Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

parlornshi yana tunani AFRAH ce tashigo parlorn da sallama, waje tasamu ta zauna kana ta k'ara gaisheshi ya amsawa yayi cikin sakin fuska da fara'a nan take sanar da shi zuwan familyn ABDULNASEER daddy yayi mamaki saboda Mommy tachai babu wani tsayayen da ke zuwa wajen AFRAH daddy bai nuna ma AFRAH komai ba yachai Allah kawo su lfya sai sanar da yan kstsina, AFRAH na barin Parlon side Mommy yayi bata parlornta direct bedroom dinta yayi xaune ya ganta kan bed tana waya zama yayi yana jiran tagama wayan, nan da nan kuwa Mommy ta sallama da kawarta kallan Daddy tayi kana tachai" Lafiya kuwa na ganka haka? "

"Lafiyan kenan, mekika ce dani game da zancen AFRAH? "

"bangane ba, mekake nufiney? Mekefaruwa? "

Wani wawan kallo Daddy ya watsa mata kana yace" kin ce dani bata da wani tsayayye, toh yanzo tazo take sanar dani Saturday yan uwan yaron zasuzo, amma kince ke baki sani ba wallahi Bilki kiyi hankali da duniya wlhy kuwa"

"Kaman ya nayi hankali da Duniya?nifa ban gane kanka ba komai in kan yaranan ne karinka zakewa kenan abinda ko yaran ka na cikinka baza kayi hakan ba"

"Yara dai duk nawa ney ni keda iko dasu bawani ba, kuma yaro ko ma na wanene ba d'an uwanka ba bakasan mai zai zama nan gaba bah d'an haka duk abinda kikayi dai dai ne, sai kikassnce cikin shiri dan ran Saturday xasu zo" Daddy ya karasa maganan yana barin bedroom d'in


Wani wawan tsaki Mommy taja kana tace wanan" mstsalan kune tinda yara naka ney ai"

Daddy ko yana fita daka bedroom din side dinsa yakoma phone din shi ya jawo ya shiga k'ran yan uwansa ya fad'i masu cikin hadda Uncle Junaid dukkansu fatan Alkhari sukayi gami da Addu'an kaiwa lokacin lfya.


Suleiman yashigo bedroom din yaga Mommy sai masifa takeyi ta inda take shiga ba tanan take fita bah, zama yayi bakin bed dinta kana yace "please mommy kiyi hakuri koma menene"

"Har ni Daddynku zai fad'a ma bakar magana kan Auran wata AFRAH chan mainene nawa ciki? Wanan ai damuwarsu ce ba tawa bah"

Tinda Suleiman yaji Mommy tachai Auran AFRAH gaban shi ya fad'i kallan Mommy yayi bakin sa na rawa yace" au.. ran AF.. RAH kaman... Yaya? "

"Duk kawanu rud'e bakayi interview d'in bane ko yaya? "

"Naji kaman kince AFRAH aure zatayi"

"Ehhhh aure zatayi menene naka a ciki? "

Sulaiman bai bata amsa bah yabar bedroom d'in cikin sauri kaman mahaukaci itama Mommy a haukacan ta tashi daka kan bed d'in tabi bayan shi kamar mahaukaciya....
[12/18, 09:04] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*


_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch ♥ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~🌸


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_




*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_


_page 54-55_


*wanan page din naku ney BIEBIE DEE NVLS GROUP I LOVE YOU All with all my heart* 💞 💞




*F*atyy na karatu babu laifi sai dai matsalan ta tara friends, friends gare ta hadda na tashin hankali kashi tanaso a ce da ita she's classy shiyasa kulin cikin siyan kaya take da kwalliya kulin cikin requesting kud'i take waje Daddy.

Wasu shegun friends tayi Haneefa da Fa'izah yan gayu ne na masifa dan sunfi Fatty nesa ba kusa ba shiyasa take masifar san su problem din su basa san karatu d'an yaran masu kud'i sosai ita kuwa duk abinda sukeyi birgeta sukeyi shiyasa take shishige masu ko kadan Fatty bata duba irin karatun LAW natsuwa yakeso da mai da hankali burinta ita dai tafita da dasu Haneefa
Yanzo haka makeup suke tayi zasu shiga 2lip cin abinci

"Babes i don't understand naga kuna shiri ne kuma kunsan munada test fa" Fatty tace

Kallan ta Haneefa tayi kana tace" i don't zan shiga lecture yau coz i have something to do"

" wat u mean? Bazamuyi test din ba kenan? "

" babe in zakije just go n dress up, akwai important person da zamu had'u a chan ne, da kike maganan rest nariga nayima lecturer magana bamuda case da wanan" Fa'izah tace tana sa eye maskara

" oky tohm bari na shirya" Faty tace

Duk sun shiya tsaf cikin gown na material ku na kunga dressing nasu kasan manyan yara ne dan sun had'u babu karya bag n shoe duk gucci ne kasan newan su Haneefa a garin abuja suke amma gida sosai da mota iyayansu suka samasu a gidan
Nan suka nufa 2lip Fa'iza ce ke driving, suna ina suka samu waje suka zauna abinci mai rai da lfya sukayi Oder sunan zaune wasu hadad'un maza masu jii da gayu da kuma kud'i suka iso nan da nan Haneefa taje tayi hugging d'aya cikin su ita dai Fatty tana kallan ikon Allah
Gaiswa sukayi da samarin Fa'izah ce ta kalle Haneefa kana tace" baby zan wuce Najeeb na jirana"

"Oky take care"

Kallan Fatty tayi sanan tace" sai mu had'u a gida" nan Fa'izah ta wuce
Hira sosai akai tayi tsakan saurayin Haneefa Majid da Fatty sai kuma friend din Majid din Musty ganin irin haduwar su yasa Fatty sake jiki da su, kafin su bar wajen sai da Musty ya amsa Number Fatty wai yana santa dadi wajen Fatty ba a cewa komai tasa mu mai kudi, sai da su Musty suka kaisu shopping a wani shegen super market na yariyan Indimi
Sai dare suka dawo gida, abakin Fa'izah takeji wai Musty babanshi tsohun minister ne, wani dadi ke ziyartar zuciyan Fartyy sai yanzo tafara yadda da zancen Mommy ashe dole ta aura mai kudi ashe mijinta zaifi ABDULNASEER saurayin AFRAH, ai cikin dare takira Mommy take labarta mata tasamu Musty murna sosai Mommy tayi bana wasa ba habaici tai tayi a gida

Haka dai rayuwan Fatty ya kasance a school kwalliya da gayu da bin friends kawai tasa a gaba karatun sama sama ney dai, dating dinta da Musty na tafi yanda yakamata kud'i sosai yake kashe kata kuma yachai wai zai aureta ita dai Fatty dadi kawai takeji.




AFRAH kam maida hankali tayi sosai kan karatun ta kuma fahimta rakeyi sosai dan duk department din microbiology ansanta, haka a fannin snacks tayi fice dan ansan ta sosai a wanan fannin
Ko kadan bata jira sai anyi mata abu tinda ta lura Mommy basu take ana yimata abin arziki ba
Tanada kudunta a account in Daddy ya bata tayi godia in bai bada bah tayi ma kanta mommy kanta mamakin irin kudin da AFRAH kesamu takeyi sau da yawa wasu daka side Mommy zasu nuna sunasan cake ko wani abun amma sai Mommy ta kushe abun tachai ai gara suje dalema ko frch cafe sunfi iyawa kuma hakan da takeyi bashi kesa mutane kin zuwa bah kulin qaruwa ma sukeyi mutane




Lamarin Hafiz a Turkey kan sai dai addu'a babu karatun da yake tsinanawa sai yawo da bin friends ga danfaran mutane ta online school din da yake zuwa ma sun korashi amma ko fada bayyi a gida ba sai da daddy yazo duba shi ne yaji wanan lamari ranshi ya baci sosai amma babu yanda ya iya sai addu'a bai bar k'asan bah sai da ya nemamai wani school din ya gama mai duk wani abu da zai bukata fada da nasiha sosai Daddy yayi mai sanan yabaro k'asan ko HAFIZ yaji ohoooo

Kafin Daddy ya dawo Nigeria Hafiz yakira Mommy ya shirya mata k'arya da gaskia ya fadi mata sai zage zage takeyi wai an cuceshii

Ko da Daddy ya dawo yake sanar da Mommy halin da Hafiz yasa kanshi ciki firrr Mommy tace wai manak'isa akayi mai wasu friends dinsa wai saboda sunga yafisu kud'i "kee a rayuwan ki baki san gskia barin ma kan yaranki, sam baki nuna masu rayuwa baki ganin yanda ABDULRAHIM ke tafiyar da rayuwan sa inace sa'an Hafiz ne? Amma shi kulin cikin matsala ake da shii" daddy yace

"A'a walhy kar kayi ma yarana baki insha Allah kanan zakaga cigaban da zasu samu, kuma da kake xacen Abdulrhm shi kaje makarantar tasu kaga yana karatun ne? Kawai ni banasan haka "

Idanu kawai Daddy ya zuba mata chan yace" Allah shirya mana yakuma sa mudace"

"Ameen " tace tana bat'a fuka.




Yau Fatty zata dawo hutu kasan cewa anyi exam na first semester amma bana tunanin Fatty zata fido wani result mai shegen xafi, AFRAH tayi mata fried rice da salad sai farfesun fresh fish sai kuma cup cakes datayi mata Mommy sai dadi takeji anyi ma yar lelenta girki
Sai 2 Fatty ta iso gidan Murna sosai Mommy tayi Afifah kam ko a jikinta masifa takeyi ma wai masifaffiya zata dawo
Bayan Fatty tayi wanka taci abunci labarin Musty taita bama Mommy haka har bedroom tasa mu Afrah taita bata labarin Musty addu'a AFRAH tayi masu na ALLAH yabar su tare
Tadawo da kwana 3 Musty yace zai zo rokon AFRAH tayi kan dan Allah tayi mai girki dayake Afrah nada pure heart haka ta fidda ta kunya tayi Musty girki masu rai da lfya bayan Afrah tagama komai da temakon Afifah da Salamatu Fatty ce tashigo kicin din kan warmers din abin cin tayi da yanda AFRAH tayi decorating wasu tayi smilling"kai gaskia sis nagode dole na bada 10k"

"Wa zakibama 10k din? "AFRAH tayi tanbayan tana kallanta da kyau

"Kee mana Mommy tace ai business kikeyi"

"Allah kiyaye na amsa kud'in ki wallahi"

"Ai kuwa dole ki amsa tinda sana'ar ki ney"

"In da kinsan zaki biya kud'i ai dawa wani restaurant din kikaje kika siyo abincin sai ki biyasu da kayau, nidai baki da abinda zaki bani coz kin wuce haka a wajena so kirike kudin kii"

Maganan AFRAH na karshe ya bata mata rai, a zuciyan ta tace bani da abinda zan bata? Niko keda abubuwan bata sai ma nan gaba dandai sana'ar girke girke bazai kai ta ko ina ba.


Musty yaji dadin tarban da Fatty tayi mai Mommy har parlorn baki tazo suka gaisa da Musty(niko biebie nace Hmmmmm)
Shoppin sosai yayi ma Fatty tunda ya lura abinda tafi so kenan sanan kud'i 100k wai a bama Mommy

Ko da Mommy taga uban shopping gode ma Allah tafarayi gakuma kud'i

"Kinga abinda nake fad'a maki kow Fatima? Da zaki wani sa ABDULNASIR a rai yaushe zai iya irin wanan shopping din shi? Naji labarin ma su UmmuAbdulnaser din arzikin baka man daa ba"

"Ohoooo wanan kuma matsalan Afrah ce dama a wahala zata kare"

"Aifa ai sai kirika temaka mata,tinda nasan daya dawo za'azo neman auranta"

"Chan su kara ta kuwa"

Kwanan Musty 5 a kaduna amma kulin zaizo sai yazo da uban shopping ita dai AFRAH nata ido, randa zai koma ne yake cemai Fatty yanasan ganin Daddyn ta dan shi auranta yakesan yayi, Fatty tachai yayi tafiya amma yadawo zata sanar dashii, koda Mommy taji wanan labari har rawa tayi da buda


A wanan hutun ne AFRAH taje katsina kwanan ta 5 sukaka dawo, suna dawo wa suka fara shirye shiryen komawa school randa akayi resuming Affrah takoma FATTY kam saida takara kwana 3 sanan takoma abujan



Ta koma da kwana 2 Daddy ya dawo tarba mai kyau yasamu bayan yaci abinci ya huta mommy ta shiga bashi labarin Musty Addu'a yayi kana yace" sai kisanar da ita nadawo ai"

"In dai zancen bikin ya kankama dubai nakeso muje siyo kaya daka nan sai naduba Suleiman duk da yakusa dawowa"mommy tace

"Sai kiyi addu'an kaiwa lfya kafin kifara wani burin" Daddy yace

"Toh Allah tabbatar mana da Alkhari"

"Ameen ita AFRAH babu wani tsayayyen ney? "Daddy yace yana kallonta

Wani miyau Mommy ta hadiye kana tace" ni gaskia ban sani ba dan bata fadamin damuwanta bata dauke ni matsayin uwa ba sam"

Shuru Daddy yayi baichai komai ba ya lura indai lafin yaran wasu ne Mommy ta rinka zakewa kenan


Kwanan Daddy 4 yawuce Lagos Snacks masu dadi AFRAH tayi Daddy ya tafi tasu 20k ya bata kudin da zatasa mai a mota dan shi bai san Mommy ta hana a koya mata Motan bah, godia tayi gami da Addua Albarka ya sa mata kana yawuce


Sai da yafara zuwa zaria dan duba Abdulrahm, Alhamdulillahi yasamu Abdul lfya kuma yana karatu sosai dan sune yan 400lvl kanshin Abdul yayi mamakin zuwan Daddy amma sai bai kawo komai bah ya nuna jin dadin shi kan ziyaran da yakawo mai, bai bar zarian bah sai da yabiya ta gidan surukan sa dan kwasan gaisuwa aikuwa Alkhari sosai Daddy yayi masu sai godia da sa mai albarka sukeyi dan Mommy ba cika zuwa takeyi ba bare ma tamasu wani abin arzikin(dama Mommy da rowa.. 🤣🤣) sai da ya cikasu da abin arziki sanan yabaro xarian, katsina yayi nan ma sha tara na arziki yayi ma yan uwansan daka nan yabi jirgin Lagos yawuce.


Soyayyan Fatty da Musty yana tafiya yanda ya kamata dan duk wani abu da yasan tanaso yana kokarin yimata kulin cikin yimata shopping yakeyi ga uban kud'i dake cusa mata abinda takeso dama kenan
Karatu kuwa tanayi babu laifi gayu kuwa sai abinda yayi gaba dan in kunga Fatty bazaku ganeta ba sabida hud'uwarta classy ce ta karshe ni kaina na sara mata wajen iya dressings(kundai san yan ABUJA.. LOL)



AFRAH ma da ABDULNASEER suna tafiyar da soyayyan su cikin natsuwa da kwanciyan hankali babu karya ko kadan a tsakaninsu tsakani da Allah suke zaune da junansu, duk family ansan AFRAH dayadawo za'azo ayi magana.




ABUJA

Farty da Musty ne zaune a parlornsu kasan cewar ta dade databar hostel tadawo gidansu Haneefah kallanta Musty yayi kana yace"baby next week fa uncles dina zasuje gidanku kinsan nakosa na aureki i love you so much"

Sai datawa juya eyes kana tace " i love you more n u knw dat, nariga nafama Daddy so don't worry babu wani problem"

"Oky Allah kaimu baby"

"Ameen sweetheart" Farty tace

Hiran soyayya suka cigaba dayi sai 11 yatashi dan tafiya, har gaban motan shi tarako shi hugging dinta yaya sosai kana yashiga fada mata kalaman soyayya" i love you so much baby u ar my everything" sun dade a haka kana yasaketa smiling kawai Fatty keyi dan a ganinta irin wanan ba komai bane, ko da yashi mota blowing kiss yaita mata itama tana yimai sai dataka yabar gidan sanan takoma ciki

Kwanciya tayi sama kujera tunanin irin daulan da zata shiga takeyi smiling mai kyau tayi da tanuna wai su ABDULNASEER basuda kud'i kamar da, dataga tunanin ba mai karewa bane tashi tayi tanufa bedroom inda taga su Haneefa nata waya, wani book ta dauka tafice a bedroom din.



Mommy tinda taji zancen Musty zai turo rasa inda zata sa kanta tayi y'arta zata aura mai kud'i
Musanman taje har gidan UmmuAbdulnaseer ta labar tamata smiling Ummie tayi kana tace" abu yayi kyau Allah ayi damu, muma ai Abdulnaseer Na dawowa zamuzo neman auran saura wata d'aya yadawo ai"

Ameen ameen Ummie Allah dawo mana dasu lafiya Suleiman shi nan da 2weeks zaidawo"

"Allah dawo dasu lfya" Ummu tace

Hiran yanda bikin na yaran nasu zai kasance sukai tayi Ummie na saka zancen AFRAH sai Mommy ta dauke wuta ko ta chanza maganan Ummu dai tana kanin ikon Allah haka dai sukaita hira sai 5 Mommy tayi haraman tafiya, har bakin mota ta rakota sai dataga Mommy tabar gidan takoma ciki tana mamakin hali irin na hajiya Bilki.







Ranan da family da Musty sukace xasuzo Saturday ney, ranan Mommy babu zama tahana AFRAH sakat girki kala kala kala da iri iri ta sata tayi masu ga uban zama'a da Mommy ta gayyato wai suzo yau za'akawo gaisuwan Fatima gida fam da mutane dan ma akwai su salamatu, Atika, safiya da Lantana da da k'ara man wahala zata sha bah sabida uban aikin da tayi ranan ba na wasa bane haka dai suka shirya girke girkenan a babban parlor na bak'i ga uban snacks da juice iri iri sabida samun waje hadda wanda zasu tafi dashi Mommy tasa ayii duk a ka jeresu a parlorn baki

Da misalin k'arfe karfe 4 bayan salan la'asar uncles Musty suka iso su 4 ney sai Aunties dinsa su 3 Daddy ma su 3 ne shii sai yaron Inna Rakiya uncle Isma'i da uncle Musa duk Isma'l yayane a wajen Daddy Musa kan k'ani ne
Tarba na mutunci sukayi masu nan uncles din Na Musty suka gaba tar da abinda yakawo su nan dai su Uncle Isma'l suka ce sunbasu nan aka saka ranan biki nan da wata 2 Addu'a sukayi Allah ya kai su lokacin lfya, su Uncles Umar basu iya cin komai ba sai drinks da snacks

Side din Mommy ma hakan ne ya kasan ce tarba mai kyau su anty Lailah suka samu wajen Mommy haka dai a ka rabu cikin girma da mutunci

Fad'an irin kayan sa ranan Fatty bat'a lokaci ne kaya ney hadda na hauka da mara sa anfani ga kuma akwatuna 3 wai kayan NAGANI INA SO abun dai sai wanda ya gani
Tanan rawa da babu irin wanda Mommy batayi ba yarinyan ta tayi goshii ranan saura 2weeks Suleiman yadawo ita dai AFRAH nan taga ikon Allah



Bangaran familyn Musty kuwa mamakin inda yasamu y'ar mutunci sukeyi kasan cewar sun san halinshi, Baban shii yafi kowa Murna da wanan auran da Musty xaiyi(nidai nace Hmmmmm) wasu daka cikin familyn Addu'a suke Allah sa auran yazama sanadiyan shiryuwan saa.




Rayuwa nata tafiya haka lokacin nata k'aratowa haka abubuwa nata faruwa
Yau ko gobe ne suke sa ran dawowan Sulaiman Murna wajen Mommy ba a magana ita AFRAH ke lissafe ABDULNASEER dinta ma nan da 10days ko 1weeks zai dawo shiima, girki dai sukayi masa dai dai ba wani mai wahala ba sai cupscaks masu kyau, kowa ya hallara a gida Abdul ma yadawo cikin ikon Allah kuwa ranan Sulaiman ya iso Nigeria da nan da nan Bala driver, Abdul da Afifah suka nufa kano dan dauko shi kasan cewar nan ya sauka

Sai 6 Na yamma suka iso kaduna cikin koshin lfya, inkunga Suleiman baza kugane shi ba yayi wani fresh ga kyau da ya kara abundai sai wanda ya gani(nii baxan iya bayani ba) hugging dinsa Mommy tayi gami da cewa "welcome home my son"

Smiling yayi yayi hugging dinta sosai kana yace" i miss u Mommy"

"I miss you more sweetheart" mommy tace tana wani Murmushi nan suka isa ciki Sulaiman sai kallan gidan yakeyi ashe haka Daddynsu yasamu cigaba

Daddy ma hugging dinsa yayi yana samai Albarka shima kara rungume Daddyn yayi yana amsawa da Ameen

"Saura Muu" yaji maganan daka sama yana juyawa yaga AFRAH da Afifah a tsaye Afifah sai wani murguda baki takeyi
Kasowa wajen yayi yayi hugging Afifah yana cewa" i miss you so much lil-lil"

" bawani bayan na shiga jss1 ma baka sani ba"

"Gashi yanzo nasani"

Jin sweet voice din Afrah yaji tana gaidashi tana wanan smiling din nata, kallanta ya tsaya yii for some second kaman yana san tuno wani abu Mommy da ke jefe kaman ta dauke AFRAH da Mari dan haushi dafashi da mommy tayi ne yadawo daka duniyar sunanin da yatafi jan hannunshi tayi suka shiga ciki, Abdul, AFRAH da Afifah suka mara masu baya Daddy dama tuni ya shige ciki.






_sweetheart mekuke ganan zai faru?? Suleiman yadawo, Abdulnasser xay dawo soon, ga Fatty zatayi aure da Musty duk ya zata kasancee neeeeey wai??????_
[12/18, 09:04] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*


_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch ♥ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~🌸


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_




*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_




_page 58-59_


*wanan Page din naku ney AUNTY MAIJIDDAH MUSA & A'ISHA MUH'D(AUNTY) thank you so much for d love, care and support, thank you so so Much may Allah guide and protect you Always ALLAH barmu tare,Thanks alot sweethearts*❤❣❤❣




*S*ide din shi direct yayi bai tsaya ko ina bah sai a bedroom dinsa, yana shigowa itama Mommy ta shiga" wai lafiyan ka kuwa?daka magana duk kabi ka rud'e" Mommy tace tana kallan shii

"Lfyalau" yace yana k'okarin shiga toilet

Takai tsawan mintin5 a bedroom din kana tabar dakin tana wasu tunani haka har takai side dinta
Zama tayi bakin bed miss called na FATY tagani har 5 nan da nan tashiga dialing number nata ringing 3 ta dauka hira suka danyi nan Mommy ke sanar da zacen zuwan familyn ABDULNASER neman auran AFRAH Fatty cewa tayi su suka sani ita bai dameta ba hakadai sukai ta hiran yan da biki zai kasan ce dan lokaci nata matsowa.


B'angaran AFRAH kuwa ranan hiran su suka sha da Adulnaseer sosai, haka AFRAH takasan ce cikin farin ciki ranan d'an ita kanta tasan tana san ABDULNASEER kaman yanda yake santa sosai



A katsina ma Mami tayi murna sosai da jin zancan auran AFRAH ya tasu nan ta sanar da k'anuwarta anty Safiya(maman Heeshmer) zancan babu b'ata lokaci Maman Heeshmer ta baza a d'angi kasancewar Familyn aunty Rabi duk mata ne, dan da nan suka kira meeting d'an susan abinyi tun da wuri(niko Biebie nachai AFRAH yar gata... Hmm)


Inna ma sosai tayi murna takuma sa Albarka a k'asan zuciyanta tana taya Sulaiman bakin ciki Amma babu yanda ta iya sai hakuri haka Allah ya tsara




Side din su UMMUABDULNASEER ma shir sukeyi sosai d'an basu tab'a aurar da kowani yaro cikin family ba kancewar bawani yawa suke dashi chan ba so fadan irin shirin da sukeyi ma b'ata lokaci ne gskia.




Tin ran Friday Zainab yarinyan uncle Isma'i ta diro kaduna haka ZARAH da Husna da Aysha gidan suka wuni dan taya AFRAH aikin yin wasu snacks, AFIFAH cikin su tashige ta zauna kaman friends dinta sai manyance takeyi wanan ranan Mommy ko fitowa batayi bah tana bedroom, amma duk hayani yaniyansu a kunnen ta mamakin inda AFRAH tasan mutane haka takeyi wanda ko Fatty da bata aiki sai bin Friends bata da irin friends na AFRAH gasu duk masu hankali da natsuwa ga wayewa da iya kwalliya

AFRAH na zaune saman freezer tana waya da ABDULNASER Lantana tashigo kikcin din kallan AFRAH tayi kana tace" Antyn Afifah hajia na kiranki" sallama tayi da ABDULNASEER sanan tawuce kiran Mommyn

Sallama tayi bakin k'ofan sai da Mommy ta amsa sanan tasa kanta cikin bedroom din" gani Mommy"AFRAH tace tana gyra zamanta


Sai da Mommy ta kalleta da kyau sanan tace" kee yanzo d'an bakida kunya d'an za'azo neman auranki shine duk zaki baza magana a gari kin tara mutane fam a gida babu ko kawaici"


"Mommy wallahi ni ban kirasu bah, Zainab ce takira Husna Da Zarah wai suzo sutayamu wani aikin cakes da zanyi shine kuma sukazo tare da sulXee bako, jiddah,hafsah, da Hawee, aysha kam zuwa kawai tayi duk basu san zancen bah ma sai dasukazo Zainab kefada masu"


"Hmmmmm kedai kika sani, kunya dai abu ney mai kyau d'an bata zuwa sai da alkhari"


"Kiyi hakuri Mommy"

"A'a nemene nawa ciki? fata ma zanyi sai asha shagali lafiya" handbag d'an ta tadauka gami da gyara mayafinta tana shirin fita, bin hayanta AFRAH tayi har suka sauko k'asa "sai kindawo Allah tsare"AFRAH tace

"Ameen" Mommy tace, da idanu AFRAH tabita tana mamakin halin Mommy na juya abu yanzo yanzo ta juyama fassara da ma'ana dataga tsayuwan bamai k'arewa bane yasa tayi cikin, haka dai sukai ta aikin

Please Login or Register in order to submit comment