Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yabita a hankali amma hakan basae taji sassaucin fitar budurci ba, ruwa mai dumi da ya tanada a flacks din tea ya zubo mata tare da bata wani magani ba musu tasha sannan ya dauketa zuwa toilet shi da kansa ya gasata sosae sannan yayi wanka ya fito itama tayi nata ta fito a hnkl tanajin raguwar zafin d gabanta keyi,mahir ya taugunna banta tare da riko hannunta yana cigaba da kwararo mata ruwan albarka tare da mata addu'a iri iri,hibba ta lumshe kumburarrun idanuwanta ranta fal da farincikin kawo budurcinta gidan mijinta duk da kasancewarta budurwar da ta dan jima ba miji amma hakan besa ta rasa budurcinta ba, jin addu'ar mahir yaki karewa harda ta shirme yasa ta bude idanuwanta tare da galla masa harara tana turo baki tace.

"ni ya isa haka ka isheni."

Dariyar da mahir ya dade yana dannewa ce ta kufce masa ya Mike yana dariya yana cigaba da mata addu'a turo baki ta sakeyi tana cigaba da hararanshi.





Tsaye take tsakiyar hadedden bedroom dinta daga ita sae pant da bra ta baza dogon gashinta har gadon bayanta, waqar Stanley enow ke tashi da karfi a dakin ita kuma sae rawanta take kamar wadda akace tayi za'a bata aword duk ilakirin jikinta sae shaking yake dama gata yar sukuta da manyan masakai tare da bombom, waqar ta canja zuwa sekem nan take rawa ta canja yarda take rawa kamar da ita akayi waqar Anwar da tun dazu yayi yatsaye baki kofa yana kallon ikon Allah wani juyi da zatayi sae ganin Anwar tayi tsaye ya zuba mata sleeping eyes nata.

Dariya tayi tare da kashe waqar a wayarta ta ta iso gabansa tare da fadin.

"yah Anwar yaushe ka shigo."

6oyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke tare da hadiye wani yawu yana sake kafe manyan boobs dinta da ido yace.

"kicigaba da rawarki mana."

Dariya tayi tare da rufe fuskarta da hannunta wae kunya, janyota yayi tare da daukarta tsam yayi bedroom dinsa da ita.




Watan su mahir biyu ana kwasar honey moon sannan aka dawo Nigeria a yola suka fara sauka sae da sukayi sati daya sannan suka dawo Kano duk yan uwa anzo anyi mata barka da zuwa.

Around 7pm hibba ce kwance kan cinyar Mahir tana sanye da arnan jordan half vest sae wandonshi, tayi wani haske sosae ga wata cika da ta sakeyi, yarda take yamutsa fuska kasan ba lfy ce da ita.

"sorry luv sannu."

Mahir ya fada cikin tausayawa domin tun jia da suka dawo kano take fama da ciwon ciki dana Mara,

"wayyo cikina."

Ta fada cikin Azaba tana damke hannun mahir din sosae.

Mahir mikewa yayi da sauri tare da kwantar da ita kan sofa din da kyau ya haye upstairs da sauri bedroom dinta ya shiga ya dauko mata doguwar riga da hijjab dinta ya fito yana rike da carkey, a kasan carfet ya sameta sae juyi take tana wani irin kuka, daukata yayi da sauri tare da Saka mata rigar sae sannu yake mata kamar zeyi kuka, ganin yarda ta galabaita yasa ya daga tsam tare da fito da ita compound din gidan sabon driver ya chillawa key din mota suka shiga tare da nufar prevet hospital dinsa, da kansa ya fara bata taimakon gaggawa tare da mata gwaje gwajen da ya dace gwajin farko ya gano cewa hibbar she's three weeks pregnant, tsurawa scaning machine din idanu yayi domin shi har ynz he can't believe he's becoming baba, da sauri ya juya yana kallon hibbar da take barci hannunta kan cikin nata a hankali ya daura nasa hannun kan nata yanajin wata zazzafar kwalla na cikin idanunsa cikin sanyi murya yace.

"we're are becoming parents."

Ya karasa mgnr hawaye na zubo masa tsabar farincikin da yake ciki, wayarsace tayi kara ya duba yaga Mum dinsa ce yayi saurin pick.

Gaisawa sukayi da Mum din sannan tace.

"ina hibbar bata wayar tun dazu nake kiranta bata picking."

"Mum hibba bata da lfy, muna hospital ma yanzu."

"subhanallah meke damunta? "

Shiru mahir yayi kunyar Fulani na taso masa Mum ta katseshi da fadin.

"kai dan kaniyarka banson shirun nan nace what's wrong with her? "

"she's three weeks pregnant."

Ya fada muryanshi a hankula.

Mum tayi saurin cewa.

"wow alhdmllh yh rabb alhmdllh ala kul ni'ima congrats son I can't wait to see grandson, yanzu meye matsalarta? "

"ciwon ciki kawai ke damunta dana mara."

"that's bad, son kamaido mini da ita nan kawai"

dasauri ya girgiza kai kmr tana ganinsa yace.

"mum she should not travel a long distance."

Mum tace.

"OK, then take very good care for her, yh rabb ya raba lafiya."

Hira suka danyi da Mum din kadan sannan sukayi sallama.......








Comments
vote
share






Oum Afaf✍🏻
[10/29, 12:16 PM] +234 812 554 4850: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*NI DA DR MAHIR*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*

_Follow me on instagram:_
*hapc20*






_Sakallahu khair my unty Hanan, ina mugun jidake unty kmr yarda nakeji da fairatπŸ€ͺ_





*πŸ…Ώ 38*

Wajen 10pm hibba ta fara idanuwanta suka sauka kan mahir da ke mata tausa, yabar wajen kafarta ya dawo saitin kanta yace.

"luv kin tashi sannu ya jikin?"

Ya fada yana kissing hand dinta.

Ya mutsa fuska ta danyi sannan tace.

"dasauki, meke damuna? "

Murmushi ya danyi yana cigaba da kissing hannunta yace.

"baby mun kusa zama iyaye."

Idanu hibba ta dan zaro cike da rashin fahimta tace.

"what do you mean?"

"I mean u are pregnant."

Ya fada a nutse fuskarsa dauke da annuri.

Idanu ta sake kwalalowa sannan ta kalli mahir din ta kalli kuma cikinta ta daura hannunta daya a kai tace.

"dagaske? "

Dasauri ya gyada mata kai yana murmushi itama murmushin tasaki sannan tace.

"am becoming a mother..."

Bata idda mgn ba ya katsata da fadin.

"and me a father."

Ya fada yana dariya.

Hibba tace.

"alhmdllh yh rabb ubangiji Allah ya albarkanci abinda yake ciki."

"Ameen super mommah."

Mahir ya fada in funny way.

Hannu ta daga ta dan dokeshi tana turo baki tace.

"sati nawa? "

"three weeks."

Hibba ta gyada kai farinciki fal fuskanta.

"yanzu what will you eat?"

ya fada yana kwanto da kansa kan pillown ta.

"tuwo."

Ta fada a takaice.

Ido ya zaro yace.

"tuwo Luv da daren nan?"

"yes miyar kuka da yajin daddawa."

Ta fada kmr zatayi kuka.

Shiru ya danyi for while kafin ya dauko wayanshi a aljihu ya kira driver ya sanar dashi yaje good restaurant ya sayo mata tuwo da miyar kuka ya hado da cheeps da shawarma.




6angaren iyayen feena kuwa gaba daya duk inda tashin hankali yake to suna cikinsa sbd kwata kwata basu da walwala ba irin hanyar da basubiba domin su samu yarsu ta fito amma beyuwu ba hakansa mummy kullum cikin kuka take tare da faffadawa president maganganun da taga dama kullum cikin tashin hnkl suke da rigima.




Three months later.

Su Suhaila da Anwar ansha amarcin soyayya kamar me suhaila sosai aka saba da rayuwar aure, anwar yana mugun kula da ita Tare da tarairaya ta mussamman, har ta koma sch alqalam duk weekend take zuwa Kano, yau Monday tun safe take kiran anwar akan yazo ya dauketa batajin dadi, hakan yasa babu shiri yataho kt daukarta tun a cikin mota zazza6i ya rufeta, anwar duk ya gigice kwantar mata da seat yayi ta kwanta har suka iso kano gida ya wuce da ita zazzabin na sake rufeta, family doc dinsa ya kira ya sanar dashi yazo ya duba masa jikinta ba'a jima ba doc yazo da kayan aikinsa.

Tana kwance jikinsa sae aikin sannu yake mata doc ya dubeta tare da fadin.

"sannu kinji."

Kai ta gyada masa kawai, tambayoyi ya fara yi mata tana bashi amsa yace.

"yaushe rabonda kiga period dinki?"

Kallon Anwar tayi sannan ta kalli doc din tace.

"na manta."

murmushi doc yayi yace.

"kai amarya kin manta lallai honeymoon yayi dadi."

Ya fada yana kallo Anwar, anwar dariya ya danyi yana murza hannun suhailar doc ya kuma cewa.

"well from all indication your wife is pregnant congratulation, duk da banyi test ba but symptoms nata na masu ciki ne, sae ka kawota hospital gobe na dubata sosai ynz zan dan bata paracetamol kawai zuwa goben insha Allah."

Anwar tun lkcn da doc yace ciki ne da suhaila yake murmushi fuskarsa dauke da wani irin annuri, suhaila kuwa cusa kanta cikin kirjin anwar din ta sakeyi sosai tsabar kunya, sallama sukayi da doc yana fita anwar ya daga suhaila chak ya fara wani juyi da ita yana zuba mata godia kmr ita tabawa kanta ciki, yana fada how much he love her, farinciki da murna ya ishi suhailar ta sake rungumeshi sosae tanajin wata irin kaunarsa na sake nunnunkuwa cikin zuciyarta.

granny ya fara sanarwa sannan ya kira mamy kusan mamy tafi anwar farinciki ma dan cewa tayi dole zata taho Nigeria a satin nan har sae suhaila ta haihu, wayar yabawa suhaila mamy tayi tasaka mata albarka, kafin ta katse wayar yana kokarin mayar da yawar aljihu tace.

"bani na kira ummata."

Ido anwar ya zaro yace.

"kice mata me? "

"nace mata to nima dae ina da ciki, am becoming a mama."

dariya anwar ya fashe da ita cikin dariya yace.

"wait hajia plz how old are you?"

Baki ta turowa tace.

"19 then"

"no wander."

Anwar ya fada cikin dariya, sae da yabata wayar takira ummanta har abbanta sae da ta kira ta sanar dashi sudae dariya kawai suke mata.



Bayan kwana uku.

Su anwar sunje an fada masu cikin suhaila ynz 2month kenan, baya sata wani wahala sam tun zazza6in da tayi bata sake wani ba sae yawo dan kullum sae sun fita, yau ma tana zaune saman kujera shi kuma yana kasa yana danna laptop ita kuma tana wasa da gashin kansa a dole sae tayiwa gashin kitso, sae jajjagula kan take tace.

"Baby yau ina zamuje ne?"

"babu inda zamu yau hutawa zamuyi."

Ya fada idanunsa kan system din.

dasauri ta duro tare da hayewa cinyarsa ta zagayo da hannuwanta ta wuyansa fuskarta dai dai tasa cikin shagwa6a tace.

"plz dear muje gidan su unty hibba kasan tunda suka dawo bamujeba kuma sunzo basu samemu ba muma muje kaga sae na fada mata ko? "

"mezaki fada mata?"

gira daya ta daga masa tare da nuna masa cikinta da ido.

Dariya ta bashi yayi murmushi tare da hade bakinsu waje daya.




Da yamma Anwar tare suhaila suka shirya cikin shigarsu ta alfarma sunyi kyau sosai kmr ka daukesu a wata sabuwar motarsa suka fito suka tafi gidan mahir din.


A compound din gidan anwar yayi parking sannan ya Kalli suhaila yace.

"princess shiga ki fito."

"au bazaka shigaba?"

"No."

Ya amsa mata a takaice.

mood dinsa ta kalla sae kuma ta basar ta fito tare da nufar kofar gidan tayi knocking, shuru ba'a budeba wajen minti biyar har ta gaji da danna door bell.

A lokacin hibba na kwance jikin mahir zazza6in yamma yana rufeta, yanajin knocking amma bayason ya Mike dole hibbar tasashi ya Mike.

Suhaila har ta juya zata koma mahir ya bude kofar ganin suhaila yayi murmushi yace.

"ah ah manya Ashe kece come in."

Yafada yana matsawa gefe murmushi tayi tana baya tsananin kyau na mahir cikin ranta saurin astagfirullah tayi sannan ta shige.

A parlour ta zauna suna gaisawa tace.

"tare muke da yah anwar yace baze shigo ba."

Mahir ya Mike tsaye yana fadin

"ah haba me yasa baze shigo bari Nashigo dashi kafin na kira hibbar, daman bata da lafiya."

Ya fada yana ficewa daga parlon.

A cikin motar ya hangi anwar zaune yana danna wayarsa, mahir yayi knocking glass din a hnkl ya bude motar tare da fitowa yana murmushi ya mikawa mahir din hannu suka gaisa mahir yace.

"mene kuma na tsayawa anan kmr wani bako plz kashigo."

Anwar yayi murmushi tare da fadin.

"okay."

Har cikin parlon suka shiga sannan ya shiga wata kofa dake karkashin stairs sae gashi a wani hadadden mini parlour mai dauke da wata dark ash cusion mai L, gefan kan hibba ya zauna tare da dagota yace.

"luv munyi visitors today suhaila nd anwar."

"dagaske? "

Hibba ta fada cikin farinciki, kai ya gyada mata yana riko hannunta, ta wata kofa yabi ya haye upstairs ya shiga dakinta tare da dauko mata Dubai jallabiya da vail ya kawomata ta cire kayan jikinta ya saka mata jallabiyar tare da yafa mata Vail din ya riko hannunta suka fito.

suna fitowa anwar idanunsa ya sauka kanta gani yayi ta chanja sosae tayi wani irin kyau da fresh alhmdllh sae yaji babu abnd yaji a tare da ita.

Suhaila da sauri ta mike tare da rungume hibbar cike da farinciki itama hibbar ta rungumeta.

Zama tayi gefan mahir suka gaisa da anwar cikin sakewar fuska tare da farincikin ganin farinciki Da kwanciyar hnkl a tare da su anwar din, hira suka farayi lkcn da masu aiki suka kawo masu drinks suhaila bakinta sae kaikayi bakinta yake ta fadawa hibba tana da ciki, mahir ya daura kan hibba saman kirjinsa dan yarda yaga tana nishi kasa kasa suhaila tace.

"yah mahir bata da lfy ne?"

Murmushi yayi yana kallon fuskar hibbar da ta lumshe idanunta kmr mae barci sannan yace.

"we're pregnant."

kusan a tare suhaila da anwar sukace.

"wow congrats."

Suhaila tace.

"nimafa....."

Anwar yayi yayi saurin rufe mata baki yana dariya, mahir yayi dariya tare da fadin.

"yazaka rufe mata baki kabarta ta fadi abnd ke ranta koh daughter."

Dariya tayi tare da rufe fuskarta jikin anwar din tana dariya, hibba cikin zafin zazza6i tace.

"wllhy suhaila baki da kunya."

Dariya suka sakeyi, lkcn sallahr magrib ne yayi mahir ya dauki hibba kamar baby yayi hanyar da suka fito suhaila ta kalli anwar tare da haraRarshi.

anwar yayi mata gwalo yace.

"ke kinyi lukuti da yawa ne ban iya..."

Bae idda mgnr sa ta janyo pillow ta jefa masa,yana dariya yace.

"menayi miki ne yar sukuta."

Pillow ta sakejefo masa ya kwace yana daria.

Mahir ya fito yaga suhaila najifansa da pillow shi kuma sae dariya yake yana kaucewa mahir yayi dariya yace.

"wanda akayi a gida bae isa ba sae anzo nan anyi mana."

Baki suhaila ta turo sannan tace.

"bashine yake cemini yar lukutaba."

dariya mahir yayi sannan yace.

"sorry daughter ki shiga ciki kiyi sallah."

Suhaila tana shiga ta tarar da hibba ta tada sallah bathroom ta duba sannan ta shiga itama ta dauro alwala, hibba na idar da sallah taja gefe akan sallayar ta hada kai da gwiwa domin ita Kadai tasan abinda takeji, suhaila na idar da sallah ta kalli hibbar cike da tausayawa tace.

"sannu unty hibba."

A hankali hibba ta gyada kai cikin jin jiki tace.

"yauwa suhaila yajikin naki kema? Kuna dae lfy da shi ko?"

Suhaila da duk jikinta yayi sanyi tace.

"ni bana ciwon komai unty hibba dan kmr ba cikine dani ba."

Kai kawai hibbar ta gyada mata tanajin wani amai na taso mata, dasauri ta Mike tayi hanyar toilet tana kakarin aman sae dea babu abnd ya zubo kasancewar babu abnd taci, suhaila tsaye kanta tana zuba mata sannu kamar zatayi kuka, murmushi hibbar tayi mata a wahalai kafin taji aman ya lafa mata ta Mike a tare da wanke bakinta ta fito suhailar tana rike da hannunta.


su mahir suna shigowa yashigo yayi kiransu domin har an jera dinner dinning, abinci mai yawa suhaila ta zage tanaci sa6anin hibba da babu abnd ya burgeta a wajen ta kwanta lamo tana kallon suhailar tanajin dama itace ke iyacin abinci haka, anwar ya kalli hibbar cike da tausayi sannan ya kalli mahir yace.

"bata Iya cin komai ne?"

"eh wllh da tana iya cin kwai da cheeps ynz kuma ma ta daena cin komai."

Ya fada a hankula.

"Allah ya qara sauqi."

Ya fada atakaice, anwar da suhaila ne kawai sukaci abinci, suna gamawa suka Mike zasu tare da masu sallama.









Oum Afaf
[10/29, 12:22 PM] +234 812 554 4850: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*NI DA DR MAHIR*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*

_Follow me on instagram:_
*hapc20*







*πŸ…Ώ 39*

Sosae hibba take laulayin cikinta domin ko ruwa tasha sae ta amayar, har cikin ya cika wata shidda, lokacin cikin ya fito sosae ga shi cikin kwata kwata ba sata kyauba tayi dan duhu duk da cewa kowa ya kalli fatarta yasan tanajin dadi amma hakan ba hanata dan duhu ba, hancinta ya zama kato ga wani kumburi da tayi sosae, kusan kullum ta kalli kanta a mirror sae tayi kukan ganin yarda ta koma haka mahir zae sata gaba yana bata hakuri tare da sake tabbatar mata da irin so da kaunar da yake mata.

Suhaila kuwa rai fas dan ita cikin ya amsheta sosae a ynz cikin watansa hudu ya dan fito kadan domin ita jikinta yabi ga wani haske da ta sakeyi sosai.

Kullum mum cikin mitar mahir ya kawo hibba take yau suka shirya zuwa yolar, karfe biyu na rana suka sauka, Abba lokacin yazo fita kenan yana zaune a bayan mota su hibba suka karasa suka gaisa Abba sosae ya tausayawa hibbar ganin halin da take ciki shi kuwa mahir wani kyau na musamman ya yaqara yayi wata irin kiba ga haskensa da ynz har kashe ido yake.

6angaren Mum sukaje, Mum na ganinsu ta taso cike da farinciki, hibba tayi saurin tsugunnawa kamar yadda ta sabawa mum din cike da girmamawa zata gaidata mum ta rikota da sauri tare da dagota cikin fada tace.

"karki sake wannan kneeling din bakya ganin halin da kike ciki karki sake banso."

Cikin girmamawa ta gaida mum din itama ta amsa fuskarta na fitar da tsananin farincikin da take ciki, masu aiki ne suka fara shigo da tsarabar da sukayowa mum din, mum ta Kalli mahir ta dan masa hararar wasa tace.

"ka kyauta mutumin kurum."

Mahir da yasan laifinsa a wajen mum din yayi saurin cewa.

"mum nifaba bani da lafiya bazan Iya doguwar..."

"karya kake bakayi kama da marar Lfy ba."

Mum ta katseshi da sauri tana kara daka masa harara.

Fuska ya dan marairaice ya kuma cewa.

"wolah mum bani da lafiya tmby luv ma kiji mum dan Allah nima ae bani da lfy ko?"

Ya karasa mgnr yana kannewa hibbar ido daya, tayi saurin dukar da kanta kasa ganin a gaban mum ne, ita kuwa Mum dariya ce ta kwace mata tare da daukar pillow ta cilla masa tana dariya tace.

"get out from my room."

Yana dariya ya fice.

Mum tace.

"mutumin kurum."

Hannun hibbar Mum ta kamo suka shige cikin bedroom din Mum ciki aka kawowa hibbar abinci, da taga masa ta zage taci sosae da miyar alayyahu, shima Mum mai aiki tasa takai masa nashi part dinsa, hibba na zaune kan sofar dakin Mum, mum ta gyara zama ta Kalli hibbar tace.

"yah jikin naki da fatan son yana kula dake yarda ya kamata?"

Hibba ta gyada kai alama eh.

Mum tace.

"hibba karki 6oyen komai ki daukeni a matsayin ummanki, remember amanarki aka bani ke kamar farida da najwa kike a wajena, karkiji kunyar fada mini abinda mahir yake miki wanda bakyaso ki fada mini dan banso ya zamana yana cutar da ke."

Hibba sosae taji dadin abnd mum ta fada wata sabuwar kirmar matar ta sake gani a idanuwanta, tace.

"Mum wllh babu abinda yake mini muna zaune lafiya."

Ta fada kanta kasa.

Mum cikin jindadi tace.

"good, haka nakeso daman, ynz inane yake miki ciwo?"

"babu ko ina mum just kasala nd ciwon kafa."

"wannan is normal soon komai ze wuce dear zaki zauna a nan gurina har ki haihu? "

Dasauri hibba tace.

"eh mum zanzauna."

Tafada tana danne dariyar ta domin tasan mahir zae ga uku idan ba ita yarda ya saba da muguwar jarabarsa.

Mum tace.

"shikkenan, ynz yi kwanciyarki ki huta."

Hibba tayi kokarin mikewa, Mum ta riko hannunta tare da nuna mata bed dinta tace.

"ki kwanta anan."

ba musu hibba ta haye gadon tare da lumshe idanuwanta tanajin kaunar mum din sosai cikin ranta, mum na fita parlonta taga mahir kwance kan kujera yana waya, mum ta doki kafarsa ya Mike zaune ta zauna kusa da shi a takaice tace.

"hibba zata zauna a nan har Allah ya sauketa lafiya."

Kutmar wolah baze yuwuba ya fada cikin ransa, a zahiri kuwa kusan kwarewa yayi da Lemon da yake sha ya ajiye gefen side table yace.

"mum idan ta zauna nan waze dinga dafa mini abinci? "

Harara Mum ta daka mishi tare da ware masa hannu tace.

"gidanku nace kaji mini dan banza da wa yake dafama abincin? Jinake da masu aiki ko restaurant ne suke hidima dake OK ynz ma na gane dan rashin imani Kana ganin yarinyar zama dakyar tashi dakyar amma dan ubanka Kake barinta tana girki."

"no mum to wai ma ita da bakinta tace zata zauna?"

Yafadan sounding out of word.

"nice nace zata zauna da magana ne?"

Idanu ya zaro domin sarai yasan halin mum din yace.

"kuma tace zata zauna?"

"kai banson iskanci tashi Ka fice mini daga parlour ."

Mum ta fada tana nuna mishi hanyar fita da sauri ya Mike yayi hanyar bedroom yanajin tana cewa karya shiga yatadata daga barci amma yayi banza da ita ya shige, girgiza kai mum tayi tanajin dadin saurin da ta gani a tare da dan nata.

A tsakiyar bed din ya ganta tayi daidai tana barcinta, hayewa kan gadon yayi ko takalmin kafarshi be cireba, hibba ta bude idanuwanta tana kallonshi yace.

"haba luv yazaki amincewa Cwthart zaki zauna anan bayan kinsan lalurata? "

Marairaice fuska hibba tayi tare da fadin.

"ya zanyi hub I can't say no wolah."

"you can't say no koh? To bari kiji yarda kika amince yasin haka zaki koma kice baki amince ba, inba haka ba yasin duk weekend ina nan kuma kinfi kowa sanin sauran."

Dariya hibba ta fashe da ita, cikin tsokana tace.

"gaskiya ni bazan Iya zuwa na fada mata haka ba, amma kai kaje Ka fada mata."

Ta fada tana mikewa zaune tana lashe lips dinta da harshenta.

"daman nasa wllh kekikace zaki zauna da ita, amma karki damu nasan maganinki."

Yafada yana kama bakinta, zare bakinta tayi da sauri tana fadin.

"meye maganin nawa?"

Takalmin kafarsa ya zare tare da hayewa kan gadon yana janyota jikinsa, ta fara mutsumutsu tana fadin.

"hub meye hakan wae?"

"kije kicewa Mum zaki bini gida just."

Ta fada yana zura hannunsa cikin rigarta, tureshi tayi tare da fadin.

"tashi muje karani toh."

Bamusu ya Mike ya dira daga gadon, ta mike sae da sukazo bakin door ta turashi da karfi tare da rufe kofar da sauri tana dariya, tanajin yarda yaja kwafa yabar wajen, ko da ya fito Mum bata parlon a main parlour ya ganta zaune da masu aikinta suna hira baki ya turo kmr yaro yana harbin iska Mum tabi bayansa tana dariya.



Washe gari.

Mahir yazo komawa kano kiri Kiri hibba taki binsa, ya kalli Abba fuska a marairaice yace.

"abba kana gani ko? "

Abba yayi murmushi yace.

"hajiya Asma'u kibarshi ya tafi da matarsa."

Mum ta kalli hibba da tayi kasa da kanta saboda kunyar abba tace.

"kibi mijinki hibba idan kinaso."

Hibba ta girgixa kai tace.

"mum zan zauna da ke."

Mahir ya kalleta da sauri kmr ze hadiye zuciya tsabar takaici mum tayi murmushi tacewa Abba.

"kadaeji abinda tafada da bakinta wahala yake bata girki yake sata."

Mum ta fada cikin dariya.

Mahir yayi saurin cewa.

"Mum wllh karya nake gata ki tAmbayeta wllh bata girki da kanta."

Abba ya dafashi yace.

"sorry son kabar Mum kasan halinta, kamar yau ne matarka zata dawo kaje Allah ya kiyaye hanya."

Kamar zeyi kuka ya mike mum tana dariya sosae tace.

"Allah ya tsare hanya son."

ko juyowa beyi ba Abba ya nunata da dan yatsa shima yana dariya kasa kasa,abba ne yacewa hibba taje ta rakashi mota, ba musu ta Mike tabi bayan mahir din.

Har ya shiga bayan mota ko kallonta beyiba sae da ya zauna sannan ya kalleta a hankali yayi mata alama tazo, ba musu ta zagaya ta shiga motar hannunta ya riko kmr zeyi kuka yace.

"yanzu baby ni zakiwa haka koh? "

Marairaice fuska tayi tace.

"ni kunya nakeji ban Iya cewa..."

Harararta yayi yana fadin.

"karki damu yan mata idan ma gudu kikeyi zaki dinga ganina duk weekend kina bani hakkina."

Dariya tayi tare da jan dogon hancinsa ta kai bakinta zatayi kissing dinsa ya kauda fuskanshi gefe yana fadin.

"malan hudu idan ja mota mu tafi."

Jin abinda ya fada yasa ta fita daga motar da sauri tana dariya, shi kuwa wani bakin spec ya dauko ya manna a fuskarsa driver yaja motar suka bar harabar gidan.



The following days

Mahir yana zaune a office dinsa, wayanshi tayi kara ko da ya duba dad din feena ke kiransa sae lkcn ma ya tuna da feena tun bayan yanke mata hukunci cikin girmamawa ya daga wayar tare da sallama.

Kuka yaji mummy ta fashe masa da shi tana fadin.

"yanzu abinda kayi mahir ka kyauta karfa ka manta duk abinda Nafisa takeyi tanayi saboda kai amma sbd kaddara ta fada mata shine ka wofantar da ita ka manta da ita sbd tsantsar butulci ko ka fada mini ka sakar mini 'ya ko kuwa?"

Ta fada cikin fada kuma still kuka take.

Mahir yayi shiru domin basan me zece ba, ran mummy ya sake 6aci a fusace ta sake cewa.

"wllh tir da

Please Login or Register in order to submit comment