Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su Abdulnaseer tazo daka London tabada akawo kuma itace ta dauki nauyi yima AFRAH amarya make-up)

Mommy Da Fatty suma ne kawai basu yii baa sosai suka shiga tashin hankali.
[12/18, 09:04] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*


_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch β™₯ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~🌸


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_




*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_



_Congratulations for d compilation of your sweet n Mazing Novel ITACE 'KADDARA TA!!! Allah bamu ikon aiki da da abinda ke cikin littafin Ameen, more grs to your shining elbow, much love n stay blessed d whole page is yours@Zee Yabour_❀❣❀


_Page 64-65_



Yau ne *Bridal shower* so gidan cike yake dam da mutane babu sauki, tin daka wajen Inna, Mami wajen Amarya ko Friends ne gasunan ba'a cewa komai Mommy kam daka ina sai sisters dinta biyu anty Azeezah da Nana

Abinci kuwa gashin duk wanda kakeso k'arfe 2pm dai wanda wanda zatama AFRAH make-up ta iso ita da yaranta watou *TARA* duk wani wanda yasan manya-manyan make-up artist toh yasan *tara* d'an tayi fice sosai ba k'adan bah zan iya cewa duk wani wanda yafara make-up toh bayanta yake. Taty ce tashigo room din da Amarya take da friends nata nan takeji wai *TARE*ce zatama AFRAH make-up friends kuma *laiyajey*suman tsaye tayi d'an ita sam batama sa TARA ciki bah sauri tayi takoma wajen su mommy dan sanar dasu

"Toh sukuwa wanan wani irin kud'i garesu? " cewai Anty Azezah


"Hmmmm ba wani shwgun kud'i garesu bah, kawai dai sunsan manyan mutane ne, toh sune ke daukan nauyi" Mommy tace

" amma ni bantaba kawowa ita wanda ta daunauyin make-up din zata iya dauko TARA ba" Cewar Fatty

"Toh aiko tunda hakane ashe bamugama ganin abun mamaki ba" Anty Nana tace

" ah'a insha Allah babu wani abin mamakin da zamuji kuma" Fatty tace tana yatsina fuska Mommy ko harara ta kaima Anty Nanan.



AFRAH tayi kyau har tagaji coz make-up mai lafiya akayi mata, kai bazNn iya bayanin irin kyau da AFRAH tayi ba gskia, gashi gown din yayi mugun ansan jikinta dass ya zauna a jikinta
white color ney sai stones din jikin gown din pink, crown πŸ‘‘ ta daura kanta pink color wanda yasha mugun ygara gashin ya sauka har gadon baynta AFRAH taso ta ayi mata dauri ne amma su Husna sukai ta zugata ita da *Mee* da sauran friends har ta yadda da crown πŸ‘‘ din... kai ni wallahi bazan iya yimaku bayanin kyaun da AFRAH tayi ba tayi kyau sosai Husnah, Xarah da sauran friends sunyi kyau sosai cikin gown pink color Husnah, Mee da Xarah komai basu sa kansu ba wai su gayuπŸ˜‚πŸ˜‚ Husnah ansha kyau ba'acewa komai sai selfie akeyi, a nan *syd resort* za'ayi d'an friends na Afrah da kansu suka zaba hall coz basunan babban nan dai suka wuce cikin Motoci na alfarma
Fadan irin haduwan da *bridal shower* Na Afrah yayi bata lokaci ne duk wani abu da kuka san anayi toh anyi shii hakama duk abinda akeci da sha toh anci kuma ansha, Humairah da friends dinta ma sunzo da Aisha da wasu emmata yaran aunties dinsu sai yarinyan anty Shuwa Leemah duk sunzo suma cikin kwalliya irin ta wayyanyun emmata, haka wasu daka cikin emmatan da ke cikin *biebie dee nvls group*ma sunzo suma sunyi kyau sosai AFRAH tasamu gifts sosai bana wasa bah, Husnah uwar pix tayi har tagaji coz ga masu hoto har guda biyu nan dipphotos da Fox photos nan, haka dai taro yatashi kowa cikin farin ciki.
Fatty mamakin irin Uban gifts da AFRAH ta samu dan ita dake masifaar bin k'awaye ko ita bata samu irin gifts din da AFRAH tasamu ba, da Fatty ta kaima Mommy ruhuto kam kasa cewa komai tayi da Al'amarin AFRAH komai a bazata yake zuwa.


🌸🌸🌸
Anty Baraka ce tashigo bedroom din Ummie, zama tayi gami da kallan Ummie kana tace" kai Ummie Abulnaseer yayi goshi komai sai ace za'ayi mai"
"Aifa gashinan kunata gatalashi da Amaryansa"

"Kinsan jiya dai hajiya Umma tazo sai fada takeyi wai sai da muka gama hada lefe sanan ake sanar da ita"

"In banda abinta ai abinda hajia Shuwa tayi ya wadatar ma bayan daukan nauyin yima Amarya make-up hadda fa wasu kudin ta bayar, sanan kuma itama tace wai zatayi? "

"Nima dai abinda nagani kenan"

"Aiko bari nama hajia Ummam magana kinsan dai ba k'aramin aikin ta bane na fiddo da wani event kuma kinga mungama tsara komai kinsan su kud'i ba matsalansu bace"


"Dama kiyi zamanki d'an har takira wata make-up artist wai LVB wai itace zatama amaeya Make-up ran daurin aure"

"toh ita wanda hajia shuwa ta kira fa? "

"Wai dama na event 2 kawai zayi jiya da yau kenan coz zarayi"

"Lallai sudai basu da dama duk wani abin gayu sune a gaba"

Daria Aunty baraka tayi kana tace" toh tashin turai

"Lallai toh duk Allah saka da Alkhari, komai muna zaune akeyi"

Haka akai ta gudanar da biki a side ango kuma suna shirin kuwa *Kamu* daza'a a ceremonical canopies, emmatan na da iyayyen kowa shiri yakeyi
Hance takasan ce a side na amarya ma, Amarya da mai mata makeup suna daki daban anata shiri haka friends ma side Mami da sisters dita da abokan arziki ma hakanne Inna da Mutanan ta ma sunata shiri, Mommy da sisters di tama shirn suketayi


Amarya AFRAH tayi kyau cikin wani arnan race purple color da touch din silver,hand ma silver haka y'ar Purse ma silver sai wani shegen high heels tasa kyau iya kyau toh AFRAH tayi shii haka make-up dinta ma yayi sosai
Friends ma duk sunyi kyau cikin Ankonsu wanan na wane wanan Fatty sosai tayi kyau itama cikin nata ankon AFIFAH kam ba'a cewa komai tayi kyau sosai sunan zaune ana k'ara gyara make-up phone din Fatty yafara ringing picking tayi kana tace"okay am coming" kallan Duk emmatan tayi sanan tace" mari ni nawuce mijina ne zaikai ni"

"Okay sis sai munhade" Husna tace

Babu dad'awa Motoci suka iso irin ta alfarma nan friend aka fara wucewa da yan uwa Zarah da Husna kam kowa saurayinta ne zaikaisu
Da Mami wai bazataje ba nan yan uwanta sukayi chaa a kanta babu shiri ta hau shiryawa, Inna kanta tsaf take nan tafara masifa Wai Suleiman zai jamata latti tana kan masifan ne sai gashi ya shigo cikin kwalliyansa yayi kyau sosai nan dai yakama hannun inna yasata gaban Mota sauran suka shiga baya sukawuce


Mami kam a motan ABDUL take ita da aunties dinsu su uku sauran k'anan Mami kam tuni suka wuce


Mommyma ita da sisters dinta cikin shiga alfarma Mommy take dan sosai tayi kyau haka su Azeezah ma babu laifi sunyi kyau, suna shirin shiga mota phone dinta yafara ringing picking tayi daka chan side din akace " hajia gamunan karasowa"

"Okay Allah kawoku lfya" nan tashiga cikin motan Bala driver yajasu sai *ceremonial canopies* hall dinda yasha decoration mai shegen kyau, iya tsaruwa kuwa hall yasha shii naina yayi kuka, mommy ai tuni tafara nemo yawun bakinta d'an gaba d'aya tanema tarasa *kamu* sai kacewani dinner haka dai akafara shan KAMU familyn ango sunyi kyau sosai cikin ankonsu mommy dai na kallan ikon Allah coz duk uban gayun da take ganin tayi amma dataga wasu sai da ta raina kanta, inada Amarya da ango ke zaunema sosai yasha decoration ABDULNASEER sai washe baki yakeyi, chan nahango yan * *Biebie Dee nvls*cikin nasu ankon sunyi shegen kyau suna picture da Aunty Baraka, anci ankuma sha komai a waye kuma a natse akayishi y'an Musty ma sunzo suma sosai bikin ya birgesu haka friends din Mommy ma

Husnah pictures da tayi Allah kadai yasan yawan shii tayi pics hadda na masifa, tayi da amarya da ango,MaMi, Mommy, inna hada su aunty baraka banda wanda aketayi da friends abundai sai wanda yagani.

Fili akabama ango da amarya dan suyi rawa ABDULNASEE ne kawai ke kayanshi babu kuya AFRAH kama tsaye kawai take takasa rawa, dai dai friends na ango suka shigo cikin gayunsu nan fa akafara lik'e photographs nata aikun su, nan kasama Amarya lalle, Babuwa Masu kyau da tsari aka rarraba haka dai taro yatashi kowa yana san barka.


Ran Friday aka daura Auran ABUDULNASER ABDULLAHI YELWA DA KHADEEJA SALIS MANI(AFRAH) Bayan ansakko dake sallahn juma'a masalacin al-manar dake kaduna, manyan mutane da dama sun samu hakarrta daurin auran tunda kan masu kudi da tan yan kasuwa mango ABDULNASIER yasa kwalliya cikin farar shadda yayi kyau har yagajii baki yaki rufuwa sai smiling yakeyi, gaisuwa yarikayi da yan uwa da kuma abokan arziki anata daukan pictures abundai masha Allah, chan gidama Amarya AFRAH tayi kyau sosai duk da wani make-up ne a face dinta ba amma tayi kyau sosai haka friends ma da yan uwa da abikan arziki duk suyi kyau kowa ciki atanpan ankonshi,su Husna babu sauki tayi kyau sosai anata pics, Mommy, Mami, inna kowa yayi kyau masha Allah nan dai ABDULNASEER da friends dinsa suka iso ana ta daukan pictures kowa yayi kyau, inkun ga mommy kamar mara lfya ita komai ta baibai yazo mata gadai kwalliya tasha amma babu walwala sam a fuskanta ita kadai tasan halin da take ciki ABDULNASEER yareke AFRAH gam wajen pics babu ko d'an kunya nan sai smiling yakeyi da ance Allah sanya Alkhari yace ameen... Haka dai aka gama pics sukawuce a gidan angoma Ummu-Abdulnaseer, aunty Murya, Aunty Rabila, aunty baraka, aunty shuwa, aunty Ummah da sauran yan uwa da abokan arziiki duk sunyi kyau abin sha'awa da birgewa su HUmairah kam gidan su AFRAH sukawuce cin nasu yinin bikin, Mami da yan uwanta yinin biki mai kyau da tsari suka shirya babu wani kida da akayi amma abinci gashin big city rentals services suka dauko suke keta rabon abinci kana da zaune

Mommy ita mamakin inda su MAMI suka iya irin wanan abu takeyi, abunda taso yi kenan a bikin Fatty amma komai yazo mata a karkace, _lol Mommy kenan_ haka akaita cikin yinin bikin cikin kwanciyan hankali anci ankuma shaa Alhamdulillahi, chan nahango y'an *biebie dee nvls group da biebie dee fans club* cikin anko sunyi masifar kyau kowa yaxo hadda wanda basa hawa online da yan labe. Lol kowa yaci gayu sun ci sunkuma sha ankuma yi pics da AFRAH kaman mai Afiface tazo taita raba abubuwa nan wasu suka fara tafiya yyayin da wasu sukace sai sunraka amarya gidanta.



K'arfe 6:00 akazo daukan Amarya wajen Daddy aka fara kaita nasiha sosai yayi maya mata gami da sa mata albarka nan akayi wajen Mami da ita nan ma nasiha mai tsara jiki tayi mata ita da yan uwanta sosai AFRAH ke kuka dakanan akayi wajen Mommy da ita, sunkai Minti 3 amma mommy babu abinda tace sai wani cika da batsewa takeyi mman Heeshmer da Anty Bee ne suce" sallama fa tazo yyimaki anty Bilki"

Mommy da tacika tayi kam, so take kawai ta amayar da wasu abubuwa da ranta kozata samu sauki cikin zuciyanta takuma chusa masu haushi kaman yanda takeji chan tace" sai yanzo ne za'a wani kawomin ita nayi mata nasiha sabida ku butulu ne, na raina yarinya tin tana k'ara sanan nice za'akawo nayi mata nasiha a k'arshe? Toh bazanyi ba duk abinda taga dama tayi wanan matsalanta" tinda Mommy ke kan kika da batsewa aunty zulaiha taje tafada ma inna so Mommy nagama fadan haka inna tashigo side, jikawai sukayi ance" in baki sa Albarkan ba samai ja'ira? Yarki ta cikin ki ma baki sa mata ba re kuma ta wasu inkinsa ba sunanki Bilki ba" nan Inna ta shiga sauke kwandon masifa wanda Mommy batasan ta iya ba, nan kaita ba inna hakuri amma sai k'ara hawa takeyi da inna ta hakura sanan suka fice a side din.


Mommy jin zuciyarta tayi na tafasa a fili tace insha auranan bazai taba albarka ba sakota za'ayi kuma wlhy bazata zaunamin a gida ba, tayi haka dan tabasu haushi takuma b'ata shirinsu sai gashi ita cema ranta ya k'ara baci
Su Axexah ne suka zauna jefanta Nana tace" sai da nace karkiyi komai amma baki jiba gashinan da girmanki an zageki abansu"

"Bazaku gane ba Nana, haushi nakeji naga abubuwa haka nafaruwa Da AFRAH d'an bansata lissafin wanda zasu cigaba haka ba"


"Mtsww toh Ai sai kiyi abinda zakiyi, yarinya dai tayi goshi na lura komai ke kan yaranki ki kikeso yafaru, da ni na Haifa Aftahn ma ashe haka zakimin" Azezah tace


"Ni kikema Magana Haka azezah d'an kinganni cikin damuwa? "

"A'a Yaya bakida wani damuwa fa, ji gidanki kedai da yaranki mubamuce muna da damuwa ba sai ke? Wanan dai sa ma kai ne"Nana tachai

"Ohhh haka ma zakuce mai kuke nufi ne? "

"Kawai kibar maAllah komai a hannunsa"

"Ni zakice nabar ma Allah komai kun manta ku irin mugun halin da kukeyi"

"Wanan Da ne banda yanzo, mun riga mungane gskia kema kum ya kamata kigane hakan"

Xaginsu Mommy tashiga yi hadda yimasu gori iri iri

"Mai da wukar gobe gobe zamu bar maki gidanki, Amma kisani akwai ranan nadama"barin Parlor sukayi Mommy ta rakasu da harara.







Sun Mman Heeshmer kuwa suna fita moto duk suka shiga dan kai AFRAH gidanta, amarya da Inna, maman Heeshmer mota d'aya suka shiga yayin da su mom fauza, aunty zulaiha da sauran yan kai amarya duk suka shigiga mota
Friends ma duk sun shiga mota wanda keda samari kuwa sune zasu kaisu.

Sun isa gidan amarya Lafiya da ke u/rimi jaaa Abdulkadir road, gida ne maidaidaice mai kyau compound din gidan za'ayi parking motoci 4 nan duk aka shiga ciki 4 bedrooms ne sai side na ABDULNASEER parlor ne da bedroom sai toilet a ciki.
Gidan AFRAH yayi kyau, yayi kyau sosai kaya masu kyau akayi mata bedrooms din duk an zuba gadaje 2 dai Daddy ne yayi kamar yanda yama Faty sauran Biyun kuwa wanan duk Aikin su Mami sunyi kokari matuwa sunkuma ba makiya mamaki Fatty gaba daya tarasa abinyii mamaki wai takeyi abinda bata taba zata ba.
Haka Mutane sukai ta san barka da sa albarka akafara wucewa, mutane sun d'an ragu nan su aunty Shuwa da aunty baraka da mai make-up sukazo, nan akasa Afrah tashiga wanka nan mai make-up tashiga yimata kwalliya tayi kyau sosai cikin material lace fited gown tayi kyau har tagaji.
Nan friends suma suka dau nasu wanka duk da basu san za'ayi dinner ba amma da kayansu in case nan suka dau walwali kowa yayi kyau su Mman Heeshmer da sauran k'anne duk anyi kyau nan aunty baraka ta aika mota a dauko maman Amarya Da sauran jama'a
Nan motan da Amarya zato aunty barakce tarakota har motan sanan ta rufe

Nashiga cikin motan wani sanyi gami da kamshi ya ratsata juyowa tayi nan sukayi 4 eyed da angon tana yayi kyau cikin shadda fara tass... Kai baxan iya bayani ba sun kyau da yawa kawai
A cin kin silversand motan tayi parking da da sauran motoci nan AMARYA DA ANGO suka fitoh hannun su cikin na juna nan pa photographs suka shiga kashe masu pictures.

Biki yayi baki waje yayi waje wanan event na manya ne coz friends na Abban Abdulnaseer ne suka had'a dinnern Husana da sweetheart dinta sunyi kyau sosai haka Zarah da Mahmoud dinta, Zainab da Muhammad dinta Suleiman da Abdul ma sunsha gayu, kowa yayi kyau familyn Abdulnaseer kuwa gayun su yayi yawa Anty maijidda, aunty aisha moh'd, Anty Baraka da sauran anties na ango duk sun sha kyau har sun gaji.

Abdulnaseer yayi rawa kaman babu gobe shida amaryansa lik'i kuwa sun shata haka akaita gudanar da Dinner cikin farin ciki anci ansha har anba uku lada ga abubuwa masu da su aunty shuwa da aunty baraka suka raba tap da jaka haka dai taro ya tashi lafiya kowa na san barka, maman Zarah da husna duk sunzo haka sukaita san barka haka musty da yan uwanshi ma, Fatty kamar gunki

12:00 aka tashi kowa yana tasan barka Mommy ko d'an bakin cikin k'in zuwa tayi.


Washegari bud'an kai ranan duk akazo ganin gidan amarya both family da abokan arziki sosai kowa ya yaba da tsarin gidan da kuma irin kayan da akayi mata, wa'azi malama Hassana tayi mai ratsa jiki sai kusan magrib aka gama k'are akayi addu'an Basu zaman lafiya hijabai aka raba sanan mutane suka kama gabansu, sai da a ka k'ara gyarama Amarya gidanta sanan kowa yawuce gida ya rage daka Afrah sai friends nata.
[12/18, 09:04] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*


_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch β™₯ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~🌸


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_




*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_


_page 66-67_



*D*uk abinda yakamata ayi anyi nan friends aka a basu abinda za'abasu, kud'i masu yawa suka samu kana AMARYA da ANGO sukaita godia, haka duk suka tafi kowa na farinciki.

Washegari duk y'an biki sukaita shirin tafiya sisters na Mommy kuwa tin 6:30 na safe suka bar gidan sabida ba k'aramin rashin Mutunci Mommy tayi masu ba ita da Farty su aunty Azeezah sunyi alkawarin bata k'ara ganinsu a gidanta, haka dai suka rabu a baran baran.

Y'an katsina ma duk sun wuce a haka y'an uwan Mami ma da mamin kanta d'an babu abin da zata tsaya yii kuma, haka dai kowa ya tafi cikin farin ciki ga bun arziki


Gida duk yan biki sun wuce Inna da aunty zulaiha ne suka rage sai Fatty itama gobe zata wuce su Inna ko sai nan da 1week

Wunin wanan ran a bedroom Fatty da Mommy suka kule suna maganganun su

"Wai maganan meye Daddyn ku kemaki dazo?" Mommy tace tana kallan Faty

"Hmmmm wai bana shigowa gaidashi"

"Toh ta inda ya bullo kuma kenan"

"Nima abinda nace kenan, kawai dai nace yayi hakuri"

"Ai koma mekikayi shine yaja"

"Wallahi kuwa"

Haka sukai ta hiran Daddy suna kushe duk wani abu da yakeyi d'an Mommy tariga ta chusama Fatty wanan dabi'ar, kaka bisani kuma suka koma shirin bikin AFRAH suna tsine ma duk wani wanda yayi rawar gani abin dakuma kushe duk wani abu da a kayii

"Ni wallahi Mommy dama a sake ta naga k'arshin rawan kai"

"Hmmm wallahi da anga ruwan bala'i dan bazatamin zawarci a gida ba"

Daria Fatty ta sosai kana tace "kai Mommy wai zawarci"

"Ehh mana haa kawai, ai nima lokacin zanma Inna rashin mutunci kaman yanda rayi min"

"Me tamaki Mommy?
Faty yace tana zare ido"

Nan Mommy ta jayyane mata komai, nan suka shiga xaginsu gami da tsine masu haka dai sukai ta hiransu.

Washe gari bayan sallan la'asar Musty yazo daukan Fatty, har wajen Inna yaje ya gaidata kana yadawo parlor ya zauna, mommy ce ta shigo parlorn cikin Fara'a gaisheta yayi mommy ta amsa cikin sakin fuska sanan tace " dama Mustapha akwai maganan da nakeso muyi da kai"

"Oky Mommy inajii, Allah sa kafiya"

"Ahhh lfyalau" mommy tayi magana tana smiling

"Toh inajinki Mommy "

"Dama inasan jin dalilinka na hana Fatima zuwa school ne"

Kallan Fatty yayi da shigowanta kenan parlorn, gaban ta ne ya fad'i wani tsoron Mommy ya shigeta

"Babu komai Mommy coz nan da 1 month zamuwu ce Turkey, inmuje chan sai ta cigaba"

Washe baki Mommy tayi sosai cikin farin cikin tace"Fatty da *Gajen hakuri*(Afrah bhai) kike shine duk kinbi kin damu kanki" tayi maganan tana kallan Fatty, smiling dinda bai kai ciki ba Fatty tayi

"Toh kutashi kuwuce kar kuyi dare"

"Daddy bayanan ne? "

"Ehh ya d'an fita ne"

"Okay inyadawo a gaidashi sosai, sai munzo maku sallama"

"Toh insha Allah zaijii, Allah tsare hanya yakuka kai ku lfya"

"Ameen ameen mommy"

Har bakin Mota ta rakosu ita dai Fatty gaba d'aya jikinta yayi sanyi faduwa gabanta kawai yakeyi, haka dai suka wuce mommy sai d'aga masu hannu takeyi har suka bar cikin gidan ita kuma Mommy ta koma ciki.

A hanya kuwa tinda Musty ya kalla Fatty bai kuma kallanta bah driving kawai yakeyi gashi sai uban gudu yake shararawa Fatty duk a tsorace take, haka har suka iso abuja

yayi horn mai gadi ya wangale mai gate yashige, inda aka tanada d'an adana motoci anan yayi parking, batare da da ya kalleta baya fita yabarta cikin moton Fatty dai gabanta sai faduwa yakeyi hata tafitoh a motan jikita sanyi qlau


Sallah duk suka farayi kana Musty yace" yayi maki kyau, kinje kinkai k'arana wajen Mommy ko? yayi maki kyau school kuma wallahi inhar kina gidanan baki sake zuwanshii har abada wallahi, kuma ko wa zakije kifadamawa a familyna kiyi aikin banza d'an babu abinda zasuyi"yana gama fad'an haka yatashi yawuce bedroom dinshi

Xubewa Fatty tayi awajen tashiga rere kuka tanacewa"mommy meyasa xakimin haka, meyasa, why why" haka taita kuka

" kibar kukanan kije kumin girki"

Nan Fatty ta tashi tayi cikin, bawani abu mai wahala tayi amma sai bayan sallan magrab tagama, kadan Musty yaci sai da yayi sallah isha'i sanan yashi ga wanka bayan ya fito shiryawa yayi cikin gayun na masifa Fatty na ganin haka tasan hau zai shiga club kenan sai kusan 9pm yabar gidan bayan ya kule Farty ta baya sanan ya amshe phone d'inta ranan tasha kuka.



, haka dai Fatty tai ta rayuwa gadai kud'i amma babu kwanciyan hankali ga Musty da saurin hannu in abunshi ya motso gashi baya tsoran kowa a familyn shi ta lura ma su lallabashi sukeyi bata zuwa ko ina sanan baya bari taje ko ina, sai inyana jin mutunci shine zai kaita gidan Anty lailah
Shima batawani dadewa gaba d'aya bata jin dadin xamanta da Musty sam gashi da san girkin masifa bai da aiki sai cin abinci.



AFRAH da ABDULNASEER kuwa sunci amarcinsu cikin farin ciki da kuma kwanciyan Hankali, sosai ABDULNSEER ke kuda da ita da duk wani abu da takeso haka itama tana k'okari sosai irin soyayyan da suke zubawa a gidan nasu abin sha'awa ne da birgewa gashi duk y'an uwanshi na santa da k'unarta shiyasa itama take kyautata masu sosao, tin sanda sukayi wata d'aya da aure suka shirya sukaje katsina d'an gaida Mami da sauran y'an uwa
Sosai kuwa duk sukai murna da ganinsu, sosai Abdulnaseer yayi masu alheri daka gagin Mami har na Daddy kwanansu 2 suka dawo tare da tsaraba iri iri.

Gida kuwa kotaje Mommy a dakile take amsa mata gaisuwa ita dai AFRAH mamakin kawai takeyi kawai ita dai tasan bata mata komai ba, haka zatawuce wajen Inna d'an har yanzo Inna bata koma katsina ba. Sai dai su sha hiransu da Afifah da y'an aikin gidan Mommy ko babu ruwan ta da ita.

Haka lokaci yaita tafiya abubuwa sukai ta faruwa ciki hadda rasa Fatty a waya ko da yaushe k'ashe Musty da hanshi yakira mommy yace ta dena k'ira ranan Mommy tayi masifa da bala'i kiran Mommyn Musty tayi amma sai mommyn nashi ta koyi bayanshii kaca kaca sukayi da Mommy shidai Daddy ya zuba mata ido (dama Fatty bakin maganshi takeyi ba) ikon Allah kawai yake kallo, haka abu buwa sukai ta faruwa Mommy ko da yaushe cikin zafi zuciyar tayake, Inna ma ba shiga harkanta takeyi ba yaka inta gaisheta ta amsa duk abinda takeso batada damuwa coz ga y'an aikin gidanan gakuma anty zulaiha.


🌸🌸🌸🌸
Har yanzo kayan su Daddy babu wani labari tun bayasa abin

Please Login or Register in order to submit comment