Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su har suka kamma duk abinda zasuyi yau, Husnah sai sana'arta takeyi watou daukan selfie haka Xee bako ma san camera kaman mee... πŸ˜‚ bayan sungama bedroom din AFRAH sukayi AFIFAH nabiye dasu sallah suka farayi sanan AFIFAH tajuyo masu indomie din da tadafa a babban tray wanda yasa vegetables ga eggs da ta yayyaka a kai decorating sosai tayi ma wanan indomie(rainon AFRAH) nan ma kafin a fara ci sai da HUSNAH ta dauki indomie dinan picture, haka suka zauna suka ci abinsu ga juice mai sanyi suka kora da shii, bayan sun gama kwashe kayan Afifiah tayi sanan ta gyara wajen tass dawowa tayi tazauna kusa da zarah, kallanta AFRAH tayi sanan tace" oya madam tashi ki dauki qur'aninki kije kiyi hadda gobe Saturday" babu yanda tayi haka ta dau Qur'anin tayi gaba, nan aka bud'e chapter na hira kowa nata bada labari nan Husnah Kebasu labarin nata saurayin hanci da baki Afrah da zarah suka sake suna kallanta d'ansu basu tabajin labarinshi ba

"Amma ke kam baki da hali, yaa ma akayi bamu sanshi ba wai" AFRAH tace tana watsama Husnah wani kallo Zarah kow taguma tasa d'an takasa magana


"Babes dama zan fad'a maku ai, kawai da bama tare bai dade sosai damuka dawo dating ba, shiyasa inyazo daukana anjima sai duk nakaiku kugaisa"


"Ohhh toh Allah tabbatar mana da alkhari"Zarah tace

Duk suka amsa da ameen, haka dai kowa yaita bada labari saurayin shi( kun dai san emmata insun had'u hiran kenan) k'afe 5 saurayin Husna IMRAN yazo gaba d'ayansu suka fita a kagaisa takuma gabartarmai dasu sanan sukayi ma juna sallma suka wuce, basu kai ga shiga ciki bah Mahmoud na Zarah shima ya k'arasu gida ta koma ta dauko bag dinta yayinda su AFRAH suka k'ara wajensa dan gaisawa, tana fitawo itama tayi masu sallama tayi gaba, aysha, Xee bako,jiddah kam da kansu suka wuce dan nasu fiance's din basunan sunyi tafiya, haka dai suka rabu AFRAH sai godia takeyi masu.










_washegari_
K'arfe 12 a garin kaduna yayi ma su uncle Isma'l, uncle musa, uncle Junaida da Uncle Umar brother din Mami, tarba mai kyauwan gaske suka samu dakawajen Daddy ga abinci mai dadi da AFRAH da zainab sukayi masu, Mommy ma har side d'in bak'i taje tagaidasu babu yabu babu fallasa, bayan sundawo daka masjid zama sukayi suna tattauna maganan auran yaran Uncle Junaid ya yaba sosai da hakin mutunci da karamci irin na daddy, sai bayan sallan la'asar bak'in nasu suka iso dai dai lokacin da akazo neman auran Fatty, ganin irin Motocin da keshigowa gidan suna parking yasa Mommy dake tsaye ta sama sakin baki da hanci tana ganin ikon Allah, sai da motoci 6 suka shigo gidankuma duk babu na banxa ciki, maza uku ne suka fara fitowa nan da nan su Daddy suka taresu cikin fara'a jagora sukayi masu har parlorn b'aki, kaman Amafarki ta hangi _Aunty maijiddah_cikin wani arnan lace wanda ak'alla kudin lace dinan yayi 150k gawani mayafi da handbag duk zafafa, chan kuma ta hango wasu mata su 3 *aunty Baraka* ce a gaba itama cikin wani masifafan material wanda nakasa kane kanshi ga mayafi, talalmi da handbag duk masu shegen zafi sai sauran mata Biyun Atanpace jikinsu super Holland suma sunyi kyau sosai duk Mommy na kallansu takasa motsi babu abinda yafi bata mamaki kaman ganin aunty Maijiddah cikinsu, cikin sauri Mommy takoma bedroom chanza kayan jikinta tayi zuwa wani lace(πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚ Mommy kenan...) Toh babu laifi tadanyi kyau

Su Aunty Baraka kuwa parlorn k'asa suka ja birki, zama duk sukayi nan da nan Zainab da su Lanta, Salamatu, Atika da sauran y'an aikin gidan suka shiga jere masu kayan motsa baki iri iri da kala kala, kafin kuce mai sun cikasu a girke girke, snacks, drinks kala da ban da ban, (dan kansu yan akin gidan sunci burin wanan ranan dole su fidda Afrah kunya kaman yanda take darajasu da mutuntasu) bayan sungama gere duk abinda yakamata tsawa sukayi suka gaishesu sosai cikin ladabi duk suka amsa cikin Fara'a suna godia
Dai dai nan Mommy ta sakko tana smiling gami da cewa"sannunku sannunku, sannunku dazuwa, Latana ya kika barsu nan baku hauro dasu ba? "


"A'a nan ma yayi mungode sosai" inji Anty baraka

Smiling Mommy tayi kace" duk dahaka banji dadi ba wallahi"

"Babu komai" Ummu Safeey tace tana smiling ita ma, gaisuwa sukayi sosai cikin barkonci nan Aunty Maijiddah ke sanar da ita ai ita kawar auntyn angoce watou Aunty baraka, smiling Mommy tayi kana tace" kawai dai aunty ango" daria duk sukayi nan mommy ta k'ara gabatar masu da abinci, basuci abincin ba sai drinks da snacks, su Ummu Safeeya da aunty A'isha suka bukaci ganin Amaryan tasu, wani haushin Suka ba Mommy talura y'an boko ne iyayinsu yayi yawa, babu yanda ta iya smiling tayi masu gami da cewa "bari na kira maku ita"






B'angaran su Daddy Ma Komai cikin Mutunci Da haramci sukayi komai d'an Familyn ABDULNASEER sosai suka yaba da halin girma irin Nasu Daddy da yan uwansa, haka suma su Daddyn sunyaba da halin mutunci irin nasu, Daddy yaso a had'a bikin gaba d'aya hadda na Fatima toh sai Uncle Umar yace yayi hakuri ba dan Daddy yaso bah hakka yahakura tsakani dai Wata daya da sati d'aya ne daidai, godiya sosai su Uncle Muhammad sukayi nan dai sukayi duk abinda yakamata kaman bada kud'in gaisuwa da na sara rana, godia suka kara yima junansu kana suka tashi Dan tafiya, kayan abincin tas drinks da snacks su Sunusi(yan aikin gidan) suka kwasu suka samasu cikin mota kasancewar basu tab'a komai ciki ba, godia suka k'arayi ka duk suka shiga mutocinsu, sai da Su Daddy sukaga fitan su gidan suka koma ciki da fara'a kunshe a fuskarsu.




Side din su Mommy kam. Bayan Zuwan AFRAH gaishesu tayi ciikin ladabi da biyyah dakuma fara'a fuskanta, duk suka amsa cikin sakin fuska nan suka sa AFRAH tsakiya Aunty A'aisha(aunty) tace a daukesu pictures haka kuwan akayi Picturs suka dauka sosai ita dai Mommy tana ganin ikon Allah da sabon salo, _Aunty Maijiddah_ taceh" baki shigo bah pictures din namu ba Mommy" tana murmushi

"Ai barin ku nayi kuyi da Amaryan taku sosai" tace hakan ne kawai amma ita tagaji da ganin sabon iskancin su, sai kace sunzo neman suran diamond ko gold

Voice din Ummusafeeya ya katse mata tunani inda take cewa" kuma Amaryan namu mai kyau ABDULNASEER yayi dace ga hankali" daria duk suka kana sukace "Aikuwa dai Alhmdulillahi" gaba daya Mommy ta gaji dasu haushe suke bata iyayinsu yayi yawa hakan dai babu yanda Mommy ta iya haka tasha picturen nasu badan taso ba tawani had'e fuska babu ko d'an smiling babu(sai kace wata gunkiπŸ˜‚)




Hmmmmmm fad'an irin kayan sa ranan da su ANTY BARAKA suka kawo bat'a lokaci ney wallahi ku kanku inda zaku ga irin kayan kuda kanku zakuce sun shiryama bikinan(toh abinda ba a tabayi ba) kayana sosai bana wasa ba, d'an komai buhu 2 suka sauke NAGANI INA SO kuwa yanda kukasan kayan lefen wata amaryan Mommy tuni tafara jin wani zafi zufa har zubu mata tacikin kaya yakeyi(yiriri nanayi injiniπŸ’ƒπŸ˜‚) haka dai su aunty bakara suka bar gidan cikin farin ciki, bayan duk girke girken sun sashi cikin mota, Mommy dai bacikin kwanciyan Hankali ta rakasu ba, sai dataga fitansu gidan sanan tadawo ciki, k'ara hangan kayan kawai datayi yasa gabanta dad'uwa, bedroom dinta tayi cikin sauri watsar da mayafin jikinta tayi sanan tajawo phone d'inta Numbern Fatty tashiga dialing amma har yagama ringing batayi picking bah, sai datayi mata miss calls 8 amma duk no answer Mommy jitayi kaman zatayi hauka tarasa yanda zatayi, shawara ta chanza Numbern k'awarta Hajia Amina tashiga dialing ringing 2 kuwa ta dauka

Wani dugon ajiyan zuciya Mommy ta sauke

"Lafiya kuwa? " hajiya Ameenah tace daka can bangaran


"Toh da Sauki dai, yau akazo neman auran AFRAH da sa rana" Mommy tace


"Toh sai maiyafaru?

"Wai fa duk d'an kar abin yayi kyau yasa ban kiraku bah, kuma kinsan babu wata matan da zatazo min gida daka katsina ta zauna lfya wai d'an kawi xa'azo neman aure"


"Ni har yanzo baki fadamin komai ba, wani mugun abun yafaru ne?


"Hmmmm hajiya wallahi inkinga irin kayan arzikin da suka kawo abin sai yabaki mamaki yanda kikasan wasu shahararrun masu kud'in Nigeria, rawan kan da sukarinka yi kuwa kaman sunzo neman auran diamond d'an bama zance gold ba, ko Familyn mijin da Fatty zata aura sun fisu kud'i amma basuyi irin abu haka kaman na wanan ba, wallah abun duk ya dameni" tak'arasa maganan kaman zatayi kuka


"Iko Allah amma Hajia nasha fad'a maki cewa AFRAH y'ar baiwa ce Allah ney duk yake bata wanan ba mutun bah, yakamata kigane haka mana, tin yarinyan na k'arama takeda wanan baiwar kike dakusheta amma hakan duk bai t'aba cigabanta ba, gaba d'aya kin raina ma yarinyan gashi tin ba a je ko ina ba cigabanta sai baiyana kanshi yakeyi kawai ido zakisa ki kalle ikon Allah"


Tin da Hajiya Ameena tafara magana bak'in cikin Mommy ya k'aru gawani zafi da zuciyan takeyi mata, sai datayi gyaran Murya kana tace" sannu da k'okari dama kina zaune da ni ne bada zuciya d'aya ba shiyasa duk zakice haka, amma ba laifinki bane nawa da har na sanar dake damuwata, biki kuwa duka biyun babu wanda zaki halarta dan nanyi canceling naki daka cikin yan gayya" tana gama fadan haka ta kashe kiran


Side din Hajiya Ameena kuwa daria tayi kana tace" sai bak'in ciki yayi ajalinki kuwa zancen kinyi cancel dina cikin yan biki ai inanan za'akawo mana I.V mayb ma muna meeting da uwar angon ko auntyn angon d'an haka sai yak'are maki chan.



FATTY takira mommy nan Mommy ta zayyano mata komai da irin kayan da suka kawo mamaki sosai Fatty tayi nan sai tace ma mommy zatashiga kadunan gobe kodan tazo taga kayan, tin 11 na safe Fatty ta iso kaduna, sosai kayan suka bata tsoro da kuma mamaki ranan dai wuni sukayi cikin bedroom suna maganganunsu dasuka saba.


AFRAH kam bata masan sunayi bah, hakan gabanta kawai taitayii, AFIFAH kuwa rawa tasha ranan hadda na ban mamaki saboda Murna, a rananne yan katsina sukayi masu sallama suka koma Sunday kenan.


Sulaiman yashiga tashi hankali sosai kasa hakura yayi har sai dayaje yasamu Daddy ya sanar da shii kallanshii da kyau daddy yayi kana yace" Meyasa toh tin tini baka sanar da ni ba sai yanzo da lokaci ya wuce? "

"Daddy wallahi bansani ba ni kaina"

"Yanzo dai lokaci ya kure sai dan kayyi hakuri Allah sa hakan ne mafi Alkhari duk da da hakan yafaru zanfi kowa Murna da farinci amma kayi Hakuri Allah zai musanyama da Alkhari kaji ko? Allah yayi ma Albarka ya kuma kawo ma tagari"


"Ameen ameen Daddy nagode sosai Allah kara girma"


"Ameen Sulaiman, yaushe ney tafiyankan naka? "


"Nan da 3 days ne insha Allah"

"Toh Allah temaka yakuma bada sa'a, kila matar tachan bauchin inda zakayi bautan k'asan"

Smiling kawai Suleiman yayi baice komai ba, nan daddy yake sanar dashi game da rashin isowan kayansu, kwantar mai da hankali Sulaiman sosai gami da Addu'a sosai Daddy yaji dad'i yaita samai Albarka, hira suka d'an yi kana Suleiman yabar side Daddyn.





Suleiman nafita Mommy nashigowa zama tayi tana karema daddy kallo, shima zaman shi ya gyara sanan yace" ashe wai Suleiman san AFRAH yakeyi sai yanzo yake sanar dani"


"Bangane ba kamar yaa? Mommy tace tana zare idanu


"Wai san AFRAH yakeyi amma baiyi magana da wuri ba sai yanzu, amma da hakan yafaru da nafi kowa murna wallahi"


"Tabdi gam, gara da Allah yasa hakan takasance d'an bazaitaba yuwu ba wallahi, haa kawai yarinya duk tabi ta addabi rayuwa ta"


"Amma ke bakida hankali, dama abinda na dade inason ji kenan gashi kuma yau kinfada, bak'in halinki da bak'ar zuciyar ki yasa Allah ya chanza mata da ABDULNASEER ba Sulaiman ba, kinbi kinsama yara ido kin rai nasu kina ganin baza suzama komai ba ko?toh ai sai ki hana in Allah yabasu kuma so nawa yaron da ba naka ba yatemake ka d'anka na cikin ka baima ba?" Ya karasa maganan yana watsama Mommy harara



"Wai duk kan wayanan banzayen yaran ne yasa kake jifana da munanan kalamai? "


"An jefeki da munanan kalaman ai baki da tunanin ne, kuma karki kuskura ki kuma kiran yarana da banzaye d'an ba banzaye bane su"


"Nice banziyar kenan ko alhaji?kan wasu yara chan kana cimin mutunci" takarasa maganan tana kuka


"Duk yanda kika dauka hakan ne, kuma ko a titi na tsinto su baici ki kalle idona kice masu yara chan ba, bare yaran d'an uwa na d'an haka ki kula sosai" Yak'arasa maganan yana shiga toilet



Mommy kuwa ranan kuka sosai tayi zuciyanta na zafi kamar zanfito waje haka dai Fatty taita lallashinta, AFRAH kam batama san sunayi ba d'an tun ran Saturday Mommy batayi mata magana haka koda Fatty tadawo ma ko magana batayi mata ba, sai AFRAHN ce keyi masu.



Yaya Suleiman har bedroom yashigo yayi Afrah Allah sanya Alkhari gami da Addu'a kaiwa lokacin lfya, sosai AFRAH tayi mai godia gami da Addu'a bashi wata ta gari, tindaka ranan Sukadawo kamar daa suna respecting junan su sosai koda ABDULNASEER yazo har inda suke Suleiman yazo suka gaisa, ashema rana d'aya zasutafi camp sai dai shi ABDULNASEER sokoto zaije ranan dai hira sosai sukayi kaman sun dad'e da sanan juna.



Mommy kam gaba d'aya tasama kanta damuwa kulin cikin ciwan kai take, Suleiman yana mamakin halin Mommy na bak'in ciki kiri kiri Addu'a dai yakeyi mata Allah ya ganar da ita.


Ana gobe ABDULNASEER sai wuce shopping sosai yayi ma AFRAH yakawo koda Mommy tagani ko magana takasa, haka dai abubuwa yaita tafiya ko da Suleiman yazo tafi bai samu wani addu'an kirki daka wajen Mommy ba d'an batacikin hayyacinta Daddy kam Addu'a sosai tayi mai gami sa samai albarka.




Haka abubuwa keta tafiya bikin Fatty nata matsowa d'an baifi saura kwana 20 bah, randa Mommy tayi ma Daddy zancan zuwa Dubai cewa yayi babu inda za'aje ya riga yasa amai order kayan gado da kujeru daka China na FATYY DA AFRAH ranan Mommy tayi kuka kamar menene d'an tariga tagama yad'awa zataje Dubai...
[12/18, 09:04] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*


_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch β™₯ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~🌸


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_




*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_


*Happy birthday sweet sis(Afrah bhai)wishing long life and prosperity, may Allah bless your new age much love n stay blessed* ❀️ ❀❀❀❀


_page 60-61_






*H*aka rayuwa taita tafiya abubuwa nata faruwa mommy kulin cikin k'unci take da bak'in rai, gaba d'aya Daddy baya shiga al'amarinta hakan gaban shi kawai yakeyi, kayansu dai haryanzo babu labari kabarma Allah komai a hannunsa duk yanda ya tsara mai kyaune a gare shii.






Duk wani haushe da Mommy keji sai tanemi saukewa a kan AFRAH amma sam bata nuna ma tadamu hakan datakeyi yana k'ara b'ata ran Mommy, haka dai lokacin Bikin Fatty keta matsowa Mommy ta k'ara d'aga hankalinta coz duk yanda taso tsara bikin bahaka yazo ba, biki taso tayi nagarari na bugawa a jarida amma kuma sai kokai yazo mata a juye hakadai tai ta dauriya amma da kamata kallon tsaf xakagane tana cikin damuwa.




Yau ne Aunties na Musty zasu kawo lefe dan haka gidan cike yake da jama'a d'an tarban su, as usual abinci mai lafiya da snacks AFRAH tayi da taimakon y'an aikin gidan komai ya kammala, fita duk sukayi a kicin din da gabatar da sallah, bayan duk sun idar k'ara gyara ko ina akayi waje dai yayi kyau masha Allah, mommy da mutananta sunyi kyau babu laifi haka ma Anty Ramlat matar uncle Isma'l, zaune suke anata hira, k'arfe 2:5pm daidai y'an kawo kaya suka iso, suna dayawa d'an zasukai su 10 sanan yan mata 4 da alama dai familyn Musty sunada yawa, y'an gayune sosai



Tarba mai kyau suka samu daka wajensu Mommyn da sauran Mutanan, sun zauna kaman da minti 3 wasu mata su suka fara shigo da akwatuna da alama dai musaman akazo da matan da shigo da kayan d'an daganinsu ba wasu bane cikin familyn haka sukai ta shigowa da akwanunan wani mutun daya ya dauko wani kuma sai su biyu sai da suka shiga da guda goma sha biyu sai wasu 2 na Mamman Amarya da babanta kowa akwati 1 a gefe nan fa dangin Mommy suka hau guda da shewa nan aka shiga bude kaya wata y'ar dattijuwa ne Inna Asabe(kanuwar Maman Mommy) tashiga bubbude kayan, aiko kayane bana wasa ba d'an an ruba januwa komai 12 ne a ciki kud'i yayi kuka a wajen kayane masu kyau da tsada ga ku'din dinki 250k ni basan ta ina zan maku bayan kan kayan kugane ba, English gold gasu nan har iri 5,kawai dai sai kun gani (ni kaina *Biebie dee* ware eyes nayi ina kallo d'an kayan sun wuce dani gskia) kowa sai san barka yake da sa Albarka 100k suka bada tukwaci sanan uban girke girke da snacks kala kala Su Aunty Lailah sai godia suke haka su Anty Azizeema sai da suka rakasu har bakin motocinsu kana suka juyo ciki, nan fa suka bud'e sabon chapter na ihu da guda AFRAH da Anty Ramlat dai naganin ikon Allah, AFRAH sosai tayaba da kyan tasa albarka gami da Addu'an Allah basu zaman lfya haka Anty Ramlat ma, ganin irin kayan da kayi ma Fatty ne yasa Mommy tad'an ji dad'i cikin ranta damuwanta yadan rage ko babu komai yarinyanta tayi goshi, wunan wanan ranan gidan cikin shewa yake sai bayan sallan Isa'l Daddy yaga kayan Albarka sosai yasaka gami da masu Addu'a.





Ranan Wednesday Fatty da friends dinta yan Baze suka iso kaduna, tarba mai kyau suka samu daka wajen Mommy har ma da Daddy batada case da Friends dinta na kd coz duk Aseeya duk takai masu invitation card, amarya Fatty ce kawai tayi lalle sai AFRAH da friends nata Aseeya da Hayfah sauran kam wai bazasuyi ba, a ranan ne zasuyi *bridal shower* a syd resort duk wanda ke kaduna dai yasan tsadan hall na syd resort, *ILAURAH*itace zatama ta make-up a duk ka events din friends kuma *LAYYAJEY* cezatayi masu wanan abu duk Anty Musty ta dau nauyin yi wato Anty Lailah, Fatty Amarya tashirya cikin pink color weeding gown kanta yasha fixsing a xubu da gashin har gadon bayanta sai wani crown πŸ‘‘ a saman kanta sai wani abu da ta aza saman gown a rubuta *bride to be* sosai *ILAURA* ta fitoh da ita cikin make-up dinta, kai kai gaskia Fatty tayi kyau ba karya wallah friends kam da su AFRAH white gown duk suka saka wasu daka cikin su sunyi daurin turban wasu kuwa irinsu HANEEFAH komai basu sa bah suma haka *layya jey* ta masu makeup kyau sosai sukayi gskia sunyi kyau masha Allah AFRAH tayi kyau sosai haka su Zarah sukai tacewa dawasu daka cikin friends na Fatty amarya, abindai sai wanda yagani haka dai suka dunguma sai syd resort haka amarya Fatty da friends da yan uwanta yamata suka ci Bridal shower depphotos ya kashe masu picture duk abinda kukadan anayi a nakuma ci a had'edan bridal shower na yaran masu kudi kuma yan gayu toh anyi a na fatty haka dai suka k'are bridal shower, sun dawo suntadda yan katsina sun iso, bedroom mai kyau da girma a kaware ma Inna, haka ma sauran jama'un, anty Rabi MA tazo mahaifiyar AFRAH y'an Zaria ma dam da gida, washe gari *KAMU* wanda za'ayi a holiday conference ranan ma kwalliya duk suka sha amarya fatty ma tayi kyau ba na wasa ba da friends dinta AFRAH, Zarah, husnah ma duk sunyi kyau haka Mommy da mutananta ma, haka aunty Rabi da sauran yan katsina,Inna ma kwalliya tayi sosai tana sa kaya tana masifa wai kawai zataje sabida ubanta amma d'an uwarta da ita kanta amaryan ba, haka akaita bata hakuri yan uwan Mommy ma sunyi kyau ba laifi. a ranan ne ya sulaiman ya dawo gida, babu bata lokaci suka hau shiri shida ABDUL da Muhammad bayan duk sun je sun gaida mutan gidan, Abdulnaseer ma yadawo shima shiryawo yayi shi da su Ummie, aunty baraka, Humairah da Aisha suka dau hanyan holiday conference


Biki yayi biki haka waje yayi waje Amarya da ango sunyi kyau sosai haka friends dinsu, familyn Musty ma sunyi kyau cikin nasu anko masha Allah kowa yayi kyau, biki yayi kyau anci ankuma sha ankuma dauku pictures anyi rabon abubuwa iri iri mai dauke da pics na ango da amarya

Abdulnaseer har wajen da aunty Rabi(Mami) da Inna yaje ya kwashe gaisuwa haka su Ummie da aunty baraka wannensu ya yadda da junansu, wajen bikin Muhammad friend din Suleiman yaga Zainab din Uncle Isma'l nan dai suka dai daita kansu bayan tagama yanganta





Wajen *kamu* akayi sa lalle, haka dai taro yatashi kowa yana san barka da sa albarka y'an *biebie dee nvls group* ma sunzo suma duk sunyi kyau amma babu wanda yayi rawa cikinsu zaune dai suke, sai kashe pic's sukeyi da AFRAH da ABDULNASEER da Afifah data likemasu dan sunyi masu kyau. πŸ˜‚ Lol







Yau Friday kuma yaune jama'a suka saida daurin Auran Mustapha Ahmad D'anbatta da Fatima Shu'aib Mani a masalacin Al-manar dake kaduna, jama'a da dama sun halata aurin auran kamar manyan yan siyasa dakuma manyan yan kasuwa, ango Musty yayi kyau sosai sai smilling yakeyi haka friend dinsa sai daukan Pics sukeyi da friends, y'anuwa da kuma abokanar arziki




A gida ma amarya tayi kyau sosai ita da friends dinta haka mommy da friends dinta da yan uwanta haka yan katsina ma AFRAH tayi kyau cikin ankonta dass gown din ya zauna a jikinta, Afifah ma tayi kyau sosai masha Allah, nan dai ango da friends dinsa suka iso anata pics, haka dai akayi yinin biki komai Alhamdulillhi duk da Mommy ba haka taso bikin yakasance bah, addu'anta kulin shine Allah sa na AFRAH yakai na Fatty data nuna irin kayan sa ranan AFrah sai gabanta yafadi amma kuma tana cewa su Musty sunfisu kud'i sai taji sanyi a ranta, gaba d'aya ta manta zuciya ne abin ba dukiya ba( Nidai nachai Hmmm, za dai mugani)




Kafin magarib akazo daukan Amarya wajen Daddy akafara kaita fad'a da nasiha mai ratsa jiki yayi mata wanda yasata zubda hawaye, haka Inna ma da sauran yan katsina nasiha sosai sukayi mata mommy ko babu wani nasiha bare wani addu'a gani kawai take y'arta ta gana dacewa da miji tinda akwai kud'i nan dai Anty Ramlat da Anty Azeezah da ina da wasu yan uwan Mommy suka wuce dan raka amarya Fatima.
Friends kuwa ga mota nan sai wanda suka so shiga AFRAH da Afifah kam ABDULNASER yakaisu Zaynab kuma Muhammad, Zarah, Husna, Haneefa da Fa'izah ma duk samarinsu suka kaisu, sun iso gidan Lfya tarba mai kyau suka samu saka wajen dagin Musty nan dai akayi abinda yakama side Fatty na nan kaduna yayi kyau babu karya daddy yayi k'okari sosai suna shirin tafiyane akace su tsaya dan uwar angon sun shirya dinner a cikin garden din gidan kasancewar duk da kwalliyansu yasa basu damu ba nan Aunty Azeeza tashiga kiran wayan wai suzo akwai dinner a family house na ango Mommy taso taje amma Daddy ya hanata zuba bubu yanda zatayi haka ta zauna badan taso bah.





Nan aka kara shiya amarya da ango sunyi kyau haka Friends ma duk kowa yayi kyau masha haka aka yi dinner, anci kuma ansha anyi pictures sosai, 12 dare su Anty Ramlat da sauran yan kawo amarya suka wuce tare da sha tara na arziki yayin

Please Login or Register in order to submit comment