Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi suka fitah


Nan sukayi garden ikon Allah kuwa yanan, tinda Fatty taga yanayinshi ta d'an saita tafiyan ta da d'an mayafi ta ( ni biebie nach Hmmmm)
Sallama sukayi gami da zaunawa a kujerun da ke wajen
Amsawa yayi cikin voice d'insa mai dad'in sauraro

"Yaa ga Fatima daughter'n Aunty Bilkisu tazo gaisheka"
Sai da ya harari Humaira ta gefen ido, sanan ya kalle Fatty'n

"Ina wuni, yakake? "Tayi maganan cikin muryan iyayi

"Lafiya, ya school? "

"School fine, mumata jiran admission ne"

"Best of luck "

Tinda kanan bai sake cewa komai ba, phone d'inshi kawai yake dannawa Hajia Fatty kam sai labari takebama Humairah da muryan iyayi da yagaji dajin maganan nata barin wajen yayi a ranshi yace "dis girl rawan kai"๐Ÿคฃ



Sai , wajen 6 su Mommy sukafara haraman barin gidan, inada Ummu ta had'ama Fatyy kayan kwalliya masu yawan gaske, godia sosai mommy da Fatyy sukayi, rakosu tayi har bakin mota

"Toh hajia nagode sosai, insha Allah inanan zuwa"

"Ahh babu komai, Allah kawoki lfya"


Kallan Mommy faty tayi sanan tace " wai sai muje gidan antyMaijiddah? "

"Nan ma zamu"

Kafin 6:20 sun isah gidan Aunty Maijiddan Fatyy sai kunbure-kunbure takeyi

Bayan sun gaisa kayan motsa baki Aunty Maijidda tasa aka kawo masu, juice kadai mommy tasha Fatty kam tin gaisuwa bata k'ara cewa komai ba saima danna waya da taitayi

"Kai gskia kayan suyi kyau"cewar Mommy

Murmushi Aunty Maijiddah tayi sanan tace " banga wayanda kika zaba ba ai"

"Gasunan laces d'inan yan 70k guda biyu, sai mayafi danakeso naji kinchai sai nan da 3days zasuzo"

"Okay toh kinkoyi zaben masu kyau, ita Fatima batasan ko jallabiya ne?, akawaisu masu kyau da su side bags na y'an mata"

Kallanta Mommy tayi sanan tace" kinaji bakiso ne? "

"Noooo barshi kawai Mommy"

"Ke kika sani bakisan abin arziki ba ke"

Kallansu anty Maidddah tayi sanan tace" ai sai a daukan ma Afrah da Afifah tinda ita bataso"

"Okay yanxo dai zantafi dawayanan, zan aiko nan da 3days a amsamin mayafin da sauran kayan, lissafi kuwa sai muyi waya kawai"

"Toh yayi sai kin aiko d'in, amma Afrahce zatazo ko? d'an ta dauki irin wanda takeso"

"Toh, saidai munyi waya"

Nan sukayi sallama da Aunty maijiddah sukayi gida.

Sun isa ana k'iran sallan magrab, bedroom suka wuce direct bayan suyi sallah ne Fatyy ta kalle Mommy sanan tace" ita anty Maididda nan yau tabani haushe, daka kince na dauka abu d'an nace banso shine hada k'iran sunan Afrah, sai kace Afran yarinyar kice, toh ma ina ruwanta"

"Ni dallah jeki kiramin Afrah"
Fita tayi tana turo baki, d'akinsu tayi kan bed taga Afrah da littafi hannunta

"Kekam baki gajiya da kallan littafi, sai kinmakace wlhy, kije mommy nak'ira"

Murmushi Afrah tayi kawai ta tafi k'iran Mommyn

"Ashe kundawo bama muji ba" Afrah tace

"Ehhh, munshigo anakiran sallah shiyasa, anko gama girkin? "

"Ehhh duk angama komai"

"Okay shikenan"

D'akinsu takoma still Fatty nan, book d'inta ta dauka d'an cigaba da karatunta

"Please kibar karatunan nabaki wani labari, kekuma Afifah kifita"

"Tap wallah babu inda zani, ai anan kikazo kikasameni"Afifah tace

"Sai na mareki stupid girl"

"Am not stupid, sai dai kifasa bada labarin mu bai damemu ba"

"Ke Baby bakiji ko? "Afrah tacema Afifah

Barin d'akin Afifah tayi tana hararan Faty, tsaki Fatty tayi sanan tace" yaushe ma Daddy zai dawo? "

"Friday ne insha Allah"

"Ohh gara yadawo acigaba da maganan sch d'anni bazanje wani poly ba, labari kam kibari anjima wanan mara kunyan tabatamin rai"ta karasa magana tana barin d'akin

Da ido Afrah tabita gami dacewa "ke kika sa kankin ai bawani ba, school kam kitafi London ni inan a KASU"


๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ

Yau Daddy yadawo bayan yayi Sallah yakuma ci abinci,duk zaune suke a palo gyran murya yayi sanan yace"ku yaushe ne za'afara screening d'in ne?

"Daddy Afrah zaka tanbaya d'an itace zatayi, ni banci jamb bah bandani"

"Okey tin dahakane kema mamana harkiyi screening d'in, private university zannema maku konan Al-hikma ne, Amma ke Fatima ba degree xasu baki ba, kinsandai komai basai namaki bayani ba, inkuka kikaje kika tsaya wasa koranki zasuyi inkuma kinsamu yanda sukeso subaki 200lvl gara ki natsu"

"Toh Daddy ta amsa kaman zatayi kuka, barin palon tayi mommy kam shuru tayi a ranta race "abinda bazai taba yuwuba kenan wallahi"

Itama Afrah barin palon tayin d'an gaba d'aya bataji dad'in maganan da Daddy yayi kan sch d'insu ba ita tafisan KASU bawani Al-hikma ba nisan duniya


Hakadai kowa ya kwana da tunani



Afrah ta yanke wukuncin samun Daddy tace tafisan KASU kawai, Fatyy kam tace dataje school d'aya da Afrah gara ta fasa gaba d'aya...



_TOH FAH READERS KUNAJI, MAI KUKE GANIN YAKAMATA DUK SUYI???_
[12/18, 09:03] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*



_PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch โ™ฅ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~๐ŸŒธ


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_




*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_




_PAGE 25-26_







""""""""""Koda Afrah ta tashi sallan subh Addu'a taitayi Allah sa Daddy ya yadda da nata choice d'in bayan ta idar k'atun Qur'ani tayi sai da gari yafara haske sanan tayi kitchen, nan taga Salamatu na goge-goge bayan sun gaisa ne Afrah tafara abinda yakawota, arish n source with egg tayi sai pepper soup na kayan ciki sai kuma ruwan tea dayaji kayan kamshi nan duk sukajere su a dinning ita da Salamatu, dakanta taje takai ma Baba Haruna(mai gadinsu) nashi, bayan sun gama duk abinda zasuyi d'akinsu ta koma dan yin wanka yayinda itama Salamatu ta dauki nata abincin tayi nata d'akin.



Koda takoma d'in Afifih bata tashi bacci ba, wanka tayi tashiya cikin gown na material red n black sai veil red da ta daura kanta, powder kawai ta shafa buh still she look cute๐Ÿ˜‡ tashin Afifah tashiga tashi " baby tashi, Afifatuh kitashi"

Mik'a Afifah tayi gami dacewa aunty baccin yau d'adi wallahi"

"Ni kimin shuru babu salati bale addu'an tashi daka bacci zaki faramin surutunki, haka da subh nace kitsaya muyi karatu kikak'i"

K'ara kwanciya Afifah tayi,salati tayi gami da Addu'a sanan ta tashi " sorry sweetheart gobe insha Allah zanyi bazan koma baccin ba"

"Good girl that's why i love you Always"

"I you more sislove, dama haka anty Fatyy take da yaa Hafiz, da duk sunji dad'i Wallahi kinfiso kirki"


Smiling Afrah tayi sanan tace"naji toh jekiyi wanka" bata wani jima sosai ba tafitoh shiryawa tayi cikin gown itama amma nata pink color sai wula da tasa a kanta palo duk sukayi kasan cewan indai Daddy na gari a duk tare suke cin Abinci


Dinning area sukaga Mommy sai bud'e bud'e takeyi k'arasa wasu sukayi
Afrah ce tafara gaisheta sanan Afifih Mommy ta amsa cikin fara'a(Mommy haka take wata rana taita fara'a wataran kuwa ta had'e fuska kaman dare batare da anmata komai bah)

"Ahh Afrah nasha ma kunun gyada zaki mana"

Smiling Afrah tayi sanan tace"ban san shikike san sha ba ai da anyi, kuma dan baki fada da dare bane"

"Ehh kinsan jiya duk da wuri mukai bacci shiyasa"

"Nifa yunwa nakeji" cewar Afifah

"Afrah jeki kira Hafiz, nakira phone dinsa kashe"

"Toh"ta amsa


Sallahma tayi a bak'in k'ofar batare da ya Amma ba yace "waye wai? "

Voice d'inta na rawa tace "Mommy tace kazo" juyawa tayi da sauri d'an batasan masifan Hafiz, d'anshi abu baikai abu ba masifa ne, kafin takai polon har ya kamota kallanta yayi gami da jan tsaki sanan yace" kinwani ci kaya red n black kamar yar mafiya" banza dashi tayi d'an ita Hafiz yafi k'arfinta Fatyyce dai dai da shii.


Nan suka fara breakfast dukkansu Daddy ne yafara gamawa, kallan Fatyy yayi sanan yace" wanne kika dafa acin abincin? "

"Ahhh ni Daddy banyi kokai ba duk Afrah tayisu"ta k'arasa maganan tasa arish a baki

"Ahhh Ahhh Mamana kodai gidan girki zan bude ma kine? "

Smiling Afrah tayi sanan tace" Daddy ai bangama iyawa ba"

"Wayace? Dan kinfi wanan yanuna Fatyy, baka taba ganin tana aiki kowani abu sai d'anna waya"

"Ehh wallahi Daddy ai karkakuma chanza mata phone ne"Afifah tace

Harara Fatyy ta watsa mata itama Afifan Hararanta tayi amma bata bari Daddy yagani ba

Dariya Daddy yayi gami dacewa" kinganki nan, ke kin iya girkin? "

"Ehh mana tanbaya Mommy ko anty Afrah"

"Toh masha Allah, kema Fatima sai ki daure ki koya in Mamana nayi kirika kallo"

Wani haushi yakama Fatty da Mommy kai kaawai ta d'aka batare da ta amsa bah

"Mommy kina jina da yaranki kinyi shuru" Daddy yacema Mommy

"Hmmmm mai zance? Ai kunfi kusa" tashi tayi tabar wajen, nan Hafiz yafara k'oran tashi shima Daddy ne ya tsaidashi " kai ya maganin karatu? Kanema sch d'in? "

"Ehhhh, wani ne a turkey"

"Okay shine sai da na tanbaya sabida nixanyi karatun ko? "

Kai Hafiz ya sosa gami dacewa "aa dama dama."

"Dama mai? kaci sa'a me inna da Sulaiman sunsa baki game da karatunka da saide nasama ido kokuma kayi anan"

"Ya hakuri Daddy"

" dole ai nayi hakurin, duk yanda akeciki kasanar dani"

"Toh Allah saka da Alkhari".

"Ameen duk suka amsa

Nan Fatyy tashiga kwashe kayan kan dinning din ( niko biebie nace su fatty anji gori๐Ÿ‘…)


Daddy nanan zaune har Faty tagama kwashe kayan, waya aketayi da abokan kasuwancin sa, bayan yagama kallan cikin palon yayi baiga kowa ba sai Afrah tashi yayi daka dinning area d'in yanufi cikin palon, zama yayi nesa k'adan da ita, sai da ya kalleta da kyau sanan yace" Mamana"

"Na'am Daddy"ta amsa

"Fad'amin damuwanki, anamaki wani abune da bakiso a gidan? "
.

Girgiza kai tayi alamun a'a

"Toh Fad'amin menene matsalan?"

Sai da tayi k'asa da kanta sanan tace" dama k'an maganan school d'in da kayi manane jiya" sai kuma tayi shuru

"Ikon Allah Mamana hala dai banine babanki ba shiyasa kikemin haka ko?"

"A'a Daddy"

"Maxa gayamin"

"Daddy dama school d'inne yayi nisa, ni hanka- lina bai kwanta ba, koma ba waje d'aya xamu zauna da Fatyy ba tinda ita ba degree zatafara ba"

"Duk na gane, yanzo wanne kikeso? "

"Ni nafisan nan garin KASU koma POLY nasamu duk inaso Daddy"

"Shikenan matsalan"

"Ehh shikenan Daddy"

"Toh shikenan Mamana angama" ya karasa maganan yana daria

"Yauwa Daddy Allah saka da Alkhari, yakara budi da wadata yasa afi haka"

"Ameen Ameen Mamana, makarantar girkinfa kina so? "

"Ehh inaso Daddy"

"Da kyau Mamana, sai kinemo wanda kikeso, duk yanda akeciki kisanar da ni zanyi magana da Mommynku ma kan makarantar Fatiman"

"Toh Daddy"

"Bari nashiga daka ciki"



Tana ganin Daddy zai bar palon tayi side Mommy da gudu, Fattyce wanke ke lab'e tinda su Afran na magana
Da k'arfi tabugo k'ofar d'akin Mommyn kawai tasa babu ko sallama

"Kee bakida hankaline kinturomin k'ofa da k'arfi"

Fuska Fatyy tabat'a sanan tace" matsalanki kenan Mommy masifa, inda kinsan news d'in da nazo maki da shi bazaki ce haka ba"

"News d'in uban mee"

"Please Mommy kitsaya kiji, Daddy nagani da Afrah a n palo suna magana"

"Maganar uban mai? " tayi ma Faty tanbaya tana gyara zama

"Toh kinata masifa inafa zakiji kan maganan"

"Ke d'an ubanki fad'amin inaji"

Nan Fatty tashiga zubo ma Mommy zance hadda k'arya a ciki, sai da mommy tagama ji tass sanan tace" tama kanta adalci"

"Kaman ya Mommy"

"Keda kina tunanin zan ba rta taje private university ne tana degree ke kina wani abun chan daban wanda ba degree ba? Taiki kenan, sai kace bana raye, ta kyauta ma kanta da tayi wanan tunan, makarantar girki kuwa taje taitayi duk wahala ne kee baza kiyi irin karatunan ba"

"Auuuu hakane ashe, ai tama kanta adalci kuwa, yanxo Mommy ki cema daddy sai next year zan fara school kafin time d'in nasake duba wani school d'in dan Al-hikkimanan bai min ba"

"Kar ki damu ko nan Abuja ne sai kije akwai private university masu kyau dai dai ke, buna na dai kiyi passing jamb"

"Insha Allah akwai inda ake biya ma akecin jamb Lailah friend d'ina kefadamin"

"Ai shinenan sai kisake kawai, ita kam chan ta k'arata a KASU"



Koda Daddy kemata zancen sch d'in Mommy cewa tayi Afran tafara kawai Fatyy zatasake jamb next year tafara nata.

AFRAH tayi duk abubuwan da yadace tayi na school daka university d'in har polyn, dan Saura 2weeks afara screening Hafiz ma sai shirye shiryen tafiya yakeyi.



๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ
Zaune suke ita da Afifah, karatu take koyama Afifahn Fatyyce tashigo d'akin babu ko sallama phone d'inta tamik'amata "gashi yaa Sulaiman zai kiraki inkingama Afifah takawo min d'akin Mommy" batajira amsa ba tayi gaba

"Wanan anty Fatty masifa"Afifah tace

"Kimin shuru"

"Wai maye ne kindawo kinamin kunbura anan" Mommy tacema Fatty

"Ba yaa Sulaiman bane yakirani wai na kai ma Afrah phone d'an"

"Kan wani dalilin? "

"Oho mai, su suka sani"

"Tapdijam bazai taba faruwa ba wallahi, ina bazan taba yadda ba sam"

"Wai menene Mommy "

"Dallah fita kibarni na san abinyi tukunna"


*muje zuwa*



_Gaisuwa mai yawa gadukkan masoyina koma masu bin labarina BIEBIE DEE na k'aunarku har cikin ranta, ALLAH BARMU TARE_โคโค๐Ÿ’žโฃ๐Ÿ’ž๐Ÿ’•๐Ÿ’–๐Ÿ’˜





~Biebie dee~๐ŸŒธ๐ŸŒธ
[12/18, 09:03] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*



_PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch โ™ฅ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~๐ŸŒธ


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_




*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_






_page 27-28_






"""""""""""""B'angaran Afrah kam waya sosai sukayi da yaa Sulaiman d'an har mantawa tayi da phone d'in banata bane, ganin Fatyy a gabanta ne yasa ta tuna(lol)

"Okay bruh za muyi magana anjima" sallama sukayi tamik'ama Fatty wayanta, amsa tayi gami da jan wani dogon tsaki, banza da ita Afrah tayi d'an tariga ta saba da halin Fatyy'n



Mommy kam kaiwa dakomo wa tai tayi a cikin bedroom tama rasa abinyi, zama tayi bakin gado tana cewa " wallahi Sai nayi maganin Sulaiman, yaro tin yana k'arami ya mak'ale ma Rabi, yanzo yakoma jininta, toh wallahi bazan yadda ba, bakar aniyar ta tabita d'an duk yarana sunfi k'arfinta"haka dai tai ta surotainta mara kan gado da lissafi.


Gaba d'ayan ranan Mommy sai cika take tana batsewa, ita dai Afrah Aikin gabanta kawai takeyi d'an tariga ta saba da halinsu, duk yanda sukazo ta nan take bidasu.

_2 WEEKS LATER_

Anata screening, Afrah nasa ran admission d'an Daddy nada hanya bata da problem, Hafiz ma nata shirin tafiya nashi sch d'in dan duk wani abu da yakamata anyi, Fatty kam bata sa komai a gaba ba, sai yawo duk wani joint dake garin kaduna tasan dashi, gayu kawai tasa a gaba babu aikin fari bare na bak'i yawo kawai sai siyan kaya a online.




Gaba d'aya yanzo bata cika zama a gida ba, sabida zirga-zirgan school,tashigo gida a gajiye, side Mommy tayi direct bayan ta gaisheta bedroom d'insu tayi, tsaki tayi gami da cewa" Fatty da tashigo waje sai ta birkitashi hankalinta ke kwanciya" kawar da kayan duk tayi saban ta shiga toilet, wanka tayi gami da Alwala, gown tasaka sanan tayi sallan la'asar d'in kwanciya tayi tana duba wani girki a online, tanan kwance har Afifah ta dawo daka islamiya, da sallama ta shigo d'akin gami da gaida Afran
"Aunty Mommy tace wai bake zaki mana dinner ba yau"

"Yes sweetheart, kai na yana ciwo kad'an"

"Sorry Allah sawake, bari naje wajen yaa Abdul yakoyamin wani assignment tinda kanki na ciwo yau"

"Yaa Abdul ya dawo ne? "

"Ehhh, nima na dawo school na ganshi, maybe daddy zai gani, yace gobe zai koma wai"

"Lallai ma, shine ko yagayamin kuma muyi waya da safe"



"Shine ko kafadamin zakazo" Afrah tace ma Abdul
" ni bansan zanzo bah"

"Kai dai kawai yaya Magana na baka wahala, da yaa Sulaiman ne ai wlhy bazaiyi haka ba"

Daria Abdul yayi sanan yace" ai dole kice haka yarinya"

"Hmmmm naji, ya karatu, ya school? "

"Alhmdulillahi, muna fafatawa, ya naki"?

"Tap ai tinkafin mufara ma wahala mukesha, gashi inaso naje katsina Inna tasa min Albarka"

"Ah lallai yarinya sai kibi Daddy zai dawo yau da dare, gobe insha Allah kuma katsina zaije daka can zai wuce Abuja"

"Na bishi wazai dawo dani? "

" see you bai da drives ne, kawai ki bishi ko Bala ma ai zai iya dawo dake"

"Toh Allah dawo dashi lafya"

"Ameen" duk sukace
.
"Ni gaskiya a jidani" Afifah tace

"Lil-lil wats your problem? "Andul ya tanbaye tah

Sai da ta d'an bata rai sanan tace" bayan nazo ka koyamin assignment sai magana kuke tayi kun share ni, kuka ni kubar cemin lil-lil"

"Ahh haba sorry babban k'awa"yaa Abdul yace

"Toh naji yaushe za a koyamin? "

Kallan agogonshi yayi sanan yace " kinga saura mintoci k'adan ayi magrib, in nadawo daka masjid kema kinyi sallah sai kixo muyi ko? "

"Toh Allah kaimu"

Fatty ce tashigo su biyu da k'awarta Asiya, anci sa'a tayi sallama, amsawa duk sukayi, ko kanlansu barayi tashige ciki sai Asiya tace tasu "ya kuke? "Suka amsa da lafya lau"


"Babe waye wanan handsome d'in? Wai ku bakuda munana a gidan ne" Asiya ta tanbaya

"Kee ina kikaga handsome d'in?

"Wanda na gansu tare da Afifah da Afrah"

Mtswww taja tsaki" brother d'in Afran ne n don't ask me anything"

"Matsala dake kenan rashin mutunci"

"Ke kika sani,

"Ni dallah Suraj d'in zaizo picking dinki ko nama driver magana ya maidaki? "

"Yana hanya"Asiya tace

Sai bayan magrib sanan akazo daukan Asiyan, A palo taga Mommy

"Ina wuni Mommy"

"Lafiya lau, ya mamanku"ta amsa cikin sakin fuska

"Lfyalau mommy, sai da safe"

"Ahh harkinfitoh? Allah bamu alheri"

Ko datazo fita ma taga su Afrah, sai da safe ta masu sanan ta wuce, tsaki Fatty tayi game dace wa"babe ni zan koma, sai munyi chatting"

"Okay bye"

Palo ta dawo ta zube kusa da Mommy
"Wallahi nagaji"

"Da kikayi uban me?" Mommy tace

"Matsala dake kenan, Mommy kin ga mutananki a wajen gida hadda Afifah? "

"Bar sakarkarun, wahalanlu,marasa anfani"

"Wai mema Abdul yadawo yine"

"Waya sani ma munafikin, ganinshi kawai nayi"

"Aifa, toh ita uwar girkinan bata samu sch d'in abincin bane? ".

"Ina nasani ma yar wahalan"
Haka dai sukata hiransu, a zaki wanan a tsine ma wanchan



Daddy bai samu dawowa ba sai washe garin ranan, girki kala-kala Afrah tayi mai Afifah da salamatu suka tayata, ko da yadawo Albarka yaita sa ma Afran d'an yaji dad'i sosai

Duk zaune suke a babban Palo dawo wanshi daka masjid sallahn isha babu dadewa, Afrah ce ta kalle Daddyn sanan tace"Daddy xan bika Katsina gobe insha Allah sai Bala yadawo dani jibi"

"Toh Allah kaimu goben lafiya"

"Nima zanje Daddy" Afifah tace

"Babu inda zakije cewar mommy, wani tafiya ni da nake zaune daku bansani ba sai yanzo? Ita dai Afran da banda iko da ita sai taje, ke kam Afifah babu inda zakije"

Banza da ita Daddy yayi bayasan hayaniya, haushi sosai Mommy taji d'an taso ya tanka ko sata samu k'arasa fad'an abunda ke ranta.


Shiryawa sukayi tsaf sanan suka shiga side d'in Mommyn, banyan sun gaisheta, ta amsa a banxache
"Mommy sai mundawo insha Allah gobe zamu dawo"

"Hmmmmmm, ina Daddyn naku?

"Yana palo", Afifah tace
Hakanan tabiyo su har palon amma a ranta Allah ne kadai yasan irn haushin da Afrah take bata.

"Har kunfitoh?"

"Da yaddan Allah"

"Toh Allah tsare, Allah bada sa'a"

"Ameen Ameen, acigaba damana addu'a akwai wani business ta muke san farawa in komai ya kankama zanyi maki bayani, insha Akwai ciga ba"

Baki Mommy ta washe gami dace wa"toh Allah tabbatar mana da Alkhari"

"Ameen ameen"

Har gaban Mota ta rakosu tana k'ara masu addu'a



Sun isah katsina lfya, Inna taji dad'in ganinsu sosai, kaya iri irin Daddy yakawo mata Inna sai Albarka takesa mai, nan yake fada mata game da business d'in dakesan yafara, Albarka sosai tasa mai gami da fatan Alheri, sai da duk ya lak'a dangi gami da masu alheri kaman yanda yasa ba sanan yamasu sallama yawuce Abuja, su Afrah kam Haruna ne zai dawo dasu(yaron Daddy ne)



๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ
Tinda su Daddy suka tafi Mommy ke masifa na babu gari babu dalili kowa haushi yake bata Allah kasai yasan irin tsar da tama Afrah d'an aganinta tafi zak'ewa bata kawai Abdul bah

"Fatty mekike ganin zanyi ne? Gaba daya labarin Afrah hauhawa yakeyi, idanuwanta k'ara budewa sukeyi" Mommy ta tanbaya Fatty

"Haka ne Mommy ni kaina yanxo Afrah bata wani cika shiga harka na ba, kawai kuyi magana da aunty Azeezah ko anty Nana"

"Toh su yanxo ina fara fad'a masu zasuce bana nemansu sai ina da damuwa"

"Ehhh, kije zaria ne d'an shopping kayan yara dai dai sauransu, kinsan zasu baki mafita insha Allah"

"Toh hakan zanyi zan fara k'iransu a waya ma"

"Toh mommy Daddy ya turo da kud'inan kuwa?"

"Ehh mai yafaru? "

"20k zaki bani a ciki akwai abunda zan siya"

"Matsalanki kenan kedai"

"Haba Mommy yanxonan fa na gama baki mafita, ko kud'in naki ne ai sai ki bani bare ma ba naki bane"

"Zanci ubanki wallahi"

"Hmmmm nidai kibani kawai Mommy" tak'arasa maganan tana barin dak'in.


๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ
Kwanansu d'aya a katsina suka dawo kasan cewar Afifah na school, Addu'a sosai Mami, Uncle junaid, Inna da sauran d'angi sukayi mata gami sa samasu Albarka kamar yanda suka sabah
Da misalin k'arfe 2 narana Haruna iso daukansu har jikin mota Inna sa Zainab jikar Inna Rakiya suka rakosu, Zainab ce tace" toh yar uwa Allah bamu sa'a yasa kuma mudace, Allah tsare duk agaida kowa"

"Toh Ameen Ameen, insha Allah duk zasuji, duk wahalan da kikasha wajen registration ki labarta min a online "

Dariya Zainab tayi sanan tace"karkidamu ai har da pictures ma"

"Kee dallah shiga kuje kubar bawan Allah najira"Inna tace

Juya idanu Afifah tayi game da cewa"ke tsohuwa me naki? Ki lallaba ki ware gida kawai sai mun hadu a waya"

"Kinganki kifita idona fa"

"Ni dama wallahi banshi gaba, indai kinaso nashiga bari nazo"

" na tsaya biye maki kwana zamuyi a wajenan, kule Allah tsare"

Haka suka shige mota suna ta dagama juna hannu..
[12/18, 09:03] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*



_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch โ™ฅ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~๐ŸŒธ


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_

*gaisuwa ga dukkan masoya nah masu bibiyan labari na,nagode sosai Biebie dee na k'aunarku har cikin ranta a duk inda kuke a fad'in dunia*โคโคโคโคโค
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_



_page 29-30_






"""""" *S*un isah kaduna lafiya, wajen Mommy suka fara shiga kafin sukawoce d'akinsu, sama sama ta amsa gaisuwan d'an Allah ne kadai yasan irin tsanar da tama Afrah

Suko Afrah suna shiga bedroom d'innasu wanka sukayi gami da Alwala, salla sukayi sanan suka ci abinci, wajen k'arfe 9:30 Innah ta kira taji ya suka iso, hira suka d'an yi sanan sukayi sallama, ta aje phone d'in babu dad'ewa Mami ma takira itama dai taji yasuka saukane sanan sukayi sallama, whatsapp ta shiga tafada ma yaa Sulaiman ma sundawo, batawani dade online d'in ba ta sauka, alwala tasakeyi sai addu'an bacci ta kwanta Afifah kam tinda taci abinci rayi baccinta.


"Haba Mommy naga dai kud'inan bafa kece kike nemowa ba, da anyi magana kice kina manege duk kudaden da Daddy ke baki ina kike kaisu? " Fatyy tace ma Mommy

"Kinsan Allah zanci ubanki"

"Kedai yau Mommy kin hau litter๐Ÿšฎ zaki sauke a kai na, Afara ke baki haushe, kijey ki cimata qaniya bani bah"

"Fitamin a d'aki dan ubanki"

"Wallah mommy Daddy yace kibani 5k kud'in subscription"

"20k d'in ranan fa? "

"Babu ruwanki kawai nidai yace kibani, ai muyi waya dashi"

"Kude kenan keda Hafiz sani magana ko? Duk k'okarin da nakeyi kanku baku gani ko? "

"Toh ai kece Mommy komai masifa, inbanda haka wazaiji kanmu nida mommy nah"ta k'arasa mafanan tana daria

"Hmmmm jeki sai da safe"

"Zaki bani kud'in? "

"amma nace kije ko"

"Toh Allah bamu Alheri"

Da ido Mommy tabita.





Please Login or Register in order to submit comment