Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»ΏCompiled By Umar Dalha Funtua.


Copied By Ummee Garkuwa.


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*HIBBATULLAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*


Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…

*Am back againπŸ‘―πŸ»πŸ‘―πŸ»*


*πŸ…Ώ 1*

Wata bakar mota kirar Bentley 2019 Mai bakin glass ce ta danno kanta cikin farfajiyar federal hospital dake cikin garin Kano, direct wata rumfa ta nufa wadda ajikin rumfar akayi symbol da babban rubutu aka saka *C. M. D parking lot* anan motar ta faka wani mutum daga gaba ya fito da sauri tare da bude murfin dama.

A hankali ya zuro da farar kafanshi dake sanye cikin wani black cover shoe na companyn Prada, kafin ya idda fitowa gaba dayan sa wooow na fada dan wani classic man ne ya fito sanye cikin wata dakakkiyar designer suit dark blue wadda tayi matukar amsar cikakkiyar halittar jikinsa, tabbas guy din ya hadu over dan kusan kamar shi ya ya zana kansa.

Daya murfin da driver ya zaga ya bude wata classic bab ce ta fito wadda kana ganinta kasan hutu da boko sun zaunar mata tana sanye da wata blue tokish gown ta yane kanta da bakin siririn veil kafarta da sanye da high heels baki mai shegen kyau, tana da kyau amma ba sosai ba ba fara bace amma yanayin Hutu da jindadin da take ciki yasa fatarta ke wani irin glowing.

Wani sihirtaccen murmushi ya sakarwa drivern nasa har sae da siririyar hushiryarsa ta bayyana kafin ya furta.

"thank bukar. "

Matar kuwa sake kicin kicin tayi da fuska ta zagayo tare da shigewa jikinsa cikin wata murya mai dauke da kissa tace..

"baby let's go."

Ba tare da yace mata komai ba suka fara takawa cikin asibitin sakale da juna da kagansu kasan manyan masoyane, duk inda suka ra6a kallonsu ake tare da miko musu gaisuwa, amma shi kawai yake amsawa banda ita matar.

Har office dinsa na CMD ta rakashi sbd tsarinta ne kullum sae ta rakashi kafin ta tafi nata office din, kissing din bakinsa ta danyi kafin ta dago ta kalleshi da kyau tace.

"take care."

Gyada mata Kai kawai yayi kafin tasa Kai ta fice.



Dai dai bakin kofa ta bude kofar kenan sukayi gware da wata matashiyar nurse kyakkyawa number daya tana da shape mai kyan gaske domin boob's dinta a cike suke ga hip dinta nan ma tubarakallah irin matan nan ne da ake kira da full option.

Da sauri taja baya tare da rike files din hannunta da kyau tayi kasa da kanta jikinta na wani irin rawa lkc guda zufa ta rufets ruf tayi kasa da kanta muryarta na shaking tace.

"am..sorry...mah...ban...ban...san...ki....!"

cikin daka tsawa mai firgitarwa tace.

"shut up stub bitch! Are u nonsense?"

Dasauri ta girgiza Kai tana kuma fadin.

"sorry...doc...wllh... "

Mtsww taja wani dogon tsaki cikin isa da izza tace.

"get out of my side dabba."

Da sauri nurse din tabar wajen har tana hadawa da faduwa tabar wajen don tasan halin doctor fina kuma tasan wace ita.



*_MAHIR ABDULMU'IN ABDALLAH dane na uku wajen tsohon NGO na Africa wato Abdulmu'in Abdullah yan asalin kasar sudan ne mahaifiyarsa kuma yar Nigeria ce bafulatanar yola ce, mahir shi kadaine namiji a wajen iyayensa sai yarsa farida da kanwarsa najwa kuma dukkan nusu sunyi aure, family dinsu masu kudin gaskene kuma cikakkun yan bokone._*
*_duk da arziki na iyayensa da family basu baya daga cikin mutane masu dagawa can nuna arzikin da iyayensu ke dashi, yayi krtn shi na medicine a Oxford University anan ya zama kwararren likitan mata mai zaman kasa Mai tsananin basira da sanin aikinsa, yayi aiki da babban asibitin dake birnin London kuma asibiti na biyu a duniya gaba daya kuma yana daga cikin wadanda akeji dashi sosai a kasar indai ta sanin matsalar mace ne, ganin cigaban da yake samawa kasar da ba tashi ba kuma yana ganin halin da tamu kasar take ciki na rashin cigaba da kwararrun likitoci irinsu yasa ya tattaro ya dawo Nigeria domin suma su amfana da shi nan take yana dawowa aka bashi CMD na federal hospital ._*
*_doctor mahir yana kirki sosai ga tausayi da taimakon mararsa shi, kusan duk shekara yana kai mutane da dama saudiya aikin hajj, sannan yana da foundation guda ta tallafawa talakawa a garuruwan arewa dama kasar mahaifinsa Sudan._*
*_doctor mahir yana daga cikin the most eligible bachelor da muke dasu a duniya, wannan dalili yasa matarshi doctor fina ke matukar kishinsa dan da wuya mace ta daura idonta akansa taji batayi wani feelings nashi ba, gaba daya shekarunsa basufi 35yrs ba._*


*_doctor Nafisa Alkasim dan baiwa, 'yace d'aya tilo a wajen shugaban kasa mai ci a ynz wato alkasim dan baiwa, mahaifiyarta hajiya kuye kuma tsohuwar manager ce ta NNPC, asalinsu yan Nigeria ne nufawan Mina, nafisa Fina tayi krtn ta na medicine a kasar Cyprus inda ta karanci abinda ya shafi hanci hunhu mak'ogwaro, tana da kwarewa sosai a aikinta Kuma tana daga cikin manyan likitocin da ake takama da su a Nigeria kmr mijinta._*
*_doc nafisa kwatata bata da mutunci bare da'a tana da jinkai da nuna isa da son asan ita ko wace, bata harka da kowa sai uwarta domin bata yarda da kowa ba sai dai tana da wani amintaccen yaronta guda daya wanda shine yasa kusan dukkan surrukanta, tana da kishi Mai zafin gaske wanda ita kanta batasan wane iri bane domin zata iya aikata komai idn kishinta ya motsa, tana da gayu da kwalliya gata komai nata sak na yan bariki domin har tattoo ne da ita a wuyanta._*
*_tunda ta auri doctor mahir sbd tsananin soyayyar da take masa kasancewar mahaifinta aminin mahaifinsa ne, ba laifi shima yana sonta sae dea sam baya son halinta da dabi'unta, wajen aiki guda suke aiki sbd tsabagen kishinta duk wata staff mace daga patients har doctors nurses babu wanda bai san halinta ba, shi isa duk mai son kansa da arziki da zaman lfy ba Mai shiga sabgar mijinta._*

Wannan kenan

Jikinta na tsananin rawa ta sauka daga benan CMD din ta nufi department dinsu na labour room, office dinsu ta shiga tare da ajiye files din hannunta ta zauna shirif tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya.

Daya daga cikin matan office din dake zaune tana rubutu a register ta ajiye beron hannunta tare da fadin.

"sister *HIBBATULLAH* lfyrki kuwa kika shigo haka kamar anjefoki ko biyoki akayi ne."

Wadda take gefe tana danna waya tace.

"kema dai sister rashida kamar bakisan daga inda take ba, wata kila tayi karo da madam."

"mtsw."

Kakeji wadda aka kira da Rashida taja tare da fadin.

"wllh kuna bani mamaki kun dauki tsoron duniya kun daurawa waccan ajawon mai siffar karuwai, ni banga abin tsoro a tare da ita ba."

Dasauri dayar ta tareta da fadin.

"aikuwa doctor Fina ita ke da abin tsoro, karfa ki manta ubanta ke da kasa."

Tsaki rashida taja kafin tace.

"aikin kutmar uba dan ubanta ke da kasa amma ai bashi ke da duniya ba, shikkenan dan tana matsayin yar shugaban kasa sae kuma akace ta taka kowa, wllh bari kiji ras nake da ita bana tsoronta ni wllh har so nake ma wani uziri ya kaini wajen CMD tym din kuma tana wajensa, tayi attempting yi mini wani Abu wllh sae na zubar mata da jini in yaso tasa a haka rijiya gaba dubu a jefani."

Hibba dake ta sauke ajiyar zuciya tayi bayyanan nan murnushi wanda ya fito da zahirin kyawun halittar da fuskarta ke dauke da shi sannan tace.

"um um dai sister Rashid banda cika baki."

"bar matsiyaciya sister hibba duk wannan zafin kan nata tasan doctor Fina taci uwarta iya shi."

"hmmm maman boy kenan ku zuba ido very soon rabb ya hadani da ita Zakusha mamakina."

"Allah ya hadaku kuwa."

cewar maman boy tana cigaba da abinda take, yayin da hibba ta Mike ta janyo dayar register ta fara cike cikenta...






*toh my fans ya kukaji labarin a cigaba ko a dakata....for commentsπŸ‘‡πŸ»*
08125544850



Vote
Share
Comments




Oum AfafπŸ–€πŸ”₯
[9/22, 2:32 PM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*HIBBATULLAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*



*πŸ…Ώ 2*

Wani hamshak'in parlour ne da girmansa zeyi 100by100 fadin tsarin parlourn is weste of time kawai kuyi imagining kyawu da tsaruwar parlon shugaban kasaπŸ€£πŸ˜›.

Tana zaune sanye da skinny jeans da half vest ta daure gashin dokinta da akayi mata kananun kalba da shi tana danna wayarta kirar iPhone x-mas, karar taunar cingum dinta kawai ke tashi hade da tashin wakar dake fita a decorder.

A hankali yake saukowa daga stairs din parlon yana sanye da wasu designer english wears red T-shirt da black trouser ya zuba hannunsa daya cikin aljihu dayan kuma rike da car key dinsa da wayanshi.

Har ya karaso cikin parlour hankalinsa na kan wayarshi da yake dannawa a gabanta ya tsaya tare da duban Rolex watch din dake tsintsiyar hannunshi yace.

"baby ni zan dan fita."

Wani irin kallo tayi mishi mai dauke da ma'anoni iri iri sannan ta Mike tsaye tare da fadin.

"Bari nasako kayana muje na rakaka."

Sexy eyes nashi ya dan lumshe tare da waresu akanta yayi dan murmushi yace.

"gidan Khalifa zani duba jikinsa I knw nasan bazaki ba."

Baki ta ta6e tare da mai da guri ta zauna tana kafeshi da ido alamar bata yarda dashi ba tace.

"ban yarda da kai ba."

"nata6a yi miki karya Fina."

"nop dear but... "

"don't saying me everything sai na dawo."
.
Ya karasa mgnr yana ficewa fuskan shi a hade.

Wata doguwar ajiyar zuciya ta saki kafin tayi saurin danna wayanta ta kara a kunne bugu biyu aka daga cike da bada umarni tace.

"gashi nan fitowa kabi bayanshi duk inda zashi."

Bata jira answer ba ta katse wayan tare da mikewa ta haye upstairs abinta.

Dr Mahir ko da yafita direct shoprite ya nufa nan yaje ya judarwa yaran Khalifa sweet da chocolate d.s yarda yake tafiya so fine nd good ne yasa ya dauki hankalin duk matan wajen har ma da maza, sai dai ko tasu bayayi yana tsaye ya Mika ATM card dinsa wata matashiyar budurwa yar gayu tazo gabanshi tare da kashe murya tace.

"hello!"

kallo daya yayi mata tare da dauke kansa yace.

"hy"

"am dan Allah zan iya..."

Murmushi kawai yayi mata tare da daga mata Hannu yashige dominn tym din har an miko masa ATM dinsa.

Daskarewa tayi a tsaye da ganin kyawawan hakoransa da suka bayyana. Bayansa tabi da kallo tana imagining gata ta zama matarshi tana sakale a jikinsa sun zo shopping ajiyar zuciya ta saki tare da biyan kudin da tayi shopping itama ta fice.

Tana kokarin tada motarta akayi mata knocking zage galas din tare da kallon bakin basamudan dake tsaye akanta wani yawu ta hadiye da kyar tare da fadin.

"malam lafiya."

A hankali ya zuro da hannunsa cikin motar tare da kai mata wani kyakkyawan naushi a kumatu har sae da ta saki kara hawaye na zubota ta dago ta kalleshi a fusace zatayi mgn yayi saurin katseta cikin harshen turanci yace.

"meye hadinki da gayen can."

Wani kallon rainin sense tayi masa kafin ta mAyar masa da cewa.

"ban sa..."

Maganarce ta rike lokacin da idonta ya sauka kan bindigar dake cikinsa jikinta take ya fara tsuma ta fara kuka wiwi tana rokanshi.

"wllh billahil azim ban sanshi ba,wllh bai ma kulani ba dan girman Allah kayi... "

"shiii, ki kiyaye."

Daga haka yabar wajen, tana ganin ya shiga motarsa ta fito tare da saka gudu....




Isar sa gida Khalifa dake unguwar jambulo bayan yayi parking a harabar gidan fita yayi tare da karasawa gaban mai gadin gidan fuska a sake ya mika masa hannu tare da dan rissinawa yace.

"barka da yamma Baba. "

Baki Mai gadin ya bude ganin girman da ya bashi sannan ya amsa cikin sakin fuska.

"barka dai dan albarka, alhj Kake nema."

"eh baba."

"bari na yi ma sallama dashi"

Daga haka ya isa cikin gidan, fitowa yayi tare da sanar masa cewa ya shigo, ledojin cikin motar ya fito dashi tare da basa ya shiga shi.


Yana isa cikin parlourn da ya hadu sosai shima, Khalifa ne zaune Wanda kusan shima a shekaru zeyi mahir din fuska a matukar sake ya Mike ya nufi mahir din yana fadin.

"your welcome Dr."

sukayi hugging juna cike da tsantsar farinciki kafin su zauna suna sake gaisawa Khalifa yace.

"Dan iska Ashe Kai ne shine har da wani turowa neman iso kamar gidan bakonka ne."

"Addini ne ya koyar damu haka ai, oh naga gidan shiru ina mutanen gidan."

"sun dauka bako ne ae, bari na kirata."

Daga inda yake zaune ya kwalla kira da fadin.

"Ramla!!!"

"na'am."

"kizo mahir ne fa."

ai kafin kace mene sae ga yara nan guda biyu mace da namiji Sun fito da gudu suna tsalle suna ga daddy ga daddy.

Hada yaran yayi gaba daya yayi hugging cike da so da kwanar yaran, suka dago tare da tsugunnawa suka ce.

"good afternoon daddy."

"afternoon sweethearts, how ur study? "

"alhmdllh daddy."

Murmushi yayi tare da shafo kansu, ramla dake zaune gefan mijinta sanye da dogon hijjab fuskanta dauke da fara'a tace.

"yau doctor ne a gidan namu kenan."

"Mrs Khalifa how far ya jikin katon mijinki."

Gaba daya dariya sukayi kafin Khalifa yace.

"kaji dan iska nine katon?"

"gashi nan kuwa kana zaune katonka da kai ka nade wai sunan baka da lfy."

dariya suka sakeyi dai dai shigowarta sanye da riga da skirt na yan kanti ta yane kanta da katon mayafi, hannunta dauke da katon tire wanda ke shake da kayan sha dana ci, cike da nutsuwa ta ajiye kan center table din dake tsakiyar parlon ta ajiye tare da janyoshi gabansa ta ajiye, kanta a kasa cikin siririyar muryarta mai taushi tace.

"ina yini."

Sai lokacin ya dauke idanuwansa daga kanta domin sosai nutsuwarta ta tafi da imanin shi cikin sanyi shima ya amsa da fadin

"lafiya lao, yh gida."

"alhmdllh."

Ta fada tana mikewa zata wuce, unty ramla tace.

"hibba ki zuba masa lemon mana."

"no tabarshi idan zansha na zuba thanks."

Wucewa tayi ba tare da tace komai ba, wata 6oyayyiyar ajiyar zuciya ya saki tare da maida idonsa kanta har ta shige.

Hira sosai suka zuba har magriba yana gidan kafin yayi musu sallama ya tafi.






Washe gari

Tun safe hibba ta tashi kamar yarda ta Saba, tashiga kitchen ta fara hada masu breakfast Mai aiki na taimakonta, 7:00 ta kammala komai nata ta gyara ko ina tsaf, dakin yaran gidan ta shiga tare da fara tashinsu.

Wanka tayi musu cikin sauri tare da shiryasu tsaf, cikin uniform dinsu parlour suka fito dai dai fitowar ramla da Khalifa cikin shirinsu na fita sai yar yarinyar dake hannun ramla Khalifa yace.

"unty hibba sarkin hidima Allah dai ya saka da alkhairi."

"amin, aini wllh bansan ya zanyi ba idan hibba tayi aure ba Dan gaba daya ta gama sangartani."

murmushi hibba tayi tare da amsar Amna tace.

"kawota kuyi breakfast karku makara Bari naje nima na shirya."

"na dauka you evening ne dake ai."

Unty ramla ta fada tana zama kan kujerar dinning

"ae ba'a kafe ruster ba tukunna."

"OK."





*_HIBBATULLAH muktar ammani shine sunanta, yan asalin garin Kano ne cikin karamar hukumar sumaila Mamata kuma yar gombe ce, su bakwai ne a gidansu maza biyar mata biyu, hibba itace ta shida a gidansu sai kaninta, yayin da ramla ita Hibba take bi._*
*_babu laifi suna da rufin asirinsu mai kyau, domin kaf yanyan gidan suna da iliminsu na addini dana Boko, hibba yarinyace mai hakuri da juriya tare da kawaici, tayi makarantar school of nursing har ta fara aikinta a federal hospital, shekarunta 26 hakan yasa iyayenta suka takurata sosai akan aure amma Allah bai kawoba wannan dalili yasa ta dawo hannun yayarta da zama._*

Wannan kenan.








Vote
Share
Comments





Oum AfafπŸ–€πŸ”₯
(Mrs doctor Ahmad)
[9/22, 2:33 PM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*HIBBATULLAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*



*πŸ…Ώ 3*

Wanka tayi ta fito tare da shafe jikinta da lotion dinta mai dadin kamshi da gyara fata tare da saka fata santsi da kyau na hutu na musamman sunan Man doctor clear, powder kawai ta shafa sai lipstick ta sanya fararen uniform dinta wanda suke a goge tas, doguwar abaya baka ta daura a saman kayan kafi tasa dan hijjab dinta fari da ya sauko mata har kasan kafadarta, wani hadadden brown din glass mai shape din cat eyes ta dauka ta saka, yayi cif da tsarin cikakkiyar fuskarta yayi mata kyau sosai, body spray ta dan fesa kafin ta dauki Jakarta da takalminta ta fito rike da Amna a hannunta.

Ba kowa a parlon sai mai aiki dake tattare kayan da akayi breakfast dasu.

A kan kujera ta ajiye Amna sannan tashiga kitchen breakfast nata ta juye a food flacks sbd ta makara tare da sawa a jaka tafito tana duban diamond watch din dake hannunta tace.

"Kamila ga Amna kiyi mata wanka plz ki sake gyara gidan, untyn ta fada miki abinda zaki dafa da Rana? "

"ah ah tace dai idan kin fito na tambayeki abinda za'a dafa din."

"okay kiyi mana rice and beans, ki daka mana yaji mai dadi kisa tafarnu cikin yajin, ungu kibawa iliya mai guga ya siyo salad, idan nadawo nayi na dare. "

Ta fada tana mika mata 100 naira.

"toh sai kundawo Allah ya kiyaye. "

"amin, ki dauki Amna kuyi baya da ita kartaga fitana tayi kuka."

Dariya Kamila tayi tare da daukar Amna tana mata wasa suka shige kitchen ita kuma ta fita.

Sai da suka gaisa da mai gadi kafin ta fito, da yake gidan nasu a bakin titi yake tsaye tayi sai ga Mai napep nan ta shiga suka kama hanya.


Yau ma kamar kullum Mr and Mrs Dr Mahir tare suka zo yau ma the same color kaya suka sa, suka jero kmr ka sacesu sbd tsanin kyau, yana shiga office nasa ya bada sanarwa cewa yana son meeting da duk wata nursing dake labour room by 10:am.


Sai 9 ta iso cikin asibitin, office nasu ta shiga tayi sign kafin ta ajiye Jakarta tana fadin.

"sannun ku da aiki sisters mun tashi lafiya."

Wata ta dan ta6e baki sannan tace.

"Ke dai wllh babu abinda yake duminki sister hibba kullum kara bunkushewa kike kina wani kara kyau meye sirrin ne."

Shewa mutanen dakin suka saka gaba daya maman boy tace.

"in banda abinki sister khady itafa hibba mai kyauce tun usuli kuma mene ze dameta da ranta da lfyrta da yan chanjinta kinga kuwa ae zero damuwa."

Wata mata da shigowarta kenan tana cire hand suck daga gani daga aiki ta fito tace.

"hibba itace ke da damuwa kuwa."

Ido hibba ta zaro tare da fadin.

"wata damuwa nake da ita ni 'yasu mum ashraf."

"damuwar rashin aure mana, shekaru 26 ace mace babu namiji kusa da ita ai kuwa wannan macen ita ke da zundumemiyar damuwa kuwa."

Rashida da tun dazu take ta rubuce rubucenta bata tankasu ba tace.

"hmm aikin kawai yo ita har shekarun nata nawa suke a gurin nan fa har da yan shekara 35 sai ita yar 26 kuma komai ai da lkcn sa ko zata dauki kanta ta Kai gdn mijin ne, kuma da wani gidan mijin ba gwanda gidan uba sai dubu ba, su masu mazajen har Mai zasu nuna mana, basai dai suce su ana cinsu ba."

"ke sister rashida karkuma fa ki fadi mgn anan."

Cewar maman ashraf cikin daga murya.

"na fada zaki dakeni ne, ko kinji na fadi sunanki ne kukan kurciya nayi kuma na baki amsa dai dai da tmbyr ki."

"to dake aike ji nake sai kibari a kasa sannan ki dauka."

Cewar khady tana daka mata harara.

"ba'a kasa daniba amma na dauka sbd kunga ita bata da baki shikkenan ko wacce Shara kuka dauko kwa zuba mata, ni zanzo watarana wata yar bura uban nan ta fadan mgn kwatan kwacin yarda kuke fadawa hibba yarinya taga yarda ake gurza baki aikin bnz baku da aiki sai gulma da munafunci da sa idon bala'i alhalin babu abnd bamu sani ba mtsw"

Fada ne ya kaure tsakanin su uku maman ashraf rashida da khady sai fadawa junsu mgn suke, shigowar metro yasa sukayi shiru cikin hada rai tace.

"jarababbu yan kata'i kullum ku kenan cikin masifa, babu yarda za'ayi aji department din nan shiru kuna nan kuna jidalinku kumbar parties kwance sbd babu naku aciki ko? Yayi kyau kuma kuyi da hujja dan CMD duk yana da wani record na rashin mutuncin da kuke da shegen rashin kula da patiies babu abnd HOD bai sanar dashi ba, sbd hka kuje yana neman ku."

Gaban hibba ya cigaba da dukan uku uku suka Mike suka fita har masu aikin yamma da na kwana da masu hutu duk sunzo, hibba suna tafe ita da rashida hibba ta dubi rashida da har ynz mita takeyi tayi dan murmushi tace.

"plz sstr rashida adinga hkr da juna a dinga Kai zuciya nesa."

Harara ta 6alla mata tace.

"ke ai daman baki san ciwon kanki ba idan ke zakiyi hrk wllh ni bazanyi ba dan banga yar kutmar uban da zatayi mini in kyaleta ba ko wace wllh, shegu duk bamuna da tarihinsu a gdn mazajen nasu ba, ita maman ashraf din bakar munafuka da komai aka gani ajikinta tace abban ashraf ne yayi mata to wllh duk karya take ko farcen susa bayayi mata komai da kanta takeyi hatta da kudin mkrntr yara ita ke biya kuma a haka ya karo mata kishiya kudin hayar gdn da suke zaune ita ke biya, ita khady dan uwarta taji ta tension din dan iskan mijinta manemin mata dan giya har kan gadonta yake kawo karuwa, yaje kuma yayi tatil dinsa yazo aci uwarta yayi mata a mai ta goge kuma, to idan kuwa irin aurensu zakayi ba gwanda ka dawwama gidan ubanka ba."

"hmmmn sstr rashida baki da dama ke dae Allah ya kyauta kawai zamuce."

Sae masifa take har suka karasa black din CMD din, a babban dakin taro dake office dinsa suka taru mazansu da matansu, dakin ya gama hAduwa da tsaruwa sai kamshi yake, kowa an ajiye masa lemo da ruwa, zancen su ke tashi kawai

Please Login or Register in order to submit comment