Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jii tayi kaman tayi hauka sabida bakin ciki da takaici zuciyarta wani zafi takeyi d'an takaici da bakin ciki wani haushin mutan gidanne duk ya kamata haka dai ta wuni cikin kunci wanan ranan.

Kwanan su Fatty 3 suka koma Abuja shipping sosai Muty yayi yakawo gidansu Fatty taji dad'in karan da Musty yayi mata rakuma ji dadin zuwanta d'an sosai Affrah tabata shawara takumayi alkawarin tayata da addu'a.



Yau kwanan Daddy 5 kenan da faruwan wanan lamari koda yaushe Daddy cikin tunanin inda kudi zasu fitoh yakee, yanzo ma zaune yake a parlor yana nunani, Suleiman ne yashigo sai da ya gaida Daddy sanan yache" Daddy Please ka rage damuwanan haka, Allah na sane damu"

Ajiyan zuciya Daddy ya sauke kana yace" hakane, kasan dai yau saura 3weeks lokacin da banki ya dinbanrmin ya cika ko? "

"Ehh nasani Daddy"

"Yanzo abinda nakeso da kai akwashe duk motocin gidanan banda naka a saidasu sanan ina da milin 6 da alhaji Sunisi biyani bashi na duk sai a hada da shii"

"Daddy aka saida Motocin gidan duka am sure zasu isa abiya abinki bashin su ai"

"Hmmm Sulaiman Kenan ai inkaga kud'inan sunkai toh sai dai asaida gidanan"

Eyes Suleiman ya zaro kana yace" Gidanan kuma? Mai zai hana musai da motacin mubasu kudin Mocin kawai milin 6/kuma sai ka far wani business din?

"A'a na fara wani? Bayan bani da tanbacin zan samu kud'in biyan ko bazan samu ba, kuma kai kanka kasan milin 6 bazaimin business ba"

"Toh yanzo ya xa'ayi Daddy? "

Ciki dakiya daddy yace" final decision shine zan sai da gidanan"

"Daddy g.. i.. d.. a faa kace" Suleiman yayi maganan bakinsa na rawa

" Ehh Suleiman gidanan zan siyar, nasan zaiyi 70 million ko ma fii, tinda Baaban gida ne sosai kuma a G R A kaga na siyar cikon kikon 30 milion kawai zanyi, shikuma in aka saida motacin nasan milin 30 zasu fitoh 6milion dinan da ke gida kuwa sai musamu wani gidan da shii ko hayane a marafa, yanxo kaje gidan Hamisu ka fadama shi komai nasan shi zaiyi komai" yana gama fadan haka ya jingina da kujera isanshi rufe

"Daddy amm.. " bai karasa ba Daddy ya katse shi" Na riga na dad'e na amsan k'adda mai kyau da mara kyau, haka Allah yaso kuma haka Allah ya tsara kuma Alhmdulillahi nagode mashi sosai dan nafi mutane dubu a duniya so kai ma ina soka *YADDA DA K'ADDARA MAI KYAU DA MARA KTAU* da ai bamu kai haka ba, Allah ya buda mana sai yanzo muce zamuyi mai butulci? Ai ko dad'in jin babu so baso kace komai sai Addu'an Allah sa hakan ne alkhari"

"Shiken Daddy Allah sa hakanne Alkhari yakuma zaba mana abinda yafi zama alkhari"

"Yauwa tashi kaje Allah ma albarka"

"Ameen Daddy"

"Yauwa inkaje ka gaidashii"

"Toh zaijii" nan Suleiman yabar parlorn Daddy ya bishi da ido yana tausayamai a hankali yace" kai kuma Hafiz in kaga kud'i basa shigowa zaka dawo da k'afarka".
[12/18, 09:04] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*


_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch ♥ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~🌸


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_




*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_


7⃣1⃣_7⃣2⃣



*S*ulaiman na fita direct gidan Malam Hamisu yayi, bayan sun gaisa ne Suleiman ya fad'a mai duk abinda Daddynsu yace sosai Malan Hamisu ya tausaya ma Daddy har yakejin dama ace yana da kud'i da bazai taba bari ya sai da gidan shii ba d'an Daddy mutum ne ya temake shi ta wajeje da dama toh Amma babu yanda ya iya sai dai ya tayashi da addu'a.



A gida kuwa Suleiman nafita Daddy yayi siden mommy, zaune ya sameta tana danna waya ganin shi yasa ta aje phone ne a jefenta sanan tace" lafiya dai alhaji? "

"Lafiya lau, Alhandulillahi"

"Toh naganka wani iri ne ai"

"Hakane, game da bashin banki dasuke bina ne"

"Ehhh" mommy tace tana gyara zama

"Toh shine na yanke shawaran sayar da gidan hadda motoci ma"

Zubur Mommy ta mik'e tana bin Daddy da wani irin kallo," bangane zaka siyar da gidan baa Shu'aibu"

"Yanda kika fada toh hakanne gskiyan magana, gidan zan siyar d'an na biya su kud'in suu"

"Amma ai bai kamata ka saida gidanan bah motoci kawai kasiyar a ya isa kabiya su kud'insuu"


"Lallaima Bilki watoh kin manta ma adadin yawan kud'in kenan ko? Da har kike cewa kud'in motoci ya isa na biya kud'in"


Cikin muryan kuka mommy tace "yanzo yakake so muyi kenan d'an gidan da muke tak'ama dashii xaka saida, wai zakasamu cikin masifa da bala'i"

"Bashi dai Allah ne yabani ikon cinshii kuma sanan hadda goyan bayankii, daki ke zancan masifa kuwa ai da na mutu lokacin zakuga masifu, jarabu, har da jafa'i ma d'an yan banki basu da sauki, tinda Allah yasa daka suma ban k'arasa ba dole na sauke wanan bashin da ke kaina ko d'an gudun tashin hankalin da yarana zasu shiga in bana raye"


"Ehhhh amma gashi xaka jefa yaran naka cikin talauci da wahala bahh"

"Ki fad'a duk abinda zaki fada gida dai nawa ne bana kowa ba, ni ne natara kud'ina na gina shii batare da temakon kowa ba, so duk mai san jin dad'i sai ya dage yanema, nayi masu mai wahalan tunda na basu good foundation"


"Wallahi ka cucemu, ka cucemu" mommy tace tana kuka sosai


"Sai ki fara shiiri d'an yau za'afara nema mana sabon gida kuma ba abin mamaki bane kiga masu siyan gida sunzo dubawa anjima gobe ko anjima ma so sai kikasance cikin shii, inkuma baki iya zama duk d'aya nee kuma bance asanar ma Fatima ko Mamana bah" yana gama fadar haka ya wuce kamar bayi da matsala, mommy kam da kyar ta iya jan k'afafuwanta zuwa bedroom sabida nauyin da sukayi mataa, zubewa tayi a kan bed tana kuka bin hakk'i da gskia kuka takeyi sosai chan tace" ni Bilki na shiga uku sai danagama juyama mutane baya duk abubuwa suka fara faruwa danii? Ko d'an wulakancin da nakeyi ne? Dama su Azeezah sunyimin baki wai zan ganii koshine na fara gani yanzoo? Na shiga uwa ga kud'in y'an meeting da naci 350k ina zan samosuu? Wanan nake sa ran samu daka wajenshi yayi k'asa ga Sulaiman bai fara aiki baa ga Fatty ita kuma bata fita bare tamin transfer, Hafiz basan halin da yake ciki bama" wani kuka Mommy ta sake da ta tuno da tijaran y'an Meeting oga hajia Adama babu mutunci ba sani ba sabo ai duk sai taji sai da gida ma bai dameta ba yanzo inda zata samu kud'in hajia Adama kawai takeyi, dayan wayan ta tajawo dake kan bedside drawer tashiga dialing number Hafiz amma switch off, mommy ji tayi kaman ta kurma ihu.







Ko da Daddy ke sanar na Inna hukuncin da yanke na siyar da gida, kwantar mai da hankali tayi sosai gami da Addu'an Allah sa haka ne yafi zama alkhari ya kuma bashi ikon ansan k'addaran da hannu biyu, yabashi ikon ciye jarabawan Da Allah ya d'auro mai a k'arshi ta samai albarka sosai gami da k'ara tausasan zuciyan shii.

Daddy yaji dad'i sosai yakuma jii sanyi cikin zuciyan shii, d'an sosai damuwar shii yarage a xuciyan shii yak'ara daukan ma kanshii alkawarin kyautata ma mahaifiyarshi har k'arshin rayuwan shii *Uwa mai dad'i, Allah ka k'ara karemana iyayenmu,ka tsare mana su, yaa Allah ka saka masu da mafificin Alkhari Allah kabamu ikon yimasu biyyah da kyauta tamasu har k'arshin rayuwanmu, yakuma sa Aljanna ce makoma AMEEN*


Inna taso komawa katsina amma sam Daddy yak'i yadda dole ta zauna ba d'an taso bah.




Cikin sata d'aya Hamisu ya nema masu wani gida haya a Marafa 4bedrooms ne da babban parlor sai B. Q yakuma kawo masu siyan gidan, anyi ciniki angama komai yanzo nan da kwana 4 ko biyar zasu bar gidan.75 million aka siya gidan, sai motoci uku da aka siyar 100 million chiff na banki suka fitoh, babu bata lokaci aka kaima banki kudinsu suna ta godia.washe gari kuma sukayi parking a sabon gidansu da ke marafa Mommy sai kwashe baki takeyi Inna ta lura da ita, Inna na mamakin halin Mommy na rainuwa da girman kai uwa uba bakin ciki da hassada,

Mai daidacin Parlor ne, sai bedroom, cikin bedroom din da toilet a ciki sai k'ofa,na Daddy kenan inkafitoh da ka nan wani parlorn babba babu Laifi sai d'an corridor sanan bedrooms guda uku kowanne da toilet a ciki sai kitchen da chan k'arshin parlor banyan kawuce wani corridor shima, mommy ce ta dauka wanda yayi nesa k'adan da guda biyun sai Inna da Aunty Xulaiha suka dauki daya sai dayan Afifah da Salamatu(sauran yan aikin kuwa duk an sallamesu) tsaf Aunty xulaiha da mutanan Inna Su maman Ishaq da mom Fauxy suka shirya gida aikuwa sosai yayi kyau B. Q kuwa bedrooms ne guda uku sai toilet a waje sai kicin na tsakar gida, gida dai yayi kyau masha Allah amma Mommy sai kushewa takeyi wai gida a matse suna jinta duk sukayi banza da ita. Sai maman Ishaq suka taya anti zulaiha girkin dare kana sukayi masu sallama sukawuce Inna nata godia gami da samasu albarka.

Duk wanan abu da aketayi Afrah batada labari kuma duk tana waya da y'an gidan amma basu fada mata ba Afifah ma duk surutunta bata fadamata ba.



Afrah ce cikin gown na atanpa tayi kyau sosai, skin d'inta kawai zaka kalla kasan tana cikin kwanciyan hankali kuma tana samun kula bana wasa ba, fitowa tayi daka *Freey delicious* bkry dinta kenan hannunta reke da kwalin cake, sai da ta aje cake din gaban mota sanan ta dawo ta zauna a mazaunin driver, phone dinta ta dauka number yaaSulaiman tashiga dialing ringing 2 ya dauka

"Yadai sis" Suleiman yace daka chan mangaran

"Lafiyalau, gani a hanya zankawo ma cake d'in yau zancika alkawari"

"Am grateful, amma kinsan mun chanza gida"

Eyes Afrah ta zaro sanan tace" chanxa gida? When? Baby bata fadamin bah"

"Aikuwa an chanza" nan ya kwanta mata, sallama sukayi kana ta aje phone din taja motan tana mamakin canza gida babu ko sanarwa haka dai harta isa uguwan Inna ta kira aikuwa Afifah tayi picking " toh waje na ganki" Afrah nagama Fadan haka takashe wayan, daka nesa kadan ta hanga Afifah k'ara sawatayina bakin gate din gidan tayi parking ta fitoh hugging dinta Afifah tayi tana cewa"i Miss u so much sweet sis"

"Dallah sakeni shine ko kifadamin kow"

"Am so sorry sweet sis, wlhy Daddy ne yachai kar nafada" tayi maganan kaman zatayi kuka

"Najii zagaya ki daukan ma yaa Suleiman cake dinsa"

"Nawa fa anty Afrah? "Afifah tace nana zagayawa gaban motan

"Next time, kee sai zakiyi birthday ma"

"Kai aunty Affrah saura fa 5 months"

"Nasani ai kaman yau ne" Tayi maganan daidai da suke shigowa parlor

D'akin Inna Afifah ta jata

"Lalelale da Amaryan Abdulnasir" Inna tace tana washe baki

"Ni barni kun chanza gida ko musa ni"Afrah tace

"Ohhh na zakima lalata ja'ira sai kije kisamu ubanki shiyace kar a fada maku ai"

"Au Allah sarki Daddynmu"

"Auu daa nii za'ayima diban albarka kenan ni da aka raina koo? "

"Hmmmm ni bari naje na gaida Mommy "Afrah tace tana mik'ewa tsaye

"Mommy batanan faa"Afifah dake lasan icing tace

"Inna wai meyasa aka tashi a chan gidan ne? " Afrah tace tana kallan Inna

"Kee jeki kai wanan abun cikin" Inna tace ma Afifah, nan ko ta dauki cake din ta fita, tana fita Inna ta sanar da Afrah komai sosai Afrah ta sausaya ma Dad dinsu hadda kukan ta

"Ke dallah bakisan kaddara bane? "

"Nasani Inna"

"Toh hakuri zakiyi kuma Daddyn naku addu'a haka Allah yayi ai godia zamuyi ma Allah inda yanzo kuma ya mutu fa ai tashin hankalin da zamushiga sai yafi wanan ke kanki kinsani gana rasuwa gakuma tijaran yan banki"

"Hakane Innah"

"Yauwa ko kefa? Addu'a shine kawai abinyi"


"Insha Allah zamu k'ara kan wanda mukeyi, bari naje kawai tunda Daddyn ma yayi tafiya"

"Tun yanzo? "

"Ehh Inna bari nake kawai"

"MAdallah ki gaida angon naki"

"Toh zaijii" nan Afrah ta tashi tawuce, hanyan kicin suka hadu da Afifah tace mata gobe insha Allah zata dawo.



Afrah na shiga Mota ATM tayi, kud'i masu yawan gske tacira sanan tawuce wani super market, shopping sosai Afrah tayi tundaka kan kayan abinci da kayan da duk tasan Daddy na siya da wanda Mommy keso da Afifah duk sai da tasiya haka aka cika mota dadi tarinkaji yau zatasa Daddy farin ciki.

Sai 5:30 ta dawo gidan nasu, har cikin gida tayi parking nan ta kwala ma salamatu da Afifah kira suka fara firfitoh da kayan, Afifah nata murna hadda rawa haka Inna ma, sai da wani mai gidan makwabtan su yatayasu shiga da kayan dan bazasu iya bah, ana gama sauke kayayyakin Affrah taja mota tayi gidanta, Inna dai sai albarka take samata.



Ana kan shiga da kayayyakin ne Mommy ta shigo gidan, bin kayan takeyi da Ido shopping ne taga ba na wasa ba, tanbayan kanta tayi"ina Suleiman yasamu kud'i haka? "

Afifah ce ta katse mata tunani da cewa"mommy ki ga shopping dinda aunty Affrah tayi?"

"Afrah kuma"Mommy tace tana kallon kayan da kyau

"Ehh mommy bai dad'e da tawuce bama"

Shuru Mommy tayi bata ce komai bah, mamaki irin shopping din takeyi, wai Afrah, Ina tasamu kud'i haka? Ta tanbaye kanta, ohoo _biebie dee tace_haka har ta isa bedroom dintaa, xama tayi bakin bed babu ehhh babu a'a chan ta dauko phone dinta a cikin jaka, number Hafiz tayi dialing buh still switch off tsaki tayi sanan tashiga dialing Number Fatty har yagama ringing batayi picking ba wani wawan tsaki Mommy takuma ja gami da wugar da phone din, chan taji yana ringing kaman baza ta dauka ba chan kuma ta tashi ta dauka phone din ganin Fatty ne yasa tayi picking da sauri

Gaishe ta Fatty tayi Mommy ta amsa cikin sanyi Murya

"Mommy ta muryan ki haka? "

Nan Mommy ta kwashe komai ta sanar da Ita hadda shopping dinda Afrah tayi yanzo, sauke nunfashi Fatty tayi kana tace"Allah sa hakane mafi alkhari, Afrah ai dama bata rowa"

"Hmmmmmm Fatima, Ni yanzo problem Dina kud'in hajia Adama ne kawai duk da nasan akwai bashin Mutane a raina amma nata duk yafi damuna"


"Yanzo yakike so ayii Mommy? "

"Kud'i nakeso Fatima"

"Mommy gskia tawaje na babu d'an yanzo ya nena bani kud'i na wajena kuma baifi 30k"

"Toh ki turomin 30k din"

"Toh Mommy sai ki jira sai randa Allah yasa na fita"

"Bangane ba sai ki fitah"

"Ehh mana, mommy toh ki tanbaya Afrah mana Am sure zata baki ko nawa kike so inhar tana da shii" kat Mommy ta kashe wayan zuciyan na zafi, ina ta ina zata fara tan bayan Afrah kudi? Zama ta ina makuwa? Tagumi Mommy tasa tama rasa abinyi.
[12/18, 09:04] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*


_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch ♥ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~🌸


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_




*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_


_page 75-56_



_this page is for sweetheart A'ISHA A MOH'D(K'arshin wahala) thank you so much for the love and support may Allah guide, bless n protect you always n forever Ana mugun tare_🤝🏻💯💖❤😁

_gaisuwa mai yawan gske masoyana, thank you all Allah barmu tare har gidan Dadi Aljannah AMEEN_👏🏻👏🏻👏🏻


Ya labarin Hafiz?

Hafiz dai a koda Daddy ya chanza mai school a turkey ba natsuwa yayi bah, baya zuwa sai yaga dama kasancewa karatun k'asar akwai wahala sosai shiyasa shidai gashinan bayyi gaba bah bayyi baya yanan inda yake dakashii har wasu friends dinshi
Tare da taimakin wasu friends dinsa y'an Nigeria suka cigaba da danfaran mutane ta online, dama wayanda ba y'an online ba, kud'i suke samu ba nawa sa ba, shiyasa duk wani kaya na celebrity Hafiz na sakawa phone kowa Saide ba'ayi lunchin dinshi ba da anyi zaysiya, dama kanshii kawai ya sani baydamu da kowa bah shiyasa ma y'an gida duk basu sani bah, bashi da complaining da requesting kudad'e duk uban kudin da yake samu baya is an shii,
Kulin cikin dan faran mutane suke, kodawani lokaci suna kan computer kawai d'an danfara da cuta(Allah karemu) ga shaye shaye sunayi duk da dai Hafiz ba sosai yakeyi ba amma yana tabawa, suna cikin wanan hakin d'aya daka cikin abokinsu Aliiii ya samu masu wani amshakin mai kud'i a online wanda dan faranshi yazamemasu masifa da bala'i dakuma danasanii babba, d'an ko wanan Alhaji baiyi da wasaba sai da yasa amai bincike sosai kansu babu zato babu tsanmani hukuman chan sukayi ram dasuu, kuma mutumin da suka danfara yace shi bayaso a cisu tare ko iyayensuu su fanshesu kawai yanasu ne a yankemasu hukunci a kullesu had sukoyi hankali, sosai suka shiga tashin hankali, nan duk aka amshe duk wani abu dasuka mallaka kana akayi da su prison sai bayan 4 months za'a fiddo suu....





Yau Wednesday Gidan Shuru Sulaiman har yanzo baydawo ba, Afifah tana gidanan Afrah daka chan ake kaita school,Salamatu nata aikace aikacenta Inna da aunty Zulaiha suna parlor suna kallan Sunna TV, Mommy ce tayi sallama duk suka amsa mata gaishesu tayi Inna ta amsa tana yin kai sama d'an talura kwana biyu wasu chaji take gani tare da ita dayake mommy bata gabanta shiyasa ko bi takanta Inna bata yii ba, AntyZulaiha ma mamakin chanxawa mommy yakeyi d'an Dai Mommy bata zama cikin suu, chan Inna tace" maza jeki cikin d'aki ki daukomin maganin ciwan k'afanan" Inna tacema Anty Zulaiha

"Ahh Inna inada ko wani magani daka Niger aka amsomin shii, na ciwan k'afa ne bari na dauko maki" Mommy tace ta kokarin tashi

"Oo oo, barshi kawai nafi gane kan nawa, ke maza daukomin" Inna tace tana bai da hankalinta kan tafsir in marigayi shirk JA'afar Adam kaman batman Allah yayi ruwan Mommy ba har Aunty Zulaiha tadawo tashiga shafema Inna Kafa da maganan, tafsir ne yakeyi kan irin Iyayen da kerike yaran da banasu ba, sai surika nuna bambanci da sanka da isgilin ai yaran da banasu ba ba isah yazama komai ba sai Wanda su suka haifa har yake bada misali da wani bawan Allah yanda marikiyanshii da yaranta suka rainashii da kyar yayi karatu a wahale yake, yaranta ne kawai kejin dadi suke kuma karatu a makaranta mai kyau a karshe yace ynzo haka shii Wanda suka raina din Yakuma tashi a wahale shine ya dau nauyinsu gabaki d'aya dan yaran nata dasuka samu gatan a sankarce suka tashi babu karatun kirki dasukayi shii wanda akeganan ba komai bane shine ya tallafi yaruwarsu gaba dd'aya sukuma datake ganan sune aishe basu bane, ai Inna wani kabbara tayi"Allah Akbar Allah mai girma watou *D'AN HAKKIN DA KARAI NA*shine zai tsolema ido, wayace masu anayi da Allah? Wanan ai yima Allah katsalandan ne kuma kaso naka duniya ta k'ishi kaki naka kuma Duniya ta soshii inji malan bahaushe"Inna ta karasa maganan taba d'an murmushii

"Wanan Haka yake Inna Allah sa dai mudacee yabamu ikon zama da kowa tsakani da Allah kuma mubi yaran kowa da fatan alkhari bada mugun nufi bah"


"Ameen Ameen Zulai, Ameen kema Allah kawo miji na gari"

Shuru Aunty Zulaiha tayi amma ta amsa a xuciya


Ameen Mommy tace a hankali, jitake kaman d'an Inna akayi tafsir Din dan duk wanan mugun hali ta ne, ga habaicin da Inna taitayi tasan da ita yakeyi, gashinan tunba aje ko ina Ba tafara ganin abinta, Allah kadai yasan irin burin da taci kan y'aran ta sai gashi dayake Allah Allah gashi yana nuna mata komai dalla Dallah, Sulaiman ma tasan mugun hali ta ne yajamai haryanxo bai samu aiki ba, Hafiz babu labarinsa rayuwan aure mai dad'i 💯Fatty bata sameshii ba, wanda takema mugun Fata itace tasamu kwanciyan💯k'aruwan Arxiki💯 da cigaba komai da komai tasamu samu, Abdull ma k'iri k'iri ta hana afita dashi karatu gashi har zaikama d'annata datama gata batasan babin dayake ciki ba, wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata d'an gskia sosai wa'azin yabi jinin jikinta wanda ta manta one last rabonta da jin tafsir sai yau, goge hawayen tayi da sauri gami da mik'ewa

"Innah bari na d'an shiga ciki" Mommy tace

"Madallah "Inna tace batare da ta Kalle ta ba.



Mommy na shiga bedroom dinta zubewa tayi kan bed ta rinka Rusa kuka jitake kaman dan ita akai tafsir din nadama ne fal zuciyanta amma girman kai irin nata yahanata neman gafara, sai datayi mai isarta tashiga toilet ta wanko face dinta bayan tafitoh daka toilet kwanciyan tayi tana sauka ajiyan zuciya aikuwa babu dadewa bacci yayi gaba da ita, ta dad'e tana bacci sai 2 dai dai ta tashii, toilet dashiga ta dauro alwala tafito, sallaya ta shinfida ta tada sallah, ta dade sosai tana addu'a cikin sujjada kan Allah sa su Afrah suyafe mata kuma Allah bayyanar da Hafiz kafin ta idar tana zaune tana lazimi phone dinta yashiga ringing tashi tayi ta dauko ganin mai kiran yasa taji wani faduwar gaba daurewa tayi ta sallama cikin sanyin murya daka d'an bangaran aka amsa kana tace " Hajiya najiki shuru ne kinsan cikin satinan mukayi da ke, kuma banji wani bayani ba"Hajia Adama tace

"Wallahi ina sane Hajia akwai wasu kudin da nake jira ne, dan Allah kikaramin lokaci"

"Hehehehehe lallai Hajia Bilki innaga kin manta k'aidar mu kenan ko? Dakike cewa na k'ara lokaci, bayan tun last month yakamata ki bata amma sabida kece yasa nadaga k'afa sai ynzo kichai nakuma dagawa impossible kenan, dokarmu nan kaman yanda kika sani inka kasa biya kotuce zatashiga tsakani ko hukuma kinsan dai nii meting dina babu fitina cikinsa yanda kikaci kudi dolene kiyi kashin saa, ki saurari xuwani Nida su Hannatuu gobe ko jibi, inkuma kudin sunqi samuwa sai mu matsa gaba watou kotu" Tana gaman bayanan ta kashe phone din, mommy ji tayi kaman ta kurma ihu dan tashin hankali, kallan bedroom din tashiga yii gami da bude drawers din dakin koxata samu wani k'addaran amma duk babu duk tagama saidasu daxatabi ya bashii bata taba tunanin rayuwa zay chanza masu bah sai gashii duk wani fariya da tak'ama datakeyi yazama na banxa da hoofii da iska tan bayan kanta tashiga yii wai ya aiketa daukan rayuwan k'ara ta kasa ajiye kanta inda Allah ya ajetaa? Ta wukakanta d'anginta da yan uwanta na jini dan kawai basuda kudi ta manta Asalinta da kuma tushinta ta manta wacece ita da har tai ta wulakanta mutane tana isgilancii, yanzo wajen wa zata neman kudi? Wama zaibata cikin yan uwa? Bayan duk tagama yimasu tijara, gashii mijinnata datake tinkawo dashii baida Sulaiman kuma tashan ba Aiki yakeba bare yasamu 350k itakuma baza ta iya tanbayan Afrah ko mijinta ba dawani idoma zatakallesu? Ta inama zata fara? Wanan ranan mommy tayi shii cikin tashin hankali ko da Daddy ya dawo ya ganta wani iri tanbatan yayi amma tace babu komai tasan kota fadamai ba kudin zata samu ba wajenshii, kilama saidai yayi mata fad'a ita kuma mafita kawai take nema yanzo.





Kwana biyunan duk Mommy tayi shi cikin matsanancin Tashin hankali, duk wanda ya ganta sai yaga alama amma ko ka tanbaya zatace babu komai, ko Sulaiman yakira ma inya tanbayeta zatacemai babu komai d'an tasan baida su, Fatty takuma tasan damuwan Mommy amma batada kudin kuma takasa fadama Afrah ma dan itama kunyan takejii
Yau Saturday Afrah daka Afifah sunzo gidan tinda sukaje suka gaida Mommy dake bedroom suka dawo parlor sunata hira, Afitah sai juba takeyi Afrah kam tana zaune a k'asa ga fruit a gabanta sanan da su ice cream da

Please Login or Register in order to submit comment