Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

danyi masa murmushi yace.

"ya ka tsaya daga nan baka shiga ciki ba."

Murmushi mahir Yayi masa tare da mika masa hannu suka gaisa rayyan yace.

"kashigo dan Allah kasan baba yace idan kazo ka dinga shiga."

nagodai yace tare da bin bayansa.....







share
vote
comments








Oum AfafπŸ–€πŸ”₯
(Mrs Dr Ahmad)✍🏻
[10/11, 8:59 AM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*NI DA DR MAHIR*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*

_Follow me on instagram:_
*hapc20*





~DEDICATED TO~
*My luvly crazy friend Ruky Apple thank for everything rabb yaraya mana safna habebbty❀*





*πŸ…Ώ 21*

Da sallama suka shiga gidan, umma ce kawai zaune ta zuba ta gumi, tausayin umma ya sake kamashi ya zaune kan kujera yar tsugunno cikin tausasa murya yace.

"barka da yamma umma."

"barka dai dannan ya gida? Ya kuma fadi tashi mungodai Allah yasaka da alkhairi."

Amin ya furta a hankula kansa a kasa zuciyarsa na sake karyewa, pure water rayyan ya ajiye masa a flate tare da zama gefan tabarmar da Umma take zaune duk sukayi shiru gwanin ban tausayi.

Babane ya shigo gidan shima ya rame sosai ya fada gemunsa ya taru sosai tare da farar furfura, mahir ya Mike cike da girmamawa baba ya miko masa hannu sae ya tsugunna tare da gaidashi.

Baba ya zauna gurin da rayyan ya Mike umma cikin sanyi murya tace.

"sannu da zuwa."

"yauwa sannu kadai."

Mahir ya sake kasa da kansa yana kuma jajantawa baba 6acewar hibbar tare da sake kwantar musu da hnkl daga haka sukayi sallama ya fito.

Umma tashare kwallar da tazubomata tace.

"Allah sarki wannan yaro yana kokari da yawa daga ganinsa kasan yana cikin halin ciwo a jikinsa."

Baba ya gyada kai kawai ba tare da yace komai ba.



Kwanci tashi yau sati guda da 6acewar hibba dukkan wani bincike babu irin wanda ba'a yi Saidai har ynz babu wani takameman magana, an baza masallatai da makarantu da majalisan karatu sosai ana zuba addu'a, IN tsaya IN fada muku halin da dangin suke to fa 6ata lokacine.




Dakin da aka saka hibba zuwa ynz ruwan dake zuba yazo mata har wuya saura kadan ya haye fuskarta iya jigata hibba tayi ga wani mugun baki da tayi da rama zuwa ynz bata Iya kukan bayyane sai na zuci babu abnd take Iya yi sai karatun Alkur'ani domin sallah ma babu damaryi dan tun ranar da feena tazo bata sake ganin kowa ba.

Yauma raira kira'arta take cikin suratu rahman cikin sanyin muryarta da ta sake raini da sanyi, kamar daga sama taji ruwa ya fara raguwa yana kasa sae gashi an bude glass din anshigo daya daga cikin wadanda suka kawotane ya shigo yana shan sigari.

Hannu yasa ya kunceta tsabar sanyin da kafarta tayi ta yanke jiki ta fadi kasa, hannu yasa ya damki gashin kanta ya dago da ita tare da hura mata hayaki ta fara tari hawaye na zubo mata.

Janta ya farayi ya kaita wani daki wannan da dan dama dama domin har da floor yayi jifa da ita ta fada da goshi har sae da ya fashe ta dan Saki kara.

ya juya ze fita tayi saurin cewa.

"duk abinda zakuyi mini kuyi mini amma dan girman Allah kubarni na dinga sallah."

Kallonta yayi da munanan idanuwansa yace.

"what are you saying?"

Cikin harshen turanci ta maimaita abinda ta fada.

"meye sallah? "

Ya tambayeta da turanci.

Goge kwallarta tayi tace.

"ni musulmace ku taimaka kudinga barina ina ganawa da ubangijina."

Karo na farko da ya fara tausayin wani dan Adam a rayuwrsa kallonta Yayi dakyau yaga yarda ta koma cikin sati tabbas feena azzalumar macece ko mai tayi mata har take kokarin rabata da rayuwarsa oho.

"me kina bukata?"

Ya fada cikin gwarin hausarsa.

"ruwa da mayafina."

Ba tare da yace mata Komai ba ya fice, ta dunkule waje daya tana sakin wani marayan kuka.





A firgice ya farka daga nannauyan barcin da ya daukeshi tun bayan sallahr asuba wanda rabonsa da yayishi tun kafin 6acewar hibba.

gama daya zufa ta gama rufeshi duk kuwa da AC n dakinshi, zaune ya Mike yana dafe kansa da sukayi masa wani irin nauyi, tabbas yau mafarkin da yayi da hibba yafi na ko yaushe daga masa hankali domin a yaune yaga zahirin wanda hibba ke kira a kullum idan yayi mafarkin tana neman taimako.

_mafarkin, wani kasurgumin dajine wanda yake cike da mugayen namin daji, hibba ce ke tsala gudu cikin wani irin hali bayanta wasu mutanene ke binta da wasu munanan makamai, sai gudu take tana ihu, daga bayan mutanen kuma anwar ne yana abin mutnen domin ya samu ya ceto hibbar, wani katon rami ta tafi zata fada anwar yayi wata irin kara tare da tsalle yasha gabanta, yana kokarin janyota wani farin haske daga cikin ramin ya fito da gudu hibba tayi gurin wannan haske tana ihu tare da kiran sunan *MAHIR* a hankali wannan haske ya fara washewa fuskar mahir ta bayyana dai dai za'a chakamata wuka yayi saurin tarewa wannan wuka ta sameshi, wani mahaukacin ihu hibba ta Saki tare da fadawa kan mahir itama wukar ta caketa_

Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un shine kawai abnd anwar ke fada domin ya jima yana wannan mafarke mafarken hibba da wannan haske sae yau ya tabbatar da waye wannan hasken, tabbas mahir shine mafaran komai a rayuwar hibba kuma shine hasken rayuwarta, domin mahir yafishi son hibba, wani irin zugi yaji zuciyarsa ta fara yayi sauri rike gefan kirjinsa tare da furta yah salama jini ya fara zuba daga hancinsa da bakinsa dasauri ya fara wani irin tari, kafin kace mai guda gudan jini sun fara zubowa, a daddafe ya mike yayi saurin shiga toilet tare da rufewa ya zura kansa jikin sink yana wani irin tari gwanin ban tausayi😭wayyo anwar dina.




6angaren mahir kuwa idan ba kyakkyawan sani kayi masa ba zeyi wuya ka iya ganeshi lokaci guda dan yarda yabi ya lalace ya rame sumarsa ta wani irin taruwa kamar mahaukaci ko aiki ya daina zuwa ya wani irin haske domin babu abnd yake iya ci sai ruwa kullum cikin kukan rashin hibba yake.


yau ya shirya zuwa yola domin ya gaji da karyar da yakewa mum kuma ta tabbatar masa matukar bezoba to ita zatazo shi kuma beson tazo taga feena bata gidan.

Airport driver ya kaishe.

Karfe biyar na yamma ya sauka a yola, drivern gdn su ne yazo daukarsa shima driver sosai yayi mamakin ganin yarda mahir din yazama sai dea be Iya cewa komai ba.

katon gidansu mai tsananin girma da kyau komai na gdn exotic suka shiga a parking lot suka tsaya kafin ya fito jikinsa duk a wani sake babu kwari, najwa kanwarsa dake aure a abuja tazo tana gidan, itace tsaye bakin mota da alama fita zatayi bin mahir tayi da kallo da dukkan alama bata ganeshiba can kuma tace.

"yah mahir?"

jiyowa yayi a hnkl yana kallo cute and fine sister din tashi Yayi wani irin murmushi wanda daga alama kasan na yakene, da gudu najwa tayi cikin gidan tana kwalla kiran mum!

Bedroom dinta ta isketa tana zuba kaya a wardrobe wata dankareriyar mata ce daga ganin kasan maman mahir ce tana sanye da wasu expensive Arabian gown.

"mum! Mum! "

Mum tace.

"ke najwa meye haka waike me yasa bakya girma ne? Kiyi gudu 'ya'yanki suyi meye hakan kike mini wannan kiran?"

"mum yah mahir fito kiga yarda ya koma kamar ma...."

Dasauri mum ta tureta tayi waje da sauri, a parlour suka hadu Mum ta kame tana kallon son din nata cike da tsoro da fargaba, hannayenta ta bude masa duka biyun tanajin wata kwalla na shirin zubo mata, da dan sassarfa ya karaso tare da fadawa jikinta ya hugging nata so tight, mum ji tayi zuciyarsa na wani irin bugawa ta dago dashi idanunta fal kwalla tace.

"son what's wrong with you? "

Zamewa Yayi tare da zama yana fadin.

"mum bani da lfy and I missed you so much."

Mum bata sake ce masa komai ba tace yaje yayi wanka yahuta suci abinci ba musu ya Mike ya nufi hadadden part dinsa na gidan.


Najwa ta zauna gefan mum tace.

"mum wllh yah mahir yana cikin damuwa ki duba fa kiga yarda ya koma kmr ba shiba duk kyau da kwalliya na yah mahir."

Mum tayi ajiyar zuciya tace.

"nasani najwa Allah ya kyauta kinfasa fitar ne?"

"mum ni ba inda zani."

Mikewa Mum tayi tana shigewa kitchen.




bayan sallahr isha mahir ya dawo part din Mum yana sanye da jallabiya a Danning ya sameta ita da najwa, sake gaisawa sukayi kafin najwa ta fara serving dinsu.

kowa ya fara cin abinci bandashi da ya zubawa flate din ido kawai yana juya spoon ko daya bai Kai bakinsa ba, lemo ya dan kur6a tare da mikewa, mum da tun dazu ke kallonsa tana karantar halin da yake ciki ta daure fuska tace.

"Kai ina zaka? "

"mum nakoshi."

"kakoshi da uban me? Me kaci da ka koshi."

"mum..."

Hannu ta daga masa fuska a daure tace.

"out! "

Ba musu ya dauki wayarsa yabar wajen ya nufi parlour, najwa ta yunkura zata Mike mum ta daka mata harara ta koma ta zauna, mum sai da ta gamacin abincinta kafin ta Mike ta shiga kitchen favorite food dinsa ta hada masa ta jero a tire ta nufo parlour kallon najwa kawai tayi ta Mike tabar parlon a center table ta ajiye sannan ta zauna gefansa.

Cheek nashi tayi dan kissing cikin sanyi murya tace.

"son I miss you"

"I missed you too love."

Keyarshi ta dan buga tana dariya tace.

"karya Kake."

"aw love zafi."

Gyara zama tayi sosai tace.

"love ka rame, kayi baki make damunka?"

Ta tambayeshi tana sakalo hannunshi.

"mum aiki ne."

"kowa kakewa wannan wahalar oho son kai ba d'a bare jika Amman your working your ass off."

Dariya ya danyi irin ta yake yace.

"mum idan bai da yara ba gakuba."

"yi mini shiru kasan sanin kanka babu mai bukatar kudinka cikin mu."

Cikin zolaya yace.

"but kinsan dea am richer than Abba."

Dariya Mum tayi tare da janyo flate ta zuba masa abincin with out wasting the time tace.

"oya haaa nayi feeding naka don da alama babu Vitamins a jikinka, anya kuwa son matarka na baka abinci."

Shafa kasan yayi yace.

"mum ina Abba ne."

"sai ynz ka Tuna dashi to be dawoba, haa nace ko? "

hannun mum ya dan ture tare da kwanto da kansa jikinta yace.

"mum ban iyaci wllh."

Ajiye spoon din tayi ta dan shafo kansa tace.

"son ka fadan damuwarka plz."

"mum....!"

"love why are you treating me like this? Ko dan ka san you are my only son? Kasan banson ganinka cikin damuwa, ko sae na sanar da Abban ka?"

"nop mum plz don't talk to abbah."

"okay what the problem? Ko Fina ce?"

Zaune ya Mike tare da kamo hannayenta biyu idanunsa na cicciko da hawaye yace.

"mum am mad in love with hibba......."

Ya kwashe komai dake tsaninsa da hibba ya sanar da ita har 6acewarta kuka yake sosai kamar karamin yaro, mum ta rungumeshi sosai ajikinta tana aikin rarrashi har ta samu ya lafafa, ta dagoshi tare da tsura masa ido sannan tace.

"ina matarka? "

"mum I don't know"

"okay tashi kaje ka kwanta..... "










Share
vote
comments














Oum AfafπŸ–€πŸ”₯
[10/11, 8:59 AM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*NI DA DR MAHIR*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*

_Follow me on instagram:_
*hapc20*






A gaggauce.... Nakusa fara exams plzπŸ˜“

*πŸ…Ώ 22*

A hankali ya mike ya nufi kofar fita, mum tabishi da kallo cike da tausayawa har ya bude kofa ta kira sunansa a hankali.

Chak ya tsaya tare da juyowa ya zuba mata shanyayyun idanuwansa tace.

"kayi kwanciyarka kayi barcin ka insha Allah damuwanka tazo karshe."

Gyada mata kai kawai yayi sannan ya fice, mum tafi awa guda zaune nan parlon ba tare da ta motsaba kawai ta tsunduma cikin tunani.


Washe gari.

Dakin da hibba ke ciki aka shigo wannan mutumin najiyane ya shigo rike da flate na abinci da gorar faro, jin shigowar mutun yasa ta dago tare da zuba masa idanu cike da tsoro da kyankyamin halittarsa, a gabanta ya ajiye flate din da ruwan, sannan ya jingina da bango yana kallonta chan yake.

"ga abinci na kawo maka, nasan da yunwa a tare da kai so oya eat before suzo su ganni ina baka abinci."

Hibba ta girgiza Kai hawaye na tarar mata tace.

"nafison kubarni nayi sallah fiye da komai, tunjiya nake rokanku kubani mayafina da ruwa na dinga sallah kunki, ko ita wadda tasa ku ajiyene bata fada muku ni Muslima bace."

Shiru mutumin yayi yana kallon yarda wonderful lips dinta ke motsawa.

A takaice yace.

"mekana bukata."

"mayafina."

Ba musu yasa kai ya fice bajimaba ya dawo da mayafin da suka daukota da shi ya bata, mikewa tayi da sauri ta amsa, sannan ta kalleshi tace.

"thank you sir plz kabani waje."

"kici abinci but."

Gyada masa kai kawai tayi,yana fita ta mike tare daukar gorar faro tana kaiwa bakinta ta fashe da kuka domin rabonta da ruwa tun ranar da aka kawota kuskure bakinta tari tare da daura alwala ruwan ta dauka ta fare goge kayanta da shi, ta yane kanta da gyalenta tare da tada kabbarar sallah, duk sallolin kanta da ake binta sae da tarama, ta dade a sujadar karshe kana kuka wiwi tana fadawa Allah ya fitar da ita daga wannan kangin masifar ta feena tare da rokon Allah ya cire mata son mahir dan har abada bata kaunar hada jinsi da abinda ya shafi feena, lallai yan uwa babu ibadar da tafi sallah dadi da falala, domin hibba jitayi kamar an sauke mata wani gungumeman dutse daga kanta wani sanyin dadi ne taji yana shigar ko wanne sako na mugudanar jininta, a sanyaye ta janyo flate din abincin gabanta ta fara ci ko loma biyu batayiba taji cikinta ya fara wani irin murdawa, tarike cikin tare da furta salati abu kamar wasa sae ta fara Ihu tana kiran sunan Allah tana kiran umma da baba, zubewa tayi nan kasa tana wani irin murkukususu kafin kace mai ta gama fita a hayyacinta, wani irin bakin a mai ta farayi kafin kace me ta zube bata numfashi innalillahi ko ta mutu ne.πŸƒπŸ»β€β™€πŸ˜‚



Mum tun safe take shirin hadawa mahir breakfast ta hana ko wacce mai'aiki shiga kitchen ma, tuwon alkama miyar busashshiyar ku6ewa da naman rago da busashshen kifi, ta hada masa da kunun tsamiya wanda aka hada da zallar tsamiya, tagama jera Komai a dinning tana kokarin shiga apartment dinta ya shigo sanye da joda trouser da polo riga duk da
[10/11, 8:59 AM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*NI DA DR MAHIR*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*

_Follow me on instagram:_
*hapc20*






_A gaggauce plz_


*πŸ…Ώ 23*

Tsaye kawai yayi yanajin dacin zuciyarsa na dade karuwa tare da ayyana hukuncin dazewa feena matukar ya tabbatar da hannunta a 6acewar hibbar sa.

Dago kanta tayi ta kalleshi da hawayen fuskarta a sanyaye tace.

"baby am sorry."

Gira daya ya dauke mata yace.

"unhm for?"

"for.... "

Hannu ya daga mata kafin ya ra6a ta kusa da ita ze wuce yana fadin.

"excuses me."

Da ido feena tabishi tana kallonsa zuciyarta na wani irin suya, da gudu tabar part dinsa ta nufi nata cikin bedroom dinta tashi tana sakin wani irin gujin kuka nan ta fara tarwatsa kayan shafen gaban mirror tana wani irin kuka wane mahaukaci komai Ta gani sae da ta fasa shi, cikin kukan take fadin.

"why mahir me yasa ka tsaneni? Meyasa baka kaunata kamar yarda nake maka why mahir menayi MA? Meyasa kafin son waccen sama Dani????"

Ta fada tana jifa da shoes rank dinta.

Ta zube nan tana cigaba da dikar kukanta.

A hankali mahir yabar bakin kofar ya koma parlour ya zauna yana sauke wata irin ajiyar zuciya Allah ya sani yana son feena amma kwata kwata halinta ne yasa gaba daya ta fice masa a rai.





β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’

6angaren hibba kuwa, gaba daya Sun nannadeta a cikin farin kyalle jira suke dare yayi suje su jefar da ita, a hankali ta fara motsi da kafarta, daya daga cikin yaran ne ya kula da haka yayi saurin mikewa tare da isa gabanta, yana kiran yan uwan nashi nan suka kwance ta fara wani irin tari, wani bakin tsimin maganin miciji suka mika mata tare da kafa mata a baki sbd azabar ishin da takeji ta fara wani irin kwankwada sae da ta shanye tas take fuskarta tayi wani irin baki wane gawayi ta fara wani irin tari ruwa suka bata tasha sannan ta kwanta nan kasan floor sai kuma barci ya dauke ta.(oh ni hibba kishigangeπŸ˜“)

Wayar feena suka kira domin sunar da ita da masifa ta dauki wayar sae dea dajin hibba ta farka yasata sassauta murya tace karsu aiwatar da komai sae tazo.


Da sauri ta Mike tare da saka gown ta dauki Jakarta da wayarta number Samuel ta kira tace ya sameta a hanya gata nan.

Tana fitowa parlonta ta gashi zaune ya daura kafa daya kan daya,dauke kanta tayi tare dayin hanyar fita.

da yake aci uwarta jin kai ko iskarta be kallaba har ta fice ranta na sake 6aci.


Tana fita ko takan driver batabiba taficewarta napep ta hau suka hadu da Samuel tashige mota suka kama hanyar mina.



sai cikin dare suka isa dajin da hibba take daga nesa ta umarci Samuel ya tsaya ta fito babu alamar wani tsoro a tare da ita haka tayi ta kutsawa ciki har ta isa gidan da hibba take, number su ta kira Allah yasa yau ba abige sukeba suka bude mata tashigo.

Dakin da hibba take tashiga a takure ta ganta tana barci hasken fitila mai haske ya haske dakin gaba daya, ganin yarda hibbar ta koma tayi da kyau kafin ta umarcesu bata ruwa mai sanyi suna kawo mata ta kwara hibba a firgice ta mike tana salati.

Hasken dakin yasa tayi saurin rufe idanunta sannan ta bude, feena tayi mata wani mugun kallo jikin hibba na rawa tana wani irin nishi ta fara mgn.

"idan kinayiwa Allah da manzon sa ki rufan asiri ki fitar dani daga nan nayi miki alkawarin...."

"quite hajia daman kinason fita daga nan?"

Ta fada a gadarance.

Muryar hibba na rawa tace.

"eh."

murmushin takaici feena tayi sannan tace.

"okay look at me, dubarni da kyau da haka nake?"

shiru hibba tayi tana kallon kumburarriyar fuskar feena da ko ba'afada maka ba kasan kukan da tayi bana wasa bane.

A fusace ta Mike tana shaketa cikin daga murya idanuwanta duk sunfito tana fadin.

"I said da haka nake? Hibba kin cuci kanki da kikayi garajen raba Nafisa dan baiwa da farincikinta, dubarni da kyau kece mutun ta farko da kika sani kukan da banta6ayin irinsa ba a rayuwa hibba me nayi miki zaki rasa mijin wadda zakiso sai nawa?"

Kuka hibba takeyi sosai sbd tsabar azabar shakar da feena tayi mata, sakinta feena tayi tare dajan baya ta zauna dirshan itama tana rusa nata kukan sosai wanda ya kusan fin na hibbar ma, hibba tsayawa tayi da nata kukan tana kallon yarda yar gayu kamar Dr feena ke kuka akan namiji Tab lallai rayuwarsu su duka tana tsakiyar teku.πŸ˜†

feena ta kuma takowa gabanta tare da kneeling down ta riko hannayenta cikin kuka tace.

"kinga nayi miki iri adalci da ban rabaki da rayuwarki ba koh? To zan rokeki ni kamar yarda zan fitar dake a yau na maidaki gaban iyayenki na rabaki da gidan nan har abada to na rokeki kifita sabagar mahir har abada ki fita a rayuwarsa ki shafe tarihin saninsa gaba daya a duniyarki, hibba zan baki kudin da zasu isheki har karshen rayuwarki matukar zakibar mahir."

"kobaki rokeni ba daman na jima da barin mahir har abada wllh nafita a rayuwarku ni dai dan Allah ki fitar dani anan ki mayar dani gida bana bukatar ko sisinki na rokeki."

Jijjiga kai feena tayi sannan ta Mike ta danyi taku daya sannan ta jiyo tare da harde hannayenta a kirjinta sannan tace.

"good yau zaki bar gidan nan bisa sharadin har abada kar mahir yasan cewa nice nayi sanadiyar 6acewarki sannan inaso kiyi pretending tsoron mahir ta yarda idan kingashi zaki dinga abu kamar hauka infac ma ki nuna ma baki sanshi ba idan bakiyi haka ba hibba hibba hibba wallahi kinsanni kinsan abinda zanyi wllhil azeem sae na kashe uwarki da ubanki a kuma gaban idanunki."

Gaban hibba ya tsananta mazari ita gaba daya rashin imanin feena tsoro yake bata.

"na amince da sharadinki."

Wani murmushi feena tayi sannan tace.

"good girl, yanzu za'a maidaki gidan ku."

Daga haka ta fice ita kuma hibba ta dunkule waje guda tana sake fashewa da wani sabon kukan.







β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’

Washe gari.

Da magriba, lokacin kowa ya shiga masallaci sallah yaran feena sukazo suka cillar da hibba a kofar gidansu.

baba tare da su yah Abbakar Sun fito daga masallaci kenan sukaga mutun kwance a kofar gidan touch light din waya rayyan ya kunna gabansa na dancing me zasu gani sae fuskar hibba da tayi wani irin bakikkirin.......









share
vote
comments







Oum Afaf
[10/11, 8:59 AM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*NI DA DR MAHIR*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*

_Follow me on instagram:_
*hapc20*




_wannan shafin nakune gaba d'aya manyan mata *haj suwaiba da haj amina* kune wanda kukaje kuka gaida manzo ya amsa nagaisheku har kasa na kuma gaidaku hajiya's yh rabb ya daukakaku ya cigabada da buda muku ya rayamuku zuri'arku...godiya Marar iyaka iyayen dakinaβ€πŸ˜†_



_A gaggauce plz_


*πŸ…Ώ 24*

A rude suka iso gabanta, ihun da rayyan ya fasane yajanyo hankalin su umma suka fito da sauri kafin kace me unguwa ta cika kowa ya fito masu kuka nayi masu jimamin rashin imanin da akayiwa hibba nayi, su yah mudan suka sata a mota aka nufi asibiti da ita, rayyan ya kira anwar ya sanar dashi anga hibba ynz hakama suna general hospital ba tare da ya 6ata dogon lkc ba shima ya kira mahir ya sanar dashi kusan a tare suka isa asibitin mahir hardashi aka shiga dakin da akebawa hibbar taimakon gaggawa domin samu aceto numfashinta.


Bayan kwana biyu.

Kwanan hibba daya ta farfado cikin hukuncin ubangiji, kuka tayi tayi ganin yarda iyayen nata suka koma da yan uwanta sakamakon 6acewarta, rayyan ne ya rungumeta sosai yana wani irin kukan tausayinta, ana haka mahir da anwar da CP suka shigo dakin, idanuwan hibba fes suka sauka cikin na mahir gabanta yayi wani muguwar faduwa wani sanyayyen murmushi ya sakar mata wanda yasa duk wani magudanar jini na jikin hibba ya amsa kokarin mayar masa da murmushin tayi sae ta tuna kalaman feena, _kiyi kokarin nuna baki sanshiba idan bakiyi haka ba hibba hibba hibba wallahi kinsanni kinsan abinda zanyi wllhil azeem sae na kashe uwarki da ubanki a gaban idanunki._

Dasauri hibba ta kalli umma da baba ta kuma kalli mahir da still yayi tsaye rungume da hannayensa yana kallonta wane ze cinyeta, wata irin kara hibba ta Saki tare da rukunkume rayyan tana cusa kanta cikin kirjinsa tana ihu kamar mahaukaciya.

Dasauri umma da baba sukayo kanta, mahir yayi saurin karasowa ze ta6ata sai kuma ya dunkule hannayensa, ihu take tana wani fizge fizge Umma ta rikota jikinta tana tofa mata addu'o'i, mahir yayi saurin danna kiran nurses sae gasu sunzo su biyu, ya kalli su umma gaba daya a rikice yace su fita, ae tanajin muryarsa ta kuma sakin wata karar tana kokarin bin su umma, tana nuna mahir da hannu idanunta rufe tana wani ihu.

Umma tace.

"hibba ta mene fada mini? "

"yafita tsoroooo."

Ta fada cikin wani irin ihu, jiki a mugun sanyaye ya fita yana kokarin danne hawayen dake shirin zubo masa, anwar yabi bayansa da kallo jikinsa a mugun sanyaye.

Baba yace.

"tor bude idanunki ya fita kiyi shiru."

a hankali ta fara bude idanunta tana waigewaige sae dea bata ganshiba wata ajiyar zuciya ta Saki, tana gyara wuyan rigarta anwar ya tsurawa kwayar idanunta ido babu abnd ke ciki sae zallar kaunar mahir amma kuma take nuna tsoronsa take kutmarπŸ˜†.

Cp ne ya fara mata yajiki shima anwar Yayi mata kamar ba ita ba tace.

"yah anwar ina granny?"

"tana gida tace a sake miki sannu kafin ta dawo."

Kai ta gyada masa kawai, anwar ya tashi ya fita da sauri tabi bayansa da kallo, cp kuma ya gyara maza sosai ya fara tmbyr hibbar game da 6acewarta kuka ta farayi sannan ta dage ta tikirkire ta zabga masa uban karya tace yan kidnapping ne suka kamasu sbd taki bada number gida yasa sukayi ta bata wahala rashin lfy ta fara yasa suka jefar da ita.

Tambayoyi cp yayi tayi mata tana lafta masa karya har ya gama sannan sukayi Sallama da su umma ya fita.


Mahir kuwa yana fita ya shige motarsa cikin wani irin dacin zuciya jiyake kmr zuciyarsa ta faso kirjinsa tsabar wani irin suya da turirin da take, ko takan anwar dake kwala masa kira bebiba ya shige Motarsa tare da barin harabar asibitin a guje.


Bayan sati guda.

Jikin hibba alhmdllh yayi sauki sosai sai dea ba'ayi discharge dinta

Please Login or Register in order to submit comment