Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dubi agogo ta mike daga shingidar da tayi tace.

"na mutu ni ramlatu, kinga har 4 tayi wai."

"ehmna ae ynz lokaci gudu yake sosai."

"Allah kasa mu cika da imani,bari na Mike kar mijina ya dawo ya ganni haka shirim babu kyan gani."

Dariya hibba tayi tace.

"wai shirim toh Allah na tuba ae ynz kun zama daya."

"wane daya😳hibba da namijin ake zama daya tab irin na da kenan banda mazan ynz dan wllh mazan zamanin nan kyar suke kana watsa ruwan ma ya kuka Kare bare ka zauna haka, bari kiji hajiya kawai ki dage ki daura damar zama karuwar mijinki, dan yasin duk macen da tace zama zatayi sun zama daya da miji hhhh zataga zama kuwa."

"haha haha kina ruwa sister amma a ganina yara uku ke da yah Khalifa ae an zama daya wane dare ne jemage be gani ba in banda na mutuwarsa."

"ae daman ba'a fatan yaga wannan daren hajiya tab, ke kullum fa fil nake zama wajen mijina domin bana wasa da kula da gyara tsaftar jiki gida da yarana, ina kiyaye dokokin hancin mijina da idanuwansa, ke yau ma in fada miki jijji6i nasa unty fati ta dafo mini yau special night zamuyi.."

Hibba sbd da dariya har da hawaye tana dariya tace.

"yauwa Allah zan mutu dariya mene kuma jijji6i unty."

"hehehe au bakisan jijji6iba to ki bari idan kinsha daga ciki zaki sanshi."

"fadan ynz mana ni daina ta6a jin nurses din wajen mu suna mgn sa so bansan mene ba."

Wani dan karamin flacks ta janyo ta bude mata tace kinga jijji6i toh."

"wow nama ne ae."

Ta fada tana kai hannu da sauri ta janye flacks din tana 6oyewa a bayanta tana dariya tace.

"kuji mini kwadayayyiyar 'ya daga nuna miki abu sai ci."

"yaban sha'awane sai kamshi yake wllh yanka daya zan dauka."

"gindin saniyar zakici."

ido hibba ta zare tare da yamutsa fuska tace.

"dan Allah mene?"

"wllh gindin saniyane ake dafawa da magunguna, humm hajia a kalla duk wata ki cishi wato gaban mace ne ke ciccikowa sosai ya matse 6am ta yarda wagga aba🍌sai tayi da gasken gaske zata shiga ga uwa uban ruwan ni'ima kamar famfo, ynz idan na baki wannan ae sae ki kama Dr kiyi masa fyade."

ta fada tana dariya ta Mike ta shige extra parlournta, hibba kuwa ME take IN banda dariya wayartace tayi kara alamar shigar message tana dubawa taga mahir ne ya rubata kamar haka.


_"on my way........ I love you"_


















vote
comments
Share


















Oum AfafπŸ–€πŸ”₯
(Mrs Dr Ahmad)✍🏻
[10/11, 8:59 AM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*NI DA DR MAHIR*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*

_Follow me on instagram_
*hapc20*






*πŸ…Ώ 17*

Bayan sallahr isha hibba ta fito zata tafi gida babu yarda basuyi da ita ta kwanaba amma taki, har bakin titi unty ramla ta rakota, suna tsaye ta samu dan sahu tashiga.

Suna cikin tafiya taga sun kauce hanya ta dubi mutumin tace.

"bawan Allah ina zamu kuma?"

"ina kikace zaki?"

"goron dutse mana naga Ka sauka daga hanya."

"sai ki zuba ido ki gani yanke nayi saboda d'ayar hanyar akwai go slow da yawa."

"amma kuwa ka dauko mu da nisa."

Ta fada tana danna Nokia hannunta.

Wata hanya mai duhu suka shiga nan gaban hibba ya soma faduwa tace.

"wai dan Allah ina zaka kaini ne? Saukeni inkasan bazakabi dani ta hanyar da bansani ba."

"amma ke kuwa ko uwar wutar cikin tsiya gareki ni banson mita kin fini sanin abinda nake ne."

Karfen ta rike cikin tashin hankali tace.

"wllh sai ka saukeni bazan shiga wancan bakikkirin din duhun can ba."

Fuzgar dai daita sahun yayi da karfi, tare da jan wani wawan burki Wanda yasa hibba dakuwa da karfen napep din, rike kanta tayi tare da furta "yah salam"

Wata katuwar jeep ce tsaye gabansu, wasu gidiga gidigan maza suka fito su biyar daga motar duk da cikin duhu ne amma kallo daya zakayiwa fuskarsu kasan babu digon imani a tare dasu, da sauri hibba taja da bawa tana kiran.

"innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un, allahuma ajirni fil musiba wakhlifni khairan min..... "

Bata kai karsheba daya daga cikinsu ya fuzgota da karfi tare da shaka mata handkerchief a hanci nan take ta fadi kasa a sume, bandir din kudi yan dubu dubu daya daga cikinsu ya bawa Mai napep din ya kar6a jikinsa na tsuma domin shi kansa tsorace yake da wadannan mutanen, hanya suka saita masa sukace ya 6ace daga nan ai kuwa da gudu mai napep din ya arta baya ko juyowa, cikin mota suka zura hibba tare da tattaro Jakarta da wayarta suka zura motar sukayi gaba.



Su umma na zaune tsakar gida suna sauraron radio karfe 9:15 rayyan yana wani assignment a wayarsa ya dago tare da kallon umma dake jingine da pillow tun dazu bata iya ko magana yace.

"umma kinga unty hibba me cewa bazata kwana ba har ynz daman nasan ta fada ne kawai amma gidan unty ramlar zata ta dawo a yini daya suda idan sukaga hadu kamar zasu hadiye juna."

Umma ta sauke ajiyar zuciya domin ita tun magriba gabanta ke faduwa tace.

"kirata a waya muji idan kwanan zatayi amma ni nan bata ce mini zata kwana ba."

Baba dake rike da radio ya ajiye sannan yace.

"A kirata kice mata me? Kema kinsan tunda takai I yanzu bazata dawoba suna can suna aikin dariyar su."

Dariya rayyan yayi yace.

"wllh kam dan idan akace Sun hadu musamman da su unty zarah(matar yah mudan) da unty safna(yah abbakar) yayyen hibba ae abun ba'a magana."

Dariya sukayi banda umma da tayi shiru ita dai ji take ajikinta akwai wani abu a kasa.



6angaren Mahir ma ya gama shirin kwanciyarsa tsaf ya kwanta a lafiyayyen gadonsa duk da yana cikin farinciki samun soyayyar hibba amma yanayin jikinsa yana nuna masa cewa something is wrong.

Wayarsa ya janyo tare da danna mata kira, sai dai har takatse ba'a daga ba sake kira yayi ba'a d'agawa sai da yayi mata wajen 30 missed call amma bata dagawa daga karshe ma sai ta dinga fadin is not reachable.

Mikewa yayi zaune tare da fadin.

"what's wrong with her ne? Bata picking call yah rabb yasa everything alhmdllh. "

Dafe gefan kirjinsa yayi yanajin yarda gabansa ke tsananta faduwa zuciyarsa na wani fat fat da sauri, still sake kiran wayar yayi bata shiga mikewa yayi ya shiga bathroom tare da dauro alwala yazo yasa jallabiya tare da tada sallah.



Haka takema ta 6angaren Anwar babu irin kalar kiran dabeyi mataba amma bai samunta, gaba daya yagama shiga damuwa da tashin hankali yanason kiran wayar umma amma yanajin nauyi, dakyar ya samu bacci ya daukesa tare da bakaken mafarkai mararsa kyau wadanda baisan nameye ba shi dai abinda yasan ze iya tunawa shine kukan da hibba keyi mai tsanani tana kiran sunan wani baya gane me take fadi amma bashi take kiraba, da ciwon kai ya tashi yayi sallahr asuba a wahalce tare da shirin dawowa kano.





6angaren su hibba kuwa da wadanda suka kamata tafiya sukayi mai tsananin tsayisun ketare daji daji da dama, basu suka isa wani katon daji mai tsananin girma da tsayiba sai karfe bakwai na safe duk kuwa da gudun da suka dinga shararawa wani gida mai tsayin gaske suka nufa ginin tsaf irin na prison, a bakin gidan sukayi parking tare da fiffitowa sai lkcn na Kare musu kallo da kyau kaf dinsu ba hausawa bane irin nufawa din nan ne masu munin halitta fuskarsu duk dinki ansha yanka.

Daya daga cikinsu wanda daga gani kasan shine babba ya dubi yaran nasa cikin yaran nufanci yace.

"kudauketa ku shigar da ita ciki."

Mutun daya ne ya sa6i hibba dake barci kamar gawa ya shigar da ita cikin gidan gaba daya Kansan gidan takin awakaine da ciyawa, wani daki mai duhun gaske suka jefata wanda shima takin ne kawai aciki da ciyawa ya fito.

Ogan yana shan sigari ya danna wayarsa tare da karawa a kunnensa.

Bugu uku aka katse kiran wayar tare da kira.

"ma'am komai ya kammala mun iso."

Daga daya 6angaren akace.

"inaso ku hanata ci da sha na tsawon kwana uku."

"angama ma'am."

Kit aka datse kiran, kuma duk maganar da sukayi sunyitane cikin yaran nufanci.


Karfe 9 dai dai hibba ta fara motsa kafarta a hankali idanunta da sukayi mata azabar nauyi ta fara budewa a hankali har tagama budesu, a hnkl ta motsa hannunta sai kuma ta Mike da sauri tana waige waige tsananin duhun dakin dako tafikan hannunka baka gani ta farabi da kallo, tsaye ta mike jikinta na wani irin rawa, inbada zare ido babu abinda takeyi, abinda ya faru da ita ta fara tunawa, wata kara ta saki tare da daura hannuwanta duka biyun kanta tana fadin.

"innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un nashiga uku na ummata babana ina ne nan?"

ta karasa maganar tana Saki wani irin kuka, Mikewa Tayi da sauri wane mahaukaciya ta fara laluban Jakarta tana neman wayarta jakar kawai ta gani ta zazzageta a kasa sai dai babu wayarta a ciki, kuka take kamar ranta ze fita tana fadin ina ne nan sai dai babu amsaπŸ˜“



har washe gari Mahir na kiran wayar hibba zuwa ynz a rufe take, gaba daya baya cikin nutsuwarsa gashi duk karatun alkur'anin da yayi gabansa bai bar dancing ba, lokaci guda wani zazzafan zazzabi ya rufeshi na fargabar mai yasa wayanta baya shiga, yana kwance cikin blanket kiran fina ya shigo wayarsa sai dai har ta katse bai dagaba haka ta kira har so uku amma baya dagawa.

Daga 6angaren Fina kuwa baki ta dan ta6e sai kuma ta tuntsire da dariya afini tace.

"kayi kagama."

Mum da dad suka kalleta sai ta dan yamutsa fuska ta Mike tana danna kiran telephone din gidan.

Kuku dake shirya breakfast a dinning ne yayi picking cikin girmamawa ze fara gaidata a dakile ta dakatar dashi cike da gadara da izza tace.

"Dr yafita ne."

"nop hajiya I tot bai fito bama."

Mtsw." taja tsaki tare da katse kiran.



2:00pm

Umma ta dubi rayyan tace.

"kai auta kiramin hibba a waya nagaji da wannan shirun."

"umma tun dazu nake kiran wayarta ta a kashe wllh itama dai unty hibba ta fidda kudi tasiyi waya taki ta tsaya da Nokia."

"kai banson magana kiran ramlatu toh."

Wayarsa ya cira daga charge ya kamo number unty ramla tashiga ta datse kiran sai gashi ta kira tana dagawa yace.

"unty ramla kirafa nayi kikayi wani rejrctive."

unty ramla tace.

"enyeh auta kenan yan university an fara samun ribar kudin transport kenan."

Dariya yayi sannan yace.

"to mugaisa ina wuni yah su boy da jidda da mahaifiya."

"duk muna lfy lao kana gida tun jiya nake neman wayar hibba da umma bata shiga baba ma nakirashi dazu bayajina bani hibba dan Allah."

Daga umma har rayyan shocked suka shiga, network din kansu dif ya dauke, unty ramla tace.

"Hello rayyan kanajina."

Ina babakin mgn umma tayi ta maza ta amshi wayar cikin rawar jiki dukkan wani part najikinta Rawa yake tace.

"ramlatu mai kike cewa daman hibba ba a gidanki ta kwanaba ko da safe ta taho."

Unty ramla taji tmbyr bankwarakwai tace.

"umma me kike fadane ai tunjiya ta taho dan babu yarda abban boy beyi da itaba akan ta kwana amma taki dakaina muka rakota har cikin dan sahu mai kike cewa ne."

"lahaula fishi'atullah innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un subhanallah."

shi kawai umma ke maimaitawa wayar ta su6uce a hannunta ta fadi, rayyan kuwa gaba daya battery din kansa yayi shutdown, unty ramla itama da gaba daya ta gama gigicewa dakyar ta iya kiran Khalifa ta sanar dashi halin dake faruwa, daga ita sai riga da wando ta fito, a bakin layin suka hade da Khalifa dakyar ya ta yarda suka koma gida ta chanza kaya tasa hijjab suka fito, su yah mudan da abbakar har da babban yayansu dake kaduna sai da aka kira ko hibba tazo amma ah ah.

Karfe hudu gaba daya family din yaya da jikoki da surukai sun hallara a gidan, tsayawa fadin tashin hankalin da gidan ke ciki 6ata lkc ne domin hannu baze iya rubutawa ba kawai ku hararo tsananin tashin hnkln da mutun ze shiga idan karasa wani naka ta hanyar 6acewa.

Duk iyakar cigiya gidan yan uwa da kawaye babu inda ba'ajeba, umma itadai tana zaune shirim tsakar gida bata iya motsa koda dan yatsanta jikokin gidan kuwa kowa kuka yake duk taurin zuciya irin ta baba idan ya kalli fuskar zuri'artasa sai yayi hawaye lokaci guda 6atan hibba ya karade unguwa gaba daya unguwar ta zama kamar anyi mutuwa kowa jimami.


Jikin mahir yayi tsanani da yawa amma yarda yakeji baze hanashi zuwa yaga halin da hibbarsa take ciki ba dakyar ya Mike rike da bango yayo wanka jallabiya kawai ya zura sai wayarsa da carkey dinsa ya fito kafarsa sanye da Gucci slippers, driver yabawa key domin shi baze iya driving ba suka nufi gidan su hibba yana kwance a back seat jikinsa in banda rawa babu abinda yake.

Shima Anwar hankali tashe ya nufo gidan su hibbar shi da granny domin rayyan ya kirashi ko yasan inda hibba take, hnkl tashe suka nufo gidan su hibbar kusan a tare motar mahir da Anwar ta tsaya, a gigice Anwar da granny suka fito suka nufi cikin gidan.

mahir kuwa yayi kir da ido yanabin bawan Anwar da kallo tabbas shine wanda suka hadu dashi da ita a green pack.

Jiki ba kwari ya fito daga motar kafarsa har hardewa take tsabar rawa da jikinsa yake, yazo shiga cikin gidan ya dan tafi luu ze fadi driver yayi saurin rikoshi sai yayi saurin dafe bango kansa ya dan dafe sannan ya Mike yashiga a zaure ya tsaya ya umarci driver yayi sallama.


yah mudan ne ya leko, kir yayi yana kallon mahir dake rike da kansa tabbas kamar ya sanshi amma ya rasa inda ya sanshi.

"bismillah ku shigo."

Dakyar ya daga kafarsa yabi bayansa cikin gidan, dim dim gabansa ya fadi jin maganar baba yana sanar dasu anwar abinda ya faru.

Dai dai ya karasa shigowa cikin tsakar gidan, tsaye dukkansu suka Mike no wonder professional doctor Mahir mijin yar shugaban kasa doctor Fina ne.

Meya kawoshi gidan kuma cikin wannan yanayin, wani irin jirine yadebeshi ai kuwa ya fadi luuuuuuuu a sume.........





~TEAML~
Dr Mahir
Barrister Anwar
Hibbatullah
Dr Fina (my love)

Where are you πŸ€£πŸ€£πŸ—£πŸ—£πŸ—£
















Share
comments
Vote












Oum AfafπŸ–€πŸ”₯
(Mrs Doctor)✍🏻
[10/11, 8:59 AM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*NI DA DR MAHIR*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*

_Follow me on instagram:_
*hapc20*




~*Last page nayi mistake wajen numbering 18 zamu tashi nasa 17 so yanzu page 19 zamu tashi kunga muna da page 17 guda biyu kenan fatan kun gane nagodai*~





_Sorry for the late postπŸ™ˆ_




*πŸ…Ώ 19*

Kansa sukayi cikin sauri driver ya tallafoshi ya fado jikinsa, ruwa aka samo aka yayyafa masa, bayan wasu 'yan sakanni ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin ya fara motsa bakinsa a hankula idanuwansa a rufe, Khalifa Abban boy yace.

"Dr open your eyes plz."

"hibbahhh!"

Shine abinda ya furta a hankula, gaba d'aya gurin kowa shiru yayi yana mamakin hadi hibba da handsome man like mahir.

Kamar an fuzgeshi ya Mike tsaye jikinsa na wani irin rawa idanuwansa sunyi masifar ja jijiyoyin kansa duk sun mimmike rud'u rud'u.

Gaban baba ya nufa tare da zuba gwiwoyinsa kansa, cikin raunin murya yace.

"baba where's my love, tell me jiya muna tare hibba tace tana sona zata aureni baba tana ina.... "

Wani irin fizga Anwar yayiwa mahir yana wani irin huci kamar mayunwacin zaki, shakeshi yayi da bango cikin daga murya yace.

"ubanwane ya baka ita who are you da Zaka dinga dangana matata da abar sonka, I said who are?"

Ya karasa mgnr cikin daga murya yana wani irin jijjigashi, wani irin turi yayi masa tare da zuba masa wasu kyawawan maruka masu kyau, ya daga hannu ze sake marinsa granny tayi saurin rike hannunsa ranta a matukar 6ace.

Ta daukeshi da wani irin mari mai zafin gaske.

"bawanka ne yaron da bashi da cikakkiyar lafiya zaka mara kai ubanwaye."

Hannun mahir dafe da kuncinsa, karo na biyu kenan tun tasowarsa da wata ko wani ya daura hannunsa a kumatunsa da sunan Mari.

Tabbas matar nan badaban girmanta ba da yau sai ya nuna mata cewa irinta dubu basu isa ba.

Jijjiga kansa yayi cike da takaicin marin yayi wani irin murmushi tare da kallon driver yayi gaba suka fita daga gidan.

Granny tayi saurin riko anwar tana kuka tace.

"sannu alhj Allah ya saka maka bakin mugu azzalumi bazamu ta6a yafe masa ba."

Gurin dai gaba daya kowa tsit yayi suna cike da mamakin abinda ke faruwa.



Mahir kuwa suna fita direct CP na jihar Kano ya kira tare da sanar dashi duk halin da ake ciki na 6atan hibbar, hotunanta da ya dinga daukarta jiya uncontable ya tura masa, daga haka suka nufi gidansa jikinsa na tsananta zafi.

Su baba gaba daya suka tafi police station domin suyi report 6atan hibban sai dea abin mamaki duk police station din da sukaje sai suji cewa sun san da sanarwar abin ba karamin mamaki ya basuba Khalifa ne kawai yasan cewa aikin bana kowa bane sai na Dr mahir.


A gaggauce..

Bayan kwana uku..


Dakin da hibba ke ciki na leka nan na hangota har yanzu tana cikin bakin duhun nan dakin in banda wari babu abinda yake, zaune na ganta ta cusa kanta gaba d'aya tsakanin cinyoyinta, wani hasken fitila mai hasken gaske ya gauraye dakin gaba daya.sai hibba tadago idonta domin ganin wannan hasken daga ina,saitaga wasu kartin maza a tsaye akanta sai gurnani sukeyi,hibba tace cikin kuka da zubda hawaye dan Allah mena muku kuka kawoni nan kuka rabani da iyayena da dangina plssss menamuku,tacigaba da kukanta sai Kawai suka sheqe da dariyar mugunta wani wanda yafi kowa muni da bakar fuska acikinsu ya murtuke yace ke yarinya stop all this nonsense crying domin bake ba fita a gidannan saide gawarki suka Kuma dariyar mugunta suka fice abunsu..




Acan bangaren kuwa mahir in hankalinshi yayi dubu yatashi baya iya Bacci balle kuma cin abinci Ita kanta feena inta kirashi yanzu ko dagawa bayayi Kawai shide burinsa aga hibba ya dugufa wajan fadawa Allah..Hakama wajan Anwar take har kakarshi tafara damuwa Kar ciwonshi yatashi saboda irin damuwar datayimishi yawa kullum tana cikin kwantar masa da hankali amma abin yaci tira saboda shi yanzu duka biyune ke damunshi ga damuwar batan Hibbarsa ga Kuma wani yazo yana kiranta da his life yarasa ina zaisa ransa ..




Gidansu hibba an dukufa anata addua kowa hankalinsa a tashe yake kana ganin wnn family din kansa something is very wrong with them ,they are not happy at all




Yaune takama ranar daza abama hibba abinci tana zaune ta kudindine ga yunwa ga ishirwa ga damuwa ga tunanin halin da danginta da masoyinta suke ciki duniya tagama Mata zafi sai Kawai taji shigowar mutane dakin....
[10/11, 8:59 AM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*NI DA DR MAHIR*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*

_Follow me on instagram:_
*hapc20*



_this's for uew my twiny cousin HAUWA ABDULQADIR (sima) kiyi yarda kikaga dama da shi....thank you for the luv nd support_





*πŸ…Ώ 10*

Hasken dakin ne ya sake bayyana wannan yasa hibba saurin mayar da idanuwanta ta rufe sbd wani irin dum da sukayi mata.

Farar kafartace ta bayyana sanye cikin wani uban takalmi mai shegen tsini kafarnan kamar ta jarire, hibba tayi saurin dago da kanta sai dai bata Iya ganin fuskar mata sbd fitilar iyakar ita kade ta haska.

Feena ce sanye cikin wasu classic English wear fuskar nan a daure babu alamar fara'a a tare da ita, bayanta wadannan da suka dauko hibba ne, kujera suka ajiye mata ta zauna tana wani ya mutsa fuska, fitilar aka kashe sae kuma aka kunna ta gaba daya dakin, idanu hibba ta fara zarewa tanabin dakin da kallo wasu zafaffun kwalla suka zubo mata, ta maida kallonta da feena dake mata wani irin kallo, iyakar tsorata da fargaba hibba tayi da ganin feena.

Feena ta dubi daya daga cikin yaranta, da sauri ya miko mata wani mug, ta bude tare da mikewa ta nufi hibba tana mata wani kallo hibba faraja da baya tayi tana girgiza mata kai idanuwanta kamar an bude famfon hawaye, batayi aurena taji feena ta watsa mata zazzafan ruwan barkono a fuskata da jikinta, wani irin kara ta saka tare da mikewa tana daka tsalle idanuwanta a rufe.

Wani murmushin mugunta feena tayi kafin tace cikin isa da kasaita.

"bude idanunki."

Cikin matsanancin kuka hibba tace.

"kiyi mini rai dan girman Allah ki fitar dani daga nan wllh na horu da azabarki nayi miki alkawarin barin rayuwarki da ta mijinki har abada."

Murmushin takaici feena tayi tace.

"good Ashe kinsan laifinki, dan ubanki open ur eyes."

Ta fada a tsawace, hibba girgiza kai tayi tana fadin.

"I can't plz."

"okay. "

Ta fada a mugance alama tayi masu da ido ae kuwa hibba batayi aune ba taji Sun dauketa Sama, ihu ta farayi tana yarfa kafa zuwa ynz muryarta dakyar take Iya fita, wani daki suka shigar da ita wanda dakin gaba daya glass ne, ciki suka shigar da ita tare da daddaure hannayenta a sama, feena ta dafata tace.

"hibba kike or what kinyi gangancin shiga rayuwata bansan bani da imani har hakaba sai danaga kina kokarin rabani da mijina, bari kiji *NI DA DR MAHIR* mutu karaba, so ki ajiye wannan zaki dawwama anan gidan har karshen rayuwarki."

Hibba tayi wani irin murmushi mai cike da tarin takaici cikin dakiyar zuciya tace.

"zaki iya aikata komai a rayuwata kici nasara domin ke marar imani ce, amma abu gudane bazaki iyaba shine raba zuciyar Dr mahir da son hibba ba, domin sona da kaunarsa a cikin jinin jikinsa suke, kuma kiji baki isa kiyi mini abinda Allah beyi mini ba kuma *NI DA DR MAHIR* zamu rayu rayuwa kuwa har ta abada."

Feena da tacika saura kiris ta fashe tayi wata irin dariya tare da dafa kafadarta ta sunkuyo da kanta dai dai fuskar hibbar tace.

"muzuba mugani shege ka fasa."

Daga haka ta hankadata baya, ta fice, tana fita hibba ta fashe da wani irin mahaukacin kuka tana kiran sunan Allah a fili, ruwa ne ya fara zubowa a kanta a hankali a hankali kamar shower lumshe idanuwanta tayi cike da azabar zuciya.





Mahir ne zaune a office din CP yana sauraron bayanin da yake masa akan irin binciken da mutanensu suke gudanarwa sai dea har ila yau zance daya ne babu wata tartibiyar magana CP ya daura da cewa cikin muryar kwantar da hankali.

"kayi hakuri Dr insha Allah sae yarda karfin mu ya Kare zamu tsaurara bincike fiye da wanda muke, ku dai kuje ku cigaba da addu'a insha Allah soon zata dawo cikin koshin lfy."

Mahir ya gyada kai tare da sauke ajiyar zuciya yace.

"but sir I think 6atan hibba ba kidnappers case bane cos da kidnapping akayi da tuni Sun fadi abinda za'a basu zuwa yanzu."

"nima bana tunanin kidnapping nata akayi nafi tunanin hannu ne ya dauketa."

gyada kai yayi yace.

"I think nima."

"dole zamuje mu gudanar da bincike akan mutanen da take mu'amana dasu."

"okay CP plzz dan Allah ka taimaka kayi mini duk wani kokari."

"karka damu Dr insha Allahu zanyi iyakar iyawata zan taimakeka mahir domin kafi karfin komai a gurina karka manta sanadiyarka da mahaifinka nake wannan matakin da nake, to dan me bazanyi amfani da damata ba wajen farantaka, Dr calm down very soon her return to you by the God grace."

Dan dadi mahir yaji ya Mike tare da mika masa hannu suka sake musabaha sukayi sallama, har bakin motarsa ya rakoshi kafin sukayi sallama yashiga mota driver yaja.


wayarsa ya duba yaga miss calls din feena kamar hauka, tsaki yaja tare da danna kiran wayar Mum da yaga miss calls dinta.

Mum cikin sauri ta dauka ta fara magana cikin fada domin batasan abinda ke faruwa ba tace.

"love ka rainani ko?"

"Mum kiyi hakuri."

"keep quiet silly child, kullum inyi hakuri where are you now?"

Mahir relaxing yayi yana shafa kyakkyawar kasumbarshi yace.

"darling ina Kano but..."

Katse shi tayi da fadin.

"meka fada mini jiya."

"mum cewa nayi zanzo yola today."

"okay yanzu kana yola?"

"mum wallahi...."

"dallah rufen baki nasan maganinka zakaci ubanka."

Daga haka ta datse kiran bata bashi damar fadin abinda ze fada ba, lumshe ido yayi yanajin wata sabuwar damuwa a tare da shi, hanyar gida zasu kama ya umarci driver da su nufi gidan su hibba.



Suna isa kofar gidan anwar na fitowa, sai da naji mugun tausayin anwar dan gayu domin tsakanin shi da mahir ban san wanda yafi wani ramewa ba, wani mugun kallo anwar yayiwa mahir shi kuwa mahir ko inda yake be kalla ba domin batashi yake ba.

Motarsa yashiga yabar wajen ransa a 6ace, shi kuma mahir yayi tsaye yana danna wayarsa, rayyan ne yazo shiga gidan ganin mahir tsaye ya matso inda yake tare da

Please Login or Register in order to submit comment