Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba sunan taso ba amma ba yadda ta iya, y'an katsina sunzo sosai dan duk k'anan Inna Hadizaa sunzo haka wasu daka cikin dagin Malam ma,anyi suna da kwana 2 duk y'an katsina suka koma yarage ina Rakiya kawai,da wata k'annuwar maman Bilkin,
shu'ibu yah'ada masu shatara na arziki sai samai Albarka suke.
Haka zaman Salis yakasance gidan komai yakeyi Bilki da kanuwarta suna samai ido har yakai inna Rakiya tafahimta amma tasa masu ido.
Saidai Bilki tayi arba'in Sanan suka shiga katsina siyaya sosai duk yaran sukama iyayensu ido kawai Bilki tasa takuma sa a ranta insunje katsinan Zaata fadama inna cewar Azeezah nasan Salis tinda talura surukan Nata masu saukin kai ne su.
Sun isa lfya sunkuma samu tarba Mai kyau amma duk da haka Bilki sai yamotsa fuska takeyi d'an ita aganinta duk dan anga mijinta nadashi ne yasa sukemasu haka.
Ana saura kwana d'aya Subar katsina tasamu inna da zanchen Salis da Azeezah Daria Inna tayi sanan tace"toh ai shi Salis d'in yakusa aure,y'ar gidan aminin malam zai Aura Rabi'atu" murmushi Bilki ta k'akalo amma dai na ciki na ciki k'ar dai wanan yaron bai fada maki ba" ina tace
"aikuwa dai bamuyi maganan bah" cewar Bilki cigaba da cewa tayi da Allah sanya Alheri yasa kuma ayi da mu"inna ta amsa da ameen..
Tindaka wanna lokacin Bilki ta k'ara tsanar duk dagin mijinta ta r'ikesu a rai.
Koda da bikin Salis din yazo bani abun arziki ta tsinana bah kasancewanta mai rowa ce ita,haka dai ayi biki lfya aka kawo amarya Rabi'atu gidanta side din da Salis d'in yake aka k'ara gyrawa sanan akasa kayan Amarya.
Haka rayuwa tai ta tafiya dai zaman gidan dai gashinan ne Dan Bilki ta k'aro wulacanci.
Rabiatu nada wata 6 Bilki ta k'ara haihuwar da namiji watau Hafiz nan fa kanta yak'ara girma wai ita maman maza d'anginta na k'ara zugata.
Tahaihu da wata 8 itama Rabiatu ta haifo d'anta d'a namiji watou Abdulrahman ita katsina tako MA saida tayi wata2 chuff tadawo kaduna.
Yara dai sunyi wayo sosai Masha Allah,Sulaiman nasan anty Rabi haka itama,Bilki ko batasan wanan Abu da Suleiman keyi Sam
Ana haka Malam Abubakar yafara rashin lfya yaran nashi duk hankalinsu yatashi masu kaduna basu Katsina,asibiti Mai kyau aka kaishi,amma ciwan na Malam sai addu'a kwananshi 12 a hospital ya rasu Inalillahiwa'ina'ilaihirajiun duk sunji rasuwa mahaifin nasu sosai amma bayanda suka iya Wanda yafisu sanshi yadaukeshi sai muce Allah jikansa ameen .
Bayan rasuwan Malam yaran sunso inna tadawo kaduna amma tace a'a sam d'an haka suka barta saidai suna kula sosai da ita kuma suna zuwa a kai akai.


Haka rayuwa yaita tafiya shu'ibu nata k'ara samun bud'i haka Salis ma.
Saida Hafiz yayi shakara 3 sanan Bilki ta sake haiwuwa, wanan karan Mace tasamu watau Farty, watanni tsakani Rabi'atu ma tasake haiwuwa sunan inna Hadiza taci suke k'iranta da Afrah.
School d'aya duk suke zuwa yaran Suleiman, Hafiz, sai Abdulrahm iyayan na k'okari sosai a kansu sai dai wani lokacin Bilki na b'atawa d'an ita bata d'auka yara d'aya ba bata had'a yaranta da kowa ba.
Su Afrah Nada shekara 4 Daddy yashirya masu birthday na gani kuma na fad'a sosai ya kashe kud'i a Birthday'n haka a kaci aka sha akasha pictures y'an Uwa da abokan arziki sanan akatashi.
Afrah nada shekara 6 Daddysu ya rasu wayyo yaran sunsha kuka haka inna ma shu'ibu ko ba'acewa komai d'an sai dayayi kwanciyan asibiti na kwanaki, hakadai sukayi hakuri sukabi marigayin da addua d'an shine mafita
Rabiatu nagama takabanta takoma Katina d'an Daddy yace babu inda yara zasu abarsu a hannunshi haka inna taita samai albarka.
Mafarinda kik'on su Afrah yakoma hannun Mommy Kenan.
Daddy yanzo bayazama abubuwa sunmai yawa Dan ta hannushi duk wani shikafa dake shigowa kaduna a hanshi yake
sanan Bilkin bata barshi haka ba D'an haka Abubuwa dayawa sukafara chanzawa sai addua kawai

Shu'ibu yarage zuwa Katsina sosai Inna na magana zaice abubuwa sunyi yawa Addu'a kawai takemai kaman yanda tasaba.
Abubuwa dayawa sunfaru ciki hadda tafiyan Suleiman school Dubai Bilki kuwa bako wace mace take bi ba d'an acewarta ita matar manyace.
Batasa Zata sake haihuwa ba babu shiri sai ga Afifah tazo🤣 akwai tazara sosai tsakaninta da Farty







*BACK TO STORY*
[12/18, 09:03] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAINA...*

_PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S_
( _we don't just entertain and educate, we also touch heart of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~🌸

_dedicated 2 amazing sister Afrah bhai_
_I also dedicated dis page 2 all members of biebie dee novels group,thanks for d love n support,MUCH LOVE_❤❤❤


_page 7-8_



""""Farty na shiga d'aki kayan hannunta ta zube a kan bed ta shiga toilet, wanka tayi gami da alwala rigan tasa mara nauyi sanan ta tada sallah, bata bar kan sallayan bah sai datayi har isha,babban palo ta fito direct nan taga mommy da Hafiz suna hira, Xamatayi kusa da mommy k'adan sanan tace" mommy wai me aka dafa yau ne?"
" kee dallah tuwo ne" Hafiz yace Farty tace" Salamatu tayi ko Afrah?" Mommy tace Afrah ce" tashi Farty tayi tabi hanyan kicin, Mommy ta bita da harara

Ta zubu tuwan kusa da Hafiz ta zauna tana danna waya,ajiye plate din tayi ta matso kusa da Hafiz shima phone yake dannawa" Hafiz plz kalla wanan guy din, kasanshi?"
ansan phone din yayi yana k'ara kallan pic din gyrawa yayi yace" kee ina kika san Ahmad Muhammad Yakasai?"
Smiling tayi sanan tace" wlhy a instagram muka hadu,jiyama munhadu a syd resort naga kai kasan mutane shine nakeson san sanin suna da ku'di ne sosai ko yaa d'an ni banasan wahala" kee yi shuru pls kinsan kud'in family din Yakasai kuwa wlhy bakida hankali" duk wanan maganganun da sukeyi Mommy na jinsu batace komai bah sai ma gyra kwanciya datayi.
Plate din tuwan Farty ta jawo tacigaba da cewa" Hafiz plx da gske kakeyi? Toh wlhy ina san shi yau d'akin Afrah ma zan kwana dan nabata labari tasan ni babban yarinyace ba k'arama ba wlh"dariya taitayi tanacin tuwanta tashi Hafiz yayi yana tsaki


Kusa da Mommy tadawo tana nuna mata pics din Ahmad Muhammad Yakasai murmushi Mommy tayi gami da cewa"Allah mana zabin Alkhari Farty tace" Amiin dai Mommy,dan Allah Mommy ya zakiyi da biki na ne? Mommy tace" ai dubai zamuwuce da ni da kee da anty Maijiddah ki zaba irin kayan da kikeso da kanki" nan Farty tafara rawa voice din Afifa sukaji tana cewa"Mommy toh anty Afrah ma za kikaita dubai d'in?"
Farty ta anshe dacewa" Dallah kimana shuru, manya na magana kina sa banzan bakin ki wajen" hararan ta Afifa tayi gami da murguda mata baki tace"gidaki d'in banxa da hufi bazan taba zuwa ba" mtwss taja tsaki, da ido Farty ta bita chan tace wlhy Mommy sai kinfara gayama yarinyanki gskiya d'an inaga haryanxo batasan ni bace asalin yayarta,jifa cewa takeyi bazatazo gidana ba kenan fa gidan Afrah zata zanga irin banzan miji da Afrah zata aura inan ai" tabe baki Mommy tayi sanan tace" bana tunan tanada saurayi ma wanan, in batasamu bah ai sai Daddy'n ku ya bincika mata a cikin dangin nasu" dariya Farty tayi sanan tace wayaga ba cigaba, ta taso a k'asa mu zakuma tak'are a k'asanmu" wani dariyan takuma bushewa dashi, Mommy zatayi magana kenan Ya Sulaiman ya shigo ashe tinda Farty tafara magana yana jinta shigowa cikin palon ne baiyi ba
K'arasowa cikin palo'n yayi,harara ya zabgama Fartyn sanan ya kale Mommy gami da cewa"wlhy Mommy kirika ma yariyanan fad'a,batada hali sam wlhy" Mommy ba tace komai bah sai ma tashi datayi tabar palon, mik'ewa itama Farty tayi zatabar palon "tsaya kee" Yaa Sulaiman yace, tsayawa tayi gami da turo baki gaba " kee haka'acemaki kud' in zakiyi kokuwa ancemaki mai kud'in zaki aurah?"da kike wani maganganun banzanki a wajen?"
Baki ta turo gaba "toh toh ni Yaa Sulaiman ba magana na keyi ba ai ba da kowa nakeyi bah" na lura da duk y'an gidanan sun raina Afrah da Abdul a gidan,ku ganinku bazasu zama komai ba ko? Tin da iyayansu basu zamaba komai bah ko? Toh ba abin mamaki bane su temakemu wata rana wlh, babu wanda yasan gobe sai Allah" Allah yakiyaye ya karemu da ganin wanan b'akin ranan" Farty tace tana murguda baki
Hannu ya kai zai duketa tayi d'akin Mommy a guje, binta d'akin shima yayi
"Keekuma lafyanki kinfadomin d'aki bako sallama?"Mommy tace
" wlhy Ya Sulaiman ne zai dukeni"
"Akan wani dalili"Mommy ta tanbaya
Farty bata kai da magana ba Sulaiman ya shigo d'akin gami da cewa" wlhy Mommy kirika fad'adama yarinyan nan gaskiya, batasan life bah sam wlh"
Kallanshi Mommy tayi a kaikaice tace metayi kuma sarkin anyi laifi?"
"Abubuwanan da takema Afrah a gidan mana gaba d'aya ta raina ta *D'an hakkin da ka raina*dai shi ke tsolema ido wlhy"
cewazakayi kaxo kamin wa'azi ba Farty bah naji toh sarkin sanin gaskiya,sai kayi gaba haka" juyawa yayi zai fita Mommy tace" saura 3weeks kakoma sch ko?"
"Ehh Sulaiman yace"
"Kafada ma Daddy'n ku dai ko?"
"Sai yadawo zamuyi magana" yana gama fadan haka yayi gaba Farty tabishi da harara
"Allah kiyaye wasu chan su temakemu a rayuwa,mu bamuyi anfani ba kenan?" fartyce ke wanan maganan
Kallanta Mommy tayi gami dacewa " waye yace za'atemakeku wataran?"
" Ya Sulaiman mana, duk a kan su Afrah yake wanan bayanin banzan" Farty tacema Mommy
Tabe baki Mommy tayi sanan tace" bazanga wanan ranan ba kuwa, inshi baimin ba Hafiz yanan gaki kuma duk nasan sai kunzama wasu a duniya, sai yaje chan ya k'arata dasu Afra da Abdul din"
" Wlhy kuwa " inji Farty haka dai sukaita hiransu da Mommy..


Afrah ta maida hankalinta sosai a kan karatunta kasancewan sukusa fara exams din su na waec da neco
Farty kuwa babu abunda yadameta sai waya da chating.
Ya Sulaiman yakoma sch gida daka Hafiz, Farty,Afrah, Afifah Mommy sai Daddy inyana gari.



Asalin LABARIN....
[12/18, 09:03] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*

_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS(We don't just entertain and educate, we also touch ♥ of the readers)_


_Story/written by_
~Biebie Dee(Ss very)~🌸


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_

_Also dedicate 2 you sweetheart,darling Ummu-Abdulnasee Thank you so much for d love,support n care I really appreciate n I love you very very much sweetheart, wishing you Allah's blessings always_



*Kema b'an manta da ke bah Munirah nagode sosai da sadaukar da littafinki a gare ni, Biebie dee nagodiya mai yawan gske sosai da sosai Allah yasa kigama lfya kamar yanda kikafara Lfya Ameen stay blessed babe*💕💕


_page 11-12




*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*




"""""Sosai Afarh ta Maida hankali k'an karatun ta bata wasa da lesson da suke a school Sam, Alhmdulilhi kuma Tana fahimta.
Yau Friday tin da Mommy ta tashi take tsaki komeye dalili oho,Afrah ce tashigo d'akin da sallama amsawa Mommy tayi ciki ciki(y'an iskan suna kanta kenan🤣🤣) kallanta mommy tayi sanan tace
" ya naganki da uniform kuma inace bazaki ba"
"a'a zanje akwai abinda zanyi school ne"
Tsaki Mommy tayi gami da cewa "Allah tsare Allazi karatu" Ameen Afrah tace tabar d'akin.




A Palo ta tadda Afifah na jiranta "baby Tasha Muje kinji" Afifah a gaba Afarh a baya, sai da suka shiga mota Afifah tace
"anty Afrah anty Fartyy bata fitoh bah zata jamana latti wlhy" tana magana tana wani b'ata fuska, murmushi Afrah tayi sanan tace "wai bazata ba" juya ido Afifah tayi gami dacewa better"
Da kikaga batan kow?,babu ruwana wlhy"
"wanna basket d'in ai ni wlhy anty bana tsoranta, kotanan ma bata isa tamin komai bah"
Haka Afifah taita zuba surutu har aka sauketa school din su,kafin itama aka Sauke ta nasu school d'in.


A gida kam Fatty bata Tasha bah sai after 11 shima Mommyce ta isheta da naci,mik'a tayi gami da hamma,hanyan toilet tayi, tabar Mommy zaune bak'in gado, harara Mommy Tabita da shi gami da tsaki dawa da baya Fatty tayi
"Mommy mekuma nayi da ka tashi Nani? "
"ni dallah maza kifitoh wanka ki daura mana wani abu"Fatyy bata kuma magana ba tashige toilet
Sanda tafitoh Mommy bata d'akin D'an tsaki tayi sanan tashiga shiryawa, gown tasa mai armless hand,phone d'inta tadauka gami da d'anna earpiece a kunne tabar bedroom d'in

Kitchen tayi Salamatu tagani tana gogegoge kunne d'aya na earpiece d'in tacire "ke ina Afrah tadawo? "
" a'a" Salamatu tace da ita
"mai Mommy tace ki dafa yau?"
"jolof na macaroni" tsaki Fatty taja sai kace kin wani iyane ma" Dariya Salamatu tayi gami dacewa" anty ko na barmaki kiyi NE? " harara mai lafiya Fatty ta dallamata ai Salamatu batasake magana bah har Fatty tagama dafa indomie d'inta tabar kitchen din Tana bin sorry na Justin Bieber


Palo ta zauna taci tana bin wak'an, ya Suleiman ne yashigo side d'in Mommy zaije yaji voice ana wak'a juyowa yayi yaga Fatty "Kee"yace da k'arfin gske, cire earpiece d'in tayi gami da cewa
" ina kwana ya Suleiman"
"lafiya" yace da ita ya shige side d'in mommy
Tsaki Fatty tayi Kai kasani masifaffe" wak'anta tacigaba da ji tana chatting.

Bayan Sun gaisa da Mommy ne yakefada mata yanasan zuwa Katsina, baki ta tabe sanan tace "yin me a katsina"
" zanje nama su inna sallama dakanan zan biya gidan anty Rabi na gaidata"
" da kyau, amma naga bak'a dad'e sosai da kaje bah ko?, gaisuwa da sallama kuma naga ko ta waya anayi ai ba sai anje bah"
Rage murya Suleiman yayi sanan yace "hakane mommy kawai inaso naga inna ne, amma ai ba dadewa zanyi bah is just 2days"
"Hmmmm kai dai kawai kafisan dagin Daddy'n ku, ko Zaria da ke nan kusa bacika zuwa kakeeyi ba amma kulin kai kana hanyan Katsina kai ko tsoro bakaji, kuma yaushe rabonka da kiran su anty Azeezah da sauran aunties d'inka? Amma kana min zanjen wata Rabi chan da bamu hada komai da ita bah" duk wanan maganan da mommy keyi tanayi ne Tana tapping phone d'in tah.




Murmushi Suleiman yayi sanan yace " ai mun riga munzama d'aya da anty Rabi tinda dai ga Abdul da Afrah kuma kowa yasan we cousins"

Harara mommy ta watsa mai "bakada wani magana sai nasu, dama nasan abin da zakace kenan, me su Afrah suka zama in ba wahala bah? D'an riko har wani abin alfahari NE a duniya?"
" wlhy Mommy ki bar cewa haka, babu wanda yasan gobe mai zata haifar, kawai mubar ma Allah komai kawai"

"Yauwa tashi kaje ni, Allah tsare na biyema haka zamutayi ai na t'abo gudan jininka su Afrah ba" murmushi Suleiman yayi yanacewa" mommy kenan ai ba yau bane tafiyan sai gobe insha Allah D'an ni da Abdul xamu anjima zaidawo"

Allah kaimu kawai tace tana danna phone d'inta, har yakusa barin d'akin mommy ta tsadashi
"in ka idar da sallan juma'a ga sak'o kabiya gidan anty maijiddah ka kai mata zan kirata" amsa yayi yafita, waya tashigayi da Ummu Abdulnaseer tana kan wayan ne Fatyy ta shigo d'akin, xama tayi kusa da mommy, nata zaune har mommy tayi sallama da Ummu-Abdulnaser zama Fatyy ta gyara sanan race "wai mai yaya Suleiman ke cewa ne?"

"mekuwa inbanda dai zanchan su Afrah"
Tsaki Fatyy tayi gami dacewa" banziya ba ta dage wai ina y'ar karatu Insha Allah babu wani abin arzikin da zata d'auko"
"inma ta d'auko a banxa tinda dai komai sai da hanya, shima Abdul d'in sa'a yaci yasamu ABU d'in D'an kawai naji daddy'n ku zai turasu kairo tare da Hafiz ne yasa nabari ya fara ABU dashima yana gida, shegu gayyar tsiya"
"mommy Hafiz za'akai kairo wlhy babu karatun da zaiyi wanan" harara mommy ta watsa mata sanan tace" har yaje ma da yadda Allah, naga dama kema sai na hana wlhy" dariya Fatyy tayi Sanan tace" haba dai wasa ne wanan, ni wlhy har na hangoni nan da 4year wayyo time d'in duk mugama school muyi kud'i, hoo wayaga mommy yaranta duk ansansu a nigeria,nasan su Afrah lokacin anata *zaman aure*" Dariya Fatyy ta bushe da shi
Mommy tace "Allah kaimu dai" Fatyy ta amsa da Amen dai.



Sai 12:45 Afrah tashigo gida kasancewar yau Friday sai da tash wahala tasamu abin Hawa.
Tama dawowa mommy taje ta gaisar sanan tayi Hayan d'akinsu,Afifah tagani kwance sai waya takeyi da anty Nana da tablet d'inta, school bag d'inta ta aje sanan tashiga wanka gami da Alwala,tana fitowa shiryawa cikin black jallabiya sanan ta tayar da sallh Bayan ta idar da sallah ne tad'anyi apply simple makeup amma sai tayi kyau sosai
Kitchen tayi d'an sa wani abu a cikinta, Tana gaba Afifah na bayanta har suka isa kitchen d'in, abin tazuba masu sanan suka zauna Palo.
Suna k'an cin Abincin ya Suleiman da ya Abdul suka shigo nan suka shiga yimasu oyoyo,


Bayan ya Abdul yaje ya gaida mommy polo yadawo nan yasamu har afrah takawo masu abinci sunaci anata hira,duk wanan abu daketayi Fatyy na kwance tin bayan gaida ya Abdul datayi batasake magana bah.
Mommy ne tashigo Palo'n bayan tazauna ne take cewa "please kubar hiranan Daddy'n ku hanya girki za'ayi" tana magana tana kallan Afrah, nan da nan Afrah'n tayi hanyan kitchen Fatyy ko nan a kwance ko motsawa batayi ba, sai da ya Suleiman yayi mata magana sanan ta tashi tana turo baki...







#toh Readers yakukaji ya kuma kuka gani
# ya kuma kuke ganin za'ayi
Duk baku sani bah sai kun biyoni


~BIEBIE DEE CE~🌸
07039732859



*Much love*❤❤❤❤❤
[12/18, 09:03] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*



_PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch ♥ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~🌸


_Dedicated 2 amazing sister Afrah Bhai_

*gaisuwa ga dukkan masoya nah masu bibiyan labari na,nagode sosai Biebie dee na k'aunarku har cikin ranta a duk inda kuke a fad'in dunia*❤❤❤❤❤
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
# *IG PML WRITERS*
# *https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
# *http://maryamsbello.blogspot.com*

_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_


_page 13-14_






"""""Koda Fatty tashiga Kitchen d'in ba aikin da tayi Afarah da Salamatu ne ketafaman aikin,wak'anta Kaiwai taketaji minti minti tana tsaki
Sai da taga sungama tass tabar kitchen d'in Salamatu na k'ara gyara wajen,Mommy tashigo kitchen da fara'arta shirye take ciki lace mai shegen kyau da tsada takoyi kyau abinta 😝 bude wamars d'in tashigayi babu ko d'an sannu da aiki sai da ta gama bud'esu tas sanan tace" yayi, sai a jeresu a dining ko, nan da nan Afrah tagama komai yadda mommy'n tace




K'arfe 6 daidai Daddy yadawo direct side d'insa na nufa, sai da yayi wanka sanan yaran duk suka shigo yimai sannu da hanya cikin Mirna duk ya amsa, sunan duk zaune akayi k'iran sallah nan duk suka Tashi, masjid su daddy suka tafi yayi da su mommy duk suka wace bedroom d'an gabatar danasu sallan



Su daddy basu shigo gidan bah sai da sukayi sallan isha
Babban Palo duk suka zauna nan mommy tayi saving Daddy yayi da Afrah tayi saving sauran mutanan Palo'n nan ko wa yamaida hankalinsa kan plate d'insa baka jin k'aran komai sai na spoons

Bayan Sun kammala Afrah tashiga kwace kayan ganin Daddy da su yaa Suleiman yasa Fatyy ma kwace wasu kayan, Salamatu ne ta k'arasa sauran aikin

Sunan zune Afifah tasasu gaba sai Zuba surutu takeyi Anita dariya Hafiz da Fatyy kam tsaki suketayi



Ya Suleiman ne yakalle Daddy sanan yace " daddy ina san shiga Katsina gobe Insha Allah ni da Abdul"

"Allah kaimu da rai da lafiya nima dama Sunday nakeson naje,tinda zaku gobe duk sai a shirya gaba d'aya muje"

K'aramin tsaki Hafiz yayi sanan yace" nikam bazan samu zuwa bah d'an ina da abinyi gskia"

" menene abinyin naka ko kana da sana'a ne? " daddy yatan bayeshi

"a'a, kawai dai" kamin shuru kowa yashirya kawai"

Suleiman bak'aramin dad'an maganan daddy yayi bah smiling kawai yaketayi

Duk wanan abu dakeyi Mommy najinsu sai da ta gyara zama sanan tace
"toh Alhaji tin da bazashi ba a barshi mana, ai Hafiz ba yaro bane ? "
Shuru kowa yayi babu wanda ya k'ara magana a Palo'n Mommy ce ta fara barin Polo'n Fatyy ma tabita Chan phone d'in Hafiz yashiga ringing tashin shima yayi

Yarage daka Daddy,ya Suleiman, ya Abdul sai Afarh da Afifah hira suka d'an tab'a da Daddy sanan shima yayi masu sai da safe
Nan suka shiga hira Afrah sai zuba takeyi ya Suleiman ya Zuba mata ido yana jin wani farin cikin a ransa wanda baisan Dalila bah

Afifah kam tini tayi bacci
Sai 12 suka ma juna sallama, sai da Afrah ta kashe duk kayan wutan sanan ta dauki Afifah sukai nasu bedroom d'in.




Da asuban fara ta tashi sai da suka idar da sallah sanan Afarh tayima Afifah wanka d'an itama yau Afifan asubancin tashi tayi sabida taji zajen xuwa KT

Kitchen nufa abu mai sauki tayi duk tazuba a warmers tazuba nata da na Afifah a plate,
Bayan Sun gama Afifah tafara shiryawa sanan itama tashiya cikin lace Riga da skirt d'inkin yayi masifar kyau, kwaliya tayi amma ba sosai ba amma zokuga kyan da tayi, face d'inta ta kalla a mirrow sai Kawai ta fara dariya

"Darian mekikeyi anty" Affifah tace da ita

"coz zanga inna da mami yau da su Arfat da fahad(Arfat da Fahad k'anan Afrah ne, bayan rasuwan Salis da shekaru 4 Rabi tayi aure shine ta aifesu)

K'arfe 6:30 dai dai su Afrah har sungama shirun su d'akin su yaa Suleiman tayi bayan Sun gaisa tace" yaya wai baku Gama bane, time na tafiya fan, ina ma yaa Abdul ne?" ta k'arashe maganan tana D'an dube dube

"yanzo zamushigo muyi breakfast sai mu dau hanya Insha Allah "

"Kai nasamaku a takeaway sai kuci a mota kasan lokaci na tafiya fa"

Dariya yayi sanan yace kedai jeki gamunan yanzo,aje a k'arasa yima Mami makeup " dariya kawai tayi ba Tate da tace komai bah

Tana komawa side d'insu bedroom d'in Mommy tayi, gaisheta tayi mommy ta amsa fuskanan kaman dare😂😂 ita dai tayi gaba Abinta
A Palo ta tadda Daddy har yashirya kaidashi tayi ya amsa gami da tsokanar ta
"mamana har kinrigani shiri,lallai Kuwa anya ma kinyi bacci?"

"nayi sosai ma Daddy "
Mommy ne tashigo Palo'n sai yatsina fuska takeyi nan Afrah tabasu waje kitchen tashiga D'an sama su ya breakfast d'insu a takeaway


K'afe 7:30 duk Sun gama shiri kowa yafitoh yayi kyau abinshi,Afarah sai washe baki takeyi

Ya Suleiman yanufo wajen da car key Hannun shi kallan Afrah yayi gami dacewa
"my sisi kiyi kyau sosai"
Dogon tsaki Fatyy ta jaa mommy kam harara mai lafya ta jefama Suleiman

Daddy mommy saiAfifah motor su da ban
Yaa Suleiman ya Abdul su biyu a nasu Motan sai Hafiz,Fatty sai Afrah nasu motan da ban suma wanan duk tsarin mommy ne kuma sabida Afrah tayi hakan....





*Toh masu karatu kubiyo ni dai muje zuwa*


_Amma ya kukejin labarin ???




~BIEBIE DEE CE~🌸🌸
[12/18, 09:03] BIEBIE DEEE: *D'AN HAKKIN DA KA RAI NA...*



_PURE MOMENT OF LIFE WRITES'S(We don't just entertain and educate,we also touch ♥ of the readers_)

_story/written by_
~Biebie Dee~🌸




Please Login or Register in order to submit comment