Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lose all my worries, that is why it can only be your that is meant for me_
_GWS habebbty_

Ta karanta letter din nan yafi karfin sau hamsin wani irin dadi da zulumi ne ya kamata, special digital dinshi ta gani a kasa ta manta da dare tayi sauri sawa cikin wayarta jikinta na rawa ta danna Kira, lokacin yana parlour yana karanta Alkur'ani mai girma wayarsa dake silent yaga ta kawo haske tsurawa wayar ido yayi har ta katse wani kiran ya sake dawowa, a hnkl yayi picking tare da karawa a kunnensa cikin sanyin murya yace.

"salam, who in the line."

Daga chan 6angaren hibba ta zame ta kwanta saman pillow tana lumshe ido murya a matukar sanyaye tace.

"Hibbatullah..... "






vote
Share
comments






Oum Afaf🖤🔥
(Mrs Dr Ahmad)✍🏻
[9/22, 2:41 PM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

💋💋💋💋💋💋💋💋
*NI DA DR MAHIR*
💋💋💋💋💋💋💋💋

Writing by
*HAFSAT BELLO*

_Follow me on instagram:-_
*Hafsat Bello*


~TEAM MAHIR~
This's for urs thanks 4 kwararo comments buh kuna takura team Fina ko dan kunga kun fisu baki😂




*🅿 14*

Wata sanyayyar ajiyar zuciya ya saki wadda har sai da hibba ta jiyota cikin whisper yace.

"lovely name for a beautiful owner."

Shiru ko wannensu yayi kafin ya katse kiran, Bin wayar tayi da kallo tana imagining fuskar mahir mai dauke da annuri, murmushinsa mai kyau take hangowa tana wannan tunanin ya kirata, kamar me jira tayi saurin daga tare da karawa a kunne.

"yah jikin naki."

Taji ya fada atakaice.

"dasauki."

Ta furta a hankula, shiru ya danyi kafin yace.

"hibba my heart love with you tun time din da na fara ganinki, na rasa sukuni nashiga damuwa akanki naji kishinki lokaci guda sai daga baya zuciya ta fada mini sonki take so bana wasa ba kuwa, kece macen da mum dita ta dade tana mini addu'ar samu domin yau na tabbatar da haka saboda kyakkyawar shedar da kika samu a wajen jama'ar dake tare da ke, hibbatullah wllh tallahi I love you nayi miki alkawarin farinciki marar musaltuwa a rayuwar auren mu zan zama bawanki zanyi miki hidima har karshen numfashina plz accept me hibba."

Ya karasa mgnr cikIn alamar roko.

Hibba kuwa gaba daya kalamansa Sun gama ratsa jini da jijiyoyin jikinta wani irin farinciki ne ke ratsata ga wani sanyi da taji zuciyarta nayi ji take kamar an yaye mata duk wani zunubanta yau wai itace professional Dr like Mahir Abdul'Mu'in ke furta mata kalmar so, kai alhmdllh burinta ya gama cika.

"habebbty kinyi shiru plz accept me."

Kasa kasa ta sakeyi da murya tace.

"I will need a time to think about it."

Shiru ya danyi kafin yace.

"ok no problem but when zan samu amsa na."

"1month."

Kwarewa yayi yana tari tace.

"what?"

"ke kikasa na kware love 30days fa kinaso kafin time din ace miki na mutu kenan, gaskiya 1month yayi yawa ina laifin 3days shine ka'ida."

Gutun murmushi ta danyi sannan tace.

"Allah ya kaimu."

"amin love me kikeyi ne haka?"

"ina kwance."

"OMG! Dama munyi aure muna tare manne da juna muna hirarmu mai dadi."

"hmm, bari na kwanta good night."

"Kai love kina korani."

Ya fada kamar ba Dr mahir da ta sani ba.

"nop inajin bacci ne."

"kk habebbty sleep well kiyi addu'a before sleep I love you too."

Daga haka ya datse kiran.

wata kara hibba ta Saki tare da cusa kanta cikin katifa cike da tarin farincikin da bata ta6ajin irinsa a rayuwa ba, komai tana ganinsa kamar a mafarki ne.

"awww...."

Ta fada tana sake gyara kwanciyarta, a ranar dai dakyar ta samu tayi bacci sbd tsabagen tunanin mahir kwana tayi tana mafarkinsa, shima hakan take a 6angarensa domin shi har wankan tsarki yayi da asuba.


Washe gari shine ya fara kiranta suka gaisa, tana mamakin ina jarababbiyar matarsa take har ya samu damar waya, ji tayi ynz kwata kwata bata tsoron haduwa da Fina, anwar ma ya kirata kamar yarda ya saba.



Ana gobe kwana ukun da tabawa mahir ze cika, tana zaune a parlour tana taya umma gyara wake, yaro yazo yace ana sallama da hibba ido hibba ta zaro tace.

"ni kuma injiwa? "

Umma ta kalleta tace.

"meye abun rudewa haka kuma, kai yaro jeka kace injiwa."

Yaron yace inji anwar wai.

"toh anwar sabon salo yau kuma baze shigo ba, kwana biyu na fuskanci kamar akwai wani abu tsakaninku."

"hmmm ummata kenan, babu komai tsakanin mu."

"gulmammiya idan tayi tsami naji, ki tashi kin ajiye shi waje."

Mikewa tayi domin ynz kafarta ta warke sumul sai dan dingisata da take kadan, hijjab dinta ta saka sai yar powder da ta shafa ta fesa turare ta fito, ta kalli umma da tayi mata kallo daya ta ta6e dariya tayi ta fita tana fadin.

"ummanta ta kaina."

Tsaye ta ganshi a bakin motarsa, yana sanye da sky blue din shadda da bakar dara yayi kyau sosai.

Murmushi ta sakar masa ta shima ya mayar mata karasawa tayi gaban motar ta tsaya tace.

"ina yini."

"kinyi lfy shugabar kyawawa."

Dan murmushi tayi tace.

"yah su granny?"

"tana gaidaki, zuwa nayi muyi sallama tafiya ta kamani zuwa Abuja yanzu ynzu."

"Abuja kuma da yamman nan kabari sai da safe mana karkayi tafiyar dare."

"ai bani kade bane, kuma a jirgi zamu tafi ynz haka ma ni kade suke jira nace bazan tafiba sai nazo nayi sallama da ke kuma naga kyakkyawar fuskanki."

Murmushi tayi tana dan rufe fuskarta, hira suka danyi kadan kafin sukayi sallama, kudi yabata amma fafur taki kar6a daga karshe gida tashige da sauri ta barshi.


Tana komawa ciki, wayarta na kara umma tace.

"keni jarabar wayar nan taki tun dazu ake aikin kiranki dauka kiji."

Dasauri ta dauki wayar ganin mai kiranta ta shige daki, umma tabi bayanta da kallo kwana biyu ta rasa wane irin nishadi 'yarta ta take ciki.

Dole ta sanar da ramla domin itace abokiyar shawarar hibba ita take sanarwa da komai nata, Tana bukatar ta bincika mata abnd ke faruwa da hibba.

Hijjab din jikinta ta cire tana kwanciya kan katifarta tare dayin rufda ciki, cikin sanyayyar murya mai zaki tace.

"assalamu alaikum."

"wslm, love ina kika ajiye wayar ne tun dazu nake kira baki receiving ba har kinsa hawan ruwana ze tashi."

Yar dariya ta Saki tace.

"bana kusa da wayar ne ykk yh gida."

"nop fine."

"why? "

"bcoz I miss you."

"hmm! "

Hira sukayi ta sha har aka fara kiran sallah magriba kafin suyi sallama.








Share
vote
comments







Oum Afaf🖤🔥
(Mrs Dr Ahmad)✍🏻
[9/22, 2:41 PM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LiFE WRITER'S✍🏻*

💋💋💋💋💋💋💋💋
*NI DA DR MAHIR*
💋💋💋💋💋💋💋💋

Writing by
*HAFSAT BELLO*

_Follow me on instagram:-_
*Hafsat bello*






*🅿 15*

Dr Fina ce tsaye gaban wani tankameman dressing mirror mai girman gsk wanda yake shake taf da costumes iri daban daban na kwalliya, daure take da wani dan 6ingilin towel red color da alama daga wanka ta fito dan kanta ajike yake, tsayawa tayi tana karewa kanta kallo, cikin zuciyarta tace magana, tabbas ita kyakkyawace tana da kyan da tafi karfin ko wanne namiji ya wulakanta ta, amma me yasa mahir yake nuna halin ko in kula a kanta, dan yaga ina sonshi da yawa, tabbas da soyayyar mahir aka halicceni kuma da ita zan koma kuma shima ae yana sona sai dai nasan baya yimini kwatan kwacin son da nake masa, hummm! Ta sauke numfashi mummy ce ta shigo cikin shiga ta alfarma da ka ganta kasan mahaifiyar Fina ce domin kamarsu daya sak hatta da girman jikinsu daya sai dai da kaga mummy kasan gogaggiyar Boko ce number 1 wadda daga yanayin jikinta kasan Hutu da rayuwar jindadi sun zaunar mata.

"Fina na dauka tuni kin gama shiryawa tundazu ke muke jira muyi dinner."

Baki fina da dan ta6e tace.

"Anya mummy zan iya cin wani Abu."

"dallah malama me kikaci tun da kikazo gidan, idan akwai abinda ke damunki ki fadan mana am ur mom baki da wata da zakiyi making shawara sama dani."

Zamewa fina tayi ta zauna kan stool ta dubi mummyn ta ta da kyau tace.

"mummy nice kuwa mai matsala tunda har ynz bangama tabbatar da cewa mahir nawa bane ni kade."

"mtsw! Wllh tunda nake ban ta6a ganin mayyar 'ya ba kamarki nafisa, kamar ba jinina ba dan ubanki meye wani mahir yadda kike kaunar yaron nan ko ubanki bakya kauna haka baki da magana sai mahir mahir, namiji dai ba abin goyo bane wllh daga lkcn da kika nuna ke shi kadaine a gabanki lokacin ze bude kafa yayi ta zuba miki bura uba, kin zauna kina aikin wahala kan namiji to idan bake kadan bace sai meye akayi."

"Ai dayake kinga ke kin kafa kin tsare a wajen dad dole ni kice mini haka, daman na dade da sani cewa Dad ne kawai ke sona ke burinki kici mutuncin mahir a gabana ki rabani da shi."

Tayi maganar cikin fushi kai ka rantse da mate dinta take mgn, baki mummy ta rike tace.

"nafisa ni kike fadawa haka?"

Banza tayi da ita tana turo baki ta nufi katuwar wardrobe dinta dake shake da kaya.

Kwafa mummy tayi ta fice daga dakin tana fadin.

"zakici ubanki indai nice dani kike zancen."

Kasa kasa Fina tace.

"badai ubana ba.😓wa iyazubillah yh rabb ka shiryamu karabamu da sharrin zamani ka shirya mana zuri'a. "

Wata 'yar 6ingilar vest marar nauyi tasa iyakar cinyarta ko bra bata saba tasa pant kawai, ta kwanta saman sofa tare da janyo wayarta ta fara kiran layin mahir, zumbur ta Mike zaune tare da dafe kirji ganin line busy tun dazu take kiransa call waiting ynz kuma busy.

Jikinta rawa kawai yake ta dubi hadadden agogon dakin taga 9 na dare.

"Kam bura....dawa yake waya this time? "

Da sauri ta danna wayar Samuel bugu daya ya dauka ta hau kansa da ashar.

"Kai dan abakazan ubanka da uwarka aikin me nasaka ne jiya? Oh kamayar dani yar iska ko wato kudin banza nake ba? No naci uwarka tashanci da rashin mutunci kasan abinda zan iya aikatawa matukar bakayi mini abinda na saka dai dai ba."

Daga chan 6angaren Samuel cikin hausan shi dabata fita sosai yace.

"ma'am tun dazu na turo miki duk wani information na yarinyar hadda pic din ta."

"ta uwaka ka turon a ina ka turon look Samuel kasan Banson rainin wayo ko?"

"ma'am ki duba whats'app din ki."

Tsaki tayi ta katse wayar tayi saurin shiga what's app din ta, da sauri ta tafi nmbr Samuel gabanta ne ya yanke ya fadin lokacin da taci Karo da lustrous skin din hibba Fuskarta dauke da kyakkyawan murmushi tana sanye da dogon hijjab blue sai likaf a fuskarta amma ta dage shi sama, jikin Fina yayi mugun saki dan ita tunda ma take bata ta6aganin good girl kmr hibba ba, ita kallon sani ma take mata, duk da sanyin dakin amma gaba daya ta jike sharaf, rubutun sama ta fara karantawa komai na tarihin hibba rubuce.

Sai lokacin ta tuna gurin da ta santa time din da suka hadu zata shiga office din mahir.

Wani murmushin takaici tayi kafin ta dauki daya wayarta ta danna wata number cikin wani irin yare kamar nufanci tace.

"aiki nakeson sakaku."

Shiru tayi kafin ta kuma cewa.

"ah ah dauke mini ita nakeso ayi ku kullen ita tare da gana mata azaba mai radaddi kafin na baku umarnin ku kasheta."

Shiru ta kumayi tana sauraran abinda ake fada mata sannan tace.

"zanyi maka transfer kudi ishashshe, aikin ku ze fara gobe, ynz zan turo ma da duk wani information na yarinyar bana son a sami matsala."

Gyada kai kawai tayi kafin ta ajiye wayar tana sake kallon fuskar hibba sosai, sae ta tsinci kanta Tana hawaye girgiza kai tayi tare da share hawayenta a fili tace.

"sai kin dandani azaba da radaddin da kikasa zuciyata a yau wllh sai kinyi dana sanin sanin mijina da kikayi."

Daga haka ta ajiye wayar tare da nufar fridge ta bude ta dauko wata karamar kwalbar cyrup ta bude ta kwankwade du...hegia kawar Ashe tana dan kora ruwa🤣🤣






Hibba kuwa karfe goma suka gama waya da mahir bayan ya turo mata zazzafan message da kullum sae anyi kusan ba adadi ajiye wayar tayi saman kirjinta tana sake jin wani sabon sonsa na musamman.

Unty ramla ce ta kirata ta daga da sauri tana fadin.

"yar halak ynz nake zancenki a zuciyata zan kiraki."

Daga 6angaren unty ramla tace.

"ke bana son gulma kina zancen sa dea tun yaushe nake kiranki busy kingama soyayyar zaki ishen da gulma ynz ni kuma."

Dariya hibba ta tuntsire da ita tace.

"kinji ki unty da wani zance kawai dan kinji ina waya sai kice soyayya nake."

"dan Allah Rufan baki kowa yaji muryanki yasan kina cikin farinciki sosai, magana zamuyi gobe kizo gida ina son ganinki."

"ko baki fada ba unty ramla dannima cike nake da son ganinki akwai muhimman maganganun da zamu tattauna, amma ki kira baba ki fada masa dan kinsan baze barni nazo ba."

"na kirashi tun dazu ma,sai Kinzo din plz ki tsaya ta kasuwa ki tahon da zo6o da kayan kamshi."

"okay tohm, ina su amna kawa sunyi barci ko?"

"tun dazu mana nima kwanciya zanyi good night."

Sallama sukayi, ta mike ta fito tsakar gida a bakin famfo tayi alwala sannan ta dawo dakinta ta tada sallah, ta jima tana nafila tare da karatun Alkur'ani mai girma sujjadarta ta karshe ta dade tana addu'ar neman za6in Allah alamuranta tsakanin mahir da anwar duk wanda yake alkhair Allah ya bata shi wanda ba alkhairi ba kuma Allah ya cire masa sonta tare da bashi wadda ta fita domin sosai takejin mugun tausayin anwar ko dan lalurarsa domin tsakanin shi da mahir ta rasa wanda yafi wani sonta, ba ita ta kwanta ba sae da tayi sallahr asuba.

Haka ma 6angaren mahir shima kwana yayi yana sallah domin shi yama riga da ya saba baifiya yin barci da daddare sosai ba, shi isa duk wani tsafin fina da mahaifiyarta befiye kamashi sosai ba.




Washe gari.......





Manage plz zuwa gobe.







share
vote
comments







Oum Afaf🖤🔥
(Mrs Dr Ahmad)✍🏻
[9/22, 2:41 PM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

💋💋💋💋💋💋💋💋
*NI DA DR MAHIR*
💋💋💋💋💋💋💋💋

Writing by
*HAFSAT BELLO*

_follow me on instagram:_
*Hafsat Bello*




_sakallahu khair ummu nawwara my God bless you nd ur fam❤_





*🅿 16*

Karfe goma sha daya na safe ta gama shiryawarta tsaf zata tafi gidan unty ramla bakar abaya ta saka tare da mayafinta, dakin baba ta shiga da sallama da yake yau bai fita ba, zaune ta iskeshi kan kujera yana duba wani littafin Islam har kasa ta tsugunna kanta a kasa tace.

"baba na shirya zan tafi."

Dago kansa yayi ya kalleta yana zare medical glass din fuskarta, tsura mata ido yayi Allah ya sani yana son hibba amma baze sakar mata ba matukar bata fitar da miji ba dan ba yarda za'ayi ace yarinya shekara 26 amma tana zaune godegode babu aure, a dan murtuke yace.

"tace zaki dan kwanar mata biyu koh? "

"ah ah baba ba kwana zanyiba domin gobe zanyi resuming aiki."

Wani kallo yayi mata sannan yace.

"aikin kenan aiki aiki kullum kamar wata inji, hibbatullah kin san dai ni ba sa'anki bane ba koh?"

Ya tambayeta seriousness.

Kanta a kasa ta gyada masa kai, jinjina kai yayi kafin yace.

"toh magana ta karshe da zamuyi dake yau akan aure kinji na rantse wallahi tallahi na baki nan da wata guda ki fitar da miji idan ba haka ba kuma, hmmm tashi kije Allah ya kiyaye."

Kai ta kada tare da mikewa tana kokarin mayar da hawayenta.

Tana fitowa taga umma tsaye jikin bangon dakin tausayin hibha ya sake kama umma, ta share hawayen da suka zubo mata tare da riko hannun ta suka shige cikin uwar dakin umma.

Cike da tausasawa umma tace.

"ki cigaba Hibbatullah har kullum Allah yana tare da masu hakuri, komai da lokacine kema lokacin ki yana nan tafe insha Allahu."

"umma ada baba ba haka yake mini ba amma yanzu duk yabi....."

"ya isa hibba mahaifinkine yafi kowa sonki duk abinda yake miki soyayyace ta jawo haka karki kuskura shedan ya darsa miki wani abu a zuciyarki game da mahaifinki, ki share hawayenki ki tashi ki tafi rana tana kuma kwallewa."

Ba musu hibba ta Mike a sanyaye ta nufi dakinta hand bag dinta ta dauko sai wayarta da flat shoe ta fito, a tsakar gida ta sami umma tana kokarin shiga kitchen tace.

"umma na tafi."

"toh hibba ubangiji Allah ya tsare sai kindawo ki gaishesu."

"toh zasuji. "

Ta fada tana ficewa, a kofar gida suka hadu da rayyan dawowarsa daga sch kenan tace.

"engineer da kansa har an dawo."

"yp ina zaki da tsakar ranar nan?"

"gidan unty ramla."

"tab gsky unty hibba bakyajin rana amma dae ba kwana zakiyi ba."

"kwana zanyi mana."

ta fada cike da tsokana, ido ya zaro tare da dan 6ata face yace.

"gaskiya ah ah kije dai ki dawo banda kwana."

murmushi tayi tare dajan sumar kansa tace.

"kaga wannan munafukar sumar da ka tara sai an cireta dana dawo insha Allah da kaina zan kaika a cire."

dariya yayi tare da danyi gaba yace.

"kinga muje na sama miki napep."

Tare suka jero har tahau napep yana daga mata hannu, sae da ta fara biyawa kasuwa ta suyo mata sautinta sannan ta dan siyawa su amna abubuwa ta shige.



Ko da taje gidan bata sami unty ramla ba sai mai aikinta dake zaune kan kujera tana bawa Amna kamu.

Cike da murna da gwaranci Amna ta taho gurinta, ita kuwa ta cha6eta tare da dagata sama tana shillawa tana dariya tace.

"my kawa I missed you too, where's mum?"

Dariya Amna ta 6ingile da ita, hibba ta kalli Kamila da itama murna tasa bakinta kin rufuwa tace.

"unty hibba tun safe nake zuba idon ganinki sannu da zuwa, yah jiki?"

Zama tayi tana daura Amna kan cinyarta tace.

"jiki yayi sauki Kamila badai har ynz untyn bata dawoba?"

"eh ynz zaki ganta dan tace bazata dade ba yau."

"lallaima tun dazu take damuna da yawa, su boy ana sch."

"eh kullum sai sunyi kuka su gurin unty hibba zasu, amma dai kwana zakiyi koh unty?"

"kwana Kamila ah ah tafiya zanyi."

"Kai unty hibba wllh hatta baban boy yace yayi kewar motsinki."

"ke rabani da wadannan iyayen gidan naki."

Ta fada tana karasa bawa Amna kamunta, wayarta dake jaka tayi kara number Anwar ta gani murmushi ta danyi sannan ta daga tare da gaidashi tace.

"yah anwar lafiya naji muryarka so weak."

Wani numfashi ya ja da kyar kafin yace.

"baby am so sick, tun jiya ina hospital ma now."

ido ta zaro gabanta ya yanke ya fadi tace.

"innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un abin har da asibiti amma dai ba ciwon bane ba koh?"

Dan tari yayi na mararsa lafiya yace.

"shine baby."

muryarta ta Fara rawa hawaye suka Fara zubo mata cike da tsananin tausayinsa tace.

"yah rabb ya akayi haka yah anwar kana sa wani abu aranka ko plz mene cikin ranka."

Tari ya farayi da karfi yana salati tare da fadin ta yafe masa ze mutu, Amna ta ajiye ta Mike da sauri ta shige dakin su boy tana sakin kuka sosai.

"kabar fadin haka yah anwar bazaka mutu ka barmu ba muna sanka ni da Mamie da granny bazamu jure rashinka ba, dan Allah ka daina fadin haka."

Ta fada cikin matsanancin kuka.

Sauke numfashi yake a hnkl yace.

"baby do you love me? "

cikin matsanancin Kuka tace.

"eh wllh I love you with all my heart plz don't leave me bazan iya jurewa ba plzzzzz....."

Wani tsalle anwar ya daka wanda har ita sai da tajishi yace.

"yesooo finally she's love me, alhmdllh abinda nakeson ji kenan baby thank you."

wayar ta dago ta kalla da kyau baki sake, domin ita idan Zaka samata wuka a ma'ogwaro batasan abinda ta fada ba, mayar da wayar tayi kunnenta tace.

"yh anwar are you OK? "

"yes cwthart daman kalau nake planing ne kawai, dan ban ta6ajin kince kina sona ba, tabbas nayi dace kuma nagodaiwa Allah Ashe haka kikesona da yawa thanks much, baby bazan ta6arinki ba duk tsanani hibbatullah duk lokacin da rasaki walahi tallah zuciyata Zata karasa bugawa zan iya jure komai a rayuwa amma banda rashinki, na rokeki da girman Allah karki rabu dani ki taimakawa mayan da ya rayu cikin kunci na rashin makusanci ki taimaka ki ceci zuciyar dake aiki da na'ura saboda tsabagen rauninta."

jikin hibba ya gama Saki In banda hawaye babu abinda take tabbas yau anwar ya kulleta da jijiyoyinta ta shiga uku ina zata saka ranta.

"baby kinyi shiru yi hakuri nasa beautiful eyes naki zubar da hawaye plz am sorry ban karawa."

"amma gsky ka daina irin wannan wasan"

"na daina baby indai kullum zaki dinga sanar dani kina sona."

"hmmm."

"okay kina ina?"

"gidan unty ramla."

"nashiga tara ni salihu jikan salihu ynz haka kika fita ke daya kika hau napep, nasan duk mazan duniya Sun gama gane mini mata."

"kajika wai duk mazan duniya, ni bawanda ya ganni."

"ban yarda ba, gsky ni banji dadin fitarki ba tare dani ba, dole idan na dawo nasan abinyi."

"hmm, kaga ni duk ka rudani bari naje nabar yarinya parlour."

dariya yayi tare da manna mata kiss ta kashe wayar da sauri tana dariya kasa kasa, toilet tashiga ta wanko fuskarta sannan ta fito parlour unty ramla tana zaune rungume da Amna dake tsala ihu, Kamila kuma tana zaune.

Harara unty ramla ta maka mata, ita kuma tayi murmushi ta zauna kusa da ita tare da daukar Amna tana jijjigata tace.

"nashiga uku ni hibba wa yasa mini kawa kuka Kamila? "

"munafuka bake kika samini ita kuka ba tun daga gate nakejin ihun yarinyar nan, wait wai kukan ubanwama kikayi ke?"

Dariya ta bushe da ita ta kalli Kamila tace.

"kuka kuma Kamila wace tayi kuka?"

Kamila zatayi mgn unty ramla tace.

"karkice komai Kamila bar yar rainin sense saurayintane yake kokarinmutuwa shine take kuka munafuka."

Dariya hibba ta sake bushewa da ita tana kissing Amna da tayi shiru tana lumshe ido alamar bacci zatayi.


bayan Sun gama lunch suna zaune parlour suna hira, su biyu nan unty ramla ta nutsu sosai ta fuskanci hibba tace.

"yar uwa mene tsakaninki da Barr anwa?"

hibba bata da abokiyar shawara sama da yar uwarta basa 6oyewa junansu komai, ta gyara zama da kyau sannan ta fara kwararo mata bayani game da tarihin anwar da soyayyar da yake mata daga nan kuma ta daura da bata labarin Dr mahir da son da take masa tun lokacin da aka kawoshi asibitinsu a matsayin CMD ta dage sosai tana fada mata irin yarda take sonshi fiye da komai ta kuma sanar da ita tausayin anwar da kullum ke sake mamaye ranta.

Ajiyar zuciya unty ramla ta saki tare da cire tagumin da tayi tace.

"tabbas yar uwa kina cikin tsaka me wuya, kina bukatar addu'a sosai tare da neman za6in Allah, amma ke tsakaninki da Allah a cikinsu wa kike ganin zaki iya aure?"

kallon unty ramlan tayi da rinannun idanunta tace.

"inason mahir gsky san da baze misaltuba, amma anwar jigone a taredani zan iya sadaukar D soyayyar mahir ga anwar ko dan ceto raunanniyar zuciyarsa, amma shima mahir din ina....."

"ga shawara hibba ki rabu da wani mahir bawai dan wani abuba wllhi zanfi kowa farinciki idan akace kin sami miji kamar Dr mahir domin mahir namijine mai nagarta da kyawawan halayen da duk wata mace zatayi farincikin samun miji kamarsa, a dan sanin da nayiwa Dr mahir tare da abban boy na gane cewa mahir yana daga cikin waliyyan maza wadanda bamu dasu a wannan zamanin sai dai abu guda matarsa, nasan kinsan wace Dr Nafisa dan baiwa, kwata kwata bata da mutunci bata da imani akan mijinta, hibba babu macen da zata iya zaman kishi da Fina domin bata da tausayi zata iya komai idan nace miki komai to komai da kika sani rashin imani akan mijinta Tana da kudi suna da milki kinga kuwa zata aikata duk abinda taso, bazanso ki jefa kanki cikin hatsariba ke kadece yar uwata mace bazan so ganin rayuwarki cikin hadari ba, yanzu ma rayuwarki tana cikin hatsarine matukar tasan abinda ke tsakaninku.
Kinga kuwa anwar gashi saurayi bashi da wani aibu gwanda gurin da hnkln ze kwanta."

Numfashi hibba ta sauke tabbas magan ganun untyn ta sunshigeta duk abinda ta fada babu karya a ciki.

"hakane unty amma ya zanyi da Dr kuma yaune ranar dazezo amsar answer soyayyarwa, wllh unty idan na rasashi zan mutu shima yana sona unty ina tausayin anwar zuciyarsa da injina take amfani."

Wannan gwagwatsula ta hibba da yawa take unty ramla ta fada a zuciyarta, kukan da hibba tasa yasa tajanyota jikinta tare da rungumeta tanashafa bayanta cike da tausayawa.

"kiyi hakuri kibar kukan haka kiyi addu'a ki mikawa Allah za6inki duk wanda Allah yayi mijinkine to ze bawa daya dagana da hakuri."

haka dai 'yar uwa ta gari da kowa yake bidar samu tayi ta kwantarwa da hibba hnkl da kalamai masu sanyi tana sake tunatar da ita saka ubangiji aduk wani lamarinka da bar masa za6i, sun shafe kusan awa 3 suna tattaunawa.

Kamila ce tashigo parlourn da sallama Amna sa6e a kafadarta tace.

"unty gata har tashi tana kukan unty ibanta(hibba)"

dariya hibba tayi tare da amsarta tanafadin.

"kawa har an gyangyada an tashi."

Unty ramla ta

Please Login or Register in order to submit comment