Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

toilet dan hadamai ruwan wanka, " ai sai kaje kayi wanka"

" toh hajjaju"

"Karka kuma kirana hajjaju, sai kace wata uwar mata"

Dariya yayi sanan yace" uwar yayana ba"

Smiling kawai Afrah tayi, kafin ya fitoh har ta fiddo mai da kayan da zaisa ta fesa turare, ya shiyar tsaf zai tafi masjid Afrah na k'ara tsamsa bedroom tace" sweetheart nifa banyi girki ba yau"

"No wahala in mun idar da isha'i zan samu mana wani abu, Abincin Ina ma kikeso? "

"Na big treat, yafi kusa"

"Tohh, sai nadawo"

"Adawo lfya Allah tsare"ya mansa da ameen yana bari bedroom din, tana gamawa alwala tayi itama ta shinfida preying mat, ta zauna har a ka Kira magrb, bata bar sallayan ba sai datayi isha gami da azkar na sallah, nike hijab da abin sallan tayi tashiga wanka, tana fitowa tasa duguwar rigar bacci har kasa Sure kawai tashafa dan tinda tasamu ciki bata san kanshi sosai, parlor ta dawo ta zauna tana jin karatun Al'Qur'ani mai girma sai 8:45 Abdulnaser yadawo, bayan sunci sunsha sunyi dam Abdulnaser ya kalleta sanan yace" baby ina cards dinnan? "

"Yan bedside drawer na bedroom dinka"

Da kanshi ya dauko ya dawo yaxauna" kinga na bikin Hashem ne da Nussy"

"Ah masha Allah abin ya matso" Afrah tace tana bude card din, ikon Allah tsakaninsu da Husna 1 week ne, lallai munada sha'ani"

"Ke baki gajiya da yawo ne wai? Shekaran jiya kuka dawo daka katsina fah, haba baby"

"Wai kana nufin bazan je bikin Husnah ba? "

"Zakije ko sau daya ne kawai dan mutincinta, gashi zakukoma sch ma, ni wallahi basan fitanan yanzo" shuru kawai Afrah tayi dan tasan bada wani problem da mijinta
"
" gobe ne zamuje hospital ko? "

"Ehh insha Allahu"

"Allah kaimu,

"Ameen"

Afrah cikinta yashiga 7 moths, anyi mata awo ita da baby sunan lfyalau.



Ran Friday da yamma Musty ya shigo kaduna yazo Fatiyy ba lafiya bayan ya gaisa da mutan gida, Hospital direct yayi da ita, suna isa akayima Fatty duk abinda yadace, angano tana da shigan ciki na 2moths, wanan karan Musty yayi murna sosai Fatty ko hamdala tayi ma Allah daya shirya mata mijinta, da suka dawo gida haka Musty ya Kira mommyshii da aunty Lailah da sauran Family yafada masu sai murna sukeyi da addu'an Allah raba lfya.

Fatty takira Afrah tagaya mata, sosai tayi murna yakuma yimasu addu'a baki dayansu na Allah ya rabasu Lafiya.

Haka Musty DA y'an uwansa nan kaduna suketa kula da Fatty, ko da zai koma abuja wanan karan ma Fatty bata bishii ba, gidanta nan kaduna take, AFRAH da kanta ta gayama Musty bikin Husna da zasuje ya yadda Fatty taje amma sai da ya damka amanarta wajen Abdulnaser.
Da Musty zai wuce gidansu ya aje Faty dan gidan nata yayi Shuru babu kowa sai dare deriver zaiso ya dauketa

Suna zaune a parlor suna hira Kaman daka sama sukaga AFRAH d Abdulnaser sun shigo da sallama, bayan gaishe gaishe hira akai tayi, Abdul, Hafiz, Abdulnaser Faty DA AFRAH cikin farin ciki da kwanciyan hankali sai 5pm su Afrah suka wuce shima Inna da mommy ne sukai musu tsiyan wai su kulin yawa suna hanya.





An fara bikin Husnah, komai cikin kwanciyan hankali akeyin shii, biki yayi kyau sosai anci ankuma sha, ango DA Amarya Husnah anyi kyau kamar babu gobe, anyi pictures sosai, event 1 kawai Su AFRAH sukaje KAMU shima da kyar sai yinin Biki watou ran daurin aure, shima duk Ba wani zama sukayi ba, Zarah ita batama zobah sai sisters dinta dan ciki ne da ita mai bata wahala sosai, Ita Husnah ma taso AFRAH ta huta dan tasan inda Afrah qalau take ita da Zarah su na daban ne, a hakama tagode sosai da abinda suka bata familynsu da mazajensu, haka akayi biki aka gama duk babu AFRAH sai Afifah dan hadda friends din ta tayi inviting, Mommy Inna Afifah su suka sha biki dan har Gidan amarya da dinner duk sunje, Daddy, Hafiz da Abdulma sunje daurin aure yaya Sulaiman ne kawai baije ba Dan ran Friday bai shigo kaduna da wuri ba, Haka Mamin Xarah da sisters dinta duk dasu akayi komai.

Uguwan dusa aka Kai Husnah, gidanta mai kyau haka kayan da a ka zuba mata ma, addu'a kowa yaytayi na neman zama lfya da samun xuriya nagari *toh Husnah Allah bada zaman lfya Amern*





Yau Sunday Sulaiman ne zaune shi da Daddy suna dan hira vaYan sun gaisa, kallan Sulaiman Daddy yayi sanan yace"Sulaiman ya zancen yarinyar da kake nema ne? "

Dan sosa Kai Sulaiman yayi san yace" Daddy bamu sasanta da ita ba gskia, last 2 weeks ma tayi aure"

"Tohh ALLAH kawo ta gari"

"Amern Daddy"Sulaiman yace a hankali

"Naga kasamu aiki ne, kuma mai tsoka shiyasa na tanbaye ka ko kuna tare sai aje ayi magana manya sushiga ciki"

"Haka ne very soon zan samu wata insha"

"Toh Allah temaka" Daddy yace yana daukan wayanshii yana duba abu chan yace " kaga dubamin message dinan nidai ban gane kanshi ba" Amsan wayan Sulaiman yayi yana duba text din, Daddy ya cigaba da cewa tin last 3weeks ago suke turowa ni bangane ba"

Zama Sulaiman ya gyara sanan yace" Daddy wanan ai sunan association din da kasa Business dasu ne a Ghana "

"Ehh nagani ai bansan inda suka dosa bane ai"

"Ina zuwa " Sulaiman ya fita da sauri

Laptop dinsa ya dauko daka dakinshi yadawo ya zauna nan ya shiga link na association din sosai yayi bincike har ya gano bakin zaran, Ashe problems sosai aka samu sai last month suka daidai ta komai, duk wanda yasa business dasu sun sai damai kayanshi shine suke turo text kayi bincike zakaga zabi inkana san cigaba da business dasu profit kawai zasu turoma ta bank tndaa kan kasa hannu a business din akwai duk wani information a kanka inkuma kadena Business dasu zasu turona uwar kud'in ka da kuma profits(riba) da ka samu a yin Bussine dasu na farko, ai Sulaiman bai jira tan bayan ra'ayin Daddy ba yatura Daddy ya bar business da suu, kancewar phone din Daddy na hannun Sulaiman baifi minti 8 ba alert yashigo wayan, uwar kudi da profit din Daddy na kayan da suka saida masu daka chan, sujjada Sulaiman yayi yana cewa Allahu Akbar ganin haka yasa Daddy shima yayi sujjada tare da cewa "Alhmdulillahi" batare da yasan dalilin da yasa Sulaiman yayi sujjadan bah, dagowa Sulaiman yayi yana wani irin Smiling sanan yace" Daddy kaga ikon Allah SA mu'ujizan sa, Daddy kaga anfanin ansan Kaddara mai kyau ko mara kyau da hannu biyu, Allahu Akbar, ALLAH mai girma da daukaka mai juya al'amura a Duk sanda yaso kuma yaga dama"

"Wanan Haka yake Sulaiman hak'ika duk wani wanda ya kauce hanyan Allah yana cin masifa da bala'i"

"Sosai Daddy kaga dai kudinka da kasa...... " Sulaiman yayima Daddy bayanin komai

"Kagani har kudadenka sun fitoh hadda riban kayan da suka siyarma" wani kabbaran Daddy yasa gami da hamdala

"Allah gagara musali, Allah mai girma da Rahma, Allah nagode ma, Alhamdulillahi, Alhmdulillahi Alhmdulillahi"kalman da Daddy yaita nanatawa kenan, Alwala suka dauro sukayi raka'a biyu bakara yima Allah godia, nan suka dan kara shawara kana Sulaiman yabar wajen Daddy cikin farin ciki.



Sai da suka dawo kada masjid suna zaune dukkansu a babban parlorn suna cikin abinci, bayan sun kanmala ne Daddy yayi masu bayanin komai, Suma kabbara kawai sukai tayi gami da yima Allah godia, Nasiha sosai Daddy yayi masu a k'arshe yayi masu Addu'a gami da samasu Albarka, Inna ma Nasihar tayi yakuma kara da sa Albarka wanan rana kowa cikin farin ciki yake mara musaltuwa.


Nan danan Afifah ta dau waya takira AFRAH da fatty ta sanar da su duk bayanin da Daddy yayi, sanan ta Kira yaya Musty da yaa Abdulnaser ma ta sanar masu, suma a side dinsu murna sukayi sosai dayima Allah godia, kan kace mai har sunzo yima Daddy murna, Daddy sai samasu albarka yakeyi, ranan Sulaiman yakoma Abuja, Musty da Fatty ma haka d'an Mommy shii duk tadamu wai yadawo da ita, haka aka rabu cikin farin ciki.



Suna barin gidansu AFRAH, gidansu Abdulnaser sukayi, Ummie ce ita da sister Anty murja sai Anty Baraka suna hira" kingani banace maku ba yanzo sai ku iya ganinsu" ummie tace tana murmushii,

"Ai ka kawota da kanka ka hutashemu" cewar Anty Murja

Ita AFRAH smiling taayi tana gaidasu, cikin sakin fuska suka amsa gami da tan bayanta karfin jiki ta masa da alhmdulillahi

"Ni ban gane ba, nakawota da kaina kamar ya? " Abdulnaser yace yana kallan Anty Baraka

"Dama ko bakuzo ba Xamuzo mutafi da ita, Inace wata na 7 take zata shiga na 8 kow? " anty Baraka baraka tace

"Toh wai akaita Ina? "

"Gidanan zata zauna, yanzo kagane kow" Ummie tace tana kallan shii

"Ehhh nagane" yace a hankali

"Da kyau sai ka koma ka hado mata duk kayyaki da shopping dinda kayi"

"Toh amma gobe zatagoma school fa"

"Toh sai akace kuma anan ma bazataje ba ko? Kai mai yasa nakada kawaici ne wai? " aunty Murja tace

"Barshi karyayi kawaicin, nan dai zata zauna har tayi 40days mayb ma tafi" ummie tace

"Ahhh Ashe nima nan din zandawo kenan"Abdulnaser yace yana ficewa daka Parlorn

Dariya kawai sukayi, AFRAH kam wajen Huraira ta shige, dan sai gobe zasuko school amma ita sai Wednesday ma zata koma.

Babu yanda ya iya haka ya kwaso duk a binda Afrah zata bukata yakawo gidan, shima kuma ya dauko nashii dan shima zaman zayyi,
Abbah kam shi zamansu ma Dadi yamai kulin yana ganinsu, Abdulnaser ke kaita sch Driver ya daukota bayan la'asar kuma ita da Huraira suje strolling, haka suke fita kulin har takoma sch itama sai kuma weekend intazo

da su Inna sukaji Afrah na gidan sirikarta sosai sukayi murna, duk sati suke zuwa dubata, inzataje awo hospital kuwa hadda Ummie akezuwa, sosai Ummie ke kula da ita kamar mai haka Abba, anty Baraka, da sauran yan Uwa, Aunty Rabiela ma kulin cikin video call suke, Abdulnaser kam babu kunya shima ko gaban waye, AFRAH najin dadin gidan sosai, Hafiz kam kulin sai yazo dan wani irin mugun shiri sukeyi wanda ko da yaya Sulaiman da ABDULL basuyi irinsa ba, dan Hafiz ya natsu sosai yanzo haka restaurant da AFRAH xata bude komai hannunsa yake.




Cikin wata daya komai ya chanza cigaba bud'e da daukaka duk Daddy yasameshi dan sana'arsa nada yakoma na shinkafa kuma wanan karan sosai Allah yasa mai hannu, ganin Hafiz suna dan business da Abdul yasa Daddy kara masu jali sosai sukayi murna gami da addu'a.


Yawan zuwa gidan Da Humaira keyi amso sak'o intadawo weekend ko zuwa hira wajen Inna yasa yaya Sulaiman ya ganta yakuma yaba dan Humairah akwai natsuwa da tarbiyya sanan ga iya gayu da wayewa.



Su Daddy suntare a sabon gidansu dake nan marafan da sati daya AFRAH ta haihu baby boy, bawani wahala tasha ba, murnar da sukayi Allah ne kawai ya san iyakansa dan fada ma bata lokaci ne, kafin kace mai yan katsina sun iso amma wajen Mommy suka sauka sai dai suxo barka, haka family Mima, ga yan adamawa dangin Ummie da Abba, ga yan uwa da abokan arziki, Daddy yazo yaga yaro yakuma samai albarka, Inna kuwa ba'a cewa komai ba'abar yan *Biebie Dee Novel group da Da Biebah place da kuma D'an HAKKIN da ka RAINA fan group* a baya ba kaf dinsu sai da sukazo barka zuga guda kamar... πŸ€£πŸ˜‚πŸƒπŸ»β€β™€ I love you all β£πŸ’―

Fatty ma cikin ta ya girma dan wata 5 cikin na6 tayi kyau sosai abinta, Xarah kam ta haihu baby girl Fanan babynta mai kyau

Abbah da kanshi yasama jariri Suna Ahmad, ranan suna kam Mommy da Mami taronsu da ban,sukayi kudi yayi kuka dan komai an tsarashi irin namasu hali, haka gidanan Ummie ma da yanwanta, Naira yayi kuka anci ansha ankuma sha pictures, maijego tayi kyau sosai tasa kaya, haka dai taro yatashi lafiya kowa nasan barka tare da abubuwan da aka raba masu k'ayatarwa, haka AFRAH da Ahmad sunsamu kaya sosai wanda ni bazan iya fada ba. *kawai Allah raya Ahmad*πŸ‘πŸ»πŸ€ΈπŸ»β€β™€


Anyi suna da kwana 5 Abdul yawuce Camp, yabar Bussine wajen Hafiz, kaya aketuro masu daka Dubai da China na maza da mata sanan materials na maza da shadda.





Afrah tanasamun kula fiye da tunanin mai karatu dan Ummie sosai take kula da Afrah, haka Aunty baraka, aunty murja Mommy kam ba'acewa komai, kafin suyi 40days AFRAH da babyta sunyi mugun kyau ga Ahmad da kyau komai na Abdulnaser hadda dimples hasken fatane kawai na AFRAH, koda sukayi 40days satin farko Adamawa sukaje gaba daya su hadda Ummie da Abbah jirgi suka bi, sati na biyu katsina sukaje shima a jirgin a sati na ukune sukaje zaria hadda Mommy da Fatty datazo amma ranan suka dawo, a ranan nekuma da dare akamayar da AFRAh gidanta...
[12/18, 09:04] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*


_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch β™₯ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~🌸


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_




*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

*wanan LAST page din nakune Pure moment, Allah karemin ku, Ameen*

*SADNAF*
*AXLAND ( SWEETHEART)*
*MSB*
*UMMIE GARKUWA*
gaisuwa mai yawa da fatan alkhari....


*PAGE 85*


""""""Wannan dare Abdulnaser da Afrah ansha soyayyah ba kada'n ba, sai addu'an ALLAH barsu tare kawai, kwana ta biyu da dawowa Ummie ta kawo mata Mai aikinta da kuma rainon Ahmad Sa'adatu, Lafiya lau suke zaune dan daka sa'adatu har AFRAH baduda problem duk da sa'adatu bawata babba bace amma batada sa magana sam gashi tana kula da Ahmad sosai.


Afrah ta haihu da 2 months aka sa bikin Yaa Sulaiman da Humairah 2 weeks kawai, babu sauki wajen Afrah, yayar amarya kanuwar ango, haka Abdulnaser ma babu zama haka Hafiz da ABDULL, Daddy dan lalle zayyi aure, mommy da Inna ma ba sauki🀣

Su Mommy suyi lefe nagani nafad'a anzuba kaya kaman me, komai mai kyau da tsada ne a cikin kayan, haka aka Kai kaya kowa nata san barka da sa albarka



Biki nata matsowa yan uwa na nesa irin su Anty Rabiela, Anty Shuwa da anty Umma tun biki nasaura 1weeks suka iso Nigeria, yeeeeeeeee fada bata lokaci, Yan katsina, zaria da yan abuja duk sunzo Kai Sulaiman yayi goshii bikinsa yayi jama'a bana wasa ba, haka Faty da Family mijinta duk sunzo, Abdul, Hafiz duk an yi gayyata babu zama babban waaa na aure, Inna kam ai walima na musanman ta shirya, wanda su Mom fauxy, mom musa, mum ishaq ne a gaba gaba, Mami ma tap gayya tayi banda yan katsina hadda jama'arta nan kaduna dan Sulaiman na hannun dabanta ne, ran kamu Amarya tayi kyau haka ango kamar kasacesu hmmmmm Afrah kam tayi wani mugun kyau ita da Ahmad ga girma da yaron yayi kowa daukanshii yaketayi dan yaron chubby ya had'u walhy *wayyo biebie niji Kaman nasace Ahmad na gudu*🀣

Ran Friday aka daura aure, wanda duban jama'a suka halarta, yinin biki ma yayi kyau so Afrah, Zarah da Husnah ansha kyau an haska, Fatty kam sai fama da gown takeyi dan ciknta ya girma, chan gidan ango amarya ta wanku tasha kyau, haka ummie da jama'arta haka aunty Baraka mai masaukin baki tasha kwalliya kawai gskia biki tayi kyau babu karya.


Kafin a Kai amarya gidanta, gidan surikanta aka fara kaita, nasiha sosai mommy da Daddy sukayi ma amarya haka akayi da ita gidan ta dake bayan government house, Ana kaita shiryawa akayi akawuce Dinner shima dai ansha kyau ankashe naira, washe gari bud'ar Kai kuma akayi walima ranan kowa yatse.. *Allah bada zaman lfya*
Amarya xaria zata fara zama sabida school, weekend wai xatayi a kaduna.









Fatty ma ta Haihu baby girl, time din Ahmad yayi girma sosai kusan 5 months, har Abuja aje kasa suna wanda ya had'u sosai anma baby sunan Mommy Musty Rakayyah za'ana kiranta da ifrahhhh

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Haka rayuwa taita tafiya cikin dan watani kowa na cikin farin ciki da kuma walwala, Bud'i da haske da D'aukaka Daddy ya samesa, haka Sulaiman, Abdul sai Hafiz da Bussine ya amshe shi sosai, Abdulnaser da Afrah Musty da Fafy kowa na cikin kwanciyar hankali shida iyalinsah.

Husnah ta haihu itama bby boy Muhammad suna cemai Hanmmad.


Mommy da kanta taba Abdul Afifah dukda yanzo ta shiga jss3,da hannu biyu Abdul ya amsa Afifah, Daddy da Inna sunyi murna sosai da wanan had'i haka Sulaiman, Hafz, Faty da Afrah, kundai san Afifah da watanta tar so bawani problem aka samu da ita ba shima Abdul din dake ba galfrd gareshi ba duk babu wani matsala da'aka samu da tashiga ss1 za'ayi auran, Hafiz kam yarinyan uncle Isma'l kanuwar Zaynab yakeso a chan katsina Rabi'atu amma Ummie akecemata.

Yanzo Mommy babu ruwanta Lafiya lau take zaune da kowa daka yan katsina har yan zarian, da bar shiga k'awaye yan karya yan uwanta sisters dinta da yaranta sune friends dinta.


Anty Zulaiha tayi aure wani abokin Daddy ta aura itace ta biyu, gidanta nan a shooting range.












*SEVEN YEARS LETTER*

AFRAH ce zaune a wani parlor da yaji kayan more rayuwa iri iri, sanye take da super wax dinkin fited gown, tayi kyau har ta Gaji, Afrah tayi Kib'a kadan ba sosai ba, da kunga ta, Kunga yar gayu kumaa mai kudi d'an yanzo restaurants 2 gareta ga brkry 2 shima sanan *Afreey house of cakes & ice cream* da ba a dade dayin launching din bud'e wajen bah, ga laboratory da take da shii na kanta (kuu Afrah tayi kud'i wallahi)
wani littafi take dubuwa, yaraney su uku na hango biyu mata wanda da ganinsu twins ne bazasifi 4yers ba sai na mijin a bayansu wanda baiwuce 6yers ba yana binsu, a guje twins din suka haye kujeranda Afrah ke zaune Kai suna cewa"Mami kinga Ya Ahmad ko? Tsayuwana na gyara da kyau ina kallan yaran dan dazo banga face dinsu ba.. Lol koman su daya da Afrah komai irin na maminsu sakin baki nayi ina kallan yaran dan sun birgeni sosai

"Mami kinga fa uztaz hadi ne yazo wai bazasuje ba, Anty Sa'a ta masu magana wai o'o" ya karasa maganan yana kanne idanu

Kallansuu Afrah tayi sanan tace "Oyaa Najma, Najwa tashi ku wuce ko a fasa zuwajen su Inna har wajen Ummie da Abbama bazakuba, tinda bakusan karatu"

Cikin sauri suka tashi duka wuce Afrah tabisu da Ido tana murmushii, ta ci gaba da duba takardan, tana Zaune Abdulnaseer yashigo parlon, xama yayi kuasa da ita gami da jan hancinta, aje takardan tayi nata kallanshii cikin so da k'auna" ina angels dina suke? " shima naganshi cikin 3 quarter da white T-shirt yayi kina na jindadi da kwanciyan hankali, gawani fresh dayayi, Dama Abuka da handsome ga kuma mud'i

"Suna chan suna karatu ustaz yazo"

"Ohh hakane"

"Suna gama sai muwuce kow" tayi magan tana daga mai gira

"Ina xamu?"

"Gida mana yau ai karshen wata, tin jia mommyn Ifrah(Faty) tace sun shigo kaduna "

"Hakane fa meeting kow?"

"A'a yawo"AFRAH tace tana mik'ewa tsaye

"Zan kamaki yarinya"

"Toh gani kamar a kama Amma babu dama" tace ta rugawa a guje, tashi yayi yabi bayan ta yana daria

Bayan su Ahmad da twins sun gama karatun k'ara shirya masu akayi cikin wasu designer gown na Najma Pink color na Najwa pitch color sai wani while hula na gayu sai low fas kowa kalan gown dinshi hadda wani side bag na gayu naga an masu crossing sai kamshi sukeyi πŸ’‹πŸ˜ twins sun bani sha'awa wallahi, Ahmad kam shida Daddysu shadda suka fara tas dikin 3 quarter suyi kyau, Afrah kam cikin lace na ganta mai uban tsada back da touch din red.. Hmmm sunyi kyau over, mota suga shiga sai gidansu Daddy.

ABDUL kam Afifah na ss1 aka daura masu aure, time din she was 15yrs, da farko NNPC yake aikin, Afifah na ss2 tayi waec, result na fitowa, shida ita sukawuce Istanbul chan Afifah tayi degree, inda shikuma yake aiki dawani company kuma yana sch din shima, 4 Afifah tagama sch dinta shima 2years kawai yayi ya kanmala, bayan Afifah tagama karatunta ne suka dawo Nigeria, suna dawowa ABDUL yafara aiki a wani babban company nayi motoci, Afifah kuma tazama lawyer sai da suka dawo Nigeria Afifah ta Haifa seeyama mai kama da Abdul sak.

Sulaiman ma yayi kudi sosai, Humairah kam tana aiki a ministry of Education.
Hafiz yazama babba dan kasuwa k'asa kasa yake fita siyo kaya matar shii Ummie kuma Norse ce Babba a nursing home da kenan kaduna





Malali sukayi direct, Gwanga road suka shiga daka frkon layin gidan yake, wani katafaren gida ne upstairs, horn yayi gate man ya budemai ya shiga, a k'arshe yayi parking dan duk an rigasu zuwa" lallai yau muyi latti" Afrah tace

Muryan yaran sukaji suna cewa " Mami pleasemu sauka"

"Babu mai fita sai nagama parking" tare suka fitoh yaran sukai ciki a guje suna kiran sunan yan uwansu.

Babban parlor ne mai girman gaske, Daddy, Musty, Hafiz da Abdul na hango cikin Parlorn, karasa wajen Afrah da yara suyi dan gaidasu, gaidasu sukayi suka amsa cikin fara'a, Abdulnaser kam sai da ya fara zuwa wajen da Inna mommy, Farty, Afifah da sauran yaran suke sanan yayi wajen su Daddy.

Hira akai tayi sai da akayi sallan azahar sanan suka zauna a makeken dining table dn cin abinci, kowa cikin shigar alfarma, Sulaiman da Humairah yaransu biyu Abdullahi(Khalifa) da Maryam, sai hafiz ya zama dan kasuwa sosai shida matar shi ummie suma yara biyu garesu salis( hanif) da Aliyu, Adul da Afifah kam 1 seeyama, sai Fatty da Musty yaransu uku Ifrah, khadija( Afrah) masake dn Afrah sai Khalid, haka sukeyi duk karshen wata su hadu da karfafa zuminci, bayan sun gama nasiha Daddy yayi kamar yanda yasa ba sanan suka cire mutanan da zasu Kai hajji wanan year din, bayan sun gama aka rufe taro da addu'a, kowa ya dau iyalinsa, Sulaiman da nashi iyalinsa gidan Ummie sukayi haka Abdulnaser sa nashi iyalin, Adul da hafiz kam nan gida suka barsu tinda su yan gida ne.





Haka rayuwa yaci gaba da tafiya bad'i daukaka da kwanciyan hankali kowa yasameshii, duk bayan wata biyu suke zuwa katsina tare da shatara na arziki Arfah sister Afrah ma 2 months ya rage ayi aurenta a Sadiya zasu zauna da mijinta sai Fahad ya kusa kammala Masters dinsa yana U.S, Mommy da mami sosai suke zuminci a tsakaninsu, Yanzo Mommy babu ruwan ta yada duk yaro na kowa ne, gidanta fal da yan mata datake rik'ewa na yan uwa kowa kirki takemai kuma lfya take zaune da kowa cikinsu.


Bayan bikin Arfah ne gaba daya su suka wuce Umara, hadda su Mama, uncle Junaid, uncle, Kannan Daddy, anty Zulaiha wanan karan hadda Xainab da mijinta Muhammad da yaronsu Masjid, gasu Nana Azeezah,Inna Safeya da dai yan uwa da yawa, 2weeks sukayi duk suka dawo Nigeria amma banda Afrah day Abdulnaser Su zasuje New York, suka jona Ummie da yara sukuma suka harba gaba.



Abdul na san Afifah kuma yana kula da ita haka itama kasancewar goyan Afrah yasa baya samun problem sam daka wajenta, Daddy, mommy Inna da sauran yan uwa kowa nasan barka da rayuwar auransu.

Fatty ma Alhmdulillahi sai godian Allah bata problem, haka Hafiz ma Alhmdulillahi

Afrah kam ita ta dabance kulin mijinta kara santa da k'aunar ta yake, haka dangin mijinta, itama

Please Login or Register in order to submit comment