Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalanshi bace ma"

" dallah zauna" Mommy tace tana jan hannun Fatty

Zama tayi tana wani kwalo idanu

"Zuwa fa tayi har bedroom tacemin wai ABDULNASEER yazo, bata fad'amin tare suke bah sabida ita Munafuka ce sai shine yake fad'amin"

Sauke ajiyan zuciya Fatty tayi kana tace" yanxo haka ganinshi tayi a hanya tace yadawo da ita, kinsan dai bazaice yana santa ba, inma ita sanshi takeyi bah kulata zaiyi ba dan koni ma bawani sakemin yake sosai bah kin dai san komai Mommy "


"Hakane zata aika taga batada saurayi shine wanda kike mu'amula da shi watou ta shige masa"

"Ehh mana ai manufar ta kenan"

"Toh k'aryanta gobe gobe zani gidan Ummun nasanar da ita nabama yarona kee, d'an nafiso kiyi aure inda zaki huta kaman ni ke harma kifini"

Wani smiling Fatty tayi wanda har saida dimple d'in dole yafito wanda ban t'abaganinta da shii ba, rugume mommy tayi sosai kana tace"mommy insha Allah ai munyi kud'u mungama tin daka kan yaya Sulaiman har Afifah Wallahi nan gama ma sai kinfi haka, kin san dai yanda akeji engineers suke ai sa a ranki kawai ma muyi kud'i sosai, ita kuma Munafukar tana ganin tayi abinci sai ta k'are a shago"

"Yauwa aini nasan duk yarana mai haifi fak'iri ba, ita kuma AFRAH ai gadon tsiya tayi d'an har ubansu yamutu yana k'arkashin Ubanku ne, so a haka zasu k'are daka ita har Abdulrahim din, aniyarsu tabisu munrika mayi masu nisa"

"Yanzu sai gobe zakije wajen Ummun ko Mommy? "

"Insha Allahu za'ayita ta k'are ba"

"Toh Allah kaimu goben lfya"

"Ameenn Ameen"

"Mommy dakika kira yaya Sulaiman maiyace maki wai? "

"Bai ce suna soyayya ba, nidai nayi warning d'inshii d'an bazan yadda da wani Auran zumicin iskanci ba, yaro ba yafi k'arfinta wallahi"


"Dama Mommy ina wata AFRAH ina yaya Sulaiman ma?? AFRAH mai abinci da aiki a LAB wai zata bud'e restaurant nan gaba injita"ta k'arasa maganan tana wani d'an iskan dariya


"Da kud'in Uban wa zata bud'e restaurant d'in?"mommy tace tana b'ata fuska


"Ina zansani mata, mommy keda kikesan girkinta sai kita siya"ta karasa maganan tana daria sosai

"Ohhhh ni Bilkisu Allah kareni, nan da shekara 3 ai duk muyi nisa"

"Wallahi kuwa, sai aita fama da shagon abinci"


hira sukaitayi duk dai zagin AFARAH da duk wani masoyinta sukeyi gajiya nayi na basu waje.





AFRAH kam waya suka sha da ABDULNASEER abinta a bedroom d'insu batasan ma su Mommy nayi ba.


Bayan ta gama wayan karatu tayi kasancewar sunada test gobe, ko a porlor ma itada AFIFAH keta hiransu Mommy da Fatty tsaki da harare harare suketayi ganin haka yasa tayi ma Mommy sai da safe tayi bedroom d'insu da harara Farty tabita har tabar parlorn.







Mommy taso zuwa wajen Ummu yau amma kuma babu hali d'an Daddy yayi waya yana hanya babu yanda ta iya hakanan ta hakura da zuwa sai k"in Ummun tayi ta saidamata indai Daddynsu ya koma zatazo

Babu yanda ta ita hakanan ta k'ira AFRAH tadawo gida da wuri Daddynsu zai dawo tazo tayi girki, d'an tasan ko sama da k'asa xata had'e Fatty bazatayi ba, toh mai ma ta iya? Daka taci sai nayi kallo taje gidan friends sufita yawo sai kuma bacci da chatting.






Yauma ABDULNASEER ne yadawo da ita buh bai shiga ciki ba, masu gadi kuma babu ruwansu d'ansu ganin Mutuncin AFRAH sukeyi sosai Mommy da Fatty kam basu san halinda ake ciki ba.

Tana shiga gidan a parlor taga Mommy gaishe ta tayi sanan tayi d'akinsu, mayafi da jaka ta aje kan bed tayi hanyan kitchen kasancewan ba sallah xatayi ba
Tana shiiga kitchen din cikin hanzari da kwarewa tafara shirya abubuwan da zatayi ai kafin 6 har tagama komai ta jeresu inda ya dace Sallamatu ta gyara kitchen d'in kaman ba ayi aiki a ciki ba, bedroom d'isu wuce tayi waka ta shiya cikn wani simple gown black color phone d'inta ta jawo tashoga chtn da yaya Sulaiman tana cikin chatting din ABDULNASEER yakira haka sukai ta waya har saida aka kira magrib sanan sukai sallama.






Sai bayan Magrib Daddy yadawo har side d'inshi duk suka shi ga sukamai sannu da zuwa ya amsa masu cikin kulawa da sakin fuska, wanka yayi ya shirya cikin farar jallabiya fita yake shirin yi Mommy tace"inace a gida zakayi sallan isha'in"

"A'a masjid xani"Daddy yace

"Ba dawowan yanzu ba kenan? Nasan sai tunda yan koranan sunan kadawo bazasu barka kadawo da wuri ba"

Murmushi Daddy yayi kana yace" Ai arziki ne"

"Nidai dan Allah kashigo dawuri abincinka najiranka"

"Toh insha Allahu indai basuzo da yawa ba ai ba jumawa zanyi ba"

"Toh inma su dayawanne ai sai kabasu wani lokacin sudawo"

"Hmmmmm Bilkisu kenan, ba ayima *D'AN ADAM* haka dankowa da anfaninsa, saina dawo" ya k'arasa maganan yana barin d'akin

Wani kululun b'akin ciki ne ya tsaya ma mommy ta tsana masu neman temakonan ta tsana taka Daddynsu na kyauta tafiso komai yasamu ita da yaranta ko y'an uwa kar ya tuna dasu, haka dai mommy taita maganganunta da zage zage gajiya tayi da magana ita kadai tabar siden din takoma parlor.


Sai 8:45 Daddy ya shigo

"Sannu da dawowa Daddy" duk sukace Fatty, AFRAH da Afifah

"Yauwa yaran Daddy sannunku" zama yayi nan Mommy tashiga zuba mai abinci already su duk sunci nasu sai wani b'ata fuska yakeyi tana gama zubawa yayi bismala yayi yafara kai loma tuwan semo miyan ogu da yaji nama da busheshen kifi, side din da AFRAH take ya kalla kana yace" wow my daughter naji dadin tuwanan dole Daddy ya bada kyauta"

"Ehh mana wallahi Daddy Aunty Afrah ta iya abinci tafi kowa iyawa"Afifah tace

"Shiyasa zan bata kyauta ai, hope kema kina zuwa kina kallan yanda takeyi?".

"Ina zuwa Daddy sosai sai dai innaje islamiya"

"Good kema za'a baki"
Afrah kam Murmushi taketayi tinda Daddy ya fara magana, mommy da Fatty kam wani haushen Daddy ne ya kamasu kan mai xai yabi AFRAH?

"my daughter kindubu catering school din kuwa"Daddy ya tanbaya

"Ehhh dama ina jiran saikadawo ne sai na fada maka"

"Ai da kin kirani da ko transfer nayi maki kinyi registration din, amma zuwa gobe zanyi maki transfer"
.

"Toh Daddy, nagode Allah saka da alkhari"

"Ameen, ke Fatima bazakiyi ba kikace? "

Turo baki tayi gaba kana tace" Ehhhhh Daddy ".


"Toh ai shikenan"

"Daddy ni zanyi toh"Afifah tace

"Nooo baby kibari sai zakije ss1"

"Allah kaimu, Daddy naga kazo da sabon driver ne, waye shi? "


"Auu sai yanzu natuna, malam bukar ne, mota zai koyama Afrah tinda ita ke zuwa sch"

Sai yanzu Mommy tasamuyin magana " magane ba, itama Fatiman kwanan nawa ne zata fara makarantan? Tare dai zasu koya"

"Toh hakkan yayi" Daddy yace

Haka dai sukai ta hira har 10:30 sanan yara duk sukayi masu sai da safe sukabar parlorn.

Bedroom din Mommy Fatty tayi, Mommy na shigowa ta ganta kwance

"Bakiyi bacci ba?"mommy tace

"Inna zanyi bacci Mommy kina ganin banbancin da daddy yaso yayi"

"Kar wanan ya dameki, zanyi maganin komai ai Azeezah da Maryam nanan shugowa kaduna nan da kwana 10(sisters din Mommy dake zaria) mota kuma babu abinda zata koya, ita har takai matsayin jan mota sai kace gidan Ubanta"

"Yauwa Mommy gara kiyi maganin abun"

"Karkidamu kiyi kallo kawai"

Mommy na gama yin abinda zatayi a d'akin nata tayima Faty sai da safe tayi side din Daddy

Sai da Mommy tayi mata wanan bayanin ranta yayi sanyi, sai da tayi chatting dinta san sanranta sanan ta aje phone din ta kwanta.






Kasan cewan yau Friday da wuri AFRAH tadawo da ka sch,zaune take a baranda waya takeyi da ABDULNASEER yanaso yazo tace yabari sai Sunday sai kaiwa da komowa Fatty keyi tanaso taji dawa AFRAH ke waya amma har tagama tsayuwarta bata gane ba.

Bubu yanda ta iya hakanan ta hakura ta koma ciki, bedroom din mommy tasa kai babu ko sallama

"Lafiyanki zaki shigomin daki haka? "

"Mommy lfya mana, AFRAH nagani a baranda tana ta waya mayb da saurayinta ne"

"Toh sai mai saurayinta d'in banxa da wufi,menene abin damuwa anan kuma? Keda zaki aura santalelen yazo ABDULNASEER ga kyau ga kud'i"

"Hakane toh naga har yanzo bakije bane, bansan madafar da nake ba"

"Dawowan Daddynku ne ya hanani zuwa itama Ummun nasan sabida Daddynku na gari yasa bata zoba, amma ai Satuday daddynku zai koma dan zaije benin"

"Oky randa ya koma zakije kenan? "

" insha Allahu"

"Toh Allah kaymu"Fatima tace

" Daddynku fa?"

"Yana can side dinshi y'an koro da y'an neman k'arin jali suncika gida"

Tsaki Mommy tayi kana tace"nagaji da wanan masifa babu da ma yashigo gari duk a cika ma mutum gida da marak'a kala kala"

"Wallahi nima haushi suke bani, nafiso naga manya mutane mazuwa wajen Daddy ba wanan masu uban yawan ba, dan munafunci har gaidasu Afrah keyi Afifah ma na tayata"

"Suna ina ne ma? "

"Baranda" Faty tace tana danna wayarta

Tashi Mommy tayi dan zuwa wajensu,kafin takai bakin k'ofa tahad'u da Abdull zai shigo, k'arasu inda take gasheta yayi cikin girmamawa babu laifi Mommy ta amsa d'an shii bata cika jij haushin shii ba kaman AFRAH
Tashi yayi na nufa side su"ka kiramin su AFRAH " tace da shii Abdull ya amsa da toh, sai da yafad'ama AFRAh da Afifah kana ya shiga siden nasu.

Suna shiga Mommy tafara masifa mara dalili mara lissafi ita dai AFRAH batace komai ba tayi kitchen dan had'o ma yaya Abdul Abinci, tana zuba komai ta jere a tray tayi d'ankin Yayan nata da shii Afifah na biye da ita.



Daddy bai natsu ba sai bayan sallahn isah'i zaune sune dukkan su a Parlor suna cin abi ci bayan su gama gyara wajen AFRAH tayi tas

sai Daddy yasan duk aninda yaran zasu buk'ata yabasu sanan aka daura da hira, 11:00 duk suka ma iyayen nasu saida safe kowa ya wuce d'an kwanciya.


Da sassafe Daddy yabar gidan d'an zai fara biyawa katsina ya gaida Inna daka can jirginsu zai tashi, addu'a duk suka mai ya amsa gami da samasu albarka.


Kafin 12 na rana Mommy ta gama shirin ta tsaf cikin wani arnan lace kalan milk n pink tayi kyau sosai komai na jikinta mai tsada ne da kaganta kaga matan manya, car key d'inta ta dauka tama Fatty sallama tayi gaba, sai addu'a Fatiy ketayi mata.. (Basaban ba😂😂)



Tana isa gidan Ummu ta amsheta da murna da sakin fuska nan da nan aka ciga gaban Mommy da kayan Motsa baki iri iri

"Ina daughter na ne bata dawo weekend bane? Mommy ta tan baya

"Ta dawo amma tana gidan *Aunty Baraka*sistern Abbansu"

"Oky yarona ma bayanan?"

"Yaronki yaje gidan Aminin shi Hasheem, mayb yadawo kan kitafi"

"Oky ai wajen shi nazu dama, albishir zanmai"

Daria Ummu tayi kana tace "tinda bai nan ai sai ni a fad'amin"

Daria itama Mommy tayi kana tace"mata na mai a gida na tazo yabani tukwici"

"A'a tsohun zance tin yaushe yaje suka dai daita da AFRAHN, babu yanda banyi da shi ba yabari naxo na sameki amma fir yak'i wai sai sun daidai ta kan su, yanzu daya dawo zamuxo neman aure"Ummu ta k'arasa maganan tana murmushi

Wani irin juyi kan Mommy yayi wanda bata tab'a jin irinshii ba....duhu take gani gawani zufa data fara duk da Ac dake aiki

"Hajiya yakikayi shuru? Ko bakisan zancen bane?"

Natsuwarta na nemu gami da gyran murya kana tace" Basan Wanan zance ba ni, ina maki maganan y'ar wajena Fatima ne"

"Ohhh Allah sarki, toh ai shi yaron Naki sun dai daita da AFRAH ai duk d'ata ne tunda duk ta wajenki suke kuma duk yaranki ne ai"

Gyaran Murya Mommy ta sake sanan tace " wallahi har ga Allah da Fatima na so shi coz ita ma ABDULNASEER din ya kwanta mata"

"Ikon Allah duk wanan bai taso ba tinda shi ya zaba da kanshi, ai Alhmdulillahi Da yadawo za'a zo ayi magana d'an yakusa kammala wa"Ummu tace

Gaba d'aya Mommy tafara jin haushin ta, tagaji da jin duk wani maganan ta kuma tasan Ummu ta fahinceta na san a maida neman kan Fatima, amma sai wani daliyewa takeyi wai ita wayayyiya, tashi Mommy tayi gami da cewa "bari naje hajiya"

", tun tanzu muna hiran abin arziki"

Musmushin dole Mommy tayi kana tace" dama ba dad'ewa xanyi ba, zancen nan ya kawo ni tinda har sun dai daita kansu ai sai muje mufara shiri" ta k'arasa magnan tana daria

Kallanta kawai Ummu keyi d'an maganar dabtayi fad'a kawai tayi bawai yakai zuci ba, har mota Ummu ta rakota kana takoma tana mamakin hakin hajiya Bilki na san kai da banbanci.....




_bye wallahi nagaji_
_insha Allahu zan cigaba gobe, amma sai Allah yabani sa'a_
[12/18, 09:04] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*


_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch ♥ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~🌸


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_




*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_





_page 45-46_



Haka kawai yau bata sake jiki suyi waya kamar yanda suka saba ba, da ta tuno yanda sukayi da Mommy sai taji gabanta ya fad'i bayan sungama wayan Mami ta kira sallama tayi cinkin sanyin murya take magana

" yanaji voice d'iki haka? Meke faruwa? Mami ta tanbaye ta

"Babu komai Mamina"

"Oky koma dai menene kiyi hakuri *wata rana*(asmy b aliyu) sai labari"

"Toh Mami insha Allah" nan AFRAH ta kwashe duk yanda sukayi da ABDULNASEER ta sanar da ita

Shuru Mami tayi sai can tace " ya zakiyi accepting mutane biyu a lokaci d'aya? Baki san babu kyau ba"

" Mami wallahi na kasa cema ABDULNASEER d'in a'a ne ni kai na bansan dalili ba Mami sai da nace naga ban kyauta ma kai na ba"

"Kar kidamu addu'a kawai shine abinyi. Nima zan k'ara kan wanda nakeyi"

"Kuma inga Mommy... " sai tayi shuru

"Na sani, aina sane da ita sarai ai ita bata isa ta hana abin da Allah ya dad'e da shiryawa ba inhar baki aura Sulaiman ba dama ba mijinki ba ne, kingane"

"Eehh Mimi"

"Yauwa ki cire wanan tunanin a ranki kidai dage da addu'a kawai"

"Insha Allahu" sallama sukayi da Mamin tacigaba da wayan da su Fahad d Arfah sai labari suke bata tana daria


ABDULNASEER kam kiran ta yaketayi amma sai call waiting yakeji hakanan ya gaji da kira sai text ya tura mata kana ya kwanta
Ko da suka gama wayan da su Arfah data karanta text d'in smiling kawai tayi a k'asan zuciyan ta tanajin wani dad'i.


Kamar kulin ta shirya tsaf cikin riga da skirt na atanfa tayi kyau sosai, d'ankin Mommy tayi d'an yimata sallama
Da sallama ta shiga d'akin gaisheta tayi Mommy ta amsa a dak'ile

"Tanbaayan ki zanyi,kuma ki fad'amin gaskia "

"Tohh Mommy Afrah tace

"Sulaiman yace yana sanki ne?" Ta k'arasa maganan tana zuba mata idanu

Xaro big n beautiful eyes d'inta tayi kana tace " niii kuma Mommy? "

"Jeki kawai sai kindawo"

Barin d'akin AFRAH tayi da sauri tana sauke nunfani da sauri da sauri, girgiza kai tayi kana tace " zan iya kuwa?" Hakadai taita tunani har tazo titi
Agogon hannun ta ta duba ganin kamar zatayi latti gashi bata samu abun hawa ba, kamar daka sama taji yace" beautiful" kallanshi tayi sanan ta dauke ido smiling tayi sanan yafito.
Bud'e mata gidan gaba yayi sai da yayta lallashi sanan tashiga.

Tinda ta gaisheshi bata k'ara magana ba har yayi parking, kallanta yayi kana yace" wani time zaku tashi?"

"Basai kazo bah zan koma da kaina"

"Please sweetheart" ABDULNASEER yace kaman zaiyi kuka

Smiling tayi mai kyau kana tace " don't worry inna koma gida i'll call you "

"Are you sure? "

"Yes sure"

"Oky take good care of yourself"

"I''ll" tace gami da barin motan
ABDUMNASEER bai bar bakin gate d'in ba sai da yadena gananta.



_Dubai_


Zaune yake yana cin pizza🍕 yana kallan wani movie phone d'inshi ne yashiga ringing ganin mai kiran yasa shi wani irin murmushi

"My Mommy i miss you" Sulaiman yace

Daka can b'angaran zama Mommy ta gyara kana tace " i miss you more my son"

Smiling Sulaiman yayi sanan ya gaidata, batare da ta amsa ba tace" tanbayanka zanyi kana jina"

Gabanshi ne ya d'an fad'i can kuma yace" ehh ina jinki Mommy nah"

" menene tsakaninka kai da AFRAH!? "

Faduwa wayan takusa yi saboda wani faduwa da gabanshi yayi

"Ba da kai nake magana ba ne"
.

"Da ina ne, kee Mommy mai kika gani? "

" ina ganin wasu abubuwa ne da ban tabbatar ba, toh kasani inma akwai alama santa a zuciyar ka to kacire shii d'an bazan taba yadda ba kai kafi kowa sanan halina"

"Ajiyan zuciya yasauke kana yace " toh Mommy duk meye yakawo maganan nan kuma? "

"Oho nidai na fada in bahaka ba ran kowa zai baci wallahi" kittttt ta kashe wayan
Da ido yabi wayan yarasa wani irin uwa Allah yabasu, wanda bata san darajan y'ayan wani bah sai nata wanda bata sai mezai faru nan gaba bah, wanda batasan ba'ayima Allah shishigi ba wani tausayin AFRAH ne ya k'ara kamashi numbern Inna yashiga dialing ringing 3 Inna ta dauka " Allah k'ara maki tsawan rai yaaa hajjahu" Sulaiman yace

Dariya Inna tayi anata b'angaran kana tace" tare da kai babban mai gida, ya karatun? Ya larabawa da turawa? "

" duk lfyalau Alhamdulillahi" yace yana daria

"Madallah Allah temaka ya kuma bada sa'a"

"Ameen ameen Innarmu ta kanmu"

Shuru Sulaiman yayi bace komai ba Innace ta katse shurun dacewa" maigida akwai magana bakinka fa, gara kayi magana kafin na kashe wayana"

"Matsalana dake kenan sababi, mekikeci na baka na zuba? Inkinsa hakuri ai zan fada maki ne"

"Tohh inajii ka"

Nan Sulaiman ya kwashe duk yanda sukayi da Mommy yafad'a mata shuru Inna tayi na minti1 kana tace" kadai cigana da Addu'a in ita AFRAH matarkace babu makawa dole ka aure ta duk yanda taso da k'in aure a tsakaninku indai Allah yaso batada yanda zatayi d'an haka kacigaba da addu'a Allah yamana jagora Allah kuma ya tabbatar mana da duk abinda yafi alkhari"

"Ameen ameen Innah nagode hajjajuwa"

"Yauwa aita hakuri dai *wata rana* sai labari lamarin Bilki sai addu'a"

"Hakane Insha Allahu Inna"

"Yauwa Allah yamaku albarka dukkanku"

"Ameen ameen" sallama sukayi Inna nata samasu albarka, smiling yayi sosai wani sanyi yaji a ranshi ko babu magana mai dad'i ma wani abu ne pizzan shi yacigaba daci yana kallan movie Muhammad ne yashigo nan zama yayi shima yana kallan movien.





B'angaran AFRAH da ABDULNASEER kam Alhamdulillahi kula yake bata bana wasa bah duk wani al'amurorinta sa kanshi yakeyi, itama yanxu ta saba dashi d'an ABDULNASER is a very friendy person gashi wayayye da shi duk ya saba da su Zarah muktar haka suma.

Sulaiman ma yana iya nashi amma ko kad'an bai taka k'afar ABDULNASEER ba yana daidai nashi, ita kam AFRAH addu'a take sosai Allah zaba mata mafi alkhari cikinsu.




Abu buwa nata faruwa time nata tafiya toh dama haka rayuwar take.
Haka takasance da Mommy na baza murki cikin gidanta, sai fitoh sa sababin hali takeyi na yau da ban na gobe da ban d'an cikin watanin nan DADDY yasamu cigaba fiye da yanda kuke zato buri mai girma ta d'aura kan yaranta Farty ma hakance takasance da ita k'awaye iri iri mulki babu irin wanda basuyi a cikin gidan shiyasa AFRAH ta yanke hukuncin ansan kudi taje tayi registration na catering sch ta huta da zaman gidan gaba d'aya.



Kallanta ABDULNASEER yayi kana yace " yau zanzo daukanki school"

"Ni kabarshi basai kazo bah fa" Afrah tace

"Meyasa toh? Ko bakiso Mummy tasan muna datting ne? "

"Noooo ni haka kawai"

"A'a dole da reason"

"Toh nidai babu" AFRAH tace tana turo baki

"Toh naji, inaso innakai ki na shiga nama Mommy sallama ne, kinsan saura 5days na koma sch, kuma akwai wuraran da zani shiyasa nakesan shiga yau, amma inbakiso yau sai nafasa"ya k'arasa maganan yana kallanta

"Ohhh shikenan Allah kyaumu anjiman"

"Ameen sweetheart " sallama sukayi kana tashiga school
Sai da yaga shigarta school ya juya.



Ai kam suna gama lectures AFRAH ta k'irashi ta sanar dashi bai wani jima sosai ba ya k'araso, sai da suka sauke Husnah da Zarah gidanjensu kana sukayi gidansu AFRAH hira sukai tayi harsuka iso, horn yayi maigadi ya bud'e gate yashigo ko gama parking baiyi ba AFRAH tafice da idanu yabita, sai da ya k'ara kin tsawa sanan yafitoh

AFRAH kam tana shiga Bedroom mommy tashiga dayasha uban gyara kamar ta sabuwar amarya, amaryanma masu hali d'an ankashe ma bedroom d'in kud'i bana wasa ba. sannu da gida taiyi mata kana ta bar d'akin.

Jinta shuru har na tsawan minti15 yasa shi k'iranta

"Sweetheart kinbarni waje kizo kishiga da ni mana"

Dariya tayi k'adan kana tace" am sorry ganinan"

Wajen Mommy takoma tasanar mata cewan ABDULNASEER yazo yana compound(bata fad'a mata tare suke ba... Ko mai yasa?)

"Jeki shigo dashi bari nafito parlorn yanzu"

Kafin sun shigo har Mommy ta fitoh parlorn
Da sallama duk suka shiga " ahh lalelale da son d'ina zauna mana ka tsaya" Mommy tace


Kitchen AFRAH tayi da kawo mai kayan motsa baki, babu jumawa kuwa tashiga parlorn da tray hannunta ajewa tayi gabanshi tayi d'akinsu

Gaisheta ABDULNASEER yayi Mommy ta amsa cikin fara'a da sakin fuska " ashe har tafiyan ta matso" mommy tace

"Ehh Mommy " ABDULNASEER yace yana murmushi

"Toh Allah ubangiji ya bada sa'a yasa agama lfya"

"Ameen ameen Mommy"

"Ya Ummu take da daughterna Humairah? "

"Duk lafiyalau, Humairah na school Ummie tana gaidaki sosai"

"Masha Allah ina amsawa, ai munyi waya jiya ma"

"Okay Mommy bari nawuce, dama nace bari nazo gaisheki kuna maki sallama tin yau dan inada inda zani da yawa"

"Ahh nagode sosai sosai my son, bakaci komai ba"

Smiling ABDULNASEER yayi kana ya d'auki cake guda d'aya sai ruwa da yasha k'adan bayan yagama ne yace" mommy bari na wuce"

"Wai har ya isheka my son? "

"Ehh mommy Alhamdulillahi"

"Toh gashi har zakawuce baku had'u da mutuniyar taka ba batanan"

Smiling yayi d'an shi har ga Allah baisan wa take magana ba kuma yasan maida wata mutuniya inba AFRAH ba "ai tare da AFRAHN muke, tare mukazo ai Mommy "

Wani abu Mommy taji duumm a ranta wani bak'in ciki da haushe duk ya kamata a lokaci d'aya,


daurewa tayi ta k'akalo murmushi sanan tace "Fatty nake magana"

"Ohh kigaisheta inta dawo" yayi maganan yana sosa kai

Har jikin motanshi ta rakoshi kana takoma ciki da tunani barkatai.

koda ABDULNASEER zai tafi bai nemi AFRAH ba tafiyanshi yayi da niyar inyakoma zai kirata, haka dai ABDULNASEER yabar gidan cikin farin ciki.

Mommy kam tana shiga parlor ta zauna jabar a kujera tanbayoyi taketayi ma kanta marasa lissafi wanda batada amsarsu "toh ma a ina shi yaga AFRAN?
Yaushe da yaushe suka saba da har zai kawota gida?
Ko dai santa yakeyi ne?
A'a Mommy tace a fili, wani dabara ne ya fad'o mata na k'iran Ummu Abdulnaseer din na sanar mata nata k'urin game da yaran nasu.



_toh sweethearts!!_

_Kuna ganin UMMU ABDULNASEER din zata yadda?????_

_ina jiran amsarku_


*Much love for u all sweethearts*❤❤❤❤ *sai an d'an kwana 2*
[12/18, 09:04] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*


_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch ♥ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~🌸


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_




*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_






_Thank you so much for d preys i really appreciate_
_Much love for you all_💋❤



_page 49-50_


A wahalce Mommy ta iso gida wani irin haushin Ummun takeji wanda batasan iyakarsa ba, ganin zaman cikin motan bazai fisheta ba yasa ta fitowa jiki a mace ko band bag dinta bata dauka ba tabar motan.



Bedroom din ta tayi direct kan bed taga Fatty kasancewar yau bata je ko

Please Login or Register in order to submit comment