Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a rai har ya vara damushi d'an yanzo banki sun fara bukatar kudadansu da yaci, toh kayan sune Hope dinsa amma suru vabu wani labari
Yauma zauna yake shin kadai parlon shi yayi nisa sosai cikin tunani har daida Suleiman ya dafa shii kana yace" Daddy tunani irin haka babu kyau"

"Nasani Sulaiman amma kuma dole ne, sabida bashin bakinan kulun da su nake kwana da shi nake tashi Suleiman wallahi Inna *Danasanin*, cin wanan bashii"

"Kar kadamu Daddy insha Allahu kayanku zasu fitoh kuma da yaddan Allah zaka biya banshi"

"Allah sa haka, kana ko samun Hafiz ta waya? "

"A'a nima maganan da nazo muyi kenan"

"Allah Dai ya shiryeshi yasa kuma yanayin karatun"

"Ameen ameen"

AFRAH tanan cikin kwanciyan Hankali ita da mijinta ga sch tana juwa haka kuma har yanzo bata dena yin cake da sauran abubuwa ba ka d'an Abdulnaseer bai hanata yana da burin tallafamata nema sosai k'an sana'ar nata.




'Yan banki sun fara sa Daddy a gaba d'an lokacin da yayi masu alkawarin biya yakusa yacika, sosai hankalin Daddy ya tashi nan da nan yakira Sulaiman ya saida mai mishi babu abinda Daddy ke tsoro kaman tijaran y'an bakinnki, babu dad'ewa Suleiman ya iso d'an anan kaduna yake service dinshi
Kwantar ma Daddy hankali, yayi kana suka fara neman mafita nan daddy ya yanke shawaran sai da gidanshi da ke Kabala sai shaguna guda biyu, sosai Suleiman ya kalleshi kana yace" Daddy kadai sai bazai su wuce 20million ko"

"Nasani Sulaiman"

"Toh nasan ai wanan kudaden zasu isa ko?

"Hmmm Sulaiman kenan bakaji nace ina danasanan cin bashin danayi bane? "

"Naji Daddy"

"Toh wallahi inhar zan had'a duk wani abinda na manlaka banda gidanan toh ba xasu biya bashinan ba, d'an bashi ne masu yawan gske kuma sanan kanka ne ni ban kasan ce mai siyan k'addara ba, dama basa hannu cikin business na Ghana ba da abin zai zo da sauki d'an kud'in da na zuba yafi 70 million"

Ido Sulaiman yazaro sanan tace "Daddy waya baka shawaran yin wanan Business din? "


"Babu kowa Suleiman, inaga k'addarata kenan kuma a shirye na ke na amsa koma wani iri ne"

Sosai Sulaiman yaji tausayin mahaifinsa ya kamashi yaji dama ace yana da kud'i ya sharema Daddynsu hawaye

Nanan Daddy yayi waya da wani yaron su Hamisu ya sanar da shi kan sai da gidan da kuma shagunan, bayan kwana Hamisu yagama komai yakawo kud'i Ihsani Daddy yayi mai Hamisu nata godia

A ranan ya turama bakin 15milion din nan dai suka k'ara mai 2 moths, addu'a Dady da Sulaiman sukai tayi kan Allah temakesu k'ansu yazo kafin lokacin.

Alhaji Yunsuf Ma Hankalinshi sosai ya tashi d'an nashi bashin yafi na Daddy yawa nan dai shi ya bada milin25 ya rage 2 months shima suka k'ara mashi nan duk suka dukufa da rokon Allah babu dare babu rana.


Afra sosai tayi fice wajen yin snacks madu dad'i da kuma kyau, irin ficen snacks dinta yayi ne yasa Ummie da aunty baraka bama Abdulnaseer yawara kan ya bud'emata join na saida snacks ai kuwa cikin lokaci d'an ya gama komai tare da ya aikin wajen sancewar akwai kudi, sosai Affrah tayi murna hadda yima Abdulnaseer kuka d'an yafara cika buri da takeda shi cikin ranta ranan wuni tayi tana k'iran yan uwa da abokan arziki tana sanar dasu ciki Hadda Fatty (d'an sometimes akan sameta a waya) Mami, Uncle Junaid, Daddy, Inna da sauran yan uwa na kusa musaman suka kira Abdulnaseer sukai mai godia gami da samai albarka Mommy kam yi tayi kaman batajii ba

Haka aka fara gudanar da aiki a Bakery na Afrah cikin kwanciyan hankali da natsuwa, in AFRAH ta tashi a school ta kan lek'a sai yamma ta dawo, bata samun matsa da ma aikatan sam coz duk sun iya aiki kaman ita sometimes kuma takanyi da kanta, cikin lokaci kad'an wajen yayi suna sosai.



Ansa Ranan Bikin Zarah da Mahmoud d'an yau nema aka kawo lefanta, masha Allah kaya sunyi kyau sosai anata san barka, su Afrah ne Gaba suke komai, koda mutane yan kallon lefe suka tafi, Su Husnah duk sunwuce sai ita kasala takeji sosai gawani irin gajiya kaman ta kwana ta wuni tana aiki tanan

kwance a bedroom na Zarah, Zarah ce tashigo dakin da cup hannunta zamatayi bakin bed kana tace" ta nass wai kodai yau nan zaki kwane"

"Ke walhy bazan iya driving ba, sweetheart xan kira ya zo ya daukeni"

"Motarki kuma fa? "

"Pakamin ita kawai a compound "

Nan dai ta kira ango na ta fadamain yaxo ya dauketa bazata iya driving ba, hankali tashe Abdulnaseer yazo duk ya damu, koda suka koma gida tattalinta yaitayi kaman kwai, amma duk da haka da zazzabi ta kwana, da sassafe ya sata tashiya ya kaita hospital, babu irin rokon shi dabatayi kan ya barta ta warke amma sam yace shi bayyada ba, ba d'an taso bah haka ta shirya suka wuce hospital din...
[12/18, 09:04] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*


_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch ♥ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~🌸


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_




*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_


_page 68-69_



*S*una isa hospital din, office din doctor Jamilah direct sukayi bayan sun gaisa da doctor ne Abdulnasir da kanshi ya fidi abinda ke damun Afrahn, aune aune da gyaje gyaje a kayi mata bayan d'an wani lokaci result ya fitoh kallan shi doctor Jamilah tayi sosai kana tace" congratulations"

Kallanta yayi irin naneman k'aran bayanin nan

Kai ta dagamai kana tace" matar ka na dauke da ciki na 6weeks"

Hamdala yafarayi kana yabama AfrahTight hug sosai nan yashiga sa mata albarka gami da kara godema Allah da kyautan Da yabasun gaba daya ya manta da doctor Jamilah gyaran murya tayi yasa yatuna da inda yake nan da basu shawarwari kana suka wuce.

Gidan su direct yayi da ita bai bari ko gaisuwa sunyi da Ummie ba ya jayyano mata komai, nan Ummie tashi ga hamdala gami da godema Allah ita dai Afrah kunya duk ya cika ta Abdulnasir kam babu ruwanshi sai kiran yakeyi yana sanar ma jama'a haka Ummie ma ita abin nasu kamar a film.

Sosai Afrah kesamun kula tin daka kan y'an uwan Abdulnaser ummie da Anty Baraka kuwa ba'a magana haka Inna da Mami ma sosai sukayi murna sunkuma yi Addu'an Allah yaraba lfya.
Musanman Inna kesawa tindaka katsina kawoma Afrah abubuwa iri iri na kwadayi wanan abu na bakanta ran Mommy addu'a tafata yi Allah sa cikin ya bare taga k'arshin rawan kai d'an har Daddy murna yakeyi d'an yanzo Mommy bakin cikinta a fili yake babu wani boye boye kaman da komai free takeyi shii yanzo bawani ginman Daddy take gani bah coz baya sake mata kud'i kaman da, Sulaima kuwa kulun cikin yima Mommy Addu'an Allah ya shiryeta yakeyi babu dare babu rana.

Zaune take a parlor sai masifa takeyi tana zage-zage Suleiman ne yashigo da sallaman shi amma Mommy ko amsawa bata yii ba, kallaanta yayi sosai kafin yace" Mommy lafiya? meya b'ata maki rai haka?"

" wai hanni Hajia Zaituna sata ma wulakanci kan dubu 100 shine takirani wai tanasan kudin nan da 3days, nama Daddy dinku magana amma har yanzo kudi sunki fitowa"

"Abubuwa ne suka ma Daddy yawa amma ai da ya biya kema kin sani Mommy"

"Naji masoyin Uba, inda kafi akwaiki kenan wajen kare Ubanka da su Afrah"

"Allah huci zuciyarki, zan baki 40k ki bata sai ki rage"

"Toh wai saura wata nawa ne kagama wanan bautar k'an? Shi Daddy ku ba company ba da yanada shi duk da kana chan kana aikin ka "

Smiling Suleiman yayi kana ce" nan da lokaci kadan zan gama, aiki kuma insha bazai yi wahala ba"


"Toh yaushe zaka kawo min kud'in dan so nake na tura mata yau, bari ma nayi trying number Fatima ma nace ta turomin yanzo Daddynku yazama abinda ya zama"

"Anjima insha Allah" nan yafita yabar mommy na kokarin kiran Faty

Cikin sa'a kuwa tasameta ringing 3 ta dauka bayan sun gaisa ne Mommy tace wai tayimata transfer din 100k daka b'agaran Fatty wani bacin rai taji tsaki tayi kadan kana tace" wai mommy sau nawa zan cemaki bana fita hum? Ko ta wayan zan maki transfer din ne? "

" d'an ubanki ni kike fadama magana?"

"Toh mekikeso nace maki baga AFRAH ba ki kirata kice tayi maki transfer mana ni kibar ni naji da abunda ke da muna please"

"Lallai ma baki da hankali nice zan kira Afrah nace ta turomin kud'i? Allah kiyaye wallahi gara na mutu babu har yanzo bata da abinda zata bani ai d'an bata kai bah kuma bata isah ba"

"Toh naji Mommy d'an Allah kin barni toh danni banda abinda zanyi maki" tana gama fadin haka ta gashe wayan tana kuka sosai sai yanzo da ta aure Musty ke koya mata hankali tafara nadamar abun da tayi da, kallon bedroom dinta tayi sosai komai najin dadi da more rayuwa a kwai shi a cikin d'akin ga kud'i ga komai amma babu kwanciyan hankali ko kadan ko da yaushe cikin tashin hankali take ga zaman kadaici sau biyu Musty na zubarmata da ciki wai bai shirya haihuwa ba kuka sosai Fatty tasha duk wannan masifar da take ciki AFRAH tayi ma fatan shiga irin wanan halin sai gashii ita ga dai kudin amma babu school babu farin ciki babu kwanciya hankali wanda ta RAINA tana ganin ita ba kobai bace kuma ita ba kowa bace ita duk tasamu cigaba dakuma farin cikin rayuwa, fuskarta na goge kana tajawo phone d'inta tashiga dialing number AFRAH har yagama ringing batayi picking ba chan sai ga call din AFRAH yashigo cikin farin ciki Fatty tayi picking gami da cewa" Sis ya k'arfin jiki? "

Dariya Afrah tayi daka chan bangaran sanan tace" lafiya lau, alhamdulillahi"

"Masha Allah haka mukeso, ya Baban baby?"Fatty tace tana daria

"Lfyanshi lau, ai munan shigowa abuja next week insha Allah"

"Allah kawoku lfya gskia nayi murna sosai"

"Ameen amern sis ina yayana yake ne? "

Sai da fatty ta kalle side dinda bedroom din Musty yake kana tace "yanan lfyalau"

"Ah gaidamin shi acemai munan zuwa"

"Toh zayji" jira suka d'anyi sanan sukayi sallama

Kallan phone din Fatty tayi sai kawai taji hawaye na zubomata amma kuma taji dadin wayan da sukayi da AFRAHN, nan dai takira yaya Suleiman, yaya Abdull, Daddy da Inna albarkan da Daddy da inna keta samata ne yaita sata farin ciki sai smiling takeyi
Musty ne yafito daka bedroom dunsa sanye yake da 3quarter da T-shirt, zama yayi a 1 sitter kana yace" Baby kin gama abincin kuwa? "

"Ehh nagama"Fatty tace a natse

"Good kedawa kiketa waya? "

"Su Daddy ne da su Yaya Suleiman na kira"

"Ohhh sunan lfya ko? "


"Ehh lafiya lau, AFRAH tace zasuzo next week"

Shuru Musty yayi na minti 3 chan yace" ohhh wanan cousin naki mai kirki da akayi bikin ta bayan namu ko? "

Baki Faty ta washe gami da cewa" yes ita"

"That's nice Allah kawota lafiya"

Mamaki Fatty tayi ganin Musty yayi saurin yadda Da zuwan Afrah, wanan ranan dai Musty da sauki bai birkice mata ba kuma bai fita ko ina bah.




Mommy yanxo babu wahala anyi fad'a da ita duk friends dinta basayi da ita yanxo sabida rashin san gaskianta y'an uwanta ma duk sunfita harkansu sabida kawai sun fada mata gskia, Suleiman dake kokari sosai a kanta amma Mommy bata gani sai rainuwa abu k'adan tace ta k'osa Hafiz ya dawo(hafiz din da ko a phone ba'a samunshii)


Kula sosai Afrah ke samu ta wurare da dama kowa santa da tattalinta yakeyi abin dai gunin sha'awa.

Bakery dinta kuwa Allah ya samai albarka sosai take samun alkhari gashi yayi fice sosai ita har mamaki takeyi, kudad'en da take samu kuwa sai dai ta temaki wanda bayida shi koda bata sanshi ba ita dai bata komai da shii d'an Abdulnaseer ya tsare mata komai, in taje katsina gaida su Mami haka takeyi ma mami da yan uwanta alkhari Abdulnasir ma yayi masu duk da basu nemi komai sun rasa ba, haka ta side babanta sai dai in bata ji abu ba, inko taji ko ta bank ne sai ta tura Afrah bata da rowa sam abunta bai rufe mata ido ba ko kadan abunda na jama'ane ko da bata sanka ba bakuma tasan da inda kafitoh bah shiyasa kowa kesama ta albarka.

Sunje Abuja tarba mai kyau suka samu da ka wajen Fatty da Musty, sosai Afrah taga changi wajen Fatty d'an hira suka sha sosai daka Abdulnadir, musty Afrah dakuma Fatty sai dare suka tafi side din bak'i da yasha gyara, kwanan su biyu suka bar abuja suka dawo kaduna, wani ikon Allah tin da su Afrah sukazo Musty bai yi wani halin banxan shi ba Fatty taji dad'in juwan su Affrah sosai dan sosai ta ragemata damuwa da take ciki, musty kaman yana jira suna wucewa takoma gidan jiya.


Suna dawowa aka fara gudanar da sha'anin bikin Zarah da Mahmoud bikin yayi kyau sosai Amarya da angonta sunsha kyau har sun gajii haka su Afrah da husna da sauran k'awaye duk suka sha shagali, Inna, anti Zulaiha sunje Daddy da su yaya Suleiman ma sunje daurin aure haka aka gama shagalin biki kowa na san barka
Ankai Zarah doctor's quarters gidanta yayi kyau sosai masha Afrah tasha girga girga hadda Abdulnasir din kanshii.
Yanzo bikin Husna ne a gaba kafin sufara exam's ne.



Yau Sunday ranan Afrah a gidan su take yini zaune take a d'akin Inna tana cin d'an wake wanda Afifah tayi mata Daddy da yaya Suleiman da yaya Abdul ne suka shigo d'akin k'ara gaisu su Afrah tayi sanan ta ciga da cin d'an wakenta Afifah na manta zance, hira sukerayi cikin farin ciki phone Suleiman ne dake hannun Afifah ya shiga ringing "laa wallahi Anty Basma ce" cewar Afifah tana daria

"Kee bani wayana" yaya Suleiman yace

"Wacece kuma Basmah"/Inna ta tanbaya

"Walhy girlfriend din yaya ce ai muna waya da ita"

"Bani wayanan ni zan dauka"inna tace

Suleiman da ke tsaye duk Afifah tabashi kunya sbida Daddy shi baiyi picking call din ba kuma shii bai ba Inna tayi picking ba " Allah sanya tabbatar da alkhari je kayi wayan ka" Daddy yace
Sosa k'eya Suleiman yayi kana yafice daka d'akin

"Kai kuma dungum yaushe zaka kawo matar taka? "Inna tace tana kallan Abdull

"Kai Inna D'an Allah ki barni"

"Auuu babu farin jini kenan? "

Daria sosai Afifah ta bushe da shii hadda rike ciki Abdul na kokarin yin magana Phone din Daddy ya hau ringing shuru duk sukayi kana Daddy yayi picking call din
Basan mai akacema Daddy bah nadai ji yana cewa"Alhamdulillahi, Alhamdulillahi Allah iso da su lafiya"

Bayan ya gama wayan Kallan dukkan su yayi cikin fara'a da kuma farin ciki kana tace" kayan mudai da zasu zo ta jirgin ruwa ne suke hanya insha Allah " Nan suka dau kabbara gami da yima Allah godia haka Suleiman ya shigo ya samesu ko da aka fadamai hamdala yayi gami da yima Allah godia duk wanan abu da akeyi Mommy bata sani ba dan bata shiga cikin su Inna wai mak'iyanta ne, haka suka wuni farin ciki sai bayan sallan magrib Abdulnaseer yazo daukanta amma basu bar gidan bah sai da sukayi Dinner.



*Bayan Sati d'aya*

Zaune suke dukkan su a babban Parlor Daddy, Mommy, Inna, Anty Zulaiha, yaya Suleiman sai Afifah d, wani series film na Philippines suke kallo Inna duk ta isha Afifah wai ta fassara mata, phone din Daddy ne ya shiga ringing ganin mai k'iran nashi yasa shi washe baki sallama yayi daka chan b'an garan aka amsa a wahalce

"Lafiya? " Daddy ya tanbata

Daka chan ban garan akace"alhaji jirgin kayanku ne keta nitsewa munyi duk iya k'okarin mu amma abin yaci tura"

"Inalillahi'wainnah'ilaihinraji'un" shine kalman da Daddy keta nanatawa

Tashi duk sukayi suna kallon sa
"Lafiya? Meyafaru?" Mommy' tace

"Shu'aibu meyafaru? kasanar damu" cewar Inna da duk ta rud'e

Sulaiman da Afifah kam kasa cewa komai sukayi haka anty zulaiha

" nii Shu'aibu ina zan kai bashin banki? Kayan mu ta jirgin Ruwa ya tsine bashin Banki ya zan yi dashiii? Ins tsoran tirajan banki, kayanmu sun nit..."bai k'arasa ba ya fad'i k'asa....




_wallahi ban da bakin da xan godemaku masoyana nagode sosai Allah saka da alkhari ina maku fatan alkhari a duk inda kuke a fadin duniya kuma ina k'aunarku har cikin raina_
[12/18, 09:04] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*


_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch ♥ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~🌸


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_




*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_





*PAGE*7⃣0⃣




*S*ulaiman ne yayi kan shi cikin sauri, baiyi wata wata ba ya dauke shii sai mota, mommy, Inna da anti Zulaiha duk sun rude Afifah kam sosai take kuka
Suleiman ba tsaya jiran suba ya jaa motan cikin sauri gaskee, gudu ya ringa shararawa kaman zai tashi sama, minti minti yana juyawa ya kalle Daddy, cikin ikon Allah suka iso hospital, nan da nan ayi kan Daddy nan Reception Suleiman ya zauna tausayin Daddysa sosai ya kaama shii hawaye ne ya fara zubowa daka idanuwan shii gogewa yayi cikin sauri nan ya shiga karanto addu'a daban daban.


A gida kuwa su Mommy na ganin haka Suma duk suka shiga cikin mota bala ya jasu sai hospital din, a reception suka ga Suleiman nan suka shiga tan bayan shii amma Suleiman kasa basu amsa yayi sai chan yace " ba'a fitoh da shii ba tukunan" Inna Addu'a kawai takeyi haka Afifah da Anty Zulaiha mommy kuwa kuka takeyi tana cewa" Yaya zamuyi da banki ni Bilki? Ga kaya sun nitse " abubuwan da taita fada kenan
Wani irin tsawa Suleiman yayi " haba Mommy muna ta rayuwa kina ta wani kaya da banki, ki barmu muji da abinda ya damemu please" idanshi jajur yakeyin maganan
Shuru kuwa Mommy tayi bata kuma cewa komai ba,aunty Zulaiha ne ta koma gida d'an danko wasu kayayyakin da za'a bukata Bala ne ya kaita.

ganan shurun tayi yawa ne yasa Afifah ta shi ta matsa chan gefe
Number Afrah tashiga dialing da Phone din Inna dake hannunta,
Afrah da ke kwance jikin Abdulnasir taji wayan ta na ringing " mik'omin sweetheart" tace ma Abdulnasir
Washe baki Afrah tayi kana tayi picking gami da cewa" tsohuwa mai ran karfe"

Daka chan b'angaran Afifah tace" ba ita bace" cikin muryan kuka

Tashi zaune Afrah tayi kana tace" Baby wht happen? Meyasa ki kuka kuma"

"Daddy baida lafiya muna hospital dinda muke xuwa"

"Meyafaru? Daka waya sai kuka" Abdulnaseer ya tanbaye taa

"Daddy ne ba lfya, yana hospital " Afrah tayi maganan cikin kuka sosai

"Kibar kuka insha Allah Daddy zai samu lafiya, insha Allah bari na sa kaya muje"
Farar jallabiya Abdulnaser ya sanya Afrah ma gown tasa ta dauki hijab dinta sukayi hospital d'in.


Duk sunan zaunen tsaye kusa da d"akin da Daddy ke ciki doctor Khalid ne ya fito nan duk suka shiga tanbayan jikin Daddy " kar kuda mu muje office please" bayan shi duk suka, kallansu dukkan su doctor Khalid yayi kana yace" bawani abu bane kawai tsorata yayi, amma insha Yana tashi daka bacci zai dawo normal yanan a room 21"

"Oky mungode sosai doctor" Sulaiman da Abdulnaseer suka ce Inna kuwa Albarka taita sama doctor Khalid.

Kwance yake yana baccin sa peaceful, matsawa kusa Afrah tayi tashiga tofamai addu'a

" please ki barshi kar ki tashe shii" cewar Mommy da ke matsowa

"Mommy kema please kitashi" Suleiman tace
Inna dai kallon Mommy kawai takeyi, tsawa kuwa tayi chan naji tana cewa" ai sai ki daure kizo sarkin Miji ya hana fita, Daddy kune babu lafya" tana gama fad'an haka ta katse wayan tana naganganu kasa kasa

Fatty kam kuka tasha gami da salati

"Wai Lafiya da ka waya sai kiwani fara kuka"Musty yace

"D'an Allah d'an girman Allah da darajan manzon Allah SAW kabarni naje kaduna gobe wallah Daddynmu ba lafya" ta k'arasa maganan cikin kuka

Tausayi taba Musty sosai dawowa kusa da ita yayi kana ya jata zuwa jikinsa sosai " sorry kinjii, insha Allah Daddy zai samu lafiya"

Janye jikinta tayi daka nashi, kkallanshi tayi sanan tace" toh zaka barni naje? "

"Shhhhhhhh kibar kukan haka, zamuje insha"

"Nagode"

"Amma nace kibar kuka ko? "

Haka yaita lallashinta hattabar kukan.



A hospital kam sunan zaune har wajen 10pm Inna ne ta kalle Abdulnaser kana tace" maxa kuwuce gida gobe da safe in Allah ya kaimu sai kudawo"

"Ah'a Inna inan har Daddy ya tashi" Afrah tace

"A'ah Affrah kinsan dai yanzo bake kadai bane ko? Sabida haka kije gida insha lafiya zai tashii"

"Zan bita Inna"Afifah tace

"Toh kuje, sai Allah ya kaimu"
Sai da Afrah ta matsa ta k'ayima Daddy Addu'a kana sukayi masu sai da safe suka wuce.


Suna wucewa kuwa Daddy ya farka da salati a bakin shii, Suleiman ne ya taima kamai ya tashi zaune ya jingina da pillow, Sannu duk sukai tamai yana amsawa a hankali, 🍵 tea Mommy ta had'a mashi ya amsa yana sha a hankali shigowa doctor yayi yace babu wani problem

Nan Suleiman yakira Bala driver yazo ya mai da Mommy da su Inna gida shikuma zai kwana da Daddy.






Washe gari da sassafe Afrah da Abdulnaseer suka iso hospital din da brkfst mai rai da lafiya gai da Daddy sukayi ya amsa cikin sakin fuska basu d'ade ba suka wuce kasan cewar Afrah nada test a school, Afifah kuwa bata samu taje ba, sun wuce babu dadewa su mommy suka iso, sunan zaune Doctor Khalid ya shigo nan ya k'ara duba jikin Daddy yace komai yayi normal.nan Daddy ya bukata sallama aikuwa doctor Khalid ya mashi tarkato komansu sukayi suka dawo gida, shigowansu babu dad'ewa Fatty da Musty suka iso, side Daddy sukayi Direct daka shii sai yaya Suleiman a d'akin cikin Ladabi Musty ya gaida Daddy gami da mashi ya jiki Daddy ya amsa cikin sakin Fusaka, cikin sakin fuska ma suka gaisa da yaya Suleiman shima itama Fatty cikin ladabi ta gaidasu nan tama Daddy ya jiki, sai Musty ya gaida Mommy da Inna kana yacema Fatty zaije gidan su nanan malali da yamma xaidawo.


Sai 2:30 Afrah suka fitoh lecture direct gidasu tayi nan ta tadda Fatty tazo murna sosai sukayi na ganin junarsu nan suka bod'e shafin hira mommy na d'aki bakin ciki duk ya isheta da da yamma Affrah da Fatty tare suka shiga cikn suka shirya abincin Dare suna saune a parlor ana gab da magrib Mommy ce ta aiko Atika tazo ta kira Fatty, Atika na bari parlor Fatty tayi bedroom din mommy

"Mommy gani" Farty tace tana daria

"Mahaukaciya cikin mak'iyanki zaki shiga ki zauna kina washe baki kina zance ko? "

"Haa kajimin mommy nifa shiyasa bana kin haushe in Musty ya hanani zuwa wlhy ko dan ke, ke kin cika masifa da k'anan maganganu walhy muna zaman lafitanmu zaki fiddo da wani salo kuma ni gskia ban san haka" Fatty ta k'arasa magan tana turo baki gaba

"Ahh lallai kema din kinbi sahun Afrah ko? Ni kike kallo ki kefada min magana haka ko? "

"A'a ni kar kimin wani muryan tausayi ke dama Haka kikeyi abu hakan gskia ba sai kiwani fara fuskan tausayi"

"Yayi kyau"

"Tohh ni nawuce parlor"

Mommy

Please Login or Register in order to submit comment