Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

halin feena koma meye ita ta janyowa kanta da ta za6i jefa kanta halaka akan namiji shikkenan kasani wllh Allah sae ya sakawa mata mugu azzalumi."

daga haka ta datse wayar yanajin yarda take kuka sosae kmr ranta ze fita, tab gsky tsakani uwa da yaranya sae Allah tabbas mummy na tsananin kaunar feena mace mai izza ta takama hadi da jin kan tsiya itace take kuka yau kamar haka tab Allah sarki ya fada a hnkl, tabbas yana son feena a da amma rashin kula da ja ajiki yasa kwata kwata bae shaku da ita sosai ba, mugayen abubuwan da ta dinga kullawa da rashin ganin darajar sa dana iyayensa dama na aureta shine babban abnd yasa yaji baya jinta a ransa a ynz, dole ze rubuta mata takaddar saki domin baze Iya zama da ita ba.......



Yanzu hibba zuba idanu take taga ta yarda labour zezo mata sbd tana watan haihuwanta ya shiga idan kaga hibba sae ka kusan tuntsura sbd da dariya amcy kinga dae kyau irin na ruky apple ko🤣🤣sannan kinga yarda ta koma da cikin suhail tor wolah tayi kyau akan yarda hibba ta koma🤣🤣🤣lol duk wanda beson ruky ba PC me.

wasu irin pimples ne suka fito mata ga hancinta da yayi fakadede idan suna video call da fam dinta hka zasuyi ta mata dariya, umma ce kawai me fadar kyanta sae kuma mum dan hatta da mahir din shima tsiya yake mata.

Daman duk weekend din duniya yana hanyar yola mum da Abba har mamakinsa suke domin da sukayin wata biyu daya basu gashinba amma ynz kuwa kullum yana tafe. Haka ze saka hibba agaba yayi ta tuntsura mata dariya at the same times kuma ze tsugunna ne har kasa yace gwaggo ina wuni sannu haka ze sata agaba wataran sae yaga tana shirin kuka sanne ze kyaleta ya shiga kuma rarrashinta.

Wata kwararriyar likita Mahir ya daukowa hibba daga Abuja irin baturiyace amma a Nigeria take zaune tasan aikinta sosae tana bawa hibba kula sosae domin har motsa jiki na masu haihuwa take saka ta, a ynz hibba a fusace take kullum domin cikin kwanakin nan kullum karajin nauyin cikin take ji take kmr ta yadashi ta huta, tun ranar Friday mahir yazo gashi yau har Monday be tafiba da mum tace meyasa bae tafiba sae cewa yayi baze tafiba har sae hibba ta haihu mum tace masa itafa haihuwa ba'a jiranta amma yayi fur yaki tafiya mum ta cika sosae da mamakin rashin kunyar mahir amma da ta tuna ynz abokanayensa da suka tashi tare ko wanne yana nan da yaransa sae ta share shi kawai.



Thursday

Hibba tana zaune kasan carpet bayan ta iddar da sallahr magriba, ta Mike kafafuwanta da suka dan kumbura kadan, mahir ya bude kofa ya shigo kallon sa tayi tare da dauke kanta cos yarda takejin haushin sa Allah ne kade ya sani, dan idan taga yarda yake sake kara kyau yana wani daukar gayu ita kuma ta kallin condition din da yasata sae ta kumajin wani kululun bakinciki, murmushi ya danyi tare da zama a kusa da ita yace.

"luv yakike? "

"lafiya."

Ta fada a takaice tana hararar sa ta gefan idanunta, wani kasaitaccen murmushi ya sakeyi wanda har sae da kyakkyawan dimples dinsa ya bayyana yace.

"habebbty nayi wani laifi ne?"

Ba tare da ta kalleshi ba tace.

"wane yace kayi wani laifi?"

"naga tunda nazo kikejin haushina gashi yau kusan Satina guda kin hanani hakkina ma."

wata irin harara ta daka masa kmr idanuwanta zasu fado tace.

"aikin kenan kullum baka da magana sae ta hakkinka, ni baka ganin halin da nake ciki tsakanin rayuwa ko mutuwa duba kaga yarda na koma kmr wata uwar mata tashi dakyar zama dakyar ni gaskiya am tired nagaji da wannan cikin."

Ta fada tana fashewa da kuka, hannunta ya kama tare da manna masu kiss cikin tausayawa yace.

"sannu dear sorry luv kin kusa hutawa insha Allahu ko wacce uwa haka ta sha fama, km kinsan aski idan yazo gaban goshi yafi zafi kiyi hkr kinji sannu."

Wata hararar ta sake 6alla mashi cike da tsiwa tace.

"ni banason sannun nan."

Dariya ya danyi yace.

"toh me kikeso fada mini."

"ni banason komai kawai nagaji."

"Bari na hada miki ruwan wanka."

Ya fada yana mikewa, bayansa tabi da kallo tana sakejin wani haushin nasa tsabar masifa ta mai ciki...hka ma unty hanan take lol🤣

Fitowa yayi tare da mikar da ita tsaye sae hararsa taken shi kuma sae aekin sorry yake fadi dan yanzu yaga aboda take tak kawai take jira ta fashe, kayan jikinta ya cire mata ya fara kokarin cire nashi ta kalleshi tace.

"meye hakan? "

"wanka zamuyi."

"ah ah kaje part dinka kayi a toilet dinka."

Hannunta yaja suka shige toilet din yana gama cire kayan jikinshi, ta sake kallonsa tace.

"wae meye haka ka fita mana."

matsowa yayi daf da ita ya marairaice yace.

"plz habebbty let's do it, naji lafiyar babyna sae kinga in Allah yasa kafin gobe kin sauka, wllh I will be lonely for a while."

Ya karasa mgnr yana kissing wuyanta, kallon katon cikinta tayi wanda ya gama yin kasa gaba daya alamar ta kusa haihu, tana mamakin halin mahir da baya gaji da abu daya, gashi itama har ya koya mata jarabarsa tureshi tayi tana turo baki ta zauna baki bowel tace.

"ni marata ciwo take mini."

"tun yaushe yake miki ciwon?"

Ya fada yana kai hannunshi kan mararta ta.

"tun dazu."

"kin fadawa Teena? Me yasa baki fada mini ba?"

"ae ba sosai yake mini ciwon ba kadan kadan."

Ta fada in I don't care tune.

"amman luv kinsan mum tace miki duk abinda ke damunki ki dinga fada, kila you are having a contractions."

Harararshi tayi ta turo baki tare da fadin.

"idan haka ake contractions da kullum zan dinga haihu."

Janyota yayi suka shige cikin bowel na wankasae da sukayi hot romance kafin sukayi wanka suka fito yana tmbyr marar tace baya ciwo, tare sukayi sallar isha rigar bacci ya saka mata ya kwantar da ita tare da rage mata AC ya janyo mata duvet cover ya rufeta ya fita.

Yana fita ciwon Marar ya dawo, jin yarda ciwon ke dan mata yasa bata dauki abin serious ba saukowa tayi ta shiga toilet zatayi fitsari tana taugunnawa taga wani abu kmr mucus (gamsai) hade da jini, da sauri ta Mike ta mayar da pant dinta ta fito tana tada teena da ke kwance kan sofa tana bacci, ta fada mata abinda ta gani, teena tace.

"kwanta."

Cikin harshen turanci, ba musu ta kwanta, ta dauko safa ta saka ta fara dubata cikin sauri tace.

"you in the labor."

Hibba ta zaro ido cike da mamaki cikin ranta tace daman haka haihuwar take amma mata idan sukazo wajen su suke masu tumasanci nayi dariya nace hmm hibba kenan.

Guraren karfe 2 hibba ido ya fara raina fata tun tana yarfa hannu har ta fara kuka kuma har zuwa lkcn ba'a sanar dasu mahir ba, karfe 3 taji contractions ya fara zama unbelievable, ta fara sanin ba tumasanci mata keyi musu ba, ta dubi teena dake danna mata waist a wahalce tace.

"ki kirawo mini mahir wayyo mutuwa zanyi ki kirawo mum."

Ba musu teena ta danna kiran Mum ta sanar da ita then ta Kira mahir shima.

Su Mum na shigowa sukaga halin da hibba ke ciki sukayo kanta hannun Mum ta rike da karfi tana cije baki, dan mintina kadan ciwon ya tsaya ta kwanto da kanta kirjin mum bacci yana dauketa, ko minti uku batayi ba ta Fara tana Saki wani irin ihu, mum ta Kalli mahir da yayi tsaye ya rasa ma abnd zeyi kmr ba doc ba ta daka mishi tsawa tace.

"katsaya mana a kai kazo ka dubata mana."

Jikinsa na wani irin tsuma ya isa gaban hibbar yana ta6ata ta sake fasa wani kukan.

"sorry luv sannu baby."

Ya fada wane zeyi kuka, cikin kuka da bala'i tare da radaddin nakuda🤣tace.

"naki sannu bazanyi sorryn ba ni ba kagama cutata ba kullum cikin tale mini kafa kake Kana....."

Saurin toshe mata baki yayi da hannunta gudun kartafadi wata mgnr gaban mum, Abba ne yayi knocking Mum ta fito yabata wani tofin ayatul shufa'a da yayi mata da ruwan zamzam yace abata tasha, mum ta kar6a ta kaimata dakyar hibba ta kar6a tasha iyakar galabaita ta galabaita mahir kmr ba doc ba sam ya rasa me zeyi teena ce kawai keyin aikinta har kuka sae da yayi mata ganin har asuba hibba bata haihu ba yace kawai su tafi hospital ayi mata c.s Abba yace abari dae a gani.

Haka sukayita abu daya har garin Allah ya waye sae wajen sallar juma'a hibba ta haifi santaleliyar yarinyarta Mace katuwa tubarkallah zuwa lkc hibba batasan inda kanta yake ba domin har karata sae da akayi sbd tsabar girman jaririyar, kaf gidan tun daren jia babu wanda yasha ko da ruwa sbd tsabar tashin hnkl, teena ce ta fito daga dakin cike da farinciki ta sanar da Mum ta haihu mahir na ciki yana stitching hibbar, Mum cike da farinciki ta kira Abba dake part dinsa tasanar dashi kafin tashiga dakin hibbar tanajin kukan jaririyar ko takan yarinyar batabiba tayi wajen 'yarta da take ta sauke ajiyar zuciya ba damar kuka tsabar azaba, Mum ta riko hannunta cikin tausayawa tace.

"sannu daughter Allah yayi miki albarka Allah ya albarkanci abinda kika haifa."

Idanuwan hibba a lumshe bata iya budesu Mum ta matsa gaban jariyar da teena keshiryawa ta zubawa photocopy din mahir din ido taji wani irin farinciki na mamayeta.

mahir na gama dinkita ya riko hannunta muryarsa a dashe tsabar tausayi hibba ta bude jajayen idonta ta sauke a kansa yace.

"am sorry habebbty for putting you through such pain, Allah bazaki kara haihuwa ba, idan muna bukatar yara we will get surrogate mother amma ke kuwa bazaki sake wannan wahalar ba."

Kukan babyn yasa ya juya tare da amsarta hannun Mum yana ganinta kmr yar wata uku a hnkl ya furta.

"masha Allah."

Mum tace.

"what did she weigh?"

Mahir yace.

"4.5kg."

Mum tace.

"that's why ta wahalar mini da daughter wato a dole sae tazo ta kamoni a kiba to kwalelenta sae dea ta tafi kano can."

"wato har an fara kishi da matar."

Abba ya fada yana shigowa dakin.

Mum ce ta hau kiran su fareeda da najwa then ta kira gidan su hibbar daga nan ta fara sanar da fam dinta hakama Abba shima fam dinsa da abokanensa ya fara sanarwa mahir ma nan ya fara buge buge yana sanar da haihuwa, ko da ya sanar da anwar sosai yayi farinciki ya koma gd yana sanar da suhaila haihuwar hibba tsabar farinciki sae ga nakuda itama tun yana dauka wasanta ne har ta fara kokarin tara masa da jama'a dama mamy tana gidan nan suka dauketa sukayi asibiti da ita.

Su unty ramla ne suka shirya tafiya can yolar Mum tace basae sunzo ba zuwa gobe hibbar zata taho gida tayi wanka a gida, kafin kace me labarin haihuwar matar Dr mahir ta fara zagaye media tare da hoton jaririyar da na mum din ta da Dad dinta da aka pic-mix dinshi sae yadawa ake a media, labarin haihuwar har villa mummy nan ta sake kuka kmr zata hadiye zuciyarta.

suhaila mafa anci kwakwa babu karya har Allah ya sauketa lafiya ta haifi santalelen danta mai kama da ita sak

A tare akayi sunansu yarinyar hibba taci sunan mum Asma'u suna kiranta husna dan suhaila kuma sunan Dad din anwar bashir suke kiransa walid gagarumin bikin suna akayi a fabs wanda aka kashe mahaukacin uban kudi, washe garin suna aka wuce da suhaila kd ita kuma hibba tana gdn su duk da mahir bai so haka ba.





mun kusa gamawa insha Allah.



...share
...vote
...comments





Oum Afaf✍🏻
[10/30, 4:07 PM] +234 812 554 4850: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

💋💋💋💋💋💋💋💋
*NI DA DR MAHIR*
💋💋💋💋💋💋💋💋

Writing by
*HAFSAT BELLO*

_Follow me on instagram:_
*hapc20*






*Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un😭kullu nafsin za'iqatul mout, tabbas a safiyar yau ta talata zainab Aliyu gidado (Mmn Ammar)ta amsa kiran ubangijinta, zainab tana daga cikin babbar masoyiyar wannan littafi kuma tana daga cikin wadda nake alfahari da ita a masoyana, yh ubangiji Allah muna tawassali da kyawawan sunayenka masu tsarki da daukaka ubangiji Allah ka gafartawa wannan baiwa taka Allah kasaka a sahun masu shahada domin ta rasune ta hanyar haihuwa, yah hayyu ya qayyum ka rayamata abinda ta bari tare da sauran yaranta😭dan Allah duk wanda ya karanta page din yayi addu'a ga wannan baiwar Allah....😭👏🏻*




*_Second to the last page...📝_*

*🅿 40*

Satin hibba uku a gida ranar asabar da safe, bayan tayi wanka ta shirya cikin wata atamfa Mai kyau irin straight gown din nan ce mai katuwar tsaga daga baya, ga wuya yayi open shoulder ne kusan rabin wuyan a bude yake, rigar tayi mata dam ajikinta ga shi shape dinta ya fita sosae hips din nan kmr ya tsaga rigar, ragowar kumburin ciki duk ya koma sbd kullum wajen wanka sae umma ta danna cikin sosai wataran hibba har kuka take wajen danne cikin, fuskarta ta fara komawa normal duk wannan danyen na ciki dana ruwan zafi duk ya fara bajewa, duk da batayi wata kwalliyaba amma fuskarta tayi wani fayau tayi kyau, daurin zarah buhari ta kafa a kanta yayi da tayi tozo da dogon gashinta daga kasa, kamshi kawai take kmr ba me jegoba, hakama baby husna an shiryata cikin overroll ta yara tsananin kamarta da mahaifinta na sake fitowa.

Umma da taga sakawa yarinyar Kwalli ta tsala ihu take ta mikawa hibba ita tana cewa.

"ayi yarinya bata son Kwalli sae abar ido kmr danyen nama, ungu bata tasha."

Hibba dake selfie a wayarta tace.

"umma rabu da ita ba yunwa takejiba jijjigata zatayi shiru."

Husnar kmr taji abnd Maman tata tace ta kuwa sake tsala wani ihu.

ba shiri hibba ta ajiye wayar tare da amsata tana.

"nashiga uku ni hibba zata fasan kunne."

Umma ta fara hade kayan shirya husnar sae mita take.

Hibba ta dauki husna a kafada suka shige dakinsu ba tare da ta bata nonon ba amma tayi shiru, gefan katifarsu ta kwantar da ita kafin ta zauna tana zuge zip din rigar da yazamana na gabane, nono ta fara bawa yarinyar har tayi barci ta sata a kafada tayi gyatsa sannan ta kwantar da ita, itama barcin taji tanaji ta gyara kwanciyarta ba tare da ta zuge zip din rigarba ta kwanta sbd ta sake da rigar.

Mahir ne ya shigo gidan sanye da wani sky blue material na maza yayi kyau sosae, umma dake kitchen tana shirin hada girkin rana suka gaisa tace masa.

"kashiga ciki inaji barci suke dan banji motsinsuba."

keyarsa ya dan sosa cike da kunya yace.

"daman bama zama zanyi ba tunda barci suke bari naje kawai."

Umma ta kalleshi tasan sarai karya yake takanas yazo domin kullum yakanzo sau uku sau biyu a rana, umma tayi murmushi tace.

"kashiga suna ciki."

daga haka ta koma cikin kitchen din.

Mikewa yayi ya shiga parlon da sallama kafin yayi hanyar dakin hibbar, labule ya sake saki sosai ya rufe dakin sannan ya shiga wani daddadan kamshin turaren wuta dana hibba tare dana husna ne gaba daya ya gauraye dakin, sosai yake yabawa da irin tsaftar umma da ta hibbar duba dea kaji daki dama gidan yarda yake kamshi kmr ba mejego a gidan sa6anin wasu matan da zakaga idan suna jego wani mugun karni da suntun karoka zakaji sunayi daga su har babyn nasu mu gyara mata.

Idanuwansa bai sauka a ko ina ba sae kan Brest din hibba dasuke zundum zundum a cikin bra, kir yayi masu da ido wani yawu ya hadiye da karfi jikake Qut, a hankali ya matsa ya zauna gefan katifar, husna dake barci ya dauka ya manna mata kiss a kumatu a hnkl ya furta.

"good morning little princess."

Ya dade yana kallo yarinyar kafin ya dauketa ya zurata cikin gadonta mai dauke da net, komai yanayi a hnkl gudun kar hibba ta farka, kan katifar ga haye bayan hibbar, dai dai hibbar tayi wani juyi ya zamana Sun koma kallon juna, idanun mahir kmr zasu fado akan Brest din hibba, a hnkl ya kai hannu ya shafa tare da saurin janye hannunsa ganin ta dan motsa yasanta bata da nauyi barci sosai, sake kai hannunsa yayi Karo na biyu ta sake motsawa sosai yayi saurin janyewa, a Karo na uku kuwa hibba saurin damke hannun nasa tayi, mahir kuwa da sauri ya rufe idanunsa shi a lallai barci yake, ganin rainin hnkln da yayi mata yasa ta janye hannun nasa tare da juya masa baya tana fadin.

"ashema bacci yake...."

"baby Idona biyu."

Ya fada da sauri yana rungumota ta baya.

tureshi tayi tana mikewa zaune tace.

"wae meye haka hub? Kasan dea gdn nan ba kmr yola bane duk wani motsin da muke anaji."

Marairaice fuska mahir yayi kmr zeyi kuka yace.

"plz luv kadan."

Hararshi ta sakeyi tace.

"meye kadan? "

Da dan yatsa ya nuna mata mamanta yana wani langwa6ar da kai kmr yaro, ita hibba dariya ma ya bata ta dan dara cike da rainin hankali tace.

"meye wannan din?"

Ta karasa mgnr tanabin jikinta da kallo tana wani sake bankaro masa da kirjin nata, jikin mahir na wani rawa ya fincikota suka fada saman katifar yana kasa tana samanshi, suka zubawa juna ido tsanin sha'awarta hadi da soyayyarta ta hango cikin kwayar idanun mahir, mutsu mutsun tashi ta farayi ya sake damketa ta yarda bazata Iya kwacewa, lonely ya hade bakinsu waje daya tare da sakar mata harshensa kmr yarda suka saba, charaf ta kama harshen tana tsotsa kamar alawa har wani lumshe ido takeyi, shi kuwa sae shafe bayanta yake zuwa bombom dinta, Sun kusan 10 minters suna abu daya, kafin ya birkitota tayi kasa shi kuma ya koma sama yayi mata runfa, gaba daya ya fara fita daga hayyacinsa, a hnkl ya zura hannunsa cikin bra dinta, ta rike hannun da sauri murya qasa qasa tace.

"stop hub umma fa."

"baby kadan zansha dan Allah."

Ya fada yana sauke mata wani numfashin kasala a kunne, nan jikin hibba ya fara laushi, a hnkl ya ya fito da shi yana zurawa a baki kmr wani jariri🙈

hibba idanu ta lumshe tanajin wani dadi na ratsata.....

Ganin mahir na kokarin zarce iyaka yasa hibba ta dawo hankalinta ta fara turjewa, da karfi ta samu ta kwace kanta duk ta gigice tace.

"hub jegoba nake."

"kin warke ea jiya fa har sallah kinyi."

Ya fada yana kokarin kamota..

Ta matsa baya da sauri tana turo baki tace.

"amma wajen ea bae warke ba."

Husna ce ta fara mutsu mutsu tare da kanenen kuka, mahir zunbur ya mike ya daukota, yana kallon fuskar yarinyar yace.

"kinga kin tayar mini da ita ko?"

"kai ka tashe dea kuma ka rarrasheta."

Kokarin zuge zip din rigarta ta fara ya riko hannunta da sauri yana daurata a cinya yace.

"yi hakuri Abla(unty) bata tasha kar ta fara kuka."

"cema tayi yunwa take ji?"

"ehmn bari kuma kiji husnaty zakisha mama ko?"

Ya fada yana kallon yar kmr tasan me yace ta motsa kafa da hannu tana fadin inya🤣ya dubi hibba yace.

"kingani ko kar6eta hajiya ki shayar mini da ita."

A cinyarta ya daurata tare da dauko hannuta ya sa a bayan keyar yarinyar ya tankwashe kafarsa ya dago cinyar hibbar ya zura a karkashin kafarsa, sannan yasawa yarinyar no-no a baki tare da bismillah, hibba ikon Allah ta tsaya gani, kwanto da kansa kafadar hibbar yayi yana kallon fuskar yarinyar da yakejin kmr ya hadiyeta sbd so, sae da ta koshi sannan ya dauketa ya daura a kafada tayi gyatsa har ta koma barcinta ya kuma kai bakinsa ta tureshi tana mikewa ta mayar da zip dinta tare da daura dan kwallinta sae lkcn yaga kyawun da shigar tayi mata yabita da kallo kmr ze cinyeta, shima tsaye ya Mike yana gyara kayansa da suka danyi squeezing ya matsa daf da ita yana riko hannayenta cikin taushin murya yace.

"this dress is making me looses my mind."

murmushi tayi tare da daura hannunuwanta kan fadarshi tana kallonshi eyeballs to eyeballs murya kasa kasa tace.

"I love you."

Rungumeta yayi tsam a jikinsa yana fadin.

"I love you too hibbatullah...."








A hankali lokaci ke cigaba da tafiya yayin da wani aminci ke kuma shiga tsakanin familyn mahir dana Anwar, baka ta6a cewa wani abu yata6a shiga tsakanin Anwar da hibba dan ynz gaba daya anwar baya ganin wata mace a gabansa sama da suhaila.

Bayan shekara biyu dukkan family din suka sake samun karuwa wannan karon duk maza suka samu hibba ta haifi mujahid suhaila kuma muhsin.


Bayan shekaru goma.

Yanzu hibba yaranta shidda cif four boys nd two girls, zuwa ynz arzikin mahir yaci uban nada domin a ynz yana matsayin minister na lafiya gaba daya, ita kuma hibba ta zama cikakkiyar doctor, gaba daya ynz a Abuja suke yayin da mahir ya gina mata wani qatoton asibiti wanda shiyyar abroad ne mai suna *NI DA DR MAHIR specialise hospital*.

yayin da Anwar da suhaila ke da 3 kinds domin su family planning suke, ynz anwar ya zama cheps of justices, yayin da suhaila take zuba business sosai kasashe ake mata oder. Every part is happy.






A hankali take fitowa daga cikin gidan prison din bayan tsawon shekaru goma da tayi a ciki, sanye take da kayan gidan yarin, bayanta prisoner ne su biyu ke biye da ita, kanta a duke a kasa bata dagoba yayin da kafarta babu takalmi, a hankali aka shigar da ita wani daki mintuna kadan ta fito sanye da bakar a baya wadda aka kaita da ita, daya daga cikin prisoner baturi ta mika mata hannu tare da fadin.

"congrats dear today is free."

sae lokacin ta dago da kanta, wayatace tayi saurin faduwa na tarota da sauri kafin ta fadi ta fashe, Dr feena dan baiwa idanuwanta fal da kwalla babu Wanda zega feena yace classic Nafisa mai manicure, pedicure zuwa spa ce zata koma kalan tausayi haka ba, tsawon shekaru goma da tayi kullum cikin kuka take tare da nadamar abnd ta aikata a rayuwa take.

Hanya wannan matar ta nuna mata kmr an cire mata laka take takowa sae ganinta tayi a main gate, ko da ta dago kanta basu sauka akan kowa ba sae akan..........










share
comments
Vote










Oum Afaf✍🏻
[10/30, 11:41 PM] +234 812 554 4850: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

💋💋💋💋💋💋💋💋
*NI DA DR MAHIR*
💋💋💋💋💋💋💋💋

Writing by
*HAFSAT BELLO*

_Follow me on instagram:_
*hapc20*

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

*_Alhmdllh! Alhmdllh!! Alhmdllh!_*




~DEDICATED TO~
*P.M.L*




*🅿 41*

Kir tayi da idanunta akansu yayin da jikinta ya sake wani mugun sanyi, lallai duk wanda yace zeja da ikon Allah shine a wahala, duba kaga hadin Allah amma ni nake kokarin rabawa, sake kallonsu tayi da kyau suna sanye da wasu designer clothes pincil jeans blue nd black leather jacket komai nasu iri daya ne sae dea shi male ita female, idanu ta sake tsurawa kyakkyawar fuskanshi ido tayi da babu abinda ta karo cikin shekaru goma sae tsananin kyau da Hutu, zuciyarta ce taji ta kara mata nauyi hango zallar kwanciyar hankali a tare da jikinsa da fuskarsa da suka nuna, ga wata lafiyayyiyar kasumba da ya ajiye wadda ta sake kara masa wani sirrin kyau.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, tanajin danasanin fitowarta daga prison din, domin domin a ynz tana hango tazara mai yawa tsakaninta da mahir din tare da rashin dacewarsu tun da can baya ganin hibba makale a gefansa ya nuna cewa tunda can da ita ya dace ba ita ba, tabbas gangar jikinta da zuciyarta basu bar kaunar mahir da kishinsa ba.

Tunaninta ne ya tsaya lkc da mummynta ta rungumeta ta baya kmr an jefota tare da fasa wani irin kuka tana rukunkumeta kmr za'a kuma kwaceta a mayar da ita inda ta fito, itama feenar tsintar kanta tayi tana hawaye sae dea sam zuwa ynz bata da wani kuzarin yin kuka, dad ne yazo ya hadasu duk ya rungume shima yana Saki siririn kukan farinciki, duk wanda yaga fam din sae yayi mugun baka tausayi yarda suka rungume juna sosae kmr masu tsoron a rabasu suna kuka, mummy ta dago tana shafa fuskar yarta ta still tana kukan takaicin ganin first class beautiful girl dinta yarda ta zama, wani kukan ta sake fashewa da shi tana takaicin tarbiyyar da tayi mata ta itace sanadiyar shigar feena duk wannan halin da take cikin domin itace ta daurata tun tana yarinya kan wannan muguwar akidar ta nuna tafi kowa tare da isa izza da daukar mutum ba a bakin komai ba, share hawayenta tayi duk da wasu na sake fitowa muryanta na tsananin rawa tace.

"sorry daughter for...."

Feena ta saki kukan da ta dade tana rikewa, ganin halin da mummyn take kmr ba itaba duk ta wani tsufa sosai ta rame tayi wani baki

Please Login or Register in order to submit comment