goshinta wanda hijabin ya dan zame, sabon salon rage muryar da ya samu ne ya yi anfani da ita wajen cewa" ni fa ake tatali ba ni ke tatalin mata ba wife,
Ki huta

Yana gama fada ya mike ya fice ya bar Rauda da gajiya tamkar ta yi aiki, da mugun kasala da wani irin yannayi


A nan Rauda ta tare, sallah kawai ke tashinta tana yi ta dawo ta afka duniyar tunani har dare yayi sosai

Asuba allhairi amaryar Sudais

Washe gari, da asusuba Rauda ta shirya ta saka doguwar abayarta ta.nemi Hafsat da ta kaita wajen momy

Rakata Hafsat ta yi ta shiga da salama
Momy dake zaune tana adu.a ta shafa ta dago tana amsa su

Har kasa Rauda ta duka kanta a kasa ta ce" barka da asuba momy

Momy ta amsata ba laifi

Rauda mikewa ta yi gabanta na dan faduwa gannin momy zata ninke salaya ta karasa ta dan duka ta karba ta ninke ta ajiye ta dan duka ta ce" a fito lafiya momy

Da ido momy ta rakata, ajiyar zuciya ta sauke ta shiga shiryawa



Mama yaune Adu.ar arba.in din matarsa, na tabata zan same shi a can kin ga sai na jefi tsuntsu biyu da dutse guda na ga matar da aka ce yar gidan sarauta ce ya auro sannan na ganshi na kuma shigar da kaina, sarah kawai nake jira ta zo mu fice gashi har karfe goma ta yi bata zo ba

Kai kawai mama ta girgiza ta ci gaba da tsince shinkafarta ta hausa bata iya cewa Aisha kanzil ba

Tana nan zaune sai ga hon din Sarah , da sauri Aisha ta tashi ta dauko gyalenta ta yafa tana fadin sai na dawo mama

Murya a sanyaye Mama ta amsata da Allah ya tsare

Tafe suke suna hirarsu ta yanda zata tunkari Elhaj Sudais , sannan su ga amaryarsa dan su san da wa zasu yi kishi

Daga kofa suka ajiye motarsu domin du an hana shiga da mota kowama idan ya zo ajiyewa yake a kofa

Cike da rangwada suke takawa suna kutsawa wanda direct Aisha ta yiwa Sarah jagora bangaren Momy domin wancen zuwan da suka yi sun hadace wajen

Zaune su Rauda suke tare da Hafsat da kawayen hafsat daidai lokacin da su Aisha suka shigo cikin falon da yar salamarsu

Irin yanda gaban Rauda ya yanke ya fadi bata san lokacin da ta mike tsaye ba ta dago yatsarta tamkar ta ga wanda ya mutu ya dawo ta......



Page na gaba na tare da cakwakiya, surprise , abin tausayi, bugawar zuciyoyi aman zai zo ne idan kun karfafa comment dinku🙂


*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




4⃣0⃣

*DAN ALLAH A JI KUNYATA KAMAR YANDA NAKE JI, KAWAR DA KAI DA MAYAR DA KAI TAMKAR SAKARAI WANDA BAI SAN YARE BA DAN A ZAUNA LAFIYA NE, THX*







Irin yanda gaban rauda ya yanke ya fadi , bata san lokacin da ta mike tsaye ba ta dago hannunta da yatsarta manuniya tamkar ta ga mamacin da ya dawo, tana kokarin yin magana Humaira da tun zamanta idonta a kanta ta dan juya dan gannin menene? Domin wajen du suna dan kakayatunsu kun dai san taron mata

Bakinta na rawa muryarta can ciki take fadin" auauaunty aunty aunty

Hafsat ta juyo ta ga Rauda a wannan yannayin daidai lokacin da suma suka ganta su Aishar

Cike da mamaki suka nufo da niyar zuwa wajenta
Da sauri Hafsat ta mike ta kama hannunta suka zagaya ta dayan bangaren suka fice a falon hakan da suka yi ya sa su aisha suka bi bayansu

Wajen lambu Hafsat ta nufa da Rauda wanda yake bangaren Sudais na da, wajen da yakan je domin hutu, ko yayi tunani mai zurfi wajen a daidai lokacin suna tsaye da Samir yana bashi wasu takardun da zai je ya kai sanadiyar kiran gagawa da akai masa kuma yana jin nauyin datijom domin takardun wasu filaye ne manya manya da ya daga dan inda suke ba waje ne mai kyau ba gwomnati ta shiga

Sauri sauri Hafsat ke jan rauda da karfi domin du jikinta ya saka ta wani firgice har nadin dan kwalin da ta yi ya konce rabi saman kanta rabi yana reto a jikinta

Suna shiga Hafsat ta kaleta da niyar yin magana muryar AISHA ta katse su,
Aisha ta shigo Sarah na biye a bayanta suma cikin dan hanzari domin wannan ai kanwar Elhaj Sudais ce, ko me ya hadata da Rauda har take taba hannunta haka? Ko dai wani mai aikin su Hafsat ne ya auri Rauda?

Aisha na shigowa ba tare da ta tambayi yar uwarta yaushe rabo ba, lafiyarta da sauransu kawai sai ta bura ta ce" Rauda, me kike a gidan nan ne? Ko dai mijinki a nan gidan yake aiki?

Gaba daya jikin Rauda ya kwashi rawa gannin ga auntynta ga Sarah , da wuya ta iya fitar da kanta, abinka da wanda ya tsorata da sauri ta matso ta kamo hannun Aisha , murya na rawa da alamar kuka ta ce" walahi Aba ne ya hada Aunty, walahi bana sonsa kamar yanda ya tsane ni, Aunty ki fahimce ni karki yi min muguwar fasara dan Allah, ke dai kin san ko ni wacece, ke zaki iya fadi abinda zan iya da wanda ba zan iya ba, kuma kece shaidar nima ban san da auren ba sai da Aba ya fada mana a tare

Du wannan sambatun maganar da Rauda ke yi Aisha ta tsareta da kallo ne na tausayi, a gaskiya tana tausayawa kanwarta kennan har yanzu basu shirya da mijin nata ba? Shi yasa da ta ganta ta rikice, gaskiya aba ya iya hukunci, han ai Allah ya taimake shi ba ita yayiwa haka ba da ya sha kunya
Aisha ta taba kafadar Rauda ta ce" haba lallana, menene? Har yanzu baki shirya da mijin naki ba?

Rauda gannin Aisha bata fahimci inda ta nufa ba ya sa ta shiga gurgiza kai tamkar ta yi laifi mamanta ta tsareta da bulala, murya a sanyaye ta ce" shi ne fa aunty?

Aisha ta ce" mene? Wai meye ne?
Gannin Rauda ta kasa amsata ta juya wajen sarah dake kallon Rauda da yannayin tambaya, irin shigar jikin Rauda da yannayin fatarta bata nuna a cikin wahala take ba duda ta dan fada aman ba wani can ba, aman wa take aure haka? Ki waye shima ba laifi somin gaskiya sam Rauda bata yi kalar wace ke cikin wahala ba
Kafin Aisha ta yi magana Sarah ta matso tana mai cire gilas din idonta ta ce" kinga Aisha mu yi mu je mu gama abinda ya kawo mu tun kafin yama yayi, domin na ga kanwar nan taki banda jaje ba abinda ta iya

Aisha ta sauke ajiyar zuciya ta kuma kallon Rauda ta ga du a rikice take tamkar ta yi karya, sai zufa ke tsatsafowa daga goshinta, hankalinta ta bata da kyau domin ta sani haka kawai Rauda bata irin haka sai da kwakwaran dalili, muryarta ta kausasa ta ce" menene? Kukan me kike?

Rauda ta kara riko hannun Aisha sa kyau ta ce" ni kaina sai da ya zo na ganshi!!!! Ta karashe tana mai fashewa da kuka

Aisha cikin kufula ta ce" wai wa?

Rauda ta dago da sauri muryarta na rawa ta ce" shishishii......elhajin, Elhaj Sudais din ,..........shi Uban masu gidan

Gaban Aisha ne ke faduwa haka kawai tun kafin ta idasa fahimtar inda ta nufa, ta ce" Elhaj Sudais, wani abin yayi maku ne? Mijinki aiki yake yi masa ko? Wulakantaku yake ko me?

Rauda ta jimke hannun Aisha , cike da sakin baki ta ce" shine Aba ya aura min, Aunty shine mijina! Aman aunty mu dukanmu a rashin sani aka yi, baya sona nima bana sonsa, aunty daman cewa na yi daga an yi adu.ar arba.in din matarsa zan nemi sakina na nemi alfarmar ya aureki, Aunty ni kaina ban san haka zata faru ba sai da na ganshi

Sudais dake tsaye shi da Samir mutuwar tsaye yayi, ba abinda ke dukan kunnensa sai bana sonsa baya so na, soma nake ya sakeni!

Karar mari ne ya saka shi kallo wajen da sauri
Aisha da ta yi mutuwar tsaye ce ta daga hannunta ta wankawa rauda wani kafirin mari mai kausashen kara da zazafen zafi, kafin ta sauke hannunta na dama ta kuma wanka mata da na hagu a dayan gefen, ta cakumi wuyan rigarta wanda har rigar ta dage, sosai ta yi mata shaka wanda Rauda taki kokarin kwatar kanta ta tsaya tamkar wata sauna Aisha na jijigata

Da gudu Hafsat ta zo ta shiga kiciniyar kwatar Rauda , Wanda Aisha ta yi kukan kura ta hankadasu gaba dayansu
Rauda da kwatakwata ba laka a jikinta ta je zube nan Hafsat kuwa ta yi tagataga zata zube

Please Login or Register in order to submit comment