Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafin kamshinsa ya kuma gauraye gurin ahnkl ya fito ta wata kofa hannunsa rike laptop dinsa ta companyn apple, sanye yake da wata arniyar amecian suit dark ash yasaka red T-shirt da red cover shoe hatta da apple watch nashi red ne fuskar nan ta kara kyau da kyalli kyakkyawar kasumbarshi Mai yalwa ta sake wani baki ga gashin kansa dake kyalli anyi masa style mai tozo daga sama abin burgewa, fuskarsa dauke da fresh smile ya Zauna tare da sallama.

Daga mazan har matan babu Wanda be tafi da a tension dinsa ba har masu aure, hibba da tayi niyyar yi masa kallo daya sai gata ta tsinci kanta da kasa dai na kallonsa.

cikin sahihin turanci Wanda kanaji kasan meyi yana da kyakkyawar alaka da turawa domin turancin da yake ko wani baturan albarka, jawabi yayi sosai tare da jan hankalinsu akan muhimmacin aikinsu na kar6ar haihuwa sannan ya gargadesu sosai akan Mai da hnkl da zuwa da wuri sannan da kula da mararsa lfy sosai yarda ya kamata, daga nan ya bada dama idan da akwai mai shawara ko wani korafi yayi mgn.

Kowa kasa mgn yayi sbd tsabagen kwarjini da haiba ta Dr Mahir, cikin nutsuwa da karfin gwiwa duk da gaban na tsananta bugu ta Mike, kallo gaba daya ya koma kanta dago da kansa yayi ya kalleta da kyau idanuwansa kan hip dinta dake bayyane sosai cikin wandonta, Allah yayi shi mutun Mai tsananin son mace hip, gyara zaman glass nata tayi da kyau kafin ta fara mgn cikin zazzakar muryarta.

Korafe korafen rashin wadatattun kayan amsar haihuwa ta fara bayarta tare da rokon a gyara masu office dinsu tare da bukatar gadaje da while chair mararsa lfy, nan fa kowa ya fara kuskus domin kusan abnd ke ran kowa, nan ta Kara da cewa ajawa doctors nasu kunne domin wata haihuwar tafi karfinsu dole sai da likita amma basa samun goyan baya, nan ma tafi aka sa daga karshe tayi addu'a da godia ga CMD cikin nutsuwa ta zauna gaba daya aka saka mata tafi don tayi mgnr dake zuciyar kowa, sosai ta burgeshi da haka aka tashi daga taron shi ya fara fita tare da radawa PRO dinsa Wata mgn a kunne ya shige.

Ita da rashida ne karshen fita har sunje bakin kofa, pro yace,

"hello maah."

"hy"

"doctor yace ki same shi a office now. "

Kallon rashida tayi itama rashida ita din take kallo cikin rawar murya tace.

"nashiga uku rashida me nayi."

Dariya rashida ta fashe da ita tare da dan bugun kafadarta tace.

"see you, ke me isa kika fiye tsoron tsiya ga yarda kika wani hargitse Kamar wadda ze Kama."

"amma sstr kinsan halin matar shifa kartazo ta...."

"mtsww dillah forget wannan stubborn din kije kiran oganki."

jiki a sanyaye suka fita tare da nufar office din marairaice face tayi sannan tace.

"Dan Allah sstr ki rakani."

"wa wannan fadan ba nawa bane naku ne na Manya."

Ta fada tana dariya, harara ta 6alla mata tare da tura kofar a hnkl cike da nutsuwa.......






Vote
share
comments






Oum AfafπŸ–€πŸ”₯
(Mrs doctor Ahmad)
[9/22, 2:34 PM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*HIBBATULLLAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*


_this is for urs my luvly monitors...bilkisu garkuwa nd her frnd rookie❀❀tnk for everything yh rabb yabar kauna da aminci na har abada my dearest🀝🏻❀_


*DEDICATED TO*
Maryam Obam❀


*πŸ…Ώ 4*

A hankali ta murd'a k'ofar ta shiga kanta a k'asa, tare da furta sallama cikin sanyin murya.

Yana rataye coat dinsa ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba har ya zauna, kansa akan wayarsa da ake kira ya daga tare da zama yana kafeta da ido ganin yarda jikinta ke Dan rawa daga gani kasan a takure take da kallon da yake mata.

Kwas kwas kake jin karar takalmi tare da sautin muryarta cikin fada tana bala'i, gaban hibba ya yanke ya fadi jikinta ya hau rawa idanuwanta suka fara ciccikowa da hawaye tare da waresu kan kofar shigowa, shi kuwa ko ajikinsa relaxing yayi kan kujerarsa yana cigaba da wayarsa da mum dinsa cikin kwanciyar hankali, bata gama shiga tashin hankali ba sai da tajita daf kofar tana kokarin shigo, da gudu tayi wani tsalle sai gata bayan Dr mahir hawayenta na kuma kwaranya wane an bude famfo,cikin muryar kuka ta zuro kanta kan shoulder dinsa tare da fadin.

"Dr plz help me ur wife..."

Mgnr ce ta rike lkcn da ta bude kofar still kanajin muryarta tana zazzaga bala'i sai da ta tsaya chak ba tare da ta shigo ba.

Da karfi ta rintse idanuwanta wani fitsarin wahala na cika mata Mara, gaba daya baya tunaninsa baya jikinsa coz yarda tayi masa mgnr sosai ya haifar Masa da wata irin kasala.

Kokarin tattaro nutsuwarsa yayi tare da nuna mata wata kofa dake gefe da gudu ta mike ta shige dai dai shigowar madam......



*******

"dole ne hibbatullah ta dawo gidan nan kuma ta fito da mijin aure domin nagaji Da surutun mutanen unguwa ace mu zubawa yarinya idanu sai abinda taga dama zatayi, to kinji abinda na fada miki dai ki kiraro ramlatun lallai lallai yau ko gobe ta dawo gidan nan lada ya isa haka."

Daga haka ya gyara babbar rigarsa ya fice, umma dake tsaye tayi ajiyar zuciya sannan tabi bayansa da kallo, tafi 10 minutes tsaye gurin kafin taja kafa ta shige cikin bedroom dinta.




*****

Wani kallo take bin kofar da hibba ta shiga kafin ta Kalli mahir da ko inda take be kallaba idanuwansa lumshe, kofar ta nufa da niyyar shiga cikin isa mahir yace.

"stop! "

Ko ta kansa batabi ba ta cigaba da takawa gabanta na wani faduwar da tunda take bata ta6a jin irinta ba.

Cikin karaji da daka tsawa ya kuma cewa.

"stop mana!!! "

Juyowa tayi a hargitse tare dayi masa wani irin kallo mai dauke da ma'anoni iri iri cikin nuna isa tace.

"me kake 6oyewa."

"kina tunanin akwai abinda zan 6oyene."

"tunda muke da kai ka hanani shiga...."

Maganarce ta tsaya chak lkc kiran waya ya shigo wayarta, kallonsa tayi a shekeke tare da yin kwafa tafice tana receiving call din.

Kusan lkc daya suka sauke ajiyar zuciya shida hibba, da sauri yazo yasawa kofar key sannan ya shiga dakin da hibba ta shiga, tana tsaye tsakiyar dakin duk da sanyin dakin amma ita gaba daya ta gama jikewa kamar wadda tayi wanka da ruwa, idanuwan nan nata kamar su fado sbd firgici, tsaye yayi tare da jingina jikin door din ya harde hannayensa a kirjinsa, yana kallonta, shi dariya ma ta bashi yayi dan murmushi sannan yace.

"na dauka ke jaruma ce."

shiru tayi batare da tace masa komai ba, a hnkl yake takowa ganin yana nufosa yasa ta faraja da baya tare da sake fiffito da idanu, duk da haka tun karota yake cikin rashin sa'a tayi tuntu6e da jikin flat bed en dakin, luuu tayi zata fadi yayi saurin tallafo bayanta ta fado jikinsa, har kirjinsa da nata na haduwa, wani mugun electric shock sukaji musamman ita da wannan ne karonta na farko da hada jiki da wani namijin da ba muharraminta ba.
Kallon junansu suke eyeballs to eyeballs ko wanne bugun zuciyarsa na dadduwa, ita ta fara janye jikinta ganin tana kokarin rasa control dinta .

Waskewa yayi tare da fadin.

"ki dinga kula."

"tohm. "

Tace a hnkl.

"ta fita ita dodon naki zaki iya fitowa ki tafi and... "

Sai kuma yayi shiru yana ficewa daga dakin.

Wata ajiyar zuciyar ta saki sannan ta nufi dressing mirror ta tsuwa kanta ido na yan sakanni ganin duk yarda ta hargitse murmushi ta danyi kafin ta furta.

"matarce bata da M yau da ta kamani tab."

Ta fada tana dariya, handkerchief ta ciro a Jakarta tare da goge fuskarta, ta dan gyara hijjab dinta tare da mayar da glass dinta, ta dubi fuskarta sosai taga tayi kafin ta fito a hnkl.

Bai dago daga aikin da yake a laptop dinsa va taji yace.

"kingama kwalliyar."

Ido ta dan zaro tare da rike baki tace.

"kwalliya kuma, ni ba kwalliya nayi ba."

shiru yayi mata Kafin tace.

"can I go?"

"yes."

Ya fada a takaice, dan rissinawa tayi tace thank u sir.

Daga hka ta kama hanya zata fita yabi bayanta da kallo ganin yarda tana tafiya hips nata yana motsawa yasan kuma maza da dama sun ganta a haka a gadarance yace.

"ki kara girman hijjab din jikinki yayi kadan ko dan Kare darajar kanki."

Daga hka ya Mike yabar wajen ransa a 6ace....

Ido tabishi da shi kafin tace.

"oh ni yasu ko ina ruwansa oho"

Nima dea nace oho kuma kuce oho🀣🀣🀣🀣










vote
share
comments






Oum Afaf
(Mrs Doctor)✍🏻
[9/22, 2:36 PM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITE'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*HIBBATULLAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*



*_Nagodai sosai da sharhinku tare da kulawa yh rabb ya tabbatar da farinciki a rayuwarmu gaba daya🀝🏻🀝🏻❀❀_*


*DEDICATED TO*
Maryam Obam❀



*πŸ…Ώ 5*

Department dinsu ta koma zuciyarta cike da tarin tambayoyi game da Dr mahir gashi dai turawa yayi ayi kiranta amma ita bataga abinda yace mata ba sai ma kusan janyo mata da yayi ta rasa aikinta ga wani irin mayataccen kallo da ta lura yanabinta hip dinta da shi har da wani cewa ta kara tsayi hijjab dinta.

"babu a house shi isa."

Ta fada a fili tare da jan siririn tsaki.

Direct labour room tashige ba tare da ta koma office dinsu ba dan tasan tana shiga munafincin tmby ma ta isheta.



Kan doguwar sofa ya zauna tare da dafe Kansan da hannayensa biyu, amon muryarta ce kawai ke masa yawo a ka tare da gizon Mayan masakanta, iska mai karfi ya fuzgar tare da furta.

"what's wrong with me ne?"

Tsaye ya Mike tare da zarya cikin dakin, yinin ranar babu wani aiki da yayi har lkcn sallah yayi...



2:30pm

Lokacin hibba tare da ramla suka fito daga ciKin asibitin, suna tsaye bakin titi suna jiran mai napep ramla tace.

"kawa ban baki labari ba."

"bani nasha Allah yasa alkhairi ne."

Dai dai suka samu adai daitan suka shiga hibba tace.

"labarin me zaki bani."

"nafasa ai nasan koda na fada miki bazaki wani dauki abin serious ba,wai dazu ya kukayi da CMD ne?"

"dadina dake fa kenan ramla dan Allah ki fadan make going kibar mgnr CMD din nan mgnr dai da muka tattauna a meeting ce akan abubuwan da nafada."

"kinji dashi dai wannan halin naki hibba sae ke ynz nima bazaki iya fadan sirrinki ba, ai shikkenan mu dae muna murna bama cikin yan..."

"haba sis ramla wannan wata irin mgn kike kinsan dai bazanyi miki karya ba wllh tallahi babu mgnr da mukayi."

"toh yayi kyau hibbatullah."

Dariya hibba tayi tare da cewa.

"fadan labarin mana."

Dan gyara zama ramla tayi ramla irin manyan matan nan ne tana da kiba sosai kuma bata da tsayi sai taimakon takalmi, kawar hibba ce tun a school of nursing sai dai ta girmi hibba sosai domin zatayi 31yrs kuma itama budurwace tana da fada sosai gashi bata da hkr duk Wanda yayi mata sai tayi masa sae dai sam bata shiga sabgar mutum bare kayi mata taki kyaleka, jininta ya hadu da hibba sosai.

"wllh kawata wani sabon malami ne yazo Kano tundaga Niger jiya jiya ina fada miki yah ladi take fesan itama a asibitinsu taji ana mgnr sa ai hibba ina ganin lokacin dagawarmu yayi dan kinsan Allah yah ladi tace aikinsa kamar yankan wuka sha ynz magani yanzu."

"ohh kawata kawata wai dan Allah har sai yaushe zaku daina wahalar da kanku da asarar kudinku wajen wadannan kaskantun bayin wadanda wata kila kafisu daraja da matsayi a wajen ubangiji, ramla karfa ki manta cewa wadannan malaman shirka suke dan duk Wanda ze buga kasa yace ma ga abinda ze faru gobe mishirikine dan babu wanda yasan gaibu sai Allah, sstr na karki manta komai fa lokacine da aure da mutuwa duk da lokacinsu, wllh Allah ramla duk saurinmu sai munjira Allah, yayi ikonsa, ramla a kullum ina guje miki harka da wadannan bokayen."

"ahh hibba wllh ba bokaye bane."

"to menE idan ba bokaye ba ai duk wanda ze shiga lamarinka da ubangiji to bokane mushiriki ne, kuma wllh kudinku kawai sukeji dan basa wani aiki sae dea kuyi ta wahala kuna ciyar da katon banza, ramla ubangiji fa yace mu rokeki ze amsa mana me yasa bazamu tashi cikin dare mu daga hannayenmu sama muyi masa kuka tare da kirari mu rokeshi duk wata bukatarmu tabbas idan muka rokeshi ze amsa mana."

*"HIBBATULLAH* Allah yasa da alkhairi."

"haka zakice kenan?"

"to ya zance ustaziya, ke har kullum bakya ganewa ne amma zaki gane idan shekarunki suka kuma ja."

"bana rokan kowa sai Allah kuma insha allahu bazan ta6a rokan wani bayanshi ba, ramla zuwa wajen wani biyan bukata kamar fa kana kaiwa wannan mutumin karar ubangi..."

"ke hibba karkiyi mini sharri kuma ahh karki shiga tsakanina da ubangiji na."

Ta fada cikin fada.

"ba haka nake nufi ba ramla ina....."

Ringtone din wayarta ne ya katse mata mgn lalubar wayar dake jaka tayi tare da cirota Samsung s7 ce zabgegiya golden color mai kyau murmushi tayi tare da receiving wayar tace.

"assalamu alaikum ummata."

Shiru tayi kafin ta danyi dariya tace.

"haba ummana jiya ne kawai bankiraki ba kuma shima wllh babu kudi a wayar tawa ne."

Jim ta kumayi tana sauraron wayar kafin ta zaro ido ta dafe kirji tace.

"umma yau kuma amma..."

Katseta akayi daga daya 6angaren umma can Kuma ta sauke ajiyar zuciya tana son mayar da kwallar idonta tace.

"shikkenan umma gani nan insha Allah."

Daga hka ta datse kiran kallota ramla tayi kafin tace.

"sakon baba koh? "

Gyada mata kai kawai tayi fuskarta cike da damuwa.

"ramla tace you see ynz sae ki koma kiji dame yazo kuma ki yarda muje gurin mutumin nan ya dan baki taimako kinki, dubarki ke ba wata mum
munar halitta gareki ba hasalima a ynz dae dakyar a samu mace mai kyan surarki da fuskarki, amma gashi babu ko Karen da ya ta6a shinshinaki sai dai yan iska gasu nan bila adadin duk bana auren, kizo muje muga me zece danni wllh ina zargin imma asiri akayi miki ko bakin aljani gareki mai hana aure."

Shiru hibba tayi ba tare da ta kuma ce mata uffan ba ramla duk ta dauka nazarin mgnrta take sai ta dafota tare da sake tausasa murya tace.

"wllh tallahi hibba yarda nake kaunar naganki a dakin mijinki koni kaina banayiwa kai na ki daure muje wajen malamin nan ya dubaki da kyau idan ma wani mugun abune ayi sauri samo mufita ni na yarda da kudina ma zan biyashi sadaka."

"kibarshi idan har tanice wllh idan zan dawwama babu aure ramla bazanje wajen wani yayi mini abinda Allah beyi mini ba kuma ramla nasan kina kaunata kuma ngd sosai amma bAzani wajen kowa ba."

Baki sake ramla ke kallon ta kafin ta ta6e baki hadi da jijjiga kai tace.

"eh lallai gsky hibba da ace a zamani farko kikazo dakyar zaki karfi kalimatush shahada taurin kanki yayi yawa."

Shiru kawai tayi mata kafin tacewa mai napep din malam in kasamu waje saukeni anan na fasa zuwa jambulo din goron dutse zani."

Tsayawa yayi ta sauka tare da dauko 500 tace

"dauki kudinka har da na kawata."

"da kinbari na biya da chaji a wajena "

Cewar ramla, Mai napep ya bata canji ta kar6a kafin sukayi sallama sama sama.

gaba daya bata cikin nutsuwarta dan tunda taji kira daga baba to abun fa babu easy tana kokarin tsallaka titi wata dankareriyar end of discussion Fara tazo tayi sama da ita.....





πŸ˜³πŸ˜³πŸ˜³πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€



.
share
VotE
comments









Oum AfafπŸ–€πŸ”₯
(Mrs Doctor Ahmad) ✍🏻
[9/22, 2:37 PM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*HIBBATULLAH*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*



*Attention❗❗❗ plz jiya nayi musket sosai wajen rubuta sunan kawar hibba wato rashida nayi ta sa mata ramla, sai da yar uwa ruky apple tayi mini mgn sannan na kula...ramla itace yayar hibba rashida kuma kawarta fatan kungane...*

*πŸ…Ώ 6*

Kiiiii kakeji aja wani mugun robust nan take mutanen gurin akayo kan motar dauke da salatin, wani mutum ya fito daga motar sanye da bakar coat hankali a tashe yana fadin.

"innalillahi WA'inna ilaihir'raji'un."

Ya tsugunna gaban hibba dake kwance cikin jini bata koda numfashi, mutanen gurin kowa ya dauka ta mutu, da sauri mutumin ya sungumeta yayi mota da ita zuwa lokacin kuka yake sosai wane karamin yaro yana furta "innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un allahuma ajirni fil'musibatie wakhlif'ni khairan minna."

Jakarta da ta tarwatse gefe wani mutumi ya tattaro mata sai wayarta da ta rotse tayi filla filla, mutane biyu ne suka shiga motar suka tafi asibiti tun a motar mutumin ya kira headquarter din yan sanda dake hotoro yace a tura masa police asibitin standal ya taho da emergency accident.

Cikin yan mintoci suka karasa asibitin gadon tura mararsa lfy aka sakata tare da turata cikin sauri akayi emergency room da ita.

Duk wani cikecike da ya kamata barrister anwar yayi, likitoci sun fara kokarin ceto numfashinta domin suman da tayi sai kuma ciwukan da taji tare da kara guda a kafarta.

Har lokacin Barr anwar baya cikin nutsuwa fatansa kawai Allah yasa beyi kisan kai ba....



Tunda ya koma gida yakejinsa wani iri gabansa na wani irin faduwa damuwa da fargaba duk sun dameshi yanajin kamar wani abu na faruwa dashi ko yana shirin faruwa da shi dan shi bae ma ta6a shiga situation irin wannan ba tunda yake.

Sake relax yayi akan flat bed din dake gefan swimming pool din gida, daga shi sae boxer sae farar singlet farar fatar jikinsa sae wani glowing take ga wani kwantaccen gashi mai matukar kyau ajikinsa, idanuwansa a lumshe yana karanto duk wata addu'a da tazo bakinsa amma still bugun heartbeat dinsa daduwa yake.

Wayarsa ya janyo tare da danno number mum nashi da akayi saving da my happiness yayi calling bugu biyu mum ta dauka tare da fadin.

"happiness how are you?"

"not fine happiness."

Ya fada in baby voice.

"yah salam! What happen to you baby."

"my heartbeat."

Ya fada murya a raunane, hankalin mum ya kuma tashi cikin harshen filatanci domin sometimes dashi takewa yaran nata mgn tun suna yara tace.

"me yake damun zuciyar taka baka da lfy ne? Ko dai matarka tayi ma wani Abu? "

"no mum just inajin zuciyana na bugawa gabana na faduwa like something is wrong."

kasa tayi da murya cikin kwantar da hankali tace.

"ayyah sorry happiness insha Allah babu abinda ze faru sai alkhairi daman haka rayuwar take watarana dadi wataran akasani haka kayi ta kiran sunan Allah kanayiwa annabi salati zakaji relief kaji."

"but mum bugun fa yayi yawa and... "

"haba only son my one and only babu abinda ze faru sai khair kaji, kaga duk muna lfy ni dad and ur sstrs so calm down babu abinda ze faru kaji habibi ko dai kanason ganin mum dinka ne yanzu ka ganni a Kano."

dan murmushi yayi tare da karajin kaunar mum din sosai da sosai yace.

"yes mum domin already miss you."

"don't worry dear ina tare da kai a duk inda kake kuma ina maka Addu'a."

"thank you I luv...."

Fizge wayar tayi da karfi tana daka masa wata irin harara idanuwanta gaba daya sun kada sunyi jazir, tun dazu take tsaye kansa.

"ke bani wayata mana kina hauka ina waya da happiness din zaki fuzge."

"na fuzge din happiness din banza happiness din ho...."

Tas tas ya dauketa da maruka guda biyu Karo na farko a rayuwarsa da ya ta6a Marar wani, ko da kuwa kanwarsa najwa danshi mutun mai Marar fada.

"first and last zaki kara fizge waya A hannuna koda kuwa bada mum nake mgn ba idiot."

Daga haka ya fizge wayarsa tare da tureta gefe saura kiris ta fada pool din tayi saurin rike karfe, shi kuwa ransa a matukar 6ace ya shigewarsa ciki ba tare ma da ya kashe wayar da mum ba kuma duk abnd suke tana jinsu......




Duk suna tsatstsaye a tsakar gidan, unty ramla da baba da umma yah mudan da yah bappaliya sai kaninsu rayyan, duk suna tsaye tun dazu suke faman kiran wayarta a rufe.

unty ramla tayi ajiyar zuciya tare da fadin.

"hibba bata ta6ayin irin haka ba tatafi wani waje ba tare da ta sanar dani ba ko abban Yasir ina balle har ta kashe waya."

Rashida ce tashigo cikin gidan hankali tashe tayi sallama tare da fadin.

"har ynz ba'a samu nmbr tata ba koh? Ni wllh tun dazu muka rabu yh rabb yasa lfy dae."

"amin."

Yah mudan ya fada.

Baba yace.

"wannan wane irin abune haka ace yarinya ta raina kowa ynz karfe nawa, duba 5 na yamma."

Kowa shiru yayi cike da jimami.



A hankali ta farka idanuwanta da sukayi mata nauyi wani irin ciwo kanta yake, duk jikinta ciwo yake ga kafarta dake matukar azaba domin ba'ayi daurin ba sbd kafar akwai ciwo ajiki sai ya warke.

Ido ta rintse da karfi duk abinda ya faru ya dawo mata, sake bude idonta Tayi a hankali tana saukesu a kansa, kallo daya tayi masa tare da rintse ido cike da azabar ciwon kai cikin rawar murya yace.

"sannu baiwar Allah, Dan Allah kiyi hakuri wllh ban kula da shigowarki hanya ba dan Allah ki yafe mini."

Cikin rawar murya tace.

"kai na."

Dasauri ya fita daga dakin yana fadin."

"let's me col d doctor."

daga haka ya fice da sauri, doctor ya kira tazo ta dubata tare da yi mata allura.










share
vote
comments









Oum AfafπŸ–€πŸ”₯
(Mrs doctor)✍🏻
[9/22, 2:39 PM] Ummee Garkuwa: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*NI DA DR MAHIR*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*



*_Attention plz❗❗❗wannan littafi Mai suna hibbatullah ya tashi daga haka ya koma ni da dr mahir sakamakon sunan da yayi daya dana wani littafin wanda shima ynz ake kan rubutashi....ngd_*





*πŸ…Ώ 7*

Wayarta da wannan mutumin ya bashi ya dauko yaga yarda screen din ya lalace wayarma bazata kama ba gaba daya, sim card din ya zare shima ya cire nasa wanda yake kan iPhone 7+ dinsa yasaka mata sim dinta a ciki shi Kuma yasa nashi a karamar wayarsa, kunna wayar yayi ya fara bin contact dinta ko ze sami nmbr wani nata yasanar masa sbd dare da ya farayi.

Number yaga anyi saving da babana, sae da ya kalleta yaga har ynz barci take cikin ransa yana zuzzuta tsabagen kyawun tsarin halittar da rabbana yayi mata amma gashi ya zamo sanadin yi mata tabo, a hnkl ya furta. "am sorry angel."

Number baba ya saka a wayarsa tare da dialing nmbr amma sai yajita a rufe, dafe kansa yayi ya cigaba da bin contact din har yaga number ummana yayi saurin daukar number tare da kiranta cikin sa'a ta shiga sai dai har ta tsinke bata daga ba sai da yayi mata 5 missed calls sannan aka daga muryar rayyan a hnkl yayi sallama.

"Dan Allah Mai wayar nake nema."

"batajin dadi ne bazata iya mgn ba ynz."

"ayyah, daman na dauki number ne a wayar wata baiwar Allah wadda na kad'e d'azu akan titin goron dutse."

Dasauri rayyan yace.

"yh salam! Unty hibba innalillahi WA'inna ilaihir'raji'un, wllh unty hibban muce yanzu kuna ina? Ina unty hib...."

Umma ce ta fizgi wayar da sauri jikinta har rawa yake tace.

"bawan Allah yanzu ina hibbatullah din mai ya sameta yh rabb yasa bataji ciwo ba? Taimaka ka bani ita muyi magana."

Sai kuma ta fashe da kuka tana fadin.

"Allah sarki hibbatullah malan anga hibba."

Baba da shigowarsu kenan shi da su yh mudan Sun dawo daga police station ya kar6i wayar da sauri tare da yin sallam.

Barr anwar jin muryar babban mutum yasa yace.

"barka da dare. "

Bai amsa masa ba ya katseshi da cewa.

"ina ita hibbatullah din? Me yasameta?"

"gata nan tana barci muna standal hospital nan hotoro, jikin nata da sauki yanzu shi isa na kira na sanar daku ko za'a turo mai kwana da ita dan jikin nata babu damar sallama sbd alluran da akayi mata."

"tohm shikkenan Allah ya bata lfy ya tsare gaba gamu nan zuwa yanzu insha Allahu."

kashe kiran yayi tare da duba missed calls na wayarsa yaga an kirkirashi da dama ciki har da granny dinsa wadda ta kira sama da sau ashirin ita ya fara dannawa kira yana dariya.

dasauri ta daga daman wayar na hannunta tace.

"yanzu me sunan Manya abinda kayi ka kyauta tun safe kasa kafarka kabar gidan nan dan kaniyarka baka waiwayeshi ba gashi ko maganinka baka shaba gidan ubanwa Ka tsaya?"

Cike da tsokana yace.

"oh granny na manta fa Ashe ban sanar miki ba, tafiyace ta sake kamani dazu bashiri zuwa Abuja yanzu hakama kin ganni a kwance."

"Abuja dan kaniyarka yaushe ka dawo ma da har zaka sake komawa toh yasin maza ka tattaro ynz ka dawo gida tunkafin naci mutuncinka. "

Yar dariya yayi tare da cewa.

"ahh lallai Ashe dagaske ana mijin dani to kwantar da hnkln ki matas,ina asibiti tun rana wllh."

"asibiti kuma? Na shiga uku ni salamatu badai jikin bane?"

"nop granny kalau nake, dazu a hanyata ta dawowa tsotsayi yasa na ka...."

A gigice ta katseshi da fadin.

"ka kashewa? Kana

Please Login or Register in order to submit comment